Share this page
da ta kusan zawace wa kafin ta hangoruwan allura da sirinji, hannu na kyarma ta fiddo shi ta zuƙi alluran, sokawa a jijiyan hannuntatayi cikin fara fita hayyaci.... Tana gama juye ruwan alluran ta saki sirinji ta zube a wajen tana sakin zantuka barkatai, bandamabuga babu abinda take, ta juya nan ta ɗago anan ta baje a can, da ƙyar abinda take fatayakawo mata ziyara ya zo ... Taka stair's take a natse, sanye take cikin three quartern wando red colour da dogon riga mezubin tazarce boter milk sunyi masifan amsanta, kai tsaye inda jerun kujerun parlorn suketanufa, zama tayi a two seater's tare da jingina jikinta da jikinshi, sallama Lawiza tayi a natsetareda faɗin "kin sami sakkowa?" Da mamaki ta ɗago kai ta zube nata tare da faɗin "baki tafi ba?Dare yayi sosai fa" murmurshi ta saki tare da faɗin "ina nan, Daddynsu yace in zauna taredake" "no su takwaran Anty fa? Tashi ki je ba na cikin ko wani matsala" ta idda maganan idonta anata... Ƙaramar dariya Lawiza ta saki tare da faɗin "akwai Umma ai a gidan, zata kula da su sosai bazasu yi kewa ba" "Umma! Hajiyar Ibrahim kenan?" Tace tare da kafeta da ido, murmurshi ta saki tare da faɗin "a'a mahaifiyata ce" tayi maganan fuskanta yalwace da murmushi, "ma sha Allah, amma duk da haka da kin koma" "a'a tashi muje ki ci abinci tun wanda ki ka tsakura da safebaki ƙara komai ba fa" tace da kulawa... Shagwaɓe fuska tayi tare da faɗin "ba na da apatite ne shiyasa" "duk da haka za ki ci, gayi cannamiki blending ɗin fruits muje ki ɗanɗana na san za ki ji daɗin shi" murmushi ta saki tare dafaɗin"wow haɗin na musamman ne kenan?" Tace tare da miƙewa ta nufa can, "sosai, se kin ma shatukun" tace cike da ƙawata mata shi, murmushi ta saki tare da faɗin "har na fara jiyo shi abaki na" tayi magana tare da jan kujera ta zauna.... Serving ɗinta tayi a natse, funkasau ne da miyan kayan ciki, gyara zama tayi tare da faɗin"wowirin wannan aroma haka dake tashi Anty Lawiza, har na ji nayi rabin ƙoshi" dariya Lawiza tasaki tare da faɗin "fara ci dai kar ya zo sauran rabin ƙoshin ya cika she kafin ki kai ga ci" ƙaramar dariya ta saki tare da bismillah ta fara ci, a natse ta cinye biyu ta goge hannu ta dau cupɗinniƙaƙƙen fruits ɗin ta tashi daga wajen, komawa cikin parlorn tayi ta zauna idonta akanhotontaita da Anty.... Sallama Gude tayi ta shigo a natse, ganinta zaune cikin parlorn yasata sakin murmushi taredafaɗin "Insu kin fito?" Kallonta tayi murmurshi faɗaɗe a saman fuskanta tare da faɗin "ehBabaMaude ya wunin ku?" "Mun wuni lafiya, ina ta zuba idon ganin fitowanki amma shiru, na cekolafiya?" Ta idda maganan tare da zube mata ido, guntun murmushi ta saki tare da faɗin"bangane ma jikin ba ne Baba Maude" tayi maganan tare da ajiye cup ɗin hannunta ta miƙe... "Da kin faɗa an kira doctor ai" tace tare da kauda kai, "no be kai har haka ba, na san in shaAllahna kwanta na tashi ze bari" "to shikenan dama Hajiya ce ke son magana dake tun ɗazu takekira" tsayawa tayi daga yunkurin wuce wa da take ta juyo tare da faɗin "ba ni numberta in na komaciki zan kira ta" ta idda maganan tare da ɗago wayanta... Ba musu ta karanto mata, "nagode Baba Maude se da