Share this page
Ali dake bin su da kallomecikeda mamaki yayi tare da faɗin "ina ga yakamata mu tafi ko?" "Ai ba su yanke sadakin ba" yacetareda kallon shi, "a'a ai duk yanda ku ka yanke yayi" ɗaya a ciki yayi saurin taran numfashinAli, murmushi Yaya ya saki tare da jinjina mai kai, miƙewa yayi a natse tare da yin gaba, kallonKabirYaya yayi tare da faɗin "bari in ganka" ba musu ya tashi ya dafa musu baya jiki a mace..... Murmushi Yaya da idon shi ke saman fuskanshi ya saki tare da faɗin "kar ka yi zargi, kar kumakayi shakku, ƴar uwanka zata faɗa hannu na gari, hannun da ya iya tarban baƙi cike da karamci" sauke numfashi yayi a hankali tare da faɗin "Alhaji kaman abun yayi wuri da yawa, kar muyi gaggawa mu aikata kuskure" "hakane Kabir ka yi gaskiya anan, se dai ka ɗauka haka na taaurenya zo, kasan kowanne aure da yanda yake zuwa, ka sa a ranka Iƙilima tayi sa'an da ba kowaccemace a cikin mata ba" bin shi yayi da ido cike da jin gamsuwar bayanin shi, "Yaya ga president ɗinƙasar mu shi ya turo a nema mai auren ta, saboda ya yaba da tarbiyyanta da hankalinta, ɗiyarmuInsu da ke tare da su ita ta ba su labarinta" Ali ya kuma cewa idon shi akan fuskan Kabir, zareidoyayi cike da mamaki tare da faɗin "Iƙiliman dai!" "Ita fa" Ali yace tare da sakin murmushi, kamabaki yayi dariya na kuɓuce mai, cike da farin ciki yace "Allahu Akbar, Baba Mama kuna ina?Kuzoku ji, inda Iƙilima za ta shiga, ku zo ku ji daga inda aka zo neman aurenta" ya idda maganantareda ɗaga kai sa6ka hawayen da suka cika mai ido suka bi yo kuncin shi.... Rungumoshi Yaya yayi tare da faɗin "kar ka damu, Allah shi ya shirya hakan, buwayan shi gabayin shi me yalwa ne" jinjina kai yayi tare da zare jikin shi da sauri tare da faɗin "yanzudamedame za su buƙata se mu samar" murmushi Yaya ya saki tare da faɗin "kar ka damu, ba sabuƙatan komai, ita kaɗai suke buƙata, ko za'a bukaci wani abun muna nan in sha Allah ba zegagara ba" murmushi ya saki hawaye na biyo kuncin shi tare da faɗin "mun gode sosai, Allahyasaka muku alheri da dukkanin hidimomin ku gare mu" murmushi Yaya ya saki tare da ba shi hannu suka yi musabaha ya juya ya shige mota ba shi hannu Ali yayi suka yi musabaha ya shige, jan mota Habibu yayi a natse ya bar anguwan.... "An tsaida!" Sadiya tace cike da zumuɗi tare da ajiye ma Kabir dake zaune fuska cike da murmushi ruwa idonta akan shi, jinjina kai yayi tare da faɗin "nan da sati ɗaya Iƙiliman Mamazata zama amarya" "sati ɗaya!" Suka ce baki a haɗe se dai kowa da dalilin da yasa ya furtahakan, jinjina kai yayi tare da bin su da ido, murmushi Sadiya ta saki me faɗi tare da rungume Iƙilimadatayi suman zaune, "wayyo daɗi, Allah mun gode maka, yanda kasan na jawo kwanakin" Sadiyatace cike da farin ciki, "sati ɗaya Yaya Kabir be yi kusa ba!" Iƙilima tace tare da zare Sadiyaajikinta jiki a mace, "ni ma na ce yayi kaɗan se dai Alhaji Abdussamad yace kar mu damu, mubi abin da addu'a da fatan alheri" jinjina kai tayi jiki a mace ta miƙe a hankali ta shige ɗaki, dariyaKabir da Sadiya da suka bi ta da ido suka saki tare da kallon juna.... "Gajiyan ne har yanzu?" Yasmin tace idonta akan Insu cike da kulawa, kwaɓe fuska tayi taredafaɗin "wallahi Mahmah, da zan yi