Share this page
ɗaya ba sannan ya ja baya a hankali ya juya, yana shirin gitta gadonidon shi ya faɗa a kanta, kwance take tana ta sharan barci hankali kwance, wani nagartaccen murmurshi ne ya ƙwace mai, bin ta yake da idanu cike da mamaki, ta gama zazzage babbar maceta dawo ɗaka tana sharɓan barci hankali kwance, matsawa yayi a natse ya ajiye mata wayanasaman bedside drower, jan mata blanket ɗin dake ƙasan ƙafafunta yayi ya haye mata da shi, binfuskanta kawai yake da duba me cike nazari, "sorry" yace a natse tare da miƙewa ya fice.... Murmurshi ta saki ba tare da ta buɗe ido ba ta gyara kwanciya, tun da ya murɗo ƙofan ta farka, dan ba ta da nauyin barci, jin ƙarar da wayanta ya ɗauka ya sata zura hannu ta jawo ta ɗagatakara a kunni ba tare da ta duba me kira ba "Insu" muryan Ziyada ya doki kunnuwanta, buɗeidotayi da sauri tare da yunƙurawa ta miƙe, "kai! Wayyo duniya Ziyada ki na raye dama?" Tacetareda sakin murmurshi, "wallahi ina nan ya kike?" "Alhamdulillah ya Teacher!" Murmushi ta saki mefaɗi tare da faɗin "Teacher na matuƙar kewanki" "wayyo ce ne mai Insu na nan tafe" "in shaAllahba zan manta ba" tace murya cike da kewa, "ya Momy?" "Tana lafiya, ke yanzu naga video's ɗinki da photo's na trending a media wai ke ɗiyar SSB ne, shine na ce bari in kira inji ina aka kwanaaragaya" dariya ta ƙyalƙyace da shi tare da faɗin "to wallahi ni ban ma san me duniyar ke ciki ba, na buɗe datan network ya ƙi haɗani da kowa".... "Wallahi ki duba ke har a gidan tv aketa fa sawa" tace cike da tabbaci "na shiga uku, mutanennan ba sa da hankali, ko da ya ke ai ɗiyar ta shi ce kar ki damu, please ki gaidamun da ɗalibanTeacher" "in sha Allah za suji" tace da kulawa, shirun daƙiku suka yi kafin ta kashe kiranbayansun ƙara sallama.... Sauke wayan tayi tare da faɗin "daughter!" Tayi maganan tare da kama haɓa, "oh AllahBabaMaude akwai ayoyin tambaya akan ki, bari in ɗan dawo da hankali na kan ki kaɗan, Allahyasakar ki rufta" tace tare da sakin murmushi, saka wayan a silent tayi ta juya kwanciya (to Insunmuasuba ta gari).... Da sauri ta sakko hankalinta gaba ɗaya akan agogon da take ƙoƙarin ɗaurawa a tsintsiyar hannunta, kai tsaye dining area tayi ta na isa ta ja kujera tare da faɗin "morning Uncle" tafaɗi tare da jan chair baya ta zauna, "morning" yace a hankali, jawo cooler tayi tare da faɗin "morninguncle's" "morning Insu" Abubakar yace tare da sakin murmushi, saurin ƙarisowa wajen Lawizatayi da ladabi tare da faɗin "me za ki ci?" "Oh barni in zuba da kai na, ya Umma da my Iman?" Murmushi ta saki tare da faɗin "suna lafiya" tayi magana tare da saka mata funkasau... Murmushi Jabir ya saki idon shi akanta, mamakin yanda ta sakko zuciya a wanke ƙyal babufushin da ta haura da shi jiya yake, ya ɗauka za ta sakko fuska a ɗaure, tana cika tana batsewa, "wow funkasau a she za'a jibgi fulawa" tace tare da gutsira ta dangwali miyan da ta ajiye mataamadai-daicin bowl ta kai baki, lumshe ido tayi cikin ɗanɗanon da miyan ya bata tare da faɗin"Allah ya ma hannun da ya inganta fulawa zuwa funkasu albarka, dan Allah uncle's ku ɗanɗanakar a barku abaya" tayi maganan tare da buɗe ido ta watsa musu.... Murmushi Ibrahim ya saki tare da kallon