Share this page
Hisham da Khalim zaune suna zaman jiranta, da ɗin bin mamaki suka zuba mata ido, ganin yanda take jan ƙafa daƙyar ya sa su sauri miƙewa tare da nufantaahanzarce, "Insu!" Hisham yace da sauri tare da taro ta saboda taga-tagan da tayi, "menene!" Khalim yace a rikice, buɗe baki tayi da ƙyar tare da faɗin "Hisham mu bar nan, dan Allahmutafi"jinjina mata kai yayi a ruɗe tare da ɗagota ya riƙe hannunta ƙaƙam, "bari mu tafi se ka zo" Hisham yace a natse tare da ƙoƙarin wuce wa, "tare zaku tafi!" Khalim yace idon shi ƙyamakanshi, jinjina mai kai yayi tare da faɗin "eh" "school?" Yace da mamaki, "ba zan iya cigaba da zamaanan ba matuƙar ba ta a nan" yace a dake tare da wuce wa riƙe da hannunta, bin su yayi daidocike da zallan mamaki.... Bayan shekara biyu.... Comments fans🥰🙏 🫀MUGUWAR TSOKA 🫀 {🫀TA'ARE KALLUƊE} [Muscle Cramp🫀] ) عضلة سيئة ( 🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_ https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 written and Created ~~~~~~~~~~~~~~ ِبسم الله الرحمن الرحيم By Yardajjiya👩 💻 Page. Fourty "Insu ana kiran wayanki" wacce ke zaune saman tabarma a madai-daicin tsakar gida me kyawunduba tace tare da kai hannu ta ɗau wayan ta juya da dubanta ga ƙofar ɗakin dake bayantatareda ƙoƙarin ɗaga labulen dake sake a ƙofan, rigata ɗagawa akayi daga ciki da sauri, "wowmashaAllah" ɗaga ido tayi ta zube a na wanda ta ɗagan, Insu ce cikin Abaya baƙa me matuƙar ɗaukanhankali, murmushinta dake daɗa ƙawata mata fuska ɗauke a saman fuskanta, ta daɗa cika, tazama cikakkiyar budurwa me ji da lokaci.... Murmushi ta sakin mata tare da miƙa mata wayan, amsa tayi ba tare da murmushin ya bar saman fuskanta ba ta ɗaga ra kara a kunni, "ka iso? Okay gani nan" tayi maganan cike da aji, zame wayan a hankali tayi ta sauke tare da maida dubanta ga wanda ta miƙa mata wayantaredafaɗin "ya iso Anty Jamila" jinjina mata kai tayi fuska faɗaɗe da murmushi, juyawa ciki tayi tasakabaƙin baby hijab me ɗauke da stone masu matuƙar ɗaukan ido ta saka medical glass ta ɗaujakata goya ta fito a natse.... "Lallin be caɓe ba ko?" Jamila tace da kulawa, murmushi ta saki tare da ɗaga ƙasan abayantareda faɗin "kin gani ba abinda ya same shi, se kyau ma da ya ƙara" murmushi Jamila ta saki taredafaɗin "tabbas dake ya samu farar fata ya baje" murmushi ta saki tare da faɗin "gaskiya kinfitodani" "ba dole na ba amarya guda fa ki ke, in ban gwangwajeki ba wa zan gwangwaje?" Karamardariya ta saki tare da faɗin "kin ba ni kunya" tayi maganan tare da ɗago hannunta da ya shazanen lalli baƙi da ja ta rufe fuska, "auh kunya kuma?" Jamila tace tare da sakin dariya, zamehannu tayi ta saki murmushi ta ƙarisa kusa da ita ta rumgumeta tare da faɗin "thank you" murmushi ta saki tare da bugun bayanta a hankali... Zame jiki tayi ta saka mata kuɗin da ta ciro a hannu ta damƙe da nata hannun tare da faɗin"karki buɗe se na tafi" "a'a wallahi ba zan amsa ba, haba ma Insu, yanzu dan na miki lalli ne sekinbiyani? Lallai ma kin kawo shubuha" tace cike da mamaki "oh Allah bakyaso in dawo gobekenan?" Tace tare da kafeta da ido, "ai ko yau ki ke so ki dawo amma ba zan karɓi ko sisi ba" "bayawa fa, ba ke na ba wa ba yarana na ba wa, na manta ban