Share this page
wannan matakin, saboda tsayuwan da yayi ne yasagaba ɗaya muke haɗe kaman ƴan uwa, ina da tabbaci akan ze inganta rayuwar ki fiye da yandazaki zato ko hasashe, Yasmin Muhammad Shureim na matuƙar ƙaunarki, tunda nake da shi, yautsayin shekara 25 kenan ban taɓa jin ya furtawa wata mace kalman so ba se ke, ba zance miki akwai waƴanda ba sa nuna ra'ayi a kan shi ba, amma ke ya gani yake so, wallahi yana matuƙar sonki, Yasmin ba wai ina faɗa miki hakan dan kasantuwar shi na abokina ba ne, ina faɗa miki nedan ki farka daga barcin da kike kar ya juye zuwa mafarki".... "Na tabbata ko wasu iyaye za su yi wa ƴarsu fatan miji kaman shi, ba din yana abokina ba nakefaɗa miki hakan, dan yakasance hakan ne shiyasa nake faɗa miki hakan, kuma matsayindanabaki na ƴar uwa yasa har na fito fili yau nake miki bayani, wallahi yana sonki, so me tarinyawa, wanda duk zurfin ciki irin na shi se da ya fito ya faɗa mana da babban murya" ya idda maganancike da fata me haɗe da magiya.... Tunda ya fara bayanin take bin shi da ido, ba ta samu kauda idanu ba se da ya kai aya, guntunmurmushi ta saki tare da jan kujeran da take kai baya kaɗan ta miƙe, hankali kwance tace"Yayana dan Allah ka daina damun kan ka akan wannan batun, ba na soyayya ra'ayina kenan, bana jin ze canza zani ko nan gaba, ka zauna ka fahimtar da shi kaman yanda ka yi ƙoƙarinhakayanzu, ya je ya samu waƴanda suke nuna ra'ayi akan shi ya ƙaunace su, na tabbata ze mantada wannan shirmen da yake ma kallon so" tana kai nan ta wuce zuciyanta na tafarfasa, tana shigaparlorn ta kalli Farisat tare da faɗin "muje" "Yaya Salman be kira ba" tace tare da bin ta daido, "muje mu hau napep, ya same mu a gida" tace tare da sallaman su ta fice, murmushi Farisat tasaki ta miƙawa na kusa da ita me suna Sofie Idris babyn ta sallame su ta dafa mata baya.... Tunda ta juya ya bita da ido da baki a sake, mamaki yake wani irin taurin zuciya take da, tundaaka fara maganan su Zubair ke ƙoƙari fahimtar da ita amma amsa ɗaya take ba su, se da akazowannan gaɓar da Shureim ke gab da sabautuwa sannan ya yanke hukuncin saka ba ki, shimagashi ya zama a banza, sauke numfashi yayi me ɗumi tare da tuno yanda Shureimke azabtuwada ƙaunan da yake mata, be gama fita daga wannan mamakin ba ya hangesu suna shirinficewa, da sauri ya tashi ya bi su, murmushi Farisat da ta hangi tohowan shi ta ta saki tare da ja gatsaya, "a she anan matsalar take" tace tare da kallon Yasmin da ta tsaya ita ma, tsaki ta saki taredafaɗin "mutumin nan ba ze barni in huta ba se na mai kyakykyawan warning" "a'a ba wani warningki barshi a haka ma, ka so ba'a so ka ba ai yafi komai ciwo" shiru tayi har Annur ya ƙariso, "badai tafiya ba?" Yace tare da bin su da ido... Murmushi Farisat ta saki tare da faɗin "wallahi zamu biya hospital wajen gwajin nan ne" "ehyakamata, na ɗauka ma kunyi tun watannin baya da ki ka ce za ku yi" "a'a wallahi ba musamuyi ba, lokacin nan muna exams kasan se a hankali" "haka ne, Zubair ya muku maganan gidanmarayun da za mu kai ma ziyara sati me zuwa?" Ya idda maganan idon shi akan su, "a'a beyi ba" Farisat tace tare da kallon shi, "ya faɗa mun na manta ban faɗa miki ba ne" Yasmin tace taredakallon