ne, gaba ko ance tayi ba yi za tayi ba, danAntytake" Nabila tace tare da isowa wajen tana danne dariyan dake taso mata, harara Insu ta bankamata tare da kallon Hajiya dake cewa "ƙafa yayi sauƙi banɗaki ma da ƙafafuna na taka babusandan jagora" murmushi ta saki tare da faɗin "Allah ya ƙara lafiya"....
Juyawa ga Yasmin da ta iso wajen tayi tare da faɗin "Mahmah an tashi lafiya?" "AlhamdulillahInsu ya kwanan Mairah da jikin?" "da sauƙi, ya jikin Uncle?" Ta idda maganan a hankali, "kezanwa wannan tambayan, ko har yanzu ba ki je kin duba shi ba ne?" Ta idda maganan tare dakafetada ido, "bari in dubo shi" tace tare da ƙoƙarin wucewa, "zo ku ci abinci ku wuce be tashi bagalokaci yana son ƙwace muku" Hajiya tace da tsan-tsan kulawa ...
Jinjina mata kai tayi tare da juyowa ta wuce dining, kallon Hajiya Yasmin tayi da mamaki taredabin bayansu, suna zama ta ja plate ta zuba ma Insu, "sannu Mahmah" tace cike da farin cikinkulawan da ta nuna musu ta fara ci, zuba ma Nafisat tayi da kulawa tare da faɗin "hanzarta6:30am" jinina mata kai tayi ta fara ci a natse....
"Ba ta mana ko za taci" Yasmin tace tare da kallon Insu, "ba zata ci ba" tace tare da ƙoƙarinkai
mata baki, kauda kai tayi tare da ɓata fuska, "kin huta" Yasmin tace tare da sakin murmushi, shigowa Lawiza tayi da sauri baki ɗauke da sallama, tsayawa tayi turus tare da faɗin "ba dai namakara ba!" Murmushi Yasmin ta saki tare da faɗin "baki makara ba yanzu sakkowansu, sunkawo abincin tun ɗazu suka ce ke ki ka ce su kammala a lokacin" ta idda maganan idonta akanLawizan, jinjina mata kai tayi tare da faɗin "eh saboda na ji za su fita da wuri" "haka ne" tacecikeda murmushi....
Jan kujera baya Insu tayi ta miƙe tare da faɗin "ina kwana Anty Lawiza?" Murmushi ta sakinmatatare da faɗin "lafiya lau, ya kwanan Mairah?" "Oh Allah kowa se ya tambayeta ba ku damudajinyanda na kwana ba ma" tayi maganan kaman zata saki kuka, "to me ruwan wani da yandaki kakwana" Nabila tace tare da sakin dariya....
"Amsheta mu tafi kar mu makara" tace tare da miƙa ma Nabila ita, kai hannu tayi da zummanamsanta wani kuka me ƙarfi ta saki tare da ƙanƙame Insu a razane, da mamaki suka kalleta, "auhlallai ma" Insu tace cike da takaici, kai hannun Lawiza tayi tare da faɗin "zo Mairah" rumtseidotayi kaman wacce tayi gamo tare da ƙara ƙarfin kukan, "oh Yaa Allah me aka mata?" Ibrahimdaya shigo yace cike da ruɗu....
"Wai ba zata zo ba" Yasmin tace tare da kai hannu, wani ƙwaƙwuma ta ma Insu wanda se dataɗan tureta, "a'a bari mana" Yasmin tace tare da kallon ta, "ku amsheta dan Allah lokaci nawucewa, zan ajiye Nafisat sannan in wuce" tayi maganan da damuwa, "tunda taƙi yarda ku je taremana" Ibrahim yace tare da kallon ta... Kallon shi tayi da mamaki tare da faɗin "haba mana Abban Iman, makaranta fa zani ba shoppingba, Anty Lawiza amsheta kuna tafiya can side ɗin za ta natsu" ta idda maganan tare da nufar
Lawiza, nan ma ƙwaƙwumeta tayi tare da fasa ihu, "kayya Mairah yau kuwa da lafiya? Barmun
ɗiya ta tafi makaranta, ba wani lallaɓaki da zanyi dan jika nake da ke ba ƴa ba ba uwa ba" Yasmintace tare da sakin murmushi, "ki je da ita dan Allah ki na ganin yanda take wannan kukanbayarda ta zauna za tayi ba" Lawiza tace da kulawa....
