da sauri ta kama fuska washe damurmushi, "ki je ki kwanta gobe zaki shiga school 8:00am" tayi maganan tare da wuce waupstairs cike da takaicin zantukan su....
Jinjina kai Nafisat tayi tare da miƙewa ta sallamesu ta wuce bedroom ɗin ta, lumshe ido SSByayi
bayan ta ɓacewa ganinshi tare da ɗagowa daga jinginan da yayi a jikin kujeran da yake kai, "meke faruwa?" Yace a hankali, zayyano mai komai Kamil yayi zuciyanshi na zafi dan se yanzurainin hankalin da suka yi ya bayyanan mai a fili, kallon Yasmin yayi cike da kulawa tare dafaɗin"ki na da ƙarfin gwiwan tunkararsu?" Jinjina mai kai tayi tare da goge hawayen da suka zubomata, jinjina mata kai yayi a natse tare da faɗin "to ki cire tsoro, ki ne mo jarumar da aka kiraki
da shi ki sakawa kan ki" jinjina kai ta kuma cike da samun sassauci daga damuwar da takedako
tun daga ranar da aka rabata da sanyin idaniyanta...
"Muna tare dake, muna kuma goyan bayanki" Alhaji Munnir yace cike da son ƙarfafata, murmushi ta sakin mai cike da jin daɗi, "Allah ya ba ki nasara, in sha Allah ke ce a sama" Kamil
yace cike da farin ciki, nan kowa ya shiga tofa na shi albarkacin bakin, "Hajiya ba ki ce komai ba" A'isha tace tare da kallon ta, murmushi ta saki tare da faɗin "na ce A'isha ina ta faɗi a zuciya, inata sa mata albarka" murmushi suka saki saboda gane akan wa take magana tare da bintadaido, miƙewa Alhaji Jamil yayi tare da umurtan Sa'eed da ya miƙe su tafi, ba ja ya miƙe a natsesukasallame su suka fice... Nan kowa ya ɗau harama kafin wucewan wasu mintoci duk sun watse, sallama Lamunde tayi aɗarare ta shigo cikin parlorn, amsawa Hajiya tayi da mamaki tare da bin ta da ido, "dama baki
tafi ba har yanzu Lamunde!" Ta jefa mata tambayan idon ta akanta....
Jinjina mata kai tayi cike ds girmamawa tare da faɗin "me gida ne yace in zo kafin in wuce" kallon SSB dake jingine da jikin kujeran da yake kai Hajiya tayi tare da buɗe baki da zummanmagana, "gobe ki samu Jabir ze baki saƙo" jinjina kai tayi jiki a mace tayi godiya duk da batasanwani kalan saƙo ba ne ta miƙe ta sallame su ta fice.... Kallon shi Hajiya tayi da mamaki, murmushi ya sakin mata tare da kauda kai, "yakamata kajekakwanta" tace cike da basar da tambayan da take son yi mai ganin kaman be so, murmushi yasakin mata tare da bin ta da ido, murmushi ta saki tare da faɗin "a iya sanina jarumi ne kai bansan lokacin da ka zama rago ba" lumshe ido yayi ba tare da yace komai ba, miƙewa tayi a natsetare da faɗin "ko wani tsoro da fargaba tunkararsu ake da ƙarfin zuciya dan a kawo ƙarshensu, komawa nesa ka tsaya ba ze baka mafita ba, ka je ga iyalanka suna matuƙar buƙatanka a kusada
su" tana kai nan ta wuce a natse, bin ta da ido yayi har ta shige bedroom ɗin ta kafin ya lumsheido ya juyo a hankalin sauke idon shi da ya buɗe yayi a kan matakala, se da ya fi ƙarfin minti 20yana zaune idon shi a wajen ya rasa wani kalan tunani ma ze yi, ganin zaman ba mafutandazebashi ya sa shi miƙewa a natse ya nufi wajen a hankali kaman me koyon tafiya, taka stairs ɗinyakea hankali kamar me gudun wani yaji shi....
Yana idda hayewa ya sauke idon shi a bakin ƙofar bedroom ɗinta, tsaye yayi ya rasa madafadaabin yi, banda bugu da ƙarfi ba abinda zuciyan shi ke yi, juyawa da duban shi kan ƙofar bedroomɗin shi yayi a natse, takawa yayi a hankali ya nufi wajen, tura ƙofan yayi a natse ya shige ...
