koka...
"Yaji faɗuwan da tayi da shanyewan da rabin jikinta yayi, se dai be ji mutuwa ba se yau a bakinSa'adatu da tunda aka kawo shi ba ta zo ba se yau, goge hawaye yayi ya miƙe tare da damƙemaganin da ta saka mai a aljihu ya fice....
Tana fita daga prison ɗin ta saki murmushi tare da tuna shuɗaɗɗun abubuwa, tun da ya matawannan dukan ta ɗau alwashin gudu ta barsu, se dai ya hana hakan faruwa, ya rufe ko wani ƙofa, ta daɗe ta na fakon hanya amma ba ta nasara, ranar da Mama ta tafi biki ranar ta ji ko ta yayaseta bar gidan, har ta fara haɗa kaya zuciyanta ya bijiro mata da wani abu, tashi tayi ta nufi indaMama ke ajiye kuɗin siyayya in anyi, saboda siye da siyarwa take, ɗaukan ɗari biyar tayi tanufi
chemist ɗin anguwarsu, maganin barci ta siyo me ƙarfi, tana zuwa ta ɗau kofin sulbanshi daakesa mai ruwa ta ɓalle su duka ta jiƙa, suna narkewa ta ƙara ruwa a kai ta bawa Sa'adiyya datakai
mai abinci ta kai mai... Haka tayi ta dakwan jira, jin Sa'adiyya na sallaman shi za ta tafi islamiyya be ce komai ba yasatasakin murmushin nasara, tana ficewa ta shige ɗakin ta sauke labule, ta saɓule mai dogonwandoda na ciki, yage kayan jikinta tayi ta dagashi ta kwanta a ƙasanshi ta haɗe jikin su tare da sakinihu da ƙarfi, "a ce ce ni, ze mun fyaɗe, wayyo Allah na na shiga uku, Mama, Anty Iƙilima, jama'ananguwa ku cece ni, wayyo Allah na shiga uku na lalace, Baba, Baba dan Allah kar ka aikatamunhaka, dan Allah kar ka cutar da rayuwata wayyo Allah na, na shiga uku na lalace, ze tarwatsamunrayuwa" irin wannan kalaman ta dinga ihun faɗi, kafin kace me mutanen anguwa sun cikagida, duk wanda ya shigo ya tadda su a yanda suke se ya juya da sauri yana furta "wa iya zi billah" ganin jamma'an da take son su sheda sun sheda yasata ture shi da ƙarfi ta jawo riga, ta nakukame taɓa zuciya, a wannan yanayi Mama ta shigo, ganin Baba sintir ya sa ta ciro zanin dakesamanigiya ta lulluɓa mai jiki na ɓari, banda kuka ba abinda take, faɗowa Iƙilima da tun a ƙofar gidaakasamu me mata bayani tayi a rikice tana shigowa ta zare na ta zanin ta lulluɓawa Sa'adatutaredazubewa a wajen.... Bayan watsewan mutane Yayinta biyu da suka dawo suka tadda batun suka mata lilis, bandakuka ba abinda Mama take, nan tace a bar maganan kar a ƙara tadawa, ita har ta manta batunma se ga Anty ta zo saboda wata maƙofciyarsu da ta kai mata labari dan tasan ta akan wannanba ta da wasa, nan labari ya dawo baya, ba yanda Mama ba ta kwaɓeta akan karta cewa Anty
komai ba amma se da ta furta, har duƙawa tayi ta roƙeta tana kuka, amma ganin dama neyazomata har gida ya sa ta hanɓare duk wani roƙon da ta mata ta ma Anty bayanin ƙanzan kuregenda ta tsarawa kanta, nan aka faɗa court, duk wani abu me mahimmaci Mama ta seda ta balauyadan ya fidda Baba amma ba suyi nasara ba, se da aka tura shi prison, ranar Mama tayi kuka, tatsine mata ta la'ance ta amma ko a jikinta, dan ita fa daman da ta samu tayi amfani da shi, yanzuza ta samu daman baje kolinta san ranta, ta kan je duk inda take so ta yi abinda ta ke so MamakoYayyinta ba su taɓa ce mata dan me ba, ba abinda yake shiga tsakaninta da su, kaman zamankanta take.... Ba ta taɓa tunanin barin gida ba duk wannan abinda ya faru se ranar da Anty ta zo dubata, ganinta yanda aka wareta ba me shiga harkanta yasata yin mata tayin komawa gidanta, duniyasabuwa, nan taji cewa lallai basiranta me amfani ne, ba wanda yace ma Anty komai, bintasukayi da ido, har Sa'adatu ta tattara komatsanta suka fice....
