Share this page
Namadi ya bayyana ras akunninshi, murmushi ya saki tare da faɗin "bana da wani kalma na godiya gare ka yallaɓai, akankabaabinda ba zan iya ba" "na sani doctor, zan ajiye wayan Sulaiman ze kira ka" "to yallaɓai" yacetareda zare wayan fuska cike da murmushi ya maida ya ma ma motan key fuska cike da murmushi yaja tare da kallon wanda ke mazaunin me zaman banza dake cewa "menene na gaba?" .... Tunda suka shiga anguwar labari ya karaɗe jama'ar anguwan, nan da nan suka bazamo ƙwansuda ƙwarƙwata, ba yara ba, ba manya ba, haka suka cika gidan tamƙam, ma su faɗan alheri nayi masu faɗan sharri na yi, ba wanda yayi yunƙurin hana su faɗin albarkacin bakunan su, seahidindimun gabansu da suke dan ba wacce a tsakanin Sadiya da Iƙilima da Harari ta zaunadanataya ta jimami.... "An kammala shiryata, Kabiru kira su Salisu mu sallaceta mu miƙa ta, an fara kiraye-kirayensallah" Baba yace murya a sanyaye dan ba ƙaramin dukan shi mutuwan yayi ba tare da kallonKabir da ya nuna kaman be ji abinda yake cewa ba, "Kabiru da kai nake!" Yace cike da mamaki, "kuje ku sallaceta Baba ba zan iya sallahtan gawan Sa'adatu ba" yace cike da gaskiyan shi, "ashsha, kayya Kabir, kayya, ya ka ke abu kaman mara imani da tawakkali, yarinyar nannatayaƙare, wannan shine gatan da zamu mata matsayinta ta jinin mu" Baba yace cike da damuwa, girgiza kai yayi tare da faɗin "Baba ba ka san abinda yarinyar nan tayi ba, kabar kaza cikingashinta kawai hakan zefi, ta mutu tone-tone ba amfani, in na ce zan buɗe baki ba lallai waƴanda suka zo da niyyan sallatan ta su sallaceta ba, kuje Baba lokaci na ƙurewa, ba zaniya sallahtan ta ba shine gaskiyan maganan" ya idda maganan cike da tabbacin abinda ya faɗa.... "Amma Kabir" "Baba dan Allah ku je" yace cikin katse mai hanzari tare da nuna mai hanyadahannu alamun gan yake da kawowa wuya, murmushi Sarari dake gefe da zugan shi ya saki tareda faɗin "barshi Baba, muje kar dare yayi" jinjina mai kai yayi suka wuce jiki a sanyaye, beiyaɗaga ido ya kallesu ba dan banda danne zuciya a tsaye a wajen ba abinda yake.... "Muje mu sallaceta" Kamil da suke tsaye a gefe suna kallon abinda ke faruwa yace tare dakallonSalman da Sadam, jinjina mai kai suka yi suka wuce, ɗaga ƙafa yayi da zumman binsu, ringingɗinwayan shi ya taka mai burki, maida ƙafan yayi daga inda ya ɗaga ya zaro wayan a natse.... Ganin me kira ya sa shi ɗagawa a hanzarce tare da tattara natsuwan shi ya ɗaga mai sallama, amsawa SSB yayi a natse tare da faɗin "kana can gidan ne?" "A'a muna gidan su Iƙilima" yaceanatse, "a wannan time ɗin!" Yace cike da mamaki, jinjina kai yayi kaman yana gabanshi taredarattafo mai abinda ya faru, "what!" Yace da ƙarfi murya cike da tashin hankali, "wallahi, abundai ba daɗi ko kaɗan" yace jiki a sanyaye, "yakamata ku koma gida" yace a dake, "eh yanzu inshaAllah, jira muke a sallaceta a kaita se mu koma" "okay in abin ze ɗau lokaci ku koma gida basekun jira ba" yace a dake cikin ba da umurni tare da katse kiran, zaro wayan yayi fuska cikedamurmushi ya maida a aljihu ya nufi inda aka kabbarta sallah.... Suna sallamewa aka cicciɓeta aka saka ta a motan Salman, kamo hannu Kabir Baba yayi fuskabawasa ya saka shi a cikin motan ba tare da ya bashi daman wani ƙorafin ba ya