Share this page
sunaye" Salman yace tare da kallon ta, "ai mun gama, brother Sagir se ka ji result, Malama ƴar jarida se kin ji ni a waya, please ku kula da kawunanku, kar ku bari wani abu ya same ku" ta idda maganan tare da sakin murmushi, murmushi sukasaki idanunsu akanta.... "Antyn Iƙilima!" Sahabee yace cike da mamaki, murmushi Iƙiliman da ta iso wajen ita da Kabir daMama ta sakin mai tare da sadda kai ƙasa, "Anty Iƙilima ba dai komawa yau ba!" Farisat tacedamamaki tare da isa inda take, "to zaman me za tayi anan ɗin Farisat? Me faruwa ta faru, zamantako tafiyanta ba ze sa Sa'adatu ta dawo ko taƙi dawowa ba, ta tafi na ta labarin anan ya kawoƙarshen" "amma Mama zata buƙaci zama da ƴan uwanta" Insu tace tare da kallon su.... "A'a Insiyyah komawanta ɗakinta shine yafi komai da ku ke tunani, ita damuwanta guda tayandazaku cigaba da kallonta bayan duk abubuwan da ya faru" fashewa da kuka Iƙilima tayi taredaduƙewa cikin rawar murya tace "ku yafe mana, ba ma da masaniya akan abinda Sa'adatutaaikata, da mun sani ko mun riski labarin kafin ku ba zamu tsaya ɓata lokaci wajen yanke matatsatstsauran hukunci ba" ta idda maganan tare da haɗa hannaye waje guda, "oh Allah AntyIƙilima me ya haɗaki da jingina jikin ki kan aikin da wata ta aikata! Ke fa ke ce Anty Iƙilimanmu, me dattako da sanin yakamata, ba ki mana komai ba, in kin yi ma mun yafe, so please a rufewannan babin anan, ke ma ki rufe shi anan ki binne shi" Insu tace tare da miƙar da ita ta farashare mata hawaye..... "Oh Anty Iƙilima se kace ba wayis ba! Menene abin damuwa a wannan maganan! Ko dalilinneyasa ki ka ƙi picking call ɗin uncle Jamil!" Ta idda tambayan cike da mamaki, "wallahi shineFarisat, ba kiran da bawan Allahn nan be yi ba jiya amma taƙi ɗagawa, nayi ban bakin na yi rarrashi amma ba abinda take faɗi se "me zance mai! Bana da bakin magana da shi" ke dagaƙarshe ma kashe wayan tayi tunda yaƙi haƙura da kiran" "lallai zamu ɓata Anty Iƙilima, muwannan abinda ki ka yi shi ze sa mu yi fushi, dan kina shirin sama uncle Jamil damuwa, wallahi jiya haka ya kirani "wai muna kusa da ita ne?" Na ce mai a'a mun dawo gida, se kin ji muryanshi cike da damuwa" Farisat tace cike da damuwa.... "To rashin hankalin fa, ga ta dai a haka kamar me hankali da wayau, amma kwankoce" Mamatace cike da takaici, "ayi haƙuri Mama ba zata kuma ba" Yasmin tace fuska cike da murmushi, "Allah yasa" tace cike da jin daɗin yanda ba su ga wani canji ba, "to yanzu ya za'ayi yankanwani ticket ɗin za'ayi?" Kabir yace tare da kallon Insu.... Murmushi ta saki tare da girgiza kai, dama ba mu soke ba, mun barshi a in an kira ba ta zobamutashi kawai" "to shikenan Allah ya sauke ku lafiya" yace cike da farin ciki "amin" tace taredaɗaga kai, ganin wanda take nema ita yake jira ya sata faɗin "uncle Kamil muje" jinjina matakai yayi tare da miƙa ma Sadam dake tsaye kusa da shi hannu.... "Wai yanzu se ku iya tafiya ba tare da munyi sallama ba!" Sadiya da suka iso wajen tace cikinsakin numfarfashi da alamu dai sun sha gudu, zare ido Yasmin tayi tare da faɗin "ba dai guduba!""Shi" Harari tace cikin sakin na ta numfarfashi, "ai waƴan nan ba sa da girma se na jikkunansu" Kabir yace tare da banka musu harara, "a gaishe