suyo musu sweet ba a siyan musudashi dan Allah" "se fa ki yi" tace cike da rashin jin daɗi, "kenan ban isa ba ki ki siyan musuba!" Tace tare da ɗaure fuska, "Insu!" Tace cike da rashin jin daɗi, "sorry ba zan kuma ba" tace taredasakin murmushi, "dan Allah kar ki ƙara ban so" tace kaman zata saki kuka, murmushi ta sakinmata tare da faɗin "na ji na amince" ta idda maganan tare da zaro wayanta dake ringing, "ohAllah yanzu ze addabeni se kin zo, 8 za'a tafi dinnern please ki zo da wuri" tayi maganantaredanufar ƙofa da sauri, murmushi ta saki tare da faɗin "in sha Allah amarya" .... Tana fita ta hangi motanshi fake a gefen gidan, da sauri ta nufi wajen, tun fitowanta ya hangotabuɗe murfin ƙofan ɓangaren shi yayi ya sakko a natse, wow ya wanku ba ƙarya, Hishamnesanyecikin wata musulmar dakakkiyar shadda wacce ta gama gajiga da walwali kallo ɗaya zakamatakasan dukiya ta koka akanta, saman kanshi ɗauke da wata ni'imtacciyar hula wacce ta daɗaƙawata kwalliyar na shi, buɗe ido tayi tare da faɗin "ango irin wannan kyawu haka!" Tayi maganan murya cike da mamaki, harara ya balla mata tare da faɗin "kya naɗe tabarmankunyarki a ta haka mana, se da na faɗa miki ki yi lallin nan tun shekaran jiya, amma dake bajinshawara ki ke ba kin dage se yau, bayan kin san mun tara jama'a, na fito tafiya wajen ɗaurinaureki ka kirani, gashi na zo kin shanya ni" ya idda maganan cike da takaici.... "Oh sorry wannan ƙorafin da ka tsaya yi ai ƙara janye lokacin yake" tace tare da sakin murmushi, takawa a natse yayi ya buɗe mata kofan ɓangaren me zaman banza tare da faɗin "shiga ni bangaamfanin lallin ba ma" harara ta banka mai ta shige, murmushi ya saki ya rufe ƙofan ya komamazaunin driver ya mata key suka ɗau hanya.... "Wallahi wani masifaffen yunwa nake ji, ji nake kaman ana sukuwa a cikina" tace tare da kwaɓefuska ta shafa fatan cikinta da hannu, juyowa yayi ya kalleta tare da faɗin "Anty Jamilanbatayi girki ba ne?" "Wallahi tayi ta kawo mun ma ni ce na ƙi ci" tace tare da sakin hamma, "kinjinmatsalar ki ko, kina jin yunwa me ne ne na wani yin fulaku," "kai dai bari yanzu nake jin damanaci" tace tare da kare baki saboda hamma da ya zo mata.... "Ni kar ki cinyeni, muna isa ki nemi ko donuts ki ci" jinjina kai tayi cike da gamsuwa, hakayacigaba da driving hankali kwance suna taɓa hira sama-sama, suna isa ƙofar gida ya taka burki, buɗe murfin dake gefenta tayi ta sauka a natse, "bakiji ba" yace tare da karkata kan shi yandazata hangeshi, juyowa tayi ta duƙo da kai ta zuba mai ido, "yayi kyau ba din taurin kan ki ba" yacetare da sakin murmushi, murmushi ta saki tare da faɗin "ka yi kyau ba din mitanka ba" ƙaramardariya ya saki tare da gyara zama ya kunna motan, ba shi hanya tayi fuskanta yalwace da murmushi.... Fitowa suka yi a natse cikin shiga me matuƙar ɗaukan hankali tare da tsayuwa a gefe gudaalamun akwai wanda suke jira, ba jimawa Gude ta fito cikin nata rantsatstsan shigan se zubawalwali take dan ba inda be ji maggi ba, rufo ƙofar parlornta tayi a natse tare da kallonHalimatare da faɗin "ina Sudais ɗin?" "Na buga mai tun ɗazu be fito ba" tace tare da kallon ta, "toshikenan ai se mu tafi, ba zamu tsaya ya ɓata mana lokaci ba, dan da wuri zamu