ya wuce nurses dake bayan shi suka dafa mai baya zukata ƙal.... Rufuwa a ƙofan suka yi suna bin shi da idon dake fidda ruwan hawayen tausayin shi, "ina ganinkomai ya ƙare yanzu ku ba shi daman hutawan da doctor yace" Hassan yace tare da kallonsu, bamusu suka baro wajen jikkuna a sanyaye suka dawo parlor, "Abbie ya warke" Nafisat tacetaredakallon Mairah dake ta lumshe ido alamun son barci, murmushi suka sakin mata idon su akanMairahn, "je ki kwantar da ita" Lailah tace cike da kulawa, babu musu ta miƙe ta wuce ɗakinta....
"Sannun ku da zuwa Abdussamad, kun tadda mu cikin ruɗu" Hajiya tace fuska faɗaɗe da amurmushi, murmushi suka saki cike da dattako, "ai mu muka yi farin zuwa, saboda munci karoda kyakykyawan albishir" Hassan yace tare da sakin murmushi, "gaskiya ne wannan, ya iyalinnaka?" "Suna lafiya suna a gaidaku" yace a natse, nan suka buɗe babukan gaisuwa cike da jindaɗinlabarin da suka tarar....
"Amarya har yanzu ki na nan!" Salwa tace da mamaki tare da kallon Asma, zare ido Yasmintayi
tare da faɗin "yau anyi sulliɓaɓɓun iyaye, ke tashi lokacin tafiyanku na ƙaratowa, wallahi samnasha'afa" "kin sha'afa ko mun sha'afa? Wallahi na ma manta da batun" Kausar tace tare da miƙewa, "ba inda zani se na ga tashin uncle SSB" Asma tace murya na rawa....
"Ke ba ma son shashanci dalla miƙe ƙila yana can yana jiranki" Lubabatu tace tare da bankamataharara, kuka ta saki tare da faɗin "Maa dan Allah ku barni wallahi ko na tafi hankalina ba
kwanciya ze yi ba, dan Allah ku bari in ga tashin shi" ta idda maganan cike da magiya idontaakanLubabatu, "in ba ki da hankali mu muna da shi, yaro ya faɗa miki lokacin tafiya sannan ki wani ceba zaki ba yanzu me ki ke nufi?" Kausar tace da mamaki, "mu bari se gobe ko jibi in Uncle yafarka" tace a hankali, "to ko a gidanki zaki yi gobe da jibin ba anan ba" Yasmin tace tare dajawowaya....
"Ku bi a hankali mana" Hassan yace tare da kallon su, "Yaya Hassan yarinyar nan ba hankali baneda ita, se ta aikata abu ta bar mu da ɗaukan lefin, tun jiya yakamata a ce tana gidan mijintakogidan Babanta, amma tayi fir tace nan zata zauna, mun biye mata kuma yanzu ta kawo zancenzama zuwa jibi, ka ga se dangin Babanta su kasa mu a faranti su yi ta ci yanda ransu ke so, kiranAnty A'isha zanyi in faɗa mata ta turo goggonnenta su zo su tafi da ita, duk inda za su kaitamasukaita, amma wallahi ba anan ba" Yasmin ta idda maganan cike da takaici...
Murmushi Yaya ya saki tare da faɗin "Asma'u meyasa ba zaki bi shi ku tafi ba?" "Ina son ganintashin Uncle ne" tace tare da sakin hawaye, tsaki Lubabatu taja tare da kauda kai, murmushi yasakin mata tare da faɗin "kar ki damu ko bayan tafiyanku idan ya farka za'a faɗa miki, kumazaki
yi magana da shi, ta shi ki bi mijinki, nan aljannar ki yake, ba kya da ikon yanke komai akarankanki se da umurnin shi" ya idda maganan cikin muryan rarrashi, jinjina kai tayi tare da goge hawayeta miƙe, sallamasu tayi hawaye be bar tsare a saman fuskanta ba, "please in ta farka ki haɗamu"tace cike da magiya tare da kallon Insu, jinjina mata kai tayi tare da bin ta da ido, juyawa tayi tashige ɗakinta a guje, ba ta jima ba ta fito canje da kaya.... Ɗaga kiran da ya shigo wayanta Nabila tayi tare da faɗin "dan Allah gamu nan a hanya" tanakai
nan ta sauke wayan tare da faɗin "jarababbu, ba abinda suka iya se ƙosawa" murmushi Sadamdaya bi su da ido ya saki tare da kallon Insu da ke share hawaye, "ba zaki musu rakiyan ba?" Yacecike da kulawa, girgiza kai tayi tare da faɗin "Allah ya tsare ya kai su inda za su lafiya" "amen, aina mijin ke aiki?" "Anan ne fa" tace tare da sakin mai murmushi....
