me matuƙar farinciki, sannan ina me sanar da jama'iyya cewa zan zamo cikakken ɗa na gari me biyayya gareta" yanakai nan ya janye jiki a natse, banda ruwan tafi babu abinda ke tashi a wajen, sauri ajiye takardanda ya amso me magana da yawun shugaban ƙasa yayi tare da fadin "bismillah" ba musuyaɗaupen dake gefen takardan ya saka hannu tare da ja gefe...
"Bismillah ranka ya daɗe police ɗin da suka hayo dan sauka da shi suka ce cike da girmamawa, ba musu ya taka ya riƙo hannun Insu dake tsaye tana bin yanda jama'a ke tafi da ido suka saukaanatse, "ma sha Allah, muna farin ciki da ba mu haɗin kan da ƴaƴan jam'iyya suka yi, sannanmuna godiya da yallaɓai ya amince da shigowa cikin wannan jam'iyya da amsan tayin da ta mishi, 24ga wannan wata da muke ciki in sha Allah za'a gabatar da primary election" yana kai nanyabarwajen da sauri ya nufi mr president, duƙawa kusa da shi yayi sosai, da alamun magana ya mai, miƙewa yayi a hanzarce tare da kallon Chief security, saurin ƙarisa inda yake yayi a ladabce, maganan sakanni ya mai ya jinjina kai ya bar wajen da sauri....
"Uncle dubi" tace tare miƙa mai wayan hannunta, amsa yayi a natse ya kai ido kai, hotunandataɗaukeshi ya na bayani ne, miƙa mata wayan yayi tare da kallon jami'an tsaron da suka zomusuiso wajen lunch ɗin da aka shirya musu, ba musu suka mimmiƙe, riƙo leɓatun hannun riganshi
tayi tare da bin takun shi, suna shiga suka tadda iyalan mr president zazzaune da alamunshigowan su suke jira, da sauri suka mimmiƙe, mazan suka bawa su SSB hannu yayinda matan
suka nufi su Hajiya gadan-gadan kamar wanda suka san juna, "please bismillah ku ƙariso" wani
me zubi da president yace tare da nuna musu wajen zama, ba musu suka karisa suka zazzauna, murmushi Jabiida ta sakin ma Insu dake kusa da SSB tare da miƙa mata hannu a natse, "Jabiida" murmushi ta saki ta miƙa na ta cike da yanayinta tace "Insu" "wow nice name" "kamar na ki" tacetare da sakin murmushi, "oh Jabiida kar ki dameta mana" Momy tace tare da sakin murmushi...
"Ita ma ba da ga nan ba" Alhaji Jamil yace tare da sakin murmushi, "uncle Jamil!" Tace kamanzata tsaga ihu, murmurshi suka saki tare da bin ta da ido, "auf na manta ba fa ita ba ne, me kamadaita ne" yace tare da kauda kai, dariya suka saki tare da bin su da ido, shigowan Mr president yasasu barin wannan zancen aka fara sabon gaisuwa, "please ku mu isa dining room" Mommy tacetare da bin su da ido, ba wacce taƙi, dan dama gayyatan da aka musu kenan, suna zama Jabiidatamiƙe ta fara zuba ma SSB, murmurshi Hajiya ta saki cike da yabawa da hankalinta tare dafaɗin"da kin barshi ba ga masu zubawa nan na aikin su ba" "zan taya su ne" tace a girmame, murmushi
ta saki tare da kauda batun....
Tana gama saka mishi ta nufi gaban Insu, murmurshi ta sakin mata tare da faɗin "I'mokaythankyou" kallonta Mommy tayi da tsan-tsan kulawa tare da faɗin "ci ko kaɗan ne daughter" murmurshi ta saki tare da faɗin, "ban jima da lunch ba nagode" "okay ko a kawo miki snacks?" Tace da kulawa, jiniina kai tayi tare da sakin murmushi,....