magana kuma a ce mun raguwa" murmushi suka saki taredakallon SSB da ke kallonta, "ba wanda ze ce miki raguwa, ai kun zaunu yau, 10 to 6 ai ba wasaba" Yasmin tace tare da sakin murmushi, "to Mahmah" tace tare da narke fuska ta kalli SSB, bandadanne dariya ba abinda su ke dan sun san so take ya tanka shi kuma ya ƙi tankawa, miƙewayayi a natse ya ƙarisa inda take ya cicciɓeta a natse ya kaita saman two seater's ya kwantar daita, duƙawa yayi akanta ya fara mata tausaya a natse, lumshe ido tayi cike da jin daɗin tausan, murmushi Alhaji Jamil ya saki tare da faɗin "barrister ya kira ni, sun yanke lokacin abunnannan da one week" zumbur Insu da maganan ya shiga kunninta ta miƙe tare da faɗin "wayyo daɗi" komawa da ita yayi ya kwantar da ita ya danneta tare da faɗin "kin gaji" "Nafsii please barni ingama jin maganan" tace tare da riƙe hannun shi.... Ɗagata yayi ya zaunar da ita tare da zama kusa da ita, "uncle Jamil muna jinka" tace a zumuɗe, "ai na gama" yace tare da sakin murmushi, "ban ji sauran ba, a dawo baya" tace tare da yunƙurinmiƙewa, danneta da hannu yayi tare da kallon ta, marairaice fuska tayi tare da kallon shi, kaudakai yayi alamun be ma san tana yi ba.... "Be ƙara cewa komai ba bayan wanda ki ka ji" Kamil yace tare da sakin murmushi, "yanzutoseme ya rage?" Tace tare da kallon shi, "se jiran ranar a ɗaura" Alhaji Munnir yace tare da sakindariya, "wayyo Anty Iƙilima har na hangota a ranar" murmushi Hajiya ta saki tare da faɗin"beyi wuri ba kuwa?" Tayi maganan idonta akan Alhaji Jamil, girgiza kai yayi tare da faɗin "be yi ba, ni na so ma nan da kwanaki uku ne kafin Abba ya fara zuwa makaranta, se barrister yace yayi kusa""to Allah ya sa hakan shi yafi alheri" tace cike da dattakon ta, "amin" suka ce bakuna a haɗe.... "Yasmin se ku je ku duba duk wani abun da ya dace, a side ɗin kusa da nawa zata zauna, nacebase sun kawota da komai ba saboda duba da lokacin da aka tsaida abun" "hakan yayi" Jabir yacecike da yabawa, "to in sha Allah, zan ma Kausar magana ta fini ido a tanan" Yasmin tace taredasakin murmushi, "zanje ni ma Mahmah" Insu tace tare da kallon Yasmin, murmurshi ta saki tareda faɗin "ba ruwana" tayi maganan tare da miƙewa tabar wajen, kallon shi tayi kaman za tasaki kuka, "kwanta in cigaba da miki tausan, "bana jin gajiyan" tace tare da tura baki ta miƙe tawuce, murmushi ya saki tare da kauda kai, da murmushi duk suka bi ta da ido, tana wuce wa, Kamil yace daughter rigima" dariya suka kwashe da shi tare da kallon SSB da ya nufo wajen, amsanMairah da tayi barci a hannun Nafisat da ta cika da mamaki naganan auren da aka yi na Iƙilimayayi tare da faɗin "jeki kwanta" ba musu ta miƙe ta sallame su ta wuce .... Zama yayi tare da kwantar da Mairah a ƙirjin shi, "kasan duk abinda al'ada ya tanar se ka yi ko?" Yayi maganan idon shi akan Alhaji Jamil, "ga ku me zanyi kuma" yace tare da hararanshi, "ni dai bani a ciki dan ina taya Anty na kishi" yace tare da kauda kai kaman ba shi ya faɗa ba, "munhutashshe shi in uku zaka kawo rana guda zamu tsaya da ƙarfin mu da lafiyar mu, dan ba mataya mara kishi kishi" Abubakar yace tare da sakin dariya, dariya suka saki tare da kallonshi, "magananka na kan hanya Yaya