ganin ki, wani nisa ke tsakanin Bertuwa da Dimau" ya idda maganankamar ze tashi sama tsaban yanda zuciyar shi ke hanƙoro "innalillahi wa inna ilaihirraji'un" Babiya tace a rikice, "kar ki nemi ɗagawa kan ki hankali akan batun su, kama tudini tudanAllahke nuna musu da idanuwan su, ta samu ta aurar da biyun da Allah ya ba ta lafiya a ɗaya neAllahya nuna mata iyakanta, se ta gode mai, ita ko wannan yaronta gab yake da haukacewa" yayi
maganan tare da nuna Gude, "subhanallah" Yaya yace cike da damuwa, "kwanan nan ko wataba'a rufa ba yaje ya sha abinda yafi ƙarfin ƙwaƙwalwanshi, haka ya fito tsakiyan anguwa yanaife-ife tare da faɗin "kowa ya gudu za'a yi yakin duniya na uku" in dai ba su tashi tsaye ya dainashaba wallahi nan da wani lokaci ze zama taɓaɓɓe, ko da yake in yi shiru dan uwar shi ba so takeanafaɗan aibun shi ba, ita kuma wannan ɗa namijin da Allah ya ɓata ɗaya-ɗaya, shi aka kamadawiwi a aljihu shima ba'a jima ba, da matasan anguwan su ka mai ribiti suka tambaye shi a indagasamo se cewa yayi "ɗan makarantan su ne ga ba shi ajiya" me makon uwan da taji haka tafaɗama uban ya tashi tsaye dan jin me shirin ɓata mai tarbiyyan ɗa se ba tayi haka ba dakecushewan ƙwaƙwalwa ya ziyarceta, se fitowa da tayi tsakiyan anguwa tana kumfar baki akan, kar su kashe mata ɗaya, kowa abinda ya ga dama yake, kuji fa, mutanen da suka tashi miki tsayeakan shiryuwan ɗanki su ki ka je kina ma wannna ɗiban albarkan, an kira ni akan batunnacesuma uban yaron magana, ban san sun mai ko na su mai ba, amma ni ma na same shi da maganankuma yanda ya nuna mun ba ze bari abun ya sake faruwa ba" Ali ya idda maganan cike daƙunanzuci....
Dago kai Gude tayi a harzuƙe tare da faɗin "in be haukace ba Ali ka haukata shi, zuƙa ba akanshi
a ka fara ba, se ma in ce a wajenka ya gani ya koya, tunda duk abinda ka sha be haukatakabashima ba ze haukace ba" ta idda maganan cike da takaicin aibanta mata ɗa da yayi, "waneshi danuban shi kan shi ya ɗau abinda na wa ya ɗauka, ke ba dadin addu'an iyaye ba kin isa ki zaunaagabana haka kina faɗin abinda ranki yake so, ruwa ne ya duki ɗan zakara, amma ki na nanki nayi
zaki shigo hannu" Ali yace zuciya a mugun ɓace, "to kunga abun ko, haka takema duk wandayatashi dan mai ɗanta faɗa a anguwan, gashi nan zata nuna muku kuma" Lurwanu yayi maganantare da jan tsaki, "yanzu ke dan Allah har kina da bakin magana?" Yaya yace tare da kallonta, "kana ji fa Abdussamad yanda yake aibanta mana ƴaƴa, jarabta ne Allah ya musu kuma munanan muna sa su a addu'a, shi yanzu ze ji daɗi in zauna a gaban shi ina aibanta ɗan shi, kamanyanda yace ba dadin addu'a da suka yi akan shi ba ganuwa ze yi shima" Gude tace zuciya natafarfasa, "wallahi indai ya aikata abinda be dace ba, ki yi sannan ki mai hukunci ba na da
matsala da hakan" Ali yace hankali ƙwance....
