kan ku da na ƴaƴanku nan gaba ku ka fita yi, ku tsarkakezuciyoyinnku ku tsaya akan manufarku, muna muku fatan nasara da cinma gaci, kuma munatareda ku muna ba ku namu goyan bayan" ya idda maganan a kamale, murmushi Farisat ta saki tareda juyawa gefen da Ishaq yake....
"To malam Isahq wani shawara zaka iya ba wa matasa ƴan uwanka da suka fita wannanwaje?"
"Shawara gaba ɗayanmu zan ba mawa malama Farisat, danni ma ina cikinsu tsundumba gudubaja da baya, shawarar kuma guda ɗaya ce, mu ji maganan manya sannan mu tsaya kan
manufarmu, kar mu yarda wasu su canza mana tunani da banzan ƙarairayinsu, ba yau mukasabaji ba, ba kuma yau suka fara tarwatsa mana rayuwa ba" ya idda maganan tare da zaro hankyyagoge fuska.... Murmushi ta saki tare da juyawa ga camera, "to masu kallonmu da ma masu sauraren muduka-duka anan muka kawo ƙarshen shirin na mu na wannan mako ba din mun gama tattauna batunba se dan lokaci abokin aiki ya ɗaga mana hannu, kar dai ku manta maudu'in mu na wannanmakon batu ne akan zanga-zangan da matasan ƙasa suka fita, munji jan kunne akan ta datarzoma da me girma gwamnan jahar Bertuwa yayi sannan mun ji goyan baya da ya ba wamatasan jahar shi, ta ɓangaren waƴanda suka fita ma munji tattaunawan da wakilan musukayi
da wasu daga cikin su"....
"Burin wannan shirin shine fiɗɗo abinda ke faruwa a ƙasata ƙasar ka, ƙasar ki, dan saninwani
hali ƙasar ke ciki, zamu nannaɗe tabarman shirin na mu ne da shawarwarimda baƙinmusukabada, kada ku manta ko wacce kalma da suka furta za ta iya amfanar ka ko ke"....
"Muna matuƙar godiya da alfahari da amsa goron gayyatan da baƙin mu suka yi, muna ƙarajankunni wa matasa akan su tsaya a inda aka umurce su, sannan su jira jiran cikan lokaci kar sucezasu ɗau doka a hannu suyi hukunci cikin fushi, su ne ƙashin bayan ko wacce al'umma, in matashi
ya ɓaci tamkar al'umman da ke cikinta ne gaba ɗaya suka ɓaci, sunana Farisat AbdussamadUmar ina muku fatan alheri, ga ma su son ganin maimaicin shirin za su iya bibiyanmu a shafukanmu na istgram da twitter ma'assalam"....
Tana kai nan suka kauda camera a kanta, miƙe baya kaɗan tayi tare da yamutsa fuska, "sannudaƙoƙari Baba da Ishaq suka ce mata fuskokinsu cike da murmushi, "sannun mu dai, ƙoƙarinnamune gaba ɗaya" tace tare da ƙoƙarin miƙewa, miƙa mata hannu ɗaya daga cikin dattijan tayi fuskaɗauke da murmushi ba musu ta kama ta miƙe a natse, sallamansu ta kuma ta wuce a hankali riƙeda wayanta da ta ɗauka ta fice a ɗakin.... Da sallama a baki ta shiga parlorn da sauri Hajiya ta miƙe tare da faɗin "Alhamdulillah, Allahnagode maka da ka dawo mun da ita lafiya, saura Insu, Allah ka kare su" "amen" YasmindaKamil
da suke zaune kusa da ita suka ce baki a haɗe, murmushi Nafisat ta saki cike da natsuwantatagaidasu da gida amsawa suka yi da kulawa, "ba dai wani damuwa a hanyar ko?" Hajiya ta jefamata tambayan fuska cike da damuwa, murmushi ta sakin mata tare da faɗin "ba komai sudakan su suka buɗa mana hanya muka wuce" "to ma sha Allah je ki kimtso ki zo ki ci abinci" jinjinamata kai tayi ta wuce a natse....