"Ba fa yarda za su yi ba" tace kamar za ta saki kuka, "wa ya isa hanata zama a class ɗin, abunasu!" Yasmin tace da mamaki, murmushi Insu ta saki tare da faɗin "a'a Mahmah na mu dai" "a'awallahi na su ne, ku a suwa? Saɓata ku tafi dama na san tunda ba Nafisat ba yarda za tayi ba" taidda maganan tare da shafa kanta, miƙa ma Nafisat ita tayi tare da faɗin riƙeta, kwaɓe fuskatayi
tare da kallon Insun.... Harara ta dalla mata tare da faɗin "wallahi ki ka yi wasa ba zaki bi ni ba" kai jiki ga Nafisat tayi asanyaye, murmushi suka saki gaba ɗayansu tare da kallonta wuce wa sama tayi ba ta daɗebatasakko riƙe da basket ɗin abinci Mairah da kayan canzawa da leda madaidaici, miƙa ma Yasminledan tayi tare da faɗin "danbun nama ne, in na dawo zamu yi wani magana dake me
mahimmanci" jinjina mata kai tayi cike da kulawa, "muje" tace tare da kallon Nafisat dakesaɓeda Mairah ba musu ta shige gaba, bin bayanta tayi tare da musu sallama, dafa musu baya
Ibrahim yayi fuska cike da murmushin yanda fuskan Insun ya koma.... Murmushi Hajiya ta saki tare da faɗin "Insiyyah ba dai karaba" murmushi Yasmin ta saki taredafaɗin "ƙarama ce da hankalin manya, amma Hajiya meyasa ba ki barta taje duba shi ba dukdabetashin ba!" murmushi ta saki tare da faɗin "ki barta ta yi niyya da kanta" jinjina kai tayi taredazama ta jawo roban dake cikin ledan....
Suna fita driver da ke zaman jiransu ya miƙe da suari ya buɗe musu motan, shigewa Nafisat tayi
a natse, kallon Ibrahim Insu tayi tare da faɗin "na ɗauka zan tadda Malam Musa se na ga sabodaban" ta idda maganan idonta akan shi da alamun tana son jin wani abu, jinjina mata kai yayi
tare da faɗin "ya firgita da abinda ya same shi, shiyasa da ya nemi ajiye aikin ba mu ƙi ba" jinjinamai kai tayi tare da faɗin "in sha Allah zanyi ƙoƙarin zuwa gaida shi" ta idda maganan taredashigewa motan, jinjina mata kai yayi fuska ɗauke da murmushi, rufe ƙofan driver yayi ya wucedriving side, yana ɗaukan hanya security's suka dafa mai baya, bin su da ido Ibrahimdaketsayefuska cike da murmushi yayi har suka ɓacewa ganin shi..... Kai tsaye makarantar su Nafisat suka yi, ba su ɓata lokaci wajen bin haɗaɗɗen makarantar daidoba suka yi office ɗin me alhakin amsa sabbin ɗalibai, bayani ta mai a gaggauce, ganin fuskantayasa shi saurin shigar da zuwan Nafisat ya faɗa mata inda department ɗinsu yake godiya ta mai
suka fice.... Komawa mota ta yi ta ɗakkota roban danbun na ma suka nufi department ɗin, suma ƙarisawagefen class ɗin da ya mata kwatance ta miƙa mata roban ta amshi Mairah dake saɓe a kafaɗanta, "kya samu na taɓawa duk da na san Amatullah za ta zo mu ku da shi" murmushi ta saki taredafaɗin "in ta zo da shi na yi miki alƙawarin dawo miki da naki" "da dai ban san dawa nake maganaba ne" tace tare da banka mata harara ta saɓa Mairah, "murmushi ta saki me faɗi tare da juyawata fuskan Mairah ta mata bye-bye, "ki na ji ko?" Insu tace cikin muryan dake nuna abinda zatafaɗa me mahimmanci ne...
