Share this page
kin yi gulman ne?" yace tare da kallon ta, kwaɓe fuskatayi tare da faɗin "to ai kai nake faɗawa" "ban tambayeki ba ai, wuce muje"yace tare da ingizata, "wash, inba se na faɗa wa Daddy" tace tare da riƙe ƙasan ƙyeyanta, dariya suka saki tare dashishshige wa mota suka ɗau hanyar govement house cike da ƙaunan juna, dafa musu bayasecurity's suka yi a natse... "Amma ai ta tabbatar mun da za ta zo yau" Yasmin da ko daman zama ta kasa samu tundasukashigo tace cike da damuwa, "to me muka sani mu kuma Yasmin? Tun jiya da na kirata bansametaba na ce a cikin Salwa ko Khadijatu duk wanda ya sameta ya faɗa mata lokacin da zamutashi, kuma Salwa ta tabbatar mun da ta faɗa mata, tun kusan 8 na safiyan yau nake kiran layintaamma ba ta ɗauka ba, har muka isa airport ba mu fasa kira ba, in kira Khadijatu ta kira, sedamuka kusan ajiye mata missed calls 20 se da na rantse ba zan ƙara kiranta ba se ga shi ta kiraKhadijatu na ƙoƙarin kiranta.... Nan na haura da faɗa tayi ta bani haƙuri tare da faɗin "gata nan" haka muka cigaba da jirantaamma shiru, to ya muka iya jiranta zamu cigaba jirgi ya tafi ya bar mu, ganin mun jera matakusan 10 missed calls ba amsa na ce Khadijatu ta taso mu tafi, ai Ɓadamayya da Bertuwanbayauta fara shigan shi ita ɗaya ba, wallahi Insu ta ɓata mun rai" ta idda maganan cike da takaici, "Allah ya baku haƙuri" Yasmin da duk hankalinta ya tashi tace tare da kara waya a kunni bayantadanna number Insu... "Ni nafi hasashen Yaya Sahabee ne ya hanata zuwa, dan muryanta yayi sanyi sosai kamar wacceta ci kuka ta ƙoshi, se dai tace barci take yi, amma Insu a yanda take banyi tunanin zata iyarumtsawa ba saboda zakwaɗi se dai in da wani abun" Khadijatu tace cike da zargi, zaro wayandaya katse ba'a ɗaga ba Yasmin tayi tare da kallonta cike da mamaki, "ze iya yuwuwa fa, danYayaSahabee murɗaɗɗene da ku ke ganin shi" Lailah tace tare da kallon ta, "ba na jin ze hana, Insutace be da matsala munyi magana da ita akan hakan" Farisat tace da damuwa... "Hmm lallai ita ma ba ta san shi ba, Yaya Sahabee da be mallaki Anty Amina ba ma a lokacinyana kaffa-kaffa da ita bare kuma wacce yawancin jama'a suka sheda igiyoyin shi akanta, kofazamu tafi bikin q familyn Mommy cewa yake tayi zamanta ba zata ba, haka zamu haƙura mutafi mu barta, ke dai ai sha'ani kawai Farisat, wallahi ze iya yuwuwa hanata yayi" Lailah tace cikedatabbaci, "oh Allah ai da ya barta bikin ƴar uwa guda" Babiya tace da damuwa, "Assalamualaikum" Yasmin da taji an ɗaga wayan tace cike da fatan ta ji murya Insu.... Gyara zama SSB dake kare da wayan a kunni yayi idon shi akan fuskan Insu dake kwance sharɓantana kwasan barcin wahala hannunta soke da drip daya sha ruwan magunguna da allurai, babuwani abu na kula da lafiyanta da ba'a saka a ɗakin ba, "wa'alaikumussalam" yace a natse cikincold voice ɗin shi, zare ido Yasmin tayi ta can ɓangaren baki na ɓari ta kallesu tare da faɗin"Uncle!" Zare ido suka yi tare da zuba mata ido, "ki yi magana" Habiba tace cike da damuwaahankali... "Am am, Uncle ina wuni" tace cike da rawan baki, "lafiya lau" yace a natse, tare da lumsheidotabuɗe a saman fuskan Insu da yayi fayau, aro dakiya tayi ta sakawa kanta cike da