Share this page
kallo, ganin fuskan SSB take kallo yasa su mutuwar tsaye cike da mamaki, murmushi Nafisat ta saki tare da takawa a natse ta ƙarisa gefen shi a natse, riƙo hannun rigarshi Mairahtayi cike da farin ciki ta kama shi, kamata yayi a natse jikin shi na rawa, cafke wuyan shi tayi cikeda farin cikin ganin shi tare da sakin dariya cike da yarintar ta, "ta san shi ne!" Kamil yacedamamaki, jinjina mishi kai Nafisat tayi tare da miƙewa ta bar wajen a natse.... "Allah me iko" Yasmin tace tare da kama baki, murmushi Hajiya ta saki tare da faɗin "Insiyyahcefa mahaifiyarta" "na gazgata Hajiya" Alhaji Munnir yace fuska yalwace da murmurshi, ƙaransakkowa daga sama ya sa su juya dubansu ga wajen, Insu ce ta sakko shirye cikin shiga namutumci, ganin irin kallon da suke bin ta da shi yasata ɗaure fuska tare da kallon Ibrahimcikintsare gida tace "amsota mu tafi" dariya ya saki me yalwa tare da faɗin "ina?" "Abban Imankadaina wasa dan Allah" tayi maganan cike da ɓacin rai, "to Allah ya baki haƙuri" yace tare dajagefe ya ba ta hanya alamun ta je ta amshenta... Ba musu ta wuce, tana zuwa ta kai hannu ta ɗauketa ta juya ta nufi ƙofa, tun da ta sakkotunanin shi ya tsaya cak so yake ya gazgata itance ko ba itan ba ce se dai ƙwaƙwalwan shi taƙi aiki, komai ya tsaya mai cak natsuwan shi be dawo jikin shi ba se da ta ɗauke Mairah, "zanyi magana dasu" yace a sanyaye zuciyanshi na bugawa da sauri da sauri dan gani yake tana fita ze farka dagamafarkin da yake, ko gizon da take mai ze ɓace, tsayawa cak tayi kamar wacce aka dannamastop, "please ki dawo" yace a hankali murya na rawa, kauda fuska gefe tayi ta juyo a hankali tawuce up stairs ba tare da ta kalli inda suke tsaye ba, bin ta da ido yayi har tw ɓacewa ganinsukafin ya saki wani ƙaƙƙarfan ajiyan zuciya me haɗe da zuwan zafafan hawaye, bin shi da idosukayi cike da tausayawa,..... Comments fans🥰🙏 🫀MUGUWAR TSOKA 🫀 {🫀TA'ARE KALLUƊE} [Muscle Cramp🫀] ) عضلة سيئة ( 🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_ https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 ِبسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~~~~~~~~ Created and written By Yardajjiya👩 💻 Page. Fifty one Miƙewa yayi a natse tare da kallon Jabir da ya zuba mai ido, "a kai musu ruwa da abinci bari inkimtsa tukun" yayi maganan murya a sanyaye ya wuce ɗakin shi na ƙasa a hankali, yana ɓacewaganin su suka sassauke ajiyan zuciya cike da samun sassauci.... "Ibrahim a hanzarta sama musu abinda yace" Jabir yace tare da zaro waya ya nemi number yadanna ya wuce da sauri ya bar wajen, zaro na shi wayan Ibrahim yayi tare da ja gefe ya faramagana, cikin mintocin da ba su yi ƙasa da 20 ba motocin manyan restaurant ta fara fakawaawajen, nan ma'aikata suka shiga musu rabon abinci da ruwa da lemuka.... Kan kace me waje ya ɗau harama, haka suka ci suka sha suka ƙoshi nak fuskokinsu ya cikadafarin ciki da jin daɗi dan sun tabbatar da abun ƙaunarsu ne ya kawo musu wannan agaji.... Tana shiga ɗakinta ta ajiye Mairah a saman gado ta zauna kusa da ita tare da tattara ƙafafuntatahaye da su sama ƙure window da ido tayi kaman me san ganin wani abu, banda mamakinyandaya mata magana ba abinda take, "wato dawo bayan kai da kan ka ka buƙaci