Share this page
faɗa mata zata ce zata zo, kuma Yaya ya cekar takuskura ta ƙara tafiya me nisa a tsukin nan" "to ai kina da dalilin ki, dan haka shareta, intaji tagama kumburan zata sakko, yawwa yau ko Nafisat ta shiga school?" "Ai ba mu tashi muntaddataba" tace tare da gyara zama, kallon daƙiku ta mata kafin ta sauke numfash da ɗan sauti, "lafiyakuwa?" Tace idanta akanta.... "Ban san abinda Amatullah ke nufi da mu ba" tace cike da takaici, "me kuma tayi!" Tace cikedarashin jin daɗi, "bana jin taje makarantar nan yau, ɗazu kuna hanya nayi magana da ita takecemun tana son zuwa gidan Khadijatu na ce makarantar fa tace ba ta da lecture" "wataƙila batadashi ne Anty Lailah, ki daina damun kan ki a irin batutuwan nan"... Tayi maganan cike da son kwantar mata da hankali, girgiza kai tayi tare da faɗin "Farisat baki san waye Amatullah ba, wallahi shiyasa ban so ya kaita can ba, na san baje kolin rashintaidontaza tayi hankali kwance tunda babu ne kwaɓa, class ɗin su ɗaya fa da Nafisat" ta idda magananzuciyanta na ƙuna, "gaskiya yakamata ki miƙe Anty Lailah, gashi ta fara zuwa jami'a" Rahmatacecike da rashin jin daɗin batun.... "Nafisat ta tafi tun sassafe kam, ki kwantar da hankalin ki, ba musan wake da gaskiya a cikinsuba, wataƙila babu lecture ma" Farisat tace cikin son kwantar mata da hankali, "ba ta yandaza'ayi Nafisat ta fita zuwa school bayan ba lecture ke ma kin sani, matsalan dai daga wajen Amatullahne, zan kuma yi maganinta" "wallahi na goya baya Anty Lailah kar ki mata da wasa" Hasinat dakeɗauke da Mairah da tayi barci kaman ba ta motan tace cike da ba ta goyan baya, "to zandai jiyemiki asalin zancen wajen Nafisat kar ki yi saurin yanke hukunci tukun" Farisat tace a natse, "tosena jiki, Rahma ku gaida su Ummi mun gode sosai" murmushi suka sakin mata tare da jinjinamatakai, rufe ƙofan driver yayi ya zagaya ya shige mazaunin shi ya ma motan key suka ɗau hanya, daido suka bi su cike da kewa .... Shiga class ɗin yayi a natse, kai tsaye inda su Insu suke ya wuce, jan kujera yayi ya zauna taredafaɗin "kin yi magana da su ne?" Girgiza kai tayi tare da faɗin "ka kira su ka ji inda suke tukun" tayi maganan tare da ɗago kai ta kalleshi, "shammatansu nake san yi fa" yace idan shi akanta, "toda kyau" tace tare da kauda kai, murmushi ya saki tare da faɗin "temaka ki kira su" "banmakaalƙawari ba, kuma address ɗin gidan ma banda shi bare shammatan ya tafi yanda ka ke so" "ohAllah Insu!" Yace tare da kama goshi, kallon sakanni ta mai kafin tace "bari in ji ko Fadila nadashi" tana kai nan ta ɗau wayanta ta danna number Fadila ta saka a speaker ta ajiye a gabanta.... Ringing biyu ta ɗaga cike da sabon da suka yi tace "matemaki ki ke nema?" Murmushi ta saki tareda faɗin "eh kuma ke kaɗai ki ka faɗomin a rai" dariya ta saki tare da faɗin "ban san daɗinbaki, ƙarfe nawa zaki gama lecture's ɗin" "wallahi se six yanzu haka mun tafin hutun minute's ne" "Allah ya temaka, ai ta haƙuri gangara ne" "to ya zamu yi, dama na ce ki na da address ɗingidanuncle Jamil kuwa?" "eh" "please turomin" "okay" tace a natse, "kar ki barni jira" tace tare daƙoƙarin katse kiran, dariya ta saki tare da faɗin "yanzu zan turo miki, naji ma Mahmah na faɗinsusister Farisat za su isa can yanzu" "okay nagode" tace tare