Share this page
na gayyan ƙiwiya" tacefuska cike da murmushi tare da miƙewa ta nufi bedroom ɗin ta.... Da murmushin magananta a saman fuska ya juya ya nufi dining area, ajiye ma Insu abincindatazuba mata Yasmin tayi tare da saurin jan mashi kujera, zama yayi a natse tare da ajiye Mairahasaman dining table ɗin, "me za'a saka?" Tace cike da girmamawa, "yau ke aka bari da aikin?" Yacea natse, murmushi ta saki tare da faɗin "ba su ji fitowanku ba ne shiyasa, ka ga na samuladaai" murmurshi ya saki tare da faɗin "samun abinda ki ka sa mata" zaran plate tayi a natse ta zubamai farfesun kayan ciki da mango juice kamar yanda ta saka ma Insu, murmurshi ya sakinmata tare da bin ta da ido, juyawa tayi da zumman barin wajen, "Mahmah ba zaki yi breakfast ɗindamu ba ne?" Insu tace tare da kallonta a shagwaɓe, juyowa tayi fuska cike da murmushi taredafaɗin "munyi na mu tun ɗazu" jinina mata kai tayi ta maida hankali ga abincin gabanta.... "Wannan yayi min yawa rufe wannan mu ci wannan" yayi maganan idon shi akan ta, kallonsakanni ta mai ka fin ta zari plate ta rufe ta miƙe ta koma kujeran dake kusa da shi tare daɗaukan cokali ta zura a plate ɗin tana ɗibowa ta kai bakin shi cike da kulawa, murmushi yasakinmata tare da buɗewa a hankali, zuba mai tayi cike da taka tsan-tsan, lumshe ido yayi a natseyana amsan ɗanɗanon da hannun dake ci da shi ya zo mai da shi.... Zaran tissue tayi ta goge mai gefen baki bayan ta fiddo cokalin, ɗibo wani tayi ta nufi bakinshi, riƙewa yayi ya juya dashi zuwa na ta bakin, amsa tayi fuska cike da murmushi, ɗibo kaɗantayi takai bakin Mairah dake ta bin su da ido, amsa tayi a natse, haka suka ci da juna da cokali gudasuka shayar da juna da kofi guda, suna kammalawa suka ja kujera suka miƙe suka yo cikinparlor, a lokacin idonsu ya sauka akan su Jabir da suka shigo babu daɗewa, dakewa suka yi suka fuskekamar babu abinda ke ɗawainiya da su a zuci, murmushi Jabir ya saki tare da faɗin "morningguy's" murmushi Insu ta saki tare da kauda kai kamar ba ta ji me yace ba.... Wuce wa SSB yayi ya zauna rungume da Mairah cike da fuskewa, murmushi Jabir ya saki taredabin su da ido cike da farin ciki, "Abban Iman ina Anty Lawiza?" "Gani" Lawiza da ta shigo tacecikeda girmamawa, "Anty Lawiza yau rowan kan ki ko ke mana!" Tace tare da kama haɓa, murmushi ta saki tare da faɗin "a'a ban yi tunanin kun sakko ba" "to zan tafi school Mairah na wajenku" tayi maganan tare da isa gefen da Alhaji Munnir da Abubakar suke, zama tayi ta gaidasu da girmamawa amsawa suka yi da na su girmamawan, "auh ni ne bw za'a amsa gaisuwata bako?" Jabir yace tare da sakin murmushi, kauda kai tayi tare da wucewa inda SSB ke zaune, "my phone"tace da kulawa idonta akan shi, zarowa a aljihu yayi ya miƙa mata, amsa tayi ta sakko da jakandake goye a bayanta ta saka ta maida a hanzarce, duƙawa tayi ta sumbaci goshin shi da naMairah ta juya da sauri ta nufi ƙofa, murmushi suka saki gaba ɗayansu tare da bin ta da ido.... Shiko gogan bin ta yayi da ido cike da wani masifaffen ƙauna dake fizganshi, kukan Mairahdatabi Insu da ido har ta fice ya dawo da shi cikin natsuwan shi, sauke ƙaƙƙarfan a jiyan zuciyayayi tare da juyota ya rungumeta tsam-tsam, "dama nasan za'ayi haka, Ibrahimamsheta