Ta ɓangaren Insu kuwa da takaicin su Kamil ta shiga ɗakinta, ajiye Mairah a saman sofa tayi tawuce dressing room, ba ta jima ba ta fito sanye da kayan barci riga da dogon wando me kauri dataushi se hula me raga da ta saka akanta, hannu riƙe da kayan barcin Mairah doguwar rigamaranauyi, zama tayi a natse ta fara cire mata na jikinta, tana gamawa ta sanya mata wanda tafiddota ɗau wanda ta cire matan ta koma da shi ciki, shafa musu oil perfume tayi a jiki ta ɗauketasukayi gado, kwantar da ita tayi ta jawo wayanta ta nemi number Salwa ta danna kira ta saka aspeaker ta rage volume ta bi Mairah data miƙe ta yo jikinta da ido....
Tana ɗagawa ta can tayi saurin ɗaga mata sallama, amsawa tayi cike da jin daɗin jin muryantatare da faɗin "se naji batun komawa bakatatan" murmushin takaici ta saki wanda Insu ta kiyoshi
rangaɗaɗau tare da faɗin "ni ma haka naji shi, banda shirin komawa yanzu samwallahi Insu, kiran Yaya yayi wai Nabil ya faɗi da keke yaji raunika sosai, shine Yaya yace in shirya mazagobein koma" "oh uncle Kabir shi dai yace kawai yayi missing ɗinki yana son ki dawo, amma bandaabinshi Nabil ɗin su kaɗai ne a gidan, ina ce suna tare da ƴan aiki" "rabu da shi, ai ze sanyamunhakan" "a'a ayi haƙuri dai, in aka duba ta wani ɓangaren ma da gaskiyan shi, tun ran fridayfaki
ke nan, ai kin jima" "haba Insu yaushe rabon da in zo in daɗe wai, ina zuwa nake komawa innadaɗe ne in yi sati, in na yi ƙorafi yace yara, dake ni ce aimata ai dole in zauna kar in yi zumunci
saboda yara, wallahi na gaji" ta idda maganan a ƙufule...
"Oh Yaa Allah kar dai kina kan tsini na kira, please ki yi haƙuri komai ze wuce ya zama tarihi, wallahi nan gaba in aka ce mai ma ya baki lokaci ba iyawa ze yi ba, komai yana tafe ne a tsari, karki damu ki shirya ki koma goben, ki nuna mai ki na jin maganan magabatan ki"....
"Shikenan Allah ya kai mu" tace a hankali, "yawwa jirgin ƙarfe nawa za ki bi?" "Wallahi bansani
ba, an dai bincika ɗazu sun ce se kusan 3 jirgi ze tashi, to ban sani ba zan bi su ne ko zanjirajibi inbi na safe se dai uncle Harun ya dawo" "ki ƙoƙarta ki bi na ukun, sannan kafin ki tafi yakamataki
zo ku yi sallama da Hajiya za ta ji daɗin hakan" "shikenan Allah ya kaimu" "amen, ina Anty
Lailahn?" "Gata" tace tare da miƙa mata wayan....
"Insu tun ɗazu nake san kiran ki Allah be amince ba" tace cike da jin daɗin jinta, murmushi tasaki
tare da faɗin "Allah ne be amince ba Anty Lailah ya gida ya aiki?" "Alhamdulillah ya wannanabuda ya bijiro mana bakatatan kuma?" Murmushi ta saki tare da faɗin "Alhamdulillah"....
"Kai Insu munga abu a anguwanmu yau, mu muka ga tashin hankali da idanun mu, bakinsangidan Alhaji Aminu Chanba dake nan anguwanmu ba?" "Eh" tace a natse, "wallahi nan matasananguwa suka ma dirar mikiya da makamai munana, ba dadin Allah yasa Yaya Sahabee ya yi
magana ba, da ba musan yanda abin ze kaya ba, Allah dai ya taƙaita, haka aka ce duk matasananguwanni summa gidajen ƴan siyasan anguwansu dirar mikiyan nan" tavidda maganancikedarazana, "kai subhanallahi Allah ya tsare dai" "sosai kuwa" tace cike da tuna tashin hankalindasuka shiga....