dawo" ta iddamaganan tare da juyawa da nufin ficewa, buɗe ƙofarshi Sudais yayi ya fito, Allah me iko, yayi baƙi ya rame sosai, juyowa tayi ta banka mai harara tare da faɗin "dan iskanci na faɗa makalokacin da zamu tafi amma ka je ka shantake kana kwasan barcinka na asara ko" ko ci kanki bece mata ba se kulle ƙofan shi da ya fara hankali kwance... Yana gamawa ya juyo ya tako a hankali yana ɗingisa ƙafa, bin shi da ido suka yi cike da mamaki, ko kallon inda suke be yi ba se wuce wa gaba da yayi, dafa mai baya suka yi cike da mamaki me haɗe da tsoro, fiɗɗo mota yayi ya faka a gefe, suna fitowa suka bubbuɗe ƙofan da kansusukashige, suna gama shiga ya ja motan suka kama hanya, gyara zama Gude tayi cike da kulawatakalleshi tare da faɗin "ƙafan ya motsa ne?" Jinjina mata kai yayi idon shi akan titi tare da faɗin"tun shekaran jiya na fara jin shi" "shine baka yi magana ba Sudais! Ciwon ƙafan nan fa kasanmatsalan dawowan shi" jinjina kai yayi tare da faɗin "ban aikata komai ba, na manta ma rabondainyi allura" "ka tabbata!" Tace cike da tantama, "to amfanin me ƙaryan ze min idan na miki?" Yace cike da rashin jin daɗi, sauke numfashi me ƙarfi tayi tare da faɗin "shikenan, gobe kojibi inbe daina ba se mu je mu ga doctor" jinjina mata kai tayi hankalin shi akan hanya.... Yana shan kwanan hanyar da ze sadashi da anguwarsu Insu ya juyo da kai ya kalleta fuskaamarairaice tare da faɗin "Mommy yanzu haka zaki zuba ido in rasa Insu?" Yayi maganankamanze saki kuka, harara ta banka mai tare da faɗin "auh dalilin da yasa ka fito kana wani shanƙamshi kenan? Ai se ka yi ta yi, yarinyar nan ba ka a kanta harkan gabanta take, ka haƙura ka amshi zaɓin da na maka, kasan ba zan taɓa zaɓo wacce zata cuta maka ba, ka bar musu ɗiyarsu" taiddamaganan cike da muryan rarrashi, girgiza kai yayi tare da faɗin "Mommy ya ki ke maganankaman ba ki san so ba, auren soyayya fa ku ka yi da Daddy ba na haɗi ba bare in ce baki sanyanda auren wanda ka ke so yake da tasiri a rayuwa ba, Mommy ki na fa da daman da za'abani Insu amma kin zubda komai kina bani haƙuri" ya idda maganan cike da damuwa, kallonsakanni ta mai kafin tace "naji, zan yi magana da Hajiya kafin in dawo" "wow! Shiyasa nake matuƙar alfahari dake uwar da tafi ko wacce uwa a faɗin duniya" murmushi ta saki tare da kauda kai cikeda jin daɗin yabon da ya mata, kallon juna Halima da Nafi suka yi tare da kauda kai .... Kai tsaye cikin gida ta shiga ɗaga ma Baba Kalla hannu tayi ta wuce hanyar da ze sadata dageneral parlor da hanzari, dan ta hangi Jummai ba ta son ta tsaidata, tura kofan tayi ta shigasallama ɗauke a baki, amsawa yawancin jama'an dake cike da parlorn suka yi, "Amarya" Shafa'atu" tace tare da miƙewa ta yo inda take, murmushi ta saki tare da faɗin "ku ce anfarashiryawa" "haba tun yaushe kuma, har ƴan ɗaurin aure sun tafi ɗaurowa" tace tare da riƙohannunta ta zuba ido akan lallin dake ɗaukan idonta, "wow! Gaskiya yayi kyau" tace tare daɗagokai ta sakin ma Insu murmushi.... "Nagode sister, ɗakina akwai mutane ko!" Tace cike da ƙosawa, "maƙil kuwa, wallahi Mamatasaukenmutanen Dimau a can" tace tare da sakin hannun ta sakin mata murmushi, "wayyoAllah, bari in je side ɗin Yaya, dan Allah ki duba