safe" tace tare da wuce wa ɓangarendining, zaran tissue tayi ta goge baki ta jefa a dustbin ɗin dake gefe tare da faɗin "Anty Lawizaki je ki kwanta" "ba wani matsala ko?" Tace cike da kulawa, "no ba komai" tace tare da sakinguntunmurmushi, "ba ni in sa miki numberta, please ki na jin wani abu ki kira ni" ta idda maganandamagiya, jinjina mata kai tayi tare da ba ta wayan.... Numberta ta saka ta yi saving ta kira, murmushi ta saki jin rurin da wayanta ya ɗauka ta katsekiran ta miƙa mata wayan, murmushi ta saki ta amsa ta wuce tare da faɗin "asuba ta gari" bintada ido tayi har ta ɓacewa ganinta, murmurshi ta saki tare da fara harhaɗa kwanonikan dataɓata, "yau zamu kwana anan kenan Lawiza?" Ta jiyo saukan muryan Baba Maude da ba ta sanlokacinda ta iso inda take ba.... Da sauri ta juyo tare da baza mata ido, murmushi ta sakin mata tare da faɗin "na ga yaukinwucelokacin tafiyan ki ne, na ce ko kwana zamu yi?" Ta idda maganan murmushi ƙawace a fuskanta, murmushi ta saki tare da faɗin "eh in sha Allah, ba ta ji daɗi sosai ba ne.... "To ikon Allah ai muna nan a gidan, da kin koma gida" murmushi ta saki tare da faɗin "ba damuwa, Daddyn Zarah yace in tsaya ko za ta buƙaci wani abu" tana kai nan ta wuce dan sanarwa masu tsaftace wajen" kama haɓa Baba Maude da ta bi ta da ido tayi tare da faɗin"kaii amma yaro yaron ne, wannan da ta san dalilin da ya haddasawa yarinyar nan ciwon wataƙiladako kallon inda take ba za ta yi ba, amma ji yanda take ta wani rawar jiki da ɓari, Allah me yandaya so, ita kuma daga jin mutum na da mata ta ɗaurawa kanta wahala, daga haɗuwa da mutumjiya-jiya ki zaƙe haka? Allah ya fishshemu taɓewa, amma wannan abu da ban mamaki yake, bazan sanar dake badaƙalar da ake ba, se dai in kai ki ki gani da idanunki, shima dake sunanshi namiji ya dake har da ce miki ki kwana, eh mana ki kwana shi kuma ya kwana yana tsaratadaƙarairayi mana, Allah dai ya kwantar da bala'i a duk inda yake neman tashi" tana kai nantafice... Tana shiga ta ajiye wayan ta tuɓe kayan jikinta ta saka na barci riga iya gwiwa da gajerenwandohula ta daura ta shafa perfume, wucewa inda ta jera jakunkunanta tayi ta zage ash colour taɗakko roban maganinta ta zage jakan ta wuce inda fridge yake ta ɗakko ruwa me sauƙinsanyi tanufi saman sofa, murda murfin tayi da ƙarfi se taji abuɗe ma yake, cike da mamaki ta bi robandaido, ganin hakan ba amfanin da ze mata ta watsar da komai ta ɗau magani ta sha ta maidamurfin ta miƙe ta ajiye a saman dressing mirror, kashe wutan ɗakin tayi ta haye gado ta jawowayanta ta danna number Hajiya.... "Ka kira ƙanwarka ka ji jikin mara lafiyan da suke da kuwa?" Shureim yace tare da kallonAnnur, miƙa ma waiter littafin hannun shi yayi tare da faɗin "kar a cika yaji a chicken pepe" jinjinamai kai yayi ya wuce, juyawa ga Shureim yayi tare da faɗin "kai me ya hana ka kira ka ji?" Zamejiki ajikin kujeran da yake kai yayi ya jingina sosai tare da faɗin "tayi blocked ɗina" "what! Ya akayi haka?" Yace da mamaki, guntun tsaki ya saki tare da lumshe ido.... "Zubair ya buɗe aiki" Sagir yace tare da sakin dariya, zare ido yayi tare da faɗin "Morata yabayyana kenan!" "Wallahi mantawa nayi