Suna gama tsatstsakura suka tarkato suka dawo cikin parlorn, dan ba wanda yaci sama dacokali
uku, nan suka yi ta ƙoƙarin jan su da hira, su Lubabatu an saki jiki ana ta kwasan hira babuwani
rashin sabo, banda bin su da ido ba abinda Insu ke yi dan ba ta za ta haka suke da sakewa bakallon Jabir SSB yayi tare da kauda kai, gyara zama yayi tare da faɗin "ina ga zamu wuce 6tayi"
"haba tun yanzu?" Momy tace cike da jin ba daɗi, murmushi ya saki tare da faɗin "abubuwadayawa mu ka soke dan amsa gayyata, a mana afwa" murmushi mr president ya saki tare dafaɗin"to mun gode da amsa gayyata" murmushi suka saki tare da fara miƙewa....
"A natse suka fito tare da rakiyan iyalan mr president gaba ɗaya, suna tsaye suna sallamama'aikata suka fito rirriƙe da gifs suka sassaka a mota, ganin suna tsaye ana ta sallama yasaInsu wuce wa gefen Ibrahim cike da gajiyawa tace "Abban Iman ina wan can wayan to?" "Najefar" yace tare da kallon ta, "Allah baka haƙuri" tace tare da juyawa ta bar wajen, murmushi yasaki tare da nufar motan da ya zo a ciki ganin sun fara shishshiga mota....
Comments fans🙏🥰
🫀MUGUWAR TSOKA 🫀
{🫀TA'ARE KALLUƊE}
[Muscle Cramp🫀]
) عضلة سيئة (
🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
ِبسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~ Created and written
By
Yardajjiya👩 💻
Page. Twenty seven
Murmushi Farisat da Yasmin suka saki tare da kallon Salman dake bin su da ido cikin serious, "me ne ne?" Yace tare da gyara zama a saman ɗaya daga jikin chair's ɗin dake gefen parkinglot, "Babu komai" Farisat tace tare da kauda kai, "ba na so" yace tare da kauda kai, danne dariyar
dake ta so mata Yasmin tayi tare da faɗin "yanzu dan Allah kai Yaya Salman aka ce maka afarashirye-shirye yanzu se ka yarda? Yau-yau fa aka tsaida lokacin" ....
"Ina ce bakwa ce ba, duk ya bi ya rikice kamar wani ze ƙwace mai ita" Usman dake zaune tagefenhagun Salman yace idon shi akan wayan hannun shi, "Yasmin ai gunda mu tsara komai kafingabatowan lokacin, kaman yau ne zaki ga lokacin ya zo, duk abinda aka tsaida mai da ranakanzoya wuce" Salman yace cike da son fahimtar da ita, "haka ne, ka fi mu gaskiya kuma" tace taredasakin murmushi tare da bi shi da ido, "yawwa daɗi na dake saurin fahimta" murmushi Farisat tasaki tare da faɗin "se ku tsara da ita, dan ni dai ba dani za'ayi wannan ba" "dama ba mu buƙaceki
ba" yace tare da banka mata harara ya juya fuska ga Yasmin dake tiƙan dariya...
"Yasmin dame-dame ki ke ganin za'a yi?" Yace cike da son sani, murmurshi ta saki tare dagyarazama, "ina ganin mu fara fidda event's" tace a natse, "kin kawo shawara ina jinki" yace tareda
miƙa mata dukkanin attention ɗin shi, "kar fa a cika event's, dan Aminan juna ma za su yi" taceidonta akan Yasmin, "rabu da ita, na su da ban damu daban" yace na shi idon akan Yasmin, murmushi ta saki tare da jinjina kai, "wai dama SSB yana cikin ƴan takarar president ne?" Usmanyace tare da ɗago kai ya kalli Salman.... Da mamaki ya kalleshi tare da faɗin "haba!" "Oh Allah ina tambayanka kana tambaya na?" Yacetare da ƙureshi da ido, "to ban sani ba ne ai, a bakin ka nake ji yanzu, a ina aka sanar?" Salmanyace tare da juya duban shi gare shi gaba ɗaya...
"Gashi nan CStv ta sanar ta media, kuma kasan ba sa sanar da ƙaryan kurege, koman susesuntabbatar da ingancin shi suke sanarwa" "haka ne, amma wallahi da ƙasan nan mun washe, Allahyasa da gaske ne" Salman yace cike da farin ciki, "gaskiya kam, wallahi zan so hakan ya tabbata, amma mugayen nan ba yarda za su yi ba, tun a primary election za su ɓarar da shi, sun fi sonci
cigaba da musgunama takala suna kishingiɗe a parlor suna kallon yanda yake jigatuwa tatv" Usman yace cike da takaici....