rufe ya wuce, badinranshi ya so ba suka ɗau hanya, suna isa aka cirota aka nufi ƙabarin da su Aminullah da sauran matasan anguwan suka haƙa, ana sakata ya juya ya nufin inda ƙabarin Baba yake, duƙawayayi baki ɗauke da addu'o'i ya fara tone gefen ƙabarin, ganin yayi nisa a wannan gefen be cimmaabinda yake so ba, ya sashi maida ƙasan ya koma ɗayan gefen cike da fata ya fara tonowa, bekai ga nisa ba ya ci karo da ƙaramin key, saurin ɗauka yayi zuciya cike da farin ciki, ya maida ƙasanya miƙe, yana juyawa ya tadda Sarari tsaye akan shi fuska yalwace da murmushi, guntunmurmushi ya sakin mai ya raɓeshi ya wuce.... Suna komawa suka tadda an gana rufeta ana duƙe ana roƙa mata rahman mahaliccinta, ɗagahannu Sarari yayi yayinda Kabir ya ja gefe, suna kammala suka shafa kowa ya fara nemanhanya, yana tsaye a wajen duk mutanen da sukai rakiyan suka fice, a natse ya taka ya isa gabanƙabarin, bin ƙabarin kawai yake da ido, lumshe ido yayi zafafan hawayen da suka cika idon suka gangaro, ɗaga hannunshi da ke riƙe da makullin yayi tare da faɗin "gashi a hannu na Sa'adatu, shikenankin gama fafutukan kin tafi ba tare da kin moraba, ba komai ha jawo miki hakan ba, se ƙwaɗayi da buri, amma kar ki damu nayi miki alƙawarin duk wani me MUGUWAR TSOKA irin taki seyabiyo bayanki, se mun kauda mugun iri a ƙasar mu, se mun tsarkaketa da ga irin ku, yau gaki ainda ki ka tura Baba da barrister Amina, ki girbi abinda ki ka shuka Sa'adatu, ba zan miki fatanRahma ba, dan baki cancanceta ba, ba zan iya miki ba" yana idda maganan ya juya da sauri yanagoge ruwan hawayen dake shatata a saman fuskanshi, kamo hannun shi Sarari dake tsayeyanajiran fitowan shi yayi tare da faɗin "komai ya wuce", jinjina mai kai yayi cike da samun sassauci.... Kallon Insu dake zaune saman dadduma Sadiya tayi tare da faɗin "dare fa na tsayi, yakamatakuzo ku wuce" tana rufe baki sallaman Sadam ya shiga kunnuwan su, "to ga su nan sun dawoma, ku muyi hoɓɓasa" Rahma tace tare da yunƙurawa, mimmiƙewa suka yi jikkuna a mace sukasallame su suka fice tare da rakiyan su Iƙilima da ta kasa kallon fuskan ɗaya daga cikin su.... Ƙara sallaman juna suka yi suka shige Salman da Sadamsuka ja suka bar wajen, goge hawayeIƙilima tayi ta juya dan komawa ciki, yafuto Aminullah Sadiya tayi tare da ja gefe ta tsaya, waige-waige Harira ta fara cike da tsoro, da sauri ya isa inda take tare da faɗin "menene?" Saurinriƙo hannun shi tayi ta matsa gefe can, "wai lafiya!" Yace da mamaki idan shi akan ta, "kasanmaƙabartan da aka binne Baba?" Cike da mamaki ya baza mata ido.... "Bar kallona haka ban amsa" tace a dake, jinjina mata kai yayi tare da faɗin "na anguwar yammaci ne, can aka kai Sa'adatu ma" jinjina mai kai tayi tare da faɗin "dan Allah muje kakai mu" zare ido yayi tare da faɗin "yanzu wai!" "Eh" tace idanta akan shi, "ko tsoro ka ke ji?" Tacedamamaki, girgiza kai yayi tare da faɗin "kiran isha'i ake ƙoƙarin yi fa" "yanzu zamu mu dawodallah" tace tare da juyawa ta inda Harira ke tsayiwan jiran su kammala ta yafutota, da sauti tayi inda suke .... "Muje Harira kar a hankalta bama nan" tace tare da riƙo hannunta da sauri, juyawa suka yi dasaurin dan barin wajen, saurin ja baya suka yi ganin Kabir tsaye yana bin su da ido, juyowaAminullah yayi