Share this page
"albarkacinkaya sa ta kasance a raye har yanzu, da ba din kai ba da ta daɗe da bin maraina wayonta" yanakai nan ya juya ya bar wajen, dafa mai baya muƙarrabanshi suka yi zukata a mugun hasale.... "Bismillah ku shiga" police ɗin da ya tura musu ƙofar office ɗin yace idan shi akan su, ba mususuka shiga a natse, kallon su wanda ke zaune a saman kujera yayi alamun shine mamallakinoffice ɗin cike da rashin damuwa yace "kune waƴanda muka yi magana da su a waya?" "Ehmune" Mama tace a sanyaye, miƙewa yayi tare da faɗin "bismillah ku biyo ni" yayi maganantareda nufar ƙofa, da sauri suka miƙe zukata na bugu suka bi shi... "Bismillah ku ƙariso" yace musu lokacin da ya isa gaban gawan Abdull idon shi akan su, a hankali suka taka suka shiga ciki, biyu daga ciki na arba da fuskan shi suka zube a waje suka fashedaraunataccen kuka, sauran kuwa saurin juyawa suka yi cike da firgicin abinda idanunsu ya gani, Mama kuwa guntun murmushi ta saki me ɗauke da ma'anoni wanda ciwo dake ɗauke da shi yabayyana kan shi cike da dakiya ta duƙa a gaban gawan, hannu ta ɗago a natse ta ɗaura a samanfuskanshi da yayi sumtum, sakin hawayen da take dannewa tayi suka ɗiga a saman fuskanshi, "ashe dama kallon ƙarshe ka juyo ka yi mun Abdullmuminu! Shikenan dama kalamanka gareni na ban kwana ne! Iya abinda ka ɗibo kenan dama Abdullmuminu! Allah ya yafe maka, ya amshi tubanka, ya saka maka, na yafe maka Abdullmuminu na yafe maka duniya da lahira".... "Wallahi ba ka taɓa saɓamin ba se haɗuwarka da yarinyar nan, shima ruɗun soyayya ne, nasheda biyayyanka a gare ni, duk me hannu wajen maka wannan wulaƙantaccen kisan Allahyatozarta rayuwar shi tun daga nan gidan duniya, Allah ya ɗauke farin ciki a sauran ranakunshi harse ya isa gare shi kun tsaya a gabanshi ya muku hisabi, Allah ya nesanta natsuwa isa inda yake" ta idda jero addu'o'in kuka na kuɓuce mata.... Ba wanda tausayinta be kamashi ba a cikinsu, hatta da police ɗin dake tsatstsaye se da jikkunansu yayi sanyi, "am ina ganin ku kamata, ku koma gida, in akwai namiji babba se a turo shi yacikeabinda za'a cike se mu ba shi gawan" babban cikin su yace idan shi akan biyun da suka zubeawajen, jinjina kai ɗaya daga ciki tayi tare da miƙewa jiki na ɓari ta riƙo Mama, miƙewa tayi anatse idanta akan gawan Abdull... "Ranka ya daɗe an gano waƴanda suka mai haka ne?" Ɗayan tace tare da miƙewa, "eh munkamasu yanzu haka suna tare damu, in sha Allah zamu miƙa su court dan ta yanke musuhukuncin da ya dace" "mun gode yallaɓai, sun faɗi dalilin da yasa suka azabtar da shi haka!" Taceidanta na tsiyayan ruwan hawaye, "a'a ƙaryatawa ma suke ta yi" yace cike da tausayawa garesu, girgiza kai Mama tayi tare da faɗin "ku saki koma waye, ku barsu su je mun bar duk wandayaaikata mai haka da Allah, Allah ya bi mai kadin shi, Abdullmuminu ba me shiga sabgan mutaneba ne, ba me shiga cikin rigingimu ba ne, na shede shi a akan ba ze iya takalan kowa da faɗaba, Allah ya saka mai ya gafarta mai" Mama tace murya na rawa tare da nufar ƙofa ta fice.... Haka suka bi ta zukata a raunane, suna fita cikin station ɗin ta kalli wacce ta kasa tsayar daruwan hawayenta tare da faɗin "ku kira mazajenku su zo su amshi gawan a samu a sallaceshi amiƙa shi