Share this page
"Yunusa dan Allah temaka mun da wayanka" "lafiya kuwa!" Yace a tsorace taredamiƙewa idon shi akan fuskanta, girgiza kai tayi tare da faɗin "please temaka mun" ba musuyaɗau wayanshi dake gefe ya miƙa mata, saurin fara jera number tayi jikinta na ɓari, tana kammalawa ta kara a kunni tare da juya dubata ga waje tana baza ido, se da kiran ta kusatsinkewa aka ɗaga daga ta can, sauke ƙaƙƙarfan ajiyan zuciya tayi tare da faɗin "zo buɗe munƙofa dalla" tana kai nan ta sauke wayan ta katse kiran tare da miƙa mai ta fice da sauri kodamayi mai godiya ba ta samu ba, da ido ya bi ta yana me mamakin abinda ya sata firgicewa haka, ganin ba me ba shi amsa ya sa shi ɗaga kafaɗa ya koma ya zauna a inda ya tashi.... Tana isa ƙofan ana buɗe ƙofan, kusan ture shi tayi ta shige da sauri tare da faɗin "kulle ƙofan" taidda maganan tare da shigewa ciki da sauri, rufewa yayi ya dafa mata baya a hanzarce, yanashiga ya tadda ba ta haɗaɗɗan parlorn, sa nufar bedroom yayi a hanzarce, yana shiga ya taddatatana ta faman tusa kaya a akwati a ruɗe, "lafiya baby!" Yace a ɗan rikice, "lafiya ka tattarakayanta da zaka iya buƙata ka koma gidanku zan neme ka in komai ya tafi dai-dai" tayi magananhankalinta akan kulle akwatin da take.... "Bangane ba! Alhaji ne ya zo? Sannan wannan ciwukan a ina ki ka ji su? Me ke faruwa dakene!" Ya idda jero mata tambayoyin tare da ƙoƙarin riƙo hannunta, ɗaga mai hannu tayi da sauri tareda faɗin "babu buƙatan waƴan nan tambayoyin haka ka je in kana son tsira da ranka da lafiyanka" ta idda magana tare da warware abayan da ta ɗago ta zare na jikinta ta zura, "bani wayanka" tace tare da miƙa mai hannu babu musu ya ɗakko ya miƙa mata.... Jera number tayi ta danna kira ta kara a kunni, ringing biyu aka ɗaga, "Ziza ki na ina?" Taceahanzarce, "gida lafiya kuwa!" Tace cike da mamakin yanda ta ji muryanta, "babu ita wallahi muhaɗu a can yanzu kar ki bar ni ina jira" tace tare da zare wayan ta katse kiran ta miƙa mai wayan, "zaka ji alert" tace tare da ɗaukan hijabin da ta ciro har ƙasa ta zura ta ja akwatin da sauri tanufi ƙofa, saurin biyota yayi cike da rashin fahimtar komai, juyowa tayi ta kalleshi da mamaki taredafaɗin "baka da abin ɗauka ne?" "Eh" yace a sanyaye, jinjina mai kai tayi ta fice yana fitowatakulle ƙofan ta juya da sauri ta tari napep ɗin da ya zo wuce wa, shigewa tayi ta faɗa mai indazekaita, ganin yana tsaye yana bin ta da ido ya sata faɗin "shigo" ba musu ya shiga.... Suna isa bakin wani haɗaɗɗen hotel ya taka burki, sauka tayi da sauri tare da faɗin "ka ƙarisadashi inda za shi ze baka kuɗin" jinjina kai me napep ɗin yayi ya wuce suna ɓacewa ganinta tajuyata tari wani napep ɗin tana hawa tace "Masna hotel" ja yayi hankali kwance suka nufi indatace, suna isa ta sauka ta zage jaka ta ciro mai haƙƙin shi ta ba shi taja akwati tayi ciki tare da waigenbaya, tana shiga reception ta hango Ziza zaune cikin wani arnen shiga tana jiran isowanta, amsankey tayi ta musu transfern haƙƙin su suka wuce ciki... "Lafiya kuwa! Meyasa me ki haka?" Ziza tace tare da jawota bayan sun shiga ɗakin, "akwai babban matsala" tace tare da zare hijabin dake jikinta, "na fahimci hakan a muryanki, sannanamagananki