Sauke numfashi tayi saboda jin wayanta na ringing zarowa daga aljihun doguwar rigantatayi
ganin Sudais ya sata ɗagawa ta kara a kunni, "sky hotel, room 23" kawai yace ya katse kiran, wani nagartaccen murmushi ta saki ta maida wayan ta tari me napep....
Comments fans🥰🙏
🫀MUGUWAR TSOKA 🫀
{🫀TA'ARE KALLUƊE}
[Muscle Cramp🫀]
) عضلة سيئة (
🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
written and Created ~~~~~~~~~~~~~~ ِبسم الله الرحمن الرحيم
By
Yardajjiya👩 💻
Page. Twenty
Winking ɗin idonta tayi tare da sakin wani nagartaccen murmushi, ita kanta ta gama burgekanta, sanye take da dogon wando wanda ake kira da skin tight blue black, se t-shirt wanda yayi mugunamsan jikinta milk colour, brown ɗin abaya ta saka a sama tayi rolling ɗin veil ɗin shi a samankai,
fuskan nan ya ƙawatu da simple make up.... Duƙawa tayi ta ɗaure igiyan takalminta me tsini, ta ɗago ta ɗauki jakanta ta saɓa a baya taɗauwaya ta fice a natse,... Tana idda sauka daga stair's ta sakin ma Lawiza dake bin ta da ido murmurshi tare da faɗin"goodmorning Anty Lawiza" tayi maganan tare da wuce wa ɓangaren dining, murmushi Lawiza tasaki
tare da bin bayanta cike da kulawa tace "kin so makara" zare ido tayi tare da juyowa cikinɗanjintsoro tace "ki ka ce 8:30 ne shiga" "eh" tace tare da sakin murmushi, "to yanzu ai 8:00 ne dubaagogo" tace tare da nuna mata tamfatsetsen agogon dake manne a bangon parlourn... Murmushi ta saki tare da faɗin "to hanzarta bar magana" tayi maganan tare da zaro plate, "ganingasashshen bread da cow leg yasa ta faɗin "zuba kaɗan" tayi maganan tare da ɗaukan
gasashshen bread ɗaya ta ɗau spoon a natse ta gyara zama, "a zuba mongo juice ne?" Tacematada kulawa....
"No ruwa ma ya isa" tayi magana tare da ɗiban kaɗan ta kai baki, "please zauna" tace taredakallon Lawiza dake tsaye a gefenta kaɗan, murmurshi ta saki ta ja ɗaya daga cikin kujeruntazauna tare da faɗin "yau ne ranar farko da za ki halarci class dan Allah ki natsu sosai in baki
fahimci darasin yau ba ba lallai ki fahimci na sauran ranakun ba" ta idda maganan cike datsantsan kulawa, murmushi ta sakin mata tare da kai kofin da ta tsiyaya ruwa baki, ta na saukewatazari tissue ta goge baki ta miƙe tare da faɗin "abinci yayi daɗi sosai, Allah ya ƙarawa hannunki
albarka" murmushi ta sakin mata tare da faɗin "ya ma na ki hannun kema, kin yi matuƙar kyau" kallon diƙiƙu ta mata tare da kauda kai ta ɗau wayanta ta bar wajen...
Kai tsaye wajen hoton su ta nufa, bin hoton da ido tayi kamar a ranar ta taɓa ganin shi, murmushi
ta saki me tattare da ma'anoni tare da kai hannunta baki ta sumbata, shafa hannun a samankumatun Anty tayi tare da faɗin "yau Anty Lawiza ta riga ki cewa nayi kyau Anty" tayi magananhawaye na taruwa a idanunta, "ke ce me fara yaban ƙawalliyata in nayi, ke ce me nunashsheni
hanya a duk lokacin da na tunkari wani abu me mahimmaci, se dai yau ba ki kin yi nisa dani" tayi
maganan hawaye na sakkowa a saman kumatunta...