ga gidan shi na gaskiya" jinjina mata kai suka yi zukata a karye.... "Ya ku ka taddata?" Mama tace tare da zama kusa da Baba da ya gigita da aika-aikan da suSarari suka aikata, girgiza kai yayi tare da faɗin "Hafsatu yaran nan ba ƙaramin ɓarna suka yi ba, sunrabata da ƙafafuwan ta gaba ɗaya, yarinyar nan da wuya ta rayu!" Ya idda maganan cike daalhini, "oh Allah, ko an faɗa musu ba ji suke ba, Allah ya kyauta gaba, ita kuma ya tashi kafaɗunta" "amin, tashi za ki yi ki shirya ki tafi can, dan ba kowa a tare da ita se Kabir, kuma kin sanKabir baze iya jinyar mace baliga ba, duk da ƴar uwar shi ce" "to fa!" Mama tace tare da kallon shi, "haƙuri zaki yi Hafsatu, kafin gobe mu ga ya za'ayi" yace cike da rarrashi, "to Allah ya nuna mana" tacetare da yunƙurawa tayi ɗakinta, bin ta yayi da ido cike da jimamin abinda idan shi ya ganemai aasibiti.... "Nayi mamakin yanda na ji shi cike da sakewa, ba ja'inja babu kawo ra'ayi" Alhaji Namadi dakezaune a saman bed a bedroom ɗin shi waya kare a kunni yace muryanshi na bayyana mamakinda ya shiga, makirin murmushi Alhaji Aminu dake zaune a na shi bedroomɗin ya saki tareda faɗin "ni ma nayi matuƙar mamaki, se dai dama nasan hakan ze iya faruwa, saboda karo daaljani ba daɗi" dariya me cike da farin ciki Alhaji Namadi ya saki tare da faɗin "bare shi da yayi karodaaljanu" "to ka gani kenan yallaɓai, ai shawararka na a ba shi ƙafa yayi amfani, a hankali zamubayyana mai manufar mu, zamu yi wasa da tunanin shi yanda yakamata, se mun damƙi maƙogoronshi ba tare da ya ankara ba, na tabbatar lokacin da ze ankara baya da wata mafitasena miƙa kai" dariya me cike da mugunta Alhaji Namadi ya saki tare da faɗin "shiyasa nakesankaAminu, saboda tunaninka irin nawa ne" murmushi Alhaji Aminu ya saki tare da faɗin "rankayadaɗe kyan ɗa ai ya gaji ubanshi, kai ne nawa uban a wannan fannin, goyanka ne ni fa" "wannanhaka yake, ina so a saka ido sosai akan former president da vice president dan na lura zalamansu ze iya buɗe mana aiki".... "Kar ka damu da waƴan nan a hannu suke, na daɗe da fahimtar hakan, na basu lokaci ne, sunaƙara wani yunƙuri da be gamsheni ba zasu fuskan ci hukunci dai-dai da abinda suka aikata, yamaganan yarinyar nan an sameta kuwa?" "Hakan yayi dai-dai ka jira lokaci akwai aikin danakesan saka su a kai, ina jiran kammaluwar komai ne, ka ga suna buɗe aiki za su zama nama wajenmafarauta, ba su kai inda take ba" dariya Alhaji Aminu ya saki cike da jin daɗi tare da faɗin"toyallaɓai, amma issuen yarinyar nan baka ganin ze iya kawo mana cikas fiye da yanda mukehasashe?" "No ƙaramin damuwa ne, zuwa gobe za'a magance shi, kar ka damu, ba na sankasakakan ka a cikin batun, zaka iya ba da ƙofan zargi" "to yallaɓai, bari in barka haka ka huta lafiya, semun yi magana" "to nagode ka gaida iyalan" .... Zare wayan yayi ya ajiye a gefe tare da bin ɗakin da ido, tsayin sakannin ya ɗauka a hakankafinya saki murmushin da ya barwa kan shi sani ya zame ya kwanta ya ja blanket.... "Nan ne ɗakin bismillah" Kabir yace a girmame tare da tura ƙofan ɗakin da aka kwantar daSa'adatu, ba musu Mama ta kai jiki baki ɗauke da sallama, tsayawa cak tayi a razane sauransallaman bakinta ya maƙale, saboda arba da Sa'adatu da tayi a kwance, "Yaa