ya kallesu cike da tambayan ya zamu yi? Da ido, saurin gyara murya Sadiyatayi saboda ganin Harira dake in,ina na shirin kwafsawa tare da faɗin "zamu ɗakko kaya a gidanBabane" jinjina mata kai yayi ya zura hannu a aljihu, wuce wa Aminullah yayi yayinda suka dafamai baya, suna zuwa dab da shi ya riƙo hannun Sadiya ya saka mata keyn da ya ciro tare da wucewagida da sauri..... Fiddo ido waje tayi tare da bin keyn da ido cike da mamakin, "Harira!" Tace cike da farinciki, saurin rufe hannun da ta ware tana kallon key ɗin Harira tayi tare da bin wajen da ido, "Harira!" Ta kuma cewa cike da ɗin bin farin ciki, "shiii! Tace a tsorace ido a waje tare da sa mata yatsaabaki cike da zargi, shiru tayi tana bin ta da ido, "muje! Muje gida" tace tare da jan hannuntasukajuya, "oh Allah an fasa ne?" Aminullah yace cike da gajiya, "eh jeka masallaci" Sadiya tacedaƙarfi tare da shigewa gida, suna shiga suka tadda Kabir ya tarwatsa taro yace ba me musuzamanmakoki a gida, ko a jikinsu suka wuce ɗaki dan suma ba buƙatan zaman suke ba.... "Oh yanzu dama Sa'adatu na da hannu a mutuwar Amina!" Babiya tace cike da tsan-tsanmamaki me haɗe da tsoro ds firgici, sauke numfashi suka yi idanunsu akanta, "wai dama ba'a yi bincikebane!" Samir yace da mamaki idan shi na yawo akan su, "waze kawo mutuwar ba na AllahdaAnnabi ba ne Samir! Naƙuda ne ya taso mata, ta mutu kafin ta haife abinda ke cikinta, shi akasanar damu, kuma muka yarda" Babiya ta kuma cewa mamaki be bar saman fuskanta ba.... "Lallai yarinyar nan ta cika butulu" Suwaiba tace cike da mamaki, "ke dai Suwaiba bar mutumindake biyewa MUGUWAR TSOKA, Allah ya shiryar da na ƙirazanmu, wannan shi ake kira dakazoabanza ka koma a wofi" jummai tace cike da takaicin da yakamata, "Allah ya kyauta, Allahyakyautata na mu makoman, muna fatan Amina ta dace" Yaya yace cike da dukan da labarindasuka kawo ya mai ya miƙe, "Kamil muje ka watsa ruwa" ba musu ya mike suka wuce side ɗinshi.... "To wai wa ya faɗa muku ma!" Gude tace tare da gyara zama, "da bakinta Anty Gude" Rahmatacetare da gyara nata zama, "da bakinta!" Suka ce bakuna a haɗe, "ai Allah ne ya matse bakinƴar banzan se ga jawabi" tace cike da takaici, "Allah ya mata abinda ta mana, dama ance "dukabindaka wa ɗan wani ba gani ze ba" kalli ƙaunan da ta nuna mata, daga ƙarshe ita ta kasheta sabodamugun nufinta" Munari tace tana tuna abubuwan da suka faru, "dan Allah mu kamo wani topicɗin mun gaji da wannan" Insu tace cike da gajiya da jin batu ɗaya.... Murmushi Ummi ta saki tare da miƙewa cikin sanyin da jikinta yayi tare da sallaman su tanufi ƙofa, da sauri Insu ta tashi ta bi ta, "to! To! to, za'a shigar da Ummi" Sadamyace tare da sakindariya, dariya su Rahma suka saki tare da miƙewa suka sallame su suka bi bayan su, ɗaukanwayanta dake ringing a gefenta Yasmin tayi ta kara a kunni saboda ganin me kiran.... Shiru tayi alamun tana sauraran me magana kafin tace bari Yaya Sadam ya shigo da ku" tanakai nan ta sauke wayan, "suwaye?" Yace idan shi akan ta, "Habbubi ne da su Yaya Annur" "okay" yacetare da miƙewa ya fice, "Yaya Samir ka watsa ruwan ko?" Farisat tace da kulawa, jinjina matakai yayi fuska a ɗaure, "oh Yaya Samir ta fa rigada ta mutu, da tana da rai ne shine za mu ce sehukunci yayi