"Eh Ammi" tace a natse tare da ba ta hankalinta, "jami'a gidan ka zo na zo ne, ba kamansecondary da primary ba ne da malamai ke sa ido akan mu, nan ko me ka yi kan ka kai mawa, bame ce maka dan me, ko wani tsuntsu kukan gidan su yake, dan haka ki yi ƙoƙarin koka irinkukanna ku gidan, kar ki ari na wani gida dan ba ko da yaushe kayan aro ke rufe katara ba, akwai dai
ƙarawa ado ƙawa, ba ni anan ba Yaya ba Farisat ba Yasmin ba Sadam ba Salman se dai akwai
Ubangijin mu, ba ya gyangyaɗi Nafisat, kome zaki aikata yana kallon ki, kar ki yi tunaninakwai
wani lungu da za ki shiga ki ɓoyewa ganin shi, ki ji tsoron mahaliccin ki, shine wanda yafi kamataki tsorata ba ni ko sauran ƴan uwana ba,ki daure ki kama mutumcin ki mutanen banza za suji
shayin tunkaranki" ta idda maganan a sanyaye tare da kafe fuskanta da hawaye ke tsere daido....
Jinjina mata kai tayi a natse tare da faɗin "ba zan yarda inci amanar mahaliccina ba, ba kumazanyi sakaci in ɓata yardan da ku ka mun ba, nayi muku alƙawarin yaƙi da duk wani dabi'adazesani zubda tarbiyyanku" "Allah ya temake ki, 3 zaku gama lecture's ki kula da lokacin shigadalokacin fita driver ze zo ya ɗauke ki" jinjina mata kai tayi cike da gamsuwa.... Murmushi ta sakin mata tare da faɗin "Mamin Mairah an girma, to shige ko" murmushi ta saki
tare da shafa kan Mairah ta ƙara sallamanta ta shige class tana goge hawayen saman fuskanta, juyawa tayi da sauri fuska ɗauke da murmushi ta wuce inda suke zaman jiranta, tun kafintaƙarisa ɗaya daga cikin security's ya buɗe mata ƙofa shigewa tayi a natse, yana rufe ƙofandriveryaja a natse ya nufi barin makarantar....
Sauke Mairah daga kafaɗanta tayi tare da sakin mata murmushi, ɗaga hannu tayi ta shafi
laɓɓanta na ta idon akan fuskan Insu dake sakin mata murmushi, "zaki Insoul yau ko?" Tacefuskanta na yalwatuwa da murmurshi, jinjina kai tayi tare da sakin mata murmushi, "zaki gauncle Hisham?" Ta kuma ce mata idonta akanta, jinjina mata kai ta kuma fuska cike da
murmushinta na yara, "to banda rigima, ban da ƙiwiya kin ɗau alƙawari?" Ta kuma cewa kamantana magana da wata babba me hankali, jinjina kai ta kuma tare da yunƙurin tashi, ɗagatatayi tazaunar tare da fito da wayanta, kai tsaye inda ta adana hotuna ta nufa tana hawa kan hotonshi taƙure da ido kamar me nazartan wani abu a ciki, kai hannu Mairah tayi da zumman amsa, saurinmatsawa da shi tayi tare da faɗin "kull" sadda ido ƙasa tayi tare da kwaɓe fuska, murmushi tasaki me faɗi tare da juyo mata da fuskan wayan ta zungureta da ɗayan hannun, ɗago kai tayi tazuba ma wayan ido, wani ƙayataccen murmushi ta saki tare fa faɗin "Abie"....
Nagartaccen murmushi Insu ta saki tare da faɗin "Abbie be farka ba muka fito amma inmukakoma za muje mu gaidashi nayi miki alƙawarin" "Abie" ta kuma cewa fuska cike da farincikinjinsunan da Insun ta kira, murmushi ta sakin mata tare da sumbatan goshinta cike da so da ƙauna....
