Share this page
a ciki na, su ɗai-ɗai har tara, ba zance abinda suke yi dai-dai ba ne, amma ku tinda ƙananu ne kuma ƴaƴa se ku yi ta haƙuri ku ɗau girman tunda su sunyada, musamman ma ke da aka ce kun haɗa kai da Sudais, wannan takun saƙan ba inda ze kai ku, wataran surikarki zata zama" zare ido wajen Farisat tayi tare da faɗin "waya faɗa miki! Ni baabinda ke tsakani na da shi se zumunci" "au ba kya son shi dama?" Babiya tace tare da kallonta, ja baya Salman da ya kai jiki a ƙofan yayi tare da kasa kunni, "ni bana son shi" tace hankali kwance, "to kuma dai, kai Balarabe ba a gabanka aka ce suna san junan su ba?" Babiya tacetareda kallon shi, "to Hajiya ta canza ra'ayi ne" yace tare da kallon Farisat, "a'a Farisat in dai ki nasonshi ki sanar da ni, da kaina zan nemi alfarma a wajen uban shi" taɓ ɗi jam, Hajiya daina wannanmaganan, mutumin da be jajanta mun akan babban rashin da nayi ba, sannan kuma yana shaye- shaye fa" tace tare da kauda kai, "to ai jarabta ne Farisat, se ki ga ana auren ya daina" "taɓni inada wanda nake so, ba zan iya auren wanda ni kaɗai nake son shi ba, wanda ke so na zanauradanna san ni ma zan so shi" tayi maganan hankali kwance babu ko nauyi, murmushi Salmanyasaki tare da gyara tsayuwa, "kaji tabbatacciyan ko? Kuna zaune tana sakin zance" Babiya taceidantana yawo a saman fuskan su Ali, "ai gaskiya ne Hajiyan Allah, da gaskiyanta se wanda takesozamu ba ta" Ali yace fuska faɗaɗe da murmurshi, "to ai se ki cigaba tunda kin samu goyanbaya, wa ki ke so?" Ta idda maganan da sigan tambaya, "gashi nan, bari in nemo miki hoton shi" tacetare da zaro wayanta, turo ƙofan Salman yayi tare da sakin mata murmurshi, murmushi tasaki tare da faɗin "ɗan hakan yaƙi anbato, muna maganan shi se gashi, Hajiya gayi nan" ta iddamaganan fuska yalwace da murmurshi, "to! Wannan ba ɗan ɗakin Amina ba ne!" Babiya tacetareda kallon Salman, murmurshi ya saki tare da ajiye basket ɗin da Baba Mari ta jero musulunchtare da gaidata, "Alhamdulillah, ka ce kai iri ka hango ka na ce" Babiya tace tare da kama haɓa, dariya Balarabe da Farisat suka saki saboda yanda kunya ya dabaibaye Salman, buɗe baki Ali yayi da zumman magana motsawan da Insu tayi ya hana shi, "ta motsa!" Farisat tace taredamiƙewa zumbur, "ku kira Dr ya zo" Babiya tace tare da yin kanta, da sauri Salman da ya hanaFarisat da tayi yunƙurin fita ya fice, be daɗe ba suka dawo da Dr Hisham da Nurses.... "Ma sha Allah ta farfaɗo, kuma cikin hayyacinta" Dr Hisham yace tare da kallon su fuska yalwaceda murmurshi, "dama jiya ba ta farfaɗo ba ne! Yau munga rashin faɗen gaskiya ta bokayenturai, yanzu me ne ne amfanin ɓoye mana halin da take ciki?, jiyan nan fa haka nayi ta farkawa cikindare ko zan ga ta motsa, amma shiru, da safe har naso yin ma Abdussamad ƙorafi se dai najabakina na tsuke, dan ba lallai ya gamsu da batuna ba, kunga a she ilai" Babiya ta idda maganancike da ɗumbin mamaki, murmushi Dr Hisham ya saki tare da faɗin "munyi hakan ne dannemamuku sassaucin damuwa, ba yanda za'ayi muna kiran kan mu da masu ceto rayuwa mu bar wani ya faɗa cikin wani hali, dole ne se mun sakaya dan samun natsuwan ku, yanzu dai a