ta, "okay ka ji yayi a she, Allah ya kai mu" "amen, Chiaman ba ze samu daman dawowaasatin ba, amma yace a je kawai" "to hakan ma yayi Allah ya dawo da shi lafiya" "amen, danAllahbanda african time, muje da wuri mu dawo da wuri" "in sha Allah" suka ce bakuna a haɗe sukasallame shi suka fice.... Murmushi ya saki tare da sauke ajiyar zuciya ya juya ciki,,,,, napep suka tara a ƙofar gidansukashige suka nufi gida kai tsaye... "Hajiya inda kin tambayi shawaranmu da baki tuntuɓeta da maganan ba ma" Habiba tacecikebda rashin jin daɗin bayanin da Babiya ta gama zayyano musu, "Habiba menene a ciki danAllah? Yau kusan shekaru biyu da wasu watanni kenan Abdussamad na zaune haka babuaure, mun san kafin ya samu me maye mishi gurbin Amina aiki ne, amma kuma ko yaya ai yakamatayasamu wata ya aura, ni kwanakinan ƙaratowa suke, ba zan zauna jiddun wala hairun da suba, keSuwaiba kina gidanki ba zuwa za ki yi ki tare da su ba, ke ma Habiba fatan ki shige ciki nakedanba ƙaunan ganinki haka ba aure nake ba, ba ma miki fatan ƙare rayuwa a haka, da yarintar ki ajiki auren shine gatan ki, Mari girma daɗa riskanta yi ke, yanzu haka kuna gani inba kama matawani aikin a kayi ba wahala take sha, in ban nemo musu ko wacce zata kamanta musu ba yazanyi?" Babiya tace cike da rashin jin daɗin maganan Habiba... "Magana na ba ze samu kaman Amina ba ma be taso ba, ai ba'a ɓarin gari a kwashe duka, sannanHajiya in haka ma kike tunani, ai me hankali zaki samo mai, me shekaru wacce ta san ciwonkanta, ko banza za ta fahimci na shi da na ƴaƴan shi, amma Allah na tuba Hajiya ke fa ke mayarinyar nan ganin wata me hankali, wallahi ban taɓa sakata a sahun masu shi ba".... Suwaiba tace tare da kauda kai, "to gani nayi goyan Amina ce, kuma suma da a kawo musubareai gunda wacce suka sani suka rayu da ita" "a'a Hajiya wallahi ba goyan Amina ba ce ita, dagirmanta da hankalinta ta ganta, kalli idanun yarinyar nan da kyau, anan zaki fahimci ba tayi kokama da waƴanda Amina ta goya ba, yarinyar ba ta da natsuwa ba ta da kamun kai, ki na ganinfaa gabanki ranar da Sudais ya zo gaisheki yanda ta dinga wani shishshige mishi, ba dangi iyababuna Baba, ko su Yasmin da suke da alaƙa da shi kinga sun yi inda yake ne duk da so su sakedashi da ya dinga yi? Ni wallahi ma abinda tace ya mun daɗi, sannan dan Allah kar ma ki ƙara tadawannan maganan, bare Yaya Abdussamad ko yaran nan su ji" Habiba tace cike da rashinjindaɗi.... "To komai ai ya wuce, tunda tace tana da wanda take so" "shikenan, Allah ya ba ta shi, shi kumain ba shi ya ce miki ya shirya aure ba dan Allah Hajiya kar ki mai maganan, ki kauda kai kamanbama ki fahimci komai ba, ba yaro ba ne da shekarun shi, da Farisat tayi auren wuri da jikoki yakeƙirgawa ba ƴaƴa ba, in yace ya haƙura da aure har abada ba wani abu ba ne, tunda Alhamdulillahyayi auren nan na tsayin shekaru 23 ga yara Allah ya ba shi bila'adadin, me kuma yayi saura?Injikoki kike so? Gasu nan kina ta ganin wulƙawan su, surikai kuwa kina sa su har yanzu ba dainakawo miki a ka yi ba" Habiba ta kuma cewa cike da jin ba daɗi, "to shikenan Habi na yi shiru, Allahya zaɓa abinda yafi zama alheri, dama kawai na ga tana zaune ne ba wanda ya taɓa leƙowayaceyana