Suna shiga Insoul ta ciro baby hijab ɗinta dake cikin basket ta saka mata, saka hannu tayi tafarafincika dan san cirewa, kama hannun tayi saurin yi tare da faɗin "zamu ɓata" kwaɓe fuskatayi
tare da sadda ido ƙasa ta zame hannun, murmushi ta saki tare da faɗin "to ba zamu ɓata ba, ai
Mairahn Mommy ba ta lefi ko ƴar albarkan Abbie?" Ta idda maganan tare da sakin murmushi taleƙa fuskanta, murmushi ta saki tare da ƙoƙarin kamo fuskanta, saurin kaudawa tayi taredasakin dariya.... Driver na dai-daita parking security's suka buɗe mata ƙofan, tattaro komatsanta tayi ta miƙamusu, amsa suka yi a girmame sakkowa tayi hankalinta akan gyara ma Mairah wuyan hijabɗinda ya karkace, "wow Mairah!" Hisham da tun shigowansu ya hangesu ya nufo wajen yace damamaki, murmushi ta sakin mai tare da bin shi da ido, da sauri ya ƙariso wajen tare da faɗin"i
really miss you my lovely daughter" ya idda maganan tare da kai mata hannu alamun ta zo, "jeki
uncle" Insu tace tare da kallonta ganin yanda take bin shi da ido, kai na ta hannun tayi dukdabata so ba, saɓata yayi tare da faɗin "Allah ya miki albarka kaman kin san ina masifan sanganinta" murmushi ta saki tare da amsan basket ɗin da sauran kayan suka wuce ciki.... Suna shiga class Nachma da hankalinta ke bakin ƙofan ta zare ido tare da bin su da shi cikedamamaki, suna ƙarisawa ta yi saurin ɗaukan jakanta dake kan kujeran Insu tare da faɗin "Mairahko!" Jinjina mata kai Hisham yayi tare da shafa kan Mairah, "dama tare da Mommynta kukazoInsu!" Tace da mamaki, murmushi ta sakin mata tare da zama a natse, "kin ji ki ko ba'a abinkirki
dake, ka ji Hisham tare ku ka zo?" Ta idda maganan tare da kallon shi, jinjina mata kai yayi tareda sakin mata murmushi, "wow gaskiya na so in ganta mutuniyar kirki ta na da harka sosai"
jinjina mata kai Hisham yayi tare da kallon Insu dake cewa "na ki dai ya zo ɗaya da ita".....
"Bari mu tafi garden ina ga se kun fito" Hisham yace tare da miƙewa saboda ganin lecturer yashigo, "baka da lecture ne?" Insu tace tare da kallon shi, girgiza kai yayi tare da faɗin "se 2" "okaytafi da wannan baske ɗin, akwai danbun na manku a ciki, ita ma tana ci" ta idda magananahanzarce tare da maida hankali ga lecturer, jinjina kai yayi ya ɗauka ya nufi ƙofa a natse... Yana kai jiki Khalim ya kawo na shi ja gefe yayi idon shi akan Mairah dake bin shi da ido
murmushi ya sakin mata tare da faɗin "zaki koma Ammi?" Jinjina kai tayi kaman zata saki kuka, murmushi ya sakin mata tare da faɗin "to amma mu je mu dawo ko?" Jinjina mai kai ta kumatareda lafewa a ƙirjin shi, ficewa yayi fuska cike da farin cikin yarda da shi da tayi... Tura ƙofan dakin Shureim yayi a natse baki ɗauke da sallama, dafa mai baya Yasmin dakecikinshiga me matuƙar burgewa tayi na ta bakin ɗauke da sallama, dafo mata baya sojan dakeɗaukeda baske yayi na shi bakin ɗauke da sallama, amsawa su Gude dake kusan cike a ɗakin sukayi
idanun su akan su, murmushi Yasmin ta saki tare da faɗin "Anty Jummai a she kuna nan?" Murmushi Jummai da Suwaiba suka saki idanun su akanta....
"Anty Gude ya me jikin?" Tace da kulawa, "Alhamdulillah ya gidan?" "Alhamdulillah" tacetaredawucewa inda Sudais yake, gaishe su Shureim yayi da kulawa amsawa suka yi cike da farinciki, "ya jikin Yaya Sudais?" Tace da tsan-tsan kulawa idonta akan shi, murmushi ya sakin matatareda faɗin "Alhamdulillah" cike da farin ciki, "ya jikin?" Shureim yace fuska a kame, murmushi yasakin mai tare da amsawa cike da jin daɗi, "Allah ya ƙara lafiya, precious zamu jira a waje" yaiddamaganan cike da kulawa... Murmushi ta sakin mai tare da jinjina mai kai juyawa yayi a natse ya sallamesu ya fice, saurinbinbayan shi sojan da ya ajiye basket yayi, "in zubo maka abincin?" Tace da kulawa fuskanta faɗaɗeda murmushi, "ai tun ɗazu shi yake jira ya ƙi cin komai" Halima tace tare da sakin murmushi...