ka miƙawaLawiza maza ta miƙa mata ita kafin ta wuce" Alhaji Munnir yace tare da kallon Lawiza, ƙarisawaIbrahim yayi da sauri ya miƙa mata hannu fashewa da wani kukan tayi tare da ƙanƙame SSB, "tofa" Abubakar yace tare da sakin murmushi, "ɗauketa ba zata zauna ba fa" Alhaji Munnir yacecikeda tabbaci, miƙewa SSB yayi tare da faɗin "ta miƙa ma Yasmin ita" yayi maganan tare da miƙamaIbrahim ita.... "Ba zata zauna ba fa" Jabir yace tare da kallon shi, "ta saba, ba zata dinga zuwa school da itaba" yayi maganan tare da wuce wa, saurin dafa mai baya suka yi a hanzarce.... "Jama'a zako a je wannan waje? Abinda aka ce tun asuba za'a fita gamu har kusan 12 na rana" Babiya tace cike da takaicin jiran da suke tare da kama haɓa, kallonta Suwaiba tayi cike dasanrarrashinta tare da faɗin "ta kusa isowa Hajiya, in sha Allahu yanzu zamu tafi" "ah to, in anfasatafiya ne a faɗa min in cire rai, amma a ce tun ɗazu na kashe ma yara hidiman gabansu natasasua gaba ina ƙare musu kallo, inda haka ne ai da na bar kowa ya tafi na shi wajen" sallamandaGude tayi ya hana Jummai da ta buɗe baki da nufin magana cewa komai, dafo mata baya Halimatayi baki ɗauke da sallama.... "To gata nan" Suwaiba tace tare da sakin murmushi, "ku yi haƙuri" Gude tace cike da damuwatare da bin su da ido, "haba Gude, haba dan Allah, tsakanin ki da Allah kin kyauta mana kenan! Ki shanyamu dan uzurinki ke ɗaya, ance ayi fitan wuri a dawo da wuri amma kin shanya mukamar wasu marassa abin yi" Babiya tace cike da takaici, murmushi ta saki tare da faɗin "dan AllahHajiya amun afwa, har na fito Yayan Daddynsu dake Ɓadamayya ya zo shi da iyalan shi, shiyasana tsaya muka gaisa" "to ai shikenan tunda ga ta ta iso se ku tashi muje, ni da ta ji tawa madazamanta tayi tunda tana da majinyaci, ai mun isa mu wakilceta" tayi maganan tare da miƙewa, miƙewa suka yi fuskoki washe da murmushi, saurin ƙarisawa kusa da Farisat dake saka facemaskHalima tayi tare da faɗin "ina Yasmin? Ba zata ba ne?" Murmushi ta sakin mata tare da faɗin"Yaya ya hanata zuwa" jinjina kai tayi tare da faɗin "brother Samir ze dawo nan da sati biyumasuzuwa" tayi maganan cike da zumuɗi, da mamaki ta bi ta da ido... Murmushi ta saki tare da jinjina kai cike da tabbaci, "yaushe ku ka yi magana da shi!" Tacedazallan mamaki, "ɗazu ya kira Daddy shine fa ya faɗa mai" murmushi ta saki tare da faɗin"lallai Yaya Samir za'a dawo, Allah ya nuna mana cikan lokacin, yasa da gaske ne kuma" "amenkowahaka yake cewa wallahi, Nafi tace in gaidaki" jinjina kai tayi tare da faɗin "ina amsawa ba zatabane?" "Ita aka bari da Yaya Sudais" tace tare da saurin buɗe mata ƙofan motan murmushi tasaki ta shige mazaunin driver, gefen me zaman banza ta shige a natse bayan ta rufe mata ƙofan, "Mommy nan za ku shigo fa" tayi maganan tare da kallon Gude dake jiran Jummai ta shigemotanSadam ita ma ta shiga.... "A'a ku muje za ku ɗauki su Tinene a waje nayi magana da Ali da Balarabe matan su za sujiramua bakin gate, Farisat ku za ku ɗauke su" jinjina kai tayi tare da ma motan key ta shige gaba, sunafita gate a dai-daita sahun da suka hayo na taka burki, babu wani ɓata lokaci suka shige sukaɗauhanya, tun da suka ɗau hanya ba su tsaya a ko ina ba se a ƙofar gidan Habiba dake