in yi nesa da kai" tacecike da takaici, rumtse ido tayi tare da faɗin "to amma Insu ke ki ka nemi hakan, kuma ki katabbatar mai da zaki fi samun farin ciki in ya barki ki ka tafin" ta idda maganan tare da buɗeidonta ta watsa akan window, "to amma meyasa be tsaidaki ba tunda yasan yana buƙatanzamadake?" ta jefawa kanta tambayan tare da jiran amsa.... "Ko ya tsaidake ba zaki tsaya ba Insu, a lokacin kin gama cire tsammani" tayi maganan taredamaida dubanta ga Mairah da ta dafata ta miƙe tsaye, dukan gefen kanta kaɗan tayi tare dafaɗin"kina gab da zarewa Insu, na tabbatar ki ka cigaba da waƴan nan sumbatun se kin zare" taiddamaganan tare da jawo Mairah ta cillata sama, ƙyalƙyalewa da dariya tayi tare da rumtse idotaƙanƙameta ƙam... A shirye ya fito cikin dakakken shadda milk color da ya ji ɗinki wuta me ni'imtaccen kyau, hulannan ya zauna daram kamar akan shi aka kirƙira, white glass sanye a saman fuskan shi wandayaƙara wa adon na shi ƙawa, banda zuba ƙamshi ba abinda yake, murmushi Hajiya dake zaunetasaki tare da bin yanda yake gyara zaman agogon da ya ɗaura a tsintsiyar hannun shi da ido, "masha Allah yanzu na tabbatar da Sahabee na ya farfaɗo" tayi maganar murmushin samanfuskantana yalwatuwa.... Murmushi ya saki tare da ɗago ido ya kalleta, "muje" yace tare da shigewa gaba, da sauri SSGdake tsayuwan jiran futowan shi ya dafa mai baya, bin bayan su su Jabir gaba ɗayansu sukayi, suna fita jami'an tsaro da security's suka mimmiƙe, da sauri SSG ya buɗe mai mota, yana shigayarufe ya buɗe gefen me zaman banza ya zauna, buɗe kusa da shi Jabir yayi ya zauna tare dabadriver umurni, gaba wasu daga cikin motocin jami'an tsoron suka yi na SSB ya dafa musubayatabaya kuwa motocin security's ne da sauran na jami'an tsaron da na su Alhaji Jamil nan dananwajen ya ɗau kuwwa.... Suna isa wajen matasan dake cike da wajen duk suka mimmiƙe suka zuba ma jami'an tsarodasecurity's da suka fiffito a hanzarce suka nemi matsaya ido, buɗe mai ƙofa SSG yayi a natseyafito Jabir ya bi yo bayanshi, wani ihun farin ciki suka saki kamar za su fasa garin, nan da nanwasun su suka fara ɗaukan shi video's wa sun su kuma hotuna, kan kace me sun fara postingakafafen sada zumunta, har inda aka tanada dan zaman shi security's da jami'an tsoro sukarakashi suka bazuu a bayanshi da gefunan shi, yana zama suka ƙara sakin wani ihun farin ciki kamarwa'inda aka wa kyautan Hajji da umra, bin su kawai yake da ido cike da mamakin ƙaunar dasukemai, dan isowan shi wajen ya ƙara tabbatar mai da ƙauna ne ya kawo su wajen, matsowa dasauri journalist's suka yi saboda umurnin hakan da aka ba su.... Matsa mai da microphone Jabir yayi a natse, gyara zama yayi cike da kamalan shi idon shi akansu, shiru duk suka yi suka zuba mai ido dan jin abinda ze ce, murmurshi ya saki dan fuskantanabinda shirun na su yake nufi, "matasa ku ne ƙashin bayan al'umma na san da yawanku sunsanda hakan, kun san meyasa aka kira ku da haka?" "A'a" suka ce da ƙarfi, murmushin shi mematuƙar burgewa ya sakin musu tare da faɗin "saboda ku ne al'umman gaba ɗayanta, inbakubata yanda mulkin ita kanta za ta tafi, ku ne ƙarfin mulkin, kuna da matukar mahimmaci ga rayuwar mutane da dama, ban cire muku kaina na ba, ku