sam" Zubair yace tare da nuna zallan takaicin kanshi dayaji, "sabone, an saba hakan" Khalid yace tare da bugan kafaɗanshi shi, ajiye musu abincikandasuka zaɓa restaurant server's suka yi cike da natsuwa, "a ci lafiya" suka ce tare da barinwajen..... "Ka fuske ka mata magana da number da ta sani" Annur yace tare da kallon shi, buɗe idoyayi tare da faɗin "har da shi" "subhanallahi ƙanwata" yace tare da zaro wayan shi a aljihu ya dannanumberta... Miƙa mata wayan shafa'atu ɗiyar Habiba dake kallo tayi tare da faɗin "ana kira" amsa tayi taɗaga ta kara a kunni saboda ganin me kiran, "Yayana tace a hankali, sa wayan a speaker yayi tareda ajiyewa a gefe ya fara cin abinci, "ƙanwata" yace a natse, "na'am kuna lafiya?" "Alhamdulillahku yi mana afwa, tun jiya ba muji komawan ku ba munyi busy ne" "no ba matsala ya shirye- shirye?" Tace a natse, "Alhamdulillah ƙanwata ya me jikin?" Shiru tayi na ɗan daƙiƙu kafintace"ta rasu" buɗe ido suka yi gaba ɗayansu tare da zuba ma wayan ido.... "Ta rasu kuma ƙanwata!" Annur yace a ɗan rikice, "eh" tace a dake, "yaushe!" Yace tare daajiyefork da ƙaramin knife din hannun shi, "jiya da yamma" "subhanallahi ƙanwata, shine ki kakasakira ki sanar mana? Kin kyauta kenan ko?" "Ka yi haƙuri mantawa na yi" tace a hankali, "shikenanAllah ya gafarta mata, in sha Allah zamu zo ta'aziyya gobe" "Allah ya yarda nagode" tace ahankali tare da zame wayan.... "Tana cikin alhini sosai" Khalid yace tare da kallon Annur, sauke numfashi yayi tare da faɗin"hakane" sauke ajiyan zuciya Shureim da ya miƙe zaune da kyau yayi tare da faɗin "rasuwar mahaifiyarsu ne ze dawo musu sabo" "haka ne" Annur ya kuma cewa jiki a sanyaye... Miƙa ma Shafa'atu wayan tayi ta miƙe a natse ta fice, kai tsaye ɗakin Farisat ta shiga, taddata tayi ita da Sha'awanatu suna taɓa hira sama-sama, zama tayi gefenta tare da faɗin "Yaya Annurya kira ni yanzu, yace gobe za su zo ta'aziyya" "Allah ya kai mu gobe ba shine ranar arebiannightba?" "Shine" tace tare da kallon ta, "se dai su yi haƙuri ba zamu samu zuwa ba" tace a hankali, jinjina mata kai tayi tare da wuce wa ƙuryan gadon ta kwanta a hankali.... Tun daga wannan rana walwalansu ya ragu, ba su ƙara halartan wani event's na bikin Annur ba, se fatan alheri da suka bi amarya da ango da shi, ta ɓangaren Habiba kuwa ta dangana ta amshi kaddararta da hannu biyu ta cigaba da neman gafaran mahaliccinta tare da bin Zuwaira daaddu'a, Suwaiba kuwa ba ƙaramin rikicewa jikinta yayi ba, ba masu jinya se su Farisat, sukejinyarta, Gude ta tattara ta koma gidanta tun ranar uku, Jummai ma Yaya yace ta komai, Munari ma ta koma dan mijin kwana ɗaya ma ya ba ta, Yasmin ta yi registration har ta fara ɗaukanlecture... Yau ta kama cikan Zuwaira bakwai da rasuwa, a yau kuma su Sha'awanatu za su koma, "inaRufa'in ya zo ya ɗauki wannna ya saka a motan" Babiya tace tare da kallon Jummai dake faɗin"har can ze kai su?" "A'a ke kuma wani can, shi da iya tuƙin shi a cikin gari ya tsaya, tasha zekai su su hau mota su tafi" Babiya tace tare da kallon Habiba da ta fito daga ɗakin Insu, "ina sukeHabiba biyu fa ta yi" "gamu nan" Shafa'atu tace tare da fitowa, "to ku hanzarta" tace tare