ma na fahimci wani abu ba dai Shila ba ce ta fiddo makaman yaƙinta a fili ba!" Tayi tambayan a ɗan tsorace, girgiza kai tayi tare da faɗin "wannan me sauƙi ne, ina da maganinta" "daga ina matsalar take!" Tace da damuwa, "Yaya Sarari!" Tace a tsorace, "Baba!" Tace a tsorace, jinjina mata kai tayi tare da faɗin "ya mutu" ta idda maganan tare da furzar da huci, "inna lillahi!"tace a ruɗe, "ba wan nan ne damuwar ba, Yaya Sarari ya yi alwashin sare mun ƙafafu kumazeiya, sannan wannan raunin da ki ka gani a jiki na yaransu ne suka mun" "subhanallah to akanme!" Ziza tace da mamaki, "saboda Baba ya mutu" tace tare da wuce wa ta zauna daɓas... "To ke ki ka kashe shi? Lokacin shi ne yayi ai" tace cike da takaici, "ba su fahimci hakan ba, doleinyi nisa da garin nan na wasu kwanaki kafin abun ya lafa, dan na san za su shiga nema na idobuɗedan cika burin su" "to ina zaki?" Tace cike da damuwa, "Yarban dole in komawa Alhaji Haruna" tace tare da kallon ta, "akwai matsala a wannan shawaran, bakar ki manta burin shi na mallakanki gaba ɗaya ne, ga kuma maganan Abdull dake ƙasa" tace tare da kallon ta, girgiza kai tayi tareda faɗin "dole in koma, dan a can kawai zan iya samun kariyar da nake nema" "Abdull fa?" Taceidonta akan ta, shiru tayi kaman me tuna wani abu kafin tace "matsayin shi na nan ba abindazetaɓa shi, tafiyana ze sa ya kasance cikin aminci, ke dai ki tabbatar da shirin mu ya cigaba datafi yanda muka tsara, ayi komai zan dawo dai-dai da lokacin cikan burin" jinjina mata kai tayi cikedagamsuwa.... "Ga wannan makullin gidan ne, ki ba ma KB zamu yi magana da shi" jinjina mata kai tayi jiki amace ta amsa, "kin samu ganin Sudais ɗin?" Tace idon ta akanta, girgiza kai tayi tare da faɗin"sena dawo, zamu je mai ya jiki" murmushi ta saki tare da faɗin "kar ki manta zamu riƙe na sadaka" ƙaramar dariya ta saki tare da faɗin "bani wayanki" ba musu ta ciro ta miƙa mata, danna numbertayi ta kara a kunni tare da gyara zama.... Ana ɗagawa ta fashe da kuka me ƙarfi, tare da faɗin "zata kashe ni my Hero" a ruɗe daga canakace "waye!" "Shila za ta kashe ni, ban san me na mata har haka ba take son dole se ta rabani dakai, tunda na kai mata maganan auren mu take azabtar dani" "what!" Yace da ƙarfi, girgizakai tayi tare da faɗin "na fita siyayya wasu ƴan daba suka tare ni a hanya, ba dukan da ba sumunba, sun tararratsa mun mota da waya" ta idda maganan cikin rishin kuka, "lallai zan wukaƙantarayuwarta fiye da yanda za ta yi tunani, kina ina yanzu?" "Ina gidan Ziza" tace a hankali, "toki zauna a nan, zuwa gobe zan shigo garin" "a'a ba zan iya zama ba, ka nema mun jirgi in zo kusadakai, ba na son ƙara awa a garin nan, kai ne garkuwata my Hero, rabani a kai take son yi, bansanme za ta iya aikata mun zuwa goben ba" "shikenan kwantar da hankalin ki bari a nema miki ticket" yace cike da muryan rarrashi, jinjina kai tayi tare da sauke wayan... Kallon juna suka yi tare da fashewa da dariya a tare, nuna ta da yatsa Ziza tayi tare da faɗin"Sa'adatu ba kya da kyau" "haka nake ko nayi wanka ba na canzawa" tace tare da miƙewa tanufi telephone ɗin dake ɗakin ta danna kira dan ba da order, se a lokacin ta ji wani masifaffenyunwa, tana