cike da jin daɗinjinmuryan ƴar uwan nata, "na'am ya uncle Shureim?" Tace murmushi ɗauke a saman fuskanta, murmushi ta saki tare da kallon Shureim dake zaune kusa da ita tare da faɗin "gashi nan" "ohmalam Ango idonka kenan?" Tace tare da sakin dariya, murmushi Hishamya saki tare da faɗin"ya zama kayi-kayi-kayi-kayi Alhaji kayi sabuwan amarya" dariya suka saki gaba ɗayansuMairahda ba ta san dalilin dariyan ba na taya su, dariya Hisham ya saki tare da bin yanda take dariyanda ido, se tayi kama da Insu sak....
"Shikenan kun hana shi magana" Yasmin da Shureim ya miƙa mata wayan saboda dauriyandayasarƙe shi tace tare da sakin murmushi, "be da na faɗa dai daga aure ya manta da ƴan uwanshi"
Insu tace tare da sakin murmushi, "to ayi haƙuri ze neme su" Yasmin tace a natse, "da ya kyauta" tace tare da sakin murmushi, "ya Nafisat da Mairah?" Tace a natse, "tana school se 3 za sudawo, Mairah kuma ga ta tana cin indomie" tace tare da gyara zama, "a shafamun kanta da kyau, acemata Umma tace Allah ya mata albarka" murmushi ta saki tare da faɗin "in ban manta ba"
"nauyin na kan ki" tace tare da sakin murmushi....
Murmushi ita ma ta saki idonta akan Mairah dake ta amsa indomie, "ya zanga-zangan a tanan?" Tace tare da gyara zama, dariya ta saki me yalwa tare da faɗin "wallahi ban san ma ana yi baseyanzu, fitowan mu daga class kenan mu ka yi sallah mu ka zo cin abinci Labib ya kawo manabatun" "lallai a gaidaku dan ba ku hau media ba ne amma tun daren jiya suka fara ai, se dai naji
me magana da yawun shugan ƙasa ya fito yayi bayani akan yana lafiya cikin aminci su yi haƙuri
su dakatar da zanga-zangan nan ba da daɗewa ba ze fara fita office" ta idda maganan a natse, "sun kashe kan su" Insu tace tare da gyara zaman wayan, "meyasa ki ka ce haka?" Ta je fa matatambayan a natse, "sunce yana lafiya, sannna kuma sun ce kwanan nan ze fara fita office meyahaɗa zantukan biyu a waje guda? Sun ba da ƙofan zargi ai, duk wani me hankali ba ze yardadabatun ba" "oh Allah yanzu se yaya kenan!" Tace da damuwa, "se ya bayyana ya musu maganadabakin shi inba haka ba za'ayi uwar watsi" "na ga alamun hakan wallahi, duk wanda ya fitomagana a media uzzira abun yake ba neman sassautawa ba" "Allah ya kyauta ban duba ba, inaschool yanzu zamu koma class ma" "karfe nawa za ku fito 4 ne in sha Allah" tace a natse, "toAllah ya kare ku ya maidaku gida lafiya, ku yi ta addu'a, ni dama kin zauna anan mu ji yandaabinze kaya" ta idda maganan cike da damuwa, murmushi ta saki tare da faɗin "ba abinda ze farusewanda Allah ya ƙaddara ki kwantar da hankalin ki, bari in ci abinci, kowa dai na gida ko?" "EhseFarisat ta na wajen aiki" murmushi ta saki tare da faɗin "kasuwan su ne ya buɗe" murmushi tasaki tare da faɗin "se Allah" murmurshi ta saki tare da sauke wayan ta katse kiran ta ajiyeagefenta.... Gyara zama tayi ta fara cin faten dankalin turawan da Nachma ta sa aka wo mata, miƙa hannuMairah tayi da niyyan ɗaukan wayan saurin janyewa Labib yayi tare da faɗin "rufa mana asiri
daughter kuɗin shi da yawa" kwaɓe fuska tayi tare da kallon shi, murmushi Hishamya saki tareda faɗin "ba ta ba zata yar ba" ba musu ya miƙa mata tare da faɗin "yaran zamani wato tunkinaƴar hakan ki kin iya riƙe waya" "Abie" tace tare da miƙa ma Insu wayan, amsa tayi ta ajiyeagefenta tare da cigaba da cin abincinta, kuka ta saki da ƙarfi tare da faɗin "Abie" "me takeso?" Hisham yace cike da damuwa, "duka" tace ba tare da ta kalleshi ba "sorry Mairah Ammi neko?" Yace tare da ɗaukan ta ya saɓa a kafaɗa ya miƙe tare da fara rarrashinta, jinjina mai kandabayagani tayi idonta akan Insu....