ƙarfafa kai tace"Uncle dan Allah ina son magana da Insu ne" kafe Insu yayi da ido cike da fargaban abindazecemata, kafin ya nemo natsuwa ya sakawa kan shi tare da faɗin "tana barci any problem?" "Nodama um yau tace za ta zo kuma ba ta zo ba" tayi maganan cike da fargaba, "ba ta ji daɗi bane" yace a natse, "subhanallah" tace ido waje tare da faɗin "akwai maganinta yana kan dressingmirror yawanci anan nake ganin in muna video call ta sha in sha Allah ze lafa" ta idda magananmurya na bayyana damuwar da ta shiga, "okay ba damuwa za ta sha" yace a natse, "amUncleɗanAllah zata zo?" Tace zuciyanta na bugu da ƙarfi da ƙarfi, guntun murmushi ya saki tare dafaɗin"in sha Allah" "thank you Uncle" tace tare da zare wayan ta katse ta watsa musu ido.... "Me ya ce!" Farisat tace cike da fargaba, "yace zata zo in sha Allah" "ma sha Allah, me ya farunaji kina kwatancen inda maganinta yake!" Ta kuma jefa mata tambaya da damuwa, "yace jikintaneya motsa" "oh Allah" tace kamar za ta saki kuka, nan duk fuskokin su ya sauya, "ni dai incewallahi muryanta yayi sanyi da yawa" Khadijatu tace da damuwa, "in sha Allah da sauƙi tundadai har ta iya amsa wayanku, kar ku damu Allah ze yaye mata gaba ɗaya" Babiya tace da kulawa, "insha Allah" suka ce bakuna a haɗe.... Zazzaune suke a ɓangaren dining suna cin abinci cike da farin ciki da jin daɗin ganin Hisham, kowa ka kalla zaka fahimci hakan a saman fuskan shi, sakin dariya Mihna tayi tare da faɗin"Allah be wani yi ƙiba ba ma brother, kallon tsoro ka mai" murmushi Daddy ya saki tare dafaɗin"to in ma yayi ƙiban ai ba wani damuwa ba ne, zaran tissue Shureim dake sakin murmushi yayi yaja kujeran baya kaɗan ya miƙe tare da faɗin "kar fa ka wani ji daɗi saurin tsufa zaka yi, kanamatashinka tunbi ya ziyarceka" ya idda maganan tare da sakin dariya ya ɗau wayan shi yanufi barin wajen, dariya su Minha suka saki tare da kallon Hisham da ya ɓata fuska, murmurshi Mommy ta saki tare da faɗin "rabu da shi, gani yayi kana son fin shi" murmushi ya saki taredafaɗin "kuma se na fishin" "ina zaka?" Daddy ya je fa mai tambayan tare da kallon shi.... "Buga ƙwallo" yace tare da juyowa, "yaune?" Mommy tace tare da kallon shi, "eh in sha Allah" yace tare da zira wayan shi a aljihu" "Mommy yau ma muka ga amaryan a airport" Mihna tacecike da murmushi, "Allah ya tsare" suka ce tare da kallonshi, amsawa yayi da amen ya iddasaficewa, "amarya a airport?" Hamid yace tare da kallon Mihna, "eh na ganta, lokacin na je faɗawabrother brother Hisham ya iso kawai na ganta, na ɗauka ma wacce yake sone, se yace amaryane, suna bala'in kama wallahi" ta idda maganan tare da sakin murmushi, "wow shine ba ki kirani in ganta ba" Minha tace cike da rashin jin daɗi... "Ni ma ba magana muka yi ba, se da ta wuce na isa wajen" tace cike da gaskiyanta, "oh" tacetareda maida hankali ga abincin gabanta, "akan wa suke magana ne?" Hishamyace tare da kallonMommy, murmurshi ta saki tare da faɗin "albishirin ka" "goro fari ƙal-ƙal kamar zuciyanki first love" yace cike da murmushi, babbar yarinyar barrister Amina ce za tayi aure" "wowin shaAllahzani ɗaurin auren" yace cike da farin ciki, "ai har gidan zaka" Mommy tace murmushi faɗaɗeasaman