gama faɗa musu abinda take buƙata ta koma ta zauna suka cigaba da shirya abubuwandasuke ganin shi ze ba su mafita, ba bu jimawa aka yo knocking, ba da izini tayi a natse, ba musuma'aikacin ya turo keken da ya jero abinci ya shigo, yana gama shiryawa a saman madai-daicindining ɗin dake ɗakin ya fice, tashi suka yi suka koma wajen, suna cikin ci kira ya shigo wayan, ɗagawa tayi tare da ma Ziza alamun ta dakata, tsayawa cak tayi tare da zuba mata ido.... "Na turo miki ticket ɗin, nan da 30 minute's jirgin ze tashi" "okay" tace a hankali, "kar ki damu, itakuma zan san yanda zanyi da ita" "se na iso" ta yi maganan tare da zare wayan ta katse kiran, blocking din number tayi ta yi delete ta miƙa ma Ziza tare da faɗin "hanzarta mu tafi" jinjinamata kai tayi ta amshi wayan ta ajiye a gefe, haka suka ci abinci a gaggauce, suna ƙoshi sukamiƙe ko wacce ta ɗau abinda ta ajiye suka fice, key ta ba su suka fice farfajiyan wajen, napeptatsaida musu suka haye, kai tsaye airport suka nufa, suna shiga ana kiran sunanta, sallamanZizatayi ta wuce da sauri tayi ciki.... A kofar hospital suka ajiye Halima da Nafi, godiya suka musu suka shige ciki jikkuna a sanyaye, jan motan Salman yayi bayan sun ɓacewa ganin su suka ɗau hanya, gyara zama Sadamyayi tareda faɗin "wallahi ban so su bar wawiyar nan haka ba, na so kafin mu iso mu tadda me afkuwataafku yanda ko za'a ceceta an gama da shafinta" ya idda maganan cike da takaici, "ai akwai watarana inda rai kere na yawo zabo na yawo watarana za'a gamu, kai kana ganin barintazasuyi?Ai yanda suka zaro takubban nan maidawa ba yanzu ba se an buga faɗan ƙarshe" Salmanyacecike da tabbaci, "Allah yasa su mata mugun illa wanda za tayi ta nadama har ƙarshen rayuwarta"yace cike da fata.... "A dai dinga fata na gari ga musulmi" Farisat tace tare da waigawa ta kalleshi, "ai wallahi wannan kar na fiddata a musulunci ne a ce banyi dai-dai ba amma ta daɗe da fita a musulunci tuntuni, zuciyan sheɗanun kafiran farko ne da ita wanda suka ƙi amsan musulunci" yace cikedatakaici, dariya Farisat da Salman suka saki tare da kallon shi, "wallahi ku bar dariya, inda anhalatta mana kisa ga juna tsaf zan iya kasheta in rage mugun iri a duniya" "maida wuƙanmalamSadam, ance fa me sunanka salihi ne shiru-shiru ba ruwan shi" Farisat tace fuska yalwacedamurmushi.... "Haba Farisat dubi fa su Iƙilima, kallo ɗaya zaka musu ka fahimci irin halin da suke ciki, ammaitashegiyan na can ta tasa duniya a gaba" ya idda maganan tare da tunano ta, "akwai ƙarshentayana nan zuwa wallahi, irin su dama Ubangiji talala yake musu, yana tashi damƙarsu zaka gayandaza su koma ababen tausayi" Salman yace tare da kallon shi, "Allah ya tsare ni in ji tausayinwannan wawiyan" yace a ƙufule, "easy" Salman yace tare da sakin dariya ya daki steering, "wallahi" yace cike da tabbaci, "tare da Sa'eed ku ka dawo?" Farisat tace tare da juyawa kaɗantakalleshi, girgiza kai yayi tare da faɗin "yana can, an ba ma uncle Jamil shi".... "Bangane am ba shi ba, Sa'eed ɗin abin wasa ya zama da za'a ba da kyautan shi haka!" Tacedamamaki tare da kallon Salman, shima cike da mamaki ya kalli Sadam ta mirror, "wallahi yaroƙane, kuma kin san Yaya in dai abu be