ku" Farisat tace tare da bin su da ido cikedamamaki, "amshi nan" Sadiya tace tare da miƙa ma Insu akwatin dake hannunta, cike da zallanmamaki ta bi ta da ido... "Ita ce ta ba mu labari akan abubuwan dake ciki kafin ta mutu, tace yana da amfani ga mr president ze temaka mai" da ido Insu ta bita tunda ta fara maganan har ta dasa aya, ganinirinkallon da take mata ya sata faɗin "na san ba zaki buƙaci wani temako daga gareta ba, ki ɗaukadaga mune kar ki ƙi amsa dan Allah, ba ma da wani abu da zamu saka ko mu biya ku hidamkua gare mu" murmushi Insu ta saki ganin yanda idanta ya tara ruwan hawaye tare da faɗin"buɗe" ba musu ta duƙa ta ɓalle maɓalli akwatin, zare ido tayi tare da ja baya a hanzarce, da sauri Kabirda ya kiɗima da ganin abinda ke ciki ya riƙota, "dolas!" Salman yace tare da takawa ya isa wajen, ya ɗakko ɗaya ya ɗaga sama dan tabbatar da ingancin su, "me kyau ne ba jabu ba ne" yacetareda mayarwa.... "A ina aka samu wannan!" Ali da ya matso yace cike da mamaki, "ajiyan Sa'adatu ne" Insutaceidanta akan kuɗaɗen, "Allah ya kyauta, to wanna ai ba temakon da ze musu" Farisat tace taredakallon Sadiya, duƙawa Harira tayi jiki na ɓari ta zaro ƙaramin akwatin da ta hango tare dafaɗin"ga wani abu" amsa Kabir yayi tare da faɗin "ina keyn?" "Gashi" tace jiki na kyarma ta miƙamai, amsa yayi a natse ya zura, yana buɗewa ya bi abinda ke ciki da ido, takardu ne jere a kwanceseUSB guda biyu, "menene a ciki?" Iƙilima tace a tsorace.... Juyo da shi yayi ya nuna ma Insu dake jiran amsa, murmushi ta saki tare da amsa ba taredatabar murmushin ya ɓace ba tace, "nagode" tare da rufewa a natse ta juya.... "Mu ƙarisa" uncle Kamil da ya ga abin ba na ƙare bane yace cike da kulawa, jinjina kai tayi taredamiƙa wa Samir akwatin, amsa yayi cike da neman ƙarin bayani, "ka duba abinda ke ciki zamuyi magana" jinjina mata kai yayi tare da bin ta da ido, "wannan fa?" Sadiya tace tare da nunakuɗinda hannu, "wannan ku yakamata ku san me zaku yi da shi, sai dai ku tuna ba halal ba ne" tacecike da san tunatar da su, girgiza kai Kabir yayi tare da faɗin "wannan kuɗin ba ze ziyarci indamuke ba" murmushi Insu ta saki tare da faɗin "Yaya Salman ka amsa zamu yi magana inkasamulokaci" jinjina mata kai yayi cike da gamsuwa, sallama suka sake musu suka juya suka shigecikeda kewan da za su yi.... Suna fitowa farfajiyan tashi da saukan jiragen garin Ɓadamayya suka tadda motoci da security'sna tsayuwan jiran fitowan su, kai tsaye mota suka nufa suka ɗau hanyar gida.... "Wai duk gajiyan ne haka Insu!" Yasmin Ɓadamayya tace cike da mamaki tare da kallonta, kwaɓefuska tayi tare da faɗin "Mahmah wallahi akwai gajiya fa!" "Ikon Allah naga tafiyan nandauncleKamil da Anty Iƙilima aka yi, amma har suka bar gidan nan ba su nuna alamun wani gajiyaba" Nabila tace tare da kama haɓa, harara ta dalla mata tare da kauda kai, dariya Fadila ta saki tareda faɗin "ki yi shiru fa" "ai nayi" tace tare da danne baki, "Insiyyah" Hajiya tace fuska cike damurmushi tare da kallon ta, narke fuska tayi tare da faɗin "na'am!" "Jeki watsa ruwa ƙila gajiyanya sauka" "to" tace tare da miƙewa ta wuce sama, da ido suka bi ta tana ɓacewa ganin suYasmintace ko ba ta so dawowan ba ne?" Ta jefa tambayan tare da