Shiru Yaya yayi duk suka gama zantukan su kafin ya gyara zama tare da gyara murya, "fatanmahaifin mu har ya mutu be wuce na mu haɗa kan mu mu zama tsintsiya maɗaurin ki ɗayaba, amma a ce kullum burikan ku se dai mu tarwatse kowa yayi na shi wajen, tsakanin ku da Allahhaka ku ka ga sauran ƴan uwa suna yi da ƴan uwan su ko da iyayen su? Ki dubi yaran ƴanuwanHajiya yanda suke da junan su, ku kalli na Baba yanda suke yi, se mu kaɗai ne muka fanɗaremuka gagara, wannan abinda muke yi sam baya farabtawa mahaifiyar mu, dan bayan da zataiyane ta koma gefe ta zuba mana idanun, ya fa kamata muyi wa kawunan mu karatun tanatsu, muguji ruɗun duniya da ƙyale-ƙyalen dake cikinta"....
"A ce muke nan cikin faɗa da juna, aibanta juna, zagin juna, ƙanana ba sa girmama manya, yakuke ganin nan gaba yaran mu za su yi, kuna ganin za su zo junan su ne? Wallahi ba za su taɓasanjunan su ba, kai in ƙarƙare muku zumunci da juna ma ba za su yi ba, kuma duk mu muka haddasaabun" jan numfashi yayi ta fesar tare da kallon yanda jikin su Ali yayi sanyi, "Alhamdulillahi taɓangarenmu mu maza zan iya cewa muna kamantawa, se dai ku mata bana jin ɗayan kunazaune da ƴar uwanta cikin aminci da ƙaunan juna, kuna goyawa bayan junanku ne dan tsoronkar
ya zo wata tace ba'a bi ta ba, ke Habiba kin aikata babban kuskure akan sakacin da ki kayi dayarinya har ta iya aikata wannan zunubin ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba, ba na jin irin tarbiyyanda mahafanmu suka miki kenan, ba yanda ki ke rainan ƴaƴanki suka raine ki ba, yakamataki
canza, ki yi ƙoƙarin gyara rayuwar ki, ita duniyar labarinta gajartacce ne, zuwa ne da kumakomawa, in ki ka yi wasa kafin kin farga zaki ji ki a inda ba ki zato ko tsammani, kinga kintafi kinbar abinda duk in aka kalla za'ayi Allah ya wadai dake da jinin ki, ki ƙi naki duniya ta so su, ki sona ki duniya ta ƙi su, wannan haka yake, kuma in ku ka ɗauki shawarata zaku rayu da yarankulafiya cikin alfahari, ku cigaba da saka su a addu'a, dan addu'an iyaye na da matuƙar mahimmaci
ga ƴaƴan su, sannan yarinyar da aka kawo akan ta zauna da Hajiya Ali zaka ɗauketa ka tafi daitagidanka na san Saratu ba ta da wasa wajen sakawa yara ido" ya idda magana tare da kallonsu.....
"Hakan yayi" Babiya tace tare da kallon shi, jinjina kai su Ali suka yi cike da gamsuwa, "a'abadai
gidan Ali ba, dan ze iya naƙasa mun ƴa" Habiba tace cike da takaici cewa da yayi Ali ya ɗauketa, "in dai yarinyar ki zata rayu anan dan san kar asirinku ya tonu to a gidan da Yaya Abdussamadyace zata zauna, in kuma ba kya buƙata ki tattara ta ku koma inda ku ka fito" Lurwanu yacefuskan shi na sauyawa, "a'a Yaya Lurwanu ga gidan Gude ai zata iya zama, da ma ita yakamatatazauna da ita, kuma ka ga akwai sa'o'inta za tafi sakewa" Balarabe yace tare da kallon Gudedataɗago kai ta banka mai harara, gane dalilin da yasa yayi maganan yasa Lurwanu faɗin "gaskiyanekuma, Yaya Abdussamad ina ganin hakan ya fi kamata" yayi maganan tare da kallon Gude, "toina ganin in za tafi sakewa a can se ta zauna kawai" Yaya yace ba tare da ya lura da sigandasuBalarabe suka yi maganan ba, "ba ze yuwuba" Gude tace tare da kallon Yaya, da mamaki sukakalleta gaba ɗayansu, "saboda me? Yarinyar ƴar uwanki ce, ke keda haƙkƙin rufe mata asiri dankar ya tonu a idan duniya" Ali yace tare da gyara zama, me gidan ba yarda ze ba, ganin irinkallonda suke bin ta da shi yasa ta faɗin "me gidan ba ze yarda ba, ko babu wannan matsalan ballantana da kwai, ba ze taɓa amincewa ta shiga tsakiyan ƴaƴan shi da wannan abin kunyan ba" tayi