"Komai ya wuce Anty Lailah ki daina damuwa a irin wannan abubuwan dan Allah" "damuwadoleInsu mutum ai be san sanda yake shiga damuwan ba, ke kinga abinda suka dinga yi ne kuwa!" Taidda maganan a razane, dariya ta saki tare da faɗin "to yanzu dai ai sun tattafi, dan Allahaƙaraba Anty Salwa haƙuri" "daina kawo mun batun ta ma Insu, ina ce ita dai ba ta da hankali ko?Totaje tayi ta aikin taɓaɓɓu, mutumin nan in ba ta gode mai ba ba zata tsine mai ba, duk wani abuinya faru ta tambayeshi kai tsaye yake amince mata duk da sanin wacece mahaifiyar shi da gutsiri
tsomanta"...
"Haka ze rufe ido ya ji komai ya dake, hakan kuma be sa ya musguna mata ba, se ita da yakamatata dinga toshe ƙofofin matsalolin ita ke buɗewa, ni banga lefin shi ba ma in yace ta dawo, ai yayi
ƙoƙari ina ce satin da ya wuce ta zo, sannan wannan ma ta dawo, in zata zauna ga waje nanbame hanata, se dai wallahi ba ruwana sannan ba zan tausheta akan ta tafi ba, tayi duk abindatakeganin shine dai-dai, masu buƙatan inda take faɗin da takura suna da yawa, wallahi in ya mataadalcine tayi wata be shigar da wata ba" ta idda maganan cike da takaici....
"A dai yi haƙuri Anty Lailah, dole ki taushi zuciyanki ki taushe na ta" tace da damuwa, "a'aInsuai
ƴaƴa sun fi wannan powern, tun ɗazu da Yaya ya kirawo ya mata maganan nake tausantatanabotsewa, amma gashi ai ke da ki ka mata magana ta amsa miki, manta da batun ta ke, kinsanYaya Hassan ya koma kuwa?" "Komawa kuma!" Tace da mamaki murmushi ta saki tare dafaɗin"yanzu ba daɗewa ya kira ni yake sanar da ni"....
"Wai ya samu kiran gaggawa jiya bayan rabuwan mu, da ya bincika ya tadda akwai jirgindazetashi da safe kawai ya yanki ticket" "ikon Allah! Ina ga Hajiya ba ta sani ba, ba ta mun magananba" "eh amma yace be daɗe da kiranta ba, bayan ya kirata ne ya kirani" "to Allah ya sa dai kiranna lafiya ne" tace a hankali tare da cire hannun Mairah dake san ɗaukan wayan....
"A'a alheri ne, yace akan aiki ne" jinjina kai tayi tare da waigawa da idonta bakin ƙofan da akabude da sauri me cike da mamaki, sauke ido tayi akan SSB da ya shigo a natse sanye da kayanbarci se zuba ƙamshin shi yake me taushi, sakin baki da ido tayi akan shi cike da zallan mamaki, "abie" Mairah da ta kai nata duban kan shi tace cike da farin ciki, "se na kira ki" tace a hankali
tare da zame wayan ta katse kiran ta ajiye a bedside drower ta zame ta kwanta tare da janblanket....
Takowa a hankali yayi ya iso bakin gadon, miƙawa Mairah hannu yayi a hankali zuciyan shi nabugu, saurin miƙa na ta tayi cike da farin ciki, ɗaukanta yayi ya sakata a ƙirjin shi lafewa aƙirjintayi kamar wata kuliya, lumshe ido yayi yana me amsan yanayin da hakan ya zo mai da shi....
Tsayin mintinan da be san ko nawa ba ya ɗauka a tsaye idon shi a lumshe, duk da rawandaƙafarshi da jikin shi ke yi hakan be sa shi neman wajen zama ba, ganin Mairah tayi barci yasaInsu faɗin "zamu kwanta" sauke ƙaƙƙarfan numfashi yayi ba tare da ya damu da goge hawayenda ya gangaro mai ba ya tako a hankali ya shinfiɗeta a gabanta, ɗaga hannu a hankali yayi yashafi kumatunta tare da jan hanci.... Nan ma tsayin mintuna ya kasa cire hannun, ganin kusancin da hakan ya ba su yana ƙoƙarincutar da ita ya sata faɗin "barci nake son yi" "meya hanaki yi?" Yace a natse murya ƙasa-ƙasa, juya kwanciya tayi ba tare da tace mai komai ba, "Insiyyah!" Yace a hankali, wani dummƙirjintaya bada dan ba ƙarya yanda ya kira sunan ya shige ta, jin ba ta amsa ba ya sa shi sake kiransunanta a hankali, "na'am" tace a hankali ba tare da ta juyo ba....