sha'awan aurenta, ga shi har Farisat ƙanwar bayanta ana shirin tsaida biki, kinji abindayasa".... "To ai gashinan ta watsa miki ƙasa a ido, Allah ya kyauta, Allah na tuba ita yanda taken nanwai har za'a mata tayin auren kamar Yaya Abdussamad tace wai tana da wanda take so, to shimadanbaki nemi jin ta bakin shi ba ne, na san ba amincewa zeyi ba" Suwaiba tace cike da takaicinabinda Sa'adatu tace.... "To ya isa haka dan Allah ku huce, a bar maganan haka ya wuce" Balarabe dake zaune a gefeyace tare da sakin dariya, "wallahi Balarabe abun ne ma da takaici, ni se yanzu ma kalamannatake ƙonani" Habiba tace tare da sakin murmushi, "kalaman wa Anty Habiba?" Farisat tace taredacire takalmi dake ƙafanta, "oh har kun dawo ƴan albarka?" Tace tare da sakin musu murmushi, "ba mu je hospital ɗin ba dai" tace tare da sakin dariya.... Ɓata fuska tayi tare da faɗin "Farisat ban san dalilin da yasa bakya son ai gwajin nan ba" "wallahi yau ba daga ni ba ne Anty Habiba, tambayi Yasmin, munata jiran kira shiru har muka gaji mukadawo" tace tare da kwanciya a saman cinyoyinta, murmushi ta saki tare da cire mata ɗankwali tafara sosa mata kai a hankali, cike da tabbaci tace "wata ƙila uzuri ne ya riƙeshi, mu jiraye shi kaɗan" tayi maganan fuska cike da murmushi, "Anty Habiba yunwa" Yasmin tace tare da narkefuska, "to uwar shagwaɓa zaki fara ko?" Suwaiba tace tare da banka mata harara, dariya tasaki tare da faɗin "Anty Suwaiba dama kina parlorn nan?"... "Ina zaki ganni tunda kin makance" tace tare da kauda kai, dariya ta saki tare da isa kusa daitatazauna tare da faɗin "yunwa ne ya makantar da ni" "to tashi maza ki nemi abinci ki ci" tacetaredaɗagata tsaye, wuce wa tayi da sauri ta nufi kitchen... Zaran tissue tayi ta goge baki tare da faɗin "ya maganan gasanku ne?" Taje fa tambayanidontaakan Khalim, murmushi ya saki tare da faɗin "yana nan saura two weeks, ba kin ce ba zaki zokallo ba" "me zanyi a wajen ball, a'a dama dai wani abun da ban ne" tace tare da kai jiki ta kwantaa jikin kujeran, dariya ya saki tare da faɗin "Nachma wannan fa ba ta san daɗin da Allahyazubawa kallon ball ba" "na ga alama" tace tare da sakin murmushi, "a'a dai ku cigaba da garatamola" tace tare da ɗaukan cup ɗin ruwa ta kai baki, murmushi ya saki tare da kallon smartwatch ɗin hannun shi, zare ido yayi tare da faɗin "subhanallahi" yana kai nan ya ciroatmɗin shi ya ajiye a gabanta ya miƙe tare da faɗin "9559 shine pin ɗin" yana kai nan ya ɗaubottlewater ya fice da sauri, murmushi Nachma ta saki tare da faɗin "hala test?" "Training" tacetaredataɓe baki.... Dariya ta saki tare da faɗin "Allah ya shiryi Khalim, training ya kewa wannan rawar jikin" miƙewatayi ta saɓa jakanta tare da faɗin "muje" ba musu ta ɗau na ta jakan suka nufi wajen biyanbill, zaro atm ɗinta tayi a jaka ta ba su, suna cire kuɗin su ta haɗa da na shi da ya ajiye musu tamaidacikin jaka ta saɓa suka fice.... Suna shirin gitta ƙofan restaurant ɗin muryan Minakshi ya doki kunnuwan su, "to ɗiyoyinfaƙirai, dama bakwa da kuɗin cin abinci a wajen ku ka shigo? tunda kun ci arziƙi an biya muku se abamutunda ba gadon tsofaffi ba ne" tace idonta ƙyam a bayan su..... Cike da mamaki Nachma ta juyo