kallon Hajiya.... "Ze iya yuwuwa" tace tare da miƙar da ƙafan da ya takure, "a daddanna ne?" Fadila tace taredakallon ta, "eh in ba kya komai" murmushi ta saki tare da sakkowa a natse ta fara daddanawa, "Iƙilima ta kasa sakin jikinta Hajiya ko ba ki kula da hakan ba?" Yasmin tace tare da gyara zama, "zata manta komai nan da wasu lokuta" Hajja tace tare da basar da zancen.... Tana shigewa ta rage kayan jikinta tayi toilet ba ta jima ba ta fito, shiryawa tayi a gaggaucecikindoguwar riga cotton me ɗaukan hankali ta zura hijab ta tada sallahn magrib da aka kira tanabanɗaki, ba ta tashi a wajen ba se da ta idar da isha'i, maida hijab ɗin da take sallah inda takeajiyewatayi ta jawo baby hijab fari ta saka ta shafa turare sama-sama ta fice a natse hannu riƙe daphoneɗinta.... Tana kusan taka matakalan ƙarshe idan Mairah dake zaune kusa da Nafisat dake shirye tsaf gunun burgewa ya faɗa kanta, "Ami!" Tace cike da farin ciki tare da dira tayi inda take da gudu, "bi a hankali" Hajiya tace tare da sakin murmushi, cike da mamaki SSB dake zaune shi da Yasminsuna magana ya bi Yasmin da ido, murmushi ta saki tare da faɗin "na ɗauka da ka hau kunhaɗu" kauda kai yayi daga gare ta ya maida ga Insu da ta ɗauki Mairah ta rungume cike da kewa, binyanda Mairah ke ta shafa fuskanta cike da kewa yayi tare da sakin murmushi... Ƙarisawa inda yake tayi ta zauna a gefen shi tare da faɗin "barka da dawowa" jinjina matakai yayi idan shi akan ta, "mu fara gaba mu yi dinner" Yasmin tace tare da miƙewa idanta akanNabila da Fadila, miƙewa suka yi fuskoki cike da murmushi, "Nafisat muje ko" tace tare dakallonNafisat da hankalinta ke kan hiran da ake da wani babban doctor a tv, jinjina kai tayi taredamiƙewa, ƙarisawa kusa da su tayi ta ɗan duƙa tare da faɗin "Ammi sannu da dawowa" "yawwaUmmi ya school?" "Alhamdulillah" "Amatullah ta je yau?" "Eh ta zo" "okay, ɗauketa kuje gamunan" tace tare da maida hankalinta ga SSB da ya samu daman riƙo hannunta.... Miƙa ma Mairah hannu tayi cike da kulawa, ƙanƙame Insu tayi tare da kauda kai, "jeki abinki barta" SSB yace fuska cike da murmushi, murmushi ta saki ta miƙe ta wuce, kallon shi Insutayi fuska a marairaice tare da faɗin "sanabene fa Nafsii, da bana nan ba a wajenta take ba" "toai kinji ke ma kin ce da bakya nan, bana son rigima Gorgeous tashi muje" tura baki tayi tare damiƙewa ta saɓa Mairah da ta maƙalƙaleta.... Suna isa ta miƙa hannu dan jan mai kujera ya dakatar da ita ya ja mata tare da mata alamuntazauna, ba musu ta zauna fuska cike da annuri tare da jan mai, zama yayi a natse, jawo platetayi tare da miƙa mai Mairah ta fara ƙoƙarin serving ɗin su cike da natsuwa, "dubi ƴar nema yandatawani cukuikuyeshi" Hajiya tace tare da sakin murmushi, "ai Mairah kwanan nan tana zubalokaci fa" Nabila tace tare da sakin murmushi, "tayi ta gama, dan ba fuska wallah" Insu tace taredaajiye plate ɗin da ta zuba musu abinci a tsakiyansu, sinne dariya suka dan jin yanda tayi maganan..... "Wai ina maciyan ne! Ko mu kenan?" Tace tare da saka cokali, "gamu ba ku kenan ba" Jabir yacetare da jan kujerar ya zauna, murmushi ta saki tare da faɗin "to waje yayi tsitt fa, ba dole intambaya ba, ina Abban Iman da uncle Abubakar" "Ibrahim ya koma