fi ƙarfin shi ba ka tambaya ya tabbatar babu me cutuwaaciki ze bada" "ikon Allah to me Insu tace!" Tace da mamaki, "me za ta ce kuwa? Me ɗa ya ba dakyautan abin shi, sannan ma ita ta miƙa ƙoƙon baran ga Yaya" ya idda maganan tare da karkacewa kaɗan ya zaro wayan shi da ƙarar message ya shigo... "Oh Allah na ma manta Uncle ya farfaɗo fa" yace idon shi akan wayan hannunshi, a sittinSalmanya taka burki, tare da Farisat da maganan ya doka suka juya ga Sadam, ɗago kai yayi da mamaki ya kallesu, "kana nufin ya farfaɗo farfaɗowa na gaskiya!" Farisat tace a zumuɗe, murmushi yasaki tare da faɗin "sosai duk an cire mai wannan na'urorin dake aiki a jikin shi, mun baro shi yanata bacci ma" ya idda maganan fuska na yalwatuwa da murmushi, "ma sha Allah!" Suka cebaki ahaɗe, "Allah ya ƙara mai lafiya" Salman yace cike da farin ciki, "wayyo daɗi ina wayana insanar ma Yasmin ko za ta samu sasauci daga halin da take ciki" Farisat tace tare da fara nemanwayanta, miƙa mata Salman yayi, da mamaki tace "ya aka yi ya zo wajenka?" "Tun lokacindamuka shigo gaisuwa ciki na ganshi a yashe na ɗauka, kin san me dukiya ba ya wasagareredashi"yayi maganan tare da shagwaɓe fuska, murmushi ta saki tare da faɗin "sorry" ta fara nemannumber Yasmin.... Suna shiga cikin parlor wayanta ya ɗau ruri, zama tayi ta buɗe jaka ta ciro, ganin me kiranyasataɗagawa da mamaki ta kara a kunni, zama Shureim yayi a kusa da ita cike da damuwan yanayindatake ciki, sallama ta yi a hankali, amsawa Farisat da suka shiga cikin anguwansu tayi taredafaɗin "albishirin ki!" da mamaki ta ciro wayan ta kalla, maidawa a kunni tayi tare da faɗin"mekefaruwa!" "Uncle ya farfaɗo!" Tace a zumuɗe, "Allahu Akbar" tace tare da fashewa da kuka, "kinji matsalarki ko, daina kuka Allah ya amshi addu'o'in mu ne" tace da kulawa, jinjina kai tayi batareda tace komai ba ta zaro wayan tare da ƙure shi da ido, ba abinda take gani a ciki se irinfarincikin da Insu za tayi "lafiya!" Shureim yace cike da damuwa, rungumeshi tayi ƙaƙamtare dafaɗin"Uncle ya farfaɗo" saurin zarota yayi ya kafeta da ido, jinjina mai kai tayi tare da sakin dariyamehaɗe da zuwan hawaye, rumgumeta yayi da ƙarfi tare da faɗin "ma sha Allah, a gaskiya nayi matuƙar farin ciki da jin wannan labarin, Allah ya sa ƙarshen wahalan kenan, na tabbata indai Insun mu ce damuwa ya gama ciwo har abada" murmushi ta saki tare da jinjina kai.... Sakinta yayi ya ɗagata ya ɗaurata a saman cinyarshi tare da faɗin "yau kunnuwan mu sunji abinda muke son ji da wanda ba ma so, haka rayuwa ta gada precious watarana mu yi farinciki watarana kuma mu yi baƙin ciki, a haka rayuwar take tafiya, mu yi haƙuri mu ma Baba addu'a, damuwa da kuka ba ze ba mu mafita ba, please kukan nan ne ban so" ya idda maganan muryaamarairaice, murmushi ta saki tare da sakin mai sumba a laɓɓa ta kuma sakin mai murmushi, murmushi ya saki tare da ɗagata suka yi bedroom.... "Kai waƴan nan yara sun yi rashi" Babiya da ta yada zango a parlor tace cike da alhini, "wallahi sune ababen tausayi Hajiya, shikenan babu uwa babu uba" Balarabe yace cike da jimami, "badangi tsayayyu kuma, da suna da dangi tsayayyu zamu iya cewa da sauƙi" Ali yace tare dakallonsu, "wallahi