ubanta, fita mazane a
anguwar ba mata ba, wasa a anguwar Sarari, wane wannan ɗan wasan dan uwarsa" Yace damamaki tare da kallon shi, fiddo ido gaba ɗaya suka yi waje tare da kallon shi, "au baka sani ba?Uwarmu ɗaya ubanmu ɗaya anguwa ɗaya ta fiddo mu, wa ya baka lasisin buga wasa a anguwarmu ba tare da sanin mu ba?" "Wata yarinya ce" yace tare da goge zufan da ya tsatstsafo mai, dariya ya saki me sauti tare da dukan kafaɗan shi da ƙarfi, basar ba dai harka ba ce ta soyayya?" Ya je fa mai tambayan tare da ƙure shi da ido, "ita ce" yace a ɗan firgice....
"Zaka iya mutumina, share ai kai nawa ne, a buga me sanyi kar yayi zafi, dan jarirai ma a
anguwarnan ba sa jumirin jiran ta huce da zafi-zafi suke ci" ya idda maganan idon shi akanshi, murmushi ya saki tare da faɗin "ba muguwa ba ce" "yayi mutumi na ka iya ka huta, ka ga ɗanMalam ka ƙi halin Malam" yace tare da sa kai da nufin wuce wa, "gayi can ya fito" muryanɗayadaga cikin yaran na shi yace tare da nuna Baba da ya fito a natse, "hanzarta" yace da sauri taredashirin tsallakawa dan taro gefe ko da yayi yunƙurin guduwa, juyowa yayi da sauri tare da bazaido a inda wan can ya nufa, yana gab da isa ya taka burki a tsorace tare da faɗin "Sarari!" Daƙarfi, dariya ya ƙyalƙyace da shi tare da duƙewa a wajen, da sauri Ɗan kuka ya juyo tare da ƙarisowawajen shi a guje ya zube a gaban shi.... Ɗago kai yayi ya zuba mai jajayen idanunshi tare da faɗin "waya aiko ku?" "Mace! Yaushelalacewanka har ya kai mace ta baka aiki ka amsa?, Baka san namiji ke aikin mazaje ba?" "Rashin
sani" yace a rikice, dariya ya saki tare da faɗin "rashin sani ze iya birneka da ranka" jinjina kai yayi
tare da goge zufa, "wacece!" "Ban san wacece ba, sunanta kawai na sani" yace tare da gogezufa, ganin irin kallon da ya bi shi da shi ya sa shi faɗin "Sa'adatu ne sunanta" kallon sakanni yamai
tare da faɗin "ƙanwace ga Sarari uwa ɗaya uba ɗaya, kar ka kuskura ka shiga cikin faɗandabakasan farkon shi ba, wannan faɗan damu aka faro bar mu dashi" "Lukumanu ka samu jam'i kuwa?" Baba da suke tafe da manyan ƴaƴan shi yace tare da kallon Kainuwa.... Miƙewa yayi da sauri cike da ladabi tare da faɗin "isowana kenan Baba amma yanzu zangabatar" "to ka hanzarta, kar ayi wasa da sallah, Allah ya ƙara shiryaku" "amen Baba Allahyadafa maka mun bi Allah da Manzon shi mun biku, Allah ya ba mu aljannarsa dan darajar fiyayyenhalitta" murmushi Baba ya saki tare da faɗin "amen" "ka Sarari kake watsa taro" Ɗan kukayaceafirgice, jinjina mai kai yayi ya wuce a natse... Suna wuce wa, yace "in ka koma ka faɗa mata Baba sarkin dawa ne dan yana tare da kariyar
Zakuna, sarki yake a dawayafi ƙarfin ƙananun namun dawa kaman ku su kawo mai hari, kumakasanar mata ɗan amanan Sarari na nan na jiran ranar da ƙafafunta za su yi kuskuren takoanguwarnan, wallahi na rantse da Ubangijin sammai bakwai da ƙassai bakwai se na raba tadasu, wannan alƙawari na ne" ya idda maganan a kausashe....
