Share this page
ya faru, ranar ya rubuta wasiƙa, yazo hurgawa Insiyyat se ya faɗa chair ɗin su, ita kuma kamilatu ta ɗauka ta kamile abu, ta buɗetakarance shi tsaf, nan da nan ta shiga cikin shauƙi, an fita break se ga saƙo ta turo na amsanwannan takardan, tun kafin SSB ya kai hannu Insiyyat ta amsa, ba ta ɓata lokaci wajen buɗewada karance komai tsaf ba, nan ta rikice ta birkice mai, babu rarrashin da be mata ba ammabaamfani, shine fa ya nemo Munnir, da ƙyar fa ta yarda ba Nuratu ya turamawa ba, daga nankumata zubda komai suka haɗe" dariya Abubakar ya ƙyalƙyace da shi tare da faɗin "au haka akayi dama, ni kasan na je mana take away ina dawowa na tadda se rusan kuka take, shi kuma yanatsaye kaman ze tsala ihu, akaramakalla me sulhu kuma na duƙe na ta fama".... Dariya suka saki a haɗe, "duniya kenan kaman ba ayi wannan rayuwar ba, yau gashi ba Insiyyat ma a doron duniya, ita ko Nuratun ma wayasan ko ta na raye yanzu?" Jabir yace tare da jimantalamarin, "tana raye" Munnir yace tare da zaran tissue, "haba!" Yace da mamaki, "eh se dai fatakama ƙasa da kyau wallahi, wannan babban hospital ɗin na titin da ze sadaka da Koli market?" "Na gane shi, ya ma sunan shi? Umm... Yawwa Kachama specialist hospital ko?" "Eh to na tane" "me ne!" Yace ido a buɗe, murmushi ya saki tare da faɗin "yanda ka ji dai, kwanakin baya kasankidney ya sako Limat a gaba, to se aka tura mu hospital ɗin dan suna da kayan aiki da ƙwararrunma'aikata, muna shiga ganin doctor na ganta zaune, ban ma ganeta ba ita ta gane ni, bayandogon bayani na gane ita ce, nan fa tayi ta tambayata mutane, har Insiyyat se da ta tambayenalokacin" "lokacin ta rasu?" Abubakat yace cike da jimantawa, "A'a da ranta" yace tare da gyarazama... "Lallai rayuwa, jama'a yakamata mu nemo waƴanda mu ka yi secondary da su dan a wannangaɓan muna buƙatan su" Abubakar yace tare da kallon su, "wallahi ni ma nayi wannan tunanin" Jabir yace tare da sauke numfashi da ɗan sauti, "ina da number doctor Nuratu na san ba zatarasa number wa su daga ciki ba" Alhaji Munnir yace cike da gamsuwa da batun na su..... Suna fita kai tsaye up stairs suka yi, yana tafe ta na bin shi a baya, suna zuwa dai-dai ƙofar ɗakinta ta tsaya tare da bin shi da ido, be Juyowa ba be kuma da niyyan juyowa, murguɗa baki tayi ta tura ƙofan ta shige, guntun murmushi ya saki tare da tura na shi ƙofan ya shige, canzakaya yayi a hanzarce ya fito a natse, ban da zuba ƙamshi ba abinda yake, ganin be tadda su Jabir aparlour ba ya sa shi leƙa dining room, harara ya banka musu ya juya ya wuce, dariya suka saki tare da tashi suka dafa mai baya.... Tunda ta koma ɗaki tasha magani ta kwanta ba ta tashi ba se 2, a hanzarce ta dira ta shigetoiletwanka tayo ta haɗo da alwala ta fito da sauri, hijab ta kabbarta sallah, tana idar da azkhar tawuce gaban dressing mirror, stool taja ta zauna ta fara shafa lotion's, ba wani ado da tayi wandaya wuce ka'ida, miƙewa tayi ta wuce gaban wardrobe, doguwar rigan lace ta zaro wanda yayi mugun haɗuwa asha colour da ya ji stone tayi ta ajiye a gefe,, gefen ƙananun kaya tayi ta cirobrada fant ta zura, dai-daita zaman rigan a jikinta tayi tare da naɗe gashinta tayi parking a