Abubakar" Kamil yace tare da mai alamun jinjina da hannu, "ahto, matar da ba ta san abinda ya kaita gidan aure ba me ne ne na kishi akanta, Allah dai yanunamana cikan sati" Alhaji Munnir yace tare da miƙewa, miƙewa SSB yayi tare da faɗin "ba dai zakarigani tafiya ba?" dariya ya saki tare da faɗin "zan rigaka duk da ina da bambanci da kai, kai zakararrashi da ban haƙuri ne, ni kuma zani a rarrasheni ne" dariya suka saki ganin yanda ya kafeAlhaji Munnir da ido, girgiza kai yayi tare da juyawa ya wuce a natse, bin shi da ido suka yi har yaɓacewa ganinsu, kwashewa da dariya suka yi tare da kallon juna, "ku fa kiyayeni" Hajiya tacefuska cike da murmushi tare da tashi ta wuce ɗakinta.... A hankali ya tura ƙofar bedroom ɗin shi hangota yayi kwance saman sofa, murmurshi ya saki tare da shiga ya rufe kofar a natse ya taka a hankali ya nufi gado kamar me tsoron wani yaji takun, shinfiɗe Mairah yayi ya ja mata blanket har wuya ya rage hasken wutan ɗakin ya nufetaanatse, ɗaga ƙafafunta dake miƙe akan sofan yayi ya zauna tare da ɗaurawa su a saman cinyoyinshi, duk abinda yake tana jin shi ta na bin shi da kallon gefen ido, amma ko motsi ba tayi babareya fahimci idonta biyu... Matsa ƙafan ya fara a hankali tare da faɗin "har yanzu gajiyan ne?" Tura baki tayi tare da kaudakai gefe, murmushi ya saki tare da saka hannu ya ɗani bakin a hankali, buɗe ido tayi da sauri saboda azaban da ya kai ma ƙwakwalwanta ziyara tare da miƙewa zumbur ta fara murza idotanaƙananun kukan taɓara, "Mairah tayi barci dai" yace a hankali, "to ba kai ne ba" tace baki a ture, "auh ba zaki daina turomun shi ba?" Yace tare da miƙa hannu, saurin kaucewa tayi tare dafaɗin"to meyasa ba zan bi su siyayyan ba?" "Saboda babu buƙatan zuwanki" yayi maganan taredajawo ƙafafunta ta nufeshi kai tsaye.... "Nafsii ina son zuwa ne" tace cike da shagwaɓa, "mun gama wannan maganan" yace tare dakafeta da ido, sadda kai tayi tare da faɗin "to zanje ɗakko amarya ko?" "A'a" "Nafsii!" Tacekamanzata fashe da kuka, murmushi ya saki tare da lakutan hancinta, "ke dake matsayin ƙirjinbiki ai sedai a zo a taddaki, ke ce me masaukin baƙi fa, ba kisan zuwa ake a tadda me masaukin baƙi aindatake ba?" Kallon shi tayi cike da son tabbatarwa, murmurshi ya saki tare da faɗin "zanje miki ɗaurin aure shikenan?" "Shikenan Nafsii ni ba inda zan dinga zuwa? Daƙyar fa in su Farisat zasukawo ta, akwai bikin ƙanwar Yaya Salman da za'ayi bayan sati da bikin, kuma ita ma nanza'akawota" "za su rakota kar ki damu, ki sha zamanki za ta zo ta taddaki har nan" yayi maganancikeda gajiya, ganin haka ya sata faɗin "shikenan".... "Yawwa Gorgeous tausan ya isheki ko ki na neman ƙari?" Girgiza kai tayi jiki a sanyaye taredafaɗin "yanzu ai ka fini buƙatan tausan, kwanta" tace tare da yunƙurin miƙewa, jawota yayi tafaɗajikin shi, "auch" tace tare da yamutsa fuska, "ko bakya son zuwa tarban Samir ne?" Yace a hankali dai-dai kunninta, zare ido tayi gaba ɗaya waje tare da ƙoƙarin ɗagowa, ƙin bata daman hakanyayi da dukkanin ƙarfin shi, "Nafsii kana nufin zani tarban shi!" Tace a rikice, "in sha Allah" yaceahankali, danne shi tayi da ƙarfi cike da farin ciki tare da haɗe bakin su ta fara ba shi ruwansumbata ko ta ina.... Kallon