"To ina za su!" Yace da mamaki, "cin amarci" tace tare da sakin ƙaramar dariya, zare ido yayi tareda jinjina kai, "ina boyfriend, be biyo ku ba ne?" Tace tare da maida hankalinta akan shi, "taremuka zo, yana Insoul" yace a natse, "wow! Ashe shiga Insoul dole yau" tace tare da sakinmurmushi, "yakamata" yace tare da jinjina mata kai.... Miƙa ma Insu ID card ɗin Nafisat na school Yaya yayi tare da faɗin "na ba su numberki dukwani
tsare-tsare na school ɗin za su dinga sanar dake" jinjina kai tayi cike da gamsuwa, "ki sakaidososai akanta, ban da ƙawayen banza banda wasa" jinjina kai ta kuma a natse, "Allah ya temaka" yace a natse, "amen" tace tare da ajiye shi a gefenta...
"Zamu tafi ko?" Yace tare da kallon Sa'eed, murmushi ya saki tare da jinjina kai a hankali, "kokana nan kusa da daughtern ka?" Ya kuma jefa mai tambayan fuskanshi yalwace da murmushi, zuba mai ido suka yi gaba ɗayansu, sadda kai yayi ba tare da yace komai ba, "ji ɗan ƙauye yi
magana mana" Salwa tace tare da sakin murmushi, murmushi Yaya ya saki tare da faɗin"ai yayi"murmushi suka saki tare da kallon shi.... Murmushi Insu ta saki tare da gyara zama cike da dattakonta tace "uncle Jamil yace yana sonzama da shi in babu damuwa" kallonta Alhaji Jamil yayi cike da jinjina sanin yakamatanta, murmushi Yaya da Hassan suka saki cikin kame kai Yaya ya kalli Sa'eed tare da faɗin "Uncleɗinka na son zama da kai, ka amince zaka zauna da shi?" Murmushi ya saki tare da faɗin"eh" sauke numfashi me ƙarfi Alhaji Jamil yayi cike da jin daɗin furucin Sa'eed ɗin tare da sakinmurmushi, murmushi Yaya ya saki tare da faɗin "to Allah ya baku haƙurin zama da Juna" "amen" suka ce baku a haɗe cike da farin ciki....
"Haba kukan ya isheku haka mana, ku yi haƙuri, ku tsananta addu'a shi ya fi buƙata yanzu" Sarari
da ya ƙariso wajen shi da zugan shi yace cikin muryan shi na ƴan Allah ya shirya tare da kallonsu, jinjina mai kai Yasmin tayi tare da janye jikinta daga na Sadiya ta zaro waya ta matsa gefe, "tokoku fa, an gama cike-ciken zamu wuce gida yanzu sun fita da shi, na sa an sanar da anguwahalinda ake ciki ku share hawayen nan ku yi haƙuri an san da zafi amma ba yanda za muyi" yacetareda juyawa ga Kainuwa, "bi su ka shiga motan asibitin ina bayanku a mashin" yayi maganantareda nufar inda ya kafe mashin ɗin shi, jinjina mai kai Kainuwa yayi tare da kallon sauran yace"muhaɗe a can" ya wuce ya nufi ambulance saboda shigar da Baba da aka yi.... Salati Shureim ya saki daga ta can kare da waya a kunni tare da faɗin "yanzu can gidan zakutafi?" "Eh zamu tafi tare da su" Yasmin tace a hankali, "please banda kuka bari in sanarwasuAnnur gamu nan, kun sanarwa brother Salman ne?" Girgiza kai tayi tare da goge hawaye murya
na rawa tace "a'a" "please bana son kukan nan kin sani, bari in sanar mai gamu nan" yace taredakatse kiran, fashewa da kuka mara sauti tayi tare da juyawa inda Sadiya take, riƙo hannuntatayi
a sanyaye suka nufi barin wajen....