garinDimau.... Iso har asibitin da aka kwantar da ita ɗanta na uku ya musu, suna shiga suka tadda ta zauneSha'awanatu ta zuba mata abinci tana ci a hankali, suna doko sallama fuskanta ya washedamurmushi bin su kawai take da ido cike da farin cikin ganinsu, "sannu Habi" Babiya tace cikedatausayawa, murmushi ta saki tare da jinjina kai, jawo musu kujeru Shafa'atu tayi cike da jindaɗinganinsu... Zazzaunawa suka yi cike da yaba tarban da suka musu, nan ta jawo pure water ta ajiye musu, "sannu Shafa'atu, ku ce duk kuna nan, ai dole ma ku zo uwa ai ba abar wasa ba ce, kamar ni neace mata gani can yashe a gadon asibiti ai na san takalmi ba zata tsaya sakawa ba, Allahdai yabaku lada, a cigaba da kula da iyaye musamman uwa, lamarinta babba ne" Babiya tace idontaakan su, murmushi suka saki ba tare da sunce mata komai ba, "Sha'awanatu ki ce kema gabki keda juyewa?" Ta kuma cewa idonta akan cikin Sha'awanatun da ya turo a riga, murmushi tasaki tare da sadda kai... "A'a daina jin kunyata ai ƙawa nake, ga waƴanda zaki ji kunya nan" ta idda maganan tare danunasu Suwaiba, "sannu Anty Habiba" Suwaiba tace da kulawa, "yawwa Suwaiba sannun ku dazuwa, Anty Gude har dake? Ya jikin Sudais ɗin!" Ta idda maganan cike da damuwa, murmushi tasaki tare da faɗin "da sauƙi, ina ta saka lokacin zuwa na ga yanayin jikin na ki, se ga wannanlabari yariske mu" murmushi ta saki ba tare da tace komai ba.... "Na ragon kaya ba, ai abun ba daɗi ne da shi ba, amma na ki Habi zance gunda haka, haba Habi dagirmanki da ƴaƴanki da jikokin ki, da sarakunanki, da kunyarki ki biyewa namiji wanda baisashshen kunya gare shi ba, ki na biye mishi se ya barki da ɗaukan nauyi ke ɗaya, yanzuinaamfanin haka, ciki da tsufanki Allah na tuba ko Munari Auta ai ba tayi gigin yin ciki yanzubaahalin nan da ake ciki".... Ta idda maganan cikin nuna zallan takaicinta, ba abinda Habiba tace se sadda kai da tayi cikedajin nauyi, "ikon Allah Hajiya yi shiru akan wannan batun tunda baki san abinda duniya ke ciki ba, kina ina tsohuwa kamar ki take ciki ta haihu" Farisat tace tare da kama haɓa, "ungo naki Farisat ban san shaƙiyanci" tace tare da watsa mata daƙuwa, kame fuska tayi tare da faɗin "serious, Allah ya baki Anty Habiba ba wani kunya da zaki ji, da yawan masu shekarunki suna so Allahbeba su ba, wannan da ya zuben ma mun ji zafi, kuma muna miki fatan samun wani very soon, muna so mu, kuma Kawu Hamidu yana son abin shi, duk me jin kunya ya daɗe be ji ba" "tobiyewaƴarki ku aikata aikin yarinta, ita ba abinda ya shafe ta" Babiya tace tare da ɗaga kafaɗa.... Dariya Gude ta saki tare da faɗin "wannan draman se ku Hajiya, amma ciki ai in Allah ya badabayanda za'ayi amsan shi za'ayi da hannu biyu a mishi godiya sannan a tarairaya" "au ke ma!" Tacetare da kama baki idonta akanta, "ai Hajiya duk muna haɗe" Jummai tace tare da sakin murmushi, "to ya yi muku kyau" tace tare da kauda kai, murmushi suka saki tare da bin ta da ido, .... Shigowa Sadam yayi a natse shi da yaronta da ya musu rakiya, "Sadam!" Tace da kulawa, murmushi ya sakin mata tare da faɗin "sannu Anty Habiba Allah ya ƙara miki lafiya" "amen" tacecike da jin daɗi, zaro wayanta dake ringing Farisat tayi tare da faɗin "kin ma yi haƙuri" dariyaHalima ta saki tare