wardrobe ɗina zaki ga farin leda a sama ki ɗakkoki biyoni da shi" tana kai nan ta wuce hanyar da ze sadata da side ɗin Yaya, jinjina mata kai tayi tawuce dan cika umurni... Tana tura ƙofan ta tadda ƴan Aminan juna cike maƙil a parlorn, da mamaki ta bi su da ido, "yauga amarya me lalli ranar ɗaurin aure" wacce idonta ya kai ga Insu tace tare da kama baki, murmushi ta saki tare da faɗin "kai sister Hafsat kar muyi haka dake fa" murmushi ta sakinmatatare da faɗin "zo mu gani, amma yayi matuƙar kyau" ƙarisawa kusa da ita tayi ta duƙa taredamiƙa mata hannu, "sassannunku da isowa, anan aka yasar daku" ta idda maganan tare da kallonsu, "ba ma son iya shegenki Insu, aka yasar damu kamar wasu marasa daraja" ɗaya a ciki tacetare da banka mata harara, dariya ta saki tare da faɗin "to maida wuƙan sister Asiya ina nufinakamuku masauki" "yanzu ki ka yi magana, wallahi muna can side ɗin baƙi Farisat tace mu dawonanza'a shiryawa Yaya da abokanan shi wajen, a can za su sauka" "okay haka ne, ku mana afwa, inatake?" "Haba ba komai fa, ba ta daɗe da fita ba, kiranta aka yi" ɗaya a ciki tace da kulawa.... "Sister Laɗifa da Momsy ina gaisuwa" tace tare da miƙewa ta fice daga side din, da ido sukabi tacike da yaba hankalinta, ba ta daɗe ba ta dawo tare da yaran su Lailah rike da ruwa da lemukamasu sauƙin sanyi, "a sanyaya zuciya ina zuwa" tace tare da ficewa da sauri, "agogo ta iso, damana ce muku se in ba ta dawo ba" wata a gefe tace cike da jin daɗi, shigowa suka kuma hannuriƙeda manyan trey dake ɗauke da gasassun nama da aka ƙawata samanshi da yankakkun tomato'sda albasa da bell pepper, banda tiriri ba abinda suke fiddawa, ajiye musu tayi tare da faɗin"bari su taya ku hira zan watsa ruwa ina zuwa" "okay se kin fito" suka ce cike da kulawa, juyawatayi tanufi ɗaya daga cikin bedroom's ɗin dake side ɗin tare da faɗin "sister's za'a kawo mun kayadanAllah ku nuna mata inda na shiga ta ajiye a saman gado" jinjina mata kai suka yi har ta shige.... Da sallama a baki ta shiga parlorn Ummi dake cike fanƙal da ƴan uwa da maƙofta da abokananarzuƙa, amsawa Ummi dake rungume da yarinya ƴar kimanin shekara ɗaya da rabi dake ta sharɓan kuka tayi fuska na faɗaduwa da murmushi "yawwa Allah ya yankewa bawa wahalaNafisat zo amshi ɗiyarku kafin ta taramun mutan garin ku" Ummi tace idonta akan Nafisat datahaɗe cikin wata musulmar dakakkiyar lace me cike da tsone wanda ya daɗa fiddo mata ƴanmatancinta, ɗinki ya zauna ɗas a jikinta kamar a jikinta aka ƙirƙireshi, murmushi ta saki taredafaɗin "wallah gaba zanyi Ummi shigo da baƙi zanyi suna gate suna jirana" "amsheta ki kai tagauwarta dan Allah ta ƙi yarda da Hasinat yau sam" tace tare da miƙa mata yarinyar da tundatajiyo muryan Nafisat ta tsahirta da kukan.... Iyye au Anty Hasinat ɗin ma baki yarda da ita ba yau lallai kin ƙaro hankali Mairah" tace taredaɗago hannu biyu ta miƙa mata fuska cike da murmushi, miƙo nata hannuwan tayi da sauri, ɗaukanta tayi ta saɓa a kafaɗa tare da gyara zaman veil ɗin saman kanta, "kin ga dake kenegashinan ta yarda" wata makofciyarsu dake gefe tace tare da sakin murmushi.... "Ai zata yarda da ita, Nafisat da Mairah ai ƙawayen juna ne tun daga yarinta" Rahma tacetaredasakin