subhanallah" tacearazane murya na rawa, danne kukan dake taso mai Kabir yayi tare da nuna mata wajen zama, "bismillah Mama" yace a dake, takawa tayi jiki a mugun mace ta isa saman sofan ta zaunadaɓas idanta akan Sa'adatu, juyawa yayi ya fice da sauri.... Kai tsaye inda ya baro su Sarari yayi zuciyarshi na tafarfasa, tun hangoshi da suka yi zaratanshi suka mimmiƙe ganin yanda ya dumfari Sarari ya sa su saurin taka mai burki, wajen tare mai hanya, murmushi Sarari ya saki ganin yanda yake sakin huci tare da faɗin "ku barshi" "Sarari!" Kainuwa yace cike da san ankarar dashi illan barin shi ya isa gareshi a wannan yanayin dayakeciki.... Murmushi ya saki tare da faɗin "Kabir ne fa, ku barshi" buɗe mai hanya suka yi suka komagefe, wani banzan tsuka ya ja ya wuce ga Sarari, yana isa gareshi yace "wai mutumne kai kuwaSalisu! Anya da zuciya a ƙirjinka kuwa! Anya kana da Imani ma kuwa! Ƴar uwarkace fa, duk lalacewartaba zata gusa daga jininka ba, wani abu ka aikata mata haka! Meyasa baka kasheta ba ta hutadawannan azaban da take sha!" Ya idda naganan a kausashe.... "Ban shirya ɗaukan nauyin da ba nawa ba, amma kai zaka iya ko din sama mata sassaucinazaba, sannan imani banjin ina da shi kamar yanda nake da tabbacin ita ma ba ta da ɗigon shi, wai kamanta wacece yarinyar nan ne! Ka manta taɓon da tama iyayenmu wanda suka koma gaubangijinsu da shi ne! Sa'adatu ne fa Kabir! Ko kamanta ne? Yarinyar da ta yi sanadiyanmutuwariyayen mu, yau akanta ka tsaya a gabana ka na ɗagamun murya!" Ya idda naganan cike damamaki.... Hawayen da ya cika mai ido ya saki cikin sanyin murya yace "ban manta da wacece ita ba Salisu, kuma ban mance wacece ita ba a wajen mu, bance maka bana jin zafi da ciwon abubuwandata aikata mana ba, se dai bana da ƙarfin zuciyan ganinta a halin da take ciki, Salisu meyasa kaaikata mata haka! Jinin mu ce fa, ɗaya daga cikin ƙannin mu" ya idda naganan murya na rawatare da riƙo hannun shi.... Fizge hannunshi daga na shi yayi da ƙarfi cike da zallan mamakin da ya kasa ɓoyuwa taredafaɗin "ba ƴar uwata ba ce, ba jini na ba ce, ƴar uwata ba zata taɓa aikata abinda ita ta aikataba, taci arziƙin masu arziƙi da har yanzu take shaƙan numfashi" yana kai nan ya juya, "SalisuBabahar ya mutu ce mana yake mu so juna, mu ƙaunaci juna, mu rungumi juna, kar ka manta" Kabir yace murya na rawa, "ba ta a cikin lissafin shi!" yace a kausashe tare da juyowa.... Girgiza kai Kabir yayi tare da faɗin "mu rumgumeta a yanda take, mu so ta, mu kasance taredaita zata shiryu, amananta iyayenmu suka bar mana" wani miskilin murmushi Sarari ya saki tareda faɗin "ban hanaka aikata ko ɗaya daga cikin abinda ka lissafo ba, se dai kar ka sa ranSarari zemata wannan alfarman" yana kai nan ya juya ga zaratanshi tare da faɗin "ku muje" ya iddamaganan tare da wuce wa, dafamai baya suka yi da sauri, bin su da ido Kabir yayi zuciyanshi narauni.... "Bayin Allah se ina haka!" Insu da shigowanta parlorn kenan tace idonta akan su Yasmindakezazzaune shirye tsaf, murmushi Rahma ta sakin mata tare da faɗin "ababen gaban mu da yawabakaman ke ba Madam, kinga dole mu miƙe da wuri" murmushi ta saki tare da faɗin "zaki gamanuƙu-nuƙunki ki fiddo batun da ki ke ɓoyewa, ku mu ƙarisa dining" ta