"Abie!" Tace da ƙarfi cikin muryanta na yara idon ta akan tvn da ake nuna hotunan SSB, ɗagota
Hisham yayi da mamaki, ganin yanda murmushi ya mamaye fuskanta ya sa shi sakin murmushi
tare da faɗin "Allah ya shiryeki Mairah" murmushi Insu ta saki tare da ƙara ƙaimi wajencinabincin kaman ba ta san me suke yi ba.... Ɗaukan ruwa tayi ta kai baki a natse tana sauke cup ɗin ta zari tissue tare da faɗin "ya akayi
Khalim ya dawo class ɗin mu?" Ta idda tambayan idon ta akan Nachma, "dole nan ze dawoai, kinmanta na faɗa miki wannan shine ƙarshen damarshi a Insoul?" Jinjina mata kai tayi tare dafaɗin"jiya ban ganshi a class ɗin ba ne shiyasa yau na yi mamaki, "ba ko wani lokaci yake shigowabakin san senior ne" tace tare da sakin murmushi, murmushi ta saki tare da jan kujera ta miƙe"zaku shiga class yanzu ko?" Tace tare da kallon Labib, jinjina mata kai yayi tare da kallonHisham, "zamu tafi da ita class" yace tare da kallon ta, jinjina mai kai tayi ta gyara zamanjakatafice Nachma ta dafa mata baya...
"Daddy wallahi kashe mu za su yi" Jabiida tace cikin rishin kuka a matuƙar firgice, juyowaformerpresident yayi a fusace ya kai ma bakinta bugu duƙewa tayi tare da fashewa da wani razanannankuka, riƙota Mommy tayi tare da kallon shi cike da takaici tace "ya isa haka, me ta maka itakumada zaka sauke haukan borin kunyarka akanta, kar ka ƙara bugun mun yarinya haka, lokacindakuke aikata tsiyatakun ku ba ta da labari" ta idda maganan tare da janye Jabiida ta nufi cikinparlorn da ita, bin ta da ido yayi cike da zallan mamaki, dan yasan a duk wani abu da yayi tanadakaso mafi tsoka a ciki sannan yau saboda tana son kwaɓe mai ta zare jikinta ta bar shi a ciki.... Ƙaran rurin wayarshi dake hannun shi ya sa shi ɗauke ido da ga kanta da azama ya ɗaga kiranyakara a kunni ba tare da ya lura da wanda yayi kiran ba, "za su ka she mu, na ce muku kasheni ni
da iyalaina za su yi su binne mu a cikin gidan nan in ba ku kawo mana agaji ba, jami'an da sukegidan nan ba za su iya tare su ba, suna yo kan su na mu ta ƙare" ya idda maganan tare da sharezufan da ya tsatstsafo mai, tsaki Mommy dake bin shi da ido ta saki tare da kauda kai....
"Ka na jina?" Aka ce daga ta can ɓangaren, "eh, yes in jinka yallaɓai" yace baki na ɓari, "tunasali
se da na faɗa maka saurin yanke hukunci ze iya haifar maka da babban kuskure, a yanzuyandamatasan nan suka ta so wa ya isa tsaidasu daga cin ma ƙudirinsu, ba ma da wani temakodazamuiya maka a wannan yanayin, ba kai ɗaya ke cikin tashin hankali ba gaba ɗayan mu muna ciki, SSBkaɗai ze iya fiddamu a wannan hali shima se ya fito yayi magana jama'an ƙasa sun tabbatar dalafiyarshi inba haka ba, muna cikin babban matsala, ba vice president ya tabbatar da ba shi amotan ba?" "Eh eh!" Yace da sauri....