fuskanta, "da naji daɗi, zan haɗu da iyalanta" yace a natse murya na bayyana irinɗinbinƙaunar da yake mata, "to ai yarinyar ta ne brother ke so" Amen yace tare da kallon shi, fiddoidowaje yayi tare da faɗin "me!" "Wallahi" yace murmushi na yalwatuwa a saman fuskan shi, "wow! Allah ya ba shi ita, da ko nayi farin ciki" yace cike da tsan-tsan farin ciki ... "To ku dai cigaba da addu'a Allah ya juyo da zuciyanta kan shi" Mommy tace na ta fuskanyalwaceda murmushi, "in sha Allah" suka ce baku na a haɗe, "wai ina ka baro daughter ne?" Tace taredakallon shi, murmushi ya saki tare da faɗin "na barta a Ɓadamayya" "ta fasa shigowa ne?" Taceidonta akan shi, "no tace dai yau za su shigo, dan ita na maida tafiyan gaba to shiru kuma basuzoba har na haƙura na ta so" ya idda maganan cike da damuwa, "to in ka huta ka taɓo ta kaji, wataƙila ko sun ɗaga tafiyan ne" "in sha Allah" yace cike da jin daɗin kulan da ta nuna mata, "wallahi ni ma na ƙosa in ganta, ko hoton ta ba mu taɓa gani ba" Mihna tace tare da kallonshi, harara ya banka mata tare da faɗin "ba kuma zaku gani ba".... Sauke wayan yayi ya baza mata ido, bin ta kawai yake da sassanyar kallo wanda shi kaɗai yasantasirin da yake da shi a inda ba'a faɗa, lumshe ido yayi yana me addu'an sama mata sassaucinhalin da take ciki a zuciya, turo ƙofar ɗakin Hajiya tayi a natse ta shigo baki ɗauke da sallama, amsawa yayi a hankali tare da buɗe ido ya zube mata, "ya jikin nata!" Tace idonta akan shi, "Alhamdulillah" yace a hankali tare da juyawa ya kalleta... "Taso muje ka samu ka saka abinci ko ba yawa a cikin ka" tayi magana a mugun sanyaye idontaakan shi, girgiza kai yayi tare da faɗin "ba na jin yunwa" "ba dan kana ji za ka ci ba, dan maganinwani cutan ne" jinjina mata kai yayi a natse tare da miƙewa a natse ya doshi hanyar barinɗakin, miƙewa Hajiya tayi ta dafa mai baya cike da tausayawa.... Tun daga wannan rana su Yasmin suka ɗau hankulansu kacokan suka maida ga shagulgulanbiki, duk da a wani lokacin sukan faɗa damuwar rashin zuwanta ko na jinta a waya amma in suntunakalaman SSB na cewa zata zo in sha Allah, se su sami sassauci, yau ki manin kwanaki biyar kenanda zuwan su Khadijatu, saura kwana biyu a ɗauka aure.... Ta ɓangaren Hajiya Insu da Alhaji SSB kuwa jinya ta sha sosai wanda ya fiddata daga hayyacinta, SSB ke kula da ita tun daga kan tsaftaceta ba ta abinci ba ta magani, ba wanda ya bar wani yamata, ajiye fita office gefe yayi ya maida dukkan hankalin shi gareta, Alhamdulillah sauƙi yasamu takan iya shiga toilet da kanta ta wanke jikinta, ta ci abinci da kanta duk da ba wani abincinkirki take iya ci ba.... Yau ta kasance ranar mother's day na bikin Farisat, tunda aka umurci amarya ta fito fili Farisat ke zubda hawaye, kuka take me taɓa zuciya su Yasmin na taya ta, ba abinda suke tunawa seAnty, so kawai suke su ganta ko na daƙiƙu ne a wajen tana bin su da kallon nan nata me cike daƙauna, ba yanda ba'ayi da su ba akan su yi shiru amma sun kasa, goge hawaye Lailah da ta taso tashigowajen tayi cikin na ta raunin tace "shin mu ba ku ɗauke mu iyaye ba ne?" Girgiza kai suka yi cikeda tashin hankali tare da kallon ta, "in kun tuna ta ku dinga mata addu'a ne, kuka tashinhankali