samuwani abu a bata taci, se tasha magani" yana kai nan ya juya ya fice Nurses suka dafa mai baya.... "Da sauri Farisat ta ƙarisa kusa da ita tare da faɗin "Insu gani nan kin gane ni!" Tayi maganantareda nuna mata kanta, ganin ta ƙureta da ido yasata faɗin "kalli nan Insu, kalli wacce ke zaune dake, Hajiya ce, Hajiyar Yaya, kin ganta?" Ta idda maganan a ruɗe , komai Insu dake jin nauyindaƙirjinta yayi ya ragu ba ta ce ba se kauda kai da tayi, "ita ce Insu Anty tayi gaskiya da mukacebata san mu ta tsane mu tace mana ba ta tsane mu ba, kin tuna abinda tace "in bata tare damuwani abu ya same mu kafin kowa ya zo gare mu ita zata fara zuwa" Insu ita ta fara zuwa dukcikinƴan uwan mu, ita ta kwana dake ba ta gajiya ba" ta idda maganan tare da share hawaye, juyowaa hankali Insu tayi tare da faɗin "Anty ba ta ƙarya" jinjina mata kai tayi tare da faɗin "eh, komai inzata furta tana kamanta gaskiya a ciki" lumshe ido tayi tare da sakin hawaye da ya cika matasusuka gangaro, goge hawaye Babiya tayi tare da faɗin "ya isa haka Farisat temaka mata ta miƙetunda sun zare mata mugun abun nan" tayi maganan tare da taɓa Farisat, dariya Ali ya saki tareda faɗin "Hajiyan Allah shi ya temaka mata wajen daidaituwan numfashi" "dan Allah rabudani da wannan batun, Allah dai ya temaketa su da kayan su me suka isa yi?" Tana kai nan ta miƙetajawo baske ɗin da Salman ya kawo..... "Ni ki daina kallona haka kar ki sa in yi mafarki" Insu tace a hankali tare da kauda kai dagagefenBabiya, danne dariyar yanda Babiya tayi da fuska suka yi tare da kallon ta, "kunga wannanyarinyar ba a iya mata, banda shegen kafiɗiri ba abinda ta iya, jiya da da ke a yashe take tananeman matemaki ai ba kuji bakinta ba, yau da ta samu ta farfaɗo shine bari ta nuna manawayeita, in kinyi mafarkina ai kin dace tunda ba da fatalwar uwarki ki ka yi ba" ta idda magananaƙufule, waigowa tayi a harzuƙe tare da faɗin "in nayi mafarki da ita na san na dace, in ko nagafuskan ki a ciki na tabbatar akwai babban matsala" ta idda maganan cike da takaici, saurinƙarisawa kusa da ita Balarabe yayi tare da faɗin "to kar ki ɓata ranki Hajiya wasa take miki" kama haɓa Babiya tayi tare da faɗin "ta zazzage uwarka a gabanka sannan kaje kana ba tahaƙuri, Allah me iko, to ki fashe ƙarikon kumbura" "wallahi se na haɗaki da Anty" tace tare da sharehawaye, "in kin bi ta ko?" Tace tare da kallon ta, "yanzu haka ma tana jinki" tace tare da sharehawaye, zare ido Hajiya tayi tare da faɗin "ba dai yarinyar nan fatalwa take gani ba! Ali kumiƙetsaye kar a haukata muku ƴa" dariya Ali ya saki tare da amsan abincin da ta miƙa mai ya zaunaakusa da ita cike da kulawa yace "Hajiya indai Anty Amina take gani ai babu abun ta da hankali" yana kai nan ya ɗibo ya kai bakinta, buɗewa tayi ta amsa a hankali, taɓe baki Babiya tayi taredafaɗin "ku dai cigaba da shagwaɓa yarinya, nan da wani lokaci gidan wani za'a kaita naga ubandaza ta dinga wa taɓaran a can" "ke zan dinga mawa" Insu tace tare da murguɗa mata baki.... "Kin murguɗawa na kusa dake wahalalle da baya da na yi" Babiya tace cike da takaici, dariyaFarisat da Salman suka saki tare da kallon ta, "a'a kuma Hajiya