"Ya Allah me ke shirin faruwa ne, abubuwa se canzawa suke a lokacin da ba'ayi zato ko tsammani
ba, yanzu wa ya fidda wannan batun kuma!" Hajiya tayi maganan cike da damuwa idonta akansuYasmin, "ze wuce Luba ne" Kamil yace cike da takaici, girgiza kai Yasmin tayi tare da faɗin"banjinza ta aikata hakan" "to wa waye?" Yace cike da takaici, "Yaya Kamil ba wacce a cikin mu zataiyafidda wannan batun duk rashin hankalin mu kuwa, mun fa san me ye asalin abinda ya haddasadamuwan, ta ya zamu fidda zancen? Fidda zancen nan tamkar kwancewa kan mu zani a kasuwane" ta idda maganan cike da damuwa....
"To waye?" Yace da damuwa, "Allah masani" tace cike da damuwa... Sallama Alhaji Munnir da Abubukar suka yi muryoyinsu da fuskansu cike da damuwa, "ya ya! Sunfara watsewa kuwa!" Hajiya tace tare da kallon su, girgiza kai Abubakar yayi tare da faɗin"bazasu taɓa barin wajen nan ta sauƙi ba Hajiya, duk bayanin da aka musu suna zaune daramdam, har
barazana jami'ai suka musu amma ko gezau" "ya subhanallah" tace cike da rashin madafa, "ba'anan matsalar take ba Hajiya, in mun shawo kan waƴan nan na nesa kuma ya zamu yi da su?" Alhaji Munnir yace da damuwa, da gudu Kausar ta fito daga ɗakin Hajiya riƙe da wayan Nabiladasuke dafe da bayanta, "Hajiya duba nan" tace a rikice tare da miƙa mata wayan dake hannunta, bayanin Cika aiki ne inda yake sanar da batun wanda ya faɗa mai SSB ya farfaɗo, zare idosukayi
gaba ɗayansu idon su akan wayan....
"Lamunde!" Yasmin tace da damuwa, girgiza kai Hajiya tayi ta miƙa musu wayan tare da zamasaman kujera daɓas, "ba za ta taɓa faɗan hakan da wani manufa na da ban ba, da tasanhakanzeiya haifar da matsala haka da ba zata taɓa faɗa ba" ta idda maganan cike da tabbaci, janyejiki
Lamunde tayi da sauri tare da share hawaye ta koma side ɗin su, dama ta zo ganin ko sunci
lunch ne ta sa a tattara plate's ɗin, "yanzu ya za'a yi Hajiya?" Kamil yace da damuwa, "se abindaAllah yayi Kamil" tace tare da kallon shi....
Sallama Lubabatu da A'isha suka yi a rikice, tsaki Kamil ya ja tare da faɗin "me ya kawo kukuma?" "Wani irin waya kawo mu kuma! Wannan wani irin tambaya ne?" Lubabatu tace cikedatakaici, "wallahi ban san abinda ke faruwa ba, yanzu Asma ta kirani ta faɗamin, shine na kiraLuba na mata bayani ita ma tace ba ta san me ke faruwa ba se a lokacin" A'isha tace cike dadamuwa "shine ku ka kwaso jiki ku ka zo saboda ba ku da hankali da tunani ko? A na cikinwannan yanayin ne zaku zubda ƴaƴa ku ta ho nan tunda ga shashashu ko?" Jamil da ya fitodagalungun ɗakin da SSB yake yace tare da iddasa shigowa parlorn idonshi akan su, ba waccetacemishi ƙala dan sun fahimci a sama yake...
"Kar ka ga lefinsu Jamil, ka ga na mazajen da suka sake su sakaka suna abinda suke so, Yasminjekira mun Alhaji ƙarami da Nafisat" Hajiya tace tare da kallon ta, jinjina kai tayi ta wuce dasauri, "ina Jabir ne?" A'isha tace da damuwa, "yana wajen SSB shi da Ibrahim" Kamil yace tare dasaukenumfashi ya kauda kai....