"Haba akwai Allah, in sun fi ƙarfin mu ba su fi ƙarfin mahaliccin mu ba, zamu yi ta kai kukanmugare shi, in sha Allah se ya hau, kai ban da abun ka ma Usman kana ganin al'umma za suyardane, ai wallahi za su tada ƙasan nan kuwa, mutumin nan ka san wai jama'an dake gare shi kuwa?Kayi
shiru kawai suma ba za su fara ba, na faɗa maka ko valot paper's ɗin ƴan Bertuwa ka ɗai yasamuze haye, kasan ba inda ya kai garin nan yawan jama'a a ƙasan nan, sannan kuma ka na da sani
akan yanda suke mugun yin shi, dan ka sheda tasirin shi a gare su" Salman ya idda maganancikeda tsan-tsan jin daɗi "haka ne, Allah ya ba shi, a gaskiya da mun tabbatar da gatan mu
matsayinmu na cikakkun ƴan ƙasa masu cikakken ƴanci" "in sha Allah ze ci, dan na san yanzutalakawan ƙasa sun duƙufa" "harda ma su arziƙin ma, ai uban su a ƴan canji ne ya fito" Usmanyace tare da sakin dariya....
"Ku tsaya, wai akan wa ku ke magana ne!" Farisat tace cike da tsan-tsan mamaki idonta ƙyamakansu, "SSB mana" Salman yace ba tare da damuwar komai ba, "wai kana nufin Uncle ne yafitoneman shugaban ƙasan ƙasar nan!" Farisat tace da zallan mamaki, "Uncle!" yace shima damamaki, ƙarisowa wajen Nafisat tayi a guje tare da faɗin "ku zo ku gani, ana nuno Uncle daAntyInsu a tv, wai Uncle na neman kujeran president ɗin ƙasar nan" tayi maganan tare da sakinnumfarfashi.... Da sauri suka tashi suka yi ciki, dafa musu baya Usman da Salman suka yi da mamaki, sunashigaparlor suka tadda an hasko fuskan Insu lokacin da SSB ya saki hannunta ya wuce dan jawabi, idobuɗe suke ƙare mata kallo, "na sha mamaki" Babiya tace cike da ta'ajibi, "Allah me iko" Habibatace tare da kallon Sadam da idon shi ƙyam ke kan tv.... Murmushi Yaya da Nafisat ta kira ya saki tare da juyawa ya koma side ɗin shi, "dama wannanneƴar SSB?" Usman yace tare da nuna ma Salman wayan shi, "ƴa kuma!" Yace da zallan mamaki, bayanin da ake yi a tvn ya sa su maida dukkanin hankulan su kai, tsaki Babiya ta saki taredafaɗin "mutane da ɗaukan ɗumi suke, yanzu waye ya zayyano wannan jawabin haka?" DariyasuFarisat suka saki cike da farin ciki tare da kallon ta, miƙa ma Usman wayan shi Salman yayi jiki amace, juyawa yayi ya fice Yasmin da Sadam suka mara mai baya.... Muje" Farisat tace tare da kallon shi fuska yalwace da murmushi, "dama Anty tana da alaƙadaSSB ne?" Yace idon shi ƙyam akanta, murmushi ta saki tare da faɗin "brothernta ne" "wow!" yacea hankali, "a can Insu ke zaune" ta kuma cewa a natse tare da ficewa da ga parlourm, "damaba'aschool take zaune ba?" Yace a hankali, "eh, a gidan shi take" "ban taɓa zatan Anty ta na daalaƙada shi ba, sannan ba wanda ya taɓa faɗamin" murmushi ta saki tare da waigowa ta kalleshi, dakulawa tace, bayan rasuwar ta mu ma muka sani" tana kai nan ta ja kujera ta matsar da shi gefeda inda su Yasmin ke zaune ta mai alamun ya zauna da ido da hannu, zama yayi ba musuidonshi
akanta, murmushi ta saki tare da zaunawa, a natse ta fara ba shi labarin da ta sani, da ɗumbinmamaki ya ke bin ta da idon da ya fiddo waje, "to kaji dalilin tafiyanta can"....