Zaburowa matasan da ke jiran jin ƙiris tun ɗazu a gefe suka yi tare da tambayan "ya ne?" "Namune ya kawo ziyara" yace tare da wuce wa ya nufi masallaci, "ku wuce" ɗaya a ciki yace taredacijebaki, tattara yaran shi yayi suka ɗau hanya zuciyoyi cike da fargaba, dan sun san wanene Sarari
da yaran shi, mutumin da ya tarwatsa ƙungiyar daba guda akan kai ma uban gidan shi hari dasuka yi, ina kuma su da aka turosu ga mahaifin shi gaba ɗaya.... Fitowa tayi a natse cikin shirin barci, riga da dogon wando cotton me taushi se hula da ta sakame raga, wayane kare a kunninta da alamun amsa kira take, kai tsaye ta wuce ƙofar bedroomɗinshi babu wani alamun shakku, bell ta danna a natse hankalinta na wajen ba da amsan a waya, ba
jimawa ya buɗe a natse, murmushi ta sakin mai tare da bin shi da ido, sanye yake cikin kayanbarci farare masu taushi... Komawa ciki yayi ta da fa mai baya, yana shirin zama tace "Uncle ga su Yasmin za su taya kamurna" ta yi maganan tare da miƙa mai wayan idonta ƙyam a kan shi, amsa yayi a natse yakaraakunni tare da ɗaga sallama ya nemi waje ya zauna a saman sofa, haka suka yi ta taya shi murnarya na amsawa cike da kamalan shi, miƙa mata wayan yayi tare da zuba mata ido, "har kungama?" Tace tare da amsa ta kara a kunni, "yawwa ina Yaya?" Tace a natse, "yana researchroom"Yasmin tace a natse, "ok shikenan, dama su Uncle suna neman ma'aikatan lafiya ne, in Sa'adatuda Rahma suna so su turo takardun su" ta idda maganan cike da yanayinta....
Shirun daƙiƙu tayi kafin tace "da kamar wuya" "gurguwa da auren nesa ba" tace tare da sakindariya, "ke fa shirmen ki yawa ne da shi" Yasmin tace tare da sakin murmushi, "to baby inqlajinki" tace tare da tattara mata natsuwanta gaba ɗaya ta miƙa mata, "Rahma ta fara aiki ahospital ɗin da Yaya Salman ya buɗe, kuma ta samu miji ana shirin tsaida lokaci, ita kumaSa'adatu ba ta samu result me kyau ba gaskiya" "oh shiit wannan karon ma?" Tace da damuwa, "wallahi" tace a hankali, "Sa'adatu wasa kawai take yi ba niyyan karatu tattare da ita, kusanshekara uku kenan tana faɗuwa" tace cike da damuwa, "to ga dai yi nan" tace a natse, "okayshikenan zan sauke wayan se na kira ki" tace a natse "nagode baby Insu se na jiki" murmushi tasaki tare da zare wayan ta katse kiran.... Murmushi ta saki tare da juya dubanta gare shi, ɗago kai yayi ya zuba mata ido ba tare da yacekomai ba, "oh Uncle" tace tare da rufe fuskanta da tafin hannayenta, guntun murmushi yasaki
tare da kauda kai, sauke hannun tayi tare da faɗin "an canza mana deputy chancellor adminregisterer students affair, examination office, se ka ga yanda students ke murna bari ma kagani"ta idda maganan tare da ɗago wayanta ta fara neman videon da ta musu, fuska yalwace damurmurshi ta miƙa mai tare da faɗin "har celebration ɗin farin ciki suka haɗa" amsan wayanyayi
ya ƙure da ido, tsayin sakanni ya ɗauka a haka kafin ya miƙa mata wayan tare da sauke numfashi
me ƙaramin sauti ya jingina da jikin sofan....
"Ka gani ko Uncle?" Tace idonta akan shi, jinjina mata kai yayi ba tare da yayi yunƙurin furtakokalma ɗaya ba, "Allah yasa waƴanda aka canza masu gaskiya ne, ba kaman su ba" tace taredaajiye wayan a gefe ta ƙurewa tv da ido...