babu Ali, saboda silliɓanci irin na ƙannin Baban haka suka watse dan yace kar azauna zaman makoki suka watse, ko ɗaya ba su bari ta zauna da yaran ba, ina ko wannandangi ya ga haɗin kai, dangin Mamansu kuwa ko ɗaya ba mu gani ba, Allah dai ya fiddo musu mazajesutafi gidajen su wataƙila su daina ƙumsar takaicin duniya haka" ta idda maganan cike da takaici, "amen, na gari Hajiya waƴanda za su zame musu mazajen marayu" Ali yace cike da alhini, "damasu ake fata Ali ba waƴan nan ƴan bana bakwan ba" tace tare da jinjina kai.... "Na ce Abdussamad ka samu dawo wa da Sa'eed ne?" Babiya tace tare da kallon Yaya dakezaunekaman baya wajen, murmushi ya saki tare da ɗan ɗagowa kaɗan tare da faɗin "yana can, zeyi karatu a wajen kawun shi Jamil" "to ma sha Allah, Allah ya sa can ɗin shine mafi alheri a gareshi, aI duk gida ne, ba ma ƙi ba" tayi maganan cike da dattako, sadda kai Sahabee yayi cike da rashinjin daɗi, murmushi Yaya ya saki tare da faɗin "takwaran ka ya farfaɗo" ɗago kai yayi a zumuɗetare da faɗin "Uncle ya farfaɗo!" Jinjina mai kai yayi cike da natsuwanshi, nan farin ciki yamayegurbin damuwoyi, "Allah sarki bawan Allah, Allah ya tashi kafaɗunshi a she, Allah ya sa jinyandaaka yi ya zamto kaffara ne" Babiya tace cike da farin ciki, "amen" Yaya yace tare da miƙewayakama hannayensu suka yi side ɗin shi, da ido suka bi su.... Yana shigewa Ali ya gyara zama tare da faɗin "Hajiya me ze hana ki ma Yaya Abdussamadmagana akan yaran nan ya zaɓi ɗaya tunda gaba ɗayansu da hankalin su da natsuwarsu, jahadi ne babba auren su wallahi, tunda na ga sun shaƙu da yaran akwai fahimtar juna a tsakaninsuzasu zauna lafiya" ya idda maganan cike da fata, bin shi da ido Babiya tayi da mamaki kafintace"Ali halan ka manta wan can maganan da aka yi tun kafin zuwan wannan lokaci? Ina ce nannazaunar da ku gaba ɗayanku na yi mishi maganan akan tunda Allahn da ya ba shi Amina yaamshi abin shi, ya dangana ya samu wata ya aura dama mun san ba'a ɓari a kwashe duka, musammanma Amina kowa ya sheda kasantuwarta mace ta gari, na kuma jaddadamai da kiman namiji bayacika se yana da mata, musamman shi da ya taɓa aure, amma yayi fir yace mun ba ze taɓa iyarayuwa da wata mace a duniya bayan Amina ba, na buga na buga yayi fir ya ƙi amincewa, alokacin yarinyar nan Sa'adatu na gidan har batun ta na kawo saboda shaƙuwan da tayi dayaran, in ma gudun kar ya zo yayi auren matar ta wulaƙanta mai yara yake to ga wacce suka tashi wajeguda, duk yace a'a, daga ƙarshe Ali ƴar ɓuya muka koma da Abdussamad a gidan nan, se daHabiba Allah ya jiƙanta ba din ta mutu ba tace mun "Hajiya ajiye batun nan a gefe dan Allahkubar shi ya yi rayuwar shi yanda yake so ba ƙaramin yaro ba ne" aiko na tattara zancen na maidagefe, aiko Abdussamad ya koma bayyana mun kan shi kamar da, se yanzu ka zo ka tsiro mindawani batun ina zaune lafiya, a'a wallahi Ali ba zan saka baki ba a wannan batu, ai yana ji yanaganin komai, in Allah ya ƙaddara zaman shi da ɗaya daga cikin su ƙarƙashin inuwa guda inazaune batun ze fito, ai ubangiji gatan bayin shi ne, yana sane da komai" ta idda zance cikedagaskiyanta, sauke numfashi Ali yayi ya ja baki ya ɓame ba tare da ya kuma cewa komai ba.... Ta