aiki akanta, se mun wanzar da adalci wa Anty ko zamu rasa rayukanmu wajennemakuwa, amma ta mutu Yaya Samir, ta je inda Antyn ta tafi, za kuma su tsaya a gaban ubangijinsuya musu hisabi" ta idda maganan cike da rarrashi, jinjina mata kai yayi alamun ya gamsu.... "Yawwa ko kaifa, Anty Gude ina su Maryam?" "Fitan ku ba daɗewa suka tafi, nace ma suNafi subi su, Sudais ne kaɗai a gidan" tayi maganan fuska cike da murmushi, "hakan yakamata za sutemaka mai sosai, su Antyn Maryam ne dai kaman be kamata su tafi ba" tayi maganan cikedamamakin tafiyan da aka ce sunyi, "eh mazajensu ne suka zo ɗaukan su, sun gaisa ma da Samir ma" tace da alamun ba ta so a ja maganan, "to ai shikenan, amma shekara nawa ba'a haɗuba, kwana ɗaya ma ya gagaresu" tace cike da takaicin su, "bakya wajen nan Farisat, amma sedaAnty Jummai ta faɗi haka a gabansu sukai finfirin fir" Suwaiba tace cike da takaici.... "Ai shikenan amma ku dai kuna nan ko?" Ta jefa tambayan idanta akan saura, jinjina kai sukayi fuskoki cike da murmushi, "yawwa ƴan gari" tace na ta fuskan cike da murmushi, "Yaya Sudaisbedawo ba ne?" Yasmin tace da kulawa, "oh Yasmin tsufan ne ya fara aiki? Yanzu fa aka gamamaganan yana gida" Farisat tace tare da kama baki, murmushi Gude ta saki tare da faɗin"ehYasmin, ina ganin se gobe, kin san sun ce kar ya dinga motsa mikin nan sosai" "haka ne, Allahyakai mu" tace a natse, "Anty Habiba ina sauran yaranki? Ɗaya kawai na gani?" Samir yace taredagyara zama, murmushi Habiba ta saki tare da faɗin "Shafa'atu ta wakilce su" murmushi Farisat tasaki tare da fadin "Sha'awanatu tayi nauyi, ni ban zata ma zata kai har yanzu ba ta kira muDimauba, Zuwaira kuma bata raye" "subhanallah! Ta rasu!" Yace cike da tsoro, "wallahi, ta kusa hadashekaru biyar yanzu" "gaskiya ta kusa" Munari tace tare da kallon ta.... "Wannan yarinyar da take dama-dama da Anty Habiba!" Yace cike da mamaki, "ita fa" Suwaibatace cike da tuna lokacin, "Allah sarki, Allah ya gafarta mata" yace cike da alhini, "AminyaAllah"suka ce cike da jin daɗi, turo ƙofan parlorn Sadam yayi baki ɗauke da sallama tare da ma suShureim dake bayan shi iso..... "To kinji dai Ummi, gaisuwa da roƙon iri ya kawo mu" Insu dake zaune kusa da Ummi taceriƙedahannunta, nagartaccen murmushi Ummi ta saki fuska cike da farin ciki tace "Allah ya zaɓaabinda yafi zama alheri Insu, ai muna farin ciki da wannan gaisuwa, bari zan ma Daddynsumagana yanzu in sha Allah, na san sun gaida ma a masallaci, amma zan ƙara mai bayani" "yawwaUmmi na, shiyasa nake masifar yinki, anjima zamu shigo in ya kimtsa" "Allah ya kawo ku" tacecike da jin daɗi, miƙewa tayi fuska faɗaɗe da murmushi tare da faɗin "ku tattara ku koma gidanbauta, kar in dawo in tadda ɗayan ku, dan mun riga da mun se da ku" tayi maganan tare dakamefuska idanta ba bin Rahma da Safinat da kallon gargaɗi, "to ai ba damuwa tunda kafin ki sedamuke muka fara se dawa" Rahma tace tare da banka mata harara, dariya ta saki tare da faɗin"ba'acin ba shinki a zauna lafiya Anty Rahamcy" "to ke kinga barin ba shi na da amfani ne?" "sosai kuwa acan ze amfaneki" "a'a a biyani haƙƙina anan kawai malama" tace tana fuska cike damurmushi.... Juyawa Insu tayi ra nufi ƙofan fita tare da faɗin "wallahi kar mu zo mu tadda ɗayanku