ba maganin da ze muku, in sha Allah tana cikin aminci" jinjina kai suka yi cike da gamsuwa, "AntyLailah na so Anty ta ga wannan ranar, yana daga cikin manyan burikanta, se dai Allah be ƙaddaramata gani ba" Farisat tace tare da fashewa da raunataccen kuka, "mun ganin mata" Khadijatutata shigo wajen tace tare da goge hawaye, "kafin ta tafi se da ta bar muku iyaye uku in wannantagaza ku je wajen wan can" Salwa da ta shigo tace tare da sakin murmushi tana goge hawaye, murmushi suka saki tare da bin su da ido, ƙarisowa suka yi suka rungumesu cike da so da ƙauna, nan murmushi ya maye gurbin kuka, zare jiki Yamsin tayi ta fice daga wajen a natse.... "Yasmin" Laɗifa tace da ƙarfi, juyawa inda sautin kiran ya fito tayi a natse, yafutota tayi taredasakin murmushi, ba musu ta isa wajen a natse, jerin ƴan Aminan juna ne zaune a wajen kowaidon shi akan fili, "please jeki da little ya yi fitsari" jinjina mata kai tayi ta amshe shi tare dafaɗin"ya daina ƙiwuya ne?" "Yana yi, kin ci sa'a ne" tace tare da sakin murmushi, wucewa tayi anatseba tare da ta kalli ɓangaren da su Shureim ke zazzaune ba, bin ta yayi da ido cike da karaya, murmushi Annur ya sakin mai tare da riƙo hannun shi.... Tana dosan gida ta tadda Nafisat da sauran yara sa'anninta na fitowa, ina zaku?" Tace taredakallon su, "gidan Ummi" Nafisat tace tare da ƙarisawa kusa da ita da sauri ta miƙa ma littleShureim hannu, "okay jeki da shi yayi fitsari zan amso sako a gate" ta idda maganan tare damiƙamata shi, amsan shi tayi suka wuce ita ma ta wuce na ta wuri.... Ajiye ma Harira dake zaune saman one seaten parlorn Mommy lemu da ruwa Safinat tayi taredafaɗin "wallahi ban yarda da gaske kin zo ba se da na je gate na ganki" murmushi ta saki cikedakamalanta tare da faɗin "na taɓa ce miki ki zo gani ki ka je baki taddani ba?" "A'a amma ai damamaki" "to daina tunda ga dai ni kin ganni" dariya ta saki tare da faɗin aiko ga ki" tana kai nanta ɗago kofi ta buɗe lemu ta tsiyaya mata tare da ajiye mata a gabanta.... "Hala sha'ani ake a anguwar na ku?" Tace tare da ɗauka ta kai baki, murmushi ta saki taredafaɗin "wallahi brothern mu ke aure, shi da sister Farisat ai kin ganeta ko?" Da mamaki ta kalletatare da faɗin "a'a banganeta ba, yanzu brothernku ze yi aure ko gayyata babu! Da ban zonagani ba ma da shikenan wataƙila" tace cike da mamaki, "haba zan sanar mana, wallahi sha'afa nayi, kin san shine na farko duk ba me natsuwa" murmushi ta saki tare da faɗin "kin kyauta" "sorrynasan ban kyauta ba, amun afwa, jibi yinin biki da dinner" "ba mu zuwa" tace tare da hararanta, "sorry uzuri zaku mun" tace cike da magiya.... Harara ta dallamata tare da faɗin "zamu duba" "Allah yasa ku duba da kyau" tace tare da sakindariya, dariya ita ma ta saki tare da bin ta da ido, shigowa su Nafisat suka yi suka wuce ɗakinSalman kai tsaye, saka little Shureim tayi yayi fitsari, ta saɓoshi suka fito dan zuwa idda maUmmi saƙon da Jummai ta aiko su dashi.... Ajiye kofin tayi a natse tare da gyara zama, "bari in ƙara miki" Safinat tace tare da ƙoƙarinzubawani lemun, saurin jan kofin baya tayi tare da faɗin "a'a wallahi ya ishe ni" tayi maganantaredaƙoƙarin dakatar da ita, "a'a dan Allah me ki ka