Shigowa parlorn Nafisat tayi a natse da alamu ta watsa ruwa dan ta canza kayan jikinta, "jeki yi
lunch rana ta fara sanyi" Hajiya tace mata da kulawa, jinjina kai tayi ta gaishesu ta wuce, "inaInsu?" Alhaji Munnir yace tare da kallon Nabila, "tana school" tace a hankali, "what!" Yaceidonshi akan ta, "kwantar da hankalin ka Munnir in sha Allah lafiya zata dawo, an tura jami'antsorocan kuma security's na tare da ita, ɗazu Ibrahim yayi magana da drivern yace 4pmza sufito, kaga yanzu kusan 3:30pm sun kusa in sha Allah" Hajiya tace cike da son kwantar mai da hankali, jinjina mata kai yayi cike da gamsuwa.... Da sallama Yasmin ta shigo hannunta riƙe da na Sa'eed, "je ka ci abinci Alhaji ƙarami" Hajiyatacemai da kulawa, jinjina mata kai yayi fuska ɗauke da murmushi ya gaishesu ya wuce, "se yanzuzeyi lunch!" Jamil yace tare da kallon Yasmin fuska a ɗaure, "tun da ku ka zo yake barci, se yanzuyama yi sallah, ina shiga yana sallamewa" tace tare da kallon shi, jinjina mata kai yayi tare dazamaa natse ya bi Sa'eed dake magana da Nafisat cike da shaƙuwa da ido....
Fitowa daga masjid suka yi a tare cike da shaƙuwan da suka yi da juna, kai tsaye parkingspacesuka wuce, tun da security's da jami'an da aka turo suka hango tahowanta suka fara shiri, tanaisowa ɗaya daga cikin jami'an tsaron ya buɗe mata ƙofa cike da girmamawa, murmushi tasakinmai tare da zaro waya a aljihun jakanta dake hannunta, danna number tayi ta kara a kunni, "zanwuce" tace a natse tare da zare wayan daga kunninta ta katse kiran... Ko cikakkun mintuna biyar ba tayi da kiranshi ba ya iso wajen saɓe da Mairah dake ta famancinbiscuit, "ah dole tayi muƙus" Insu tace tare da sakin murmushi, murmushi ya saki tare da faɗin"jeki Ammi" yamutsa fuska tayi tare da narke fuska a haɗe, dariya Hishamya saki tare da faɗin"yau kuma!" "kai ko ta samu duniya" Insu tace tare da shigewa mota, tun kafin ta dai-daitazamaMairah ta fara miƙa hannu tare da ƙananun kuka, dariya suka saki gaba ɗayansu tare da kallonta, miƙa mata hannu tayi ta tafi da sauri, "da ki ka ce baki zuwa" Nachma tace tare da kai hannuta
shafi kanta, saurin ƙarisowa wajen Labib dake riƙe da madai-daicin ledan dake cike da biscuit'sda chocolat's da sweet's yayi tare da miƙa ma Insu, "iyye wannan duka na Mairah ne? Lallai
Mairah ta samu kayan daɗi, godema uncle" ta idda maganan tare da kallon ta, ƙoƙarin riƙoledantake fuska cike da murmushi, "ce uncle nagode tukun" Insu tace tare da janye ledan, "kokukode"tace kaman za tayi kuka, murmushi suka saki idon su akan ta....
"Please gobe ki zo da ita" Hisham yace tare da kallon ta, "banyi alƙawari ba" tace tare da kallonpolice ɗin dake tsaye yana jiran umurni, saurin rufe ƙofan yayi tare da bugan motan a hankali, dahanzari duk suka shige mazaunin su, shigewa ɓangaren me zaman banza yayi a natse driver yaja mota a hankali suka ɗau hanya....
Suna tsaye a wajen har se da suka fice daga makarantan, sauke ajiyan zuciya Hishamyayi taredasaƙalo wuyan Labib, "sake ni kar ka kashe ni" yace tare da bugun kafaɗan shi, "wallahi inasanyara haka, ba ruwanta" Nachma tace tare da saki murmushi, sakin wuyan Labib Hishamyayi tareda faɗin "sa'a aka ci fa, amma Mairah ƙarshen ƙiwiya ce" "a hakan!" Tace da mamaki....
Jinjina mata kai yayi tare da zaro wayan shi a aljihu, "ban gani ba, wuni zungur tayi fa ba taredaMamanta ba, kuma ka ce mun tana ƙiwiya" tace cike da rashin gamsuwa, dariya ya saki taredafaɗin "wa ya ce miki ba tare da Mamanta take ba?" Ja tayi ta tsaya tare da kafe shi da ido, murmushi ya sakin mata tare da fadin "ita ce mahaifiyarta" wani banzan kallo ta jefa mai taredafaɗin "um'hum" murmushi ya saki tare da faɗin "fahimtar da tayi tana ɗauke da cikinta neyasatajanyewa da Khalim, ita ce silar kawo ƙarshen soyayyansu, duk da dama can shike ƙiɗi da rawar
shi bin shi take da ido" yana kai nan yayi shiru, bin shi suka yi da ido a razane cike da mamaki...