uban mu danayin shi kuwa" Farisat tace fuska yalwace da murmushi, "ban gani ba, in yana da nayi me ze zaunar da shi hakayana ba gansamemiyan nan abinci a baki" "kuma ba wata Hajiya da zance miki, dan ba ki jekoinaba" Insu tace tare da juya mata ido, "ban nema ba, bana gayyan karere a lamurana, na ƴaƴanama ya isheni" "ba wani Makka da ki ka je suna ta wani ce miki Hajiya" ta kuma cewa a ƙufule, "naga uwarki har ta koma ga mahakiccinta ba ta je ba ita ma, hakan kuma be hana a kirata Hajiyaba" ƙwal-ƙwal tayi da ido tare da faɗin "ai dan ta rasu ne da se taje" "kar ki yi kuka Insu, albishirinki Hajiya, jira Yaya yake ta haihu ku tafi, an gama komai na tafiya, Allah ne be ƙaddara zataba" Farisat tace tare da kallon Babiya, "ni ma ina da labarin yace in ta haihu zaku tafi shi ita dake" Ali yace tare da ajiye wa Insu ruwa, cike da mamaki Babiya ta bi su da ido, wato tana can yaranazugata tana hawa a she su suna nan suna mata shirin ban mamaki, ba ta da wani buri bayannazuwa ta sauke farali, a she Allah ze tabbatar mata da zuwa kafin ta mutu, tun tana saka rai har tahaƙura ta cire dan Gude ta tabbatar mata Amina ba zata taɓa bari Abdussamad ya kaita hajji ba..... Farisat zuba mun abincin nan yunwa nake ji over, rabona da abinci me galmi-galmi tun darenjiyada na bar nan" Balarabe yace tare da kallon Farisat babu musu ta sauka da sauri ta zuba mai tamiƙa mishi, "Yaya Ali in zuba maka ne?" Tace idonta akan Ali, girgiza mata kai yayi tare dafaɗin"ni da abinci se na dare kuma" kallon Salman tayi da kulawa za tayi magana yace "I'mokay" jinjina mai kai tayi ta juya ga Babiya, za tayi magana tace "se da ki ka gama zagayen sannanzaki dawo kaina, da kin bar shi ma ina da hannu" dariya ta saki tare da faɗin "Hajiya in gama daiyayetukun wai, ke na ki na musamman ne" "kin kyauta ai, zuba mun" tace tare da gyara zama, bamusu ta zuba mata ta miƙa mata, ganin ta miƙe ba ta sakawa kanta ba yasa Salman kafetadaido, murmushi ta saki tare da sadda kai, "ke ba zaki ci ba ne?" Ali yace mata da kulawa, murmushi tasaki tare da faɗin "na ƙoshi ne" "me ki ka ci? Daga makaranta fa ki ke" Balarabe yace taredakafeta da ido, miƙewa Ali yayi ya zari plate ya zuba dai-dai ya koma ya zauna tare da faɗin"zoki ci" ba musu ta isa gefen shi ta zauna, ɗibo wa yayi ya kai mata baki, riƙo hannun shi da cokalintayi ta ƙarisa da sh baki tare da sakin hawaye, "oh Allah Farisat rage wannan hawayen manakokya samu na zubdawa ranar aurenki, kar a kai ki ido ƙamas su ce a soye ki ke" Babiya tacetaredakallon ta, kwashewa da dariya suka yi gaba ɗayan su, dan ba ƙaramin dariya ta ba su ba, yanagama bata ta amshi plate ɗin ta saka a basket ɗin ta ɗauka cike da kulawa ta ƙarisa gadondaInsu ke kai ta rungumeta da kyau tare da faɗin "ki kula" jinjina mata kai tayi ba tare da tacekomai ba, "Hajiya zan tafi lokacin makaranta yayi" tace tare da kallon Babiya, "to se kin dawo, dan Allah ki sauka ta gida kar ki ce zaki zo ta nan" "a'a Hajiya kar muyi haka dake, gaba ɗayanmunan zamu sauka" tayi maganan tare da wuce Salman dake zaune a gefe, tana fita ya sallamesuya fice, "ikon Allah shi kuma wannan me ya fiddashi kenan?" Murmushi