"Kin san wani abu Anty? Ina ga Anty Lawiza za ta maye gurbin wannan, dan a wani zubinkalamanta na kamanceceniya da na ki, I'm proud of her, because she is care of me, tana kuladani
sosai fa, fiye da yanda zaki hasaso" ta tsahirta idonta ƙyam akan hoton...
Shafo hawayen dake zarya a saman kumatunta tayi tare da sakin murmushi me faɗi cike dayanayinta tace "auf Anty dubi ina ɓata kwalliyan kuma" tayi maganan tare da nuna mata
hannunta, dukan kanta kaɗan tayi tare da faɗin "na san me zaki ce rigimammiyan yarinyako?" Tayi maganan tare da zare ido, murmushi Lawiza da hawaye ke zarya a saman kumatuntatasaki
tare da sharewa....
"To duk ba wannan ba Anty yau zan fara ɗaukan darasi, Anty Lawiza ta hutashshe ki, tayi munnasihan da na san in kina kusa shi za ki yi, Allah ya gafarta miki yasa kina cikin aminci byesenadawo" tana kai nan ta juya inda Lawiza take ganin yanda hawaye ke tsere a saman fuskantayasa ta zare ido waje tare da faɗin "ke ma saurin kuka ne da ke?" Juyawa da sauri tayi ta zari tissuetayi inda take ta miƙa mata tare da faɗin "goge" ba musu ta amsa ta fara goge fuska...
"8:15" tace tare da nuna mata agogo, juyawa tayi da sauri ta fice, dariya ta saki tare da ɗaukanbottle ɗin ruwa ta bi ta da shi da sauri...
Tana fita ta hango Ibrahim tsaye da alamun ita yake jira, da sauri ta gangara tare da faɗin"Ibrahim muje mun kusa makara" "kin ɗakko ID card ɗin ki?" Yace tare da kallon ta, "eh yanajaka" tace tare da buɗe kofan me zaman banza ta shige, da sauri Lawiza ta ƙariso ta miƙa mataruwan tare da faɗin "kar ki zauna da yunwa please" jinjina mata kai tayi tare da faɗin "Ibrahimmuje" ja baya tayi ya shige ya ma motan key ya nufi gate da sauri ...
Suna ficewa gate ɗin ta juya dan komawa ciki, "da wuri kenan za ta je?" Baba Maude daketsayeabayanta tace tare da sakin murmushi, da sauri ta ja baya dan ba ta san da tsayuwanta ba taredafaɗin "wai ai har na tsorata Baba Maude, ban san da tsayuwar ki ba" "ai tunda ta fito naketsayeba ta hankalta dani ba, kin san ance hankali ke gani ba ido ba, to hankalin na gare shi" ta iddamaganan fuska faɗaɗe da murmushi, murmushi Lawiza da ba ta fahimci inda maganan natayadosa ba ta saki tare da faɗin "hankalin ya kaɗa can, ta kusa makara ne" tana kai nan ta wuce...
Tsaki Baba Maude ta ja me ƙarfi tare da faɗin "dan Allah ji ni da mara sanin ciwon kai, yarinyataɗau ado haka kaman zata gasan fidda gwanin kyan duniya ki barta ta fice da mijinki, sannansaboda galbace ke har da rakota ki na mata fatan sauka lafiya....
"Muje dai zuwa, za ki fahimta ne a hankali, Allah yasa kafin ki fahimta kar lokaci ya ƙure miki" tana kai nan ta juya ta nufi side ɗin su..... Nuna ID card ɗinta tayi tare da kallon security's ɗin, buɗe musu hanya suka yi cike da
girmamawa, kai tsaye parking space ɗin school ɗin yayi, sakkowa tayi da sauri tare da faɗin"se5pm fa" jinjina mata kai yayi tare bin ta da ido har ta shige department ɗin su na ƴan
international law, dan shi aka zaɓa mata, murmushi ya saki ya shige motan ya mata key yajuyaya nufi barin makarantar.... Tura ƙofan shiga calss ɗin tayi a natse ta shige baki ɗauke da sallama, baza mata ido student'sɗin suka yi cike da yaba kyawunta, bin class ɗin da ya ji kujeru da tebura na alfarma tayi daidocike da burgetan da yayi, ko wani teburi kujeru biyu ne zagaye da shi, ba matsi ba takuri cikedatsari....
