murmushi ta saki tare da faɗin "ina son ganinirinrayuwar da Insu za ta shinfiɗa a gidanta" dariya me sauti ya saki tare da faɗin nima ya sumbaci
laɓɓanta murmushi ta saki tare da sumbatan na shi...
"Oh Allah my Jannah saura kaɗan in yi katoɓara" Farisat tace cikin nishin na sha da ƙyar, murmushi ya sakin mata tare da faɗin "kar ki damu Uncle wayayyene, ba abinda ze kawoaranshi" "duk da haka my Jannah, ita ma Insu da na ta lefin da ba se ta ankarar da ni da wuri ba" taidda maganan cike da takaici...
"A'a Kushi yanda ki ka ɗakko dogon bayanin nan ta ya za ta tsayar dake?" "Oh Yaa Allah" tacetare da tuno abinda tace, "zo wajen aljannarki babu wata damuwa" yace tare da miƙa matahannu, kamawa tayi ta haye jikin shi tare da haɗe fuskansu waje guda... Fuska cike da murmushi ya ajiye wayan ya dira daga saman gadon shi, ficewa a ɗakin yayi cikedanatsuwa kai tsaye ɗakin su Sahabee ya wuce, tura ƙofan yayi a hankali ganinsu kwance sunatakwasan barci hankali kwance ya sa shi jawo ƙofan a hankali ya wuce ɗakin Babiya, yana turaƙofan ya ganta zaune riƙe da waya a hannu, da mamaki ya shige tare da faɗin "Hajiya har yanzuba ki kwanta ba!" "Wani kwanciya zanyi Sadam? Yanzu ƙanwar ubanka Suwaiba ta dannominkira har na fara barci, wai Habiba ta yi ɓari, kaji fa tada zaune tsaye" ta idda maganan cikedadamuwa, "ciki kuma! Anty Habiban?" Yace cike da mamaki tare da neman waje ya zauna kusadaita....
"Wallahi har na fara barci, shine na ce mata dama Habiban ciki ne da ita? Wai ai ciwace-ciwacenda take tayi dama cikin ne ke sata, yanzu tsakani da Allah ina zan gano cike ne ya haddasamatahakan Sadam, matan da rabonta da haihuwa shekaru 20 da ɗori, to tunda ta haifi Zuwaira, datahaifi cikin jikinta ma wataƙila ɗiyar ta tasa yanzu, ina Habiba ina haihuwa a yanzu tsakani daAllah, shima dai Hamidun be dubawa kan shi ba, wannan ai abin kunya ne, tsakiyan ɗiyoyi dasarakunai ka zabgawa mace ciki" ... Murmushi ya saki tare da faɗin "to Allah ya kawo, za su ja da ƙaddaran Ubangiji ne, Hajiyawasuda shekarun da ya wuce na su ma son haihuwan suke Allah be ba su ba" "kayya Sadambanƙi takaba, ga waƴanda ba su haifa sun kuma haifa ba ko, amma ita Habiba wani haihuwa ne ba tayi ba,
maza uku mata uku, dan Allah ya ɗauki ɗaya ne ma yanzu suka koma biyar, ko Suwaiba waccetayi shekaru goma sha rabonta da haihuwa a mata fatan yi yanzu bare kuma Habiba da ta mantama ana wani haihuwa" "oh Allah Hajiya shikenan ya wuce ai tunda cikin ya ɓare" "ya fi gaskiyagunda da ya ɓaren hankalin kowa ya kwanta, ungo nan dama so nake in kira Farisat in sanar
mata da halin da ake ciki, ance mugun ɓari tayi ga ta can a asibitin Dimau kwance ana mataƙarinruwa da allurori, maza danna mata kira na sanar da ita, dan gobe fitan asubahi zamu yi" "to!
Subhanallah abun har ya kai ga asibiti!" Yace murya a sanyaye....
"Auh kai kana ɗaukan abun da sauƙi ne! Abun fa babba ne maza kira ta a sanar da ita" ta iddamaganan tare da tura mai wayan, amsa yayi ya nemi number ya danna kira, ringing biyutacafketare da faɗin "Hajiyan Allah kira a tsohon daren nan haka Allah ya sa dai lafiya!" Tace muryacikeda ɗan tsoro, "ba ni nan Sadam in mata bayani da kaina" Babiya tace tare da miƙa hannu, miƙamata yayi tare da bin ta da ido...