"Fitowa suka yi hannu riƙe da juna suka nufi ƙofa, zabura wacce ke kusa da Shila tayi a zafafedanufin bin su, riƙo hannunta da sauri Shila ta yi tare da faɗin "ba yanzu ba Ziza ki bari se mungama fahimtar menene asalin abinda ke tsakanin su tukun, ba ma da tabbacin akan abindazuciyan mu ke hasashe" ta idda maganan cikin muryan rarrashi, "haba Shila ki ga fa tunyausheya shiga ɗakin nan, sanna ki duba ki ga lokacin da ya fito" ta idda maganan hawaye na cikaaidonta, "duk ina sane, shi dama bariki ya gaji haka, ke dai ki ƙara haƙuri" kauda kai tayi taredagoge hawaye ta miƙe ta shige ɗakinta kamar me shirin tashi sama....
"Ka ji dai yanda mu ka yi da su" Baba yace tare da kallon Sarari dake zaune a gefen tabarmandayake kai, "wannan yarinyar butulu ce kafataninta, babu alheri a tare da ita, ka ga fa butulcindata ma waƴanda suka tsaya mata suka ci da ita suka shayar da ita suka tufatar da ita, suka
ilmantar da ita, shiyasa tun Mama na da rai na so ta bar ni in bazama neman shegiya in aikatainda ba'a dawowa amma ta ƙi, yanzu gashi tana shirin zama bala'i masifar ga al'umma" "dukwannan zantukan ba na yi ba ne yanzu Salisu, daina wannan batu ma sam, Allah dai ya shiryatain tana da rabon shiryuwa, ba dai zamu sare da bin ta da addu'a ba shi kaɗai ne gudunmuwar dazamu iya ba ta" Baba yace cikin karayar zuci...
"Shikenan, bari in leƙa wajen nan haka, ke Sadiya zuwa jimawa kaɗan ki kawo mana abinci ƙofargida" yace tare da tashi ya fice, "to" tace duk da tasan ba jiran ji ze yi ba, "Allah ka shirya mana
zuri'a" Baba yace tare da kauda ido daga bin inda ya bi da yayi....
"Uncle can I gist to you?" Tace tare da maido dubanta gare shi, girgiza kai yayi tare da faɗin"goto your bed" "am not feeling sleep right now" tace tare da shagwaɓe fuska ta kalleshi, kallonsakanni ya mata ya kauda kai, "wow shiyasa nake bala'in tsan-tsan sanka Uncle" tace taredajuyowa gare shi gaba ɗaya, ko lura da halin da furucinta na ƙarshe ya jefa shi lokaci guda batayi
ba....
"Wanni ma labari zan baka?" Tace tare da ɗaga ido sama, alamun tunani "yawwa bari inbakalabarin Anty lokacin da take da cikin Sa'eed" tace tare da ƙyatta yatsu, lumshe ido yayi taredabuɗewa ya baza mata, "bakya jin nauyin an batan sunayen nan haka ne?" Yace a natse idonshi
akan ta, dariya ta ƙyalƙyace da shi tare da faɗin "Uncle ba Baba na ba ne ba ai Kaka na ne, sunanku ne ya zama dole mu ɓoye ba na su ba" lumshe ido yayi ba tare da yace komai ba...
"Lokacin da cikin ya girma ba ta iya ko tafiya, ta kummubura sosai fa, ta daina cin abinci kullumse ruwan Lipton, in ta tashi magana kullum se tace "ba na jin zan haifi wannan cikin, wataƙilaajalina na dakko, wataƙila ba na da rabon sake ganin fuskan mahaifiyata ne" buɗe ido yayi sosai
akanta cike da mamaki, "eh yee ai Hajiya Yasmin ba ta taɓa zuwa gidan mu ba har se lokacinbikin Anty Salwa, sannan ba ta amince Anty taje inda suke ba" da mamaki yace "meyasa" "bansani ba, Anty dai ta taɓa ce mana akwai dalili ita ce kuma dalilin da yasa ta haramta mata" "yasubhanallah" yace a ƙasan maƙoshi...