"Allah sarki ɗan uwana wallahi yau na tashi da ciwon kai ne, shiyasa ban kammala da wuri ba, kayi haƙuri" tace tare da miƙewa ta isa inda sojan ya ajiye basket ɗin ta fara zuba mai, "ohAllahsassannunku" tace tare da kallon sauran jama'an dake ɗakin, murmushi suka saki tare daamsawa da kulawa, murmushi Suwaiba ta saki tare da faɗin "sannu da aiki Yasmin Allahyabadalada, ina Farisat?" "Gani nan Anty Suwaiba na" Farisat tace tare da shigowa cikin shirin tafiyaaiki, "ƴar halak kin ƙi anbato" tace tare da sakin mata murmushi...
"Wannan kaɗai ya isa sheda zamtowata ɗiyar halal" tace tare da sakin murmushi, "ke Farisat yaƙarin haƙuri kuma!" Jummai tace cike da damuwa, "Alhamdulillah Anty Jummai" tace muryaasanyaye, "kai wannan bawan Allah ya sha jinya, ze iya kai shekara biyu fa ya na fama ya tashi yakwanta" tace cike da damuwa, "ze fi ma" tace tare da gaida mutanen dake ɗakin, "kar ka ragekoloma" Yasmin tace tare da sakin mai murmushi, murmushi ya sakin mata tare da fara ci a natse, "gawa ka ƙi rami ya jikin?" Farisat tace daga inda take tare da kallon shi, murmushi ya sakinmata ba tare da yace komai ba...
"Ban san tsiya Farisat" Jummai tace tare da sakin murmushi, murmushi ta saki tare da faɗin"toai gaskiya ne Anty Jummai ɗan ku ya dage wai be gama cin duniyan ba" tayi maganan taredabuɗe jakanta, zaro leda madaidaici tayi ta ƙarisa kusa da shi ta ajiye a gefen shi tare da faɗin"gayi nan ya dinga taya ka hira in abokan hiran basa kusa" tayi maganan tare da juyawa, "meyasamu?" Suwaiba tace murya cike da alfahari, "milk donuts ne Anty Suwaiba" tace tare da sakinmurmushi, "ah lallai Sudais ɗan gatane" tace tare da bin su da ido....
"Zamu tafi can ne tare? kin san zan tafi aiki" Farisat tace tare da kallon Yasmin, miƙewa tayi
zumbur tare da faɗin "Habbubi ma fa jirana yake muje" ta idda maganan tare da ɗaukanjakantata rataya, "ina ne anguwan na su? In mun tashi se mu je mu musu gaisuwa" Suwaiba taceidontaakan su, "can muka yi yanzu haka in zaku mu rankaya" Farisat tace tare da kallon su, miƙewasuka yi zumbur Suwaiba dake gyara zaman hijab ɗin jikinta tace "shikenan kuwa, dama tunaninyanda zamu je can ɗin muke, da tunaninmu mu biya ta can mu rankaya da su Hajiya tundagaku
zaku ai mun huta komawa baya" "ko kun je can ba za ku tadda su ba, tun safe suka tafi ita daBaba Mari" Farisat tace tare da dumfarar ƙofa, sallaman su Yasmin ta kuma ta dafa mata baya... Kallon su Nafi dake tsatstsaye Sudais yayi tare da faɗin "ku bi su mana" kallon Gude dakekallonsu suka yi tare da marairaice fuska, "kuje amma ku dawo da wuri" tace tare da kauda kai, dasauri
suka sallameta suka fice, murmushi Jummai ta saki tare da faɗin "bari mu leƙa mu musugaisuwa" jinjina musu kai tayi cike da kulawa, "Sudais Allah ya ƙara lafiya, in mun samu dawowakafin a sallameku ma to in ba mu samu ba kuma se mun haɗu a gida" jinjina musu kai yayi dakulawa, juyawa suka yi suka fice....
"Yaran nan sune yaran Abdussamad ƙanin ki ko Gude?" Dattijuwan dake gefe tace tare dakallonGude, jinjina mata kai tayi tare da kallon Sudais dake maganan a ƙara mai abinci, miƙewatayi
cike da jin daɗi ta nufe shi, "yau na ga hankali da sanin yakamatan da ake kiran musu, tabbassungaji karamci" matar tace fuska cike da murmushi tare da kallon wa ƴanda ke kusa da ita, ƙaramai tayi ta koma ta zauna, zuciyanta na mai-maita kalaman matan....