gida ni kuma gani" Abubakaryace tare da iddasa shiga wajen, "ku ce dai kuna gefe jira ku ke a kira ku, to uncle Munnir matso" ta idda maganan cike da yanayinta, dariya suka saki saboda ganin yanda tayi maganan taredakallon ta, juyawa tayi dan ganin yana ina, "be zo ba" "toh se mu fara, uncle Kamil ya yi gida, uncleJamil kuwa ba dawowan yau ba" tayi maganan tare da ɗiban abinci dai-dai ta kai bakin Mairah, buɗe baki tayi a hankali ta amsa, haka suka ci abinci cike da farin ciki suka tattara suka dawocikin parlor.... "Kukan nan be isa haka ba ne Meenat!" Uncle Jamil dake zaune kusa da Iƙilima yace cike dadamuwan da kukan ke haifar mai, girgiza kai tayi tare da faɗin "na daina, kukan ne yaƙi dainawa""oh Yaa Allah, Meenat, lokacin Insiyyat ne fa ya yi tunda ki ka ga ta rasu a lokacin, nayi imani dalokacinta be yi ba babu abinda sistern ki ta isa mata, addu'a take buƙata, kuma na san suInsudahaka suka yi imani shiyasa ba su ce komai ba" jinjina kai tayi tare da faɗin "haka ne" "yawwakukan ya isa haka ki tashi ki wanko fuska, ki fita ga ɗanki, yana murnan dawowanki ya ganki haka duk ya tashi hankalin shi" "subhanallah!" Tace tare da kallon shi, jinjina mata kai yayi tareda faɗin "ya shigo wajenki dan miki barka da dawowa ya tadda kina kuka, cike da tashinhankali ya zo gare ni ya faɗa min" jinjina mai kai tayi tare da miƙewa jiki a sanyaye.... "Amma meyasa ki ka dawo yanzu!" Yace tare da kafeta da ido, "ba amfanin zaman ne a can" tacea hankali, "no Meenat kar ki ce haka, duk lalacewar da damu ze yi ba ze tashi a damu ba, sannanduk wani abu da ya faru da shi zamu tsaya mai in ma na farin ciki ko akasin shi" "haka ne sedai wannan babu amfanin zama" tace a dake tare da goge hawaye, murmushi ya saki tare da faɗin"to gashi kin sa Hajiya na mun faɗa akan ni na sa ki ka dawo, ita a batun ta ma se anyi sati biyuhaka sannan ki dawo" murmushi ta saki tare da faɗin "Yaya Kabir ba ze yarda ba, ka ga yandayauzzuramin in shiryo in fito kuwa!" Tace cike da mamaki tare da kama haɓa..... Murmushi ya saki tare da miƙewa cike da farin cikin sakewan da tayi yace "ya ko kyauta" "ai dama haka zaka ce" tace tare da wuce wa toilet, murmushi ya saki tare da fice wa a natse, yanafita ya tadda Sa'eed zaune duk a dame idan shi akan ƙofan, murmushi ya sakin mai tare dafaɗin"ga tanan fitowa, kanta ke ciwo tasha magani ya lafa za ta fito yanzu, jeka shiryo ka raka ni" jinjina mai kai yayi ya wuce dakin shi cike da samun sassauci.... "Allah sarki" Nabila dake riƙe da wayan Insu idanta akan videon tarban Salman tace cike datausayawa, "gaskiya kun sha kuka" Fadila tace jiki a sanyaye, "ai an daɗe ba'a haɗu ba fa, dukancire rai" Insu tace tare da amsan wayan da Nabila ta miƙa mata, miƙa ma Nafisat tayi taredafaɗin "kalli kin gane shi?" Murmushi ta saki tare da baza ido, jinjina kai tayi tare da miƙa matawayan, "kaman wayan na cizonki!" Nabilla tace cike da mamaki, murmushi ta saki tare dafaɗinkira ne ya shigo".... Amsa Insu tayi da sauri ganin Lailah ne ya sata ɗagawa da sauri, "ke kin dawo ne babu labari?" Tace cike da ɗan faɗa, "oh Allah Anty Lailah yi haƙuri wallahi ba mu wani jima ba, na bari nemuɗan huta gajiya" "to shikenan, ki dinga dai maida komai da mahimmanci