danmakuji, Ummi se mun zo" ta idda maganan tare da ficewa, "sha kuruminki ana hanyan zuwa ɗaukanmu" Safinat tace tare da sakin murmushi, murmushi Ummi ta saki tare da faɗin "Insu kenan, yanayinta ɗabi'unta, kamanninta sak irin na Amina, ba abinda ta bari nata" murmushi sukasaki cike da fahimtar hakan da suka yi..... "Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un!" Yasmin Ɓadamayya tace cike da firgici idanta akan Alhaji Jamil da ya gama koro musu bayanin da Kamil ya kora mai, "lallai ta yi musu yankan baya, shiyasa wallahi bana ganin lefin mutanen da suke gujewa temako a wannan lokaci, ka fiddamutun a rana ne ka kawo shi inuwa shi ya hankaɗaka cikin ranan nan, bayan yasan ƙunandake cikinta" Yasmin Ɓadamayya tace tare da goge hawayen, tausayin su Insu.... "Haƙuri shi ne kaɗai abin yi, gashi ta gama shuka abinda zata shukan ta tafi, ba shikenanbatajeinda ta tura mana ita, gwanda ita muna fatan dacewa gareta, ita ko fa! Ba wanda ze ce gatatamakoman, ba kiji abinda Jamil yace ba har mahaifinsu ita ce silar barin shi duniya, kinga ai sedai muce Allah ya tsare zuri'armu daga shigowan irin su, na tabbatar Insiyyat zuciya guda ta jawotagareta dalilin da yasa ba ta yi nasara akan cutar da yaranta ba kenan, a hakan ma godiya zamuwa mahaliccin mu" Hajiya tace cike da jinjina butulci irin na Sa'adatu, miƙewa SSB dake zauneagefe yayi rungume da Mairah da ta gama ƙananun kukan kiran Amminta tayi barci yayi taredasallaman su ya wuce up stairs, bin shi da ido suka yi har ya ɓacewa ganinsu.... Sauke numfashi me sauti Jamil yayi tare da faɗin "kaman yanda ki ka ce ne Hajiya, se dai mucigaba da ma Insiyyat addu'a kawai, ko mun ce zamu tada maganan ba amfani, dan waccezamuyi shari'ar da ita ba ta raye, kunga ba amfani kenan" "ai shine gaskiyan Jamil" Hajiya tace idantaakan shi, "ita ma ɗiyar taki se kiranta nake tun ɗazu ba ta ɗaga ba" yace tare da ƙara dannanumber Iƙilima, haka yayi ringing har ya katse ba ta ɗaga ba, "ka mata uzuri ƴar uwarta cetamutu, duk lalacewarta na ta ne , ba zata ƙita ba" jinjina mata kai yayi tare da faɗin "ina gazuwaranar uku se muje mu musu ta'aziyya ko?" "hakan yayi Allah ya nuna mana, Yasmin kin yi magana da ƴarki kuwa?" "Eh tun ɗazu dai kafin faruwan abun ne ina ganin" "to kar ki takuramata da kira a wannan lokacin" "to" tace cike da gamsuwa, kallon su Fadila da jikinsu ke asanyaye Hajiya tayi tare da faɗin "ku ba mu waje" ba musu suka miƙe har sun juya tace "inaNafisat kuwa ban ƙara jiyo motsinta ba?" "Tana ɗakinta ita da Anisa tana mata assignment" Nabila tace cike da taka tsan-tsan, jinjina mata kai tayi alamun ta ji suka juya suka bar wajen.... Gyara zama tayi tare da faɗin "ɗazu Yasmin ta same ni da magana, shine nace in ka zo na sanar maka" "to ina ji" yace tare da bata dukkanin natsuwan shi, "game da maneminta Barrista ƊanAsabe ne" "to Hajiya Allah yasa lafiya" yace idan shi akanta, "a'a lafiya ƙalau, ya tuntuɓetaakanbatun tsaida lokacin da yakamata su kawo ƙarshen komai ne, tunda ka ga ba yara ba ne baresu tsaya jani in jaka" "hakane" yace cike da farin ciki, "to tace dai tace mai nan da sati biyu, yace"sati biyu yayi yawa ina lefin sati" daga ɗaurawa har tarewa, daƙyar dai suka dawo kan kwanaki goma, shima badan ranshi ya