magana idonta akan su, murmushi Babiya ta saki tare da girgiza kai, "to ke Suwaiba fa?" Balarabe yace tare da kallon ta, wurga mai harara tayi tare da faɗin "ni ina nake da ƙarfinriƙeta, sanann anguwar mu ma shiryayyun nan sunyi yawa, kar yazo garin gyaran gira a rasa ido, danbanatsuwa ne da ita ba, ni kuma ba zan zauna zaman saka mata ido ba, tunda Yaya Abdussamadyace ta zauna a gidan Yaya Ali ta zauna mana me ye na wani zantuka tunda neman matsuguni
take ga yarinyar, ita ma banda abin Yaya Habiba menene na tattaro yarinya ta kawo ta, gari anafama da kai" ta idda maganan cike da son kare kai, "Jummai ke fa?" Balarabe dake sakinmurmushi yace idon shi akan ta, gyara zama tayi tare da faɗin "Allah ya ba mu ikon zama lafiya, ta zo mu zauna, abinda muka sawa bakin mu ai shi zata saka ma nata" kallon Habiba da tacikadamamaki Lurwanu yayi tare da faɗin "ga masoyanan, masoyan da ba za su iya share miki
hawayenki a lokacin da suke kwaranya ba, wai a haka ku ke ikirarin kanku a haɗe yake, Allahshi
kyauta, kin yarda Jummai ta riƙeta?" Yace tare da kallon ta, jinjina kai tayi jiki a mace, "toAllahya kyauta, ku kuma kun san abinda yakamata ku yi ai" yace tare da kallon su, "Allah ya baki
haƙuri Babiya ba mu yi tunanin abin ze baƙanta miki har haka ba" Suwaiba tace ko a jikintaakanmaganan da tayi akan ƴar Habiba, murmurshi Yaya ya saki cike da mamakin halayensu....
"Ka maida su kawai" Yaya yace tare da kallon Balarabe, ba musu ya miƙe, "ku muje" yace taredanufar ƙofa, mikewa Gude da ba ta ce komai ba tayi tare da faɗin "Allah ya sadamu da alheri
Babiya a yafe mu" tana kai nan ta dafa mai baya, miƙewa Suwaiba tayi tare da kallon Habibacikeda kulawa tace "tashi muje" "a'a ina nan tukun" tace ba tare da ta kalleta ba, bin ta da kallomecike da zallan mamaki tayi, miƙewa Jummai tayi tare da faɗin "zan dawo ko zuwa gobe neBabiya" "Allah ya nuna mana muna masu rai da lafiya da imani" "amen" tace a girmame, "zomutafi Suwaiba shi dama gaskiya ɗaci gareshi, se daga baya ake fahimtar abinda yake tare dashi, agaɓan da aka furta ba iya fahimta ake ba, amma in banda rashin san gaskiya ƙarya a kawayarinyar? Ina ce ita ta saketa sakaka a shekarunta 18 ciki uku, banda lalacewa meye wannan, dama aure ki ka mata da kin nisanta kan ki da hawan jinin da take gab da saka miki, se da ki kalalata komai sannan ki ka ɗaɗɗako ta ki ka zo wahalallu su gyara miki, yanda ki ka ɓata kezaki
gyara ƴan kayan ki, ita ma Jumman na ganin ido ne, ba iyawa za tayi ba" Gude tace rai ɓacetareda ficewa daga parlorn, da sauri Suwaiba data dafa mata baya, miƙewa Habiba tayi a harzuƙezata bi su Ali da Jummai da ta ƙara tsorata da halin ƴan uwan nata suka riƙota, "menene naharzuƙa? Ai kema kin san hakan ze iya faruwa tunda ba dan Allah ku ke ƙaunan junan kuba" Ali
yace tare da zaunar da ita "ka bar ni Ali in nuna mata ƙarshen lalacewa" Habiba tace cike daƙunan zuciya, "dan Allah Anty Habiba kar ki ce komai, kema fa kin san yanda take, menenenaɓata ranki a kan kalamanta" Jummai tace hankali a tashe....