sha?" "Na sha mana" tace tare da kare kofindahannu, "to shikenan" tace tare da maida bottle ɗin ta ajiye, murmushi ta saki tare da faɗin"kokefa" murmushi ita ma ta saki tare da bin ta da ido, gyara zama ta kuma a natse tare da faɗin"akwai abinda ya kawo ni, amma dan Allah ina so ki sirrinta sunana" da mamaki Safna ta dubetatare da faɗin "kin sa ƙirjina bugawa, Allah yasa lafiya dai!" Ta idda magana a tsorace, "to agaskiya ba lafiya ba" tace idonta akan ta, ja Nafisat dake yunƙurin wuce wa tayi ta tsaya taredabin su da ido.... "Subhanallah! Me ne ne dan Allah!" Safna tace kamar zata saki kuka, "a gaskiya na kasa cigabada dannewa ne, a da Mama tace in bar maganan wa zuciyata na bi shawararta se dai a kwanakinnan ina yawan mafarki da wata baiwar Allah na cikin matsanancin hali, shiyasa na yanke shawaran zuwa in sanar da ke ki sanar da makusantar ta, amma dan Allah kar sunana ya fito" taidda maganan cike da rauni tare da kallon Safinat, jinjina kai tayi cike da ƙosawa tare da faɗin"ina jinki" "ina yarinyar barrister Amina da ki ka ce tana ɗauke da Heart problem?" "Um'hum- um'hum" tace a hanzarce tare da jinjina kai, zare ido Nafisat tayi tare da miƙa ma ta kusa daitalittle Shureim dan yanda jikinta ya ɗau ɓari "ita ce Sa'adatu ta canzawa magani lokacin dazata tafi school" "what!" Nafisat da Safinat suka furta baki a haɗe idanuwa a waje, kallon Nafisat dahawaye suka wanke wa fuska nan take tayi cike da fargaba tace "wallahi da bakinta ta faɗamin, na so sanarwar Safinat amma Mama tace kar in fara saboda za ta iya cutar dani in taji magananya fita" ta idda maganan tare da goge hawayen da suka gangaro mata... A sittin Nafisat da Safinat suka fice parlorn, Nafisat tayi waje, Safinat tayi garden inda suSalmanke zaune suna tsara dinner da za'a yi,, yanda take gudun kawai ya isa sanar da a matuƙar firgicetake, damƙo Yasmin da ba ta daɗe da dawowa ba tayi tana sakin numfarfashi tare da faɗin"Insu! Insu!!" Kafe ta ido tayi cike da mamaki tare da faɗin "ta zo!" Girgiza kai tayi hawaye na tsereasaman fuskanta, "wannan wani irin iskanci ne! Meye!" Tace a tsawace, "Sa'adatu ta kasheInsu!" Tace da ƙarfi tare da fashewa da kuka, wani gigitaccen mari ta kwasheta da shi tare da turetadaƙarfi, nan tayi taga-taga ta faɗi tare da sakin razanan nan kuka, ba kukan marin da hankaɗatanda tayi take ba, kukan abinda ya sami Insu take yi.... Tana shiga garden ta wuce inda ta hango shi tare da faɗin "brother! brother!!" Ɗago kai yayi damamaki tare da faɗin "lafiya!" Duƙewa a wajen tayi tare da faɗin "Sa'adatu ta kashe Insu, tacanza mata magani lokacin da za ta tafi school" a matuƙar razane Salman da Sadamsuka miƙetare da kallonta a rikice, da gudu Sadam ya isa gareta ya ɗagota a rikice ya girgizata tare dafaɗin"inji wa!" "Harira" tace cikin rishin kuka, sakinta yayi ya fice a sittin.... Nan da nan hankulan jama'a ya dawo wajensu da sauri su Shureim suka shiga wajen, sunniyyantambayan me ke faruwa Sadam ya iso a rikice tare da kallon su, kafin ya jefa kalma ɗaya Salmada Safinat da Harira sun ƙariso, "me ke faruwa!" Muryan Yaya da kukan Nafisat ya fiddo dashi yace tare da ɗaga Nafisat dake riskan kuka, "kaji abinda tace mun Yaya!" Yasmin