ƙasankai, ɗankwali ta daura irin daurin da ƴan matan zamani ke yayi na gaban goshi, madaidaicinveil taɗauka ash colour kalan lace ɗin ta ajiye a gefen gado, kallon time tayi ganin 3:40 ya sata kabbarta sallan la'asar, tana idarwa ta ja takalmi da jaka ta yafa mayafin a gefen kafaɗa taɗauwayanta ta fice a natse, tana sauka Lawiza tace "abinci" "na ƙoshi se na dawo" tace tare daficewa da sauri.... Tana fita ta tadda Maude tsaye kusa da Ibrahim suna magana, murmushi ta saki tare da faɗin"yau kwata-kwata ban sa ki a idanuna ba Baba Maude" murmurshi ta saki tare da faɗin "damasassara na kwana se yanzu da na samu Doctor ya mun allura na fara jin dai-dai" "subhanallah"tace da kulawa, "ke dai bari har kin fito tafiya makarantar?" "Eh wallahi" tace tare da sakinmatamurmushi, "to Allah ya tsare, ya jiƙan magabata, jiya Lawiza ke ce mun ashe mahaifiyar taki tarasu ma" murmurshi ta saki tare da faɗin "amen Baba Maude" "yanzu haka zuwa nayi inmaIbrahim gaisuwa, irin wannan rashi da aka yi, tace ma ke ɗaya ta haifa" da mamaki ta kalletatareda faɗin "muna da yawa" tayi magana tare da kallo Ibrahim da ya ɗaure fuska, "a'a tace munkeɗaya ta haifa wa yallaɓai" tayi maganan da mamaki, "inji wa?" "Tace ita ma da mamaki, "Lawizako dai ba'a take mun?" "Oh" tace cike da gano inda maganan ya dosa.... "Ina nufin yaranta ne muke da yawa" tace cike da son daƙile zancen, "au bayan sun rabudayallaɓai ta sake aure ne?" "Sosai kuwa, ai muna nan da yawa, kusan mu tara ta haifa fa" "ohAllah sarki wato yallaɓai ne kaɗai ke da ɗaya, "eh sauran duk na mijinta na can ne" ta idda maganantare da shigewa mota, "muje Abban Iman" tace da sauri, murmushi ya saki tare da girgiza kai... "In jiraki ne?" Girgiza kai tayi tare da fadin "Nachma za ta mun kitso" "okay kafin six zandawo" yace tare da ma motan key, kai tsaye department ɗin su ta wuce, tana shiga ta tadda ana tasubmitting assignment, ba da nata tayi ta wuce inda Nachma ke zaune, ajiye mata littafi tayi agaba tare da faɗin "ban manta ba" "kin kyauta" tace tare da ɗauka ta fara dubawa, "yau zamuyi kitson ne?" "Wallahi cikina matsanancin ciwo yake da ƙyar na iya taƙarƙarowa na zo" "okaybadamuwa, muje pharmacy ki amshi magani" tace tare da miƙewa, "no ki zauna in ki na da abunyi, zan iya zuwa" Nachma tace da kulawa.... Harara ta zabga mata tare da miƙewa suka fice daga class ɗin, tafiya suke sannu a hankali, tagefen department ɗin su Hisham suka bi, suka yi pharmacy, kallon Nachma tayi tare da faɗin"yacikin ke yi? Murɗawa ko kartawa?" "Ke na period ne fa" tace murya ƙasa-ƙasa kaman za tasaki ihu, kallon kin gama damu ta mata kafin ta juya ga wanda ke tsaye a gaban waiting tablenapharmacyn, kauda kai tayi saboda zuba musu ido da yayi, murmushi ta saki tare da faɗin"relief medicine za ka bata" kallon ban fahimta ba ya mata tare da kafe ta da ido, guntun tsaki tasaki tare da gyara tsayuwa, cike da dakewa tace "na period" "okay" yace tare da nemo musu, yanabasu suka ba shi ƴan canjin shi suka fice da sauri.... Dariya Nachma ta saki tare da faɗin "ɗan iska yana fa sane da me ki ke nufi" "fita zabganshi, mujeki sha ki kwanta za ki ji sauƙi, kin dai ci abinci ko?" "Wallahi ban iya ci ba" "kin