"In ba zaki iya riketa ba Jummai ke ma kar ki ɓoyemun zan kwashesu gobe mu koma" Habibatace cike da ɓacin rai, "a'a wannan batun na ta duk faɗa take in sha Allah zamu zauna lafiya, sedai ba lallai ta samu duk abinda take so a waje na ba, kin san yanda rayuwar ta koma" jinjinamata kai tayi tare da sakin huci, "to Yaya Abdussamad taya kake zaton wai za'a haɗa kai bayanda
Gude a tsakanin mu, ai se dai ayi sha'ani kawai, amma wannan matan da kake gani sheɗancintayafi ƙarfin tunanikanmu, ke dai Hajiya ki yi ta bin mu da addu'a kamar yanda ki ka saba, Allahyashirya mu ya ganar damu, amma Gude se Ubangiji ya saukar mata da aya wataƙila ta hankalta" Ali yace cike da takaici, "duniya zata ganar da ita menene rayuwa, fatan mu dai Allah yasakar
tayi nadama a ƙurarren lokaci" Babiya tace dabi'un Guden na baƙanta mata, "ai ko a yanzulokaci
ya ƙure mata bare nan gaba kuma, Allah dai ya ganar da ita" Lurwanu yace tare da miƙewa, "Jummai muje in ajiye ki a gida, ina da maganan da nake so muyi" yace tare da kallon ta, "tozamu biya ta gidan Anty Gude mu ɗau Zuwairan" "shikenan muje" yace tare da sallaman suyafice, miƙewa tayi ta sallame su ita ma ta bi bayanshi, gyara zama Yaya yayi tare da faɗin "kar ki sakaabinda ya faru yau a zuciyanki Hajiya, komai ze zama tarihi nan kusa in sha Allah, kamar yandaAli yace ki cigaba da addu'an da ki ke mana kar ki fasa, Allah maji roƙon bayin shi ne ze ji naki insha Allah" cike da gamsuwa tace "kai ma kasan ba komai nake sawa a rai ba Abdussamadyawuce, ai tana da hankalin sanin dai-dai da akasin shi ba mahaukaciya ba ce, ba kuma yarinyabace bare mu ce ƙuruciya ke damunta, matan da ta ɗau jika me kuma ya rage, inda nake godewaAllah ta haifa ita ma an kuma haifan mata" ta idda maganan a raunane, "a'a Hajiya ba za'ayi hakaba, a yanzu ma ki kalli yanda take ina ga kuma da kin riƙeta a zuciya" "ban riƙeta ba ko kaɗangata ga rayuwa nan" tace tare da kallon Habiba, "kin ce zaki tafi gobe ko? To kafin ki tafi ki jewajenBabanku Hamisu ki gaida shi, dan yana ta fama da ciwon ƙafa" tana kai nan ta miƙe ta nufi sideɗin Yaya inda su Farisat ke zaman jiran su gama meeting ....
Bin ta da ido kawai suka yi dan sun san yanda take da kafiya, se dai in ba'a cika ta ba, ba tasakkowa ta sauƙi" sauke numfashi me sauti Ali yayi tare da faɗin "zan wuce ke tashi mujecangida ki kwana kafin Allah ya kai mu goben" ba musu Habiba da kuka ke ta so mawa ta miƙeficewa yayi ta bi bayan shi babu um babu um-um, bin su da ido kawai Yaya yayi yama rasataindaze ɓullowa al'amarin, sauke numfashi yayi ya miƙe ya dafawa Babiya baya....