dabinta da ido, fitowa Sha'awanatu tayi tare faɗin "ina Sa'adatun?" "Ta tafi school ɗazu ba jimawa" Farisat tace tare da kallon ta, "to a yayyafi juna, zamu tafi Allah ya saka da alheri, munji daɗinzaman da muka yi da ku, kuma mun samu gamsuwa a zukatan mu, mun tabbata mahaifiyar muba zata kasance cikin damuwa ba, za ta kasance cikin aminci.... " Mama dan Allah ki cigaba da ga yanda ki ke yanzu, kar wani abu ya canza ki, wallahi rayuwahaka yafi daɗi" tayi maganan hawaye na taruwa a idonta, "ba komai Sha'awanatu ni kainanagamsu da canzawan da tayi, ku ma ku zauna lafiya a gidajen ku, dan Allah ku riƙe aurenkuda kyau, ku yi biyayya ga mazajen ku, se sun ɗaga ƙafa za ku shiga aljanna, ni dai har Allahyarabani da Malama wallahi irin waƴan abubuwan be taɓa shiga tsakanina da shi ba bare in ce ni kukaga ina yi ku ka je kuna wa mazajenku, to ita dai mahaifiyarku Allah ya kawo ƙarshen zamantaagidan mahaifin ku, se ku rungumi ƙaddara ku rayu da na ku mazajen lafiya"... Tun asali da ma bamu taɓa jin ance yau ga ɗaya daga cikin ku biyun nan an kawo ƙararta ba, sedai in kuma Habiba ɓoye mana take, amma mu dai ba mu ji ba, to yanda ku ke lafiyan nankuƙaragayyato lafiyan nan ku ƙulla abota ta har abada da ita" jinjina kai suka yi cike da gamsuwa, miƙewa suka yi suka ƙara sallaman su suka nufi ƙofa, dafa musu baya Jummai da su Farisat sukayi, dan rakiya... Kallon Habiba Suwaiba dake kwance tayi tare da faɗin "Anty Habiba dan Allah mu manta bayamu gyara gaba" murmushi ta saki tare da faɗin "na daɗe da manta baya Suwaiba, da zaniyagogeshi daga ƙaddarana da na goge dan ba na so jikokin mu su riski labarika marasa daɗin ji dasaurara" jinjina mata kai tayi tare da faɗin "wallahi munyi kuskure, mun aikata babban kuskurewanda in na tuna ni da kaina takaici da baƙin cikin kaina nake ji" tayi maganan tare da sakinhawayen da suka cika mata ido suka gangaro... "A she haka kunya yake, ban taɓa zaton kunya ya kai haka ba se a wannan yanayin, ki dubaki ga, yaran Amina suke ɗawainiya da ni tunda ciwon nan ya kwantar da ni, ba su taɓa gajiyawa ba, damuwan su su ga na miƙe, ko yaran da na haifa ba su damu har haka ba, kina gani suna gidacan, zuwa ma duba ni se la'asar in sun ga dama, amma su ko da yaushe idon su hankalin su na kaina, wallahi kunyar su nake ji, ji nake tamkar ƙasa ta tsage in shige a daina ganina" ta idda naganankuka na ƙwace mata... Juyawa ga Babiya Habiba tayi tare da faɗin "Hajiya dama haka yaran nan suke? Dama ba suƙullace mu ba? Dama kimanmu da darajanmu na nan a idanun su ba abinda ya taɓa su?" "HmmHabiba kenan, yanda ki ka gansu haka Amina take, ba ta tafi da ƙullin ko ɗaya daga cikinmuba, ta koya musu san mu, da ƙaunarmu, da mutuntamu da darajtamu, da haƙuri akan duk wani abuda zamu bijiromusu da shi, rayuwar da nayi da su na fahimci kyakykyawan zuciyan da Allahyama Amina, dan shike jikin ƴaƴanta"... Jan majina Suwaiba tayi tare da faɗin "tabbas ni ma na fahimci haka, Allah ka kyautata zukatanmu, ka nesanta su daga sahun mugayen tsokoki wanda ba sa ganin alheri se sharri, wandabasayaba karamci, wanda hassada da ƙyashi da san kai ya ma yawa butulci shine adon sakayyansu" "amen" suka