Sauke numfashi yayi da ƙarfi tare da faɗin "ki na son ki ce mun, wai ma, ma, matan shi ce ayanzuhaka!" Yayi maganan cikin ɓarij murya da laɓɓa, jinjina mai kai tayi tare da faɗin "eh" "wow! zataiya in sha Allah" jinjina kai tayi tare da faɗin "in sha Allah" cike da damuwa, murmushi ya saki
tare da mata alamun smile da hannu, murmushi ta saki tare da bin shi da ido.... Ƙaramar dariya Jabir dake riƙe da waya ya saki tare da ajiyewa SSB dake zaune chairn dakekusada na shi, ɗago kai yayi ya kalleshi da mamaki, "ta ya ni gani please" yace fuska yalwace damurmurshi, ɗauka yayi a natse ya kafe shi da ido, ajiyewa yayi a natse ba tare da yace komai ba, ya zuba wa matakalan dake fidda sauti ido, "me ke faruwa?" Alhaji Jamil yace tare da kallonJabir, murmushi ya saki me faɗi tare da faɗin "masaniya suke nema game da Insu, se dai kuma basutambayi masana ba" "nayi zaton jin hakan" yace tare da sakin murmushi...
"To ai abu ne sabo ga kowa, ba'a saba gani ba, se gashi bakata ltan, dole su yi ta lalube danganoasalin lamarin" Abubakar yace fuska yalwace da murmushi, "wallahi na san za'ayi haka, shiyasaban so yarinyar nan ta bi mu ba" Lubabatu tace rai ɓace, kallonta Kamil yayi da mamaki taredafaɗin "to me ye na ki?" "Haba Kamil me ye nawa kuma! Taya za ma ka ce haka?" Tace fuskaamugun muttuke, sadda kai yayi saboda bayyanuwan da tayi, sanye take cikin kayan barci rigadadogon wando masu kauri da taushi, se baby hijab dake sanye a jikinta army color kamar yandakayan suke....
"Ɗauka mana Yaya Ali" tace tare da jan chairn dake kusa da nlwanda Ibrahimtlke zaune tazaunaa natse, sauke wayan daga kunninta tayi tare da maida kira ta maida kunni, "wai ma wa yafiddawannan magana ne?" A'isha tace murya ba daɗi, zare ido Maude dake tsaye ita da Lamundeagefe tayi cike da tsoro, "Maude zaku iya tafiya" Hajiya tace tare da kallon su, da sauri ta haɗiyeyawun tsoro ta wuce kamar wacce ake hankaɗawa, dafa mata baya Lamunde tayi da sauri...
"Oh Allah Yaya Ali ina ka yasar da wayan!" Tace kamar za ta saki kuka tare da ajiye wayantaɗago kai, murmushi Kamil ya sakin mata cike da kulawa, murmushi ta saki tare da faɗin"yunwanake ji sosai uncle Kamil" tayi maganan tare da sa hannu ta jawo food flaks, "ki ka ce kinƙoshi acan!" yace da mamaki, murmushi ta saki tare da faɗin "matsewa kawai nayi, amma yunwanakeji
sosai, kalan abincin ne be mun ba ana buɗewa na ji ahh" ta idda maganan tare da zaro harshetaɓata fuska tare da yunƙurin amai, dariya ya saki me sauti tare da faɗin "Allah ya shiryeki" .... Dariya ta saki tare da faɗin "ina kallon Uncle spoon ɗaya kawai ya ci ya ɗau drinks" tayi maganantare da kallon SSB dake cike da mamakin yanda aka yi tasan cokali ɗaya yayi, tare da sakinmurmushi "ki ce kallon yanda mutane ke ci ki ka zauna yi" Alhaji Munnir yace tare da kallonta, murmushi ta saki tare da faɗin "kai ma ai biyu kayi, uncle Jamil uku, uncle Abubakar ɗayakamanUncle, uncle Kamil biyu, uncle Jabir ko be ci ba, ina kallon yanda yayi ta jagwalgwala abincindaaka zuba mai, my Anty's da Hajiya kam sun ba ma food kunya yanda yakamata" ta idda maganantare da fashewa da dariya....