"Kana nufin wai Mairah yarinyar Insu ce halak malak! Ita ta ɗau cikinta wata tara ta haifetatashayar da ita!" Nachma tace a rikice, "wallahi" yace cike da gaskiyanshi idon shi akan su, "YaaRahman" tace cike da jinjina buwayan gagara misali, "nayi mamaki sosai" Labib yace cikinshock
ɗin da be gama fita ba, "ba ku ba kowa ma in yaji ance ita ce mahaifiyarta se yayi matuƙar
mamaki"...
Yace tare da sakin dariya, "na mu ze fi Hisham, ni wallahi duk maganan da take na ta na daaureban taɓa yarda ba, babu wani alamu da ya nuna hakan a jikinta" Nachma tace mamaki bebar
saman fuskanta ba, murmushi ya saki tare da faɗin "idan na ce miki SSB ne mijin kuma yazaki
yi?" "What!" Suka ce ita da Labib bakuna a haɗe idanu a waje, dariya ya ƙyalƙyace da shi taredajinjina musu kai ya wuce....
"Tsaya Hisham dan Allah da gaske ka ke!" Labib yace tare da bin bayan shi, jinjina mai kai yayi batare da ya juyo ba, "Yaa Allah! lallai mun zama kidahumai na bugawa a jarida" Nachma tacetareda kama kai cike da tsan-tsan mamaki, kalle-kalle ta fara ganin hankulan student's ba akantayake ba ya sata saurin dafa musu baya dan san jin yanda aka kwana a ragaya.... Miƙa ma Ibrahim iPad ɗin dake hannun shi yayi tare da faɗin "zanyi magana da manema labarankawai, ina ganin hakan shine kaɗai mafita" girgiza kai Jabir yayi tare da faɗin "ba mafita awannan shawaran, tsayuwan minti biyar ƙyam ba ka iyawa ta ya zaka ce zaka yi magana dasuahaka, dube ka fa ka raame sosai kallo ɗaya za su maka su fahimci wani abu ya faru da kai, kagagarin gyara anyi ɓarna, abinda muke gudu shi ze faru" "to me ne ne mafita Jabir?" Yace cikedagajiya, "mafita ɗaya ce, ina ganin kawai a razana su sosai su watse wani gyaran da ɓarna akegyarashi" kallon daƙiku ya mai ya kauda kai tare da faɗin "bana jin wannan mafitan na ka meɓillewace, ka dai sake tunani kafin cikan lokaci" yana kai nan ya yunƙura, saurin ƙarisawakusada shi Ibrahim yayi tare da faɗin "bi a hankali" murmushi ya sakin mai tare da faɗin "na fikaƙarfi
fa Ibrahim ina ka bar Gorgeous?" Murmushi ya saki cike da yaba sanin yakamatan shi taredafaɗin "tana tare da Mamanta, murmushi ya sakin mai ya dira a hankali.... Zaro tissue tayi ta fara goge mata baki a natse, ɓata fuska tayi kaman zata saki kuka, murmushi
ta sakin mata tare da faɗin "ki na son zama ƙazamace?" Girgiza mata kai tayi tare da shigewa
ƙirjinta, "a'a kar ki shafamun datti" tace tare da ƙoƙarin cirota, ƙarar da wayanta ya ɗaukaneyadakatar da ita daga ƙoƙarin ciro Mairah a jikinta da take, ganin me kiran yasata ɗagawa takaraakunni tare da faɗin "malama ƴar jarida" dariya Farisat ta saki me faɗi daga ta can tare da faɗin"malama lawyer" "to ya wuninki?" "Alhamdulillah se yanzu nake lunch" "subhanallah! Meyahanaki yi da wuri?" "Program na gabatar se yanzu na samu natsuwa" "ki fa dinga kiyaye lafiyarki
Mommy" tace cike da rashin jin ba daɗi....