agogo dake ɗaure a tsintsiyar hannunta tayi ganin lokacin sauraran shari'ar ya kusayasata ɗago kai cike da damuwa tare da faɗin "lokaci ya gabato ga shi har yanzu Yaya be isoba" taidda naganan cike da damuwa, murmushi Yasmin ta sakin mata tare da faɗin "kar ki damu, yanahanya in sha Allah" ba ta gama rufe baki ba motan barrister Ɗan Asabe da ya je ɗakko Yayayafaka a wajen, yana fitowa ta tashi ta nufeshi da sauri, tana ƙarisawa inda yake ta rungumeshi ƙaƙam tare da faɗin "nayi kewa Yaya" murmushi ya saki tare da shafa bayanta cike da sodaƙauna, miƙewa Yasmin da Kausar suka yi suka nufesu.... Gaggaisawa suka yi cike da mutumta juna, "da sauran time muje daga can gefe dan mu ƙaratattaunawa dake" barrister Ɗan Asabe yace tare da kallon Yasmin, murmurshi ta saki taredajinjina kai, ba musu suka nufi inda ya nuna musu, waje ne tamkar garden tattare yake da natsuwa na musamman.... Ƙwanƙwasa ƙofar office ɗin da yake tsaye a gabanshi tare da jiran izini wani matashin lawyer dake sanye da kayan aikin shi yayi, ana ba shi izni ya murɗa ya shiga a natse, "barrister Ashirulafiya kuwa?" Wanda ke sanye da kayan alƙalai yace tare da kafe barrister Ashiru da ido, "yessir"yace a natse, "okay bismillah" yace tare da nuna mai kujera ba musu ya ja ya zauna.... "Me ke faruwa?" Yace idon shi akan shi, gyara zama yayi tare da faɗin "akwai gagarumar matsalamatuƙar ka amincewa buƙatun su Alhaji Sammani, shari'ar nan ba karabitin shari'a kamar yandasuka ce ba ne" "bangane ba Ashiru fito mun a mutum" Alkali yace tare da baza mai ido, saukenumfashi yayi da ƙarfi tare da faɗin "wacce ta shigar da ƙaran ƙanwa ce ga doctor SahabeeSadam wato president, sannan lawyern da ze tsaya mata ba barrister Ɗan Asabe ba ne kamar yanda muke tunani" "waye!" Yace ƙirjin shi na bugawa, "barrister Abdussamad Umar Bertuwane, iyalan Mr president duk sun halarci court ɗin nan, maza da mata, har matarshi ta zo idanundabamu gani ba ma ƙyar yake a court ɗin nan yau har da na mr president kuskure ɗaya ze iya jawomana matsalolin da ba mu san da zaman su ba".... Sauke ƙaƙƙarfan numfashi yayi tare da zaro hanky ya goge zufa cikin rawar baki yace "wani lawyer suka ɗauka?" "Barrister Kamal ne" "jeka turo mun shi" ba musu ya miƙe a natse yafice.... "Tun ɗazu suka iso, suna ciki" Kausar tace tare da kallon Yaya da ya tambaye su Alhaji Jamil, "karku samu damuwa, in sha Allah nasara na tattare da mu" "in sha Allah" Insu tace cike da damuwa, "barristern gobe ya da tsorata haka?" Yaya yace tare da sakin murmushi, kama hannunshi tayi tamatse tare da faɗin "Yaya rashin nasara a shari'ar nan ze iya tarwatsa rayukan mutane dayawa" "ki sa a ranki nasara na tare damu" yace tare da matse hannunta da ke cikin na shi, jinjinakai tayi tare da bin shi da ido, "yakamata mu shiga daga ciki" Yaya yace tare da miƙewa riƙe da hannunInsu, mimmiƙewa suka yi suka dafa musu baya, suna shiga cikin ɗakin shari'ar suka hangi suAlhaji Jamil da suka daɗe da zuwa, nan suka ta so suka fara gaisawa cike da kamlansu.... "Yes sir" barrister Kamal yace tare da tsayuwa a gaban me shari'a "zauna" yace a natse taredanuna mai kujera, zama yayi idon shi akan shi, "nawa su Alhaji Sammani suka baka akan