da faɗin "halan Yasmin ce?" "Ita" tace tare da ɗagawa, "gata" tace taredamiƙewa ta miƙawa Habiba wayan.... "Anty Habiba na ya jikin naki?" Tace cike da kulawa me haɗe da damuwa, "AlhamdulillahYasminya gidan da Muhammad?" "Alhamdulillah Anty Habiba na, Allah ya ƙara miki lafiya" "amen" taceda kulawa, "to se mun ƙara magana, na kira wayanki wannan ɗan ƙauyen ya ɗaga" tace cikedatakaici, murmushi ta saki tare da kallon yaronta dake tsaye yana sakin murmushi, "ƙyaleshi zanamshi abuna" "yawwa Anty Habiba na, zan kira ki zuwa anjima" tace tare da katse kiran, miƙamata wayan tayi cike da jin daɗin maganan da tayi da Yasmin, "na huta, tun muna hanya takekira" murmushi ta saki tare da bin ta da ido.... Haka suka wuni a hospital ɗin se da suka yi sallahn la'asar sannan suka fara shirin tasowa, "nayi ma Insu Bitimis da Kantun Ghanan da tace inyi mata ya za'ayi ya isa gare ta?" Shafa'atu tacetareda kallon su, "har kin yi da wuri haka?" Babiya tace tare da kallon ta, murmushi ta saki tareda faɗin "shekaran jiya da ciwon ya fara tasoma Mama shine tace inyi ta tafi da shi da can za tazo, to kafin safiya abun ya tsananta ba zata iya zuwa can ba, shine muka kawota na nan" "Allahsarki Habi ki na wannan hali me haɗari amma kina tune da abinda ɗiyarki ke so" Babiya tace kamar zata saki kuka.... Murmushi Habiba ta saki ba tare da tace komai ba, "ki saka a mota kawai se ki kirata ki sanar daita ta tura a amsan mata, ba kina da numberta ba?" Sadam yace tare da kallon ta, "wallahi bani da shi" tace tare da kallon shi, "ina da shi" Sha'awanatu tace tare da kallon ta, "to shikenanma" tace tare da sakin murmushi.... "In dai baki da nisa jeki ɗakko in tafin mata da shi, nan da sati biyu zamu je can" Farisat tacetareda sakin murmushi, "zaku kuma!" Babiya tace tare da kama haɓa, murmushi ta saki tare dafaɗin"Hasenat zamu kai" "auh mijin ya dawo bikin ya taso kenan?" Babiya tace tare da kallonta, "ehjiya my Jannah yace mun gobe za su kawo lefe nan da sati biyu kuma biki" "ma sha Allah, Allahya kawo ƙarshen jira, wannan yarinya Allah ya ba ta ladan jira, ta sha jira, tun kafin bikinYasminake ta maganan na ta ga shi Yasmin har tana sati na uku" "lallai ta sha jira" Gude tace taredakallon ta... "Tun kafin a tsaida lokacin na Yasmin aka tsaida nata, amma shiru, mutane na ta magananyaudaranta ya yi kawai, se gashi ya dawo" Farisat tace tare da sakin murmushi, "to a dai ƙarabincike, kar ya zo ya ƙara guduwa" Suwaiba tace cike da mamaki, dariya Farisat da SadamdaHalima suka saki tare da kallon ta... "Wallahi da gaske, yaro ya ɓace ɓat yanzu ya dawo a ce biki ya tashi, in kuma ya banka mataciki ya ƙara ɓacewa fa!" Tace cike da gaskiyanta, ficewa Sadam da yaron Habiba suka yi cikindannedariyar da suke yi, dariya Farisat ta saki tare da faɗin "ba fa guduwa yake ba, ba kuma ba'asaninda yake ba ne, irin dai yayi shiru da maganan nake nufi" "oh to Allah ya sa a ƙulla alheri, HajiyaFatima zata aurar da auta, Allah yasa kar tayi zazzaɓi" Suwaiba tace tare da sakin murmushi.... "Aiko za tayi" Farisat tace tare da sakin murmushi, "ai sun shaƙu gaskiya" Jummai tace taredasakin murmushi, "to ke Shafa'atu mu jira ki ne ko mu tafi?" Babiya tace tare da kallon ta, "bari inɗakko" tace tare da