Lawiza dake kallon shi fuska yalwace da fara'a, "hanzarta lokaci na ƙaratowa" Lawiza tace da kulawa tare da barin wajen, gyara zama tayi tareda faɗin "Uncle yaushe zamu fara campaign?" Tayi maganan hankalinta a kwance tare dakai loman funkasu baki, da mamaki ya ɗago kai ya zuba mata ido cike da rashin fahimta, murmushi Jabir ya saki tare girgiza kai, ganin yanda tayi magana da dukkanin gaskiyanta ya sa Alhaji Munnir faɗin "au camping ma in za'a yi dake za'ayi?" "Eh mana uncle Munnir, na Uncle nefa, inbanyi ba wa ze mai, na san da Anty na da rai ita ce za ta yi ruwa tayi makarɗiya, ba ta nankumaai gani magajiyarta" ta yi maganan da iya gaskiyanta cike da yanayinta.... Jinjina kai yayi ya kauda ba tare da yece komai ba, kauda kai SSB yayi dan ya manta ma daanawani campaign sam se da ta faɗa yanzu, "to baiwar Allah ai ba yanzu za'a fara ba, se anyi primaryelection daga nan ne zamu ga ko za'ayi ko ba za'ayi ba" Abubakar yace da kulawa, "ai ya ci ma, kai yanzu kana ganin Uncle ba ze ci ba ne? To ka daina wannan tunanin ze ci, kasan saboda mene?" Ta je fa mai tambayan tare da zaran tissue ta fara goge hannu... Ganin yanda suka zuba mata ido ba tare da sun ce komai ba ya sata faɗin "saboda su sukakawoƙoƙon bara har gida, ba za su taɓa bari ya faɗi ba, saboda shi suke so ya hau kan karagan, baruwan Uncle da neman ƴan bangan siyasa saboda yana da shuwagabannin su a gefe za sukullada duk wannan ɓangaren" ta idda maganan hankali kwance tare da ɗaukan cup ɗin juice ɗintatakai baki.... Bin ta suke da kallo me cike da nazari, dariya ta saki tare da ajiye cup ɗin cike da yanayintatace"da ma za su kwantar da hankalin su ayi zaɓen lumana na san Uncle shine da nasara, ze basuwuta ya shige ta tsakiyan wutan ya fice fitt" tayi maganan tare da nuna yanda ze fice fitt dahannu, murmushi ya saki tare da kauda kai, ɗaukan wayanta dake neman agaji tayi ta karaakunni tare da miƙewa... "Hello Anty Lailah" tace tare da kallon Ibrahim, "kin tafi makarantar ne?" Lailah tace dagatacanɓangaren a natse, "a'a yanzu dai zamu tafi, da na ce yau zan biyo ta gidan ki, se dai yau munadakallon gasan ball, ina ga se ko zuwa jibi dan gobe ba zan fito school da wuri ba" "shikenanAllahya nuna mana, Yaya Sahabee ya dawo lafiya ko?" "Eh ya dawo lafiya" tace tare da marairaicemaIbrahim dake zaune yana cin abinci a hankali fuska.... "Dan Allah ki miƙa mana saƙon gaisuwa, kunyi magana da Yaya ne?" "In sha Allah, a'a meyafaru?" Tace da ɗan kulawa, "Salwa ne ta haihu jiya da yamma" "what! ta haihu! Dama AntySalwana da ciki ne?" Tace cike da zallan mamaki, "to mu ma babu me labarin cikin se haihuwa" tacemurya na bayyana shock ɗin ita ma da ta shiga da jin labarin, "tab ɗin jam, lallai Anty Salwaseabarta, to yanzu wa ze je kenan? Tunda Anty ta yi nisa" tace a ɗan sanyaye, zuba mata idogabaɗaya suka yi saboda yanda tayi maganan.... "Zamu tafi zuwa jibi, ni da Khadijatu, Yaya ma yace Farisat da Anty Habiba za su biyo bayanmu" "wow hakan yayi zan kira shi in roƙan ma Sahabee" "subhanallah" SSB yace tare da kaudakai, betaɓa jin wanda ya kira sunan kai tsaye babu sirki ba se ita ko a yarinta SSB shi a abokanshi kekiran shi da shi, a gida kuwa su Hajiya da su Jamil