"Bismillah" yarinyar da tayi mata yaƙin shiga office ɗin registerer tace tare da nuna matakujeran dake kusa da na ta, murmushi ta saki tare da takawa ta ja kujera ta sauke jakanbayantata zauna tare da ajiye wayanta a gabanta, murmurshi ta sakin mata tare da ba ta hannua natse, zaro na ta tayi ta ba ta fuska kadaran kadahan, "kin gane ni kuwa?" Tace idonta a nata, murmushi
ta saki tare da faɗin "ina ta ma fuskan kallan sanni, se dai ban san a ina ba" murmushi ta saki tareda faɗin "a office ɗin registerer" "oh yes ke ce?" Tace tare da sakin murmushi, jinjina matakai
tayi tare da sakin murmushi....
"Daga ina ki ka zo?" Tace tare da gyara zama, "daga Yarban" tace a natse, ƙaramar dariya tasaki
tare da faɗin "ki ce shiga tsakanin ƴan gari ɗaya na yi" murmushi ta saki tare da faɗin "aikuwa, kefa?" "Bertuwa, na ji daɗin haɗuwa dake sunana Insu" murmurshi ta saki tare da faɗin "sonice, myname is Nachma" murmushi Insu ta saki tare da faɗin "wow sunan yayi min daɗi sosai fa"...
"Be kai na ki ba" tace tare da sakin murmushi, turo ƙofan da vice chancellor da deputy chancelloradmin da lacturer's uku su kayi ya dakatar da Insu dake shirin magana, tsitt suka yi tare dabinsuda ido.... Murmushi Abubakar ya saki ganin yanda Insu ta kame kaman ba ta san shi ba tare da faɗin"student's" "yes sir" suka ce da ƙarfi, gyara tsayuwa yayi tare da faɗin "kun san abinda ya kawoku nan ko?" "Yes sir" suka kuma cewa bakuna a haɗe, "to ku gayyato jajircewa da juriya danatsuwa a duk inda suke ku ƙulla amintaka na har abada da su, ba ma haɗa hanya da wannanbeshirya inganta rayuwar shi ba, maida hankalin ku shi ze sanar damu kun shirya ko ba kushiryaba"....
"Akwai abinda yakamata ku sani wanda sanin shi na da matuƙar mahimmaci a gare ku, kubuɗekunnuwa da kyau ku saurari abinda zan faɗa, duk wanda grade level ɗin shi na ƙarshensemesterya kai 1.49 or down ba ze wuce 200level ba, sannan har in ya ƙara maimaita hakan makatantazata sallame shi dan be shirya karatu ba" jinjina kai suka yi jikkuna a mace, "kun fahimta?" Yacetare da bin su da ido, "yes sir" suka ce cike da tabbatarwa....
"Okay muna ma ko wannen ku fatan wucewa, yanda ƙoƙari ya kawo ku muna fatan shi zefiddaku, ga lecturer's ɗin da za su dinga baku lecture's nan akwai barrister Sabi'u Khamis, ga barrister
Tiyo Emanuel, se barrister Shamsudden Alhasanu, sune za su ba ku lecture's a wannan shekaran, ku dage wajen kwasan ilimin da za su baje muku, muna matuƙar alfahari da ku" ya idda maganantare da sakin musu murmurshi, "thank you sir" suka ce baku a haɗe....
"Alright deputy chancellor admin bismillah a basu oath" Abubakar yace tare da kallon nakusada shi, ba musu ya gyara tsayuwa tare da ɗaga hannu, ɗagawa suka yi cike da natsuwa, rantsuwaya ba su na za su yi karatu da gaskiya da amana kuma zasu tabbatar da gaskiya a ayyukansu, yana gama ba su ya kalli barrister Tiyo tare da faɗin "za mu barka anan, all the best" jinjinamai
kai yayi cike da gamsuwa, juyawa suka yi suka fice a natse....