"Ba kyason kallon fuskan Uncle yanzu ko? Haushi shi ki ke ji ko Insiyyah?" Ya idda maganancikinfidda harafin ha ɗin ƙarshe wanda ya tsargama Insu dake kwance luf tana sauraren shi, zagayawa ta inda fuskanta yake yayi ya duƙawa a gabanta tare da faɗin "Uncle yayi lefi megirmawanda ba kowa ze iya yafe mai ba, se dai yana da tabbaci akan Insiyyarshi ba zata gaza yafemai
ba, gani a duƙe a gabanki ki yi ma Uncle haƙuri ki yafe mai lefukan shi" ya idda maganancikedanatsuwan shi, jin tayi shiru ba tace komai ba kuma ba tayi wani hoɓɓasa na cewa ba yasa shi
sakin guntun murmurshi tare da miƙewa a natse ya fice a hankali... Goge hawayen da suke tsere a saman fuskanta tayi tare da miƙewa zaune ta bi ƙofan da ido, itafa ba abinda ke mata ciwo se saka hannun da yayi a takardan amincewa raba aurensu babuwani
dogon tunani, maida dubanta ga Mairah dake miƙa tayi tare da fara shafa kanta a hankali, wani
ƙaƙƙarfan kuka ne ya kuɓuce mata, saurin damƙe bakinta da hannayenta tayi tare da shigar dakanta tsakanin gwuwoyinta, dan motsin da zuciyanta ke yi yafi ƙarfin ta iya dannewa, hakatasharɓi kukanta a natse, se da ta gamsu dan kanta sannan ta ɗago da kan ta baza ma Mairahdaketa kwasan barci hankali kwance ido.... Ringing ɗin da wayanta ya fara ya sata ɗauke idonta akan tare da miƙa hannu ta ɗakko wayan, ganin haɗakan kira ya sata saurin goge hawaye tare da sai-saita muryanta ta ɗaga ta karaakunni tare da ɗaga musu sallama, "ba dai har kin yi barci ba!" Salman yace da mamaki a muryanshi, murmushi ta sakin mai tare da faɗin "na dai fara" "kya fara mana" Farisat tace cike datakaici, murmushi me sauti ta saki tare da faɗin "yanzu se ace na yi lefi ko?" "Eh mana kin yi, amfasanarmiki da za'a yi kiran" Yasmin tace murya cike da murmushi....
"Rabu da ita Yasmin ta na ƙaryan mantuwa ne" Farisat tace a ƙufule, "to na ɗauka an fasa ne" tace tare da kare hamma, "mu kar ki tsaya jan mana zance haɗa mu da wanda muke sangaidawa" tace a ƙufule, "a huce haka malama ƴar jarida" Sadam yace tare da sakin dariya, "wallahi takaicinta yawa ne da shi, ba daɗewan nan fa Yasmin ta tabbatar min da ta ƙara faɗamata" "to ayi haƙuri dai, ina uncle Shureim ban ji yo shi ba" tace tare da sakin murmushi, "yanakimtsawa yanzu ze fito" Yasmin tace cike da jin daɗin kulawan da ta nuna akan shi, "to shikenan
Hajiya ƴar jarida ki haɗa kiran da Hisham" "to ina Uncle ɗin?" Tayi tambayan da alamunsamunsassauci daga fushin da take...
"Yana ɗakin shi bari in kai mai" "bangane yana ɗakinshi ba! Ki na nufin ba ɗaki ɗaya ku kekwanaba ma!" Salman yace da mamaki, "Allah ya kyauta" Farisat tace cikin ko in kula, murmushi
Yasmin ta saki tare da faɗin "ko network ɗin be jonaka da ita ba ne?" "Tana ji fa" Farisat tacecikeda tabbaci, "Assalamu alaikum yau kuma zumunci ake ji" Hisham yace murya cike da murmushi, "dan Allah kar ku rikata mana waje, Hisham kana ji ba, Uncle zamu gaida da jiki yanzu, Insutashi
ki kai mai" "to Mommy" Hisham yace cike da shaƙiyanci, "hmm" tace ba tare da ta ƙara wani abua kai ba, "to ku jira zan ƙara accepting ɗin kiran" tace tare da fidda kanta daga kiran.... Numfashi me sauti ta fesar tare da ƙure Mairah da ido, ganin tana jan musu lokaci ya satasaukeajiyar zuciya ta zura ƙafafunta a ƙasa a hankali ta sauka, cicciɓo Mairah tayi ta saɓa a kafaɗatagyara zaman kayan jikinta da kyau ta ɗau wayan ta juya a natse ta fice daga ɗakin...