kuwa Khalifa suke ce mai, su Lubabatukumasuka bi bakin Insiyyat ɗin shi suna kiran shi da Yaya Sahabee, amma karon farko ya ji waccetakira sunan kai tsaye babu ko ɗarr, Insu kuwa da ba ta san halin da ya shiga ba kuwa cigabadazantukanta tayi.... "Shine be taɓa zuwa ba, yana son zuwa garin nan, in ya amince se ya biyo su Farisat, tundayazama comon entrance be fara zuwa secondary ba" "to hakan yayi se na ji yanda ku ka yi" tacedakulawa tare da sauke wayan, zame wayan tayi tare da faɗin "dan Allah Abban Iman ba ni keyintafi" harara ya banka mata ya miƙe ya sallame su cike da girmamawa ya fice, ƙarisawa indaSSBke zaune tayi ta rungume shi ta baya tare da faɗin "fatan wuni me cike da aminci Uncle" tanakai nan ta sake shi tare da ɗaga ma su Abubakar hannu ta fice da sauri.... Da kallon ƙasan ido ya bi ta har ta fice, sauke numfashi a hankali yayi ba tare da ya ɗagokai ba, murmushi Jabir ya saki tare da faɗin "maganan Insu ya na buƙatan nazari, duk wanda ya miƙomaka ƙoƙon bara akwai abinda yake son ka zuba mishi" "tabbas shiyasa hankalina ya kasakwanciya da mutanen nan" Alhaji Munnir yace cike da damuwa, "ku ba su ƙafa" SSB yace taredaɗago kai ya ɗau ruwa ya kafa baki... "Oh Allah wannan fa!" Tace da mamaki tare da nuna motan da Ibrahim ke ƙoƙarin hawa BMWcebulletproof, murmurshi ya saki tare da faɗin "gift mr president ya aiko miki dashi jiya bayan dawowan mu" "ni!" Tace cike da zallan mamaki tare da fiddo ido waje, "yeah" ke fa" yace taredashigewa, dariya ta ƙyalƙyace da shi tare da buɗe gefen me zaman banza ta zauna cike da yanayinta tace "wai shima tunanin shi ni ɗiyar Uncle ce?" "Eh mana" yace tare da kallontafuskawashe da murmushi, "amma a gaskiya ya wahala, Uncle ya san an kawo?" "Dama akwai wani abuda ze shigo gidan nan ba tare da izinin shi ba ne?" Yace tare da kallon ta, "tambayanka kawai fanayi" tace tare da kauda kai, murmushi ya saki ba tare da yace mata komai ba ya ma motankeyya ja suka fice.... Miƙa mai papern dake hannun shi Alhaji Munnir yayi tare da faɗin "list ɗin waƴanda mukebuƙatan canjin su ne, mutane 300, sun bautata ma campany da dukkanin abubuwan da yakamata, sun ba campanyn gudunmuwa fiye da tunani, zamu canza su ne dan suna buƙatanhutu ba dan mun gaji da kasancewa da su ba" ya idda bayanin cike da natsuwa, jinjina kai yayi tare da faɗin "a bincika idan suna da ƴaƴa waƴanda za su iya maye gurbukansu, a ɗauke su, idankuma ba za su iya ba a nemi gurbin da ya kamata a ba su, sannan a ƙara yawan ma'aikata akowani campanyn dan ƙorafi yana yawa" jinjina kai suka yi cike da gamsuwa, "amsu kuma asallame su dukkanin abinda ake sallaman ma'aikata" jinina kai Alhaji Munnir yayi saboda wannan aikin shi ne cike da fahimta, miƙewa yayi tare da faɗin "yakamata Abubakar ka kai ziyarawa mutanen ka" murmushi ya saki tare da fadin "satin da ya wuce ma na leƙa su, ba sa buƙatankomai, sanan an ƙara ma'aikata" ganin kallon da yake mai ya sa shi faɗin "teacher's an doctor'sse me kula da jaririrai, dan watan da ya shige mun samu baƙin jarirai biyu" jinjina kai yayi taredafaɗin "hakan yayi yakamata mu hanzarta tafiya inda yakamata" ya idda maganan tare da nufar ƙofa.... Dafa mai baya suka yi da tsan-tsan