ce bakuna a haɗe, "gobe zan koma gida, se ki zo mu koma can tare ko?" Suwaibatace tare da goge hawaye, jinjina kai Habiba tayi cike da gamsuwa, "shi nan ɗin ba gida baneSuwaiba?" Yaya da ke tsaye a ƙofan shigowa yace tare da fara takowa ciki... "A'a Yaya Abdussamad gida ne, gani nayi kaman be dace ta zauna a nan ɗin ba" murmushi yasaki tare da zama a natse, "se gidan ki ne ya kamata ko?" Yace hankali kwance, girgiza kai tayi taredagoge hawaye, "anan za ta cigaba da zama, Allah ya ba mu ikon haƙuri da juna" yace tare damiƙewa ya nufi side ɗin shi, fashewa da kuka Habiba tayi tare da haɗa kai da jikin kujera, batataɓa zato ko tsammanin ze barta ta zauna a gidan shi ba.... "Sa'adatu Sama'ila" wani gandiroba dake riƙe da farar takarda a hannu yace tare da kallonjerunmutanen dake zazaune, miƙewa Sa'adatu dake sanye da hijab har ƙasa da facemask tayi tanufeshi, "muje" yace tare da yin gaba ta bishi, buɗe musu babban ƙofar shiga prison ɗin masutsarosuka yi suka shige, ja yayi ya tsaya tare da nuna mata inda zata shiga, tana shiga ta tadda policeuku tsaye biyar kuma zaune a gefe, isa wajen waƴanda ke tsayen tayi a natse, ɗaukan na'uranbincike ɗaya daga ciki yayi ya fara bincikanta, jin babu wani abun da be tace ba tattare daitayanuna mata wani ƙofa, turawa tayi ta shige, tadda gandirobobi maza da mata tayi zazzaunekowana aikin gabanshi, "akwai abinda ki ka zo mishi da shine?" Daya daga ciki tace tare da kallonta.... Girgiza kai tayi tare da faɗin "ba komai" "okay muje" tace tare da miƙewa, bin ta tayi a natse, ƙwanƙwasa babban ƙofar da ze sadasu da inda prisoner's suke ta yi, buɗe musu aka yi sukashige, nan ta tadda prisoner's barbaje, kowa na aikin da ya dace, ratsa ciki suka yi suka nufi wani officeda ake ganawa da wanda aka zo dubawa, suna shiga, ta sanar da sunan wanda suka zo nema, kiran waya ɗaya daga ciki yayi ya sanar, ba ta kujera a ka yi ta zauna tare da baza ido danganinta inda ze shigo.... Zamanta babu jimawa se gashi ya shigo da rakiyan gandirobobi uku, nuna mai kujeran zamasukayi suka ja gefe dan jiran ya gama, "mintuna goma ki ke da" wacce ta shigo da ita tace taredanuna mata shi ta ja gefe, tashi tayi da sauri ta nufe shi tare da faɗin Baba" a razane ya ɗagoyasauke idanun shi akan ta cikin ɗin bin mamaki dan ba ze iya manta muryan nan ba har abada.... Rungumeshi tayi da ƙarfi tare da fashewa da kuka, so yake ya tureta se dai ko motsi maraƙarfi ya kasa bare me ƙarfi, yasan be da wannan ƙarfin ba ze iya ba, sakin shi tayi ta duƙa a kusadashi tare da faɗin "gidan da daɗi? Ya fi waje daɗi ko?" Ta mai tambayan idonta ƙyamakan fuskanshi, kafeta da ido kawai yayi, kaman be ganeta ba, murmushi ta saki tare da goge hawaye, "abubuwabiyu ne ke tafe da ni, ɗaya na farin ciki ɗaya akasin shi, bari in fara bakq mara daɗin wataƙilainna faɗa maka na farin cikin ya wanke shi, se dai ina fata yaranka ba su rigani ba, dan ba zanji daɗin hakan ba" ta idda maganan tare da sakin murmushi ganin ko ƙifta ido be yi ba yasa tasakinmurmushi tare da ƙara ƙasa da murya.... "Matar da ta zaɓe ka akan ƴarta ta mutu, matar da ta nemi kuɓutar da kai ta mutu, matar datarusa rayuwar ƴarta dan naka