"Me ke faruwa ne!" Tace cike da shan jinin jikinta, "Habiba uwarku ce tayi ɓari da gabatowanyammacin nan" tace tare da gyara zama, "subhanallahi cikin ya zube!" Tace cike da damuwa, "auh kin san da maganan cikin ne!" Tace da mamaki, "eh mana Hajiya, Allah ya ba ta lafiya" "tokaji a she ni suka bari a duhu, da asubahin gobe dai zamu wuce, zuwa faɗuwan rana mu dawodanba zamu kwana ba, shiyasa na ce bari na faɗa miki in zaki se ki shirya mu wuce" "ai dole maHajiya, Allah ya kai mu" "to amen, in mun fito ma sanar miki" "to" tace jiki a sanyaye ta katsekiran....
"To ka gani ai an fita haƙƙinta ko" jinjina mata kai yayi tare da miƙewa a natse ya amshi wayanyasaka mata a caji ya ɗago bargo tare da faɗin "kwanta in lulluɓa miki" ba musu ta zame ta kwanta, "ki yi barci in sha Allah zata samu sauƙi" yayi maganan tare da lulluɓa mata bargon, murmushi tasakin mai cike da farin cikin kulawan shi gareta, "se da safe" yace tare da juyawa, "wajenAbdussamad zaka?" Tace tare da sakin hamma, "eh" yace ba tare da ya juyo ba, "to ka faɗamai
dan ina ga kafin ya tashi zamu wuce" murmushi ya saki tare da ficewa ya ja mata ƙofan....
Da sallama ɗauke a baki ya tura ƙofan parlorn side ɗin Yaya, amsawa Yaya dake zaune idonshi
akan tv yana kallon news yayi cike da kulawa tare da maida duban shi gare shi, murmushi yasakin mai ya tako a natse ya shigo ciki, zama yayi a natse tare da mai barka da hutawa, murmushi
ya sakin mai tare da jinjina mai kai ya juya duban shi ga tvn, haka suka cigaba da zama har akagama nunawa, murmushi Yaya ya saki tare da juyo da dubanshi kan shi tare da faɗin "ba kayi
barci ba?" Murmushi ya saki tare da jinjina kai, cike da taka tsan-tsan yace "eh yanzu nakesonzuwa in kwanta in sha Allah" "hakan da kyau, ya shari'ar ku ta yau?" "Da alamun nasara a ciki" yace a ladabce, jinjina mai kai yayi tare da faɗin "Allah ya tabbatar muku da shi"....
"Ku dage, ku zama kaifi ɗaya babu wani azzalumin da ze kasance a saman ku, nasara da cigabazasu kusanto ku, in ku ka yi haƙuri za su kasance abokan ku na kusa" "in sha Allah" yace cikedajindaɗi, murmushi ya sakin mai cike da ƙauna, "am yanzu muka gaisa da Uncle" murmushi yasakinmai tare da faɗin "kun kyauta ya jikin na shi?" "Da sauƙi sosai, ni aka barni ma zance ya warke" dariya ya saki tare da faɗin "Allah ya tabbatar da hakan" "amen, Anty Habiba tayi ɓari da
yammacin yau" "subhanallah!" yace cike da damuwa, "Anty Suwaiba ce ta kira ta faɗawa Hajiya, tana asibiti ina ga abin be zo mata da sauƙi ba ne, in Allah ya amince gobe zan bi su naga yanayinjikin nata" nagartaccen murmushi ya saki tare da jinjina mai kai, murmushi ya saki dan yasanabinda ya yalwata murmushin fuskanshi tare da miƙewa a natse ya sallame shi ya fice, dakallome cike da ƙauna ya bi shi har ya fice.... Ta ɓangaren Hisham kuwa cike da mamakin yanda SSB ya mai farin sani ya ajiye wayanshi agefen shi, abin ba ƙaramin mamaki ya ba shi ba yana cikin ƙoƙarin fiddo dalilin kira ya shigowayan shi, ɗauka yayi ya bi screen ɗin da ido, ganin heartbeat ya sa shi katse kiran ya maidamata da wani, tana ɗagawa ya zame ya kwanta tare da jan bargo ya lula duniyar masoya...