"Har ta rasu ba su gana ba!" Yace a tsorace, girgiza kai tayi tare da faɗin "sun gana lokacinbikinAnty Salwa, ta zo ita da su Anty Khadijatu suma shine zuwan su na farko a iya sanin mu, sekumabayan sun koma Hajiya Yasmin tayi rashin lafiya Anty taje ta ɗakkota ta dawo da ita gidanmu
saboda ba me kula da ita a can" gyara zama yayi idon shi akanta tare da faɗin "su Lailahnbazasuiya zama da ita ba ne?" "Sun yi iya ƙoƙarin su, har hakan na shirin taɓan auren Anty Khadijatushiyasa da Anty Lailah ta kira ta sanar Anty ta roƙi Yaya alfarma shi kuma ya amince" jinjinamata kai yayi cike da mamaki...
"Hassan fa?" Yace a hankali, zare ido tayi tare da sakin hamma ta zame jiki kaɗan ta kwantatareda faɗin "ba mu san ma a inda yake ba, sau ɗaya muka taɓa ganin shi shine lokacin da HajiyaYasmin ta rasu, tunda a wajen Anty ta rasu, be zo ba har se da ta kwana kusan uku, sannandayazo yayi ta zagin Anty wai ita ta kasheta, dama yasan ita za tayi ajalinta, ta zama annoba, irinwannan maganganun yayi ta faɗa mata ita kuma tana ta kuka tana roƙon ya tsaya ya sauraretaya ƙi, haka ya fice a zuciye tun daga lokacin ba mu ƙara jin halin da yake ciki ba" "be zo ta'aziyyaba?" Yace a hankali, "ya zo shine ai yayi ta zagin Anty ko kabarin da aka binne Hajiya Yasminbenema ba ya bar garin, su Anty Lailah ma sun ce ba me labarin shi, kwana ki dai Anty Khadijatutace mijinta yace ya gan shi a ƙasan Nigeria" ta idda maganan tare da sakin hamma ta lumsheido, cike da nazari yake bubbuɗe zantukan nata yake sa su a mazaunan su, kenan da Yaya yacemusuya je ta'aziyya Anty ba gaskiya ya faɗa musu ba.... Buɗe mota yayi ya shiga a natse, shiga kusa da shi tayi tare da faɗin "ji nake kaman kar katafi" tayi maganan a shagwaɓe tare da kwanciya a saman ƙirjin shi, murmurshi ya saki tare da bintada ido, "ko mu koma ne?" Yace tare da sakin murmushi ya ɗagota kaɗan, jinjina kai tayi idontaana shi, "sorry na san yanzu haka Mommy ta fara zuba idon ganin ta inda zan ɓullo, amma nayi
miki alƙawarin ina nan zuwa mu yi sati tare se na gama shirya plan ɗin tukun" dariya ta saki cikeda farin ciki tare da faɗin "na san zaka iya" "sosai ma" yace tare da shafo kumatun ta ya sumbaci
laɓɓanta, "okay kar in ɓata maka lokaci, ka kira ni please" "wannan ai dole ne" yace tare dabintada ido har ta sauka, rufe ƙofan tayi ta ja gefe ta tsaya, jan motan yayi ya bar wajen a guje, murmushi ta saki tare da juyawa da nufin komawa ciki....
Fizgota aka yi aka hurgar a gefe tare da yin kanta gadan-gadan, a razane ta fara yunƙurinmiƙewa tare da ja baya a hanzarce, damƙota yayi tare da zuba mata marika uku masu ratsajiki, da ɗin bin mamaki ta baza ido dan ganin me wannan ƙarfin halin ganin Ɗan kuka dake sakinhuci
kamar mayunwacin zaki yasata ƙoƙarin ture shi, se dai yunƙurinta ya kasa tasiri saboda bariƙon
wasa ya mata ba...
"Menene!" Tace a ƙufule, sharara mata wani marin yayi a zafafe tare da watsa mata rinanunidanshi, kiciniyar ƙwace kanta ta fara dan ta lura tsaf ze iya aikata mata aikakka a yanda yakennan, dan da alama ya shawo wanda yafi ƙarfin shi ne, sakinta yayi zuciya a ɓace tare da faɗin"kafin ki yi sanadiyyan tsayuwar numfashi na se na fara naki, wato ni ki ka maida ɗan iska, saboda kin rainani har ki ka iya kusantoni da abinda ze iya sanadin rayuwana" ya idda magananaƙufule....