"Se ki ka ji labari jiya" Farisat tace tare da kallon Yasmin, murmushi ta saki tare da faɗin"kedai
bari, kin yi magana da shi ne?" "A'a na dai kira mun gaisa da su Hajiya na taya su murna sunmungaisuwan Baba, shi kuma doctor yace ya huta sosai, amma da Anty Lailah suka koma gidatakirani tace mu kira Insu ta haɗa mu da shi mu gaidashi" ta idda maganan tare da kallon ta, jinjinamata kai tayi tare da faɗin "nayi magana da ita da kusan 6:20am tace be tashi ba ita kumatanasaurin tafiya school" "okay mu jira se ta dawo ina ga se in haɗa mana kiran ze fi" Farisat tacetareda ƙoƙarin buɗe motan ta, "ina Yaya Salman?" Yasmin tace tare da buɗe ma su Suwaiba bayasuka shige, "yana hospital ya samu kiran gaggawa" tace tare da shigewa driving side, gefentaHalima ta shiga Nafi ta shige baya, wucewa na su motan tayi bayan Farisat ta ma nata key, tanashiga Shureim ya kwaɓe fuska tare da kallon ta, "sorry" tace tare da sakin murmushi, jawotakusa da shi sosai yayi tare da ba ma sojan drivern umurnin ya ja mota...
Fitowa suka yi shirye tsaf gunun burgewa daga shi har matan, kyakykyawan gani yayi da
yaranshi mata biyu dake zaune a cikin parlorn, yana shirin zama matan tayi saurin ce mai "dininga shirye yake" cike da karairaya, murmushi ya sakin mata tare da kallon yarinyar ƴar kimanintenyear's ɗin dake gefen shi cike da ba da umurni yace "je ki kiramun Yaya Abba a ɗakin shi" "Daddysunan shi kenan Yaya Abbah?" Tace cike da mamaki, jinjina mata kai yayi tare da faɗin "YayaSa'eed sunan shi" "ni zan kira shi" ɗayan yarinyar ƴar kimanin shekaru 6 wacce take kamadatafarko sak tace tare da wuce wa a guje tayi ɗakin da ta san baƙi na yawan sauka, murmushi yabi
ta da shi tare da wuce wa dining area....
Jan mai kujera tayi ya zauna a natse tare da kallon yarinyar da ya aika da farko fuska ɗaukedamurmushi me cike da ƙauna yace "Mommyn ku tace ance ku dawo gida" jinjina mai kai tayi tareda faɗin "mutane ne a waje da yawa wai suna zanga-zanga shine HM yace a koma da kowagidaza su sanar da ranar da zamu koma in komai ya dai-daita" ta idda maganan a ɗan tsorace, "zanga-zanga!" Yace da mamaki idon shi akan ta, "wallahi fa Dear, se ka ga abinda ake ta nunawaamedia, matasa sun fito akan se uncle ɗin su ya fito sun ga lafiyar shi, dan sun samu masaniyaakan harin nan da aka kai an cutar da shi" matan tace cike da rashin damuwa a zuci, "subhanallah wannan maganan ta ina kuma ta fita!" Yayi tambayan cike da damuwa taredazarowaya....
Jan kujera wacce ta je kiran Sa'eed tayi ta zauna tare da faɗin "gayi nan Daddy" jinjina matakai
yayi tare da kara wayan a kunni, ana ɗagawa yace "ka ji abinda ke faruwa a garin nan kuwa!" "Bagari ba ne ƙasa ce gaba ɗaya" muryan Jabir ya bayyana cike da damuwa, "yanzu ya za'ayi kenan!"Yace cike da neman mafita, "abu na shirin rikicewa kaina ya kulle, se dai na ce ma SSGa tabbataran tsaida faruwan abun kar yayi nisa" "gani nan" yace tare da zare wayan ya miƙe, "Dear inazakakuma? Please ka zauna mu ci abinci tukun se ka tafi" matan tace a marairaice cike da damuwa, komawa yayi ya zauna tare da fesar da huci....