"To ya aka yi yanzu batun yana ciki ya fito?" "Wallahi yallaɓai ban sani ba, su ma waƴandasukayi
aikin sun tabbatar mun da ba ya ciki" yayi maganan a rikice, "se mi jira abinda Allah ze yi, sannanga shawara zan baka ka tsananta addu'a ya fito yayi magana kafin lokacin da suka ba da nasanganin jawabin shi ya cika sannan in Allah yasa ka sha ka tattara kayanta ka bar ƙasan danzakafi
rayuwar inganci a wajen ƙasa saboda jama'a sun san kai ka kasa aka kai wannna harin" yanakai
nan ya katse kiran, da mamaki ya ciro wayan tare da bin shi da ido....
Jiyo hayaniyan matasa dake zagaye da gidan suna kuwwa ya sa cikin shi kartawa, da sauri yayi
bedroom ɗin shi jin zawayin da ya tsarga mai na gab da fitowa, da ido Jabiida da Mommy sukabi
shi na su zuciyoyin na tsananta bugu dan sun fahimci ba mafita se abinda Allah yayi....
"Lokaci ya cika" matashiyar budurwan da ta leƙo cikin office ɗin Farisat tace tare da kallontafuska cike da murmushi, murmushi ta sakin mata tare da jinjina mata kai, ficewa tayi taredafaɗin "ki hanzarta" miƙewa tayi a natse ta ɗau takardun da ke gabanta ta fice a natse, ɗakinmake up ta wuce kai tsaye, gyara mata fuska suka hi hanzarce ta fito ta nufi ɗakin gabatar dashirye-shirye, "yawwa bismillah" dattijan mata biyu dake tsaye a gefe suka ce mata tare dasakinmata murmushi, murmushi ta sakin musu ta wuce inda aka tanada dan zamanta....
Tana zama ta ajiye takardun hannunta tare da gyara zamanta a natse, se da suka gama gabatarda duk wani al'ada kafin su dasa mata camera ɗago kai tayi fuska ɗauke da murmushinta kamarko yaushe tare da faɗin "Assalamu alaikum jama'an ƙasata barkan mu da yau barkan mudasakesaduwa da ku a cikin wannan shirin na ku da ku ke matuƙar so da ƙauna watooo (meke faruwaaƙasata) shirin me ke faruwa a ƙasata shiri ne da ke kurɗawa saƙo da lungu birane da
ƙauyakubdan fiddo muku da abinda ke faruwa a ƙasarmu ta gado, yau ma kamar ko yausheshirin yayi mana babban kan mu ku kasance tare da Ni Farisat Abdussamad Umar wacce zatajaragaman shirin kamar ko yaushe" tana kai nan aka ɗauke mata camera na minti guda, jinjinamata hannu suka yi alamun aiki na kyau.... Ana dawo da Camera ta kuma gyara zama tare da faɗin "kamar yanda al'adan shirin na muyakebe canza zani ba yau ma yayi nitso ya cafko muku baƙi biyu dan tattaunawa da su akan abindakefaruwa a ƙasata a ƙasarka da ƙasarki, jama'a ku zo mu taru mu yi musu barka da zuwa" ta iddamaganan tare da miƙewa tsaye ta fara tafi idonta akan mutane biyun da suka shigo fuskacikedamurmushi, murmushi suka sakin mata cike da burgewa, "bismillah" tace tare da nuna musuwajen zama, ba musu suka zazzauna, zama tayi tare da faɗin "barkan ku da shigowa cikinshirinmeke faruwa a ƙasata" "barkan mu dai Malama Farisat" suka ce fuskoki cike da murmushi, murmushi ta saki tare da faɗin "bari mu faɗa cikin shirin na mu kai tsaye, da fatan baƙinnamusun shirya?" "In sha Allah" suka ce baku na a haɗe....
"Bari in fara da kai Baba zamu iya cewa kun ga shekaran jiya da jiya ga ku a yau a na damawadaku muna kuma muku fatan gobe a dama da ku in sha Allah" murmushi ya saki tare da faɗin"insha Allah" tare da gyara zama,....