Jiki a mugun sanyaye ya koma bedroom ɗin shi, be hango sauƙi ko kaɗan ba tattare da ita, besanme ze yi ba kan shi ya gama kullewa, tunanin shi ya tsaya waje ɗaya cak, Hajiya gani takeabinnada mugun sauƙi shiyasa tayi magana kai tsaye, amma shi kaɗai yasan abinda yake hangowaaidonta da muryanta, zama yayi a kan sofa ya ɗaura hannunshi a saman fuskan shi yana tunanoshuɗaɗɗun shekaru, "Yaa Rahim sa'idni" yace a hankali ƙwaƙwalwanshi na taka burki daganemamai mafita zuciyan shi na bugun tsoron abinda ze iya biyo bayan shirunta, a wannan yanayintaturo ƙofan ɗakin a hankali baƙi ɗauke da sallama, a firgice ya ɗago kai ya zuba ma ƙofanbirkitattun idanun shi, saurin kauda idonta tayi dan ganin sarƙaƙƙun abinda ke cikin na shi idon.... Miƙewa zumbur yayi tare da ƙarisa inda take tsaye da sauri ya miƙa hannu, ba shi Mairahdabata
san wainar da ake toyawa ba tayi a hankali, ƙarisawa saman gado yayi ya shinfiɗeta a hankali
cike da taka tsan-tsan, ganin yanda yake komai da taka tsan-tsan ya sata kauda kai daga garesutare da saddawa, miƙewa yayi a hankali tare da zube mata ido, jan rigar jikinta ta fara dantayi
mugun tsarguwa, murmurshi ya saki tare da takawa ya isa kusa da ita, riƙo hannunta yayi anatse, saurin ɗago kai tayi ta zube mai ido, murmushi ya sakin mata tare da fara takawa da ita a hankali
suka shige ciki, zaunar da ita a saman sofa yayi ya duƙa a gabanta, kamo ɗayan hannunyayi yanabuɗe baki da zumman magana kuka ya ƙwace mai.... Ɗaga kai sama tayi dan son maida nata kukan, se dai ya kasa dannuwa, ambaliya kawai hawayeke yi a saman fuskanta, nan take jikinta ya ɗau ɓari, tsagaitawa yayi jin yanda ƙafafunta dahannayenta ke ɓari tare da jawota ya rumgumeta ƙam-ƙam, fashewa da wani ƙaƙƙarfankukatayi wanda ya haddasa ma Mairah motsawa, "na wahala?" tace da ƙarfi cikin rishin kuka laɓɓantana ɓari, "na jigata, na yanke tsammani, duk a cikin shekaru biyun nan da suka shuɗe, ji nakekullum dama na mutu na huta, na gaji da jiran zuwanka, na gaji da gizon da ka ke mun daganesa, na gaji da zuwa mun a cikin mafarkai da ka ke, shin me na yi maka haka da zafi Uncle da kakasabani gurbi ko kaɗan a rayuwarka? Ni ban nemi soyayyanka ba, bance ka soni ba, ka barni dawanda nake maka kaɗai ya isheni kammala ƙanƙanin rayuwata da kai, amma ka kasa Uncle, kakasa gane dakon da miskiniyar zuciyata ke yi, kullum son fahimtar da kai nake se dai ka rufezuciya da idanunka daga gani, ba zan iya kishi da wacce ka ba wa zuciyarka ko nuna rashinjindaɗina ko na second guda ba, dan ita ta bani kyautanka, sannan ita ce garkuwan da ke tsayedanba wa rayuwata kariya, dan Allah ka ba ni masauki ko kaɗan ne in raɓu zan iya jurewa, ba zanyi
ƙorafi ba" ta idda maganan cikin rishin kuka.... Ƙara ƙanƙameta yayi tare da faɗin "waya ce miki ban buɗe miki zuciyana ba?, Ban bar kowacceƙofa a ƙulle ba, na buɗe ƙofofinta gaba ɗaya dan ki shiga ta inda ki ke so, ba ki da shamaki dawannan, ba ƙaramin masauki ba, gaba ɗaya filin wajen naki ne ke ɗaya, kar ki yi mamaki idannace miki gangar jikin Sahabee da zuciyarshi na ki ne, ke ɗaya na mallaka wa, ban aikata hakandanabinda ki ke tunani ba, na aikata ne da fatan samun aminci da farin ciki a gareki da rayuwar dazaki yi nan gaba" ya idda maganan hawaye na gangaro mai ta gefen kunni, ɗaga kai tayi dasauri
tare da zube mai ido, jinjina mata kai yayi cike da tabbaci, girgiza kai tayi tare da faɗin "bani dawani farin ciki matuƙar baka tare dani Uncle, kai ne cikon farin cikina" tayi maganan taredaƙarafashewa da kuka....