tace taredaisakusa da shi "wai Insu ta rasu, Insu fa tace ta rasu!" Ta idda maganan da ƙarfi tare da kallonYayada ya bi ta da ido, "me!" Farisat tace ido da baki a sake tana kallon su, girgiza kai Salmanyayi tareda faɗin "ba ta rasu ba" "me ya sami Insu! Yaya Salman me ya faru!" Yasmin tace tare da juyawainda yake.... Girgiza kai yayi tare da faɗin "ban sani ba Yasmin, yanzu Safinat ta zo tana faɗa mana wai Sa'adatu ta canza maganin Insu lokacin da zata tafi school" ya idda maganan a tsorace, "me!" Suka ce a razane tare da kallon shi, jinjina kai yayi ido na zubda ruwan ƙwalla, a guje Yasmintayi kan Safinat kamar taɓaɓɓa tare da faɗin "Safinat waya faɗa miki! Yaushe ne!" Ta idda maganantare da girgizata tana kuka me taɓa zuciya.... "Harira ne gata yanzu ta faɗa min" tace cikin rishin kuka, kallon da suka bi ta da shi yasatafaɗin"eh haka tace ita da kanta ta canza da Dr ya kawo ta saka wani" tayi maganan a tsorace, kukaFarisat Yasmin Sa'adatu Sahabee Sadam Sa'eed suka saki a tare idanuwan su akan Harira, "tacesaboda wai Sudais yace yana sonta ne, ba zata bar duk wanda Sudais ya furtawa kalmansoba" salati Babiya dake sharar ƙwalla ta saki tare da faɗin "wannan yarinyar a she ba haka ta tafi salinalim ba se da ta sare mu, sara me munin gaske" "shikenan Insu ta mutu, na san ta daɗe damutuwa ɓoye mana suke" Yasmin tace tare da sakin firgitaccen kuka, kamota Yaya da ya shigashock da jin kalaman Harira lokaci guda yayi tare da faɗin "shii ba ta mutu ba" "Yaya ta mutu, Insu na raye cikin ƙoshin lafiya ba zata taɓa jira har yau ba ta zo bikin Farisat ba, duk hotunandavideo's ɗin da na tura mata ba wanda ta duba, ko ciwonta ya tashi takan ɗau waya, ba ta turomunsaƙo a waya ba ta jira na tsayin kwanakin nan Insu ba zata taɓa wuni ba ta ji lafiyana ba, Sa'adatu ta kashe mana Insu! Shikenan, inna lillahi wa inna ilaihirraji'un, me muka mata dazafi haka! Wani soyayya ba mu nuna mata ba, har yau in Insu ta kira se ta tambaye ni ita, inna lillahi wa inna ilaihirraji'un" ta idda maganan tare da zamewa ƙasa ta zauna daɓas tana cigaba dagabzan kuka me taɓa zuciya.... Farisat kuwa kamar taɓaɓɓiya haka ta koma, se da Habiba ta riƙota ta fara tofa mata addu'o'i sannan ta fara samun natsuwa, su Nafisat kuwa haɗa kai suka yi suna rera nasu kukan gununban tausayi, Sadam kuwa a wannan lokaci mace ya koma dan kuka yake kashirɓun kamar mace, ba wanda ba su ba tausayi ba a wannan wajen daga masu share hawaye se waƴanda ba susamudaman sharewa ba, haƙuri Yaya yake basu yana share na shi hawayen a fakaice, zaro waya Suwaiba tayi ta danna number babban ɗanta ta kara a kunni, yana ɗagawa tace "kwaso manazugan motan ƴan daba ako ina suke zamu biyasu za su yi aikin lada yau" tana gama faɗanhakatasauke wayan tare da faɗin "kuka ba namu ba ne, in ta tafi inda ta tura ta se mu yi zamankukan" miƙewa Yasmin tayi tare da faɗin "da hannu na zan kashe ta kada wani ya taɓe ta" ta iddamaganan a kausashe tare da nufar barin wajen, saurin riƙota Shureim da ya tabbatar da ayanayin da take za ta iya aikata fiye da abinda ta furta yayi tare da faɗin "tsaya" fizge hannuntatayi a fusace ta hankaɗashi tare da faɗin "waye kai!" Riƙota Yaya yayi tare da