dafa ne?" Tacedakulawa, girgiza kai tayi tare da yamutsa fuska, "muje ki yi take away" tace tare da karkaratafiyanna su zuwa restaurant.. Suna kai jiki da zumman shiga ciki aka finciko Insu da ƙarfi a kai hurgi da ita gefe guda, rumtseido tayi lokacin da ƙaran screen ɗin wayanta ya shiga kunnuwanta, da azama Nachma ta saki ledan maganin dake hannunta da jaka tayi kanta tare da riƙota, ɗago kai tayi ta sauke a naMinakshi dake tsaye idonta jazur da alamun ta ci kuka, da mamaki ta yunƙura ta fara kakkaɓejikinta, miƙewa Nachma tayi zuciya a mugun ɓace tare da faɗin "ke dabban ina ce da zaki fizgotahaka ki jefar!" "Dabban ubanki ne" tace a zuciye tare da nufar Insu gadan-gadan.... Saurin shiga gabanta Nachma tayi cike da mamaki, "wallahi ba ki isa ba, ba ki isa shiga tsakani nada farin ciki na ba, ta dalilin ki yau bakin da yafi shekara goma yana faɗamin kalaman soyafaɗamin na ƙi, saboda ke ɗin nan, wacece ke? Me ki ka fini? Ni ma macece kamar yanda ki ke mace" ta idda maganan tare da zaburan riƙo Insu da ta yi sakace tana bin ta da ido..... Duƙewa tayi cikin matsanancin kuka tare da faɗin "wallahi ba ki isa ba, baki isa shiga tsakaninada shi ba, dakon san shi nake tun kafin in san ciwo da zafin kaina, da san shi na taso na rayu, bazan taɓa bari ki zo daga sama ki ƙwace mun shi ba, kin san wahalar rainon da na yi tun yanajariri zuwa girma kuwa? A sama ki ka san shi, baki san daraja da kiman shi ba, bazan bari ki shigatsakanin mu ba" ta idda maganan tare da fashewa da raunataccen kuka, cike da zallan mamaki ta bi ta da ido, so take ta fahimci abinda take nufi amma ta gagara, "wai me ke faruwa ne!" Nachma tace cike da gajiya da sauraran kukan, "brother Khalim ba tsararki ba ne, ya wucewasanin ki, kar ma ki yi mafarkin samun shi, dan iyayen mu sun mai mata kuma ita ce a gabanki" Sunaina tace cike da ɓacin rai, kallon Nachma da ta kalleta tayi da mamaki, tare da mata kallonwai akan me suke magana!, Ɗaga kafaɗa tayi tare da faɗin "to ni ma dai ban kai ga fahimtaba"... "Zaki fahimta ne in ki ka yi ƙoƙarin shiga gonar da ba taki ba, wallahi baki isa amsan shi dagagare ni ba, ke ko kunya ma ba kiji ba" Minakshi tace murya a kausashe tare da miƙewa a zabure, "look ɗan tsaya mana, ki na ta wani zabura aka barki da ita wani tsiyan zaki ɗauka a jikinta?" Nachma tace rai ɓace, tureta tayi da ƙarfi tayi taga-taga zata faɗi, ko lura da halin da takeciki batayi ba tayi kan Insu da ta gaza fahimtar komai gadan-gadan.... Saurin riƙota Khalim da ya iso wajen yayi cike da mamaki, tare da kafe Minakshi da ta jiyodaido, janye jikinta tayi da sauri tare da bin shi da ido, muttuke fuska yayi tare da faɗin "wani rashinhankali ku ka zo ku na nunawa a nan?" Yayi maganan cike da kame fuska, guntun murmurshinyaƙe Minakshi ta saki tare da faɗin "ka kira ni da duk sunayen da kake so, ka faɗa min dukkalaman da ka ga sun dace da ni, ba zance maka dan me ba, amma kasani in rashin tunani nakenunawa to kai ka sani, Khalim kai ka haukatani, kai ke shirin tarwatsamun ƙwaƙwalwa, wallahi ba zan juri ganin ka na son wata na ba, me take da shi da bana da shi? Na fita komai, me kahangaa gareta wanda ni ba na da?" Ta idda maganan cikin