"A safiyan yau muka tashi da wani babban lamari Baba, dole mu kira shi da babban lamari dubada abun ya daɗe be faru ba tun bayan ba wa ƙasarmu ƴancin kai da turawan Burtaniya sukayi awan can lokacin, kwatsam se ga shi a safiyan yau mun tashi da shi" jinjina kai yayi cike da
gamsuwa, "zanga-zangan lumana matasan ƙasa suka tashi da shi akan san sani da jimhalindame girma shugaban ƙasa Sahabee Sadam Ɓadamayya ke ciki, saboda wasu zantuka da akayaɗa
daga jiya zuwa wayewan garin yau media, matasan sun yi ikirarin in ba'a bayyana musu asalinhalin da shugaban ƙasar ke ciki ba za'ayi gagarumin tashin hankalin da zamu iya cewa Allahyakare faruwan hakan, shin Baba kana ganin wannan zanga-zangan da matasa suka fito ya yi dai-dai da tsarin doka ta ƙasa? dubabda ba wani dalili a bayyane wanda ze sa su fiton" ta iddamaganan a natse idonta akanshi.... Nagartaccen murmushi ya saki tare da faɗin "malama Farisat su ke da dalili na fitowa kuwa, sannan zanga-zangan da suka fito ya isa tabbatar ma ƴan ƙasa da kasantuwarsu ƴan ƙasamasuhalarci, abinda suka fito nema wa shugaban mu shi kan shi halarci ne ɗan halak shi yasanhalarci
malama Farisat, kuma ina basu cikakken goyan baya na, abinda suka fito sani ai ba wani mewuya ba ne, in har an tabbatar da lafiyan me girma shugaban ƙasa ƙalau take ina ganinwannanabun me sauƙi ne ya fito ko sallama ya musu shikenan komai ya wuce, amma matuƙar za sunema a kasa ba su cikakken amsa to kinga abinda suke zargi ya tabbata, sannan zamu sakezaburar da su akan su nema ma mutumin da ya zame musu garkuwa bango jingina inuwar fakega raɗaɗin afin rana adalci" ya idda maganan a natse... Murmushi ta saki tare da faɗin "da alama Baba ya dau zafi da yawa bari in juyo gare ka MalamIshaq Isa me za ka iya cewa akan abinda ke faruwa a ƙasata?" Gyara zama yayi kaɗan taredafaɗin "abinda ke faruwa dama shi yakamata ya faru tun kusan shekaru biyu da suka wuce, mundanne zuciyoyinmu matsayin mu na ƴan ƙasa na gari dan kar mu ta da tashin tashina a cemanaba ma son zama lafiya"....
"Abu ne a bayyane, ba su ɓoye ba, mutanen nan in muka musu sanya cutan mu za suyi, tundabawan Allahn nan ya hau kujeran mulkin ƙasar nan ba mu jin wani ya ƙara saka shi a ido ba, sedai Alhamdulillah ayyukan shi na isko mu, to muna son ganin baya goya marayu da ma suuba, hari kusan so biyu a ka kai mai na farko ɗiyar shi ina ce har se da aka bar da ita ƙasan nangudunkar su cutar da ita, zamu fito aka danne mu muka dannu, na biyu shi da kanshi akan hanyarshi nazuwa wannan gari na mu, se aka ɓoye mana dan an san zamu magantu in aka bayyana, namahaifiyarshi aka bayyana mana kawaialama Farisat ki duba wannan abun da kyau inba rami me
ya kawo maganan rami, sannan jiya se ga maganan ya farfaɗo ya fito kenan kinga duk tsayinkwanakin nan da aka kai mai harin yana cikin mawuyacin hali ne wanda ba za'a iya sanarwaƴankasa ba....
Zanga-zanga yanzu muka fara ba kuma ba zamu daina ba se mun idda manufar mu, danmukayi
sake mutanen nan naƙasamu za su yi su cigaba da juya mu kaman yanda suka saba, munsamumun sha daƙyar a hannun su, da roƙon Ubangiji da haɗa kai da muka yi wajen dannawa nagari
ƙuri'unmu sannan saboda ba arziƙi ne da su ba su ce za su naƙasa mana goben mu to wallahi iname magana da babbban murya zanga-zanga ba gudu ba ja da baya, kuma sani munsan sukamaryanda matasa ke faɗa, Allah yasa muji wani batu wanda be mana ba za su sha mamaki ai munƙuna yanzu" ya idda maganan a kausashe.....