idda maganan tare dajuyawa ta fuskanci dining area, miƙewa suka yi gabaki ɗayansu suka dafa mata baya Rahmadadariyar saman fuskanta be gushe ba tana faɗin "ke ma kin san in ina da abin faɗa faɗa zanyi kai tsaye babu ko ɗarr... Jan dining chair tayi a natse tare da ƙoƙarin zama, "Uncle ya fita ne?" Farisat tace tare da zaunawa kan wanda taja, kallon mamaki ta bi ta da shi tana niyya magana muryan Yasmindasuka iso wajen ita da Hajiya ya katse mata hanzari, "yana office ɗin ciki" tayi maganan fuskantafaɗaɗe da murmushi tare da jan kujera a natse, saurin jan ma Hajiya Insu tayi tare da bintadaido fuska cike da murmushi... "An tashi lafiya Hajiya?" Tace cike da girmamawa, "Alhamdulillah ya kwanan ku? Ina uwar nunaƙoƙon asali?" Dariya suka saki tare da kallon Mairah dake jikin Hasinat, "Auh tana kusa makenan?" Tace fuska faɗaɗe da murmushi, murmushi Yasmin Ɓadamayya ta saki tare da kallonInsu cike da kulawa tace "zauna mana" murmushi ta saki tare da shagwaɓe fuska, harara tabanka mata ta cire ido daga gare ta, murmushi ta saki tare da juyawa da sauri.... Ja baya tayi da sauri saboda karo da ta kusa yi da Lawiza dake dauke da flaks, murmushi Lawizata saki tare da faɗin "kar ya huce" "yanzu zan dawo" tace tare da raɓeta ta wuce da sauri, murmushi Hajiya ta saki tare da girgiza kai, su Farisat kuwa banda farin ciki ba abinda sukeazuciyoyin su, "yau zaku gidan su Lailahn?" Hajiya ta ce idonta akan Farisat, murmushi ta saki tareda maida natsuwanta gaba ɗaya gareta cike da girmamawa tace "eh in sha Allah, daga canzamuwuce gidan amarya dan gobe muke san komawa" "gobe kuma!" Yasmin Ɓadamayya tace cikedamamaki, murmushi suka saki idan su akanta, "eh in sha Allah Anty Yasmin, ai mun ƙoƙartakwana biyu fa, kuma marasa auren mu kaɗan ne, zamu wanke ƙwarya dan gobe ne" Yasmintacefuska cike ea murmushi, "duk da haka dai Mommyna, na ɗauka zamu yi sati daku! Murmushi sukasaki ba tare da sunce komai ba, gyara zama Hajiya tayi fuska cike da murmushi tare da faɗin"hakan ma sun yi zumunci mun kuma gode, Allah ya sa muku a mizani, Allah ya kai mu gobenmuna masu numfashi" murmushi suka saki tare da faɗin amin suka maida hankulansu ga abincinda Lawiza da sauran ma'aikata da suka iso wajen ke zuba musu.... A hankali ta tura ƙofan office ɗin ta shiga kamar wata mara gaskiya, sarƙewa idansu yayi wajeguda, nagartaccen murmushi ya sakin mata tare da yafuto ta, murmushi ta saki tare da takawaanatse tayi inda yake, riƙo hannunta yayi ya zaunar kusa da shi ya cigaba da duba takardunda yake, murmushi Jabir da SSG suka sakin mata cike da girmamawa, maida musu da martani tayi cike da mutumta kai, ajiye takardan hannun shi yayi a natse tare da sakin numfashi me huci, kallon shi tayi cike da kulawa tare da ɗaga hannunta ta ɗaura a nashi, juyowa ta inda takeyayi takalleta fuska a shagwaɓe, murmushi Jabir ya saki tare da faɗin "ya za'ayi da batun kenan?" Juyawa yayi ya kalleshi tare da faɗin "shawarar SSG yafi namu ƙarfi, ina ga mu ɗauke shi kafinmu samu wan can mafitan" jinjina kai yayi ya miƙe a natse.... Miƙewa SSG yayi suka fice tare, bin su da ido suka yi har suka fice, maido da duban su ga junasuka yi a hankali, murmushi suka sakin ma juna cike da shauƙi tare da kai