murmushi, murmushi Nafisat ta saki tare da faɗin "aikoni Anty Habiba tayi wajenki fa" "toina ji Allah yasa samu ne" tace tare da sakin ƙaramar dariya, murmushi ta saki tare da faɗin"aikuwa samu ne, tace ku fiddo wannan gift's ɗin ƴan ɗaurin aure sun kusa dawowa" "wallahi badamu ba, kawai ta ja mana miƙewa tsaye muna zaune lafiya, Insu tace kar a sake a fiddo setabada umurni" Safinat tace tare da kallon Nafisat, "Anty Safinat ba ta dawo daga wajen hennabakuma sun kusan dawowa" Nafisat tace tare da kallon ta, "ai ta kirata kawai ta tambayeta intacea fiddo se mu fidda, amma ba ta amince ba ba ta yanda zamu aikata haka" Rahma tace cikedagaskiyanta, "ta kira ba ta amsa ba" "Nafisat ki na fa ɓata lokacin ki ne, ba ta yanda zamuyi wannan gan-ganci, kin fi kowa sanin Insu in ta murɗe, dan haka ki tafi sabgan gabanki, ki kai yarinya ki je ki shigo da baƙi, ita kuma ki ce mata ta kira Insu" Safinat tace cike da tabbaci, "shikenan, bari na je na faɗa mata" tace a natse tare da gyara zaman kan Mairah dake sassaukeajiyan zuciya a kafaɗanta ta fice a natse.... Da ido suka bi ta har ta fice, murmushi Hasinat dake tsaye a bakin bedroomɗinta ta saki taredafaɗin "na so ganin fuskan Insu" dariya suka saki tare da kallon juna, "fuskan sister Farisat nasogani in Mairah ta isa, yanda ta gama ɗaukan wankan nan ai akwai matsala" dariya suka saki tareda barin wajen, "shiryayyu ƴan albarka" Ummi tace tare da sakin murmushi, "ina ruwanFarisat, ai zata fi soma ta ganta a kusa da ita" wacce ke gefe tace tare da sakin murmushi, "wallahi kuwa"wacce ke a kusa da ita tace tare da sakin murmushi, "Ummi na ce ko za'a ba autana aurenwannan ɗiyar ta ku?" wacce a girme zata girmi Ummi tace tare da kallon ta.... "Wacce!" Ummi tace murmushin ƙayace a saman fuskanta, "Nafisat" murmushi ta kuma saki tareda faɗin "wallahi manema ne da ita da yawa, duk an dakatar da su se ta kammala makaranta" "ina ce ta zana jarabawar fita babbar secondary bana?" Tace tare da gyara zama, "eh ta zana, sekuma gaba in sha Allah, ya shigo jerunsu ai ba damuwa in rabon shi ne se ki ga shi da ya zoabaya ya sameta" Ummi tace cike da murmushi, "wallahi natsuwar yarinyar na burgeni" tacecikeda ɗin bin kula, "ai gaba ɗayansu haka suke, Allah dai ya cigaba da tsare mana su" Ummi tacecike da ɗin bin son da take musu, da amin suka amsa zukata ƙal... "Amshi wannan Sha'awanatu ki kaiwa Anty Munari bari in leƙa mutanan can" Farisat dakesanyecikin lace irin na Nafisat sak tace tare da sakin mata murmushi amsa tayi tare da faɗin "nadai faɗa miki ki cire wannan tsitstsinan takalmin" murmushi ta saki tare da faɗin "ba abinda zefaru""a'a Farisat gudun wahala ake, ke dake ɗauke da ciki me ze kai ki saka wannan takalmin, "ohAllah ina cikin? Abinda ko wata biyar be yi ba, wallahi manta shi ma nake a jiki na" tace cikedagaskiyanta, "to ai shikenan" tace tare da wuce wa da sauri.... Juyawa ta yi da zumman nufar side ɗin Yaya, da hanzari ta ja baya tare da faɗin "wayyo AntySalwa kin razanani" ta idda maganan tare da dafa ƙirji, "kya razana mana tunda baki da gaskiya, ina ce se da Anty Khadijatu ta ce kar ki saka takalmi me tsini" "oh Allah bari in cire tunda baki yayi yawa" tace tare da duƙawa a natse