"In sha Allah kin koma gida ne?" "Gamu akan hanya dai ba daɗewa zamu isa" "to shikenansekunisa zuwa anjima zan haɗa mana kira ni da Yasmin da Sadam da su my Jannah mu gaida Uncle"
jinjina kai tayi tare da faɗin "to shikenan Allah ya kai mu, yau kin leƙa gidan gaisuwan ne?" "Ehdaga can na wuce aiki, Iƙilima tace jiya bayan tafiyan mu kin kirasu" "eh mun gaisa" "kinkyauta"
"to Anty Farisat" tace sautin murmushin ta na fita, dariya ta saki tare da faɗin "hospital ɗinmamunje" "Allah yasa muku a mizani, har yau ban samu magana da shi ba, na dai kira Halimatahaɗa ni da Anty Gude lokacin yana barci" "to ki ƙoƙarta shima ku gaisa" "in sha Allah" taceanatse, "bari in barki se kin koman" "to nagode jarumar barrister Abdussamad da doctor Salman" dariya ta saki cike da nishaɗi ta katse kiran.... Tana zare wayan suna karya kwana a titin da ze sadasu da white house, da mamaki ta zubawamutanen dake cike da bakin titin fal ido, buɗa musu hanya suke cike da ladabi saboda faɗamusuwacce suka ɗakko da suka yi, kallon driver tayi tare da faɗin "am na ce ba tun yaushe mutanennan ke wajen nan?" "Tun kusan 8am ranki shi daɗe" yace a girmame, "subhanallah" tace taredabin su da ido, "abinci da ruwa fa?" Ta je fa mai tambayan idon ta akan shi "ba a basu komai baMa"jami'in dake gefen me zaman banza yace a girmame, jinjina kai tayi tare da gyara ma Mairahkwanciya a ƙirjinta, iya ƙololuwan ɓacin rai tayi shi a wannan lokaci banda fat-fat babu abindaƙirjinta yake....
Yana dai-daita parking ta buɗe ƙofan ko jira a buɗe mata ba tayi ba, saɓa Mairah tayi ta wuceahanzarce ko takan karikitan ta ba tayi ba, saurin buɗe mata ƙofan parlorn ɗaya daga cikinjami'an da aka saka a wajen yayi shigewa tayi da sauri baki ɗauke da sallama...
"Ma sha Allah" Hajiya dake zaman jiran ganin shigowanta tace tare da miƙewa cike da farinciki, "Ammi" Nafisat da Sa'eed su ka ce cike da farin cikin ganinta tare da miƙewa suka yo indatake, bin su da ido tayi cike da zallan mamaki, "lafiya Insu!" Yasmin tace tare da kafeta da ido...
"Lafiya ƙalau Mahmah, ba abinda ya ke faruwa a ƙasan, ku cigaba da zama a parlor AC na hurakutv na aiki ku kalli duk tashan da ku ke son gani, ga ma'aikata nan barkatai ko wanka ku kesozasu muku" ta idda maganan a zafafe... Wani magana ki ke haka Insu!" A'isha tace da damuwa, "magana nake akan al'umman da
jajircewan su ya ka wo ku ga gacin da ku ke damawa, ga su can a waje cikin azababben zafinrana, suna zaune dan nema muku adalci, ko darajan ruwa me ɗumi ba su samu dan jiƙa maƙoshinsubabare a je ga me sanyi ko abinci, menene hakan ke nufi!" Ta idda maganan a zafafe..
"Zo ki zauna ki natsu tukun" Alhaji Munnir yace mata da kulawa, girgiza kai tayi tare da faɗin"yi
haƙuri uncle Munnir ba zan iya zama ba, meyasa ba zaku fahimci abinda nake faɗa ba ne wai!
Al'ummanku ne zaune a saman titi cikin zafin rana fa" ta idda maganan da ƙarfi wanda yajahankalin ma'aikatan side ɗin gaba ɗaya suka rankayo wajen, firgita Mairah tayi tare da fashewada kuka, saurin amsanta Nafisat tayi na ta jikin na ɓari ta fara girgizata....