Juyowa Farsiat tayi jiki a mace tare da faɗin "ku koma ciki Halima an barshi shi ɗaya" girgizakai
Nafi tayi tare da faɗin "Mommy na kan hanya ku muje can" tayi maganan cike da sanin yakamata, jinjina mata kai tayi suka fice, suna fita sojoji biyun da suke tare da Yasmin suka ta so da sauri
dan ba su daɗe da amsa kira daga ogansu ba, buɗe musu mota suka yi suka shige, suna ficewadaga asibitin Yasmin ta danna number Yaya.... Miƙewa Insu tayi ta koma kusa da Yaya, murmushi ya sakin mata tare da kallonta cike da kulawa, murmushi ta sakin mai tare da faɗin "ina son magana da kai" jinjina mata kai yayi tare da batadukkanin natsuwar shi, jawabi ta koromai na tsayin mintoci a natse a hankali yanda ita dashi
kawai suka ji, banda jinjina kai ba abinda yake, tana saka aya ya sakin mata murmushi taredafaɗin "zanyi magana da barrister Salahudden, in yana da lokaci se ya tsaya a kai in ba ya dashi
kuma, za mu ga abinda za'ayi a kai" jinjina mai kai tayi cike da farin ciki tare da faɗin "I'mproudofyou" murmushi ya sakin mata tare da shafa saman kumatunta, zaro wayan shi dake nemanagaji
yayi a natse ganin me kiran ya sa shi sakin murmushi tare da faɗin "baby" murmushi Insutasaki
tare da faɗin "ɗan lokacin nawa take kishi da shi ko?" Tayi maganan a shagwaɓe, murmushi yasaki tare da ɗaga kiran a natse ya kara a kunni, yana shirin ɗaga mata sallama sautin kukantayadoki kunnuwan shi....
Cike da kamewan shi ya gyara zama tare da faɗin "lafiya?" Jinjina kai tayi kaman yana ganintatare da faɗin "Baban Sa'adatu ya rasu yanzu Yaya" "inna lillahi wa Inna ilaihirraji'un" yaceanatsekaman ba wani abu da ya dokan mishi ƙirji, kallon shi suka yi da mamaki, sai-saita muryanshi
yayi tare da faɗin "kina ina yanzu?" "Gamu a hanya zamu koma can gidan" tace a hankali, "tokukula da yaran nan da kyau" yace tare da zame wayan a natse, ganin irin kallon da suke mai yasashi sauke numfashi a hankali tare da faɗin "Mahaifin Sa'adatu ne Allah" tun kafin ya ƙarisaInsu
tace "Baba ya rasu!" Tayi maganan a tsorace tare da miƙewa da ɗokacin razana, riƙota yayi tareda faɗin "haka Allah ya tsara, ba tsimi ba dabara" kuka ta saki tare da zame jikinta ta zaunasaman kujera daɓas... Ban da salati da sallallami da jinjina buwayan mahalicci ba abinda su Lailah ke yi cike da jimami, kallon Hassan Yaya yayi tare da faɗin "ina ganin zamu wuce yanzu" jinjina mai kai yayi taredafaɗin "tare zamu wuce" "a'a please ka zauna babu damuwa, in ka gama abinda ya kawo kakafinka wuce can se ka bi yo can ina da magana da kai" yayi maganan cike da dattako...
"Yaya zan bi ku" Insu tace tare da kallon shi a sanyaye, kallonta yayi a natse fuska yalwacedamurmurshi, jinjina mai kai tayi tare da komawa ta zauna, murmushi ya saki tare da sallamanHajiya a mutumce ya fice, tashi su Alhaji mazan suka yi gaba ɗaya suka dafa musu baya....