ta watsa mata razanannun idanunta da suke ɗauke da zallanɓacin rai, buɗe baki tayi dan bata amsa Insu ta riƙo hannunta tare da faɗin, "tsofaffi ba subatatarbiyyan yin magana da mutane ta hanyar da yakamata ba, tunda ba ta kira sunan ki ba ai badake take ba, wuce muje" tana kai nan ta ja hannunta suka bar wajen, kallon Sunaina daketsayea gefenta tana cika tana batsewa Minakshi tayi tare da faɗin "yau se na ga uban da ya tsayamata" tana kai nan ta dafa musu baya janye da hannun Sunaina.... Kai tsaye library suka nufa, jan kujera tayi da nufin zama Minakshi da ta ƙariso a matuƙar fusaceta jawota da ƙarfi ta ɗaga hannu da nufin kai mata mari, wani banzan fizga Nachma ta matacikinzafin nama ta jefata gefe, "wash" tace da ƙarfi tare da riƙe ƙafa, zare ido Sunaina tayi taredafaɗin "ke dan ubanki kin san wa ki ka wa haka?" "Dan naki uban na tambayeki sani ne? Banadamatsala da sanin waye ubanta, ko dai mata zama ne? Dan wannan rashin hankalin da takeyi kaman ba lafiyayyen namiji ba ne ya haifeta" tayi maganan ko a jikinta tare da nufarta zuciyaamatuƙar ɓace, murmushi Insu ta saki tare da riƙota cike da rashin ba ma abinda ya so faruwamahimmanci tace "basar mana Nachma, ai da kin barta ta yi gigin saka hannunta a jikina dasunan duka da uban na ta da take buɗa kafaɗu dan shi yayi nadaman saka ta a wannan makarantar, ko da yake mata maza ne barshi da ƙaddarar shi" tana kai nan ta ja kujera ta zauna... "Wallahi se kun san kun mun haka, wallahi se wawayen iyayenku sunyi danashinan haihuwarku"Minakshi da ta ƙoƙarta ta miƙe tace tare da goge hawaye, tana kai nan ta kama hannunSunainadata miƙa mata suka wuce fuuu, "wawaye marasa hankali" Nachma tace cike da ɓacin rai, "lafiyakuwa!" tace tare da watsa ma students ɗin dake tsaitsaye suna bin su da ido harara, saurinzazzaunawa suka yi tare da maida hankali ga littafan gabansu, dariya Insu ta saki tare da girgizakai.... Suna shiga reception Salman yayi gun me rubuta suna, tarbansu yayi da mutuntawa taredatambayansu da abinda ze iya temaka musu, rasa me ma ze ce yayi, kallon Usman yayi taredasauke numfashi, "am akwai wata yarinya da ta shigo nan yanzu babu daɗewa ita muke sansaninabinda ya kawo ta" Usman yace tare da kafe shi da ido, girgiza kai yayi tare da faɗin "da farkobanma san akan wacce ku ke magana ba, sannan ko da na sani doka ce ba ma fitar da sirrincustomer's ɗin mu" fiddo waya da sauri a aljihu Salman yayi tare da nemo hoton Sa'adatudasauri ya nuna mai, girgiza kai yayi tare da faɗin "babu wani temako da zan iya muku".... Rai ɓace yace "bangane baka da wani temako da zaka iya mana ba, ƙanwar mu ce muke nema, maza ka ba mu bayani ko yanzu ka fahimci su waye a gabanka" ya idda maganan a kausashe, jada ba ya yayi da sauri cike da ɗan tsoro dan yanda ya ga fuskan shi ya sauya nan take, dafashi Usman yayi tare da faɗin "calm down please, bari in yi magana da shi" yayi maganan cikinmuryan rarrashi, ja baya yayi zuciya na tafarfasa, danna number Yaya yayi ya kara a kunni .. Zaro ID card ɗin shi Usman yayi ya nuna mai tare da faɗin "jami'in farin kaya, kamar yandayacemaka ƙanwar mu muka biyo, ba wani tashin hankali ya kawo mu ba, bamu bayani mu kamagaban mu, ba ma da