wannanshari'ar?" Ya jefa mai tambayan a dake, murmushi ya saki tare da sadda kai ya fara sosa ƙyeya, "tell me stupid" yace da ƙarfi, "biyar ce ba yawa yallaɓai" "to in zaka iya maida musu ka maidamusu ka fuskanci aikin ka matsayinka na lawyer, in ba zaka iya maidawa ba, ka ta na ji matakankare kai sannan ka tsaya akan aikin ka" "bangane ba sir!" Yace cike da mamaki dan yasanshi kesasu a duk wata hanya, "wannan shari'ar ta sha bamban da waƴanda ka saba fuskanta, dashugaban ƙasa za su yi shari'a, idan ka shirya tsiraran kuɗi su tarwatsa maka rayuwa banadamatsala game da hakan, na kira ka na sanar da kai illar da biye ma manufarsu ze iya illatarayuwarka ne saboda kasantuwan ka na ɗan hannu me biyayya" share zufa yayi tare da faɗin"nagode sir, se dai kuɗin nan ba ze maidu ba, dan na tsakuri wani abu daga ciki" ɗage kafaɗayayi tare da faɗin "dama bance dole ka maida musu ba, Allah ne ya matsesu suka ba mu na mukason"murmushi ya saki tare da miƙewa cike da girmamawa yace "lokacin zama ya cika sir" "okayganinan" jinjina kai yayi ya fice da sauri..... "Duba da nazarin tsanaki da court tayi bi sa hujjoji da bayanan da lawyer me ƙara ya bayar masuƙarfi, court ta gamsu da dukkanin hujjoji da bayanan, sannan ta ba wa ƙannin marigayi Alhaji Sagiru kwana bakwai da su tattaro gadon magada wanda suka taɓa da wanda ke hannunsu, sudawo dashi gaban court inda court za ta miƙa gadon zuwa shari'a court dan rabawa magadahaƙƙinsu yanda addini ya shar'anta, sannan court ta yarjema mahaifiyarsu cigaba da juya gadon da kula da shi ga mahaifiyarsu, sannan ta maida mata da yaranta dake hannun su gaba ɗayatacigaba da rainonsu, Allah ya ba ta ikon tarbiyantarsu bi sa tafarki madaidaiciya amin" yanakai nan ya miƙe ya fice, rungume Yasmin Insu tayi da ƙarfi tare da danne bakinta da hannu dantasan za ta iya sakin ihu, nan fuskokin su ya yalwata da murmurshi me cike da farin ciki, na suAlhaji Sammani kuwa kaman ze yi aman wuta, haka suka shiga taya juna farin ciki a wajen, sedasuka yi me isarsu sannan suka tattaro suka fito farfaɗan wajen, wuce wa wajen Yaya daketsayekusa da motan barrister Ɗan Asabe Insu tayi da sauri.... "Ma sha Allah Yaya, nasara mu ta kawowa ziyara" Insu tace cike da farin ciki, murmushi yasaki tare da bin ta da ido, ƙarisawo wajen Yasmin tayi ta mai godiya cike da jin daɗi ta wuce, tundataiso wajen suka fara magana Insu ke bin su da ido, tana wuce wa ta matsa kusa da shi taredafaɗin "Yaya Anty Yasmin na da kirki ko?" "Sosai kuwa" yace tare da sakin mata murmushi, murmushi ta saki tare da bin shi da ido, kafeta da ido yayi cike da zargi, ganin yanda murmushinsaman fuskanta ya kasa ɓacewa ya sa shi faɗin "kar ki yarda da zancen da zuciyarki ke sanriyamiki ba ze taɓa yuwuwa ba ƴar albarka" yayi maganan cike da kulawa, "meyasa Yaya!" Tacecikeda mamaki, "saboda Abdussamad dan Insiyyat aka haifeshi ta fuskan aure" "amma Yaya Antybata raye, kuma cikan kamalan ka ne ka kasance da mata" tayi maganan cike da rarrashi, shafakanta yayi fuska cike da murmushi tare da faɗin "Abdussamad baya da wata mata a duniyabayan ita, ta mutu ba shine ke nufin ta mutu a zuciyata ba, ba zan taɓawa wata mace adalci baindai ba ita ba, barrister Ɗan Asabe ya