Juyawa ga white board ɗin dake gaban bangon class ɗin yayi tare da ɗaukan white boardmarkern dake ajiye a gefe ya rubuta(law), juyowa gare su yayi tare da faɗin...
"Who among of you tell me the meaning of law?" Ya idda tambayan tare da bin su da ido, miƙewaɗaya daga cikin maza yayi tare da faɗin "gaskiya" murmushi ya saki tare da mai alamunyazauna, miƙewa ɗaya daga cikin mata tayi tare da faɗin "jajircewa akan gaskiya" jinjina kai yayi taredamata alamun ta zauna, tashi wani daga cikin maza yayi tare da faɗin "kawar da zalunci" murmushi ya saki tare da mai alaman ya zauna, tashi Nachma tayi tare da faɗin "fidda gaskiyadatsayuwa akan shi" murmushi ya saki tare da mata alamun ta zauna,.... Miƙewa Insu tayi tare da faɗin "Justice" "good, good kun ji abinda tace?" Yace da ƙarfi, "yes sir" suka ce bakuna a haɗe, "me tace?" Yace da ƙarfi, "Justice" suka ce da ƙarfi, "Justice, wannanshine law, adalci shine law, tabbatar da adalci shine law, duk kunyi bayanin da yaja hankali na,
hakan kuma ya sa na ji alfaharin kasancewa ɗaya daga cikin waƴanda za su samu lokaci daku, dan haka wannan kalmar ita ce mabuɗin buɗe darasin mu na yau" alama ya ma Insu da tazaunaya juya ga white board.... Be samu fita ba se da 12:00pm ta buga, sallaman su yayi ya fice a natse, mimmiƙewa sukayi cikeda gajiya suka fara fita, kai tsaye sculpture garden Nachma ta kai Insu dan yanda ta ga gajiyannanuƙurƙusanta, "wow" Insu tace tare da bin haɗaɗɗen garden ɗin da ido, duk wani abu na
burgewa da jan hankali an zuba a garden ɗin, zare takalmin ƙafarta tayi ta zauna a samangrassɗin da ke samun kula na musamman, murmushi Nachma ta sakin mata ganin yanda ta lumsheido tana amsan yanayin da wurin ya zo mata da shi, "bari in amso mana drinks a shop" tayi
maganan tare da juyawa ta fice.... Wani ni'imantaccen iska da ƙamshi flower's ne ke dukan saman fuskanta da hancinta, ba kaɗanba taji daɗin yanayin, jiyo sautikan tsintsayen dake shawagi a sararin samaniya ya sa ta buɗeidota ɗaga kai sama, "wow" tace cike da mamaki tare da ware ido akan su, jawo wayanta tayi tashiga camera ta fara musu biyo, duk inda suka bi tana biye da su, "wow beautiful" ta jiyo saukanwani natsatstsen murya ya doki kunnuwanta... Sauke wayan tayi ta juyo a natse, tozali tayi da wani kyakykyawa saurayi me kimanin shekaru26da haihuwa yana sakin mata wani nagartaccen murmushi me cike da ɗin bin kulawa, ....
"You said something?" Tace idonta ƙyam a kan shi, murmushi ya saki tare da fara takowa anatse, se da ya zo gab da ita ya ja ya tsaya tare da ƙasa da murya kaman me gudun a ji shi yace, "didyouknow that you are beautiful?" Ya jefa mata tambayan cikin soft voice ɗin shi idon shi na yawoasaman fuskanta, guntun murmushi ta saki tare da faɗin "i know" "wow I saw" yace tare dajanyefuskan shi...
"You saw what!" Tace da mamaki, "just forget I'm Khalim" ya idda maganan tare da miƙa matahannu, bin hannu tayi da ido kafin ta saki murmushi ta juya ta nufi inda ta baro takalmi dajakanta tare da faɗin "Insu" "wow nice name" yace muryanshi na bayyana murmushin da yasaki, murmushi ta saki tare da faɗin "i know" tana kai nan saka takalminta ta saɓa jaka ta nufi barinwajen, saurin dafa mata baya yayi, tana fita ta tadda Nachma dake ƙoƙarin shiga...