biyayya, suna ficewa, driver's suka mammatso da mota, sunaficewa motan escort's suka dafa musu baya.... Tana sauka ta yi department ɗin su kai tsaye, murmushi Nachma ta sakin mata cike da kulawa, jan kujera tayi ta zauna, tare da faɗin "ba ki da kirki ba kira ba message" murmushi ta saki me faɗi tare da faɗin "na ga wayan ta ci screen ne shiyasa ban kira ba" "oh haka ne fa, Uncle yacanzamun" tace tare da ajiye wayan a gabanta, "wow" tace tare da ɗauka cike da yabawa, ɗagokai tayi ta kalleta tare da faɗin "Uncle ko Daddy Insu?" Dariya ta saki tare da faɗin "ko wanne ki kaɗaukashine" "wallahi kin shammace mu, dama haka ki ke? Ni se jiya nake gani a labarai" murmurshi tasaki tare da gyara zama saboda shigowan da Barrister Tiyo yayi.... Ba su samu daman fita a class ba se biyu, kai tsaye masjid suka wuce, suna fitowa suka nufi restaurant, suna zama Khalim ya ja kujara ya zauna, ba abinda tace ba kuma tayi yunƙurincewanba, "Insu" yace da kulawa, ɗago wala-walan idanunta tayi ta zuba mai ba tare da tace komai ba, "i love you" yace kaman ze saki kuka, kauda kai tayi tare da faɗin "thank you" girgiza kai yayi tareda faɗin "ba haka nake son ji ba, please ki fahimce ni, na faɗa sanki tun ranar da na fara ganinki, wallahi matuƙar ƙaunanki na ke" ya idda maganan kaman ze saki kuka.... Murmushi ta saki ba tare da tace komai ba, "am ina ga Khalim ka bari zamu yi magana akanwannan" Nachma tace tare da kallon shi, girgiza kai yayi tare da faɗin "a'a Nachma, yakamatataji irin dakkon abun da nake a zuciyata, Insu wallahi sanki nake, I need you in my life" "I'msorryzancen farko ba ze canza ba, shine a salin gaskiyan" tace a natse, "ƙarya ki ke, ba wanda yaisamallakar ki you are mine" yace da ƙarfi tare da kafeta da ido, "please Khalim" Nachma tacetareda kafe shi da ido, jan kujeran da yake kai baya yayi ya miƙe ya fice zuciya na ƙuna.... "Meyasa ki ke haka ne Insu? Da gaske Khalim ke sanki, meyasa ba zaki ba shi dama ba, yakamataki san duk wanda ya furta mana kalman so ya wuce wulaƙanci har gaban abadan a wajenmu, sannan yafi wanda ke shakkan furta mana" Nachma tace da tsan-tsan kulawa, "please stopI don't like" tace tare da baza mata ido, "wai meyasa to?" "Saboda ba na so" tace idonta ƙyamanata.... "Okay" tace ba din ta gamsu ba, "thanks for understanding" tace a natse ba tare da ta kalletaba, "ba gamsuwa na yi ba dan ba yanda na iya ne" tace tare da banka mata harara, murmushi tasaki tare da faɗin "forget" "meyasa? Ikirarin sonki fa yake" "ikirarin hauka dai, inda aka ce ba'abuƙatan ka haƙura ya kamata kayi ka nufi inda ake yinka a tunani na dai" "gunda da ki ka ceatunanin ki" tace tare da sakin dariya, "mu ci abinci" tace tare da gyara zama.... Suna gamawa suka fito a natse, stadium suka wuce suna taɓa hira sama-sama, suna shigatahango Hisham zaune cikin Jersey, suna haɗa ido yayi saurin kaudawa, murmushi ta saki taredawucewa inda yake, tana zama tace "sorry" "for what!" Yace tare da juyowa ya kalleta, "for everything" tace tare da kallon shi, "nothing" yace a hankali, murmushi ta saki tare da faɗin"ranar wani magana ka ke yi ma?" Murmushi ya saki tare da faɗin "Mommy ce ke son maganadake" murmushi ta saki tare da faɗin "zan