"To ma su bibiyan wannan shirin na mu baƙin nawa duka ba sauƙi in yanzu ka iso ga akwatintalabijin ɗinka muna tattaunawane akan zanga-zangan da matasan ƙasa suka fito dan nemamame girma shugaban ƙasa adalci daga hare-haren da ake kai mishi shi da iyalan shi, bari mujeni
da baƙina mu ji abinda me girma governorn jahar Bertuwa yace dangane da zanga-zangandamatasar garin shi suka fito kar ku matsa muna dawowa".....
"A matsayina na shugaba ga al'umman wannna jaha ta Bertuwa ɗa kuma ga wannan ƙasataƁadamayo ina me ba wa matasan jahata goyon baya akan zanga-zangan lumana da suka fitodannemawa uban wannan ƙasa adalci, zanga-zangan lumana zaku fita banda cin zarafin ƴanuwawaƴanda suka fito neman na kansu, duk wanda aka kama da cin zarafi ko shirin tashin zaunetsaye zamu kama shi sannan ze fuskanci hukunci dai-dai da abinda ya aikata, sannan ba zamusaka shi cikin ɗaya daga cikin waƴanda suka fito nemawa shuganmu adalci ba" ana kai nanakaɗauke fuskashi, juyo da fuskanta tayi gare su tare da faɗin "bari in dawo kan ka Baba, kaji abindame girma governor yace, shin me girma governor ya aikata abinda ya dace ko ya yi san rai kamaryanda wasu daga cikin al'umman ƙasa suke faɗa?"....
"Ai Malam Farisat cikin kalaman me girma gwamna babu wacce ke nuni da san rai ko zuciyaaciki, abu ne wanda ya dace a ce ko wani governor ya yi, Alhamdulillah kuma mun jinjina mishi
sannan kima da darajan shi ya daɗa ƙaruwa a idanunmu, duk da daga baya na ji ance saurangovernor's ɗin dake arewaci sun ba wa na su al'umman goyan baya, amma za mu ce governor
Sharifudden Muhammad shi ya fara buɗe musu ƙofa, Allah ya saka mishi da alheri wallahi muntabbatar da adalcin shi a gare mu mu ƴan jahar Bertuwa" ya idda maganan cike da alfahari....
"Am abinda ze baki mamaki malama Farisat ko da ya ba da goyan baya akan a fita be bar mukarazube ba, jami'an tsaro na tare da mu sannan ruwa da abinci be yanke mana ba" Ishaq Isa yacetare da gyara zama, "ma sha Allah lallai governor Sharifudden Muhammad zamu iya cewayanunawa duniya yana tare da al'umman shi" Farisat tace fuska cike da murmushi, "wannanhakayake Malama Farisat, dama shi shugaba haka yakamata ya zamto" Baba yace tare da jinjinakai, "to bari mu leƙa wajen zanga-zanga dan muji zantawan da wakilanmu suka yi da waƴannanmatasa"....
"Ya sunan malamin?" "Sunana Aliyu Muhammad" "malam Aliyu a wani jaha ka ke?" "Kautal" "tomalam Aliyu ga ka mun sameka a wajen taron zanga-zanga shin me ya fito da kai wannanzanga-zangan?" "Na fito nema ma shugabana adalci ne akan bi ta da ƙullin da wasu ƴaƴan iska kebinshi da shi" yayi maganan a fusace, "to malam Aliyu shin kana ganin kwalliya zata bi ya kuɗinsabulu kuwa?" "Dole, ai wallahi dole kyaɗa tayi mai in taƙi tasha matsa, dole su fito su bayyanamana halin da adalin shugabanmu ke ciki in ba haka ba muna nan a nan babu gudu babj jadabaya" "to malam Aliyu mun gode" "ni ke da godiya, a haskani duniya ta ganni, ni ne nan AliyuɗanKautal, duk mun san ku mun san mazaunin ku, wallahi se mun bi ku ɗaya bayan ɗaya munaikatamuku aika-aika ku dai jira mu ji saɓanin abinda muke san ji, dalilin wannan bawan Allahnyaunamallaki gida na mallaki abin hawa na daina galantoyin bin majalisu ina kashe wando" ....