"Daina kukan nan haka Insu" Khadijatu tace cike da damuwa, "Baba Anty Khadijatu, Baba shimaya rasu, ya tafi inda Anty taje" tace tare da miƙewa a guje tayi ɗakinta, murmushi Lailahtasakinma Hajiya tare da faɗin "sun shaƙu da mutumin sosai ne" jinjina kai Hajiya tayi tare da faɗin"Allah ya gafarta mai" "amen" suka ce a sanyaye, fitowa Nafisat tayi a natse ganin ba YayadaSadam da Hassan ya sata faɗin "ina su Yayan?" "Yanzu suka fita" Salwa tace da kulawa taredamiƙa mata hannu.... Ba musu ta ƙarisa kusa da ita ta zauna fuska yalwace da murmushi, "tayi barcin ko?" Lailahtaceidonta akan ta, "eh tayi tun ɗazu" tace tare da sakin murmushi, "ina Sa'eed?" Tace kamar wacceaka muntsila saboda ganin ba shi a inda ta bar shi, Lailah na shirin magana Sa'eed ya shigojiki asanyaye, tun da ya ga su Yaya sun fice yaji dama ya bi su, "ina ka je?" Ta jefa mai tambayanidonta akan shi, "raka su Yaya" yace a hankali tare da wuce wa ɗakin shi....
"Sun tafi ne!" Tace da mamaki tare da kallon su Lailah, jinjina mata kai suka yi a natse, sakkowaInsu tayi cikin amintaccen shiga goye da jaka a bayanta, da mamaki suka bi ta da ido, "ina zaki!" Khadijatu da ta samin ƙarfin gwiwan motsa laɓɓa tace cike da mamaki a muryanta, murmushi tasakin mata cike da dakiya tare da faɗin "Insoul" jinjina mata kai suka yi tare da bin ta da ido, "Hajiya se na dawo" tace tare da kallonta, jinjina mata kai tayi da kulawa tare da sakin matamurmushi, juyawa tayi ta fice a natse, sauke numfashi Hajiya tayi tare da sakin ma su Lailahmurmushi ...
"Haƙuri za ku yi kukan nan ba abinda ze amfana muku, musamman ma ke Farisat, ba wani ƙoshinlafiya ne da ke ba, tashin hankalin nan ka iya haifar miki da wani matsalan" Babiya da na sudaɗeda isowa ba ita da Baba Mari da Balarabe tace tare da kallon su cike da tausayawa, jinjinamatakai Farisat tayi tare da jan hanci, "yawwa ku daɗa haƙuri dan zafi da zafi, rashi anyi shi babbamakuwa, bawan Allah mutumin kirki mutum na mutane, wallahi ko da Balarabe ya faɗa minbanyarda ba se da muka iso na ga tabbaci, mu daɗa haƙuri kukan ba rahama take nema ma mamaci
ba, ba kuma ta ba da mafita, wallahi ko yau se da ya faɗo min a rai, na ce ko ya yake ciki dajiki?Ashe yana kan hanyan amsa kiran mahaliccin shi, Allah ya sa jinyan da yayi kankaran zunubai ne, Allah ya sa yana kyakykyawan makoma, Allah ya kula da abinda ya bari" ta iddasa addu'anmuryana karyewa.... Da a amen jama'an da suka cika gidan maƙil suka amsa, shigowa masu ɗaukan gawan sukayi
jikkuna a sanyaye dan zuwa sallatan shi, kai tsaye ɗakin da aka kimtsa shi suka shiga, ba sujimaba suka fito saɓe da makaran a kafaɗunsu, kuka Sadiya da Iƙilima suka fashe da shi a tare, yunƙurawa Sadiya tayi da zumman bin su, wata makofciyarsu tayi saurin riƙota, fizge jikintatayi
da ƙarfi tare da faɗin "kar ki sake riƙe ni, gatan da yarage mana kenan za'a fita da shi fita naharabada, amma ki ke riƙe ni, shikenan mun rasa komai" ta idda maganan tare da fashewa daƙaƙƙarfan kuka ta zube a wajen, "haba Sadiya da girmanki da hankaliki da iliminki ki ke furtairinwannan kalaman, kar ki zama butulu ga mahaliccinki mana, shifa ya amshi abin shi bayanya