su Ali suka saki batareda sun ce mata komai ba, hararanta Insu tayi tare da faɗin "to ke me ruwanki" "kun gani kurabani da tabbatacciyar ƴarku tun muna iya fahimtar juna ni da ita" dariya Ali da ya miƙe ya saki tareda faɗin "aminiyarki ce fa Hajiyan Allah, in mun shiga tsakanin ku mu zamu ji kunya" yanakai nan ya sallameta a ladabce ya fice, "ni ma fa zan zo in leƙa filin nan ne" Balarabe yace taredaajiye plate ɗin da ya gama amfani da shi, "oh ka ga ta tattara sauran ta tafi da su, ban lurabadana ce ta tsahirta ta haɗa da wannan" "ni ma na sha'afa ne" Balarabe yace tare da miƙewa, "Insuse dare zan dawo ki kwanta ki ƙara hutawa kinji" yace idon shi akan ta, jinjina mai kai tayi fuskakadaran kadahan ta zame jikinta ta kwanta ta ba wa Babiya baya.... Comments fans🥰🙏 🫀MUGUWAR TSOKA 🫀 {🫀TA'ARE KALLUƊE} [Muscle Cramp🫀] ) عضلة سيئة ( 🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_ https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 written and Created ~~~~~~~~~~~~~~ ِبسم الله الرحمن الرحيم By Yardajjiya👩 💻 Page. Nine "To ka dai ji Abdussamad in Allah ya kai mu gobe zan tafi kamar yanda na faɗa maka" Babiyadake zaune cikin two settern tace tare da kallon Yaya dake zaune a ƙasa kusa da ƙafafunta, gyara zama Yaya yayi tare da kallon su Farisat dake gefe a zazzaune, "Hajiya na ce ba zamuƙarazama ba tukun" yace a ladabce, "ikon Allah to Abdussamad me yayi saura? Yarinya ta warketasse zuba tijara ma da take, Alhamdulillahi ƴan uwanta sun sami natsuwan da muke so, tozamanme kuma zanyi? Ba se in tattara in koma inda na fi wayau ba" ta idda maganan tare da kamahaɓa, jinjina mata kai yayi tare da faɗin "haka ne Hajiya, amma in ki ka ƙara mana kwanaki bazamu ƙi ba, muna buƙata, zaman da ki ka yi damu ya temaka sosai wajen kore mana damuwoyinmu" yayi maganan cike da fata, "ba tun yau ba fa Yaya Abdussamad muke fama da Hajiya akantazauna da ku, ni banga abinda za ta yo ma a can gidan ba, banda kewa me ne ne a gidan, itaɗayace fa, se su Gude da suke kai mata ziyara lokaci zuwa lokaci, nan ga ki ga su Farisat ga YayaAbdussamad za ku rungumi juna ku amshi duk wani sauyi da rayuwa ya zo muku da shi, bawanda yaji bare ya gani" Lurwanu yace cike da damuwa.... "Hajiya dan Allah ki ma daina wannan maganan, Yaya Ali fa yace ba inda ma zaki koma" Balarabeyace tare da kallon ta, harara ta banka mai tare da faɗin "tunda haihuwa na yayi ai se ya sakamun doka inbi" "to wai meyasa ku ke damun kan ku akan ta zauna ne? Ta tafi mana kewanmuma ba ze barta zama lafiya ba" Insu tace tare da kauda kai, "kaji ko Abdussamad wannanyarinyarta na mun hawan ƙawara, in na rufe ido na cafkota se ta fahimci ainihin Nafisatu dan ba zanyi dubi da bata da ƙoshin lafiya ba, ko asibiti ne akanta se ta lallasu" ta idda maganan tare danunayanda zata lallasata, Babiya tace murya ɓa ce, dariya su Farisat suka saki tare da bin ta daido, murmushi Yaya ya saki tare da faɗin "Hajiya ina ganin mu bi maganan Ali, dan ina ga hakanzefi dai-dai" "to Abdussamad ba wai ƙin ta naku nayi ba, da gidana me ze kai ni rufowa in dawogidanƴaƴa in reshe, ai be ma yi ba" "a'a Hajiya ai dalili ne yasa, da da babu