ɓangaren su Iƙilima kuwa suna shiga gida suka wuce ɗakin su, zama suka yi jigum-jigumgunun ban tausayi banda tuna wani shuɗaɗɗen rayuwa ba abinda suke cike da fata da muradinganin rayuwar ya dawo musu baya kaman da, a wannan yanayin kiran sallah ya riski kunnuwansu, tashi suka yi suka ɗauro alwala suka kabbarta sallah suna idarwa suka gyara zama sukacigaba da lazimi ba su miƙe daga wajen ba se da suka sallaci isha'i hayaniyar matasan dakeiskosu ne ya sa su miƙewa da mamaki suka nufi ƙofar gida, zugan matasan Sarari ne tsaye kowadamakami a hannu, da mamaki Iƙilima ta ɗauka daga saman matakalan ƙofar gidan ta wucegunKainuwa dake tsaye cikin shirin fita aiki, "Yaya Lukman lafiya!" Tace a ɗan tsorace, "fi ta nemazamu yi wallahi yarinyar nan ta sake ta shigo hannu se mun aikata inda ba'a dawowa" yayi maganan cike da tabbaci, bin shi da ido tayi babu wani alamun razana kafin tace "idan kungantakafin ku kasheta ku faɗa mata Allah na sonta da ya zaɓeku matsayin makasanta ban so tayi mutuwa me rahma haka ba, na so tayi mutuwar walaƙanci ne" jinjina mata kai yayi tare dafaɗin"ki ɗauka a kunninta ki ka faɗa" jinjina mai kai tayi ta juya da nufin komawa ciki, karo sukakusanyi da Harira dake ɗauke da madai-daicin basket dake ɗauke da kula babba da ƙarami... Murmushi ta sakin mata tare da faɗin "ina zuwa a wannan lokacin?" Murmushi ta sakin matatareda faɗin "Mama ce tace in kawo muku" murmushi ta sakin mata tare da faɗin "mu shiga ciki" tayi maganan tare da riƙo hannun Sadiya dake tsaye tana bin su da ido, ba musu ta dafa musubayasuka koma ciki..... A natse suka shiga ɗakin cike da fargaban abinda za su tadda, zaune suka tadda shi jinginedafuskan gadon da yake kai idon shi akan ƙofa, haka suka shigo gaba ɗayansu, lumshe ido yayi lokacin da suka gama shiga tare da buɗewa a natse, "ya jikin?" Jabir yace murya na rawa, guntunmurmurshi ya sakin mai tare da jinjina mai kai, "Allah ya ƙara maka lafiya" yace cike da farincikin ganin shi a zaune, ƙarisawa kusa da shi Hajiya tayi ta riƙo hannun shi ta damƙe tare dafaɗin"lallai lafiya ta samu" murmushi ya saki tare da bin ta da ido, "nan kowa ya gaida shi cike dakulawa, ba wanda ya buɗewa baki ya amsa se ido da yake lumshewa ko ya jijjiga kai, "sannuYayaSahabee Allah ya zamtoshi kaffara" Lailah tace da kulawa, murmushi ya saki idon shi akantatare da motsa laɓɓa a natse yace "amen" "su ɗin ne dai, ga su nan sun dawo ga Mamarsu" Alhaji Jamil yace cike da farin ciki, jinjina kai yayi fuskan shi na bayyana jin daɗin maganan da Alhaji Jamil yayi, "ina ga yakamata a ragu ko" Hassan yace tare da kallon Jabir, jinjina mai kai yayi tareda faɗin "mu rage yawa dan Allah" ba musu suka fara raguwa.... Motsa laɓɓa yayi tare da kallon Alhaji Munnir a natse yace "a haɗa mun ruwa me sauƙinzafi" jinjina mai kai yayi da sauri ya juya ga A'isha ya faɗa mata abinda yace, wucewa toilet ɗintayi ahanzarce dan haɗa mai, ba ta jima ba ta fito tare da sanar da shi ta haɗa, motsawa yayi a hankali, da sauri Kausar da Yasmin suka matsa suka temaka mai ya sauka, jinjina musu kai yayi alamungodiya ya wuce toilet a hankali, yana shigewa Lailah tace "ina ga da an kira Insu ta zo ta temakamai ko?" Ta yi