da katse kiran.... "Ka ji ma yanzu za su can, bari ta turo address ɗin" tayi maganan tare da kallon Nachma dakecewa, "wallahi na so zuwa ganinsu" murmushi Insu ta saki tare da faɗin "in yaje ya kira vidkugaisa" ta idda maganan tare da ɗago wayanta saboda ƙaran shigowan saƙo da taji, tura mai tayi ta ajiye wayan tare da faɗin "Mairah na tare da su" wani nagartaccen murmushi ya saki taredamiƙewa ya sallamesu ya fice da sauri, "shi da Labib za su ko?" Nachma tace tare da kallonta, jinjina mata kai tayi tare da maida hankalinta ga nazarin da take..... Suna kai jiki parlorn suka hangi Iƙilima zaune tana fuskantan ƙofan ihu suka saki tare da iddasashigewa da sauri, murmushi ta sakin musu tare da miƙewa ta nufesu cikin na ta saurin cikedanuna tsan-tsan jin daɗin ganin su da tayi, "wow wallahi amarya ki ke me capasity irin wannanzuba ƙamshi da murmushi haka" Farisat tace tare da zame jikinta a nata, murmushi ta saki tareda miƙawa Mairah dake wajen Halima hannun, kamawa tayi ba musu, "nayi kewanki Mairah" tace tare da saɓata a kafaɗa.... Ja baya kaɗan Farisat tayi tare da ƙare mata kallo cike da shaƙiyanci tace "kai jama'a komai yabi ya fa" ta yi maganan tare da sakin dariya ta juya gefen Rahma ta ba ta hannu suka tafa, "adingasara ana duban bakin gatari dai" Yasmin tace tare da wuce wa saman kujera ta zauna, kamabaki Farisat tayi da sauri tare da fiddo ido waje... "Uncle Jamil na nan ne!" Tace a tsorace tare da waige-waige, ƙaramar dariya Iƙilima ta saki idanta akan yanda ta tsure, girgiza mata kai tayi tare da faɗin "be jima da fita ba" "to! Allahnagode maka, kar a je a zubda mutumci" tayi maganan tare da wuce wa dan neman wajenzama, "kafin ku zazzauna ku muje dining" tace cike da kulawa, "wa! Ai wallahi cikin nan namu a cikeyake" Safinat tace tare da sakin murmushi, ɓata fuska tayi tare da faɗin "haka zamu yi da ku!"... "Lefin na Anty Lailah ne, munyi-munyi ta barmu mu taso tun ɗazu ta ƙi, abincin ma muƙi ci sedata nuna mana ɓacin rai" Yasmin tace fuska faɗaɗe da murmushi, "duk da haka dai za ku ci wannan, wallahi danku na dafa" "to zubo dai-dai, banda abin ku ma wake saurin faɗin hamdanagirkin amarya musamman ma tamu me capasity, zubo Anty Iƙilima" Farisat tace tare da zarowayanta dake neman agaji, "yawwa Farisat shiyasa nake yinki" tace tare da ƙoƙarin wucewadanzuba musu, "kawota in riƙe miki ita" Nafi tace tare da ba ta hannu, ba musu ta miƙa mata Mairahta wuce da sauri, "kar dai ki ciccika wallahi a ƙoshe muke" Sadiya tace tare da miƙewa ta bi bayanta.... "To fa! Alhaji ƙwazzabu halan yaji labari ne" tace tare da ɗaga wayan ta kara a kunni, tanashirinɗaga mai sallama kalaman shi da ya shige ta ya sata miƙewa a zabure tare da faɗin "da gaske!" Shirun daƙiku tayi alamun ta na sauran shi kafin ta nufi ƙofa tare da faɗin "gani nan, wallahi inƙarya ka ke Hisham me rabani da kai se Allah" tana kai nan ta fice.... "Hisham ne ina ganin" Hasinat tace tare da miƙewa tayi dining, mimmiƙewa suka yi gaba ɗayansu suka nufi can, ba su jima da zama ba Farisat ta shigo tare da faɗin "bismillah kushigomana duk mune" sallama suka yi cike da kama kai suka shigo a natse, fiddo ido Yasmin tayi cikeda mamaki tare da faɗin "wai da gaske dama su ne!" "Gashi ma kin gansu, ina fita na taddasutsaye a