rumgumetatsamtsam, dan yanda yaga jikinta na ɓari.... "Kun san inda take ne?" Jummai tace tare da kallon Suwaiba, "zata wuce gidan ubanta ne?Kumaai sun je ko Sahabee ze gane gidan" tace a fusace, "ba ta can" Harira tace a hankali, "damawandake da ɗabi'u irin nata ai gidan uba yayi mishi kaɗan" Munari tace tare da share hawaye, "amplease ku ɗan saurara, inda wanda ke da numberta a cikin ku ya ba mu zamu bincika mugakozamu gano inda take" Shureim yace tare da bin su da ido.... "Wake da shi?" Habiba tace cike da jin daɗi, girgiza kai Farisat tayi tare da faɗin "ba na da shi" "kaifa Sadam?" Tace idonta akan shi, girgiza kai yayi ba tare da yace komai ba, ke fa Yasmin?" Fashewa da kuka tayi cike da ƙunan zuci tare da haɗa kanta da ƙirjin Yaya, "Nafisat" girgizakai tayi tare da faɗin "ban da shi" "246..." Sahabee ya zayyano da ka tare da goge hawaye, miƙawaShureim tracking phone ɗin da ya kwafe number Annur yayi tare da faɗin "ba tayi nisa sosai ba" "okay" yace tare da kallon inda na'uran ya nuna musu, juyo da duban shi gare su yayi taredafaɗin "dan Allah ku kwantar da hankulan ku, zamu tabbatar da ta amshi hukuncin abinda taaikata, ku je ku yi sallah" "zani" Yamsin tace idonta ƙyam akan shi tare da zame jikinta a naYaya"kallon sakanni ya mata tare da faɗin "okay ki gabatar da sallah tukun" yana kai nan ya wucedantafiya masjid, gida suka nufa gaba ɗayan su a guje dan ko waccen su na son zuwa.... Comments fans🥰🙏 🫀MUGUWAR TSOKA 🫀 {🫀TA'ARE KALLUƊE} [Muscle Cramp🫀] ) عضلة سيئة ( 🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_ https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 written and Created ~~~~~~~~~~~~~~ ِبسم الله الرحمن الرحيم By Yardajjiya👩 💻 Page. Thirty five Yaye bargon dake lulluɓe a jikinta tayi a hankali ta dira daga saman gadon da take kai a natse, takawa a natse tayi ta isa gaban ƙaramin jarkan dake bayan ƙofa ta ɗauka ta buɗe labulenɗakinta fice a natse, ganin tsakar gidan ba ko alamun kowa ya shige da customern shi ya sata sakanwani guntun murmushi me cike da takaici ta wuce ƙofar ɗakin Ziza, ajiye jarkan hannuntatayi agefe ta zaro key a haɓar zaninta ta saka a ƙofan, cike da fatanta kuwa ƙofar ya buɗu, nagartaccen murmushi ta saki ta ɗau jarkan ta tura ƙofan a hankali ta shige.... Bin su tayi da ido cike da ɗin bin takaici, Ziza da Sudais ne kwance saman gado sun faɗa duniyarharkan saɓon mahalicci ba sa ji basa gani, takawa a natse tayi ta tattara kayan su dake yasheatsakar ɗakin ta watsar a gefe, komawa tayi ta ɗau jarkan ta buɗe a natse ta yarda murfintayi kansu a natse zuciyanta na hanƙoro, ɗaga jarkan a natse tayi ta fara diddila musu abinda ke ciki, afirgice suka dawo hayyacin su saboda warin fetur da ya duki hancinansu, zare ido gaba ɗayansusuka yi tare da baza mata shi a matuƙar firgice... "Sa'adatu!" Sudais yace a mugun tsorace tare da ja gefe da sauri, "shii" tace tare da zaroi idowajeta ɗaura yatsanta a saman laɓɓanta, haɗiye yawun tsoro yayi dan be ga sauƙi a idonta ba, guntunmurmushi me cike da ka raina mun wayai ta saki ta ajiye jarkan a ƙasa ta saka hannu a ƙirji taciro kwalin shana ta ciro tsinke ɗaya ta nufi jikin a shannan da shi, zare ido suka yi a

Chapter 48 of 109