"Akwai wanda yace su fito ne? Su suka ga za su fito suka fito ba mu muka sa su ba, mutanennanfa ban yarda ma abinda suke faɗa ya kawo su wajen nan ba, ku ƙyamesu in sun gaji za sutattarasu koma inda suka fito" Lubabatu tace a zafafe ganin kaman Insu na son nuna musu isa da
gadara ne, kallo ta bi ta da shi me cike da mamaki, buɗe baki tayi da zumman magana Abubakarya tari numfashinta da faɗin "ba ki san siyasa ba Insu ya wuce tunaninki, wallahi wannanabindaki ka ga sun yi ze iya zama shirine kawai da abokan adawa suka shirya su kuma suka gabatar" wani guntun murmushi me cike da takaici ta saki tare da faɗin "da kyau, gaskiya kun burgeni, daina tunanin wasun su ba su da kyakykyawan tunani, ashe akwai waƴanda suka fisu gurɓacewantunani a kusa da ni, saboda ba su da hankali ba su san me suke ba, se su fito tsakiyar ranahakasuna haɗa zufa cikin matsanancin yunwa da ƙishin ruwa duk dan su ɓata ma ɗan uwankusuna, dakyau wallahi kun burgeni"..
"Mutanen nan saboda ɗan uwanku suka fito, dan nema mai adalci, saboda so da ƙauna dasukemai sun kashe duk abubuwan su masu mahimmanci sun zo sun zauna tare da ikirarin se yasamuadalci za su koma ga ahalinsu, a hakan ku ke son ku ce mun yarfene na abokanan adawa? Kufaragyara tunanin ku kafin ku kalubalenci tunanin wasu" ta idda maganan a kausashe....
Zabura Lubabatu tayi da zumman magana Hajiya ta dakatar da ita da faɗin "ya isa haka, Insiyyahzo zauna tukunna" girgiza kai tayi tare da faɗin "ba zan iya zama ba Hajiya se bayin Allahsunsamu adalci" "adalcin da suke magana Insu yana da wuya, SSB suke san ya fita yayi maganasuganshi, be da isashshen lafiya, jiya ya farfaɗo, ko tsayuwa da kyau ba iyawa yake ba" A'ishatacecike da damuwa, "wa yake maganan ya fita su ganshi Anty A'isha!, su fa burin su yayi maganasuji su gani ne, babu buƙatan se ya taka ya fita ya tsaya a gaban manema labarai, yana kwanceakan gadonshi ma ze iya magana kuma su jishi su saurareshi, burinsu be wuce shi din ya musumagana su tabbatar da lafiyanshi ba, "to a yanda yaken nan ki na ganin ya musu magana
hankulan su kwanciya ze yi?" Alhaji Jamil dake bin ta da ido yace a natse....
"Wani hali yake uncle Jamil? Kwance yake ba ya motsi? Ko jan numfashi daƙyar yake? Tundaharya iya cin abinci ya iya shan ruwa kuma ya iya magana da ku cikin fahimta ina ganin maganadansu natsu ba ze gagareshi ba, komai fa akan shi suke yi, rashin maganan Uncle shi ze hassalasusugazgata zantukan da ake faɗa su aikata aika-aikan da ku ke tsoro, kun duba media kun gaabinda
ke faruwa kuwa? Kun ji irin furucin da matasan ƙasa ke yi kuwa?, A halin yanzu a kewayesukedagidajen waƴanda suke zargi kuma babu abinda ze hana su afkawa su aikata abinda zuciyoyinsuke ingizasu se shi"....
"Idan kuna son matasan ƙasa su zama makasa to ku cigaba da zama kuna shan Ac kuna kallontv, shi kuma ɗan lelen na ku ku lulluɓeshi da barguna goma dan kar wani ya gan shi, se dai kusani
mu ma zamu fita ayi damu"...
Ta idda maganan tare da baza musu ido, "ke da wa!" Kamil yace da mamaki, "al'umman ƙasagaba ɗayansu ƴaƴa ne gare shi, tunda har ze iya rufe kunnuwan shi daga jin kiran cetondasukemai, ya rufe idanuwan shi daga gani to mu ma dake ƙarƙashin shi ba tsira zamu yi ba wataran, zamu je ayi zanga-zangan damu ko mu kashe ko a kashe mu" ta yi maganan cike da gaskiyanta, murmurshi Ibrahim ya saki tare da takowa a natse ya iso gabanta, "aka ce ke dawa?" Ya jefamatatambayan idon shi akan ta, "Mairah" tayi maganan tare da juyawa da nufin barin wajen, daidosuka bi ta cike da mamakin hasalan da tayi, tana gab da isa matakalan bene ƙirjinta ya badasautin dammm, ya buga da ƙarfi saboda cin karo da da fuskan SSB dake tsaye ƙyamfuskanshi
ɗauke da matsanancin mamaki....
hargaginta ya fiddo su shi da Jabir da Ibrahim, mutuwar tsaye yayi lokacin da kunnuwanshi sukaci karo da muryanta dake fita a kausashe, be sare da lamarin ba se da ta jiyo idanunshi sukawanke da fuskanta dake cike da damuwa, kauda kai tayi daga kan fuskan shi ta raɓeshi tawuceup stairs da sauri....