lokacin ɓatawa" sauke numfashi yayi tare da faɗin "yallaɓai ba na da wannan daman, zan iya rasa aikina, se dai in kira muku manager" "okay kira shi" yace taredagyara tsayuwa ɗaukan telephone yayi ya danna number office ɗin manager jiki na ɓari.... "Mutumin ki ze bar school" Nachma tace tare da kallon Insu da ta ɗago kai ta kalleta, ganinirinkallon da take mata yasata faɗin "Hisham" a natse, "meyasa!" Tace cike da mamaki, "gradelevel ɗin shi ya yi ƙasa sosai" tace tare da kallon ta, "nawa?" Tace tare da maida idonta ga littafin gabanta, "1.47" tace a hankali, "what! To menene amfanin karatun da yayi na tsayin shekarakenan?" Tace cike da mamaki, ɗaga kafaɗa tayi ba tare da tace komai ba, "ai yana da wani daman, se ya faro daga farko" tace tare sa sauke numfashi... "In za su barshi ya wuceba wani shekaran ba" Nachma tace cike da takaici, "kaman Yaya?" Tacetare da kafeta da ido, tsaki taja tare da faɗin "wallahi yayi ƙoƙari, kafin a tafi holyday ankafemusu matakan makinsu kowa ya ga abinda ya samu, jiya kuma wai ya samu kira daga officeɗinstudents affair, wai anyi kuskure wajen ba shi marking da ba na shi ba, yayi haƙuri ga asalinmakin shi, tsakani da Allah da adalci a wannan? Sannan Labib yace mun me wannan markingSunaina Ahmad Yarban ce, ita kowa ya ga ni da shi, sannan yanzu ana maganan ta a secondclasslower shi kuma ko darajan third class be samu ba se pass degree" ta idda maganan cike datakaici, "to bayan jin hakan, wani mataki ya ɗauka?" Tace a natse.... "Wani mataki ze ɗauka kuwa? Ba fa daga office ɗin masu tsara jarabawa da fidda sakamakofayaji wannan batun ba, daga students affair yaji, inda in aka cuceshi yake da daman kai ƙara, meze yi banda ya rungumi ƙaddara, yace ya sanar da gida ma su zo su ɗaukeshi gobe, dan bazekoma farko ba, dan be san me kuma za'a mai a gaba ba, da makaranta ta kore shi, ya rasa madafagunda ya haƙura" taɓe baki tayi tare da faɗin "Allah ya kyauta" "amen" tace cike da takaici.... "Yace tun jiya yake son faɗa miki tafiyan shi, be samu fuska ba shiyasa kawai yayi shiru, ni maɗazu Labib ke faɗamun a studio, da muka je na tambaye shi kuma ya tabbatar mun" jinjinamatakai tayi ba tare da tace komai ba, kallon littafin gabanta take amma ta kasa gane me takesonkarantawa, banda tafarfasa ba abinda zuciyanta ke yi, so take ta manta da maganan ammazuciyanta ta ƙi amincewa hakan, rufe littafin tayi ta maida mazaunin shi ta kalli Nachma datayi nisa wajen nazari tare da faɗin "bari in leƙa wajen can" jinjina mata kai tayi ba tare da tacekomai ba.... Tana ficewa ta saki murmushi tare da faɗin "za ku ci ƙaniyanku gaba ɗayan ku" ta yi maganan hankali kwance tare da maida hankalinta ga littafin gabanta.... Miƙa ma manager da ya fito cikin suit hannu Usman yayi suka yi musabaha, "meke faruwa?" Yacetare da kallon shi, gyara tsayuwa yayi t8a kora mai bayanin komai, "akan wa kuke magana?" Yace a natse, "Salaman nuna mai hoton ta" Usman yace tare da kallon shi, buɗe wayanyayi yanuna mai, "oh wannan ce?" Yace tare da juyawa ya kalli me shigar da rahoto tare da faɗin"bayarinyar Sudais ba ce?" "Ita ce" yace baki na ɓari, shigowan da Yaya yayi ne ya dakatar da Salmandake shirin jefa mai tambaya.... Ba