Ƙanƙameta ya kuma tare da faɗin "shiii, ba zan ƙara aikata hakan ba, ba zan ƙara bari ki yi nisadani ba, ke ce cikon nawa farin cikin, ina sonki Gorgeous, ke ce ƙarfin gwiwata, ke ce SahabeeSadam Ɓadamayya, kar ki ƙara ambata min kalman rabuwa in na iya jurewa na farko ba lallai iniya jurewa na biyu ba" ya idda maganan tare da matseta, ɗaga nata hannayen tayi ta matseshi daƙarfi kaman me gudun wani ya ƙwace mata shi, haka suka sharɓi kuka hankalinsu kwancebameƙarfin zuciyan hana ɗayan shi, se dai wannan karon kukan ya ban-banta da na farko, danwannanna farin cikin jin abinda MUGUWAR TSOKA ke kitsa musu ba gaskiya ba ne, sun ɗau zancenƙanzon kurege na MUGUWAR TSOKA sun kasa tsayawa su saurari gaskiyan zukatansu yandayakamata.... Rurin wayanta ya sa su sakin juna, bin ta da ido yayi a natse, murmushi ta sakin mai tare daɗaukan wayan a hankali, ganin Hisham ne ya sata zare ido, da alamun sun gaji da jiranta neyasasuka wakiltashi ya kirata, in dai zata faɗi gaskiya ta mance da abinda ya kawota ɗakin ma, "lafiya!" Yace da kulawa tare da matsawa jikinta sosai ganin ta ja riƙe da wayan har kiranyatsinke ba ta ɗaya ba, jinjina mai kai tayi tare da sakin mai guntun murmushi.... Murmushi ya sakin mata tare da juyo da ita ta fuskance shi da kyau, "me ya faru!" Yace a natse, "su Farisat, oh su Yaya Sadam, oh" se kuma tayi shiru tare da sadda kai, murmushi ya saki taredafaɗin "un hum?" "Suna son gaidaka ne" ta ce a hankali,murmushi ya saki tare da faɗin "okay"
jinjina mai kai tayi ta amshi kiran ta saka a speaker, "gaskiya Insu ba ki da kirki ko kaɗan, kinsanmuna zaman jiranki amma ki ka shanya mu kaman wasu marasa abin yi, ke game miji kintafi kinbanzaci lamarin mu ko" Farisat tace a ƙufule, murmushi ta saki tare da sadda kai, murmushi yasaki tare da jawota jikin shi a natse ya amshi wayan ya ɗaga musu sallama, zare ido Farisat tayi
ta can tare da kallon Salman da ya zare na shi idon, murmushi Yasmin SadamShureimdaHisham suka saki dan ba ƙaramin kunya suma suka ji ba....
Shiru duk suka yi ba wanda ke da ƙarfin gwiwan magana a cikin su, Insu kuwa banda dannedariya ba abinda take, murmushi ya saki tare da faɗin "Hajiyata ba kya kusa ne?" Zare idotakuma tare da kallon Salman, jinjina mata kai yayi fuska cike da murmushi, "ina kusa Unclekanalafiya? Ya ƙarfin jikin?" Ta jero tambayoyin a kunyace, murmushi ya saki tare da faɗin
"Alhamdulillah ya aiki? ya gida kuma?" "Alhamdulillah Uncle Allah ya zamtoshi kaffara a gareka""amen Hajiyata" yace cike da farin ciki, "Uncle an wuni lafiya?" Salman yace a natse, "Alhamdulillah, Daddy ne?" Yace a natse, "a'a mijinta ne" Yasmin tace a kunyace, murmushi yasaki tare da faɗin "Salman ko?" "Eh Uncle ya sahan jikin?" Yace cike da farin cikin ganeshi dayayi, "Alhamdulillah ya aikin? Ya family?" "Alhamdulillah Uncle Allah ya ƙara lafiya" "amen nagode" yace cike da farin ciki....