"A gaisheki me sa'ido" Abubakar yace tare da sakin murmushi, murmushi ta saki tare da kallonIbrahim, "a'a" yace tare da sakin murmushi, dariya ta ƙyalƙyace da shi tare da faɗin "ka ɗanci
amma ba sosai ba, da ina ƙirgawa ana kawo mun snacks na mance ƙirgan" ta idda magananmurmushi cike a muryanta, girgiza kai Hajiya dake ta bin ta da ido tayi tare da faɗin "ci abinci"
jinjina kai tayi tare da maida natsuwanta ga abincin da ta zuba....
"Hmm yanzu dan Allah wannan tarbiyya ne? Yarinyar da ko wanne mu anan ya haifa ya juyatazauna a tsakiyan mu tana sakin zantukan da ta ga dama, yanzu kalli yanda take magana dasuYaya Jamil, yanda ku ka san sa'anninta, da za'a ce be kamata ba kuma se cibi ya zama ƙari, ammawannan ba so ba ne, a gaskiya Insiyyat ta lalata rayuwar ɗiyar da ta haifa da kanta, wa zeyi fatada mararin wannan yarinyar ta zo inda yake, in dai yanda yarinyar nan take haka sauranƴan
uwanta suke to gaskiya Insiyyat ba ta iya haihuwa ba, ko da yake ba abin mamaki ba ne, itakantaba cikakken tarbiyyan ne da ita ba, tunda har ta iya tsallake maganan mahaifiyar da tayi
ɗawainiya da ita tun daga ciki zuwa futowa duniya zuwa girma banga dalilin da ze sa ma inyi
mamaki dan ɗiyarta ta kasance haka ba" Lubabatu tace cike da takaicin labarin da suka riskawanda media tayi ruddugu wajen yaɗawa....
Tunda ta fara jero zancen Insu da ta ɗibo abinci zata kai baki ta maida tare da sadda kai tanaamsan yanayin da maganganun na ta suka zo dashi, tana fara zance akan Anty ba tarbiyyagaretaba ta rumtse ido zuciyanta na tsananta bugu, ban da ɓari babu abinda hannunta da ƙafafuntakeyi....
"Yanzu tsakani da Allah me ya kawo wannan maganan a wannan lokacin? Luba meyasa baki
ƙaunan a zauna lafiya ne? Ba fa na son shashancin da zubda girma" Hajiya tace rai ɓace, "ki yi
haƙuri Hajiya, ai ba wani abu na furta ba, abinda na hanga na faɗa, yarinyar nan samba tadanatsuwa, ba ta da kamun kai, ba ta da sanin kima da darajan wanda ke gaba da ita, yanzuinbanda rashin tarbiyya har ta kalle ki damu tace mun ba wa abinci kunya yanda yakamata?Ai kouwarta da ta gama fitsare idanunta ba ta isa kallan ki ta faɗa miki wannan maganan ba, kodayake ba isashshen kunya ne da ita ba tsaf zata iya, saboda ta kwashe komatsanta ta faɗa duniya""stop!" Insu tace da ƙarfi tare da miƙewa a mugun harzuƙe, bin yanda jikinta yake ɓari kawai
suke da ido cike da mamaki me haɗe da tsoro.... Nuna ta tayi da yatsa manuniya tare da faɗin "ba ko wani banzan kalma nake ɗauka akanmahaifiyata ba, wacece ke da zaki dinga alaƙantata da waƴan nan muggan kalaman? Ke kunyarne dake? Tarbiyyan ne dake da ki ka zauna gaban ta ki mahaifiyar kina zuba zance san ranki
bayan ta gargaɗeki akan furtawa? To ya isheki, mahaifiyata komai na ne, zuciyata ba ta jinkirinaiwatar da hukunci ga duk wanda yayi ƙoƙarin faɗan kalman ɓatanci gareta, in kuma ki nasonganin zahiri game da hakan zan iya nuna miki, mutumta ki nake saboda kasantuwarki ta ƴar
uwar ta" ta idda magana a kausashe ƙirji na sama da ƙasa ...