iya magana da ita?" "Why not" yace tare da saurinzarowayan shi... Miƙa mata yayi bayan ya faɗa ma Mommy, amsa tayi ta kara a kunni tare da ɗaga sallamaanatse, murmushi ta saki jin Mommy na gaidata, cike da nauyi tace "kuna lafiya Mommy?" "Alhamdulillah ya karatu?" "Alhamdulillah" tace a natse, "muna godiya da abinda ki ka maHisham Allah ya bar zumunci, ku cigaba da dagewa, Allah ya kare ku daga sharrin duk wani meshirin baku matsala a karatun ku" "amen mun gode sosai" tace tare da sakin murmushi tamiƙamai wayan.... "Okay Mommy zan kira ki zuwa amjima" yace tare da sauke wayan, murmushi ya saki taredakallon Insu da idon ta ke kan shi, "Daddy baya nan, brother's da sister's sun tafi school, ammazanhaɗa ku zuwa gaba" murmushi ta saki tare da faɗin "ba komai" "nagode" yace a natse, "jekasunshiga fili" tace tare da kallonshi, da sauri ya miƙe ya nufi filin, "all the best" tace da ƙarfi, juyowayayi tare da faɗin "thank you" ya juya ya shige, dariya ta saki tare da matsawa Nachma datagaji da jira ta ƙariso, "Allah ya shirya ki" tace tare da bin ta da ido, murmushi ta saki tare da faɗin"kafatanin shi dariya yake ban, yanda ki ka san ɗan fari" dariya suka kwashe da shi tare dakallonjuna, "you are bad" Nachma tace cike da dariya, "i know" tace tare da ɗaga kafaɗa ta maida hankalinta ga wasan da aka fara bugawa ... "Kun buga wasa me kyau" tace tare da kallon Hisham dake tsaye kusa da Nachma da Labib, "kuma kin san ba su yi zato ba sam muka ba su mamaki" Labib yace tare da sakin murmushi, "gaskiya kam, godiya ga jajirtaccen coch ɗin da ya baku horo" tace fuska yalwace da murmushi, dariya suka saki tare da bin ta da ido, "ba fa na son kallo" tace tare da banka musu harara, ɗaurefuska Nachma tayi ganin Minakshi da Sunaina na doso inda suke, "ku mu ɗan matsa daga nan" tace da kulawa, zaro wayanta a jaka Insu tayi tare da faɗin "tafiya ma zanyi bari in ji AbbanImanna ta ina" ta idda maganan tare da kara waya a kunni ta matsa gefe... "Lafiya dai ko?" Nachma tace idonta a kan su fuska a matuƙan muttuke, "ba ki ga alama ba" Minakshi tace tare da watsa mata na ta idon, "kun ga please ku je abun ku ba ma son wani tashinhankali anan" Labib yace fuska a matuƙar ɗaure, "dakata malam ka iya bakin ka ka kuma sandawaƴanda ka ke magana" Sunaina tace murya a kausashe, "da wa yake magana kuwa bandadake, wallahi ku ka ce zaku ta da mana da hankali a wajen nan ganewa jikin ku za ku yi" Hishamyaceazafafe tare da watsa musu ido, da mamaki suka bi shi da ido, dan sun san be cika tankawaakanirin wannan zantukan ba.... Juyowa tayi a natse tare da faɗin "wallahi se na ta da rikici an bani key na dinga drivingdakaina, Abban Iman akwai abinda ya ke nufi da ni a kwanakin nan" tayi maganan hankali kwancetaredakallon su, ganin yanda ko wanne su zuciya ke wuya yasata faɗin "ku mu ƙarisa social center kafinya iso" tayi maganan tare da yunƙurin barin wajen "kin kyautawa kan ki da ki ka nemi hanyar nisantar shi, dan wallahi na ɗau alwashin duk wacce ta yi ƙoƙarin shiga tsakanin mu za tafuskanshi hukunci dai-dai da lefinta" Minakshi tace tare da gyara tsayuwa, idonta na bin fuskanInsudake sakin murmushi... Dogon tsaki Nachma ta ja tare da faɗin "useless, an faɗa miki wai haukan ki ne yasa ta ƙi amsantayin shi? To ganin damanta ne dan ba abinda za ta yi da shi, wannan se ke" tace hankali kwance, kai hannu tayi da zumman marin Nachma Hisham yayi saurin riƙe hannunta tare da hurgarwaazuciye yace "ku bar nan ko yanzu jikin ku ya faɗa muku" "mu zaka duka! Kasan su waye mukuwa?" Sunaina tace da ɗin bin mamaki, "wawaye mana, ƴaƴan ɓarayi" Insu tace tare da sakindariya, dariya gaba ɗayansu suka saki cike da nishaɗi, "beb amma kin iya format" Nachmatacetare da kama hannunta suka bar wajen zuciyoyi ƙal.... Comments fans 🙏🥰 🫀MUGUWAR TSOKA 🫀 {🫀TA'ARE KALLUƊE} [Muscle Cramp🫀] ) عضلة سيئة ( 🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_ https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 ~~~~~~~~~~~~~~ ِبسم الله الرحمن الرحيم Created and written By Yardajjiya👩 💻 Page. Twenty eight Ɗago kai tayi daga daƙilar wayan da take tare da faɗin "Abban iman ai na fasa zuwa, in najezanyi dare" tayi maganan tare da maida kanta ga wayan hannunta, "ba can nayi ba" Ibrahimyacehankalin shi akan hanya, "ina muka yi?" Tace ba tare da ta ɗago kai ba, "inda mu ka yi" yacetareda danna horn, ɗago kai tayi ta zuba mai ido, ganin be nuna yasan tana yi ba ya sa ta kaudaidotamaida ga gate ɗin da aka wangale musu, "ya subhanallah!" Tace a saman laɓɓa idon na yawoaciki inda ta fuskanta, parking space ya wuce a hanzarce, yana dai-daita parking ya zare belt yasauka da sauri tare da faɗin "ki zauna anan, ba zan jima ba zan fito mu tafi" fiddo ido wajetayi tare da zare belt a hanzarce ta ɓalle murfin ɓangarenta ta dira tare da faɗin "haba AbbanIman, kai ma kasan ba zan iya zaman jira a mota ba, bare wannan tint ɗin da ban so" ta idda maganantare da narke mai ido.... Girgiza kai yayi tare da nufar ƙofar da ze sada shi da entrance ɗin companyn ba tare da yacekomai ba, da sauri ta dafa mai baya, suna isa bakin kofan shiga ƙofar ta buɗe kanta, shigasukayi a natse se da ta gama bincikan su tsaf sannan ta buɗe su faɗawa reception suka yi kai tsaye, faffaɗan waje ne wanda ya gaji da haɗuwa, ma'aikata na ta hurɗoɗinsu, yayinda masu jirakezazzaune a sofa's dake gefe kamar waƴada ke tsakiyan parlorn su, kai tsaye gefen wani ƙarfeyabi inda security's uku ke tsaye cikin uniform, ciro ID card ɗin shi yayi ya saka a wata na'uradakegefe, tana gama bincika ta fiddo mai ya ɗauka ƙarfen yayi sama ya shige, da sauri Insu ta dafamai baya kafin ta kai ga shiga ƙarfen ya maida kan shi ya ɓame, sauri tsaidata suka yi taredatambayanta inda za ta, marairaice fuska tayi tare da kallon Ibrahim da ya waigo, murmushi ya saki tare da ma ɗaya daga cikin security's magana, da sauri ya buɗe mata tare da gaidata agirmame, murmurshi ta saki tare da banka mai hararan gefen ido.... Girgiza kai Ibrahim dake hankalce da ita yayi tare da isa lifter, danna number yayi suka shige, dakewa tayi ba ta nuna ko wani alama da ze bayyana ƙauyancinta ba duk da a ta ciki bandasalati ba abinda take, suna isa ƙofan ta buɗe suka fito, "shiga nan office ɗin oga Munnir ne in nafitozamu wuce" yace tare da ƙoƙarin saka ID card ɗin shi a bakin ƙofar, "MD" tace a natse idontaakan sunan dake gefen glass ɗin da ya kasance bangon office