ta cire, "ki ma barshi, ke ce da shan wahala ba wani ba, ki je ki fiddo Yasmin su gaisa da mutanen ku, tun ɗazu suna can ba wani tare da su, wai Farisat meyasa ba ki ba komai mahimmanci ne yanzu?" Marairaice fuska tayi tare dw faɗin "wallahi Daddyn Mairah ne ya kira ni" "hmm ai se ki cigaba tunda haka ki ka zaɓan wa kan ki, mutanesunbaro gidajensu sun zo danku sannan ki zube su ki yi tafiyanki".... "Wayyo Allah wallahi suna raina Anty Salwa wajensu zani yanzu, jinjina mata kai tayi ta nufi barin wajen, "Insu ba ta dawo ba ne?" Tace tare da juyowa "wallahi ban sani ba yanzu na shigo" tace tare da wuce wa da sauri.... Kai tsaye ɗakin Yasmin ta nufa, tana shiga tace "dan Allah ku mun lamuni bari in ga abar ganinminti biyar" dariya wata abokiyar aikin Yasmin ta saki tare da faɗin "to sister Farisat wallahi kingama kashe ni da kyawu" "oh Allah nagode" tace tare da riƙo hannun Yasmin dake sanye dakayairin na ta sak, "muje ki gaisa da mutanen kirki, tun ɗazu suka iso" tace tare da iddasa ficewa... "Insu ta dawo ne!" Yasmin tace cike da fata a hankali, "ina zan sani" tace tare da shigewa sideɗinYaya, "wayyo bayin Allah kumun afwa, wallahi Daddyn Mairah ne ya sani wani aiki amma yanzukomai yayi dai-dai" harara matan Zubair me suna Mardiyya ta sakin mata tare da faɗin "shanyanda ki ka yi ya bushe, ba dadin Allah ya turo Insu ta kwashe ba da ya faɗo ƙasa" "oh sorry sister Mardiyya wallahi kuna raina tun ɗazu ku nake tunani" "to munji matso mana da abar ganin, ohsister Yasmin a karshe dai kin zaka tamu" Laɗifa tace cike da iya shege tare da miƙa matahannu, murmushi ta sakin mata tare da takawa ta isa kusa da ita, "wallahi kin gama haɗuwa, Allahyasaa ƙulla alheri" tace cike da yabawa, ba abinda ta iya ce mata se zama da tayi a natse suka faragaggaisawa da sauran, "bayin Allah me ku ke buƙata?" Farisat tace tare da kallonsu.... "Zo zauna mun fi buƙatan ki samu hutu, wannan jeka ka dawon da ki ke ai se jikin ki yayi ciwo" wacce suke kira Momcy saboda sunan Anty da take da shi tace da kulawa, zama kusa da itatayi tare da faɗin "nagode Momcy wani kulawan se uwa, wallahi buƙatan hutun nan nake, ammawanda ya tara ai se ya miƙe" "haka ne, ki dinga hutawa daughter ba ke ɗaya ba ne, shima nacikin wahala ze yi" tace da ɗin bin kulawa, jinjija kai tayi cike da gamsuwa, "oh jama'a yau Chairmangirma ya samu, wallahi mamaki nake" Hafsat tace tare da sakin dariya,.... "Au da be da girman ne!" Mardiyya tace tare da kama haɓa, "a'a bance ba, amma ai wannangirman na da banne" tace tare da sakin murmushi, "ina Insun! Na ji kaman kun yi magananta" Farisat tace kaman an tsunguleta, "tana ciki tana shiryawa" "Laɗifa tace tare da kai bottleɗinlemu baki.... Shigowa parlorn tayi a hanzarce tare da kallon Sarah matan Hassan cike da natsuwa tace"AntySarah baki ga Antyn Farisat ba?" Girgiza kai tayi tare da faɗin "yanzu na fito, baki ga Anty bakuwa?" "Tana waje ita da su zainab" tace tare da saurin wuce wa hankali a tashe tace "ohAllahina kuma ta shiga!" Tayi maganan tare da wuce wa ɗakin Babiya, tana shiga ta tadda dandazonƙawayenta da ƴan uwa, juyawa tayi da sauri, kafin ta kai ga barin wajen muryan Babiya yadoki kunnuwanta, "takwara" juyowa tayi tare da