"Allah ya kyauta, ban haɗa komai da ita ba, wallahi ba ƴar uwarta ba ce, ƴan uwana ba suhaifi
ɗiyar da zata tsaya a gabana haka tana mun magana ta sigan da ki ke mun ba, sannan ma inani
ina haɗa zumunci da butulu" Lubabatu tace zuciya cike da mamakin yanda Insu ke sakinhuci....
"Ze fi miki kyau ki nesanta kan ki daga farfaɗan maganganun banza gareta kamar yanda ki kanesanta kan ki da wani alaƙa da ita, wannan ma yana daga cikin tarbiyyan ɗiyoyi na gari rusaginin da iyayen su suka yi da hannayen su ba dare ba rana, ba tare da gajiya ko fargabandukanruwa da iska ba" tayi maganan a harzuƙe tare da watsa ma Lubabatu kallo me cike da gargaɗi, zabura Lubabatu tayi za ta cafkota, saurin riƙe ta Alhaji Munnir da zuciyan shi tayi mugunɓaci
yayi tare da daka mata tsawa....
"Lefi na ma kake gani kenan? Kana ganin yanda ƴar ciki na ta tsaya a gabana tana farfaɗanmunabinda ta ga dama, wacece ita?" "Ƴar Insiyyat da Abdussamad ne, cikakkiyar ɗiya me karekimada mutumcin iyayenta da dukkanin rayuwarta, ku barta ta yi gigin taɓa ko ƙumbata ta gani, banhaɗa komai da ita ba tumurmusata zanyi, dan ba kunya ce dani ba, sannan ba ingantaccentarbiyya a ka bani ba, dama in tsoho be ji kunyar hawa jaki ba ba ta yanda jaki ze ji kunyar kadashi" ta idda maganan zuciya a wuya....
"Insu!" Ibrahim yace tare da kallon ta, "kar ka ce ma inyi shiru, kana zaune take aibanta waccetasadaukar da lokutanta da kulawanta dan ganin na rayu cikin aminci, kowa na zaune take zaginmu uwa ba wanda maganan shi yayi tasiri akanta, sannan dan ina bata amsa dai-dai da hasashenda tayi kace wani Insu, ba zan yi shiru ba, ba zan dakata ba, ba zan ƙyaleta ba, mahaifiyatatanuna mun girmama wanda ya girmama kan shi ne, ba ta ce mun in mutumya walaƙanta kanshi a
idona In ɗauke shi da daraja ba, ba ta da sauran kima a idanuna, ta zubar da mutumcin da nakeganinta da shi, shi kuma mutumci madara ne, in ya zube ba ya kwasuwa, Insiyyat da ki kekiradaikirarin ba ta da tarbiyya ta fiki tarbiyya, dan ko banza ba zata tsaya gaban Hajiya Yasmintanamaida magana haka bayan ta haneta ba, ki je ki bincika wacece mara ingantaccen tarbiyyatsakanin ke da ita kafin ki zo ki na buɗe baki ki na banbancewa" ta idda maganan a harzuƙedaalamun tana da sauran batutuwa a baki da bata gama fiddowa ba....
Zaran tissue SSB da tun da suka fara zantukan ya maida hankalin shi ga abincin gaban shi yayi
tare da goge bakin shi ya miƙe a natse, "wuce ɗakin ki" yace a dake tare da kallon Insu dakecikatana batsewa, juyowa tayi a zafafe ta watsa mai rinannun idanunta cike da ɗinbin takaici mehaɗe da baƙin ciki, ganin na shi idanun a nata yasata ture plate's da food flaks ɗin gabantatawuce up stairs da gudu tare da fashewa da kuka me ciwo, bin ta yayi da ido har ta idda hayewakafin ya sauke numfashi a natse ya juyo ga Lubabatu dake jin kamar ta tsaga ihu dan irinwankinda Insu ta mata, "kar ki ƙara shiga sabganta daga yau, this is a last warning" yace idon shi ƙyamakanta, jinjina kai tayi tare da juyawa ta bar wajen ta na me haɗiyar zuciya.... Riƙo Lamunde Maude dake tsayuwan jiran fitowanta tayi tare da faɗin "Lamunde na boni" "shii