INSU 💘 SSB
Sunkuyo kan shi yayi yanda za su iya kallon juna, murmushi ta saki tare da ƙoƙarin kauda idonta, murmushi ya saki tare da faɗin "kun gama maganan ne da ki ka kashe?" Jinjina mai kai tayi anatse, "okay" yace tare da birkitota ta zauna daram a saman cinyoyin shi suka fuskanci juna, ganin yanda ta dibibice ya sa shi faɗin "kunyata kuma yau ki ke ji?" Sadda kai tayi da sauri, ƙoƙarin ɗago kan ya fara fuska cike da murmushi, kifa kan a ƙirjin shi tayi tare da ɗaura hannuasaman fuskanta, dariya ya saki me sauti cike da nishaɗi.... Ba yanda be yi ba ta ɗago fuska amma ta ƙi, ƙyaleta yayi ya bi ta da ido cike da tsan-tsansodaƙaunan dake taso mishi, jin ya daina ƙoƙarin ɗagota ya sata ɗago kan a hankali, caraf idonyasarƙe waje guda da hanzarin ta fara ƙoƙarin maida kanta, sauri riƙo fuskanta yayi tare da faɗin"ya isa haka Gorgeous" yayi maganan tare da zameta cike da salo ya kwantar da ita fuskantayakifu a saitin fuskanshi, ɗaukewa numfashinta yayi na wani daƙiƙu dan ba tayi tsammaninhakanba sam, "ba na son kunyan nan" ya yi maganan cikin asalin gaskiyan shi idon shi akan ta, sautinfitan maganan shiga maido da ita cikin hayyacinta, jinjina kai tayi tare da sunkuyar da kai ƙasa...
"Da wa Mairah ke kama ne?" Yace idon shi akan ta, "dani" tace a hankali tare da sakin murmushi, "a'a dani ne" yace cike da zolaya, ɗago kai tayi da sauri ta kalleshi tare da faɗin "dani takekama, lokacin ina shekarunta kaman mu ɗaya, tana girma kaman ze fito" tayi maganan cike da
yanayinta, girgiza kai yayi tare da faɗin "banga kaman ba ni" "ai baka da ido kai" tace cikedajinhaushi, murmushi ya saki tare da faɗin "ina ganin se Gorgeous ta bani aron nata" murmushi tasaki cike da nauyin abinda tace mai tare da faɗin "to dawa take kama?" Tayi tambayan
mamakinta na bayyanuwa....
"Dani mana" yace tare da bin yanda ta saki baki da ido ta bi shi da kallo me cike da mamaki, murmushi ya saki tare da saka hannu ya shafa saman goshinta zuwa haɓarta, riƙo hannuntayi dasauri tare da faɗin "ba ta yo kama da kai ba ko kaɗan, dubeta fa ka gani" tayi maganan taredanuna Mairah dake kwance tana ta kwasan barci da hannu, murmushi ya saki tare da faɗin"nagani kaman mu ɗaya" ɓata fuska tayi tare da faɗin "ta dai ɗakko ɗabi'unka na yamutsa fuskadarashin magana amma kama dani take yi" dariya ya saki me yalwa tare da faɗin "ni ne bana
maganan?" "Eh mana ba ka magana sosai, se dai ka jinjina kai ko ka bi mutumda ido" tayi
maganan cike da jin haushin ɗabi'an, rungumota yayi cike da nishaɗi tare da faɗin "oh YaaMalikka shirya ma Gorgeous mijinta ya dinga magana" murmushi ta saki cike da kunya tare da kaudafuska...