"Oh sorry na daɗe ko, wallahi akwai mutane ne da yawa, "no problem, yakamata muje cafeteriamu samu wani abun mu ci, dan na fara jin yunwa" "okay muje" tace tare da ƙoƙarin zaro wayantada ta jiyo ƙarar shigowan text, "ba za ku samu irin abincin da ku ke so a cafeteria ba, ammanasan inda za ku samu kalan na ku, a mun lamuni ko sau ɗaya in ba damuwa" Khalimda ya isowajen yace tare da kallon su, da mamaki suka zuba mai ido, "no ba za'a fita cikin school ba, aciki
ne" yace tare da sakin murmushi, murmushi suka saki ba tare da sun ce komai ba, "muje ko" yacetare da kafesu da ido, "muje" Nachma tace tare da kallon shi, "Khalim" yace tare da ba ta hannu, "Nachma" tace tare da jan hannun Insu suka ja gefe, murmurshi ya saki gane abinda hakankenufi, shigewa gaba yayi suka dafa mai baya....
"Ina waiter's na kawo muku costumer's a zo a karramasu" yayi maganan tare da nuna musukujeran zama, zaunawa suka yi a natse, da sauri suka kawo musu ruwa da lemu tare da
marabtansu cike da kulawa, murmushi waitern dake riƙe da littafi ya saki tare da miƙa mai
littafin a natse, murmurshi ya saki tare da faɗin "ka kiyayeni Ibrahim" yana kai nan ya zaɓi abindayake so ya ajiye ma Insu a gabanta, tura ma Nachma tayi idonta da hankalinta na ga dubasaƙonda Yasmin ta turo mata....
"Kin ce fa kina jin yunwa" Nachma tace tare da kallon ta, "eh zaɓan mun founded yamya isheni" tace ba tare da ta kauda ido daga waya ba, "okay" tace tare da zaɓa ta miƙa mai, ba su jimabaaka kawo musu abubuwan da suka zaɓa, "to Hajiya me waya a ajiye ga abinci ya iso" Khalimyacefuska faɗaɗe da murmushi, murmushi ta saki tare da ajiyewa ta ba wa abincin natsuwanta...
Se da ta cin fir rabi sannan ta ja baya ta zari tissue, "duk sanki da shi ba zaki iya cinyewa ba?" Khalim yace tare da kallonta, "I'm okay" tace tare da shafa ciki, murmushi ya saki tare da faɗin"wannan taɓawa kawai ki ka yi" murmushi ta saki tare da kallon Nachma da ta ajiye spoontareda faɗin "hanzarta lokacin sallah ya gabato" "na gama" tace tare da kai lemu baki, "okay muje" tace tare da miƙewa, "kun san inda masjid ɗin yake ko?" Khalim yace da kulawa .... Murmushi ta saki tare da faɗin "eh" "no kar ku ga lefina, kun san yawancin newcomer's basusani
ba se an nuna musu" murmushi Insu ta saki tare da faɗin "mun sani" tana kai nan ta wucewajenbiyan bill, tana cikin ƙoƙarin fiddo atm a jaka ya miƙa na shi da ya ciro a aljihu, "no" tace taredagirgiza kai, murmurshi ya saki tare da faɗin "ba shi ne zaki biyani gobe" murmurshi ta saki tareda maida jakan ta zage ta saɓa.... Har bakin female mosques ya kai su ya wuce na maza, kai tsaye wajen alwala suka wuce sunaidarwa suka shige masjid suka kabbarta sallah, bayan sun idar da azkhar suka fito a natse, "ohdubi Khalim mu yake jira ina ganin" Nachma tace tare da nuna mata shi, kallon wajen tayi taredafaɗin "ya samu aiki kenan" suna ƙarisawa ya sakin musu murmushi tare da faɗin "se ina?" "Class, muna da lecture 1:30 to 40pm, ga shi 1:20 yanzu" murmushi ya saki tare da faɗin "okay ni mainada shi 2 to 4pm" "level nawa?" Tace tare da kafe shi da ido, "300level" "wow dama mu ne fa, kafara jiyo ƙamshin ƴanci" murmushi ya saki tare da faɗin "kuma kaman yau ne ai" "i know" tacetare da jan hannun Nachma suka nufi barin wajen, "wani course ku ke karanta?" Yace da ƙarfi, "international law" Nachma tace da ƙarfi, "wow department ɗin mu ɗaya" yace da ƙarfi taredaƙoƙarin bin su....