yakamata ku liƙe duk wata kafa taɓarna inta ɓull, kar ku zama ma su buɗeta da hannayenku"... Tsahirtawa kaɗan yayi idon shi akan su kafin ya cigaba da faɗin, "Allah ba ya maraba da dukwani me tada fitina duk ƙanƙantan ta, mun sanku, mun san abinda zaku iya, sannan ba zamu ƙalubalanci ƙaunar da ku ke nuna mana ba a wannan tafiyan, ba zan bari ɗayanku ya cututadalilina ba, in har hakan ta faru zanyi kaico da danashinan kasancewana uba gareku, duk wani uba na gari ba ze bari ɗanshi ya ɗau makamin dan fito na fito da azzalumi ba, tausasanshi zeyi sannan ya nunashshe shi ga bin doka, ku yi haƙuri ku koma ga mahallanku, ba makaminwani daya cutar da niz ciwo ne daga mahaliccina kuma Alhamdulillah na samu sauƙi, kar ku cutar dawani ta dalilin hakan, ku barsu da halayensu, kar ku ɗau nauyin zunubansu na tsayin shekarudasuka yi ku bar doka ta hukuntasu".... "Ku ji magana, ku zama yaran kirki ga ƙasa, ina matuƙar alfahari da kasantuwana ɗaya dagacikinku" yana kai nan ya matsar da microphone ɗin ya miƙe, da sauri security's da jami'an tsarosuka matso, a natse ya fara takawa dan barin wajen, "se ka yi ka kuma ka kuma kumawa ɗanƁadamayya, ƙaryan duk wani mugu kusantan inda ka ke, gaba ka ke da su, Allah ya dafamajarumin mu, ka zarcesu ka zarce ababen koyin su, na mu ba irin na su ba ne" haka suka dingakoɗashi suna ƙoƙarin binshi jami'an tsoro na tare su.... "Wallahi mun jika mun bi umurninka, mun bi Allah mun bika, mun barsu su je da halayensuƴanbanza haihuwar tsakar kasuwa, in sha Allahu se sun ci sarƙa matuƙar kana raye" magananCikaaiki ya shiga kunnuwan shi a dai-dai lokacin da ya saka kai dan shiga mota, murmushi ya saki yashige a natse, yana dai-daita zama ya sauke ajiyan zuciya a natse yana me fatan su ji abindayacesu kuma yi aiki da shi, murmushi Jabir da ke dai-daita zama ya saki tare da faɗin "ina fatansukasance yara na gari kamar yanda ka ce" murmushi ya saki ba tare da ya kalleshi ba ya lumsheido.... Haka suka tattara suka fara barin wajen cike da farin ciki da jin daɗin kalamanshi, suna meyabakaramcin shi, nan take maganan SSB da hotunan shi suka fara biye ƙasa da wajen ƙasa, kafinwuce wan awa masu zanga-zanga sun tattara komatsansu sun koma gidajensu, a lokacinababenzargi suka numfasa daga tsoron afko musu da suke... Da sauri ta ajiye Mairah da ta wango tas a saman sofa ta ɗau wayanta dake saman table ɗindaketsakiyan bedroom ɗin ta ɗaga kiran da aka mata a zumuɗe ta kara a kunni, "baby sorry wallahi nasha'afa ne shiyasa ban kira ki ba amma mun koma gida lafiya ba wani matsala" murmushi Yasmin ta saki daga can tare da faɗin "na sani baby Insu ya Uncle ɗin? Duk da yanzu na gamaganin shi a tv yana ta ma matasa bayani" murmushi ta saki tare da faɗin "auh yayi musumaganan?"