so ba, to kaji dai matsayar su" ta idda maganan cike da dattakonta... Gyara zama yayi cike da farin cikin da labarin ya haddaa mai tare da faɗin "yayi sosai Hajiya, insatin ne ma ai ba wani abun damuwa ba ne, da gaskiyanshi ba abinda za'a jira" "to yanda kacebaka wajen haka nace mata, da satin da kwana goma duk ɗaya ne ai" "wannan haka yake, tundasun tsayar haka kuma sun samu gamsuwa shikenan, yanzu se ki lissafa abinda ki ke buƙataki total ɗin kuɗin ki turo min, an faɗawa SSB ko?" "A'a na dai ce bari in fara maganan da kai tukun" jinjina kai yayi cike da yaba dattakon mahaifiyar na su tare da faɗin "to zanyi maganan dashi zuwa gobe" "Allah ya amince maka" tace tare da miƙewa, "har zaki shiga ne?" "Eh in sha Allah, naji idanun sun fara nauyi" "to a tashi lafiya" "Allah ya amince ka gaidamin yaran" "za su ji inshaAllah" yace fuska cike da murmushi, godiya Yasmin ta mai cike da jin daɗin kalaman shi tamiƙeta bi bayan Hajiya.... "To mr Chairman ga Yaya Samir, Yaya Samir ga Mejor Muhammad Shureimmijin baby" Farisat tace fuska cike da murmushi tare da nuna kowannen su sa hannu, murmushi Shureimya saki cike da jin nauyi, ƙaramar dariya Samir ya saki tare da faɗin "na gane shi tun shigowan su" "tokaji dai mr Chairman" tace cike da yanayinta, "Allah ya shiryeki personal assistant" Annur yacetareda sakin murmushi, "a'a assistant Chairman so fa nake su fahimci juna, dan akwai shaƙuwanamusamman tsakanin su da juna wanda ba su kai ga sani ba".... "Oh Allah dan Allah Farisat ki mana shiru" Balarabe yace tare da isowa wajen ya zauna kusadaZubair, turo ƙofan parlorn Insu tayi tare da faɗin "Uncle Shureim wallahi ina binka ba shi" murmushi ya saki tare da bin ta da ido, "tunda aka hanani magana a can ai nan ba me hanani" tace tare da zama kusa da Yasmin, "mun manta fa muce muku ta zo" Farisat tace tare da kallonsu, murmushi Khalid ya saki tare da faɗin "mu haɗu a waje, da ita zata shigo damu se aka cebrother Sadam ze mana iso" "auh ashe kun haɗu ma" tace tare da sakin murmushi, "Malamaƴar jarida jira in kora musu jawabi tukun" "to kora" tace tare da bin ta da ido.... "Wai wannan yarinyar da ta dakatar dani daga nace ina da ƙorafi waye ita?" Ta jefa mai tambayacike da tuhuma, kallon sakanni ya mata kafin ya kauda ido akanta ya maida kan Yasmintaredamata tambaya wace da ido, sadda kai tayi ba tare da tace komai ba, "wacce!" Yace cike damamaki tare da maida dubanshi gareta, "wannan (daddy's girl) ɗin take ko wa" tace cike datunaabinda ta mata, "bangane ta ba" yace cike da gaskiyan shi, murmushi Annur ya saki tare dafaɗin"yarinyar nan da Chairlady ta sako watannin baya" "oh na gane ta, me ya haɗa ku!" Yace cikedamamaki.... "Auh ba ma ka lura ba! Daga nayi tagging ɗin sunanka na ce ina da ƙorafi, shikenan yarinyatafara zuba, wai dan Allah mu dinga sanin maganan da zamu faɗawa na gaba, sannan mu sani bazaune ka ke kara zube babu abinda ka ke ba" tace cike da mamaki, murmushi ya saki taredafaɗin "ban san da maganar ba" "to Allah yasa hakan" tace tare da kauda kai, murmushi yasaki tare da faɗin "ke fa neman maganaki yawa ne da shi, yaushe garin yawaye, bare ki fara tunaninwata daren" "ai a zalamanku na maza wannan ɗin ba komai ba ne, ku kan iya jawo shi ma daƙarfi" "Allah ya