muje can" Lamunde tace tare da zare ido ta riƙo hannunta suka nufi side ɗin su, kai tsayedakinMaude suka yi, suna shiga ta riƙo Lamunde dake ƙoƙarin rufe ƙofa tare da faɗin "Lamundeidanyallaɓai yaji ni na fidda batun nan ya zanyi kenan?" "Oh Maude kafin ki aikata yakamata ki
wannan tunanin ba bayan kin aikata ba, bakya neman shawara sam se kin aikata ya kwaɓesannan ki dinga wuri-wuri da ido ki na mena mafita" "wallahi azal ce ta sa ni furta wannanbatun, wutan ciki irin tawa" tace kaman zata saki ihu, "to ta dai riga ta fita tunda ga shi duniya tashedayau, se ki kiyaye gaba, maza ba ni kasona dan na san gwagwgwaɓan biya aka miki" ta iddamaganan tare da miƙa mata hannu, "kin ji ke fa matsalan ki kenan, me zan baki? To biyat wannanidon nawa be kai ga gani ba" tace tare da kauda kai, "ah wannan ganganne Maude, ba fa ƙaramanake ba, Allah na tuba ni da ke dame kwaɗo ta ɗararwa gaya? Ai ba wani tazara ne tsakaninmuba, in zaki bani ki bani, in kuma zaki jira se maganan ta fasu ne zan fi san hakan, dan na tabbatain ba'ayi 50-50 ba za'ayi 40-60" ta yi maganan hankali kwance, "se kuma ki yi, ke dai ba kyagani
ba ki saka rai ba, wallahi Lamunde ki canza hali, jeki na tura miki na shan milo da madara" "tokoke fa, da zaki zauna ɓata ma kan ki lokaci ki haɗa da na bread da sugar dan cikin zefi ɗauka" tayi
maganan fuska washe da murmushi tare da buɗe ƙofa ta fice....
Da harara Maude ta rakata tare da jan dogon tsaki, "duk ni na jawa kaina da na buɗe baki har ki
ka san halin da nake ciki, oh ni Maude na ga ta kaina, yanzu idan yallaɓai ya fahimci ni na fiddawannan batu ya ze ji kenan? Me ze ce na zama? Allah ka kwantar da bala'i a duk inda yakeyacigaba da barci, ka rufa mana asiri duniya da lahira, kar ka sa mu jin kunyar waƴanda sukayardadamu" ta idda maganan tare da miƙewa ta nufi toilet....
Tana shiga ɗaki ta faɗa saman gado ta kanannaɗe jikinta waje guda ta cigaba da risƙankukadadukkanin ƙarfinta, so take a barta ta ma Lubabatu dukan mutuwa yanda ko nan gaba aka cetabuɗe baki ta faɗi wani abu akan Anty ba zata kuma ba, se dai an shiga tsakaninta da cikanburinta, wannan dalilin ya sata zubda hawaye masu zafi da raɗaɗi wanda ita dake fiddasubatagaza jin yanda zafinsu ke ratsa kumatun ta ba, jawo hoton Anty tayi ta rungume tare da faɗin"zan rama miki, se na tabbatar da a gaba in ta kuma haƙwaranta na gaba ba su ƙara moruwaba, ba zan barta haka ba" ta idda maganan cikin gunjin kuka.... Har parking space ya rakasu, ja baya kaɗan yayi bayan su gama sallama ya bi su da ido har sukafice daga gate ɗin farko, juyawa yayi a natse ya koma ciki, kai tsaye dining arean dake parlornyawuce dan anan aka shirya musu dinner, ruwa ya tsiyaya a natse ya kafa kai, yana ajiye cupɗinyaɗau wayanta da ta bari anan ya nufi up stairs, bin ƙofar ɗakinta yayi da ido a natse kamanmeneman wani abu, se da ya ɗauki kusan 5 minute's ba tare da yayi wani yunƙuri na shiga konawuce wa ba, lumshe ido a hankali yayi tare da buɗewa ya baza ma ƙofan ido, a natse ya takayakama handle, murɗawa yayi cikin rashin ƙosawa ya shige a natse.... Baza ma ɗakin ido yayi cike da nazari, faɗawa idon shi yayi kan bangon dake cike da hotunansu, takawa yayi a natse ya isa gaban bangon, bin hotunan yake da idanu buɗe, se da ya tabbatar
idonshi be tsallake ko guda
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 36 Chapter of 109