"Ban san ina yi ba wani zubin se Jabir ne kan faɗamin, amma saura bi na da ido kawai sukeahakan" yace cike da gaskiyan shi, "ɗabi'arka ce hakan, Anty tace tun kana yaro haka ka ke" guntun murmushi ya saki tare da faɗin "tasan yarinya na ne?" Ɗago kai tayi ta kalleshi taredafaɗin "sosai ma kuwa, ka manta tare ku ka taso" bin laɓɓanta dake motsawa yayi da ido kafinyace "ba ta san yarintana ba, ta dai sanni sosai" "ita ma kenan baka san nata ba?" Tace idontaacikin na shi, jinjina mata kai yayi fuska cike da murmushi, dariya ta saki me ɗan sauti taredafaɗin "wato baka so a ce an san yarintar ka ko?" Murmushi ya saki tare birkitata tayi ƙasa yakoma samanta "ke za ki yarda a ce an san yarintar mijinki?" Ɗaga hannu tayi a hankali ta shafi
kwantaccen sajen dake kwance a saman fuskan shi me haɗe da sirkin furfura ɗaiɗaiku taredafaɗin "in dai wacce ta sanin ta kasance Anty ne ba" murmushi ya saki tare da ƙasa da kanshi, baza mai ido tayi dan ganin inda ya nufa, murmushi ya saki tare da haɗe bakin su waje guda, wani aminataccen sumba ya kai ma laɓɓan cike da masifaffen ƙaunar dake fizgan zuciyanshi, ɗago ido yayi ya kalleta ganin yanda take bin shi da ido ya sa shi sakin mata murmushi ya yi
hitting ɗin fuskanta a natse ya yunƙura da nufin janye jikin shi, janyo shi tayi a hankali, bintadaido yayi kaman wani mara wayau, saka hannunta biyu tayi ta riƙo lallausan fuskan shi ta haɗebakin su, tare da lumshe ido, wani musulmin sumba ta kai mai wanda ya kwance mai notikanƙwaƙwalwanshi gaba ɗaya, be ankara ba se da yaji tana ƙoƙarin yanje laɓɓanta cafkowa yayi dasauri tare da sunfutan ta yayi gado da ita, yana shinfiɗeta ya miƙa hannu ya kashe glove ɗinɗakin....
Iya farantawa juna sun yi shi ba ƙarya a wannan dare, sunyi kuka tamkar ba za su tsagaitaba, sea wannan karon SSB ya tabbatar da kasantuwar shi cikakken namiji me cikakken lafiya, tundawan can karon baya cikin hayyacin shi, ta ɓangaren Insu ma abin zame mata sabo yayi danji tayi
tamkar a ranar ya fara faruwa da ita, se a yau ita ma ta fahimci kasantuwarta lafiyayyiyanmacewacce ta isa a kirata da sunan jinsinta, cicciɓanta yayi kai tsaye suka yi bathroom, gefenshoweryayi da su, ya danna ruwan ɗumi ya sakin musu, saurin shigewa jikin shi tayi ta ƙankameshi ƙamtare da sauke ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya, murmushi ya saki tare da jawota sosai ya haɗe goshinsuwaje guda idanunsu ya sarƙe waje guda, fayyacewa junansu sirrikan dake cikin ƙwayanninidanun junansu u suke a matse zuciya na gazgatawa gan-gan jiki na karɓa tare da marabacikedafarin ciki....
Se da suka ɗauki kusan 30 minute's a haka kafin ya kashe ruwan ya janyeta a natse suka nufi
gefen bathtub, zaunar da ita yayi a gefe inda chair's ɗin roba ke jere, fara haɗa mata ruwanzafi
yayi a natse, yana gamawa ya ɗauketa caraf ya saka a ruwan a hankali lumshe ido tayi sabodadaɗin da ruwan ya mata tare da zamewa ta kwanta a ciki, murmushi ya saki tare da bin tadaido, goge hawayen da suka zubo mai yayi saurin yi idon shi akan ta....
Ya gama cire tsammanin ganin wannan rana sam a rayuwa, ya haƙura ya fidda hakan a zuciyarshi
duk da tunanin hakan ya kasa barin shi, se ga Ubangijin shi gwanin adalci ya nuna mai a kusa, buɗe ido tayi a hankali ta sauke akan fuskanshi, murmushi ya sakin mata ba tare da ya kaudanashi ba, "ya salafce" tace a hankali cikin disashshiyar muryanta, lumshe ido yayi tare da kai hannuya taɓa jin yayi sanyi sosai ya sashi saurin danna madannin dake kwashe ruwan, nan da nanruwan ya soma bin kafofin dake gefen bahon wankan, kunna wani yayi idon shi akan ta, yanahayowa sama ta lumshe ido, shigewa yayi a hankali tare da jawota jikin shi, a tare suka saukeƙaƙƙarfan numfashi tare da lumshe ido....