bakin gate kaman samarin da suka zo zance" Farisat tace tare da wuce wa gefenfridge, murmushi Hisham ya saki idan shi akansu, zamewa daga jikin Nafi Mairah tayi ta nufe sudasauri, nagartaccen murmushi suka saki tare da buɗe mata hannu, faɗawa jikin Labib dake gaba tayi cike da farin ciki, ɗaukanta yayi ya ɗagata sama cike da farin cikin yanda ta gane shi tare dafara juyi da ita, banda ɓaɓɓakan dariya ba abinda take cike da farin ciki.... Saura kuwa bin su suka yi da ido fuskoki cike da murmushi, miƙawa Hishamita yayi tare dabintada ido, amsanta yayi cike da farin cikin ganinta ya rumgumeta tsam, "auh kuna tsaye! Malamai ku wuce ku samu waje" Farisat da ta ɗakko musu ruwa da lemu tace fuska a kame, "ho Mommyrikici" Hisham yace tare da ƙoƙarin zama a two seater's, "a'a ku wuto nan mu yi lunch" Iƙilimatace cike da kulawa, "wallahi a ƙoshe muke Anty Iƙilima" Hisham yace tare da zama a natse.... "Lallai Anty Iƙilima kina da sa'a! Ke Hisham ya ce wa Anty haka hankali kwance!" Murmushi tasaki idanta akan Farisat da tayi maganan, "to Allah ya ba ta girman ne ai, uncle ɗin mu takeaurefa, ina Sa'eed ne?" Ya idda maganan tare da jefa mata tambaya, "yanzu shigowan mu fa, zamanakenan ka kira" tace tare da juyawa ga Iƙilima, "tare suka fita ya kai shi islamiyya" tace a natse, "toka ji dai" tace tare da ajiye musu lemu da ruwa ta wuce dining.... Haka suka ci abincin sama-sama suka tattaro suka dawo cikin parlorn, "Anty Iƙilima albishirinki"Sadiya tace tare da kallon ta, da mamaki tace "goro" gyara zama tayi tare da faɗin "kin sanwai Insu aure ne da ita kuwa?" "Aure kuma!" Tace da tsan-tsan mamaki, "ƙwarai tana da aure, ƙarinabin mamakin kuma Mairah ɗiyarta ne!" zare ido Iƙilima tayi waje tare da faɗin "me!" "Wallahi jiya aka fashemun baƙi aka ƙaramun bayani a kai" kallon su Yasmin tayi da mamaki, "damahakaku ka ɗauke mu!" Tace cike da rashin jin daɗi, "yanda ta faɗa miki abun ba har haka yake dasauƙi ba fa!" Farisat tace tare da gyara zama ta koro mata bayani.... Cike da zallan mamaki tace "SSB kuma!" "Shi" Hasinat tace tare da sakin murmushi, "Allahmeiko, na daɗe ina mamakin yanda Mairah ta yi mugun kama da ita wallahi, ban dai furta ba ne, Allah ya zaunar da su lafiya" "amin" suka ce zukata cike da jin daɗi, "ku bayin Allah ku muyi hoɓɓasa" Rahma da ta kalli lokaci tace tare da kallon su, "eh magrib na gabatowa, amma yakamata mu miƙa gaisuwa wajen Hajiya uwar gida, yama sunanta ne?" Ta idda maganantaredakallon Yasmin, "wallahi ban sani ba" tace tare da jawo jakanta, "Anty Malika ko?" Hishamyaceanatse, da mamaki suka kalleshi, murmushi ya saki tare da faɗin "ina jin sunan a bakin Insu" jinjina mai kai suka yi tare da yunƙurawa, "wai da gaske tafiyan ne!" Iƙilima tace cike da mamaki.... "In sha Allah yanzu ma kuwa, nayi magana da Anty Lailah akan sama miki snacks wanda zaki dinga ba wa mutane in sun zo, tace in sha Allah za su aiko miki da shi, sannan in kin cika sati zasu zo duba ki, baki da kowa anan se su, kar ki yarda wani ya juya miki tunani akan kar ki saki jiki da dangin miji, dangin mijin ki sune gatan ki anan, ki riƙe su da hannu biyu, ki kyautata musuki so su, ki so yaran su, kuma ki ziyarce su akai-akai, banda nuna wariyan launi, ki ce zaki rungumi wannan ba zaki rungumi