ya Salman ɗinyadawo? Babu wani matsala ko?" "Wallahi lafiya lau, cike da nasarori" "to ma sha Allah, ki kiraKhadijatu ki sanar da ita" "to in sha Allah" tace cike da girmamawa, "ki gaidamun da su Hajiyadakyau, zamu shigo ma akan tariyan Yasmin" "to shikenan za ta ji" tace cike da mamaki, katsekirantayi bayan ta ƙara sallamanta.... Zame wayan tayi tare da kallon Yasmin cike da mamaki tace "Mahmah tariya! An ɗaura ne!" Murmushi ta saki tare da girgiza mata kai, "to Anty Lailah na maganan tariya" "duka za'a haɗe lokaci guda" Jabir yace idan shi akan ta, "ma sha Allah yaushe!" "Saura kwana shida yau, daancegoma jiya, to Jamil yace se dai a barshi a bakwai kamar yanda barristern ya nema" Hajiya tacecike da jin daɗi, "Allah ya nuna mana, yawwa ina Ani baby ne ma?" "Tana gidan Kausar ɗazusukaje suka barota a can" jinjina kai tayi tare da kallon wayanta dake ruri.... Ɗagawa tayi ta kara a kunni tare da ɗaga sallama, amsawa Yasmin tayi tare da faɗin "wanannɗiya kina komawa kusa da Uncle ba'a ƙara gane miki" murmushi ta saki me faɗi tare da faɗin"tokinga lefina matan soja?" "A'a bangani ba, shiyasa na ce bari in tintiɓoki ai" dariya ta saki mefaɗi tare da faɗin "kin kyauta, Ya uncle Shureim? Kin dai koma ko?" "Eh daga airport can nayi, yanalafiya ya leƙa government house ba daɗewa" "to a gaidashi in ya dawo" "ze ji in sha Allah, nacekin turawa brother Sagir wannan alƙawarin kuwa?" "Oh Allah ban ma yi magana da ita ba, wallahi duk gajiya ne ya hallaromin" "to Allah ya huta gajiya, ki samu ki kwanta ze ragu, sannanki samu ki tattauna dan da gaske yake babu wasa a lamarin" "to shikenan in sha Allah bari intaɓo Malama ƴar jarida" "okay" tace tare da katse kiran... Maida akalan kiran ga number Farisat tayi cike da doƙi, tana ɗagawa tace "Malama ƴar jaridayajikin?" "Ke zan wa wannan tambayan dan ni lafiyata garau, ya ku ka tadda Hajiya da su Uncle?" "Alhamdulillah suna lafiya, gamu duk waje guda" "ina gaidasu ɗaya bayan ɗaya gani ga AntySalwa" "what! Wai ta zon!" "Wallahi gamu, wuce wan ku babu jimawa ta iso, amma gobe zatakoma, ta zo ganin ɗan uwanta na yarinta ne" ta idda maganan cike da yanayinta, dariya Insutasaki tare da faɗin "ta kyauta a ce ina miƙo gaisuwa, sun haɗu ko?" "Yanzu ma haka suna tare" "toshikenan a gaidamin Yaya Salman da kyau" "ze ji, my Jannah baby Insu na gaidaka" tace daƙarfi, "oh masu Jannah" tace tare da katse kiran.... Maida akalan kiran ga Khadijatu tayi tana ɗagawa suka gaisa ta tabbatar mata da dawowansulafiya ta kashe, "ajiye wayan haka" SSB dake bin ta da ido yace tare da kauda kai, fiddo idotayi taajiye wayan tare da kallon Hajiya cike da girmamawa tace duk sunce a gaidaki" "ina amsawa" tace tare da sakin murmushi.... "Ina ganin yakamata fa a buɗe office ɗin first lady" Jabir yace tare da kallon SSB, murmushi yasaki tare da kauda kai, zare ido Insu tayi tare da fadin "saboda me!" "Saboda yakamata aceyafara aiki" "eh kam, ai ga su Mahmah nan" tace tare da kallon Yasmin, "a'a ni ce first ladyn?" Tacetare da sakin murmushi, "to kuwa a nemi me zama, dan ni fa bana da sha'awan zama a officekokaɗan" "to in kin kammala karatun me zaki yi?" "Zama mana uncle Abubakar" tace cike dagaskiyanta, "daina wannan tunanin, karatun