ma manager hannu yayi suka gaisa, cike da mutunta kai yace "tun yaushe ta fara zuwanan?" "Tab ɗin jam, shekarun da yawa, amma ze iya kai 5 zuwa sama" rumtse iso Yaya yayi zuciyanshi na bugu da ƙarfi, "please Yaya ka kwantar da hankalin ka, ban kira ka dan ka tada hankalinkaba"yana kai nan ya juya ga manager tare da faɗin "am zamu iya samun videon shigowanta yau?" "Badamuwa" yace tare da musu iso zuwa cikin office ɗin shi.... Kai tsaye Male hostel tayi, yawancin su ba sa nan, wasun su na wajen kallon ball wasunsunaclass da sauri da sauri ta shige, side ɗin new comer's ta shiga, fara bin jerin sunaye tayi daido, tana zuwa kan sunan shi ta gyara tsayuwa tare da ƙwanƙwasawa.... Buɗe ƙofan Labib dake ta ya shi haɗa kaya yayi tare da baza mata ido cike da mamaki, yasandukhaukan da abokin su ke yi na yana son ƙawance da ita ba ta taɓa ɗaga kai ta kalleshi ba, "bani waje in ka gama ƙare mun kallon" tace tare da mai alamun ya kauce da hannu, saurin batahanyayayi tare da mata maraba, shiga tayi baki ɗauke da sallama, ɗago kai daga zage zip ɗin akwatinshi yayi da sauri tare da faɗin "Insu?" Harara ta zabga mai tare da faɗin "tafiya babu sallamahakaake ƴan uwantaka?" Murmushi ya saki tare da saurin sadda kai saboda hawayen da suke shirin sakkowa, "oh Allah kai ka zama namiji mana, namiji fuskantar duk abinda ya tunkaro shi yakecike da mazantaka ba guduwa yake ba, da kake son tafiya gida wa zaka wa asara kenan?".... "Makaranta? Ita wacce aka ƙwace haƙƙin ka aka bata ko kai da aka ma ƙauce? ka ga ka amshi faɗuwa biyu kenan, gaskiya baka burgeni ba, da kake shirin tafiya, kasan wani abu da nayi tunanin amsan hannun ƴan uwantaka da ka ke ta miƙo mun, amma yanzu gaskiya se na ƙaranazari" ta idda maganan tare da baza mai ido, share hawayen dake gangaro mai yayi taredasakin mata murmushi.... "Duk cikin ƴan uwan Insu babu lusari, jarumai ne, marasa yarda da zalunci, babu rago a ƴanuwana, da jarumta aka haife mu, da shi muka tashi, a haka kake son zama ɗaya daga cikinsu, toka cire zuciya akan zaka zama, in dai za'a zalunceka ka koma gefe kana kuka mara sauti" tanakai nan ta juya, da sauri ya bita tare da shigewa gabanta ya duƙa tare da fashewa da kuka, "banadaƙarfin gwiwansu na sani, amma ba zan juri ƙin zama ɗaya daga cikin su ba, Insu Daddy na zeiyafushi dani in yaji na tanka, yana yawan ce mana duk wanda ya cuce mu ko ya zalunce mu, mubarshi da Allah, shi ze mana alƙalanci a gobe ƙiyama, bana da bakin magana duk da na santarwatsa burina da na iyayena nake shirin yi, da burin zama lawyer na tashi, shine muradina, sonake in zama tsayayyen lawyer kamar barrister Amina Sa'eed Umar Bertuwa, bana da wani buri se wannan, ya zanyi" ya idda magana cikin matsanancin kuka.... Tunda ya ambaci sunan Anty taji tsigan jikinta na tashi, nan da nan haƙwaranta suka somahaɗewa waje guda, maganan da ya cigaba ne ya dawo da ita cikin natsuwanta, "zan zaɓi shirukoda zan cutu fiye da haka" ya idda maganan cikin rishin kuka, wani takaici ne ya lulluɓetasotake kawai taga tana ball da shi a wajen, se dai yanda yake kuka ya sa ta kasa hakan.... "Da nawa ka fita?" Tace cikin danne ɓacin ranta, "3.49" second class lower?" Tace idonta akanshi, jinjina