matsanancin kuka tare da riƙoshi, fizgehannun shi yayi tare da hankaɗeta a zafafe, saurin taro ta Insu tayi cike da zallan mamakinkalamanta, fizge jikinta tayi a zafafe tare da faɗin "ku barshi, ku barshi ya kashe ni, ku ƙyaleshi wataƙila tunkuɗan ya jefani ga ajalina komai ya ƙare".... Bin ta kawai take da ido cike da matsanancin mamaki, kallon Sunaina dake sharɓan kuka tayi kafin ta bi student's ɗin dake tsaitsaye suna bawa idon su abinci, sauke numfashi tayi a hankali, tare da kallon Khalim da zuciya ya kawo wa wuya, cikin danne matsanancin fargaban daketasomata tace "me suke faɗa ne? Meyasa zaka ture ta haka? Duk wannan abun saboda me takeyi?" "Saboda ina sonki, ke na ke so ba ita ba" yayi maganan da ƙarfi tare da kafeta da ido, a firgicetabi shi da ido cikin ɗin bin tsoro da firgici..... Kokawa ta fara da numfashinta dake ƙoƙarin ɗauke mata jinta da ganinta, daƙyar ta iya samundai-daiton shi, salati ta fara maimaitawa da addu'o'in da bata san ko na menene ba a ƙasanzuciyan, "so!" Ta furta a ƙasan maƙoshi tare da baza mai idon da suka canza launi cikin daƙiƙu, duƙawa tayi a natse kamar babu wani abu lakka a jikinta dake, kamar ba wani abu dake nuƙurƙusanta zuciyanta ta ɗau wayanta da screen yayi ratsa-ratsa ta ɗau jakanta ta maidabayata raɓe Nachma da mamaki ya mamaye a hankali ta nufi barin wajen.... Da sauri ya sha gabanta tare da faɗin "I love you Insu, I really love you" yayi maganan cikedatabbaci, ba abinda take iya gani se duhu, kauce mai tayi cike da dakiyan da ba ta san ta nadashi ba, shan gabanta ya kuma tare da faɗin "i love you more than i can say Insu, I love you thedepthof my heart Insu, I want you to give me a chance to understand my word please" ya idda maganan cike da tsan-tsan magiya me ɗauke da fata, rumtse ido tayi da ƙarfi tare da dannekukan dake son ƙwace mata, raɓe shi tayi da zumman wucewa, riƙo hannunta yayi da sauri tareda faɗin "please Insu don't say no, please" fizge hannunta tayi da ƙarfi tare da wuce wa dasauri, a guje ya bi ta tare da ƙoƙarin riƙo hannunta.... Juyowa tayi a fusace tare da faɗin "don't touch me again" tayi maganan a rarraɓe cikin matuƙarfusata tare da nuna shi da yatsa manuniya, duƙewa yayi a gabanta cike da matsanancinfargabatare da faɗin "na ji, amma please kar ki ce mun a'a, ba zan iya jurewa ba" wani tuƙuƙin baƙinciki ne ya taso mata ya danne ƙirjinta, cikin rawar murya me haɗe da ɓarin jiki tace "bana sonka, bazan taɓa sonka ba, ka komawa budurwanka ze fi maka alheri" tana kai nan ta juya a harzuƙe.... Riƙe jakan bayanta yayi da sauri tare da faɗin "ba gaskiya ba ne, wallahi ƙarya ki ke faɗa, wallahi ki na so na, ina da tabbaci akan hakan" ya idda maganan ruwan hawaye na taruwa a idanunshi, da sauri Nachma da ta farfaɗo daga suman tsaye na wucin gadi da tayi ta nufe su ganinyandaƙirjin Insu ke sama da ƙasa, ture shi tayi da ƙarfi tare da faɗin "bana sonka!" tace da ƙarfi taredasakin kukan da take ta dannewa, "saboda me?" Yace a hankali tare da bin ta da ido, sabodaI'mmarried, I have husband" ta faɗa da matuƙar ƙarfi tare da duƙewa a wajen.... Sakin ido da baki yayi yana bin ta da rikitaccen kallo, ba shi kaɗai ba hatta Nachma da sauran student's