da ki ka yi na da amfani ga al'umma, zaki tsayadanal'ummar ki, zaki zame musu bango majingina, jigon nunawa" SSB yace a natse, shiru tayi taredabin shi da ido.... "Yawwa Hajiya ɗiyarki fa tayi kasuwa" tace tare da kwantar da Mairah da tayi barci a jikintaagefenta, "wa kenan?" Tace a natse idanta akanta, "Fadila" tace cike da farin ciki, "ma sha Allahaina?" Jabir yace cike da zaƙuwa, "a Bertuwa, Captain Sagir, soja ne abokin uncle ShureimmijinYasmin" "ma sha Allah" Hajiya tace cike da farin ciki, bin ta da ido Yasmin kawai tayi farinciki naratsa zuciyanta.... Ya ganta a stutut na ne lokacin bikin Asma, aiko yayi ta dako se da na jen nan ya mun maganan, nace baka da matsala ai ɗiyata ce" dariya suka kwashe da shi saboda yanda tayi maganan" "Allahyasa shine alherin" Abubakar yace cike da farin ciki, "amin uncle Abubakar wallahi mutuminkirki ne" "ai mun haɗu da su gaskiya suna da hankali" yace cike da yabawa.... "To Malama Fadila ba wani tsayawa lallaɓanki ko kora miki bayani zan ba, zan tura miki numbershi zan tura mishi na ki, ku gare ta can" murmurshi Fadila ta saki ba tare da tace komai ba, miƙewa Nafisat tayi a natse ta sallame su ta wuce, miƙewa su Jabir suka yi suka sallamesusuka fice, miƙewa yayi ya saɓa Mairah ya haye, "tashi ki je ki samu ki huta" Hajiya tace idantaakan ta, murmushi ta saki tare da miƙewa ta sallame su ta dafa mai baya a hanzarce.... Faɗawa jikin shi tayi tare da ƙanƙameshi, "oh Gorgeous yace tare da mata masauki me kyau, "nayi kewa" tace tare da haɗe bakinsu waje guda, se da suka ɗau lokaci a haka kafin su janyegajuna, "na fiki" yace idan shi na yawo a cikin nata, murmushi ta saki tare da kai baki ta sumbaci goshin shi ta gangaro idon shi ta sauka kan hancin shi ta tsallaka laɓɓanshi, "kar ki zawatani" yace a hankali tare ra riƙota "na daɗe da zawace Nafsii, a zawace nake" tace tare da ƙanƙameshi, murmushi ya saki tare da birkitota ya fara ba ta kula na musamman.... "Meenat yanzu rashin ɗaukan abubuwanki da mahimmaci ya kai a ce ki ka sa zuwa ki wa ƴar uwan zamanki ta'aziyya?" Uncle Jamil dake tsaye a ƙofar bedroom ɗin malika yace tare dakallonyanda ta baje a sama gado tana kallon tiktok, ɗago kai tayi tare da faɗin "Meenat ka barotaacan, sannan maganan ta'aziyya ban san wanne ka ke nufi ba" cike da mamaki yace "kina nufinbaki san ƙanwarta ta rasu ba!" Zabura tayi ta miƙe zaune cike da firgici tace ƙanwarta dai! Ka nanufinuwa ɗaya uba ɗaya!" "Daga ita se ita" yace tare da sakin numfashi me ƙarfi.... "Wallahi ban sani ba, kaima kasan da na sani ba zanƙi mata ta'aziyya ba, ai mutuwan na kayawuci wasa, Allah ya gafarta mata, amma meyasa ta dawo?" Ta idda maganan cike da sanyindajin mutuwan ya haddasa mata, sauke numfashi ya kuma tare da faɗin "ba sa zaman makoki" "a'ada damuwa, duk da haka da sun barta ta zauna ko na kwana bakwai ne tunda ba a gari takebayanzu, rasuwan ɗan uwa fa, haba dakwai ciwo matuƙa" tace cike da ganin ba su kyauta ba, "ni mana so ta zaunan, tunda sun dawo da ita shikenan se ta bi ta da addu'a" "haka ne, Allah ya rahamsheta, tunda dare yayi bari se zuwa gobe na leƙa in mata ta'aziyyan" "hakan yayi Allahyabaki iko" yace da kulawa, "amin" tace tare da komawa ta kwanta, sallamanta