yaba da hankalinta tun ranar da yaje tattara bayanai, idanhakan ze yuwu ki shigar da zancen shi a gare ta" "to Yaya in sha Allah" tace idonta akanshi.... Murmushi ya sakin mata tare juyawa, "samun miji kaman ka a duniya ze yi wuya Yaya" taceahankali, murmushi ya saki tare da juyowa, murmushi ta sakin mai tare da gyara tsayuwa, "babuwuya Insu ga Uncle ɗinku, ɓata tsayin shekaru yayi dan jiran zuwanki, shima jarumi ne" murmushi ta saki tare da faɗin "be kai Yaya jarumta ba" murmushi ya saki tare da shigewamotana natse, ja baya tayi idonta akan shi ƙarisowa wajen Alhaji Jamil yayi da sauri tare da faɗin"dagaske yanzu zaka koma ba zamu je gida ka huta ba?" Murmushi ya saki tare da faɗin "akwai shari'ar da zan sauka akai ne in na koma, tunda na samu jirgi bari in gaggauta" "shikenansemunyi magana" yayi maganan tare da ba shi hannu, ba shi na shi yayi tare da faɗin "se mun gankudai" fuska cike da murmushi, murmushi ya kuma saki tare da ja baya ya bi motan da ido kamanyanda Insu tayi har suka fice daga wajen.... Juyawa tayi jiki a mace, sauke ido akan Yasmin dake tsaye da Alhaji Sammani kai a ƙasa tayu, daalamun zazzaga mata masifa yake yi, ƙarisawa wajen tayi da sauri, tana isa ta ɗaure fuskataredafaɗin "lafiya kuwa Mahmah!" Ta jefa tambayan fuska a ɗaure, ɗago kai tayi ta sakin mata murmushi tare da faɗin "ba komai muje, ina Anty Kausar din?" "Tana mota jeki gani nan" tayi maganan murya ba wasa, wuce wa tayi ba musu, tana barin wajen ta ɗago kai ta zube a samanfuskan shi tare da faɗin "ku kauda idanunku a saman fuskanta, ina nufin rayuwarta da na ƴaƴanta, matuƙar zuciyoyinku suka kasa haƙurin kaudawa zan shayar da ku mamakin da har kumutu ba zaku manta ba, ba ruwana da alaƙan da ke tsakanun ku da mariganyi" tana kai nantajuya a natse tabar wajen, murmushi Kamil dake tsaye a gefen ya saki tare da bin ta da ido, tanashiga motan driver ya ja su suka bar wajen.... "Se me dan sun cire hannun su akan yaran! Dan Allah daina damun kan ki" Kausar tace hankali akwance, "a'a Kausar iyayene su dole nan gaba yaran su buƙace su musamman in auren suyataso" Hajiya tace tare da kallon Kausar da ke kallonta, "mun yafe musu, ba ma buƙatan su, akanyo hayan iyaye a titi ma in ba'a da na gari su yi walicci bare su masu iyaye birjik se wanda sukadarza ze tsaya musu" Insu dake sakkowa daga up stairs tace saɓe da Mairah, murmushi Kausar tasaki tare da faɗin "wallahi Insu" miƙama Kamil Mairah tayi tare da faɗin "har yanzu ba'a ɗakkoyaran ba ne?".... Ta idda maganan cike da zallan mamaki, murmushi Yasmin ta saki tare da faɗin "mu jira sukawosu" "ba jiran da zamu yi, wallahi dan yanzu dare yayi ne, amma gobe da sassafe za'a ɗakkosu" tana kai nan ta wuce gefen Alhaji Jamil ta zauna, "to za'ayi sirri kenan" Jabir yace tare da sakinmurmushi, "kaiii uncle Jabir!" Tace tare da kallon shi, murmushi ya saki tare da ɗaga hannusama, "uncle Jamil ka turawa Farisat kuɗin gyaran jikin da kitso da lallin da amarya za ta yin?" Murmushi ya saki tare da faɗin "na tura mata ta kira ta yi godiya" murmushi ta saki tare damiƙewa cike da farin ciki tace "mun gode uncle Jamil Allah ya ƙara arziƙi" ta idda maganantareda zama kusa da Kausar.... "Amin" suka ce bakuna a