waya ganki? Kamawatayi" Yaya yace cike da natsuwa, "to shi gidan can fa? Wallahi yaran anguwan nan ba kirki ne dasuba, suna kula da babu kowa za su iya haurawa su yashe ni, to me aka yi kenan?" "Hajiya ba gaBalarabe ba, ai shi ze dinga kwana" Lurwanu yace tare da kallon ta, "kayya Lurwanu bar batunnan, Balarabe in ya fice tun safe ba komawa ze ba se yamma, da ma ina can ne ko din cinabinci ya dawo, amma ba na nan ba kallon gidan ze yi ba in ba barci yaji ba" "ai Hajiya bakya nankobarcin ma ba koma yi zanyi ba, kin san inda ki ke nan nake" Balarabe yace cikin gaskiyanshi, harara ta zabga mai tare da faɗin "tunda nono ka ke sha ai seka cigaba da naniƙemun" ta iddamaganan cike da takaicin shi, danne bakuna su Yasmin suka yi dan kar su saki dariyan da yakawo musu ziyara.... "Malam ka zama namiji fa" Lurwanu yace tare da sakin ƙaramar dariya, "kar ka ga lefina malaminda fa gaskiyana" yace tare da gyara zama, "ka ji Yaya Balarabe ka zo mu zauna in ita ba zatazauna ba ta tafi" Insu tace tare da sakin mai murmushi, "to tabbatacciya, duk cikin ku ke cemebakin magana" Babiya tace tare da watsa mata harara, "ai muna tare Insu baby ita ma zatasakkone" Balarabe yace tare da sakin mata murmushi, "am Hajiya ina ganin shi gidan a saka ƴanhayatunda ki na gudun a barshi haka" Yaya yace cikin sigan san jin ta bakin ta.... "To shikenan ya na iya tunda kunfi ƙarfi na, ance sarkin yawa yafi na ƙarfi, se in zaunan, sedai shi gidan Lurwanu ya koma shi da iyalin shi tunda a haya yake zaune, har yau gama gininshi yagagare shi" "hakan ma yafi" Balarabe yace tare da gyara zama, "to shikenan kai Lurwanusekukoma can ɗin, kayanta da zata iya amfani da su anan kai Balarabe se ka kwaso mata, wandabazata yi anfani da su ba se a tattarasu waje guda a adana" jinjina mai kai sukayi da kulawa, gyarazama Yaya yayi cikin komawa serious yace "Hajiya akwai abinda ya faru wanda ban miki bayani ba" yayi maganan a ladabce, ba shi dukkan natsuwanta tayi tare da zuba mai ido, "ban yankehukunci a lokacin da nuna muku baku isa ba ko wani abu na daban, na yanke ne dan damandanasamu a lokacin, in na ce zan tsaya fahimtar da ku kafin in aiwatar da abun daman ze kuɓucemun" jinjina mai kai tayi cike da fahimta, "na ɗaurawa Insiyya aure ranar da mahaifiyarsutacikakwana uku a ƙasa" "to! Allah me iko, ita kuma se ta riga ƴan uwanta kenan, a ina mijin yake" Babiya tace kamar ba ta san da maganan ba, murmurshi ya saki tare da faɗin "Allah ne yaƙaddara na ta gaba da na su, amma ita kanta ba ta san da maganan ba se da aka ɗaura" damamaki duk suka kalleshi, jinjina kai yayi tare da gyara zama a natse ya fara koro musuasalinlabarin da ya haddasa ɗaura auren, "Allahu Akbar Allah sarki Amina ba ki zo kin tadda abindaki ka hasaso tattare damu ba, akasin shi ki ka tarar, baiwar Allah duk abinda muka mata batataɓaɗaga ido ta kallemu ba, se uzuri da take mana, ban zame mata uwa kamar yanda ta so ba, munmuzguna mata, mun ƙunsa mata baƙin ciki wanda ni kaina yau in na tuna ina jin kunya datausayin kaina, Allah ka gafarta ma Amina, kasa aljanna ya zama mako ma a gareta, sabodajinina ta bar wanda ke matuƙar ƙaunanta, saboda ta rayu