yayi ya fice anatseFitowa yayi sanye da rigar wanka Insu ɗafe a ƙirjinshi tana tsane mai ruwan kai da tewol ɗinhannunta, sauketa yayi ya ja stool ya zaunar da ita tare da bin ta da ido, murmushi ta saki tareda saka tafin hannu ta tufe mai ido takai baki ta sumbaci laɓɓanshi, murmushi ya saki tare dajawota, ya ɗau tewol ya fara goge mata kai, ganin ta fara lumshe ido ya sa shi faɗin "a'a Gorgeous" tura baki tayi tare da narke fuska.... "Sorry" yace tare da cigaba da goge mata, yana gamawa ya wuce Wardrobe ya ciro kayan barci me taushi riga da wando, "oya miƙe ki saka" yace tare da duƙawa, miƙewa tayi ta dafa kan shi tare ɗaga ƙafa ta saka, yana kammala saka mata ya tatsi mai yafarashafa mata, ganin yanda take ta tura baki ya sa shi sakin murmushi tare da faɗin "to angama" yaidda maganan tare da cicciɓanta ya wuce saman gado.... Kwantar da ita yayi tare da bin bayanta ya jawota, sakin hamma tayi tare da faɗin "ƙanwar Sa'adatu ta ba mu wani abu yau, tace yana da matuƙar mahimmanci a gareka, na ba Yaya Samirakan ya duba, na san in yagama tattara bayanai ze faɗa mana abinda ke tattare da shi" jinjinakai yayi tare da shafa gashinta, "night Nafsii" tace tare da tare Hamma ta kwanta luf, murmushi yasaki tare da ƙara shigar da ita jikinshi baki ɗauke da azkhar ɗin barci.... Comments fans🥰🙏 🫀MUGUWAR TSOKA 🫀 {🫀TA'ARE KALLUƊE} [Muscle Cramp🫀] ) عضلة سيئة ( 🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_ https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 written and Created ~~~~~~~~~~~~~~ ِبسم الله الرحمن الرحيم By Yardajjiya👩 💻 Page. sixty four A ɗan hanzarce take taka stairs ɗin cike da ƙosawa, tana idda sauka ta tadda gaba ɗayansuzazzaune cikin suturu na kece raini se hada-hada suke, da sauri ikilima da suka iso ba daɗewatamiƙe jin yanda Mairah dake biye da Insu ke tsala ihu kamar wacce ake yankawa, "oh Yaa Allahme aka mata!" Tace tare da nufarta a hanzarce.... Komai Insu dake jin kamar ita ma ta tsala ihun ba tace mata ba se wuce wa da take ƙoƙarinyi aɗan hanzarce, "zo ki amsheta" SSB dake zaune shi da su Jabir yace ba tare da ya kalleta ba, ɓatafuska tayi cike da takaicin kukan da take yi ta juyo ta nufi Iƙilima dake ta ƙoƙarin rarrahshinta, miƙa mata hannu tayi a natse fuska a ɗaure, cif tayi tare da damƙe mayafin Iƙilima ta baya, danta san ƙarshen batun, "jeki Ammi Mairah" Iƙilima tace cike da kulawa, ƙara damƙe mayafintayi tare da shagwaɓe fuska, ƙwafa ta saki ta juya a ƙufule ta nufi general kitchen.... Tana ɓacewa idanunsu Fadila da Nabila suka kwashe da dariya tare da kallon Lubabatu dakecewa "ikon Allah!" "Ai ba zata ba, ta san kwanan zancen ina Nafisat? Anisa jeki kirawota taamsheta" Yasmin Ɓadamayya tace tare da sakin murmushi.... Ba musu Anisa ta tashi ta wuce a guje, "ya masu jeren ne? Kun kira su kuwa?" Lubabatutacetareda kallon Yasmin, "ba jimawa nayi magana da Anty Lailah tace sun kusa" "to shikenan se mukasance cikin shiri dan na ce ma Kausar in sun kammala su zauna a can in munje se munrankayogaba ɗaya kawai" "gaskiya hakan yayi" Alhaji Munnir yace cike da yabawa shawaran na ta.... A natse ta fito cikin na ta suturan na gani da faɗi, duƙawa tayi gefen Hajiya dake ta sakinmatamurmurshi

Chapter 103 of 109