ficewa a guje, "dan Allah ji ƙauyanci, da girmanta take tiƙan gudu haka, intahaɗe da mijin a hanya kuma se tace mai me oho" Babiya tace tare da nufar ƙofa, "mene abindayashafi Shafa'atu kuma" Baba Tinene tace fuska cike da murmushi, murmushi matan Balarabetasaki tare da bin ga da ido, "ku jirata yanzu za ta dawo ba ta da nisa da nan" Sha'awanatutacetareda sakin murmushi, "to Habi zamu tafi Allah ya ƙaro ingantaccen lafiya, ki ɗau maganata zeamfaneki" Babiya tace tare da nufar ƙofa... "Insu na lafiya dai ko?" Habiba tace da kulawa tare da kallon Farisat, murmushi ta sakinmatatare da jinjina kai, "sosai kuwa, yanzu ma ba ta san baki da lafiya ba ne na san da ta addabemuda kira, yanzu kuma na san tana makaranta shiyasa ban kirata ba, amma zan faɗa mata zatakiraki" murmushi ta saki tare da jinjina mata kai, sallamanta suka yi suka fara ficewa, "ku jira tabazata daɗe ba zata dawo" tace tare da kallon su, "zamu jirata a bakin ƙofa, dan yanda Hajiyatafitan nan in ba mu fita ba zamu fara amsa kira a gigice" Suwaiba tace tare da ficewa da sauri, "toTinene ina godiya sosai, ku gaidamun da mazajenku" murmurshi suka sakin mata suka ficebayansun amsa mata da za su ji, "Anty Habiba se na kira, Allah ya ƙara miki lafiya" Farisat tace taredajan hannun Halima dake sallamanta suka fice .... Suna isa inda suka faka motocin Shafa'atu na dawowa, "auh ashe baki da nisan da gaske?" Babiyatace tare da kallon ta, murmushi ta saki tare da miƙa ma Halima da ta miƙa mata hannumadaidaicin ledan dake riƙe a hannunta, "kina shan kwanan lungun nan gida na uku nannake" tace tare da nuna mata lungun da hannu, "to se gaba in mun zo, ma shishshiga" Jummai tacedakulawa, "amen, zamu zo in Sha'awanatu ta haihu in sha Allah" Farisat tace tare da buɗe mota, "da gaske Farisat!" Sha'awanatu da ta biyo su dan yi musu rakiya tace cike da farin ciki, "inshaAllah" tace fuska washe da murmushi ta shige, "Allah ya so" tace tare da matsawa gefe, sunatsaye suka shishshige suka tada mota suka ɗau hanya bayan Farisat da Halima sun ɗaga musu hannu, suna ficewa daga hospital ɗin suka juya dan komawa ciki..... Comments fans🥰🙏 🫀MUGUWAR TSOKA 🫀 {🫀TA'ARE KALLUƊE} [Muscle Cramp🫀] ) عضلة سيئة ( 🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_ https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 ~~~~~~~~~~~~~~ ِبسم الله الرحمن الرحيم Created and written By Yardajjiya👩 💻 Page. fifty three A natse suka shiga restaurant ɗin babu wani hayaniya a tafiyan su, suna zama Nachma takalli Insu tare da faɗin "ba zan ƙi ce miki na girgiza da jin wannan maganan ba" murmurshi ta saki tareda buɗe ruwan da aka ajiye musu ta kafa kai, tana cikin sha wayanta da ta ajiye a gabantayaɗaururi, ajiye bottle ɗin ruwan tayi ta ɗau wayan tare da bin sunan dake yawo a saman screenɗindaido, wani guntun murmurshi ta saki tare da lumshe ido, "ta shiga jazaba" Labib yace tare daƙyalƙyacewa da dariya, murmushi ta saki tare da ɗagawa ta kara a kunni tare da tattaro dukkanin natsuwanta ta zube akan wayan.... Murmushi SSB ya saki daga ta can tare da lumshe ido ga zame kaɗan ya kishingiɗa a jikinsofanda yake kai, "Assalamu alaikum" muryanta me cike da shauƙi da marari ya doki kunnuwanshi batare da wani shamaki ba, faffaɗan