Sosai suka gasa jikinsu, se da ya gamsu da ruwan ya ratsata sosai sannan ya fiddota ya haɗamusu na tsarki, tsarkake jiki suka yi a tare jan babban towel yayi ya fara goge mata jiki, jiyokukan Mairah ya sata saurin amsan rigan wankan da ya ciro dan saka mata ta zura a gaggaucetajuya da sauri da nufin ficewa, "ash!" Tace a hankali saboda zafin da ya ratsata, saurin riƙotayayi
tare da tambayarta lafiya a ruɗe, bin shi tayi da ido fuska cike da murmushi, ganin yanda
damuwa ya bayyana a saman fuskan shi ƙarara yasaya shafa fuskan tare da girgiza mai kai, juyi
sautin kukan Mairah na ƙara ƙarfi ya sata juyawa a hankali ta fice, bin ta yayi da ido cike datausayawa, shi da kan shi ya gazgata jarumtar ta a yau, saurin saka na shi rigan wankandayaciro yayi ya dafa mata baya a hanzarce....
Da sauri ta yi inda Mairah ke kwance tana yunƙurin miƙewa zaune, ɗagota tayi tare da kunnawutan ɗakin, "Ami" tace cike da samun sassauci dan fitsari ya tashe ta ta kirata ba taji motsintaba ga ɗaki dinɗim shiyasa ta saki kuka da ƙarfi dan a kawo mata agaji, murmushi ta saki taredafaɗin "duhu ne?" Jinjina mata kai tayi tare da bin ta da ido, "rabu da duhu" tace cike da kulawatare da zaunar da ita a jikinta, "lafiya kuwa?" Yace da sauri tare da zama kusa da ita ya amshi
Mairan, "Abie shi-shi-shi" tace da ƙarfi, bin fuskanta yayi da ido dan be gane me take nufi ba.... Saurin amsanta Insu tayi jin ta ambata har sau uku tare da faɗin "fitsarine ya matseta" ta iddamaganan tare da shigewa toilet, miƙewa tsaye yayi tare da bin su da ido, ba ta jima ba ta fitosaɓe da ita, miƙa mata hannu yayi tare da faɗin "saka kayan barci" ba musu ta miƙa mai itatakwashi kayan barcinta dake baje a ƙasa cike da kunya ta warware igiyan rigan wankan dakejikinta ta maida a natse, murmushi ya saki tare da wucewa ya shinfiɗe Maira, tana gama sakawata nufo wajen a natse, miƙewa yayi ya ba ta waje ya nufi saka na shi....
Yana fitowa ya hayo gadon komawa gefen Mairah ta baya tayi shi kuma ya kwanta ta gabasukasakata a tsakiya, ɗaura hannunta a saman na shi dake jikin Mairah tayi tare da sakin mai
murmushi, murmushi ya sakin mata idon shi akan ta, "zanyi barci" tace a hankali, "yi" yacebatare da ya kauda idonshi a nata ba, tura baki tayi tare da kallon shi, murmushi ya saki taredafaɗin "ba shi ki ke ji ba kenan" "shine mana" tace kaman zata saki kuka, maida dubanshi gaMairah yayi ganin ta koma barci ya sa shi zare jikin shi a hankali ya koma ta bayanta tare dabirkito Insu ta koma gabanshi shi ya koma bayanta, ya jawota jikin shi yayi sosai ya rungumetada hannayenshi biyu tare da faɗin "to yi barci" yayi maganan a dai-dai saitin kunninta taredasumbatan kunnin, lumshe ido tayi cike da yanayin da hakan ya haddasa mata... Haka sukayi luf ba wanda yayi barci a cikinsu ba kuma me ƙarfin motsa ko yatsa, "kin yayetane?"Ya jefa mata tambayan a hankali, jinjina kai tayi tare da sauke numfashi a hankali, "ba ta isayayeba ai Gorgeous" yace a hankali, "ita ta yaye kanta" tace a hankali, leƙa fuskanta yayi cike damamaki tare da fadin "sure!" Gajeran sumba wanda be kai tsayin second biyu ba ta kai mai alaɓɓa tare da sakin murmushi, murmushi ya saki tare da maida kan shi, "tayi baƙon dauroneshine ta daina sha" tace a hankali tare da sakin hamma, "okay" yace tare da zame hulandatasaka, "ki barshi a haka ya sha iska, tunda ba ki busar ba" yace cike da kulawa tare da shafagashin
da ya kwanta lub, a haka wani amintaccen barci ya kawo musu ziyara ya ɗauke su cak ya luladasu wata duniya wanda ba kowa ke iya zuwanta ba se wanda ya yarda gajeriyar kalman nanaidofaɗinta ya cika duniyar ciki da wajen zuciyar shi, (asuba ta gari Ammi da Abbien Mairah😌)....