Dafa kafaɗan shi da yaji anyi ne ya sa shi tsayawa tare da saurin juyowa da riƙe hannundaƙarfi, sauke numfashi me ƙarfi yayi tare da faɗin "ka tsorata ni Junaid" "kai dai matsoraci ne, inatajiranka a sculpture garden ba ka zo ba" harara ya zabga mai tare da faɗin "bayan ka barni senemanka nake kamar mara aikin yi ko?" "No maida wuƙan ina can ciki, wajen bishiyoyinmango"
"to da haka kamun kwatance ai ba zan sha wahala ba, "okay muje masjid lokaci yayi" "ka jedai nadaɗe da gabatar da nawa, ka same ni a class" yana kai nan yayi hanyar department ɗin su.... Kai tsaye class suka koma, zaman su ba daɗewa barrister Shamsudden ya shigo ya fara bajemusu baiwan da Allah ya mai, sosai suke ganewa dan ya san salon fahimtarwa, be fita ba seda4:00pm ya buga, "wash na gaji sosai, daga nan se gida ko?" Insu tace tare da sakin hamma, "baki
shiga sport ba ne? Akwai sauran awa ɗaya da yayi saura, na wasanni ne" Nachma tace taredakallonta, "ba na jin na shiga" Insu tace da mamaki, "okay mu fara zuwa ki zaɓa se mu wucedramavillage" jinjina mata kai tayi suka tashi suka fice a natsa, kai tsaye wajen shigar da wasandakakeso suka yi, tsayawa a gefe Nachma tayi ita ta shige, "na zo zaɓan wasa ne" tace tare da zubemamutumin dake zaune ido, be ce komai ba se zaro register da yayi tare da tura mata gabanta, "rubuta sunanki anan" yace tare da zuba mata ido, rubutawa tayi ta mayar mai gaban shi, "munada football, handball, basketball, dance, song, music, goge, fiano, jita, gudu, tsalle, da sauransu, gashi nan ki duba se ki zaɓi wanda ki ke so"....
Ya idda mata bayanin tare da bin ta da ido, shirun daƙiƙu tayi idonta akan abinda ya ajiyemata, se da ta gana nazarta sannan ta ce "dance" jinjija mata kai yayi tare da faɗin "kin iya ko koyozaki
yi?" Murmushi ta saki tana tuna wa ce Insu a wannan fannin kafin tace "na iya" "okay tomzaabaki waƴanda zaki koya wa, kuma kina da daman buɗe group ɗinki na musamman, dan shigakowacce gasa da makaranta za ta haɗa" jinjina kai tayi tare da faɗin "zan iya zaɓan suna da kai na?""Sosai kuwa ki na da dama" yace da ɗin bin kulawa, "white dancer's" tace tare da kallonshi, murmushi ya saki tare da ciro file a gefe ya ajiye a gabanshi, biro ya dauka ya rubuta sunan, sannan ya tura mata tare da faɗin "ki rubuta sunan ki da irin rawar da ki ka iya, sannan daadadin
mutanen da ki ke so a cikin group ɗin" jinjina kai tayi tare da rubutawa, tana gamawa ta turamai
tare da miƙewa a natse ta fice....
Tana fitowa Nachma ta sakin mata murmushi tare da faɗin "me ki ka zaɓa?" "Ke me ki ka zaɓa?" Tace tare da kallon ta, murmushi ta saki tare da faɗin "waƙa, ina son waƙa sosai, Abbana nayawan ce mun ina da daɗin murya zan iya waƙa" jinjina mata kai tayi tare da faɗin "rawa" "wowrawa! Amma fa ze da ce dake" tace cike da tabbatarwa, murmurshi ta sakin mata ba taredatace komai ba, kai tsaye suka shige wajen....
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 26 Chapter of 109