"Ni fa da za'a nemi shawarata duk a rabu da su, wacce taji jau zata dawo kan hanya" Sadamyacetare da kallon Farisat da duk ta damu, "ku fa kuna son ɓata zuciyanku akan mutanen nannefa, ku ƙyalesu su shuka duk abinda suke son shukawa hankali kwance, tunda ba su nemi temakon
kowa wajen shukawa ba, kunga ranar girbi za su girbe abun su da kawunan su, dan ba metayasugirbewa" Insu tace ko a jikinta, "oh Allah Anty Yasmin kin ko ga saƙonnin da aka ajiye miki awhattapp kuwa? Wallahi sun yi yawa" Nafisat dake zaune riƙe da wayan Yasmin ɗin tana dubawatace tare da kallonta, "ke ni fa wannan whattapp ɗin yanzu ba damuna yayi ba" Yasmin dakekwance a two sitter tace tare da ɗaga kai ta kalleta, "sunyi yawa ga shi nan a groups ma anatatagin ɗinki" tace tare da nuna mata fuskan wayan, "duba ki gani wanda ya cancanci amsa ki basu, wanda be cancanta ba ki bar shi kawai" jinjina mata kai tayi ta maida natsuwanta a kanwayan, "Yaya Salman yaushe zamu fita shan iska ne?" Sahabee yace tare da kallon shi murmushi Salmandake zaune kusa da Sadam ya sakin mai tare da riƙoshi ya zaunar kusa dashi, sallama Babiyatayi
tare da shigowa, "Hajiya" suka ce bakuna a haɗe tare da mimmiƙewa, "a'a ku sha zamankudamazuwa nayi in duba ku" Babiya tace da kulawa.... Murmushi suka sakin mata tare da bin ta da ido, "Hajiya ki shirya gobe mu fita mu ga gari" Salman yace fuska ɗauke da murmushi tare da kallon ta, murmushi ta saki me faɗi tare dafaɗin"to Allah ya nuna mana goben Salmanu, Insiyyah kin sha maganin ki kuwa?" "Na sha sarauniyaNafisat" tace tare da ɗago kai ta kalleta, "to kin kyautawa kan ki" tace tare da juyawa indaYayada yayi sallama ya shigo, amsawa suka yi tare da sakin mai murmushi, "ba kwa gajiya da surutuko" yace idon shi akan su, miƙewa Salman yayi tare da faɗin "bari in koma gida Hajiya Allahyaƙara lafiya, please ki kwanta da wuri ki samu hutu" jinjina mai kai tayi cike da jin daɗi, "sedasafeYaya" yace tare da ficewa, bin shi sukai da ido cike da yabawa da karamcin shi, "ke Farisat tashi
ki raka shi mana" Babiya tace tare da kallon ta, "Hajiya dare yayi ba nisa yana fita ze shigegida"
jinjina mata kai tayi tare da faɗin "tashi ki tafasamun shayi to, na san yanzu Sa'adatu tayi nisaabarci, Mari kuma tun safe mura ke nuƙurƙusanta" "to" tace a zumuɗe tare da tashi ta fice....
Neman waje tayi ta zauna kusa da Sadam tare da faɗin "ina me sunan Malamda Sa'eedu?" "Sunyi
barci tun ɗazu" Sahabee yace tare da kallonta, "ka tashi kaje kaima ka kwanta gobe akwai
school" Yasmin tace tare da kallon shi, miƙewa yayi tare da musu se da safe, "ka tabbatar kasakayan barci kafin ka kwanta, sannan kayi alwala ka yi addu'a" Insu da ke bin shi da ido tacetareda kauda kai, jinjina mata kai yayi ya wuce...