baku shi na tsayin shekaru" wata dake gefe tace tare da kallon ta.... Ɗago kai tayi tare da share hawayen da suka kasa tsayuwa, cikin tuƙuƙin baƙin ciki tace "akodayaushe godema Ubangijin mu muke da dukkanin ni'imominshi, sannan duk lokacin da ya jarabcemu amsa muke da hannu biyu dan munsan ƙarfin imanin mu yake san gwadawa, amma kufa! Baabinda ku ka iya se tasa rayuwarmu a gaba, ta dalilinku ku ɗin nan muka rasa farin ciki dadama, kun ɗau abinda ba'a yi ba kun baza a duniya ku da mazajenku, me ake da maƙofta irin ku, masusan ganin maƙoftansu cikin halin ha ula'i, wannan wa'azin waƴanda ba su san suwaye kubazaki
je ki ma wa, amma mu mun haddace komai sannan mun fahimci inda ku ka saka gaba, kuntarwatsamana rayuwa, kun muzantamu, me ku ka zo yin mana anan! Kun zo ganin yanda zamukasance ne bayan ba shi! Ku sha kurumin ku, ba zamu sha fiya-fiya mu kashe kawunan muba, dan mun san na mu kwanakin dab suke da ƙarewa, rayuwar da babu matallafa ba tsayi takedashi ba, ku tashi kuje, an fita da shi kome ya ƙare, Iƙilima da Sadiya za su cigaba da kasancewaayanda ku ke musu fata, ku fice mana a gida" ta idda maganan cikin rishin kuka tare da nunamusuƙofa.... Gaba ɗaya jikkunansu ne yayi sanyi da jin maganganunta, nan wasun su suka fara kuka wasunahaɗiyan zuciya, riƙota Babiya tayi tana na ta kukan, tare da faɗin "yi haƙuri Sadiya Allahnasaneda ku, ba yayi muku hakan da ba ya sanku ba ne, hasalima hakan wata ƙaunar ne, Allahnatareda masu haƙuri, ku yi haƙuri ku dangana ku godewa ubangijinku" jinjina kai tayi tare da sharehawaye, miƙewa Iƙilima tayi ta shige ɗaki ba ta jima ba ta fito sanye da ƙaramin hijab ta wucebakin murhu kunna wuta tayi ta koma ta ɗakko ƙaramin tukunya ta ɗaura bisa murhun, bandabin ta da ido me cike da tausayawa ba abinda suke, miƙewa ɗaya daga cikin ƙannin Baba tayi
tare da faɗin "Iƙilima me zaki yi ne?" "Ɗumame zanyi" tace a hankali murya a disashe, "jeki zauna, bari in miki" girgiza kai tayi tare da faɗin "in na zaunan ƙirjina bugawa da sauri da sauri yakekarku damu, Baba yace ba ya so a zauna mishi makoki" ta idda maganan tare da kauda kai....
"Ni ma ya faɗa mun, jira muke a dawo daga kai shi se kowa ya watse" jinjina kai tayi tare da
juyawa ga murhun, komawa tayi ta zauna a inda ta tashi jiki amace, kallonta Babiya tayi taredafaɗin "su yaran anan za'a bar su kenan?" Girgiza kai tayi tare da faɗin "a'a yanzu kamdolemutattauna a tsakanin mu su koma gidajen mu kafin Allah ya kawo musu na su gidajen" girgizakai
Sadiya tayi tare da faɗin "ba zamu koma ko ina ba, muna nan a gidan nan anan muke fatannamumutuwan ta riske mu" "a'a Sadiya daina magana irin haka mana, ku ɗiyoyi mata ne, ku na
buƙatan komawa gaban manya, zamanku a haka ba ze yuwu ba" Baba Mari tace cikin muryanrarrashi, fashewa da kuka tayi tare da faɗin "ba inda zamu mu samu kwanciyar hankali BabaMari, su barmu a inda suke ganin mu mun gode, lokacin da mahaifiyar mu ta rasu, mahaifin munaakulle ba wanda yayi tunanin mu ɗiyoyi mata ne wani abun na iya faruwa da mu ya kai mugidanshi dan tsira da mutumcin mu, mu kaɗai muke rayuwa a gidan yanda Allah ya tsare mu a wancanlokacin haka ze tsare mu a wannan ma, mun gode wallahi, su bar mu nan ne rufin asirinmu, zafinrayuwar baya be sa mun kauce hanya dw iyayen mu suka nuna mana ba, haka wanda ze zoagaba in sha Allah ba ze sa mu kaucewa ba" ta idda maganan tare da miƙewa ta shige ɗakinsu.... Bin ta da ido suka yi ba tare da ganin lefinta ba, da babu ƙarya a dukkanin furucinta, da nasulefin, to ya za su yi? suma a ƙasan wasu suke, sannan mazan cikinsu babu me ƙarfin riƙe sukowafama da na shi yake, duk da rashin ɗaukan zumunci da mahimmaci ya taka rawar gani, "a gaskiyakun taka rawar gani sosai a irin kallon da yaran nan suke muku" Babiya tace cike da gaskiyanta, shiru suka yi ba tare da ko wani motsi dan kare kawunan su ba, dan sun san maganganunsugaba ɗaya na kan hanya, muryan da ko a mafarki suka ji za su sheda me shi ne ya doki