murmurshi ya saki tare da motsa laɓɓa a hankali cikinƙasadamurya ya amsa, sautin murmushin da ta fidda ne ya kawo mai ziyaram gaggawa, murmushi yasaki yanda za ta iya jiyo sautin tare da gyara zama a natse cike da natsuwan shi yace "me matanSSB ke yi ne?" Murmushi ta saki tare da kallon ma'aikaciyan da ta ajiye musu abinci tare dafaɗin"lunch za ta yi, me mijin Insu ke yi?" Kwaɓe fuska yayi kaman ta na ganin shi tare da faɗin"aiki, sun ƙi bari na huta tun ɗazu" "ka shiga office ne!" Tace da mamaki, "eh Gorgeous ya zanyi?Yakamata in fara fita tunda na samu sauƙi" jinjina kai tayi kaman yana ganinta tare da faɗin"kayi lunch ne?" "A'a" yace a hankali, "yakamata kayi Nafsii" tace a hankali, lumshe ido yayi sunanna ratsa zuciya da gan-gan jikin shi.... "Ka na ji na?" Tace a hankali kaman me gudun wani yaji, jinjina kai yayi a hankali tare da motsa laɓɓa da ƙyar dan jikin shi ya mace murus da jin sunan da ta kira shi da shi tare da faɗin"ehGorgeous!" "Okay uncle Jabir na tare da kai ne?" Tayi maganan tare da ɗaga kai ta kalli suHisham dake ta cin abincin su hankali kwance kaman ba sa jin maganan da take, "eh gashi nan" yace tare da zare wayan a natse ya sa a speaker ya ma Jabir da maganan da yayi ya jawohankalin shi kan shi alamun ya ƙariso kusa, "okay uncle Jabir kana jina?" Tace a natse cikedakame mutuncinta.... "Eh ranki ya daɗe" yace tare da sakin murmushi, murmushi ta saki tare da faɗin "dan Allahatemaka mana da lunch, zamu ci mu sha magani" tayi maganan kai tsaye babu wani shamakinnauyi ko kunya, murmushi ya saki me faɗi tare da faɗin "an gama ranki shi daɗe, yanzu kuwa" "yawwa uncle Jabir na sanka ba wasa nagode" tayi maganan cike da jin daɗi, murmushi yasaki ya tashi ya bar wajen, cire wayan a speaker yayi tare da maidawa kunni, "please ka ci da yawaNafsii" tace a marairaice, "da yawa ma kuwa Gorgeous" yace a natse cike da shauƙi, murmushi tasaki ba tare da tace komai ba, murmushi ya saki tare da faɗin "ki yi lunch, kar in cika ki dasurutu"murmushi ta saki a natse ba tare da tace komai ba, murmushi shima ya saki wanda sautinshi yadoki kunnuwanta.... "Murmushi ta kuma saki tare da ƙoƙarin zare wayan, "kina ji?" Muryan shi ya doki kunnuwantaanatse, maida wayan tayi da sauri tare da faɗin "ka ce me ne?" Tace a natse tare da dai-daitazaman wayan, murmushi ya saki tare da faɗin "ki ci da yawa" murmushi ta saki tare da faɗin"kaci da yawa" murmushi ya saki tare da jinjina kai ya zare wayan a natse fuska cike da murmushi yaajiye a gefen shi, murmushi Jabir dake ta bin shi da ido ya saki tare da faɗin "an gama shiryalunch a shigo da shi ne?" Kallon sakanni ya mai tare da jinjina mai kai, murmushi ya saki taredajuyawa ya fice a natse.... Da murmushi a fuska ita ma ta ajiye na ta wayan tare da gyara zama ta ɗauki spoon a natse, "ai na ɗauka ƙauna ya ƙosar da ke?" Nachma tace tare da sakin murmushi harara ta dallamatataɗibi abincin a natse ta kai baki ba tare da tayi yunƙurin ba ta amsa ba, murmushi ita ma tasaki tamaida hankalinta akan na ta dan ta san ba za ta ce komai ba.... A natse suka kammala cin abincin suka fito, "zaki tsaya ayi submitting ɗin assignment dakenekozaki tafi?" Nachma tace tare da kallon Insu dake gyara zaman jakan da ta goya, "zan