haɗe, "tunda yanzu yara za su dawo wajenki, se ki fara tunaninyandazaki inganta rayuwarki" Kamil yace idon shi akan Yasmin, murmushi ta saki tare da faɗin"YayaKamil kenan" "auh Yaya Kamil kenan!" Yace tare da riƙe baki, "da fa gaskiyan Kamil Yasmin, baki wuce auren nan ba Malama, ki buɗe zuciyarki ki ba manema dama, dama abokin Abbansutunzuwan da ki ka yi mu ka yi jinyan Sabir ya ƙyasa se maganan yake ma Abbansu" zare ido tayi tareda kallon ta, "wallahi" tace cike da gaskiyanta, "ai ba wannan maganan Anty Kausar, wannanlodin yaran ina zan kai su? Ke ma kin san ba zan zubda su in tafi aure ba" "to aimata uwar marayu" tace tare da banka mata harara, murmushi Jabir ya saki tare da faɗin "Yasmin fa tanadagaskiyanta Kausar, se dai ba zan goyi bayan ta ƙare rayuwarta haka ba aure da yarintar tabakuma, amma me ze hana mijin da zata fidda ya dinga bi yo ta gidanta kinga ba gidan shi banebare a ce ta kwashi yara ta je gidan wani da su" "hakan fa ba ze yuwu ba, wani mara saninciwonkan ne ze wani biyo mace zugui-zuguI gidanta, kenan ita ke auren shi ma ba shi ke aurentaba, kuma a gaskiya riban aure a ji daɗi a ga mutunci juna shine mace ta kasance a mahallindamijinta ya ajiyeta ba wai a wanda zata ajiyeshi ba" Abubukar yace cike da ganin abinda Jabir yacebe yi ba" murmushi Hajiya dake sauraran su ta saki tare da faɗin "to Allah dai ya zaɓa abindayafi zama alheri" "Amin ni dai a bani Suhailat" Kamil yace tare da kallon ta.... Murmushi ta saki tare da faɗin "ai taka ce" "to godiya nake" yace tare da sakin murmushi, "wai wasu yara ma ake magana dan Allah, ni banga yawan yaran da ba zata iya aurenta ba" Kausar tace rai ɓace, "ba fa yara wallahi" Jamil yace tare da kallon ta, "to yanzu ga Kamil ya ɗauSuhailat, Amjad da Aslam maza ne ko a wajen Hajiya za su iya rayuwarsu babu matsala, Anisa kuwaƙarama ce da ita ma zata iya tafiya gidan miji ba wani matsala" "gaskiya kin raba gardamaKausar" Alhaji Jamil yace tare da kallon ta, "aiko shikenan faɗuwa ta zo dai-dai da zama damabarrister ya gani ya ƙyasa" Insu tace tare da sakin murmushi, zare ido suka yi tare da kallonta, "wani barristern!" Kamil yace cike da mamaki, kallon yanda suka zuba mata ido tayi cikinsakanni na karanci tunaninsu, murmushi ta saki tare da faɗin "ba Yaya nake nufi ba fa" "auh" sukacecikeda samun sassauci, dariya ta saki tare da faɗin "in shine ma ai ba wani matsala" "a'a" Hajiyatacecikin taren numfashinta, "meyasa Hajiya!" Tace da mamaki, "ba aure tsakanin mijin Insiyyat daɗaya daga cikin su" "Hajiya Anty ai ba ta raye" tace da mamaki, "ana barin halas ko dan kunya, inba ta raye mu muna raye" murmushi ta saki tare da faɗin "to shikenan, barrister Ɗan Asabenakenufi".... "Ai na sani wallahi, tunda na ga yanda yake wani zabura da zabari na fahimci inda ya dosa" Kausar tace tare da sakin murmushi, "kai Kausar ido wato ki ka sa mai" Kamil yace tare dakallonta, "wallahi Kamil ya kasa natsuwa idon shi akan duk motsinta, "to ai kin ji ya fiddo muradinshi" yace tare da sakin murmushi, "yace ma Yaya yana son Mahmah in ta amince da shi ze aureta" "ai shikenan kuwa ya zo a yi magana da ma babu amfanin cigaba da zaman haka, amma matanshi nawa?" Kausar tace

Chapter 87 of 109