wannan ba, gaba ɗayansu na ki ne, in sha Allah zamu dinga wayabazamu zubda ke gaba ɗaya ba" ta idda maganan cike da yanayinta tare da sakin dariya.... Murmushi Alhaji Jamil da maganganun Farisat suka takawa burki daga yunƙurin shiga dayakeya saki tare da jinjina sanin yakamatan su, "Anty Iƙilima duk wani abu da zamu faɗa miki kinrigada kin rigayemu sani matsayinki ta babba gare mu, dan Allah a kula mana da uncle Jamil dakyau, ayi tsafta, a kuma nemi yardan Allah a dukkanin lamuran da za'ayi" Yasmin tace tare da kallonta, jinjina mata kai tayi cike da gamsuwa, "a to, dan Allah a baza capasityn nan da muke ta jonamiki, ki riƙe shi ƙaƙam ya biki, a dinga ɗaukan ƙwalliya ana saka matsiyatan kaya yanda za'a saceƙalbin uncle Jamil" Rahma tace tare da sakin dariya, "yaran nan lamarin ku da gyara ku mimmiƙe, Hisham ku tashi mana" Farisat tace tare da kallon su, murmushi suka saki tare da miƙewaanatse, "bari mu leƙa Anty Malika tukun Sadiya mu haɗe a waje" Farisat tace tare da nudar ƙofa.... Wani ingantaccen murmushi ta saki ganin Alhaji Jamil da yayi saurin saita kan shi ya bayyanakaman isowan shi wajen kenan, murmushi ya sakin mata cike da so da ƙauna, "uncle Jamil barkada dawowa" tace cike da farin cikin ganin shi, "yawwa Hajiyata" yace cike da kula, ƙarisowa wajen zugan su Yasmin suka yi nan kowacce ta miƙa mai gaisuwa cike da girmamawa, amsawayayi cike da nuna tsan-tsan kulawa, "ba dai tafiya ba!" Yace idan shi akan su, murmushi Yasminta saki tare da faɗin "in sha Allah uncle, ai tun ɗazu muke anan" "to ni ban ganku ba ai Mommyna, ku zo mu koma" zare ido suka yi fuskoki cike da murmushi, murmushi ya saki tare da faɗin"toshikanen ku muje" ba musu suka rankaya suka fice, "zamu gaida Anty Malika ne" Farisat taceganin sun nufi parking space, murmushi ya saki tare da faɗin "ta fita" "okay a gaidata da kyau" suka ce cike da farin ciki dan dama ba san zuwa suke ba.... "Kin yi waya da Yaya Kabir yau ne?" Iƙilima tace idanta da ya cika da ruwan hawaye akanSadiya, girgiza mata kai tayi tare da bin ta da idon, "na kira shi be ɗauka ba ni ma" tace a hankali, "wataƙila be tare da wayan ne, na san in ya gani ze kira ki, bari in je kar su yi ra jirana, danAllahki kwantar da hankalin ki, Allah ya ba da zaman lafiya ya kauda fitina" jinjina mata kai tayi tareda sakin hawayen da take ta dannewa ya zubo, da sauri ta juya ta nufi ƙofa tana sakin natahawayen, tana ficewa Iƙilima da ta bi ta da ido ta fashe da kuka tare da juyawa ta nufi bedroomɗin ta a guje.... Miƙawa Mairah hannun Yasmin tayi, maƙye kafaɗa tayi tare da kama rigan Hishamƙam, zareidotayi tare da faɗin "to nayi nan, ina ganin school ɗin zaka koma da ita" tayi maganan tare dashigewa mota, murmurshi ya saki tare da faɗin "Mommy amsheta" "a'a bana san ta yarfani" tacecike da yanayinta, dariya suka saki tare da kallon ta, miƙa mata hannu tayi tare da faɗin"zomujeAbbie Mairah" ba musu ta miƙa mata na ta hannun, "to Allah yayi" tace tare da sakin murmushi, "to zamu wuce se mun yi waya" Hisham yace tare da shafa kan Mairah, "to Allah ya bada ladanzumunci" Farisat tace fuska cike da murmushi, sallama suka yi da sauran suka bawa Alhaji Jamil hannu suka yi musabaha suka juya suka shige motan da Alhaji Jamil ya umurci driver da yaɗauke su, suna