tsayaba'awasa da ko wani mark fa" tace tare da kallon ta, dariya ta saki tare da faɗin "gashi yace zeiyazama test" "ai mugu ne" tace cike da takaici, "a'a barmu mu faɗi hakan, gunda da ke aurenki dagata" Nachma tace tare da kallon ta, komai ba tace mata ba se zaro wayanta da ke ringingdatayi, "ganin sunan Yaya ya sata sakin nagartaccen murmushi tare da faɗin "excuse" tayi maganantare da ja gefe ta zauna saman ɗaya daga cikin jerun kujerun da suke wajen, murmushi sukasaki tare da wuce wa class.... "Yayana!" Tace a zumuɗe, murmushi Yaya ya saki daga ta can tare da faɗin "Insu baby" murmushi ta saki tare da fara gaishe shi a ladabce, "barrister Ɗan Asabe ze zo gobe dan tattaunawa daAntynku akan wannan issuen, barrister ya ba da uzuri akan ba ze samu tsaya mata ba sabodashari'o'in da yake dashi a wannan tsukin da yawa, na karɓi uzurin shi" ya idda maganan cikedakamalan shi, "to Yaya ba komai, yanzu shi barrister Ɗan Asaben ne ze tsaya a shari'ar?" Tajefamai tambayan cike da rashin gamsuwa da maganan na shi.... Murmushi ya saki tare da faɗin "a'a ze zo ya tattauna da ita ne dan tattara hujjoji, in sha Allahni zan tsaya a shari'ar" wani nagartaccen murmushi ta saki cike da farin ciki tare da faɗin "Allahyabiyaka da sakamako wanda ze girgiza ƙwaƙwalwan ka Yaya, Allah ya faranta maka kamar yandazaka faranta zuciyar uwar marayun dake ta zubar da hawaye tsayin shekara saboda haƙƙinƴaƴanta, Allah ya sa burin mu na samamata adalci ya tabbata" "amin" yace zuciya cike dajindaɗi, addu'o'inta.... "Se ki sanar da ita sannan ta shirya ta zama jaruma kar tsoro ya hanata magana yanda ya kamata" "in sha Allah za ta ji, ai jarumace Yaya, tun asali danneta aka yi shiyasa ba ta iya cewa komai" tace cike da farin ciki, jinjina mata kai yayi fuska cike da murmushi, "dama ina sonkiranka yau Yaya" tace a natse cikin tattaro natsuwanta.... "Ina jinki, lafiya dai ko!" Yace cike da nuna zalaman jin abinda za tace a muryan shi, murmushi tasaki tare da faɗin "lafiya lau Yaya, abun farin ciki ne, Anty iƙilima ne tayi miji" ta idda maganancike da yanayinta, "Iƙilima ta mu ta nan Bertuwa!" Yace cike da zallan mamaki, "eh Yaya" taceanatse, "waye mijin!" Yace cike da mamaki, "uncle Jamil" tace kai tsaye ba tare da wani shamaki na tsoro ba.... "Ma sha Allah! Ma sha Allah! Allahu Akbar, Allah gwanin adalci, adalin sarki wanda adalcinshi yacika bayin shi" ya jero kirarin cike da zallan farin ciki, ban da murmushi ba abinda Insu ke saki cike da farin cikin yanda ya amshi maganan, "a ina suka haɗu?" Yace a natse, gyara zama tayi takoramai duk yanda suka yi da Alhaji Jamil, banda murmushi ba abinda yake saki, tana sakaayayace "zan tuntuɓi Kabir da maganan in sha Allah" "to Yaya kome ake ciki dai kune zaku tsayaakan maganan, zanyi magana da Farisat taje ta sameta in ta amince se su faɗi inda za'a jeatambayo auren kawai" "hakan ya kamata, ina matuƙar alfahari dake Insu, Allah ya tabbatar daalherin shi a cikin wannan haɗi da ki ke fata da niyyan yi" "amen Yayana se na kira bari inkomaclass" "to shikenan ki gaidamun da sarauniyar ƙiwiya" yace tare da sakin murmushi ya katsekiran, murmushi ta saki cike da farin cikin ganin abubuwa na tafiya yanda tayi fata ta miƙetanufi class

Chapter 83 of 109