dake tsaitsaye sun sha matuƙar mamaki, miƙewa tayi tare da share hawayenta ahanzarce zuciya na matukar ƙuna tace "what more would you like to hear?" Ta je fa mai tambayan idonta ƙyam a kan shi, girgiza kai yayi kaman wani mara hankali tare da faɗin"lied!, islied! You are not married" ya idda maganan tare da nufarta gadan-gadan, ɗaga mai hannutayi afusace tare da faɗin "wannan shine gaskiyan, akwai igiyoyin wani a kai na, don't ever talktomeagain, mind your business" tana idda maganan ta juya da sauri, "Insu!" Hishamda ya hangesutsai -tsaye yace da ƙarfi tare da ƙarisowa inda take da sauri, be kula da yanayin da take ciki bayace"Insu" "what!" Tace a fusace tare da baza mai razanannun idanunta, saurin ja baya yayi taredaɗaga wayan shi dake riƙe a hannun shi tare da faɗin "Mommy want to talk to you" yayi maganancike da fargaba, rasa me za tace mai tayi, dan ba ƙaramin haushi ya ba ta ba, juyawa tayutawuceda sauri ta bar wajen.... Bin ta da ido suka yi har ta doshi gate, ba wanda ya iya bin ta ba kuma me ƙarfin gwiwanfurtakokalma ɗaya, tana ficewa Nachma ta sauke nannauyan numfashi tare da juyawa ta kalli Minakshi da ke tsaye tana zare ido, "komai ya yi miki yanda ki ke so ko? To je ki tunda kin tarwatsa matafarin cikin wannan lokacin, in dai wannan haukan ki ke kira da so, to ba so ki ke ba, kuma baKhalim ba ko da wani saurayi ki ka yi nan gaba ki ka cigaba da tafiyar da shi kaman yanda ki kema Khalim se ya guje ki" tana kai nan ta juya ga Khalim cike da ƙarfafa mai gwiwa tace "I'mverysorry, abun ya zo mata bakatatan ne, ta firgita sosai, inda ka kalli idonta zaka fahimci hakan, asama taji batun" jinjija mata kai yayi tare da faɗin "da gaske ta na da aure?" ya idda tambayanidon shi akan ta, girgiza kai tayi tare da faɗin "ban sani ba se dai banjin tana da shi, inda tanadashi zamu fahimta cikin mu'amalanta" jinjina kai yayi cike da samun sassauci..... "Ka je zanyi magana da ita in sha Allah" godiya ya mata ya wuce jiki a mugun sanyaye, kallonHisham da ke ta baza ido tayi tare da sakin dariya, kwaɓe fuska yayi tare da faɗin "me akamatakuma!" "Sorry ka taka sahun ɓarawo ne" "oh god" yace cike da rashin jin daɗi, "me ya faru?" Tacetare da fara takawa dan barin wajen, "Mommy ce ke son magana da ita akan wannan issueɗindaya wuce, shine na kawo mata wayan fa" yace kaman ze saki kuka, tare da bin bayanta, "kayi haƙuri, ka ba Mommy haƙuri na san indai ta samu natsuwa zata yi magana da ita" tace cikedason gamsar da shi, Jinjina mata kai yayi tare da fadin "nagode se anjima zan shigo side ɗinku" "okay" tace tare da bin shi da ido har ya ɓacewa ganinta, sauke ajiyan zuciya me ƙarfi tayi taredafaɗin "aure! Aure fa Insu?".... Tana fita ta tsaida taxi, ko gama daidaita tsayuwa be yi ba ta buɗe ta shige, banda duka babuabinda ƙirjinta ke yi, har wani ɗaɗɗaukewa numfashinta yake, da ƙyar ta sami zarafin faɗamai inda ze kaita, babu ɓata lokaci ya ɗau hanya, tunda ya shiga cikin anguwan yake satan kallontata mirror, mamaki yake me wacce ta fito daga anguwarnan za tayi a taxi, ganin ba me ba shi amsa ya zubda ɗinbin tambayoyin shi, yana taka burki ta ɓalle murfin ta fito ciro mai kuɗinshi tayi a hanzarce ta ba