maganan idonta akan Lubabatu... "Abinda nake son faɗi kenan yanzu, wato na riga ki a zuci kin riga ni a baki" tayi maganantaredasakin murmushi, "a'a ku barta a gajiye ta dawo, sannan ba na so a dinga matsa mata gamedaabinda ya shafi rayuwarsu ita da shi, in tana son zuwa inda yake da kan ta za ta zo, kun sanbata cika son aikata abinda ba tayi niyya ba" Hajiya tace a kamale, "amma Hajiya abinda yakamatane"Khadijatu tace cike da ladabi, "haka ne Khadijatu, ku dai barta tukun tana buƙatan lokaci" taceanatse, jinjina mata kai suka yi duk da ba haka suka so ba.. "Yasmin jeki amso mai tea wataƙila in ya fito ya sha" Abubakar yace tare da kallon Yasmin, bamusu ta fice da sauri, ficewa a ɗakin suka yi dan ba shi daman kimtsawa in ya fito, se da sukakintaci lokaci sannan suka koma, tadda shi suka yi zaune kaman yanda suka tadda shi a shigowan su na farko, murmushi Hajiya ta saki tare da faɗin "Salwa zubo ma Yayanki shayin" bamusu ta duka ta tsiyayan mai ta miƙa mai, ɗaga ido yayi ya kalleta tare da faɗin "har yanzubaki kile ba ne?" Dariya suka saki gaba ɗayansu tare da tuna wani lokaci, ƴar ƙauye yake kirantatunta so wanta, saboda wawtan autanci da take.... Murmushi ta saki tare da ajiye mai a bedside drower, "a she kin fara hankali" ya ƙara cewaanatse kaman ba shi yayi maganan ba, murmushi suka saki tare da bin shi da ido, "ɗauki kashakarya huce" Hajiya tace da kulawa, jinjina mata kai tayi ya gyara zama ya ɗauki cup ɗin a hankali ya kai baki, wani iri yake ji gaba ɗaya a jikin shi, ji yake kaman ba na shi ba, a hankali yakeshababu garaje kamar dai yanda ya saba cin abinci... Kiran sallah ya saka su Hassan ficewa suka nufi masjid su Lailah kuma suka fice dan yi ananparlor, "ka yi alwala ne?" Hajiya tace cike da kulawa, jinjina mata kai yayi a natse, "zaka iyatsayuwan ko?" Jinjina mata kai yayi a hankali, "in ba zaka iya ba ka yi a zaune" tace tare daficewa, bin ta da ido yayi har ta fice kafin ya sauke numfashi a hankali ya lumshe ido cike da tausayinkanshi.... INSU BABY🤗 Ba ta jima a toilet ba ta fito ɗaure da babban tawul wucewa dressing roomtayi kai tsaye, nanmaba ta jima ba ta fito sanye da dogon hijab wuce wa ɓangaren da praymat yake tayi a natsetakabbarta sallah, tana idarwa a na kiran isha'i, tana kammala azkhar ta miƙe ta kabbarta isha'i tana idar da azkhar ta miƙe a natse ta koma dressing room ba ta jima ba ta fito sanye da abayabaƙa se walwali da ɗaukan ido yake, jan stool tayi ta zauna ta fara shafa lotion tana kammalawata zari toilet paper ta goge fuska ta saka a dustbin ta ɗau body spray da oil perfume ta baɗejikinta da shi, tana ajiyewa ta wuce gado a natse.... Kwantawa kusa da Mairah dake ta barci tayi tare da jawota kaɗan ta taɓi goshinta jin ba ɗuminjikin ya sata sauke numfashi a hankali ta lumshe ido gajiyar da ta kwaso na sauka a hankali.... Ta parlor kuwa suna idar da sallah suka buɗe hiran farin cikin tashin SSB cikin ƙoshin lafiya, jawowayanta dake neman agaji Lailah tayi ganin Farisat ne ya sata saurin ɗagawa ta kara a kunni, "barkan mu da arziƙi Anty Lailah" tace a zumuɗe, "barkan mu dai Farisat" tayi magananmuryanabayyana farin cikin da take ciki, "ba jimawa Sadam

Chapter 74 of 109