sakin mata murmushi cike da kulawa tace "na'am".... "Ma sha Allah kin yi kyau" "murmushi ta saki tare da faɗin "banyi rabin ki ba" murmushi mutanen dake ɗakin suka saki cike da yabawa, "wa ki ke nema?" Tace da kulawa, "Anty Habiba" "yanzu kuwa ta bar nan, duba ta can a farfajiya ita da Lailah" "to" tace tare da wuce wa da sauri.... Tana fita farfajiyan gidan ta hango Habiba da Gude da su Sudais biye da su a baya, da sauri tanufeta tare da faɗin "Anty Habiba tun ɗazu nake nemanki" "yi haƙuri Uwata, na je shigo dasuAnty Gude ne" "oh ba komai sannunku da zuwa" tace tare da kallon Gude, amsawa tayi kadarankadahan, su Halima kuwa sakin mata murmushi suka yi cike da ƙauna, "sun ce se dai ki kirata" tace tare da maida dubanta ga Habiba, "oh barshi Shafa'atu tace ta ga dawowanta ma, damakarya zo su rigata dawowa ne yasa nayi wannan tunanin" ta idda maganan tare da kai hannuzataamshi Mairah kuka ta saka tare da ƙanƙame Nafisat, "tafican maƙiwaciyan kawai" tace taredadungure mata kai, murmushi Nafisat ta saki tare da wuce wa da sauri.... "Yanzu takwaran Babiya ne ta haɓake haka! Ai in na haɗu da ita a hanya ba na shedata ba" Gudetace da mamaki, murmushi Habiba ta saki cike da mamaki tare da faɗin "kin mance ɗiya macekuma da saurin girma Anty Gude" "wallahi fa, lallai girman ɗan mutum ba wiya, wacece tasaɓoakafaɗa?" "Ƴar wajen Farisat ce" "oh mace ta haifa ko?" "Eh" tace tare da juya dubanta ga Sudais, "mazan duk sun tafi wajen ɗaurin aure, ko zaka bi su ne?" jinjija kai yayi tare da faɗin "wani masallaci ne?" "Masjidirrahma, na anguwar ƙarfe, ka gane masallacin?" Jinjina mata kai yayi tareda faɗin "na gane, bari in hanzarta" yayi maganan tare da juyawa da sauri, "to se ka dawo, AntyGude mu ƙarisa ciki" ba musu suka bi bayanta.... Ƙarisawa inda ta hango Lailah da Khadijatu da Salwa da Munari da Jummai da Suwaiba daTineneda Saratu matan Lurwanu da Sakinat matan Balarabe tayi tare da faɗin "dan Allah ba kuganemun Anty Farisat ba!" Tayi maganan cike da ƙosawa, "daga ina ki ke haka?" Lailah tace taredakallon ta, "Anty Habiba ne ta aiken, se Ummi kuma tace in kai wa Anty Farisat Mairah" "baki shigo da ƙawayen naki ba?" Khadijatu tace da kulawa, "suna can bakin gate suna jirana, AntyFarisat nake so in kaiwa Mairah, "tana side ɗin Yaya" Salwa tace tare da kallon ta, da sauri tajuyako sallamansu ba tayi ba ta wuce, dariya Baba Tinene ta saki tare da faɗin "gashi Mairahuwar ɗafa ba ta yarda da kowa bare a amsan miki ki tafi a miƙata wajen uwartata" "ita ma taci arziƙinrashin uwar ne" Suwaiba tace tare da sakin murmushi, "a'a takan yarda da ita da Sa'eedjefi-jefi, amma Insu da Yasmin da Sahabee da umar ba ta cika yarda da su ba" "ai se su ƙare lafiya" Lailahtace tare da maida hankalinta a aikin da suke.... Tana shiga parlor Nafi ta tare ta da tambayan inda Yasmin take, "tana ɗakinta" tace tare dayunƙurin wuce wa, "Insu fa?" Tace da ɗan ƙarfi saboda nesa da tayi da su, "wallahi ban sani ba" tace da ƙarfi tare da tura ƙofan side ɗin ta shige, "buɗe ido tayi sosai ta baza musu, hangoFarisatda tayi ya sata nufarta da sauri tare da faɗin "tun ɗazu take ta kuka, tana nemanki" "ta farkane!"Tace da mamaki tare da gyara zama,

Chapter 58 of 109