Yamutsa fuska tayi tare da miƙa hannu a hankali ta cafko Mairah dake ta gwale mata idodantatashi, tunda ta samu tayi sallahn asuba a daddafe ta koma gado, ko azkhar ɗin idar da sallahcikin barci ta kammalashi, shiko SSB ba ta san lokacin da ya dawo ba, ta dai san shi ya tashetayakaita toilet tayi alwala ya ba ta hijab ta saka ya fice, dariya Mairah ta ƙyalƙyace da shi taredafaɗin "Ami" "barci, mu yi barci" tace a hankali ba tare da ta buɗe ido ba, "good morning matar
Sahabee" SSB yace tare da sunkuyar da kanshi akanta ya sumbaci goshinta da laɓɓanta, "morning mijin Insiyyah" tace tare da buɗe ido ta baza mai, murmushi ya saki tare da janhancinta ya zauna a gefenta, "kin san wani abu?" Yace tare da jawota jikin shi, girgiza kai tayi
tare da kallon shi, "ina sonki" yace tare da sumbatan idonta, "I know" tace a hankali tare daɗagakai ta sumbaci laɓɓanshi, murmushi ya saki tare da shafa saman kumatun ta....
Lumshe ido tayi alamun wani barcin take san komawa, "a tashi haka sarauniyar barci 11:20" yayi
maganan a natse tare da ƙoƙarin ɗagota, buɗe ido tayi da zallan mamaki ta miƙe zumbur tazauna tare da zaunar da Mairah dake jikinta, murmushi ya saki tare da bin ta da ido, "da gaske!" Tace tare da kallon shi fuska a shagwaɓe, jinjina mata kai yayi tare da faɗin "yanzu aka tasheni, shiyasa na ce a tashe ki kema" ya idda maganan tare da nuna mata Mairah dake ta bin sudaido, sauka tayi da sauri tare da faɗin "zan shiga school 12 ashhh" ta kai ƙarshen maganan taredwrumtse ido saboda zafin da ga kai ma ƙwakwalwanta ziyara, "ina ga yakamata ki ƙara shigaruwan nan" yace tare da miƙewa ya riƙo hannunta, murmushi ta sakin mai tare da girgiza kai cikeda dakiya tace "zan shiga a can, bari in hanzarta kar time ya wuce" tana idda maganan ta juyatayi bakin ƙofa, fasa kuka Mairah dake bin ta da ido tayi tare da ɗaga mata hannu alamunzatabi
ta, dawowa tayi ta ɗauketa ta fice da sauri, kauda kai yayi daga bakin ƙofan da ya bi su daido....
Tana shiga ɗaki ta ajiye Mairah a saman sofa ta wuce toilet, a gaggauce ta watsa ruwa ta fito,
ɗaukanta tayi ta koma ta wankota tas ta fito, jan stool tayi ta fara shafa lotion da sauri, tanagamawa ta zari tissue ta goge fuska ta wuce dressing room, ba ta jima ba ta fito sanye da lacewhite an golden riga da zani yayi masifar amsanta, wuyan nan ya ji sarƙa golden se ɗaukanidoyake, haka kunni, hannu sanye da farin agogo da awarwaro da zobe me ɗaukan ido, ta kasheɗaurin da ake kira da ture ka ga tsiya, gashin da ta tattara ya zuba ta baya, wuce wa gabanmirrortayi ta sanya nostril fari me adon apple, ɗaukan oil perfume da body spray tayi ta wanke jikintada shi, murmushi ta saki tare da ɗaukan lotion Mairah ta wuce inda take.... A hanzarce ta shafa mata ta goge mata fuskan ta tsaidata ta ɗaki kayanta da ta fiddo doguwar
riga me matuƙar kyau maroon colour ta sanya mata hula ta ɗauka maroon ta sanya ma, "iyyenba" tace tare da zaunar da ita, takalmi me sauƙin tudu ta saka mata ta matse belt ɗin jiki yandaze kama ƙafan tsam-tsam, tsaidata tayi ta wuce ta ɗakkota oil perfume ta shafa mata, maidawatayi ta wuce dressing room a hanzarce ta fito goye da jakanta me suffan cat ta ɗauki Mairahtasaɓa ta fice, fitowanta yayi dai-dai da isowan SSB ƙofar ɗakin, bin shi da ido tayi cike da yabakwalliyan da yayi...