shirye ki Insu" yace tare da gyara zama, "a'a ko ni fa na lura da yarinyar nashishshigewa duk wani abu da ya shafeka a group take" Farisat tace cike da gaskiyanta, "wallahi kuma ban ma taɓa lura ba" yace cike da na shi gaskiyan, "kana nufin bakwa magana a private!" Insu tace tare da kafe shi da ido.... "Ba wata mace a gidan nan da nake magana da ita ta private se ku ƴan uwana, bayan kubawata""to yanzu na ji dai-dai, dole in taka mata burki ta sake katsalandan kuwa" dariya Annur yasaki tare da faɗin "ashe masu jiran tan da yawa, dan Minha ita ma jira take, ban san meyasa batatsani ganin motsin yarinyar a group sam" ya idda maganan tare da sakin murmushi, "ai abunbadaɗi, ba kayi magana da mutum ba yayi caraf ya safke, ranar kaman zan bata amsa na dai ƙyaleta, wai ya suke kuwa! Ko ta waya yanzu sunyi ɗif" Insu tace tare da gyara zama... "Suna lafiya, ke ce ba san zumunci ne dake ba, nayi mamaki ma har da ki ka san yarinyar nagidan" "ai ta shigo gonata ne Yaya Annur, wallahi busy nayi, karatu yayi zafi, ba ma da wani hutu""ai ku se da uzuri" Zubair yace tare da sakin murmushi, "wallahi Yaya Zubair sun sako mugaba, dama ranar fa magana zan mai akan Mahmah Ɓadamayya na son a saka ta a tafiyan, ga Nachmada Labib ma duk suna so, shine fa kan in kai ga magana ta taka mun burki" "to ke banda abinki ai kina da daman sakawa ba an baki admin ba" Sagir yace tare da kallon ta.... "Admin! Wai ni ɗin! Yaushe!" Tace cike da mamaki, "wai kina nufin baki san an baki ba!" Sukacebakuna a haɗe cike da mamaki, "wallahi ban lura ba" tace cike da gaskiyanta, "bana faɗa mukuba" Shureim yace tare da kallon su, "lallai Insu bakya tare damu, be ma kamata a baki adminba" Zubair yace da mamaki, "a'a wallahi ina tare daku, lura ne banyi ba" "duk sanarwan da akayi dagabatarwan da aka yi, da fatan alherin da member's da admin's suka miki duk baki gani ba, sannan ki ce kina tare damu!" Yace cike da mamaki, "wayyo Allah bari in duba" tace tare daɗaukan wayanta dake jikanta.... "Yanzu godiyan da Hisham ya turo da amsa fatan alherin da aka miki duk baki san da suba!" Annur yace tare da kama haɓa, "wayyo Allah boyfriend, na san zaka iya, ai tunda yayi kamanni nayi" "Allah ya shiryeki, kar ki ce mun sanarwar taron da za'ayi shima baki gani ba!" Khalidyaceidanshi akanta, "dan Allah ku daina mun wannan kallon zan duba wallahi ban da lokacinchart yanzu sam" "ko da ma ba shine dake ba" Sadam yace tare da banka mata harara.... "Kije ki duba, zamu yi general meeting ne, sannan za'a karrama mutane bakwai za'a bawamutane 8 admin's" "Allah ya kai mu yaushe ne?" Tace cike da farin ciki, "se nan da wata huɗu fa, anadai sanarwa ne dan kowa ya kasance a ankare, kar lokaci yazo muji wani zance na daban" dariyatasaki tare da faɗin "shakuruminka me girma accounter zuwa dole" "to ko ke fa" yace tare dasakindariya, "suwa za'a bawa admin's ɗin?" "Mutane da yawa fa" Annur yace tare da sakin murmushi, "a bani satan amsa mana" tace nata fuska cike da murmushi.... "Matan mr Chairman" "wannan na san a zaune yake" tace tare da sakin murmushi, harara Shureim ya zabga mata tare da kallonYasmin da kamar ba ta wajen, "se brother Salman da Sadam da Yaya Balarabe, se Minha sebroHisham, sauran baki san su ba"

Chapter 101 of 109