Zaran plate tayi ta zuba mai madaidaicin abinci ta tura mai gaban shi tare da faɗin "baƙonkaya
tafi tun ɗazu yace akwai wani uzuri da ya taso mai" jinjina mata kai yayi tare da faɗin "munyi
magana da shi tun daren jiya, ana neman shi a wajen aikin shi ne" yayi maganan cike da damuwada zancen da yaji yanzu, "can Nigerian ya koma!" Tace da mamaki, jinjina mata kai yayi a natse, jinjina kai tayi tare da faɗin "baka ce min komai akan yaron da muka zo da shi jiya ba" ɗagokai
yayi ya kalleta tare da faɗin "ɗan ƴar uwata ne, ze zauna tare da mu" "ban gane ba!" Tacedaɗinbin mamaki me haɗe da tsoro....
"Yaren ki ka daina ganewa ko me?" Yace idon shi ƙyam akanta, "na ji kaman ka ce ze zaunadamu, ka na nufin anan ze cigaba da rayuwa!" Ta idda maganan zuciyanta na tsitstsinkewa, "ashekinji" yace tare da ɗaukan cokali...
"Ba ze yuwu ba Dear, ba ta yanda zamu ɗakko ɗan wasu mu haɗa da na mu, wai kamanta nafaɗamaka bana da ra'ayin riƙe ko ƴaƴan ƴan uwana ne bare kuma na wasu can wanda ba kuhaɗakomai da su ba" ta idda maganan cike da ɗin bin damuwa, da zallan mamaki ya kalleta, "gaskiyane Dear dan Allah kar ma ka fara wannan maganan" tace cike da rashin jin daɗi, "gida dai gidanane, sannan ni ke aurenki ba ke ki ke aure na ba, dan haka yaro a nan ze cigaba da zama wannanshine hukunci na" ya idda maganan a kamale, "ba ze taɓa yiwuwa ba Dear, wallahi ba zanriƙeɗan wasu ba" "Meenat anan Sa'eed ze zauna" yace a kausashe, "to ka sani ba hannuna akanshi" tace ita ma a kausashe, "me hakan ke nufi!" Ya je fa mata tambayan idon shi ƙyamakanta....
"Ya zauna ga gida nan ga ɗaki nan, yayi rayuwarshi tunda dama gidan na ka ne amma ba hannuna wajen riƙe shi" murmushi ya saki me ciwo tare ra faɗin "kar ki damu zan kawo me kula dashi""ze fi" tace tare da jan plate ta fara serving ɗin yaranta, ajiye cokalin da yake hannun shi yayi tareda jan kujera ya miƙe ya bar wajen, yana shiga parlor Sa'eed na fitowa daga ɗakin da aka bashi, murmushi ya sakin mai me faɗi tare da gaishe shi, murmushi ya sakin mai cike da danne abindake damun shi ya riƙo hannun shi tare da faɗin "muje" ba musu ya bi shi ...
Tsaki Meenat ta saki tare da miƙewa ta bar wajen, kallon juna yaran suka yi cike da rashinjindaɗi, tura baki ƙaramar me suna Yasmin ana kiranta da Intisar tayi tare da faɗin "yau ma Mommyta ƙara ɓatawa Daddy rai" tayi maganan kaman zata saki kuka, "shiii" babban me suna Farisat
ana kiranta da Hafeeza tace mata tare da kallon Meenat da ta fito riƙe da waya, "zo muje
bedroom" tace a hankali tare da miƙa mata hannu, tashi suka yi suka wuce saɗaf-saɗaf kamanɓarayi.... A guje wata matashiyar budurwa ta fito daga ɗakinta tare da faɗin "Shila ta farfaɗo!" Da azamaShila ta miƙe ta yi ɗakin da matashiyar budurwan ta fito da sauri muƙarrabanta suka dafamatabaya, ganin yanda matashiyar budurwan da ta raka su Sarari gidan Ziza ke fizge-fizge taredasumbatu yayi matuƙar sanyaya jikin su, kamota Shila da ta zauna a gefenta tayi tare da dukankumatunta a hankali cike da ɗan fargaba tace "ƴar ƙwaisa dubi nan mu ne tare dake, suntafi, baabinda za su miki" fashewa da kuka tayi me ƙarfi tare da ƙanƙame Shila, tarba
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 76 Chapter of 109