"Ni ka mara har sau huɗu!" Tace zuciya a matuƙar ɓace, zaro wuƙa a ƙasan marar shi yayi taredafaɗin "se in kashe ki in binneki a nan dan ubanki" yayi magana tare da nufarta gadan-gadan, saurin ja baya tayi cike da razani, "ashe ke ƙaramar ƴar iska ce, da ki ka ce ke babba ce, sabodalalacewa uban da ya kawo ki duniya ki ka aikani in ma walmukalafatu saboda kin kwashekayanki kaf daga gaban me duka to mu duk iskancin mu muna ragawa iyaye shiyasa muke ganindai-dai, wallahi ba zamu taɓa ɗai-ɗaicewa ba, ke kuwa kina gab da halaka" da mamaki Sa'adatutabi
shi da ido cike da firgici ta nufeshi tare da riƙoshi ƙam-ƙam baki na ɓari tace "kun mai abindanace? Kun bazar da shi ya kasa motsi? Kun faɗa mai ni na turoku ku aikata mai hakan?" Ta iddatambayoyin cike da zaƙuwan jin amsa...
Fizge hannunta daga jikin shi yayi tare da ingijeta da ƙarfi, "anya ke ƴar halas ne kuwa?
Mahaifinki ki ke magana a kai fa" yace da zallan mamaki, "eh mahaifina ne, akan shi nakemagana, ba ruwanka tunda ba akan na ka mahaifin nake magana ba, faɗamin ka aikata abindana umurce ka? Baka da damuwa akan tunatar dani waye shi, tun daga yarinya na san matsayinshi a wajena" ta idda maganan a fusace, a fusace ya ɗago wuƙan hannun shi ya kai mata yanka, duk da ta yi saurin matsawa se da ya karci tsintsiyar hannunta, a mamakance ta ɗago ta watsamai idon da ya cika da firgici, ganin ya ƙara kawo mata wani yankan ya sata juyawa ta nufi gidana guje, dafa mata baya yayi a hanzarce, tana shiga ta ɓame ƙofan tare da jingina a jikin shi, "daki
tsaya ki ga aiki da cikawa ƴar iska wacce ba ta gaji arziƙi ba, kafin ki kai ga kasheni ni zanfaraaika ki, kuma wallahi Kainuwa na nan na jiran kafarki ya taka anguwan nan yayi alƙawarinseya
raba ki da su" ya na kai nan ya wuce a zuciye ya bar wajen....
"Go and sleep" yace a natse tare da kallon inda take, ganin ko motsi ba tayi ba ya sa shi fahimtartayi barci ne, miƙewa yayi a natse ya shige dressing room be jima ba ya fito riƙe da blanket mesauƙin kauri, rufa mata yayi ya kashe wutan ɗakin me haske ya kunna dumlight ya wuce samangado a natse ya haye ya ja blanket addu'a a saman laɓɓa...
Tana tabbatar da tafiyan shi ta juya da nufin shigewa ciki, ja baya tayi da sauri ganin Shilatsayetana bin ta da ido, guntun tsaki ta saki tare da raɓeta ta wuce, tana shiga ɗaki ta janyo wayantata danna number Harira ta kara a kunni, sakanni kaɗan ta ɗaga tare da ɗaga mata sallamacikeda tsoron kar ya zo taji wani labari akan zuwan da su Safinat suka yi ne...
"Harari" tace ba tare da ta amsa sallaman ba, "na'am" tace cike da danne firgicinta, "Yaya Salisuya dawo gida ne?" "Eh ya kusan wata uku da dawowa" tace a natse, "okay nagode" tace taredaƙoƙarin zare wayan, "lafiya kuwa?" Tace cike da fargaba "no ba komai" tace tare da zare wayan, numfashi me ƙarfi ta sauke tare da faɗin "mutanen nan ba za su bari ka mutu a can ba wato, seda suka fiddoka, Yaya Salisu kana son ɓata mun shiri" tayi maganan cike da tashin hankali... Kiran sallahn farko ta farka, hamma ta saki tare da janye blanket ɗin jikinta ta miƙe tare dawareido a ɗakin, "wayyo Allah a nan na yi barci?" Tace tare da miƙewa, murɗo ƙofan dressingroomyayi a natse ya fito sanye da farar jallabiya me taushi, murmurshi ta saki tare da faɗin "goodmorning Uncle" "morning" yace tare da nufar ƙofa ya fice, yana idda ficewa ta taɓe baki taredafaɗin "morning" tana kai nan ta naɗe blanket ɗin ta ajiye a saman sofan ta fice da sauri....