"Assalamu alaikum ya sunan malamin?" "Sunana Isma'il Shehu" "malam Isma'il a wani gari kake?" "Yarban" "shin zaka iya faɗa mana me ya fito da kai zanga-zanga yau?" "Sosai kuwa" yace
tare da kafe camera da ido, "muna jinka" "yawwa na fito ne dan san sanin abinda ke faruwadajarumina wato shugaban ƙasata Sahabee Sadam Ɓadamayya, dan munji labari akan harindatsinannun nan suka kai ya same shi ɓoye mana aike, mun fito sanin tabbaci, in yana lafiyaabayyana mana shi mu gan shi in kuma abinda muka ji ya tabbata hmm-hmm-hmm, wallahi jikinkowa se ya faɗa masa gobe in an ce su ƙara gigin taɓa farcen ƙaramin yatsan shi ba za sukumaba" murmushi me ɗaukan rahoton ya saki tare da faɗin "me magana da yawun shugabanƙasayafito ya sanar da lafiyarshi shin hakan be gamsar da ku ba ne?" "Rabu da waƴan nan duk
maƙaryata ne, mu ba faɗa muka fito ba dalilin da yasa ku ka taddamu zaune waje guda kenan, zanga-zangan lumana muka fito yi, amma matuƙar lokacin da muka ba da ya cika ba muji abindamuke san ji ba, ba zan iya ce muku ga abinda zamu iya yi ba, muke danne wasu akan kar sutadatarzoma, amma matuƙar ba mu samu abinda muke so ba mu da kan mu zamu shiga a yi damu, mun fa san su ba wai ba mu san su ba ne" "to Allah ya cika muku burin ku" "amen".... Comments fans🥰🙏
🫀MUGUWAR TSOKA 🫀
{🫀TA'ARE KALLUƊE}
[Muscle Cramp🫀]
) عضلة سيئة (
🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
written and Created ~~~~~~~~~~~~~~ ِبسم الله الرحمن الرحيم
By
Yardajjiya👩 💻
Page. Fifty
"Sunana Kamalu Ƙasim daga jahar Bertuwa" "malam Kamalu me ya fiddoka wannan waje?" "Auf
ka ji ka da wani magana dan Allah malam ɗan jarida, zanga-zanga mana, zanga-zanga na fitodanneman adalci ga shugabana me ƙauna na da ƙaunar cigaba na mana" "ma sha Allah malamKamalu shin baka ganin abinda ku ke buƙata ze iya wiya ku samu a wannan ƙanƙanin lokacinduba da me girma shugaban ƙasa ze iya haɗa shekaru biyu ba wanda ya ji ɗuriyar shi" "ahkai nedai ba ka ji ɗuriyarshi ba, amma mu munji, da ma ka ce mun ba wanda ya ƙara ganin shi ne, amma ɗuriyarshi kam muna ji, tunda ayyukan da yake shinfiɗawa na iso mu" "haka ne" "toyakasance ko kar ya kasance malam ɗan jarida tunaninka ne, mu dai gamu mun fito, kuma munanan a wajen nan har se lokacin da aka bamu ya cika....
Se dai fa zamu aikata aika-aikan da tunani be hasaso ba matuƙar ba mu ji gamsashshenamsaba, dan mun gaji da wannan rainin hankalin da wayon da suke mana, banda ma daƙiƙanci kuhari ƴarshi ya muku shiru sannan ku koma ku hare shi, wanda ma fa muka ji kenan, wataƙila wandakunnuwan mu ba su ji ba da yawa, to mun ɓara, kuma mun yunƙuro, duk wanda ya fasa ƙoƙarincutar da shi a cikin su be haifu ba...
Za mu nuna muku ba tsoro ya samu ajiye makaman yaƙin mu ba, isa da mu da aka yi ne yasamuka ajiye, kuma waƴanda suka isan sun ce mu zaro mu ɗauke kawunan ku sheɗanu" ya iddamaganan kaman ze shige cameran, sauri kaudawa suka yi dan ganin yanda matasan gefesukazaburo....