mata kai yayi tare da share hawaye, "Daddynka yace in wani ze tambayi dalilin da yasaakacuceka ka hana shi?" Ta jefa mai tambayan tare da ɗaure fuska idonta akan shi, girgiza matakai yayi tare da share hawaye, "muje su faɗa mana inda aka kwana a ragaya" tayi maganantaredaficewa, zare ido Labib yayi tare da sakin nagartaccen murmurshi, da sauri ya riƙo hannunshi suka fice, tana fita ta tadda Nachma tsaye tana sakin mata murmushi, harara ta zabga matatawuce, murmushi ta sakin ma Hisham da suka haɗa ido tare da faɗin "kana da ƴar uwa ta musamman, na san ba zata taɓa bari wani ya cuce ka ba" tayi maganan nagartaccen murmushi faɗaɗe a saman fuskanta, murmushi ya saki ba tare da yace komai ba.... "Tashi mana, bana son wannan lalacin da ki ka koyo" Sudais da ya fito daga toilet sanye cikinrigar wanka yace tare da banka ma Sa'adatu dake kwance sanɓal haihuwan uwa da uba a kangado harara, "no please" tace tare da narke fuska, "na ce miki akwai inda zani, kin kuma sani, sannan ke ma ki na da exams, ki tashi ki watsa ruwa in sauke ki a can tunda da sauran time, zasuiya miki alfarma" miƙewa tayi da sauri ta yi inda yake cike da son rikitashi ta haɗe bakinsu, hannayenta na kai saƙwannin a gan-gan jikin shi, se da ta tabbatar ta ba shi saƙon da ya amsadahannu biyu sannan ta zare bakinta a hankali tare da shafo fuskan shi cike da tabbatar mai daabinda za tace ta sumbaci laɓɓan shi tare da faɗin "kafi komai da kowa a waje na, buƙatankayafi na kowa" shafo fuskanta yayi tare da faɗin "yau kin tabbatar min da hakan, na kuma gamsudakaramcin da ki ka nuna mun, ban ɗauka zaki zo ba se ga ki" "na gummaci rasa komai a duniyadana rasa ka, ka riƙe wannan ba zan amshi nisanta da kai ba dai-dai da second guda" murmushi yasaki tare da ɗaukanta a hanzarce dan ta gama rikitashi, saƙalo wuyanahi ta yi da sauri taredasakin dariya ... Nan suka ƙara lulawa duniyar saɓon mahalicci, basu ankara ba se da 3 ta buga, shima dankiranwayan shi da aka yi ne, tsaki yaja tare da jawowa ya kara a kunni, "wai Sudais kana da hankali kuwa? Ce maka nayi fa kai nake jira" murya Gude ya karaɗe kunnin shi, tsaki ya kuma saki tareda jefar da wayan ya miƙe zaune ya sauke ƙafafun shi a ƙasa, jawo wandon shi dake yasheyayi yafara zurawa a ɗan hanzarce, dan yamanta da batun jiran da take mai sam.... Kai hannu tayi zata jawo shi da sauri ya buge hannun tare da faɗin "bana san jarabarki wandabeƙarewa, jirana ake" yayi maganan tare da saka riga, miƙewa tayi tare da faɗin "tafiya za kayi kabarni anan?" "Zaman jiranki zanyi ne ko me ki ke nufi?" yayi maganan tare da ɗaukan wayanshi da carkey ya fice da sauri, tsaki taja tare da faɗin "daɗina da kai wani zubin murɗaɗe ne" tayi maganan tare da jawo wayanta ta danna number ta kara a kunni, a na ɗagawa tace "ina jirankaaSD hotel room 106" tana kai nan ta katse kiran ta sauka ta nufi toilet... Comments fans🥰🙏 🫀MUGUWAR TSOKA 🫀 {🫀TA'ARE KALLUƊE} [Muscle Cramp🫀] ) عضلة سيئة ( 🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_ https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 written and Created ~~~~~~~~~~~~~~ ِبسم الله الرحمن الرحيم By Yardajjiya👩 💻 Page. Twenty two Tsatstsaye suke a bakin

Chapter 28 of 109