Ɗakinta ta nufa, tana shiga ta wuce toilet kai tsaye, ba ta jima ba ta fito fuska a jiƙe alamunalwala ta yo, ɗaukan hijab ta yi ta saka ta haye kan praymat ta kabbarta sallah, tana idar daazkhar ta miƙe ta haye gado ta ja blanket, ba ta samu tashi ba se 10:40 da sauri ta dira tayi toilet, ruwa ta watso ta fito ta ja stool ta zauna ta jawo lotion's a hanzarce ta fara shafawa, tana
gamawa ta zari toilet paper ta goge fuska ta jefa a dustbin ta wuce gaban wardrobe... Riga da siket na cotton lace me taushi ta jawo ta yafa veil a saman ka ta jawo jaka da plat shoesta fice da sauri, da sauri-sauri ta ke taka stairs ɗin, tana sauka ta hangesu zazzaune a diningarea, ƙarisawa tayi da sauri tare da faɗin "morning guy's" murmushi Jabir ya saki tare da girgizakai, sauran kuwa duk bin ta suka yi da ido, jan kujera tayi ta zauna tare da ƙoƙarin serving ɗinkanta, "dama zaki school?" Lawiza tace tare da janyo coolern alkubus ta saka mata biyu, "zani wallahi
test ne ma dani" tace tare da gutsira ta kai baki, murmushi ta sakin mata ta zuba mata
markaɗaɗɗen fruits ta matsa mata da bowl ɗin da ta zuba mata miyan kifi dake ta tashinƙamshi
ta ja gefe ta tsaya, "nagode Anty Lawiza Allah ya hana Abban Iman yi miki kishiya" tace cikedayanayinta, "to fa in ya na da ra'ayi fa?" Abubakar yace tare da kallon ta, "Allah ya cire mai, AntyLawiza ta isheshi" tace tare da kallon Ibrahim dake ta sakin murmushi, "ko ba haka ba AbbanIman?" Tace idonta akan abincin gabanta, murmushi Lawiza ta saki tare da juyawa dan barinwajen...
"Lawiza please ƙara volume ɗin tvn nan" Jabir yace da kulawa, idon shi ƙyamakan tvn, "to" taceagirmame tare da ɗaukan tv control ta ƙara volume ta wuce, "haba malam Sulaiman ai wannanmaganan abuɗe take, taya ma jama'a da hankalin su da tunanin su za su dannawa mutumindayakasa riƙe mace ɗaya kuri'arsu, kar fa kamanta shekarun baya da suka shuɗe nan wata matatafito media tana kuka akan wulaƙanci da ya mata, ya aureta ya je ya jingine kamar hoto ya cigabada hurɗoɗin gaban shi, babu wani kula bare a zo kan mu'amala ta aure, tsakaninta da shi sedai
ta hangoshi a tv, daga baya da ta ga ba za ta iya jurewa ba ta nemi court ta raba auren, tomalamSulaiman kai ya ka ke ganin ze iya kula da rayukan dubban nan mutane bayan ga kasa kuladamace ɗaya a gidan shi, wannan mutumin fa raɗe-raɗin rashin cikakken lafiya ake mai, tayaza'ace wanda be iya tafiyar da iyalin shi ba ze iya tafiyar da ƙasar mu, wannan ma ganganne malam
Sulaiman, shi ba abinda ya sani se Kasuwanci, ya tsaya a tanan ya ɗau biyar ya juyata ta komagoma" ya idda maganan tare da ɗaukan kofin ruwan gaban shi ya kai baki, murmushi Sulaimanya saki tare da faɗin "eh to da kuma aikin ko dan na ji ance babban doctor ne" ya idda maganantare da sakin murmus....