... "Ke fa ba ki da kirki zaki ce mun baki sani ba ne?" Tace tare da sakin murmushi, "wallahi bansani ba fa, ban kunna tv ba" tace cike da gaskiyanta, "aiko yayi bayani me ratsa zuciya matasa duksunwatse wallahi gari ya yi tsitt" "ma sha Allah haka ai ake so" tace cike da nuna jin daɗi a muryanta... "Na ji kaman ki na uzuri ko?" Tace cike da kulawa, "ba wani uzuri wanka kawai zanyo" "yakamataai, gaskiya a darje ma Uncle wanka wanda ze ƙara susutashi" "Allah ya shiryeki wato uncleShureim dai ya gama lalata ki" tace tare da kama haɓa, "auh wato ya lalatani lallai kin ce wani abu, je ki watsa ruwan na ji an fara kiraye-kirayen sallah in kin fito kin natsu zamu kira mugaisada Uncle" "to shikenan ƴar jarida ma ta faɗa min in na fito zan kira ki" "to shikenan kar ki mantaki kira Anty Salwa gobe zata wuce" "okay in sha Allah" tace tare da katse kiran ta ajiye wayan... Murmushi ta sakin ma Mairah dake ta bin ta da ido tare da faɗin "bari in yi wanka kar ki sauka" murmushi ta sakin mata tare da zamewa ta kwanta idonta akan kofar toilet ɗin... "Halima kira yaran nan ki ji suna lafiya" Gude dake zaune saman sofan ɗakin jinyan Sudais tacetare da kallon Halima dake zaune gefenta ita da Nafi, "Mommy tunda ki ka ji haka suna lafiyane, ba wanda yayi tunanin kiran ki a cikin su se ke ce zaki kira su" Halima tace cike da takaici, "danAllah Mommy ki daina damuwa da su, su fa hidiman gabansu suke" Nafi tace da damuwa... "Yasmin da Farisat nake nufi fa" tace a hankali idonta akan su, "Yasmin da Farisat!" Suka cecikeda mamaki idon su akan ta, murmushi Sudais ya saki tare da kauda fuska, jin tayi shiru yasaHalima saurin ɗaukan wayanta ta fara neman number Farisat dan gani take tana ƙara sakanguda Guden zata fasa.... Miƙa mata wayanta dake ringing Salman da ya shigo kitchen yayi tare da faɗin "ba tayi?" "Bismillah" tace tare da goge hannu a tewol ɗin dake gefenta ta amsa ta ɗaga da mamaki taredaɗaga sallama a natse, "ta ɗaga" Halima tace a hanzarce tare da miƙa ma Gude wayan, "kungawautan da nake faɗa muku tana da shi ko?" Gude tace tare da nuna ta da hannu, ganin tanatsaye da wayan ta rasa yanda za tayi ya sa Nafi amsa tare da faɗin "sister Farisat" ... "Na'am tace tare da danne dariyar maganan Gude da tayi, "Mommy ne tace a tambayi kunkomagida ba wani matsala ko?" "Alhamdulillah, ba wani matsala" tace da mamaki a muryanta, murmushi ta saki tare da faɗin "to shikenan Allah ya huce gajiya" "amen nagode" tace taredazare wayan ta katse kiran, bin wayan da ido tayi cike da mamaki, kallonta Salman dake juyamiyayayi tare da faɗin "lafiya kuwa?" "Lafiya lau" tace tare da ajiye wayan ta jawo cabbage ta farayankawa.... "Kira Yasmin ki ji yanda ta koma" Gude tace idonta akan Nafi, jinjina kai tayi ta nemi number tadanna ta saka a speaker, "zo ki ban ruwa" Sudais yace tare da kallon Halima, da sauri ta tashi tayi inda yake, ɗagawa Yasmin tayi ta can da mamaki a muryanta ta yi sallama, amsawa Nafi tayi asake, murmurshi ta saki tare da faɗin "Hajiya Babiya ke ce da kira haka yau?" Murmushi tasaki tare da faɗin "Mommy ne tace a kira a tambayi ko kun koma gida lafiya" murmushi ta saki mefaɗi tare da faɗin "Alhamdulillah lafiya lau, dake ai abun be yi nisa ba, komai ya wuce yanzu" "shugaban ƙasan yayi magana da su ne!" Tace da mamaki, "eh yayi" "ma sha Allah wallahi tunanin komawa gida nake yanzu, amma tsoron abinda zamu tarar duk ya kashe mun jiki" dariyata saki me faɗi tare da faɗin "ku jira su kawo abinci se su sauke ku a gida" "oh Yasmin ki cebaki huta ba" tace cike da jin daɗin karamcinta, "to Hajiya Babiya za'a fara manyancen ko" tacemuryacike da murmushi tare da katse kiran... Zaro wayan tayi fuska cike da murmushi tare