shi, da sauri ta bar wajen tayi bakin gate, banda farin ciki babu abindayake, dan ba ƙaramin biya ta mai ba.... Buɗe mata madaidaicin ƙofan shiga ɗaya daga cikin security's yayi cike da mamaki, wucewatayi ba tare da ta musu ba'an da ta saba ba, kallon ɗaya a ciki wanda ya buɗe mata ƙofan yayi taredafaɗin "waya taɓa Insu yau?" "Ina ga Ibrahim ne, tunda gashi da alamun a taxi ta dawo" ɗayadagaciki yace tare da kallon su.... Tana isa gate na biyu, ɗaya daga cikin dirobobi ya fiddo mota ya ɗauketa, har kusa da ƙofandazesadata da babban parlorn side ɗin ya kaita, godiya ta mai ta shige da sauri, ba ta ko lura daLamunde da Maude dake tsaye suna nuna ma ma'aikata abinda za su yi ba, kallon MaudeLamunde tayi tare da faɗin "wa ya taɓa gimbiyar shugaban masu gida?" "To Allah masani" tacecike da mamaki tare da karkara kai.... A guje ta haye up stairs, saboda tsaban sauri haɗe stairs ɗin bibbiyu take, da ƙarfi ta tura ƙofar bedroom ɗin ta faɗa, ko takalmi ba ta samu zarafin cirewa ba ta faɗa saman gado tare da sakinraunataccen kuka, kuka take kamar wacce Allah ya aiko, ta kasa gane dalilin yin kukan, sannanta kuma ƙi dainawa, miƙewa zaune tayi tare da tattaro jikinta ta takure waje guda, ta cigabadarera kukanta, juyawa ga bedside drower tayi ta ɗauki hoton Anty dake tsaye a kai ta ƙurawaidondake shatatan hawaye, "me nayi ke nan Anty? Me ke shirin faruwa da ni ne? Me yasa ba ki kwaɓeni lokacin da nake shaƙuwa da shi ba? Cewa yayi yana sona da dukkanin zuciyan shi faAnty, cewa yayi yana matuƙar ƙauna na fiye da yanda ze iya furta mun Anty" ta idda maganantare da rungume hoton ta fashe da kuka... "Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un, me zance ma mahaliccina? Na banu Anty na ci amananubangijina na, na ci amanarki, ubangiji na tuba ka yafe mun, Anty ki yafe mun, zan nesantadashi ko da shaƙuwan da na yi da shi ze illata farin ciki na, ba zan ƙara kula shi ba ko da hakanzezamabarazana ga kwanciyar hankali na, zan iya shine kalman wasiyyanki ta ƙarshe, zan tabbatar danaiya" ta idda maganan cikin kuka me gunji tare da kwanciya rungume da hoton.... Comments fans🙏🥰 🫀MUGUWAR TSOKA 🫀 {🫀TA'ARE KALLUƊE} [Muscle Cramp🫀] ) عضلة سيئة ( 🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_ https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 written and Created ~~~~~~~~~~~~~~ ِبسم الله الرحمن الرحيم By Yardajjiya👩 💻 Page. Twenty six A natse ta sakko down stairs, babu wani hanzari ko garaje, tun ɗazu da ta haye ba ta sakkobaseyanzu, miƙewa Lamunde da ke zaman jiran sakkowanta tayi tare da washe baki, cike da mamaki ta kalleta sanin ba ta kwana a gidan tare da faɗin "Baba Lamunde har yanzu ba ki tafi ba?" Murmushin saman fuskanta ta faɗaɗa tare da faɗin "ai idan yallaɓai na gari kwana nake, barekuma yau Maude ba daɗi take ji ba sam" "oh haka ne fa tace ta na zazzaɓi, ya jikin nata?" "Alhamdulillah ah da sauƙi sosai, dan ma dai tana buƙatan hutu ne amma ai ba wani zazzaɓi bane wanda yayi ƙamari".... Ta idda maganan cikin son saƙa zance, "to Allah ya ba ta lafiya" tace tare da nufar diningroom, "in zo in serving ɗin ki ne?" Tace da ɗan sauti, "no kar ki damu, zan iya se da safe" ta idda maganan tare