"Ami" Mairah tace cikin kuka tare da miƙa hannu alamun son bin ta, riƙo hannun Nafisat tayi jiki
a sanyaye, baza mata ido SSB yayi jikin shi na rawa, saurin riƙoshi Jabir yayi tare da wucewadashi saitin kujerun da ya fi kusa da wajen, yana zama ya sauke wani ƙaƙƙarfan ajiyan zuciyatareda lumshe ido ya buɗe lokaci guda, "gizo ne" yace a ƙasan zuciya tare da rumtse idonshi daƙarfi
ya buɗe akan Mairah da ke ta kiran "Ami" rumtse ido yayi da sauri saboda wani bugawa dazuciyanshi tayi nan take, nan da nan jikin shi ya ɗau ɓari, murmushi Jabir da ya hankalta dayanayin da ya shiga lokaci guda yayi tare da faɗin "Farisat Mairah ita ce ɗiyar da Allah ya
azurtaku da ita" ya idda maganan idon shi akan Mairah.... A sukwane ya buɗe ido ya juya a firgice ta inda yake tare da baza mai birkitattun idanundasukabirkice lokaci guda, hannun shi dake ɓari a saitin inda Mairah take, jinjina mai kai yayi cikedatabbaci.... Wani ƙaƙƙarfan kuka ya saki a rikice tare da ƙudindinewa waje guda, sautin kukan shi ya dawoda hankulan su Hajiya dake zanta maganganun da Insu tayi akan maganan da yakamata SSByayi
dan samun kwanciyar komai, nan da nan suka rufu akan shi tare da tambayan abinda ke faruwa, bayanin komai Jabir yayi musu a natse, murmushi Hajiya ta saki tare da zama kusa da shi taɗagokan shi a hankali ta ɗaura a saman cinyoyinta, bubbuga bayan shi ta fara a hankali cike dasodaƙauna, tun sautin kukan na fita da ƙarfi har ya koma a hankali har ya ɗauke ɗif, murmushi tasaki
tare da ɗago kan shi a hankali, sauri zaran tissue A'isha tayi ta miƙa mai, amsa yayi jikinshi nakyarma ya fara goge jawayen....
"Haka Allah ke ikon shi Sahabee, ikon mahaliccinka ya fi ga hakan, Allah ya azurtaku da ƴamukan mu ba mu sani ba se a kwanakin nan, Insiyyah ta tafi se dai ba ta barka, tana can tanarainonjininka, ba ta sare ba har yanzu" ta idda maganan cike ds kulawa, kallonta yake kaman wani dolo, murmushi A'isha ta saki tare da faɗin "ba ta saka hannu a takardan nan ba, ta kasa Sahabee"
lumshe ido yayi hawayen da suka cika idon suka sakko....
"Ka saurari zuciyanka ta faɗa maka wa take son rayuwa da shi, ita dai ta gama saurarannatazuciyan" Hajiya tace a hankali tare da shafa fuskan shi, yafuto Nafisat dake ta can ɓangarenrungume da Mairah dake ƙananun kuka akan bin Insu Jabir yayi a natse, takowa tayi a hankali tayo wajen, "kawo ta" yace tare da miƙa ma Mairah hannu, yamutsa fuska tayi tare da kwaɓewaahaɗe ta ƙanƙame Nafisat, "to yau ƴan albarkan na kusa" yace tare da sakin murmushi, "tunsafeahaka suka sakko dalilin da yasa ta tafi da ita makarantar kenan" Hajiya tace tare da sakinmurmushi.... Ɗago kanta Nafisat tayi tare da faɗin "jeki uncle" taɓe fuska tayi alamun gab take da sakinkuka, duk abinda suke ba jin su yake ba dan idanun shi da hankalin shi kacokan na ga fuakan Mairah, "abie!" Mairah tace tare da ɓashe baki, kallonta suka yi gaba ɗayansu da mamaki tare da kalloninda take
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 79 Chapter of 109