da faɗin "Mommy tana lafiya, har tayi girki za'akawo yanzu" jinjina mata kai tayi zuciya cike da saƙe-saƙe, "Halima shirya in sun kawo abincinzamu bi su su ajiye mu a gida" tace cike da azama tare da ajiye wayan ta miƙe... "Yakamata ku zo ku koma gidajenku" Alhaji Jamil yace tare da kallon su A'isha, "yanzu kuwa" tace tare da kallon SSB da ya shigo cikin parlor cike da natsuwa shi, sannu da fitowa sukamai cike da farin cikin ganin yanda ya ƙara samun ƙarfi a jiki, murmushi ya sakin musu tare daneman waje ya zauna, "Yaya Jamil dan Allah idan yaran nan sun ɗau hutu ina son Hafeeza ta zo taminnata a gida, yara na ta san ganinta" Kausar tace cike da magiya, "in ki na sonta gaba ɗaya majeki ɗauketa" yace a natse cike da gaskiyanshi.... Bin shi suka yi da ido cike da mamaki, "a'a ni ko hutun na samu ma yayi min" tace tare da sakinmurmushi, jinjina kai yayi tare da faɗin "Allah ya nuna mana" "amen, yau ba bacci" tace taredasakin dariya, "su Salimat za'a ji albishir kenan" Yasmin tace tare da sakin murmushi, jinjinamatakai tayi murmushi be bar saman fuskanta ba... "Hajiya dinnern ya kammala" Maude da ta shigo parlorn tace cike da girmamawa, "to Maudesannu da aiki, ina Lamunde yakamata ta zo ta tafi gida tunda garin ya dai-daita" "tana shirintafiya yanzu" Maude tace a girmame, "to shikenan" tace tare da miƙewa, kallonsu tayi da kulawatare da faɗin "kuyunƙuro, Lawiza kira ƙawayen naki" ta idda maganan tare da wuce wa diningarea, murmushi Lawiza ta saki tare da wuce wa kiran su Nabila... Miƙewa SSB yayi a natse, yana zuwa kusa da Maude yace "kafin ta wuce ta zo ina son ganinta" yayi maganan tare da wuce wa, rikicewa tayi tare da bin shi da ido dan ba ta fahimci abindayaceba, "Lamunde yake nufi" Jabir dake bayan shi yace fuska cike da murmushi ya dafa mai baya.... Jinjina kan da be gani ba tayi tare da sakin ma su Nabila da suka zo wuce wa murmushi, martani suka sakin mata suka wuce a natse, juyawa a natse tayi ta nufi side ɗin su, ɗaukan cup teaNafisat tayi a natse ta fara ƙoƙarin haɗa ma kanta tea, "a'a Nafisat saka abinci ne, ba na sonƙincin abincin nan na ki" Hajiya tace da kulawa, murmurshi ta saki tare da sadda kai a hankali tace"na ƙoshi ne Hajiya" "me ki ka ci?" Kamil yace da mamaki, "na ci abinci a school sannan naci bayan na dawo" tayi magana a hankali, "saka ko kaɗan ne ki ci" Hajiya tace da kulawa.... Jinjina kai tayi ta zari plate a natse, "Alhaji ƙarami saka abinci ka ci" Hajiya tace da kulawatareda kallon Sa'eed, murmushi ya sakin mata tare da jinjina kai cike da girmamawa ya ɗau plate, gyara zama Alhaji Jamil yayi tare da faɗin "Hajiya a duba mun a dangi ina son ƙara gida" yayi maganan a sukunance cike da gaskiyan shi, da mamaki Hajiya ta bi shi da ido, "na san a rina" Lubabatu tace a hankali tare da kallon Yasmin, murmurshi ta saki tare da kauda kai da sauri.... Murmushi Kamil ya saki tare da faɗin "wa ya isa taɓan namiji ya zauna lafiya, namiji ka kebamiji kaɗai ba" ya idda maganan tare da sakin dariya, "Kamil!" A'isha tace tare da kama haɓa, "dagaskiyana Hajiyar Allah, dama ai ba girman shi ba ne zama da mace ɗaya tal kaman wacceakamusu auren zobe, ka ƙara gida mutumina ina goyan bayanka" ya idda maganan cike da