kunnuwansu cikin nema musu aminci.... A firgice Iƙilima ta ɗago kai ta watsa ido a bakin ƙofan shigowa, ilai kuwa itan ce sanye dawani
arnen abaya da kallo ɗaya zaka mai kasan ya gama cin kuɗi, ta caɓo ado kamar zata gasankyaujaka saɓe a kafaɗa gashin ido da wanda ta ƙara a kai sun ba zu se ɗaukan ido suke, takalminnankuwa a sama saboda tsaban tsini, babu wani alhini a fuskanta dan dagani ba ta san da labarinmutuwan ba, banda bin su da ido ba aninda take da alamu ta fara shan jinin jikinta....
Babu wani mamaki a saman fuskan Iƙilima da ta gama ƙare mata kallo ta saki wani guntunmurmushi me ciwo tare da faɗin "ya mutu, wannan bawan Allahn da ki ka daɗe kina fata daƙaunar ganin mutuwanshi yau Ubangijin shi ya raba gaddama ya amshi abin shi, kin ji daɗi?"....
Ta idda maganan fuska faɗaɗe da murmushi, zuba musu ido jama'an dake wajen kawai sukayi
suna kallon ikon Allah dan sun kasa fahimtar inda kalaman Iƙiliman suka fuskanta, Farisat daYasmin kuwa banda bin ta da kallon kyama da tsana ba abinda suke, Babiya kuwa kallontausayi
take bin ta da shi dan ace wanta abar tausayi ce ita, ɗaga ƙafa tayi da niyyan takowa ciki muryanSadiya da ba wanda ya hankalta da fitowanta ya doki kunnuwan su a tsawace....
Tana fita, driver da ya hangi fitowanta ya iso da sauri tare da tambayanta fita za su yi, jinjinamai
kai tayi tare da sakin mai murmushi, ba musu ya wuce inda motan ta da Ibrahimya ba shi keytundawowanta ya mata key ya fiddota, har inda take tsaye ya jawota fitowa da sauri yayi ya buɗemata ƙofa, shigewa tayi a natse tare da jinjina mai kai, da sauri ya koma ciki ya danna hornɗinsanar da fitan su ya nufi gate a natse, da azama security's suka nufi na su motocin suka bi bayansu, waigawa baya tayi a natse, ganin su a bayansu ya sata sakin murmushi tare da maida dubantakan hanya.... Kai tsaye Insoul suka nufa, suna ƙarisawa aka wangale musu ƙofa babu wani dogon bincikesukashige ciki, yana dai-daita parking ya ɓalle murfin bangarenshi ya fito, ko kafin ya kai hannugaƙofan ɓangaren da take ɗaya daga cikin security's da ya nufo wajen da sauri ya buɗe mata, fitowa tayi a natse tare da jinjina musu kai ta zaro waya a natse ta nemi number ta dannakiratakara a kunni....
Ringing biyu ya ɗaga cike da gajiyan da ya kwaso "boyfriend" tace a hankali, "oh brother Sadamya karya alƙawari, shikenan na iso ina cikin Insoul, na so se na huta ne in kira ki in yi surpriseɗinki" ya idda maganan cike da gaskiyan shi, murmushi ta saki tare da faɗin "ka kyauta, gani acikinInsoul" zare ido yayi daga ta can tare da faɗin "girlfriend ba ta ƙarya bare in ce tayi ƙarya, sannanba ta zolaya bare in ce ta zolayeni ne" "to ka fito mana se ka ban-bance wanne a ciki na fara" tayi
maganan murya cike da murmushi, miƙewa daga kan gadon da yake kwance yayi zumbur yaficewaya kare a kunnin shi, tun daga balcony ɗin su ya hangeta tsaye security's tsaye a bayantamurmushi ya saki tare da fara sauka a natse ba tare da ya cire wayan a kunnin shi ba...