jiki ga juna, ɗaukantayayi ya ɗaura bisa cinya tare da faɗin "me matan SSB ke son tambayan SSB ne?" Murmushi tasaki idanta cikin na shi tare ra kai laɓɓa ta sumbaci na shi cike da salo na musamman, bintayayi da idon dake bayyana irin tarin so da ƙaunarta dake ciki, shafo kwantaccen sajenshi tayi taredafaɗin "yunwa!" Rumtse ido yayi tare da faɗin "I'm sorry Gorgeous" yayi maganan tare da yunkurawa da ita a jikin shi, sauketa yayi a natse ya riƙo hannuta suka fice... Suna isa wajen ta ja mai kujera a natse "thanks ƴar aljannah" yace a hankali tare da janmatanakusa dashi, zama tayi ta ɗau plate ta fara zuba musu abinci, "barka da fitowa Uncle" Farisat tacecike da ladabi, murmushi ya sakin mata cike da kulawa tare da amsawa, nan suka shiga gaidashi cike da takatsan-tsan, shi kuma yana amsawa cike da kulawa, "waƴan nan sune ƙanninYayaSamir ba su fahimci maganan da ake jiya ba, se bayan mun koma ɗaki muka musu bayani, shinesuke san maka godiya" Yasmin tace cike da ladabi, murmushi ya sakin mata idan shi akantakafinyace "kar ku damu, ku yawaita addu'a, in sha Allah ze yi free" jinjina mai kai suka yi cike dagamsuwa, "Allah ya saka da alheri ya raya zuri'a, ya doraka akan maƙiya da mahassada dabutulai" Halima da Nafi suka ce muryoyi na rauni, "amin" yace a natse.... Ajiye mai cokali a gaban shi Insu tayi tare da gyara zaman kujeranta ta fuskance shi da kyau, miƙewa suka yi a natse suka fara barin wajen, murmushi ya sakin mata tare da faɗin "kinkoresu" ƙaramar dariya ta saki tare da faɗin "ba ruwana" "ke ko ke da ruwa" yace tare da ɗaukancokalin ya ɗibi dai-dai yakai bakinta, buɗewa tayi a natse ta amsa tare da zaran tissue da gogegefen bakinta, ɗibo wani yayi ya kuma kai mata amsa tayi ba musu se da ta amshi kusancokali shida sannan ta amsa cokalin ta fara ci da shi cike da kulawa, "I'm done" yace a hankali tareda shagwaɓe fuska saboda ganin tana ƙoƙarin ɗibo wani, "to amshi wannan da na ɗibo shikenan" tace tare da kai cokalin bakin shi, buɗe baki yayi a natse ya amsa tare da bin ta da ido, murmushi ta sakin mai bayan ta zare cokalin tare da goge mai gefen baki... "Ta so ki zo" yace tare da miƙa mata hannu, kama hannun tayi ta nufe shi, ɗaukanta yayi caraf yaɗaura a saman cinya tare ra ɗibo abincin ya kai mata baki amsa tayi tare da da faɗin "Nafsii" "na'am matan Nafsii" murmushi ta saki tare da juyowa ta fuskance shi, "yi tambayanki kai tsaye" yace tare da kai mata wani loman, amsa tayi tare da faɗin "to kar ka ce na cika ƙosawa fa" murmushi ya saki tare da faɗin "nayi alƙawari" murmushi ta saki tare da faɗin "to ranar yausheza'a yi zaman ƙarshen? Sannan wani lawyer ne se jagoranci zaman?" murmushi ya saki taredafaɗin "Monday talata kuma ya dawo in komai ya tafi yanda muke so" jinjina kai tayi tare dafadin"Allah ya amince, akwai bayanan wan can zaman da Anty ta tattara a wajen Yaya jiya nayi magana da shi, inba damuwa se ya turawa lawyern da aka ɗauka wataƙila akwai abinda zetemake shi a ciki" kai mata loman da ya ɗibo yayi tare da faɗin wannan labari ne me matuƙar mahimmaci hakan yayi, se dai shi muke dan ya jagoranci zaman" murmushi ta saki me cikedajindaɗi tare da da faɗin "kaman ka shiga zuciyata" ta idda maganan tare da kai kanta