da shigewa, tana shiga ta hangoshi zaune saman ɗaya daga cikin dining chair'syana cin abinci a natse, kallonta Ibrahim dake zaune nesa da kujeran da yake kai yayi baki cikeda tambayoyi.... Jan kujera tayi ta zauna tare da faɗin "Uncle barkan da dare" tayi maganan cikin cool voicetareda kallonshi, ɗago kai yayi ya kalleta saboda yanda tayi maganan a sanyaye, daga jiya zuwayauya fahimci yanda take sosai, marairaice fuska tayi tare da zuba mai na ta, da sauri ya kaudakai yamaida ga abincin dake gabanshi... "Waya na ya ci screen Uncle" tace tare da sakin hawayen da suka cika mata ido ta ɗago hannuntadake riƙe da wayan ta ajiye a gabanta, da mamaki ya ɗago kai ya ƙara baza mata ido, mamaki yake akan wayan take kuka ko me? Gyara zama Ibrahim yayi tare da muttuke fuska cikinkamegida yace "wayan ki ke ma kuka kenan?" Girgiza kai tayi tare da goge hawaye, "to me ya saki kukan?" Ya jefa mata tambayan tare da gyara zama... Fashewa kuka tayi me ciwo tare da faɗin "hotunan Anty da video's ɗinta na ciki, sannanvideongawanta da na ƙabarinta ma suna ciki, ga hotunan su Farisat" ta idda maganan tare da sharehawaye, ɗago kai yayi cike da mamakin yanda ta kira sunan kai tsaye, be ta ɓa jin wanda yakirasunan haka a gaban shi ba se ita a yau, maida kai yayi ba tare da yace komai ba, "ya aka yi ki kadawo baki jira ni ba ma?" Yace a natse, "na gama abinda zanyi ne, da na ga baka daɗe da tafiyabase na tari taxi" tace tare da jan hanci, "kar ki kuma, ko yaushe ne ki kirani kawai" jinjina kai tayi anatse, ɗaukan wayan yayi ya fara dubawa, "kuma har da hoton da muka yi da Uncle yau faaciki" tace kamar za ta saki ihu.... "Ya isa" Ibrahim yace fuska a ɗaure, shiru tayi ba tare da ta kuma cewa komai ba, "ki ci abinci" yace a dake, jawo coolern tuwo tayi ta saka rabin malmala, miyan ɗanyen kuɓewa ta zubatajuyekusan naman ciki duka, duk abinda take suna kallonta ba dai wanda ya yi yunƙurin tanka mata, wanke hannu tayi a matse ta fara ci... Tusawa kawai take dan gaba ɗaya apatite ɗinta ya gudu, jin tana ƙoƙarin amai yasata tureplateɗin daga gabanta ta jawo ruwa ta kafa kai, ajiye cup ɗin tayi tare da marairaice fuska ta kalleshi, saurin kauda idon shi dake bin ta da kallon ƙasan ido yayi tare da maidawa ga abincin gabanshi, duk wani abu da take yi yana biye da ita da ido.... "Uncle please ka aramun phone ɗin ka" tace a marairaice ido na tara ruwan hawaye, da mamaki Ibrahim ya ɗago kai daga abincin da yake ci ya zuba mata ido, tura baki gaba tayi tare da kaudakai daga inda yake, "kaji Uncle" ta kuma cewa a narke tare da shagwaɓe fuska, ɗaukan wayandake gefen shi yayi ya ajiye a gabanta, murmushi ta saki cike da farin ciki tare da faɗin "Allahyabaka abinda ka ke so duniya da lahira Uncle" tayi addu'an tare da ɗaukan wayan, "amen" yaceaƙasan laɓɓa, ɗin bin mamaki ne ya kusa kashe Ibrahim dan abinda be taɓa zato ko tsammani bane ya faru... Tana buɗe wayan wani kyakykyawan hoton baby girl ya marabceta, ba ta bi ta kai ba ta wuceappɗin kira kai tsaye saboda ba wani security da ya sama wayan, number Yasmin ta jera ta dannakiran tare da miƙewa tabar wajen.... Bin ta da ido suka yi har ta fice, gyara zama Ibrahim

Chapter 34 of 109