Sanye yake da dakakkiyar shadda white me walwali wanda taji ɗinkin zamani, kan nan kamar koyaushe sanye da bugaggiyar hula me ɗaukan ido, ya ƙawata adon da duk wani abu da ya daceajikin shi, murmushi ta sakin mai tare da faɗin "kayi kyau" murmushi ya saki tare da amsanMairahdake ta miƙa mai hannu tare da faɗin "kin ma ƙwalliyar kyau sosai" murmushi ta saki me faɗi
tare da bin shi da ido, "muje" yace a natse tare da riƙo hannunta, "bari in ɗakko phone ɗinaaɗakin ka" tace tare da ƙoƙarin wuce wa, "yana tare dani" yace tare da fara takawa riƙe da
hannunta, yana ɗaga ƙafa take sauke na ta a natse....
Tun kafin su bayyana a idanunsu Hajiya dake zaman jiran fitowan su ƙamshin turarukanjikinsuda ƙaran takunsu ya isko kunnuwan su, baza ido suka yi zukatansu na fatan ganin abinda
zuciyoyinsu ke burin gani, lumshe ido Hajiya tayi lokacin da suka bayyana a idanunsu taredafurta "Alhamdulillah" hawaye na bi yo kuncinta, miƙewa Yasmin tayi da sauri tare da faɗin
"sannun ku da fitowa" murmushi ya sakin mata tare da bin ta da ido, "Mahmah kin tashi lafiya"
Insu tace a ɗan kunyace, murmushi ta saki tare da faɗin "lafiya lau Insu ya kwanan Mairah?"
"Alhamdulillah" tace tare da zare hannunta a na shi tayi inda Hajiya ke zaune ta na bin sudaido....
"Hajiya shine kin jini shiru ban sakko ba ba ki nemi ba ko?" Tace tare da shagwaɓe fuska, murmurshi ta saki me yalwa tare da faɗin "na san hutawa ki ke, bana son takura miki" murmurshi ta saki tare da faɗin "kun tashi lafiya Hajiya ya ƙafan?" Murmushi ta saki cike dakulawa tare da faɗin "Alhamdulillah" murmushi ta kuma saki tare da miƙewa ta koma kusadaYasmin....
"Muje dining" tace mata da kulawa, "ina sauran maciyan?" Tayi maganan tare da juyawa sukawuce ita da Yasmin, "sun zo ba ku sakko ba suka tafi amma sun ce za su dawo zuwa jimawakaɗan" jinjina kai tayi tare da jan kujera ta zauna, ƙarisawa kusa da Hajiya yayi ya zauna anatse, murmushi ta sakin mai tare da ɗaga hannu ta damƙi hannun shi, "na cire rai da ganin wannanrana, se ga shi Allah ya nuna mun da idanuna da kuma lafiyata, na yi matuƙar farin ciki daganinku yau, ka riƙeta amana, kar ka sake ka saki hannunta har abada duk rintsin da rayuwazata zo da shi" jinjina mata kai yayi cike da tabbatarwa tare da gaidata, "Alhamdulillah zamanjiransakkowan ku dama nake, tunda kun sako na kuma ga lafiyarku zanje in miƙe kaɗan, jinjinamatakai yayi ya miƙe tare da faɗin "ina son shiga office yau in sha Allah" "hakan ya kamata, Allahyabada nasara, ya sa a shiga a sa'a" "amen" yace tare da yunƙurin miƙewa, "zo Farisatu" tacetareda miƙa ma Mairah hannu, ƙanƙame shi tayi tare da kwaɓe fuska, "jeki ba
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 82 Chapter of 109