gefenkafaɗanshi, "ai ina ciki Nafsii, tashi ki cinye sauran abincin nan" "na ƙoshi!" Tace a shagwaɓe, "noNafsii tashi" yace tare da ƙoƙarin ɗagota... "Please Nafsii cikina fa ze fashe" "ba ze fashe ba ƴar albarka tashi ki ƙarisa" yayi maganancikedararrashi, ɗagowa tayi baki ture a gaba, danne dariyar dake taso mai yayi tare ɗibo wani yakai mata baki, kallon shi tayi fuska a shagwaɓe tare da buɗe bakin a hankali, zuba mata yayi taredashafa gefen fuskanta cike da kulawa yace "hanzarta ƴar aljannah lokaci na wuce wa" jinjinakai tayi tare da fara motsa bakin... Suna gamawa suka tattaro suka dawo parlorn, wuce wa gefen su Farisat tayi kai tsaye, tanazak8a tace "guy's zan shiga school ya zamu yi?" "Ya ko zamu yi!" Rahma tace tare da bankamataharara, ƙaramar dariya ta saki tare da faɗin "lecture's ne dani masu zafi, dole in shiga school" "towaya hanaki? Mu ma gidan su Anty Lailah zamu daga can zamu wuce gidan Anty amar-amar" Rahma tace idonta akan ta, "ku bari gobe ba ni da school se muje tare" Insu tace cike da magiya.... "Goben in kin gammu kenan" Safinat tace tare da sakin dariya, "me ku ke nufi!" Tace tare dakallonsu cike da mamaki, "muna nufin gobe gidajen mu zamu kwan" Farisat tace tare da miƙewa, "gobe kuma!" Tace tare da kafe Yasmin da ido, murmushi ta sakin mata tare da ɗaga ƙafafuntabiyu, "dama ba zamu juma tare ba!" Tace tare da kallon SSB dake magana da Hajiya kamanzatasaki kuka, "se haƙuri ƴan nan masu kambu sun murza" Rahma tace tare da sakin dariya, "danAllah ku ce ba yanzu zaku koma ba" tace cike da magiya, "ba fa me zama, kar ma ki wani tsayaɓata lokacin ki, gunda ki miƙe ki tafi" Farisat tace tare da wuce wa ɗakin da suka sauka.... Wuce wa inda su Hajiya suke tayi tare da faɗin "Hajiya kin ji wai gobe za su tafi!" Tayi maganancike da rashin jin daɗi, "gobe kuma?" SSB yace da mamaki, jinjina mai kai tayi idanta akanshi, murmushi Hajiya ta saki tare da faɗin "to kun san dai ba zaman kan su suke ba, a ƙarƙashinwasusuke, ba damuwa mazajen na su ma sunyi ƙoƙari" jinjina kai SSB yayi tare da miƙewa a natseyariƙo hannunta, miƙewa tayi jiki a sake, "kar ki damu, zamu dawo nan kusa" Yasmin tace fuskacike da murmushi, harara ta dalla mata ta wuce janye da hannun SSB, dariya suka saki cikedanishaɗi... Murmushi Hajiya ta saki tare da faɗin "bana son neman rigima fa" murmushi Yasmin Ɓadamayyata saki tare da faɗin "ta haura sama kuwa" "waye ya haura sama?" Farisat da ta fito cikinshirinfita tace tare da zama kusa da Hajiya, murmushi Hajiya ta saki tare da faɗin "da Insiyyahsuke" "ai wannan in aka biye mata ba za'ayi aikin hankali ba, Hajiya bari mu leƙa su a gurguje" tayi maganan cike da ladabi, "to ku gaidasu da kyau, da takwararki zaku tafi ko?" Murmushi tasaki tare da faɗin "eh" "to Allah ya kai ku lafiya" "amin" tace tare da miƙewa, tashi suka yi sukatafi kimtsiwo, "Anty Yasmin bari mu leƙa su" tace a girmame, "to ku gaida su Anty Lailahn da kyau, kar ku mance da amso ma Insu danbu" "in sha Allah" tace tare da juyawa ta nufi ƙofa, tanagabdaficewa ta buɗe murya da ƙarfi tare da faɗin "duk wanda be gaggauta ba ze same ni a can" tanakai nan ta fice, fitan ta ba jimawa suka fiffito suka sallame su suka fice a hanzarce... Tunda ya shigo