da shi ta saɓawa iyayenta, se dai ni banzame mata uwa ta gari ba, ta rayu damu a marainiya ta mutu a marainiya" ta idda maganantareda fashewa da kuka, kuka tayi sosai wanda ita kanta ta manta lokacin da tayi kuka irin hakan.... "Hajiya dan Allah ki yi haƙuri, Amina ba ta taɓa ƙullatan ki ba, kullum magananta shine zaki fahimci wacece ita, zaki ƙaunaceta da dukkan zuciya ki, zaki gane gaskiya, zaki rumgumetakamar yanda iyayenta suke rungumarta" Yaya yace murya na rawa, jinjina kai tayi tare dasakinhawaye cikin rawar murya tace "na sani Abdussamad Amina ba ta da ƙulli, da tana da shi natabbata ido ba zata ɗaga ta kalli ɗaya a cikin mu ba, duk hasashen da take be tabbata ba, yazame mata mafarki Abdussamad, ban gane gaskiya ba se a ƙurarren lokaci" ta idda nagananmurya na rawa, "haka ne wannan" Lurwanu yace jiki a sanyaye, "wallahi na goya baya ɗari bisaɗari, Allah ya ba su ikon cika mata burinta" Hajiya ta kuma cewa tare da share hawaye, "amen- amen" Yaya yace tare da goge na shi, fashewa da kuka Babiya ta kuma jiki na ƙyarma tace"Allah ka yafe mu ka yafe ma baiwar ka" "Hajiya dan Allah ki yi haƙuri" Balarabe yace a sanyaye, "kayyaBalarabe kayya, barni inyi, Allah ka ɗai yasan irin bakin cikin da yarinyar nan ta ƙumsa a zamantakewan da tayi damu" "to ku barta tayi mana tunda a na ta rarrashinta ta ƙi dainawa, inmu muke yi tace ba ma da tawakkali" Insu tace tare da miƙewa ta share hawayenta ta ƙarisoindatake ta ciro hulan kanta ta fara goge mata hawayen da suka kasa tsayawa na ta idanunnazubdaruwan hawaye, kallon saman parlorn tayi tare da faɗin "Anty ki na ina? Zo ki ji yau Hajiya Nafisatu ce ke miki addu'a, duk abinda ki ka faɗa mana yana ta tabbatuwa" ta idda maganantareda sauke kanta, jawota Babiya tayi tare da faɗin "Allah ya jaddada rahma gareta" "amen" sukacebaku na a haɗe, tasowa su Farisat suka yi gaba ɗayansu suka dawo inda take suka rumgumetacike da so da ƙauna tare da goge fuskokin su da hawaye ya wanke tas.... "Yanzu Yaya Abdussamad da shi SSB aka ɗaura mata aure!" Balarabe yace tare da kallonYayaatsorace, murmushi ya saki tare da faɗin "eh Balarabe" Yaya yace tare da ajiye wayan dakeriƙeahannun shi a gefe, zare ido yayi tare da faɗin "Yaya Abdussamad ba ka ganin da matsala! Insuƙaramace fa, sannan ba lafiyayya ba ce" "kar ka damu Balarabe, Allah ze temaketa, munatasataa addu'a" "in sha Allah" Lurwanu yace cike da ta'ajibin labarin da suka gama saurara, "ni kaɗai gayya Yaya Balarabe, Anty ta yarda da ni bazan bari taji kunya ba, zan tabbatar mu ku da ƙwarewata" Insu da ta ɗago fuska tace idanta akan shi, "in sha Allah" Babiya tace tare da shafakanta, murmushi su Lurwanu suka saki zukata cike da mamakin wannan lamari, maganansakanni a kunni Farisat ta ma Yasmin, kallon Insu Yasmin tayi tana niyyan magana tace "ni cekan" "jamilun" Farisat tace da karfi, "goran" Yasmin tace tare da kallon Nafisat ta ƙyalƙyacedadariya, "goruba" Nafisat tace cike da takaici, "ku muje" Farisat tace tare da tashi ta nufi tsakar gidan a guje, dafa mata baya suka yi zuciyoyin ƙal, bin su da ido su Yaya suka yi cike da tausayawa ... "Baba Kalla ba mu aron tabarmanka" Insu tace