ya haska ta mutuuuu" taja u ɗin ƙarshe da tsayi, lumshe idoyayi hawayen da suka cika idon suka sakko, banda bugu da tsintsinkewa ba abinda zuciyanshi keyi semai-maita kalman ta mutu yake... "Ta mutu ta barka a duniyan, duniyar ta mu ce ni da kai, ya ka ga abin ze kasance, ta mututanakiran sunana, gunun burgewa, kowa na tunanin ina raye ne zuciyarta, so take ta ganni, sedai ni na san ta daɗe da burneni duk da ina raye, kuma duk saboda kai, kai guda ɗaya, ka san abindatake so ta faɗa musu a wannan lokacin?" Jin be yi ko motsi ba yasa ta faɗin "duk da ba za kasosani ba zan faɗa maka, so take tace musu sharri Sa'adatu ta mishi be aikata abinda ta ce yayi ba, so take tace ƙazafi ta mai saboda ya kamata turmi da taɓarya da maƙofcinshi, so take tacemusu, Sa'adatu maƙaryaciya ce, ta aikata hakan ne dan san kanta, so take tace musu in kunyi idohuɗuda Sa'adatu ku tabbatar mata da la'antata a kanta, se dai Allah be bata ikon faɗin ko ɗayaba, yaamshe ta tana yunƙurin furtawa, ta tafi an rufe shafinta, daman cika buri da muradina akaban"... "Da ka barni na tafi salin alim lokacin da na nuna na fi ƙarfin ku da yau ba ka zo wajen nanba, dasunanka be ɓaci a idon duniya ba, kai Allah yayi ma barrister Amina Sa'eed Garba albarakabadadin ita ba na san da se ka birne ni da raina, ba da din ita na da kayan ɗakin da matarka ta sedayace ce ka, shikenan ka fita daga tarkon da na ɗana maka" tana kai nan ta ƙyalƙyace da dariya, "nasan dama wannan amsan kake dakon jiran ji ko?" Ta je fa mai tambayan tare da ƙasa da murya, "eh ni ce nan, ni ce na shirya komai, kuma na yi nasara, tunda ga ka zaune waje ɗaya, ba shigabafita, yanzu waye ya isa hanani rawar gaban hantsi? Kai ne? ko matarka? Ko wawayen yarankamarasa amfani?" Ta idda tambayan tare da sakin murmushi, haɗiye yawu yayi da ƙyar taredabinta da ido.... "Yau gaka a jail, matarka tana ƙasa, duk yanda ku ka so tarwatsamin rayuwa hakan be yuwuba, gani cikin aminci, ina rayuwa a inda nake sha'awa nake fata nake buri" ta idda maganantaredasakin murmushi, buɗe ido yayi ya bi ta da kallo me cike da tsana da ƙyama... "A'a tukunna adana wannan kallon ba yanzu ba se nan gaba kaɗan, dube ni a yanzu na isanakawo komai sun cika cif-cif, abinda nake fata ina samu a ko da yaushe, se in wuni guda inaɗibandaɗi ba me katse mun" ta idda maganan tare da zaro harshenta ta lashi leɓanta na kasa taredanuna irin zallan daɗin da take ji, ɗaga mai gira ɗaya tayi tare da faɗin "mabuƙata a kullumƙarayawa suke, kuma ba su nake, ko zaka hana ne?" Ta idda maganan da ɗan sauti.... "Gana farin cikin, abun farin ciki shine sauranka shekara ɗaya rak kayi free, zaka tashi kamantsuntsu, firi-firi" ta ƙarishe maganan tare da sakin murmushi, juyowa tayi fuska a matuƙar muttuke tare da faɗin "zan tabbatar maka da na cika ɗiya ta gari, wacce a kullumku ke tatsuniyar na zama, Isma'ila se na tabbatar da ka bi wannan matar da ka yi sadiyyan mutuwanta"tayi maganan cike da ƙunan zuci, ja baya kaɗan yayi cike da mamaki, "kai ka kashe munmahaifiya, kai ne sillar shiga halin da ta shiga, kai ne silan azabtuwar da tayi kafin mutuwarta, zaka bi ta ko da hakan ze sa jama'a dubu su mutu, wannan