farinciki.... "Ungo na ka nan Kamil" Hajiya tace tana danne na ta dariyan, murmushi ya saki tare da jinjinamata kai, juyawa ga Alhaji Jamil tayi tare da faɗin "lafiya ka ke son ƙara gida haka yanzu?" "Wacce zata zame ma Abbah uwa nake buƙata" yace a hankali tare da miƙewa zaune dagakishingiɗar da yayi, "an zo wajen" Kausar tace tare da ƙasa da kai, "wallahi bakin ki da maganaKausar" Kamil yace tare da sakin dariya, zare ido tayi tare da ɗago kai a sukwane.... "Ba mu da sa'annin aurenka a family yanzu, ka yi haƙuri ka je ku fuhimci juna, in ba ta fahimcekaba se ka yi haƙuri ka barshi a inda ze fi samun kwanciyar hankali, kar wannan dalilin yasa kayanke hukunci cikin fushi, wacce za ta shigo ita ma ba lallai ta iya riƙe maka shi ba" Hajiyataceanatse idonta akan Alhaji Jamil, "Amin afwa Hajiya a wannan karon ban jin zan iya haƙura dawannan shirmammun halayen nata" "good" Lubabatu tace a hankali, "to ni dai bana da waccezan baka" "ni ina da ita uncle Jamil" Insu tace cike da yanayinta, juyawa suka yi da sauri taindasuka ji yo sautin muryanta.... Tsaye take saɓe da Mairah da ta cin ma ado me cike da burgewa idonta akan su, "ma sha Allah" Hajiya tace a hankali cike da jin daɗin ganinta, faɗaɗa murmushin saman fuskanta tayi tafara takowa wajen a natse, tana isowa Lawiza tayi saurin jan mata kujera, "nagode Anty Lawizazaunaplease" tace tare da kallonta, ba musu ta ja kujera ta zauna a natse ta fara serving ɗin ta.... "Abie" Mairah tace idonta akan SSB da ya sadda kai ƙasa, tunda ya musu kallo ɗaya ya diririceyasadda kai be ƙara ɗagowa ba, "jeki Mamy" Insu tace tare da miƙa ma Nafisat ita, kai hannutayi dazumman amsanta ta ƙanƙame Insu tare da ture hannun Nafisat, ɗaga hannunta a natse tayi tasauke akan hannunta dake ture Nafisat ta buga a hankali, fashewa da kuka tayi cike da jinzafindukan da ta ma hannun tare da faɗin "mammy" rumtse ido SSB da ke bin su da kallon ƙasanidoyayi cike da rashin jin daɗi... "Insu!" Yasmin tace cike da rashin jin daɗi tare da banka mata harara, murmushi ta saki taredafaɗin "sorry Mahmah hannun Mamynta ta ture" tana kai nan ta juya ga Jamil tare da faɗin"uncleJamil in dai wacce zata riƙe maka ɗanka saboda Allah ka ke buƙata ina da ita, se dai kumazakamun alƙawarin riƙe ta ita ma tsakani da Allah" ta idda maganan cike bayyana gaskiyan abindatafaɗa, murmushi Lawiza ta saki tare da ajiye mata abincin da ta zuba mata da kulawa, "thankyouAnty Lawiza" tace tare da ɗaukan cokali... "Baki da matsala da wannan Insu ke dai kawo ta" Kamil yace fuska ɗauke da murmushi, "angamauncle Kamil, se dai fa tattaki za ku yi har garin bayin Allah masu ɗaukaka addinin Allah" taiddamagana cike da yaban garin, murmushi suka saki tare da bin ta da ido, "duk ba ki da matsaladawannan, ke dai ba da numberta" yace cike da zumuɗi, dama ya daɗe yana jiran irin wannanrana.... "A'a za mu yi magana da ita tukun, daga nan se komai ya bi yo baya" tace tare da ɗiban romonkai takai baki, lumshe ido tayi tare da faɗin "wow kai jama'a! Wani girkin in ka ci se kaji kamanba'aduniya aka girka shi ba" dariya Nabila da Fadila suka saki tare da kallon ta, saura kuwa semurmushi, kai hannu Mairah tayi da zumman jawo cokalin da takai baki, kauda fuska tayi dasauri