parlorn Alhaji Namadi ke bin shi da ido, zama yayi a ladabce ya gaidashi a girmame, ɗaga mai kai yayi alamun amsawa, gyara zama yayi tare da faɗin "ba wani bayani tareda ita" jinjina kai yayi idon shi ƙyam a kan shi, "an musanyata, sannan ba ta wayi gari yauba" "yaku ka yi da gan-gan jikin?" "Jiran ji daga gare ka muke" yace a girmame, "ku miƙa shi gidanta, sauran kuma kar a bari su yi free" jinjina kai yayi tare da miƙawa a ladabce ya fice.... "Anty Lailah hanzarta tun ɗazu fa Amarya ke jiran mu" Farisat dake ƙoƙarin saka facemasktaceidanta akan Lailah dake saka roban danbu a leda, "bana san wutan cikin nan naki Farisat, wai kuwa ma kun je side ɗin uwar gidan jiya?" Ta jefa mata tambayan tare da ɗagowa ta kwasoledojin dake gefe alamun ta kammala, "muje mu yi mata me! Wallahi ina tsoro" tace taredasakin dariya, dariya Lailah ma ta saki tare da faɗin "duk wannan fi'ilin da ku ke dama matsoratane ku?" "Kar ki ga lefin mu, nesa-nesa" tace tare da ɗaukan jakanta ta saɓa, turo ƙofan parlornKhadijatu tayi tare da faɗin "duk fa sun shiga ke suke jira" "gani nan Anty Khadijatu" tace taredanufar ƙofan da sauri.... Suna isa drivern motan da zata shiga ya buɗe mata ƙofa, murmushi ta sakin mai tare da faɗin"nagode" juyawa ga su Lailah tayi cike da kewa tace "yanzu kam cewa zan se kun zo" murmushi suka sakin mata cike da so da ƙauna, "muna tafe in sha Allah, ke dai bari yara su yi hutu" "Allahya yarda, wai kuna jin uncle Hassan kuwa!" "Be ƙasan fa, numbershi ba ya shiga, shekaranjiyancan nayi magana da matar shi" "to Allah ya dawo dashi lafiya" tace tare da shigewa ta zaunakusada Rahma dake ta sakin musu murmushi, "ungo nan Rahma wannan na ku ne ku duka" Lailahtace tare da miƙa mata ɗaya daga cikin ledan hannun, amsa tayi cike da farin ciki tare da faɗin"mun gode Anty Lailah Allah ya ƙaro kasuwa me albarka" "amin Rahma, wannan ki kaiwa Ummi"ta idda maganan tare da miƙa mata wani ledan, fuska cike da murmushin jin daɗi ta amsataƙaramata godiya.... "Ke kuma riƙe wannan na Hajiya Babiya ne, wannan kuma na Salman, saura ki hau kai zankirashi inji" murmushi Farisat ta saki tare da faɗin "ba fa kura bace ni Anty Lailah!" Dariya sukasaki tare da bin ta da ido, "oho dai na faɗa miki" tace tare da wuce wa motan da Yasmin ke ciki.... "Yaushe zaki koma bakin aiki?" "Satin da ze shigo in sha Allah" "Allah ya amince, se ki kamagirma da mutumcin da Allah ya baki" "in sha Allah" tace cike da jin daɗin kulawanta, "riƙewannan ki kaiwa Hajiya da takwararki, wannan kuma na Muhammad ne, wannan kuma ki kaiwaInsu" "to Allah ya ƙara buɗi, ina na mu!" Ta idda maganan kaman zata fasa kuka, "yana wajenRahma" "to mun gode" tace a natse, "Anty Lailah ai mun kwashe jarin!" Safinat tace idontaakanta, murmushi ta saki tare da faɗin "ai kune masu ɗorawa" tayi maganan fuska cike da murmushi tare da wuce wa motan da Farisat ke ciki ... "Khadijatu bar su su wuce haka la'asar ta kawo jiki" tace tare da iddasa ƙarisawa ƙofan motan, jinjina kai Khadijatu tayi ta wuce motan da Yasmin ke ciki, "Allah ya tsare, kuna isa ki sanar mana" "to in sha Allah, ba fa a faɗawa Anty Salwa auren ba" "to lefin waye?" Tace tare da bankamata harara, "wallahi tsoro na ji dan na san ina

Chapter 93 of 109