da ƙarfi tare da isa wajen shi, tashi yayi da sauri ya shige ɗakin shi, be jima ba ya fito riƙe da tabarman ya miƙa mata, "mungode Baba Kalla" tacetare da wuce wa da sauri, murmushi ya saki ya bi ta da raunataccen kallo, girgiza kai yayi yakauda daga gare ta tare da goge hawaye, "Allah ya kai rahma gare ki Hajiya" yace murya narawa, a guje ta ƙarisa inda suke tare da shinfiɗa tabarman ta zauna, zama suka yi gaba ɗayan su, tareda ware yatsu huɗu gaba ɗaya suka ajiye a kan tabarman tare da faɗin "waraaa wara" bakunaahaɗe, ɗaga yatsa manuniya na ɗayan hannunta Farisat tayi tare da sakawa a yatsanta manuniyatare da faɗin "jamilun, goran, goruba, kan, jamilun, goran, goruba, kan" haka tayi ta lissafayatsun su tana tsayawa a ƙarshen yatsan Insu ta naɗe yatsa ɗaya tare da sakin murmushi, hakata dinga zaga yatsun su, duk wacce ƙarshe ya zo da wanda ta zaɓa za ta cire yatsa, Insu cetafaracire hannunta akan tayi winner, se Farisat se Yasmin Nafisat ce ta zo a ƙarshe da raguwanyatsaɗaya da ba ta cire ba, zare ido tayi tare da yunƙurin miƙewa, jawota Insu tayi tare da faɗin"wallahi baki isa ba" ihu ta saki tare da kiran Yaya, dariya Yasmin da Farisat suka saki taredafaɗin "lallai su Nafisat iyayen wayau, to zo mu ci" "wayyo Allah ku mun afwa hannuna ciwoyakemun" tace a marairaice, "ai ko tsintsinkewa yake se mun sha na bati yarinya" Insu tace taredagyara zama, haɗa hannu tayi tare da ɗagowa a hankali, na ta hannun Insu ta ɗago tare da sakinmurmushi, "a hankali please Anty Insu" tace kaman zata saki kuka, jinjina mata kai tayi taredasakin murmurshi, ɗago hannayenta dake haɗe waje ɗaya tayi a hankali, kai hannayenta biyuInsutayi tare da dukan hannayen Nafisat dake haɗe, "ɗayayan-ɗayayan" tace yayinda ta ɗagoyatsunta ma bi da ƙarami, Nafisat kuma ta ɗago manuniya, dariya ta saki cike da jin daɗi taredafaɗin "baki ci ba" tana kai nan ta ƙara kai mata bugun, babban yatsu ta ɗago ita kuma ta ɗagoƙanana, haka su ka dinga sosai Insu ta sha hannayen Nafisat, se da ga ƙarshe suka nuna iri ɗaya, nan Nafisat ta saki ihun farin ciki tare da kallon Insu dake cewa "na dai sha, saura ƴar kauce, saita mun hannu" tace tare da gyara zama, haka ta dinga kai ma tafin hannun Nafisat duka, dukda in ta kawo tana ƙoƙarin kaucewa amma se Insu ta samu, nan ma se da suka fafata Allahyabawa Nafisat sa'a ta kauce, gyara zama Yasmin tayi dan ita ma tayi na ta .... Se dai tafiya be yi nisa ba Nafisat ta yi nasara, juyawa ga Farisat dake sakin murmushi Nafisat tayi tare da faɗin "muje" gyara zama tayi ita ma sosai suka fafata kafin Nafisat ta kuɓuce ahannunta, "a ƙara zubawa" Yasmin tace tare da gyara zama.... Haka suka cigaba da rayuwa, tun ba sa sakin jiki suka fara, sun rungumi ƙaddaran su da hannubiyu, ba wai ba sa tuna rayuwarsu da Anty ba ne, suna yawan tunawa akai-akai, se dai addu'o'insu yafi kukan su yawa, ba su yarda damuwa ya rinjayi addu'o'insu gareta ba, sallama Salmanyayi shida Sadam da ya ɗakko daga makaranta, murmushi Farisat ta saki tare da faɗin "ɗan jami'a" zama yayi tare da fesar da numfashi da ƙarfi cike da gajiyan da ya kwaso yace "kai wannancoursɗin bala'i ne,

Chapter 11 of 109