Yana ƙarisawa wajen yace "yanzu Labib ya gama gulmanki akan ki na jin isowana zaki zo" murmushi ta saki tare da faɗin "gaskiya ya faɗa ai" "ya daughter?" Yace fuska faɗaɗe da
murmushi, "na barota tana barci, ina Labib ɗin?" "Ya tafi fili za su buga wasan ƙarshe a gasandasuke yi" "wuh ba sanya kenan, kai wai yanzu ma kana wannan wasan kuwa?" Tace tare da kamahaɓa, "tsohon labari na zubar tun ranar da na samu daughter, ai na girma" yayi maganandaiyagaskiyan shi, murmushi ta saki tare da faɗin "gan-ganci ne wannan, in ya zo muku a test fa?"
"Shikenan se in faɗi" yace tare da sakin murmushi....
Juyawa ga security's tayi cike da kamewa tare da faɗin "in ba damuwa ku jirani a nan zamushigaciki" jinjina mata kai wanda alamu ya nuna shine babba yayi tare da faɗin "please in da watadamuwa ki yi gaggawan sanar mana" jinjina mai kai tayi suka wuce a jere, "yau kuna da lecture'sfa" yace a natse, kallon shi tayi da mamaki tare da faɗin "ya aka yi haka?" Ɗaga kafaɗa yayi tareda faɗin "na iso ban tadda Nachma ba, da na kira ta ta sanar mun tana class" "oh Allah kasanarda ita zuwana garin ne!" Tace da damuwa, "no" yace tare da kallon ta, jinjina mai kai tayi taredafaɗin "bari in leƙa class ɗin" ba musu ya dafa mata baya dan rakata....
"Yana ga yanayinki ya sauya ne?" Yace da kulawa tare da kallon ta, kallon me ka gani ta mai tareda kauda kai, "kin yi sanyi da yawa, what's wrong?" Sauke numfashi tayi tare da faɗin "zaniyacemaka abu biyu ne, da me daɗi da akasin shi" ta idda maganan tare da kallon shi, "fara ba ni
akasin me daɗin se ya kauda mun da akasin" yace tare da ja ya tsaya, girgiza kai tayi tare dafaɗin"ba na jin ze iya tafiyar da shi da sauri"....
"Me ne ne?" Yace a natse, "Baba ya rasu" tace a hankali, fiddo ido waje yayi da ɗokacin mamaki
tare da faɗin "ki na nufin Baba na Bertuwa! Baban su Anty Iƙilima da Sadiya!" Jinjina mai kai tayi
cike da jimami, "inna lillahi wa inna ilaihirraji'un! Yaushe?" Yace a hankali, "yanzu babu daɗewa, su Yaya ma sun koma" "Allahu Akbar Allah ya gafarta mai, lallai anyi rashi babba" yace a sanyaye, jinjina mai kai tayi tare da faɗin "ubangijinshi ya raba gaddama" jinjina mata kai yayi a mugunsanyaye.... Murmushi ta saki tare da faɗin "mu saka shi a cikin addu'o'in mu ze fi buƙatan hakan" "inshaAllah yana ciki" yace a hankali, "Uncle ya farfaɗo" tace a hankali tare da kallon shi, zaro idogabaɗaya waje yayi tare da faɗin "da gaske!" Jinjina mai kai tayi tare da sakin murmushi, "wayyoAllahdaɗi! Yace tare da rufe bakin shi da tafukan hannayen shi, murmushi ta saki tare da juyawatacigaba da tafiya, "subhanallahi girlfriend ya ganki!" Yace a zumuɗe....
"No yana barci ai" tace a natse, "kai amma na daɗe ban ji labari biyu da suka rikitani haka ba, rayuwa kenan" yace a hankali, "tashin wani faɗin wani" tace tare da kallon shi, jinjina matakai
yayi tare da faɗin "Allah ya jiƙan Baba shi kuma
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 72 Chapter of 109