alƙawarina ne, kwanciyar hankalinkashine ka mutu kafin lokacin fitanka, ka mutu murus a rufe shafinka" tana kai nan ta zura hannuacikin fant dinta ta zaro sachet ɗin magani ta zura mai a aljihu tare da faɗin "ze temaka maka" tana kai nan ta miƙe ta nufi ƙofa, bin ta kawai yayi da idon dake zubda zafaffan hawaye, yanatuna shuɗaɗɗun abubuwa.... Tun ta sowanta ta taso da rawar kai, taƙi tsayawa tayi karatu, duk ranar da taje se ta gudukafinatashi, daga yau a ce an ganta a ɗakin wannan saurayin se gobe a ce an ganta a ɗakin wancan, abun ya wuce waje ya dawo har gidan shi, dalilin faruwar matsalan yamata da maƙofcinshi Alhaji Gambo me kuɗin anguwarsu, suna aikata masha'a a zauren gidan shi, ganin ba ma su luradawanzuwan shi ba ya sa shi shiga gida afujajan ya ɗakko taɓarya ya rabka mai a ka, jan jiki tayi cikin jin azaba ya fice sintiri haihuwar uwa da uba, yayi gidan shi ba tare da ya buɗe ko baki babare yayi ihu dan yasan yana ihu kan shi ze tonawa asiri.... Janta yayi kiyyy har cikin gida yana shiga ya hurgata dakin Mama ya mata dukan mutuwa, sumanta uku ta na farfaɗowa, banda numfarfashi ba abinda take iya saki, se da ya gama dukanta sannan ya zube ya fashe da kuka ya zayyane ma Mama abinda ya gani, Mama tayi kuka kamar zata mutu, ta zageta ta aibantata, se dai ganin hakan ba ze yi maganin komai ba suka komamatanasiha tare da nunashsheta hanyan ƙwarai, haka suka yi jinyarta har ta warke, ya hana tafitakobakin ƙofa, aikin gida kuma aka hana kowa yi se ita, a wannan lokacin ta jigata, dan ta kasajurewa neman me biya mata buƙata take ko ta halin ƙaƙa, gashi ba me shiga harkanta a gidabare ta samu fuskan yin ƙaryan da ta saba ta fice.... Ranar da ya zamemai rana mafi muni a rayuwa shine ranar da Mama ta tafi bikin ƴar ƙawarta, al'adanshi ne in dai ana zafi be iya zama da full kaya a jikin shi, tube riga yake ya zauna dashi sesinglet da dogon wando, yana dawo sallahn azhar ya tube riga ya ɗaga labule ya ɗau mafici yafara fifita... Ƙanwar Sa'adatu me suna Sa'adiyya ta kawo mai danbun da aka yi na rana ya ci lafiya ya koradaruwa ya kishingiɗa dan gyangyaɗa ƙailulan da ya saba, kafin a kira sallahn la'asar, tun dagawannan lokacin be ƙara fahimtar halin da duniya ke ciki ba, ya buɗe ido ne yaga Mama akanshi tana kuka jikin shi lilliɓe da zaninta, Sa'adatu duƙe gefe tana kuka zanin Yayarta lulluɓe ajikinta, be fahimci halin da ake ciki ba se ji da yayi wani maƙofcinshi na faɗin "Allah ya kyauta wannanjakanci da me yayi kama, ka rasa wacce zaka nema se ɗiyar cikin ka" nan ya fahimci me kefaruwa, kallon Mama yayi idon shi na zubda ruwan hawaye, ze yi magana ta girgiza mai kai tareda faɗin "kar ka ce komai, ko duk duniya za su yarda ni ba zan taɓa gazgatawa ba" in da yaji daɗi kenan, sauran yaran shi ma duk ba wanda ya amince, anyi haka da sati biyu ya ji an maka shi akotu, ana tuhumar shi da ma ƴar cikin shi fyaɗe, wannan shine abinda ya girgiza rayuwarshi, bafaɗi tashin da Mama ba tayi ba dan fiddashi amma babu amfani, dan wacce ta tsayama Sa'adatuba ta wasa ba ce, haka suna ji suna gani aka wuce da shi prison, yayi kuka har hawaye sunƙafemai, kullum in Mama ta zo se sun

Chapter 25 of 109