tsatstsaye har suka fice .... Murmushi Farisat ta saki ganin Sadiya ta iso kai a ƙasa tare da faɗin "uncle Jamil se ka zo" murmushi ya sakin mata idan shi akan su suka shishshige mota, suna fita daga gidan Farisat takalli Rahma tare da faɗin "kwalliya ta bi ya kuɗin sabulu kinga yanda goshin uncle Jamil keƙyalli kuwa!" kwashewa da dariya suka yi cike da shaƙiyanci.... Comments fans🙏🥰 🫀MUGUWAR TSOKA 🫀 {🫀TA'ARE KALLUƊE} [Muscle Cramp🫀] ) عضلة سيئة ( 🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_ https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 written and Created ~~~~~~~~~~~~~~ ِبسم الله الرحمن الرحيم By Yardajjiya👩 💻 Page. Fifty eight Zaune suke cike a parlorn se kwasan shafta ake, kamar ba wannan ne farkon zuwan su Rahmagidan ba, sallama Nafisat tayi a natse hannu riƙe da kayan tean da Lawiza ta aikota da kawomusu, ajiyewa tayi a natse ta koma gefe ta zauna cike da natsuwa.... Ɗago kai Farisat tayi ta kalleta tare da faɗin "ina ki ka je yau!" "School" tace a natse, "wani school ɗin?" Tace murya na canza amo, "Farisat lafiya kuwa!" Yasmin Ɓadamayya tace idanta akan su, juyawa ga SSB dake zaune system a saman ƙafafuwanshi tayi tare da faɗin "Uncle amanan da aka ba ku na rawa, ku bincika Nafisat da kyau, yau ta fita gidannan da nufin zuwa school se dai Amatullah ƴar Antyn Lailah ta tabbatar da basu da lecture'syau"juyawa ga Nafisat da ke bin ta da kallo me cike da razani tayi tare da faɗin "zaki faɗi inda ki kajeko se ranki ya ɓaci!" ta idda maganan a kausashe, bin su da ido kawai su SSB ke yi cike da mamaki... "School taje" Insu dake zaune gefen Yasmin tace idanta akan Farisat, girgiza kai Farisat tayi tareda faɗin "ba su da class yau Insu" "suna da shi, dan yau darasi uku suka yi, ina da jadawalindarussan" Insu ta kuma cewa murya a kame, kallon sakannin Farisat ta mata kafin tace "yaakayi Anty Lailah ba ta da shi?" "Wannan kuma ita zaki tambaya" tayi maganan tare da kauda fuska.... "Dama na faɗa muku tun a can, se dai in Amatullah ce ke raina musu hankali, amma na sanNafisat babu lecture's ba zata je school ba" Rahma tace cike da tabbaci, jawo waya Farisat tayi tadanna number Lailah ta saka a speaker ta gyara zama, ringing biyu ta ɗaga, sallama ta ɗagamata cike da ladabi, amsawa tayi murya a sake tare da faɗin "kun koma gida ko?" "Eh tunɗazuma" "to ma sha Allah" tace murya cike da murmushi, "yau fa da lecture's Amatullah ne batajeba" tace a natse.... "Dama na faɗa miki ze iya yiwuwa itan ce ba ta ga daman zuwa ba, yanzu kamban san yandazanyi da yarinyar nan ba, Amatullah ba ta san karatu kwata-kwata ta fi maida hankali ga shashanci, "gaskiya yakamata ki miƙe Antyn Lailah" Yasmin Ɓadamayya tace murya cike dajinba daɗi, "wallahi Yasmin ban san abin yi ba, can gidan kakanninta take, ba ruwan kowa datajekoba ta je ba" tayi maganan cike da damuwa, "kin ji ba, daga nan dama matsala ke fara kunnokai" tace cike da rashin jin daɗi.... Ina Nafisan?" Tace cike da damuwa, "tana jinki" Farisat tace tare da kallon Nafisat da dukjikintayayi sanyi, "Nafisat tana zuwa makaranta sosai kuwa?" Tayi maganan muryanta na bayyanafargaban amsar da zata ba ta" jinjina kai tayi a natse tare da faɗin "eh amma ba kullumba, sannan ko ta zo ba ko wani lecture take tsayawa ayi da