"To kaji ma, ni ban ma san da hakan ba se yanzu da ka faɗa, ya koma can ya cigaba da abubuwanshi da ya saba na yau da kullum, maganan neman mulki da ya fito ya ma janye dan ba ze iyaba, haba malam Sulaiman ai aka ce juma'ar da za tayi kyau tun daga Laraba ake iya ganeta, toshi
wannan Laraban tashi ma ba tayi kyau ba bare mu sa ran juma'ar shi za tayi" ya idda maganancike da shaƙiyanci, gyara zama Sulaiman yayi tare da faɗin "honorable ɗan Asabe zamu iyacewaLaraban SSB tayi kyau, duba da yanda talakawan ƙasa suka goya mai baya, tun daga fitowanmaganan neman takarar shi zuwa wannan lokaci da ya ci primary election, talakawa sunfitomedia sun jaddada batun kuri'unsu na shi ne, duba da yanda kowa ya san waye shi da kumameya sa a gaba tun kafin fitowan wannan zance" "to ba zan ga lefin su ba malamSulaiman, kasanmutumin dake matuƙar ƙauna da so ba ya taɓa hangan aibu ko kuskuren abinda yake ƙaunaharse ya ɗanɗana mishi abinda muke mishi fatan ƙin ɗanɗana, tabbas SSB ya tallafi rayuwar matasada yawa a wannan ƙasan, amma hakan ba shi ze sa idon mu ya rufe mu kasa hasaso gobenmuba, jama'an ƙasa mu farka da ga farkin da muke, SSB ba abinda ya sani game da siyasa, a samayakenemanta, sannan in ya samu a saman ze mulke ku, baya da wani ƙwarewa a wannan fannin, ƙwarewarshi shine kaman yanda na faɗa ya koma ga kasuwancin shi da aikin shi, yafi ganewaallura da sarrafa biyar zuwa gom..." Kashe tvn Alhaji Munnir yayi ba tare da jiran jin ƙarishe abinda ze ce ba tare da jan dogontsaki, azuciye yace wannan mutumin ɗan iska ne wallahi" "tantiri ma" Abubakar yace na shi zuciyanawuya, "dan jam'iyyar adawa ne, ya fito tallata na su ɗan takaran ne kawai" Jabir yace cikedatakaici, "ya fito tallata ɗan takaransu shine ze zauna yayi ta zuba zance haka, har da ta ɓoprivatelife ɗin shi" Alhaji Munnir yace a harzuƙe, guntun murmushi SSB ya saki ba tare da yace komai
ba....
"Politics ɗin kenan uncle Munnir calm down" Insu tace tare da kallon shi fuska faɗaɗe da
murmurshi, juya dubansu gareta suka yi cike da mamaki, matsar da plate ɗin gabanta tayi tareda faɗin "shi dama siyasa ba komai ne a cikinta ba se tonan asiri, abinda ba ka san ka aikatashi
ba ma ranar da ka rungumeta za'a fiddota, wanda be kai tsayuwa a gabanka ya ɗaga muryawajen gaisheka ba ma se ya zageka da ƙarfi yanda ze isko kunnuwanka, democracy kenan, kowana da freedom of speech, freedom of expression, freedom of press, ko da kuwa kalamanzezaɓarɓaka zuciyoyin mu ne se mun saurara kuma mun yi haƙuri dan ba ma da abinda za muiyayi, ƴancin kenan" ta idda maganan tare da zuba musu ido.... Da mamaki yake bin ta da ido cike da nazartan kalamanta, "gaskiya ne fa ku daina kallonahaka, fitowa aka yi dan a harzuƙo Uncle, wasa ne kawai ake son bugawa da shi, yana nuna gazawashikenan ya shigo hannu, amma in ya nuna jajircewa ze fita da number yabo wanda jama'anƙasagaba ɗaya za su fito dan taya shi murnar amsa, shikenan fa ya tsallake lafiyan Allah, uncleJabirzan cika gyara kaɗan a maganan da ka yi ɗazu, ba wani jam'iyyar adawa a siyasa, duk ɗayasuke, kansu a haɗe yake, talakawa da wanda be kusance su ba suke nunawa haka dan wasa da tunaninsu, amma asalin gaskiyan uwa ɗaya uba ɗaya suke, babu wani bare a cikin su, ka duba da kyauzaka ga in abun taya murna ko na kokawa ya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 40 Chapter of 109