"Assalamu alaikum ma su kallo da saurare Zainab Kabir ke tare da ku a cikin shirin rahotanninmu, gani a garin Ɓadamayya inda na yo muku kamun wanda ya fara posting ɗin halin da megirma shugan ƙasa ke ciki, ku kasance tare da ni dan ganin yanda zantawan damu ze kasance, Assalamu alaikum ya sunan malamin?" Tace tare da kara ma cika aiki microphone ɗin hannunta, "Shagari nake cika aiki ba" yace idon shi akan Camera, "ma sha Allah malamShagari kai nemutum na farko da aka tabbatar da ka fara wallafa batu akan harin nan da aka kai har shugabanƙasa ya shafa shin zamu iya sanin cikakken masaniya daga bakin ka?" ....
"Ƙwarai kuwa, mahaifiyata a gidan shi take aiki tun kafin Allah ya ba shi shugancin nan, kodasuka koma can tare da ita aka koma saboda yalwatuwan adalcin shi, kuma ita ta sanar dani
farfaɗowan shi a daren jiya" "kenan ba ya ma cikin hayyacin shi tsayin wannan kwanaki?"
"Wannan haka yake, se jiya ya farfaɗo" ihu matasan wajen suka saki tare da zage-zage....
"Kuma duk mun san su waye ke aikatawa, wallahi matuƙar wani abu ya same shi duk se munɗauke su ɗaya bayan ɗaya, shegu waƴanda ba su san kowa ba se kawunan su, kun jamua jiki kuncuci rayuwar mu kun bar iyayen mu da kuka da haɗiyan baƙin ciki, kun inganta rayuwar ƴaƴanku, shi ya fito ya ce hakan be dace ba ya rungume mu yace mu ma ƴaƴane ababen alfahari gaiyayenmu sannan ku ce za ku cuta mishi to wallahi mu na nan akan bakanmu se mun idda
manufar mu, harin ma ba yanzu suka fara kai mai ba, kusan uku kenan duk da wannan, akwai
wanda suka so kashe shi suka saka mai poison a shayi da ƙyar aka ceto rayuwar shi, duk munadalabari muna nan tafe zaku ci gidanku, ku jira lokaci ya cika" ya idda maganan a kausashe, ihumatasan kusa da shi suka saki tare da shigewa cikin camera suna jaddada abinda za su aikata.... Numfashi me ƙarfi Farisat ta saki tare da faɗin "kai na ya ɗaure akan wannan lamarin" "ai
malama Farisat kwanciyar hankalin kowa shine a fito a bayyana ma ƴan ƙasa halin da ubanƙasake ciki" Ishaq Isa yace tare da sakin murmushi, "shikenan" Baba yace tare da ɗaga hannu, "tomalam Ishaq ka na ganin fitowa a bayyana abu saɓanin wanda suke san ji ze haifar da ɗa meidokuwa?" "Wallahi makaho za'a haifa malama Farisat abinda suka shuka za su girba, sun aikataabinda ransu ke so za su ga abinda ba sa son gani dan ko ni banyi alƙawarin zan bar batunba" .... Murmushi ta saki tare da faɗin "bari in dawo kan ka Baba, na ga alamu malamIshaq yana sonƙara rura wutan abun ne, Baba kasan duk lokacin da abu irin wannan ya taso, akwai ƴantadazaune tsaye dake gefe suna jiran irin wannan dama su shiga ciki su aikata abinda ransu keso, inan tashi magana se ka ji ana kuɗin goro, shin in matasa suka ji saɓanin abinda suke sonji yakakeganin wannan ƙasa zata kasance?" "Cikin aminci malama Farisat, za su tsaftace mana ƙasanesutattara duk wata sharan da aka zuba mana a ciki su zubda a wajen ƙasa, in kuma aka kamawani
da aikata ma ɗaya daga cikin ƴan ƙasa wani abu na daban to wannan mun san ɗaya ne dagacikinsu, za mu sa matasan mu su haɗa da shi dan shima ya zama datti".. Ya idda maganan cike da kamalan shi, murmushi ta saki tare da faɗin "wani shawara zakabawamatasan wannan ƙasa musamman waƴanda ke cikin wannan yaƙi tsundum" "to ƴaƴana ƙanninaƴan uwana ku sani neman ƴancin
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 78 Chapter of 109