ita ba" "kun ji ko" tace muryanta nabayyana tashin hankalin da ta shiga.... "Anty Lailah kwantar da hankalin ki, kar ki damu muna raye fa" Insu tace tare da miƙa maFarisathannu, miƙa mata wayan tayi a natse, "Insu ya zanyi!" Tace cike da neman mafita, "ba abindazaki yi, dama ke ce wacce yakamata ta san komai dangane da school ɗinta, zan dinga turomiki jadawalin darussan week in sun turo mun, tanan kuma zan sa Nafisat ta dinga saka mata idozamu yi maganinta, tunda muka zo a sister's ɗinta ai se ta yi karatu dole" murmushi ta saki tacantare da faɗin "ah to, yakamata ta san su waye a gabanta" ta idda maganan cike da farin cikinjin abinda Insun tace, "bar mu da ita Anty Lailah tana san sanin asalin mu ne, zaku ma ta sani" "Allah ya temaka ku gaidamin Hajiya dan Allah se da safe" "Allah ya tashe mu lafiya" tacetaredamiƙa wa Farisat wayan.... Amsa tayi fuska faɗaɗe da murmushi, "wai to shi Baban na ta be san abinda ke faruwa ba ne?" Kamil yace cike da mamaki, "wannan be da lokacin kan shi ma bare kuma na wata ɗiya, shi dai baya sata a makarantar ba, ai a ganin shi komai ya ƙare" Farisat tace idanta akan shi fuskantacikeda murmushi, "akwai matsala babba kuwa" Alhaji Jamil yace tare da kallon su, "ba ƙaramabawallahi" Yasmin Ɓadamayya tace cike da mamaki, "Allah ya ganar da ita ta fahimci wasa takedadamanta, ita kuma Lailah ya shiryar mata da zuri'a, bari in je in mike ƙafa" Hajiya tace taredayunƙurawa, miƙewa Yasmin Ɓadamayya tayi tare da faɗin "muje a gasa ƙafan tukun kafinki kwanta" murmushi ta saki tare da wuce wa gaba ta dafa mata baya.... A hankali suka dinga miƙewa suna barin wajen, kallon Farisat Alhaji Jamil yayi tare da faɗin"ƙarfe nawa zaku tashi?" "11:00am ne uncle" "to Allah ya kai mu" yace tare da nufar ƙofa, "murmushi SSB ya sakin musu tare da miƙewa a natse ya wuce sama, kallon Insu Farisat tayi tareda mata alamun ta bi shi da ido, kauda fuska daga gareta tayi kaman ba ta lura da abinda takenufi ba, saƙa hannu Yasmin tayi ta muntsileta saurin ja gefe tayi tare da riƙe hannun da takeƙoƙarin ƙara mintislinta tare da faɗin "uncle Kamil wai haka zaka saka musu ido su tafi bataredasunje gidanka ba" tayi maganan tare da sakin murmushi.... "Gamamatu Insu Allah ya shiryeki" Farisat tace tare da ƙoƙarin jawota, murmushi Nafisat daYasmin suka saki idan su akanta, "to ya zanyi daughter, Allah ya kai mu gaba in sun zo a canmaza su sauka" Kamil yace murya cike da murmushi, "yawwa uncle Kamil kar ka ɗauki zuginta, inmuka dawo se kun gaji damu kun kora mu" Yasmin tace tare da sakin murmushi.... Miƙewa yayi fuska cike da murmushi tare da sallamansu ya fice, jawo Insu Farisat tayi taredafaɗin "na san kin fahimci abinda nake nufi, tashi malama kije ga mijinki" murmushi ta saki tareda faɗin "yau ranar ta ku ce" tayi maganan tare da zamewa ta kwanta a saman cinyoyinta, "a'aInsu kar mu yi haka dake" tace tare da shafa gefen kumatunta, "shi da kan shi yace in zaunatareda ku" tace fuska cike da murmushi, "a'a mun yafe, miƙe ki je kar mu yi aikin marasa hankali" Yasmin tace tare da sakin murmushi, murmushi Insu ta saki tare da miƙewa ta zauna, nansukashiga hiran yaushe gamo su taɓo nan su taɓo can, se kusan 1:00am suka kora Insu suka tattarasuka yi ɗakin Nafisat dan ƙarisa na su daren a