ɗin, "shiga zaki tadda abinkarantawa da yawa a ciki" yace tare da buɗe mata ƙofan, "Uncle na nan ne?" Tace idonta akanshi, "eh yana conference hall, meeting suke me mahimmanci" yace tare da kafeta da ido, "ina neoffice ɗin shi?" Tace hankali kwance tare da ƙure shi da ido, harara ya banka mata tare dafaɗin"shige Malama sauri nake ana jirana" "to ka je mana, zan nemo da kaina" tace tare da zareIDcardɗin shi da sauri ta juya, girgiza kai yayi tare da wuce wa.... Bin muƙaman office's ɗin da ido tayi ta yi a natse, har ta iso na CEO, "wow dama inda aka samuMD yakamata a tadda CEO a kusa da shi" tace tare da saka ID card ɗin a inda ta ga Ibrahimyasaka ana MD, ya na nuna alamun ya buɗu ta zare ta murɗa ta shige a natse, sakin baki da idokawai tayi tana bin wajen a rikice, "wannan anya babu almubazzaranci kuwa!" Tace tare dakamahaba cike da tsoro, da sauri ta isa saman sofa ta zauna tare da faɗin "wani ni'iman ma firgici nega me kallo, Allah ka sa Uncle a aljannarka maɗaukakiya, aljanna a duniya aljanna a lahirakomai zam-zam" ta idda maganan tare da zare takalmi ta kwanta ta zaro waya ta haye tiktok... A natse ya tura ƙofan ya shiga ya nemi wajen zama ya zauna, murmushi ya sakin ma SSBdaketabin shi da ido, kauda fuska yayi tare da maidawa ga Alhaji Munnir dake tsaye a gaban majiki yanabayani, gaba ɗaya zuba mai ido suka yi cike da fahimta, be wani jima da shiga ba aka ƙarƙarezaman cike da nasara, jan kujeran da yake kai yayi a natse ya miƙe, da sauri ɗaya daga cikinma'aikatan wajen suka buɗe mai ƙofa, ficewa yayi a natse ba tare da ko wawaye ba, dafa mai baya Kamil da Jabir suka yi a natse, hanyar office ɗin shi yayi kai tsaye, tun da ya doso na'urake sanar mai da yana da baƙo a ciki, da mamaki Jabir yace "waye a ciki!" Saurin saka IDcardɗinshi Kamil yayi tare da buɗewa ya shige, ko kafin ya hangota SSB da Jabir sun shigo, kauda kai yayi dan yana shiga ya hangota.... Saurin miƙewa tayi saboda motsi da taji tare da baza musu ido, murmushi Kamil da se a lokacinya ganta ya saki tare da faɗin "Insu!" "Na'am uncle Kamil" tace murya cike da farin ciki, murmushi ya saki tare da wuce wa inda SSB ya ma kan shi mazauni, ajiye file's ɗin hannunshi yayi a natse, "ka duba please in ka samu dama, a satin gaba muke so a shigo da kayan" yacecikeda ladabi, jinjina mai kai yayi tare da bin shi da ido, "ka huta lafiya" yace tare da juyawa, "uncleKamil zan zo office ɗin ka" tace tare da sakin murmushi, murmushi ya saki tare da faɗin"tosekinzo, ina hawa na 12" jinjija kai tayi tare da bin shi da ido.... Jan chairn dake gaban teburin da ke gaban SSB Jabir yayi tare da zama a natse, tasowa Insutayi ta ja na kusa da wanda yake kai tare da faɗin "uncle Jabir ya aiki?" "Alhamdulillah" yace fuskaawashe, "Uncle ya aiki?" Tace tare da baza mai ido" "Alhamdulillah" yace a hankali cike da natsuwa, "Allah ya temaka" tace tare da gyara zama, "ya a kayi ki ka shigo nan?" Jabir yacetareda kallon ta, secret ne" tace tare da sakin murmushi, murmushi ya saki tare da fadin "damaakwai secret ɗin da za'a ɓoyewa Uncle?" Dariya ta saki tare da ciro ID card ɗin Ibrahimta ɗagasama tare da juya ido cike da yanayinta tare da faɗin "ɗan jagora"

Chapter 37 of 109