"In sha Allah Hajjin bana damu za'ayi Hajiya in muna da rai" Yaya yace tare da kallon Babiya, zareido tayi tare da kallon shi, murmushi ya saki tare da jinjina mata kai, ihu Insu ta saki tare damiƙewa ta fara taka rawa tana juyi a gabansu, "ke fa yarinyar nan jikin ki baya faɗa miki dai-dai" Sadam yace tare da jawota, ƙwace jikinta tayi tare da cigaba da takawa, banda dariya ba abindaYaya da Babiya ke yi, "meya faru da taka rawa haka?" Farisat tace tare da miƙawa Babiya tendata haɗo ta jero a trey, amsa tayi tare da faɗin "Babanku ne ya biya mana hajjin bana" zareidotayi
tare da ajiye treyn da sauran kofunan shayin ke kai ta rungume shi da sauri, "ma sha AllahYaya, Allah ya saka da alheri yasa kuyi karɓaɓɓiya" hitting ɗin bayanta yayi cike da farin ciki taredafaɗin "amen" ɗagowa tayi ta ɗau kofin shayin ta miƙa mai, amsa yayi cike da alfahari, ba maSadam tayi ta bawa Yasmin, "Nafisat gashi" tace tare da miƙa mata, ɗago kai tayi ta amsataredafaɗin "bari in miki posting a statut Anty Yasmin" "posting ɗin me!" Tace da mamaki, "tafiyahajjinda za suyi mana" tace tare da sakin dariya, ɗaukan na ta Farisat tayi ta zauna tare da fara sha, "toita ina na ta?" Babiya tace tare da kallon Farisat, murmushi ta saki tare da faɗin "ba ta shantea"
"yaushe kenan!" Tace tare da baza mata ido, "tuntuni" tace tare da sakin dariya, "to kenanwannan da ya rage nawa ye?" Tace cike da mamaki, "na Anty" tace cike da sha'afa, kallontasukayi jikkuna na sanyi.... Miƙewa Insu da ta danne abinda ke taso mata tayi tare da ɗauka ta nufi Babiya, "ha" tace taredakai kofin bakinta, buɗe baki tayi a hankali taja kaɗan, murmurshi ta saki ta kai ma Yaya shimakaɗan ya sha, inda Farisat ke zaune ta je ta ba ta ta zuƙa, bakin Sadam ta kai kofin a natse, zuƙayayi tare da kallon ta, murmushi ta sakin mai ta kai bakin Yasmin zuƙa tayi cike da karayanzuci, kai kaɗan tayi baki tare da ɗan yamutsa fuska, murmushi suka saki tare da bin ta da ido, kai maNafisat da ta goge hawaye tayi ta ja kaɗan, ajiye kofin tayi a natse tare da ɗagowa cike dayanayinta ta ɗaga kai sama tare da faɗin "Anty tasha nata, iyalan Anty sune Anty, duk waccetake da wani abu da take son Anty ta ci ko ta sha ko ta saka to ta bawa iyalanta Anty za tayi farinciki, haka ne ko Anty?" Ta idda maganan tare da sakin murmushi, tashi Yaya yayi da sauri yarumgumota tare da faɗin "Allah ya muku albarka" "amen" suka ce baku na a haɗe....
"Ni dai Hajiya in kunje tsarabata jallabiya da agogo ne, kar ki kawo mun kallo-kallo" Sadamyacetare da sakin dariya, dariya suka kwashe dashi tare da kallon Babiya dake faɗin "ungo nakaSadam" "Anty Yasmin ga wani yayi ta turo miki message tun ranar ukun Anty har yau se dayaturo" "tab ɗin be gaji ba?" Farisat tace tare da amsan wayan, tana gama gani ta miƙa matatareda faɗin "a gaishe shi, yayi ƙoƙari" "duba mun a wani group ya cire numberta" Yasmin tacetareda ajiye kofin hannunta, dubawa tayi tare da faɗin "ba a inda ku ka haɗa group" "ikon Allah" tacecike da mamaki, "ya sunan shi?" Tace a hankali, "Morata" tace tare da sakin dariya, "arne nemakenan!" Tace da mamaki, "no se dai in amfani yake da sunan kawai dan ra'ayi" Sadamyacetareda kallon ta, "haka ne Yaya Sadam dan ƙwallon ne hoton shine ma a profil ɗin shi" Nafisat tacetare da miƙa mata wayan, amsa tayi tare da fara duba saƙonnin, sosai suka faranta mata dannasihace da jan hankali akan haƙurin rashin da suka yi tare da jera ma Anty addu'a masufarantazuciya, murmushi ta saki ganin inda ya rubuta "na kusa gajiya baiwar Allah" gyara zama tayi tareda rubuta, Aslm Alkm, naga saƙonni nagode sosai, ban samu daman dubawa ba se yau Allahyasaka da mafificin alheri, sannan please wake magana bangane number da suna ba🙏" tanakai
nan ta tura tare da ajiye wayan, "yawwa Insu ina son hoton nan da ki ka sa a profil ɗin ki" Sadamyace tare da kallon ta, "ni ma ina so, na sha'afa sam tunda na gani nake son yin miki magana" Farisat tace idonta akan ta, jinjina musu kai tayi ba tare da tace komai ba, "wani hoto ne?" Yasmin tace tare da kallon su, "wanda muka ɗauka ranar da Anty zata tafi ta bar mu" Farisat tacetare da kallon ta, "wow ni ma ki tura mun" tace cike da zaƙuwa....