can.... Zazzaune suke cike da jimami me haɗe da tsoro da firgici idanuwansu ƙyamakan gawar Shiladake gabansu, babu abinda suke tunani se dama Shila zata mutu a wannan lokacin! Sunsanmutuwa dole ne ga kowa, sun san kuma kowa se ya ɗanɗanata kamar yanda Allah yayi alƙawarinse dai ba su taɓa kawo mata mutuwa yanzu ba, mamakin be wuce yanda take kwance sanɓal agabansu ba ta da daman motsa ko ɗan yatsanta ba, umurni da tursasawa ya ƙare, sauke ajiyanzuciya me sauti Ɗan ladi yayi cike da jimami yace "bari in kira su Ƙaura su temaka mana mubirneta" "ku binneta a haka!" Zinariya tace cike da tsoro... "To me zamu mata bayan hakan! Ki na da wanda ze sallaceta ya binneta ne! Ko kinga wandaakataɓa sallata a wannan gidan in ya mutu?" Yayi maganan cike da gaskiyan shi, "gaskiya yakamataa sallaceta" Jamcy tace jiki a sanyaye, "to bari mu bar muku gawan har ku samu masu sallatansemu binneta, wari kaɗai ya isheku zuwa nan da gobe da kan ku zaku fiddota ku jefar" yace taredamiƙewa.... "Ɗauketa ku je ku binneta" Shuwa tace tare da miƙewa, ba musu ya nufeta sauran dake tsatstsaye suka temaka mai suka fice da ita, bin su da ido suka yi har suka fice, goge hawayeShuwa tayi tare da faɗin "gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah, yau ga yanda ƙarshenShilayazo, ta sanadinta ne gaba ɗaya muka kasance anan, ita ce uwar mu kuma ita ce uban mu, kafinitamun ga ƙarshen da yawa a cikin mu, kuma ba mu ga wanda yayi kyakykyawan ƙarshe ba, duk haka suke tafiya kamar dai yanda ta tafi, dan haka duk wanda ya wa'azantu da mace-macennanyakamata ya nemi hanyar inganta sauran rayuwar da ya rage mai, ni dai daga yau na ajiyedukwani makaman yaƙi, dan bana buƙatan yin wannan mummunan ƙarshen da sallatana ze gagari al'umman Annabi, na tuba akan dukkan zunubaina, Allah gafururrahim ne" tana kai nantawuceɗakinta da sauri idonta na tsirarar ruwan hawaye, da idon dake zuban hawaye suka bi ta sunajinjina kai alamun kalamanta ya shige su..... "Amma har airport zamu je rakiya ko?" Insu tace idanta akan SSB dake tsaye a gefe idanshi akansu Farisat da ke shirin shiga mota, "ba inda zamu nan ya isa" yace ba tare da ya kalleta ba, kwaɓefuska tayi tare da wuce wa inda suke tsatstsaye... "Zanyi kewa girl's" tace tare da rungumosu, murmushi suka saki cike da kewanta da za suyi tareda rungumota, "se mun zo" Yasmin tace tare da sakin murmushi, "se na zo dai" tace tare dasakinmurmushi, "haka ne fa wanga mata ta kusan juyewa" tace tare da sakin dariya, "ke in zaki zoki zo, ni fa ba anjima ne ba bare yanzu da saura" Farisat tace tare da bankawa Yasmin harara, dariyasuka saki tare da bin ta da ido, "to jirgi dai be jira" Rahma tace! tare da shigewa mota.... "Wayyo Anty Rahma kaman ki ƙosa ki daina ganina! Tace kaman zata saki kuka, "ku shigemuje, kar ku biyewa wannan ba barin mu zata yi mu tafi ba" Safinat tace tare da jan hannu Yasmin, shishshigewa suka yi fuskoki cike da murmushi, ƙarisawa bakin motan tayi tare da faɗin"kugaidamin da mazajenku, masu samari a miƙa mun gaisuwa" murmushi suka saki tare da bintadaido,.... Isowa wajen Kamil dake saɓe da Mairah yayi tare da faɗin "Hajiyata kin yi mantuwa" ya iddamaganan tare da ƙoƙarin miƙawa Farisat dake sakin mai murmushi Mairah, ƙanƙame shi tayi tare

Chapter 94 of 109