"Mommy!" Yace a natse, "na'am Uncle kana lafiya?" Yasmin tace a kunyace, "AlhamdulillahMommy ya aiki? Ko har yanzu karatu ake?" "A'a na fara aiki shekara ɗaya kenan, ya jikinnaka?" Tace cike da jin daɗin kulawanshi gareta, "Alhamdulillah, Allah ya ba da nasara" "amenUncleAllah ya inganta maka lafiya" "amen" yace cike da jindaɗi, "ga shi zaku gaisa" tace a kunyace, tunda ta faɗi haka ya gane wa take nufi, "barka da dare Uncle" Shureim yace a natse, "barka dai
Mejor" yace fuska yalwace da murmushi, murmushi ya saki shima tare da faɗin "ya ƙarfinjikin?"
"Alhamdulillah" yace a natse, "Allah ya ƙara maka lafiya me albarka" "amen, ya Daddynka?"
"Yana lafiya Alhamdulillah" "a gaidamin da shi da kyau dakyau" "in sha Allah Uncle mungode" murmushi ya saki ba tare da yace komai ba....
"Ina Daddyn nawa?" Yace a natse, "gani Uncle ka wuni lafiya?" Sadam yace cike da farinciki, "Alhamdulillah Daddy ya aiki?" "Alhamdulillah Uncle ya ƙarfin jikin?" "Alhamdulillah" yaceanatse, "Allah ya ƙara maka lafiya me albarka da nisan kwana me amfani, takwaranka da Umar
sun ce a gaidaka" "amen-amen, ina suke?" "Sun yi barci" yace a natse, "to ina amsawa, idansunafree se ka kira ka haɗa ni da su" "to in sha Allah Uncle" yace cike da jin daɗi, "madallah" yaceanatse....
"Ga Hisham nan zaku gaisa" yace a hankali, "an wuni lafiya Uncle?" Hishamyace cike da
girmamawa, "lafiya ƙalau Hisham ya makaranta?" Da mamaki yace Alhamdulillah ya ƙarfinjikin?" "Alhamdulillah" "Allah ya ƙara maka lafiya" "amen, ka dawo cikin school ɗin ko tukunnadai?" Murmushi ya saki tare da faɗin "ina cikin school" murmushi me faɗi wanda suka jiyosautinshi ya saki tare da faɗin "to Allah ya temaka, ku dage da karatu, wannan shekarannadagiya ne, dalilin da yasa aka buƙaci ku dawo cikin school kenan, kuskure ɗaya ze iya wargazamuku nasaran da ku ke hange" "in sha Allah Uncle" yace cike da jin daɗin kulan da ya nunamusu, "to Uncle mun gode" Salman yace a girmame, "to ma sha Allah" yace tare da miƙa ma Insuwayan, amsa tayi a hankali ta katse kiran....
Comments fans🥰🙏
🫀MUGUWAR TSOKA 🫀
{🫀TA'ARE KALLUƊE}
[Muscle Cramp🫀]
) عضلة سيئة (
🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
written and Created ~~~~~~~~~~~~~~ ِبسم الله الرحمن الرحيم
By
Yardajjiya👩 💻
Page. Fifty two
Murmushi Yasmin ta saki tare da kallon Shureim da yake sakin na shi murmushin cike da jindaɗi, "na jiyo murmushinta tana cikin farin ciki sosai" tace cike da jin daɗi, murmushi ya saki taredafaɗin "ni ma naji, shima Uncle yana cikin farin ciki"....
"Allah yasa abinda muke tunani ne ya faru" tace cike da fata idonta na tara ruwan hawaye, murmushi ya saki tare da ɗaukanta cak ya ɗaura a saman cinya tare da faɗin "ina fatan hakanni
ma, zan so ganin rayuwa me cike da ma'ana"
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 81 Chapter of 109