Rayuwa ta cigaba da tafiya su Insu suna ta samun natsuwa, sun dangana fiye da yanda mutanesuka yi zato da tsammani, Babiya ta tsaya musu da dukkanin ƙarfin da ya rage mata, Yayayarungumi ƴaƴan shi sun zame mai manyan aminai, ba yi da wani tunani se na su, in ka ganshi yanafarin ciki to tare yake da su, ya tabbatar da a yanzu baya da wani farin ciki bayan na su, sunjeHajji shi da Babiya sun sauke farali sun dawo cike da aminci, su gwangwaje su Insu da kayanakece raini, Insu da Yasmin sun zana jarabawar fita daga sakandiri, Alhamdulillah sun fita da makinda ake buƙata, ta ɓangaren Babiya da ƴaƴanta mata kuwa kadaran kadahan ne tsakanintadasu, in sun zo gaidata ta gode, in ba su zo ba kuma ba ta ma nuna Allah ya halicce su....
Ta ɓangaren goga ɗan garin Ɓadamayya kuwa, rayuwa ya cigaba cike da kewan insiyyarshi, yadaɗa kamewa da duniya fiye da da, kasuwancin shi kuwa se da ɗa gaba yake, yana tafiye-tafiyesosai, amma be wuce wata biyar wata shida ya dawo ba kaman da da zefi karfin shekara bakwai
ko takwas ba, ....
"WASA FARIN GIRKI" yanzu labarin ze fara, kar ku manta Yardajjiya na tare da ku🥰Comments fans🥰🙏
🫀MUGUWAR TSOKA 🫀
{🫀TA'ARE KALLUƊE}
[Muscle Cramp🫀]
) عضلة سيئة (
🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
written and Created ~~~~~~~~~~~~~~ ِبسم الله الرحمن الرحيم
By
Yardajjiya👩 💻
Page. Eleven
"Kin ɗau littafan islamiyyan ki?" Yaya dake tsaye gefe yana kallon yanda suke haɗa ma Insukayayace tare da kallon ta, jinjina mai kai tayi tare da faɗin "suna jakan da aka kai mota" jinjinamatakai yayi be ce komai ba tare da bin ta da ido, leƙowa Sadam yayi tare da faɗin "Yaya ku fito12fa"yana idda maganan ya juya da sauri, "ku muje Abdussamad" Babiya tace murya a karye taredamiƙewa dmta riƙo hannun Umar da Sa'eed ta fice, ɗagowa daga zage jakan da suka gama turawakaya Farisat da Yasmin suka yi tare da sakin mata murmushin ƙarfin hali, "an gama" Farisat tacetare da nuna mata hakan da ido, jinjina kai tayi ba tace komai ba, ɗaukan jakan Yasmin daNafisatda duk dauriya suke suka yi tare da ficewa, "muje" Yaya yace tare da miƙa mata hannu, ɗaukanhoton su da Anty da na ta da Anty da aka wanko aka maidasu manya tayi tare da rungumewa, sanye take cikin riga three quarter da wando pencil baby hijab brown a jikinta se jakan bayamadaidaici da ta goya, fuskan nan banda mai ba abinda ta shafa mai, se hujin hanci da ta ƙawatada ado me ɗaukan hankali, miƙa mai hannu tayi suka fice jikkuna a sanyaye....
Suna fitowa farfaɗan gidan suka tadda jama'an anguwa a cike, sakin hannunta Yaya tayi anatseta bi su duk sukai sallama, narai-narai Ziyada tayi da ido tare da kallon ta, murmushi ta saki tareda faɗin "ki gaidamin Teacher da kyau" jinjina mata kai tayi dan ta kasa magana, murmushi tasaki tare da rungume Mami, ƙanƙameta tayi ƙam-ƙam tare da faɗin "ki maida hankali akanabinda ya kai ki Insu, kar ki yi wasa da karatu" jinjina mata kai tayi ta zame jikinta tare da kamohannun Mamin cike da magiya tace "ƴar uwata Mami, amana a gare ku" ta idda maganantaredasakin hawayen da take ta dannewa, jinjina mata kai tayi tare da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 109