tare da faɗin "uncle Sa'eed ɗauketa".... Kuka ta saki da ƙarfi tare da ƙanƙameta, "aiko se kin je" tace tare da ƙoƙarin janye hannuntadake ƙanƙame da wuyanta, "barta mana Insu tunda ba ta so" Kausar tace cike da damuwa, "meka ke jira!" Tace tare da kallon Sa'eed, da sauri ya ja kujeran da yake kai baya ya miƙe ya isawajen, "ɗauketa" tace murya a kame fuska a ɗaure, ba musu ya kai hannu a natse tare da sakinmata murmushi, kwaɓe fuska tayi tare da kallon Insu, murmurshi ta sakin mata tare da faɗin"jeki uncle Sa'eed" ba musu ta kama hannun ba din ta so ba.... Murmushi Nafisat ta saki tare da matsar da plate ɗin gabanta gefe kaɗan, "ƙara abincinnan" Insutace a dake, wuce wa Sa'eed yayi ɗauke da Mairah ya koma inda ya tashi, ba musu Nafisat tamatso da plate ɗin ta fara ƙarawa, haka suka ci abincin a natse, duk da wasun su zuciyoyi badaɗi suna kammalawa suka tattara suka koma cikin parlor... "Mahmah na yi magana da Yaya akan problem ɗinki da familyn su Fadila, sorry ban sanar dakebakafin in yi maganan, abin ya damen gaskiya tunda Hajiya ta bani labarin abinda ya faru, inaganinba barin su ne abinda ya dace a yi ba, kamata yayi a amshi duk wani abu da suke hange a barsuda yaran mu gani in za su iya riƙe su tsakani da Allah" Insu tace tare da kallon Yasmin da tayi mutuwan zaune, "ashe ba ni ɗaya nake ganin ba a yi adalci ba da aka barsu" Kausar tace cikedafarin ciki, "ai batun a barsu ma be taso ba, dan Allah kar ki ce a'a ki bari a shiga court a bugaAllahya ba wa me rabo sa'a" ta idda maganan tare da kafeta da ido ... Jinjina kai tayi a hankali tare da sakin ƙaƙƙarfan ajiyan zuciya, "mutanen nan a ankare suke, karku manta rubda ciki suka yi fa akan dukiyan bawan Allahn nan ta ya kuke zatan za su zaunahakakawai ba tare da wani shirin ko ta ɓaci ba" "Kamil yace cike da ganin abinda wuya" "ai Insudakin bar zancen kawai ta barsu da mahalicci shi sakayya yanzu tun a duniya ake farata a ƙarƙareacan" A'isha tace da damuwa, girgiza kai tayi tare da faɗin "Anty A'isha mahaliccinta ma cewayayi a tashi se yayi temako, ba cewa yayi a zauna ze temaka ba, dukiyan da suka hau kai suka zaunaɗare-ɗare ba na ɗan uwansu ba ne yanzu, na ta ne, na yaranta ne, dan haka batun ta barsusuci mata haƙƙi be ma taso ba, ba raguwa ba ce da zata zauna tana kuka a ɗaka kullum, tana hangomaƙiyanta na dariya daga nesa.... "Jarumace, za ta fita filin dagan kare martabanta da mutuncinta, uwace fa kar ku manta, uwacekamar yanda ku ke iyaye, an kwashe mata ƴaƴa gaba ɗaya saboda san rai ba ta san hali dayanayin da suke ciki ba, ku yi duba da kan ku, tsayin yaushe zaku iya ɗauka ba ku saka ƴaƴankuaido ba? Ta ɓangarena ba zan iya awa ban saka tawa ɗiyar a ido ba, amma ta jure tsayin shekaraba ta saka ko ɗayansu a idonta ba, ba miji ba ƴaƴa"... "Kun san raɗaɗin rashin abubuwan nan kuwa? Ko da yake ba zaku sani ba tunda ba waccetataɓanisa da ɗaya daga cikin abinda ta rasa a cikin ku, amma duk da hakan kullumƙoƙarin sakamurmurshi take a saman fuskanta kamar ba komai, ba zan iya cigaba da ganinta cikin wannanhalin ba, za ta shiga court da su zata ja da su, na yarda da kaina kuma na yarda da wanda zetsayamata" tana kai nan ta miƙe tare da miƙa ma Mairah hannu,

Chapter 80 of 109