tare da gyara zama, "ba yi da mata, matan shi ɗaya ta kuka rasu tunkusanshekaru takwas da suka shuɗe, yarinyar shi ɗaya, an aurar da ita ko wata uku be yi ba" "mashaAllah, Allah ya jiƙanta, kinga shikenan se ku je ku maye gurbin abubuwan da ku ka rasa" Kausartace cike da farin ciki, "Abie" Mairah dake jikin Nafisat tace da ƙarfi idonta akan SSB da yashigoamugun gajiye, miƙewa Insu tayi da sauri ta nufeshi fuska yalwace da murmushi, kauda kai Alhaji
Munnir da Ibrahim da suka shigo tare da shi suka yi tare da shigewa ciki.... Buɗe mata hannu yayi ta shige da sauri tare da faɗin "sannu da dawowa Nafsii" lumashe idoyayi
tare da jinjina mata kai, se da suka ɗauki tsayin sakanni a haka kafin ya janyeta ya riƙo hannuntasuka tako ciki, murmushi ya sakin ma Yasmin dake kallon su fuska cike da murmushi, "anyi
nasara Allah ya baki wuyan ɗauka" yace cike da gajiyan dake nuƙurƙusan shu "amin" sukaceidon su akan shi, "anyi nasara an dawo da tsaraba" Kausar tace tare da sakin dariya, "gulmaajali"Kamil yace tare da taya ta dariyan, murmushi ya saki ya maida duban shi ga Hajiya, "har kungana meeting ɗin?" Jinjina mata kai yayi a natse, "ma sha Allah, jeka kimtso muyi dinner kai
muke jira" jinina mata kai yayi tare da miƙa ma Mairah hannu sauketa da sauri Nafisat tayi tanufesu da hanzari, ɗaukanta yayi suka wuce sama cike da burgewa, "Nafisat jeki kira waƴancanda aka wa kamun su fito" Hajiya tace idonta akan ta, murmurshi ta saki tare da miƙewa tawuce, sallama Lawiza tayi ta shigo hannu ture da keken da suke shirya abinci su shigo da shi ciki, "sannu da aiki Lawiza" Hajiya tace mata ra kulawa, murmushi ta saki tare da faɗin "yawwa" tareda wuce wa.... Ajiye madaidaici treyn da ta ɗaura jug da cup's biyu tayi ta center table ɗin gaban shi tareda
jawo shi kusa da shi, murmushi ta saki ajiye cike da karairaya tare da faɗin "Honey a zuba ne?" Jinjina mata kai yayi tare da miƙewa daga kishingiɗar da yayi ya zauna, zubawa tayi ta miƙamai
cike da salo, amsa yayi tare da faɗin "banji ɗuriyar yaran nan ba" "sun kwanta tun ɗazu" kallontayayi tare da faɗin "lafiya kuwa!" "Eh ni na sa su yi, saboda ina son kasancewa daga ni se kai" tayi
maganan a narke, guntun murmushi ya saki tare da kai cup ɗin baki, se da ya sha fin rabi sannanya ajiye tare da faɗin "Abba fa?" Kame fuska tayi tare da faɗin "ban sanin mishi ba, be fitobakwata-kwata" tayi maganan ko a jikinta....
"Kina nufin be ci komai ba tun safe!" Yace a tsorace idon shi ƙyam akanta, "ina zan sani kumaHoney, na ce maka be fito ba, zuwa zan in fiddo shi ko me" tayi maganan cike da jin takaicintambayan da ya mata, rumtse ido yayi cike da ɓacin rai tare da miƙewa a natse, "amHoneynagasaƙo ɗazu ya shigo nagode sosai fa, wallahi naji daɗin gani kaman kasan so nake in canza mota" ƙin juyowa yayi dan ya tabbata ya juyo ze iya aikata ɓatacciya, har ya wuce wata zuciyantaingizoshi ya juyo tare da faɗin "ba dan ki canza mota na turo miki ba, dan ki je ki sayi abinda ki kebuƙata ne, nan da kwana uku za'a kawo miki abokiyar zama" yana idda naganan ya juya.... A zabure ta miƙe murmushi saman fuskanta ya ɓace ɓat, saurin shan gaban shi tayi tare dafaɗin"ban fahimta ba! Me ka ke son ce mun ne!" Ta udda maganan ido a waje, "banyi mamaki badanna san ba fahimtar ne dake ba, wacce zata kula da amanar da aka ba ni zan kawo kamar yandaki
ka buƙata, bani hanya" ya idda maganan a dake, "wallahi baka isa ba Jamil, ni zakawa kishiya!
Kishiyan ma a walaƙance haka" tayi maganan cike da mamaki, "kinfi ƙarfin ayi miki ne?" Yajefamata tambayan hankali kwance, "wallahi na wuce ajin kishiya, wallahi ba ka isa ba, wallahi bazan zauna da wata a gidanka ba, se dai ka zaɓa ko ni ko ita" raɓeta yayi a natse ya wuce taredafaɗin "kar ki manta ki rufe mun ƙofa in kin fita, sannan kada ki yi kuskuren ɗaukan mu ƴa koguda ɗaya" yana kai nan ya shige ɗakin Sa'eed.... Bin shi tayi da baki da ido a sake har ya shige, wani dogon tsaki taja tare da faɗin "an faɗamakadama zan ɗauka ne, wallahi in dai ba ka janye wannan maganar ba ba ni ba gidanka" tanakai nan
ta wuce ɗakinta a fusace, kamar me shirin tashi sama...
"What!" Shila tace tare da miƙewa zumbur, saurin taro mata zaninta dake shirin faɗuwa
muƙarrabanta suka yi tare da bin ta da ido ganin yanda jikinta ke ɓari, "kamar yanda ki kaji, acikin abubuwan da ta gudu da su, akwai rayuwata a ciki, ta sake ta taɓa wannan abun, dagakehar ita ba zaku shaba, kin fi kowa sanin waye ni Shila" muryan dake fita a kausashe ya ƙaradakankunninta a mugun fusace, "wallahi ba ta zo nan ba yallaɓai, ba zata taɓa zuwa gidan nanbadantasan ba zan barta ba se na tona mata asiri, na daɗe da faɗa maka Sa'adatu makira ce, maƙaryaciya ce, tana da mugun manufa akan ka amma ka ƙi saurarana, to ga shi ta nuna makawacece ita ka gani" Shila tace cike da son kare kanta, "ba wannna dogon bayanin na tambayeki
ba, ki sa mutanen ki su baza ido a ciki da wajen garin in dai suka ganta su ƙaddamar matasannansu amso mun abinda nake buƙata kuɗin kuma ku riƙe" "to yallaɓai an gama, ka kwantar dahankalin ka kamar an kamata ne, in dai tana cikin garin nan to tana a hannu" Shila tace cikedafarin cikin jin abinda za ta samu, ƙitt, ya katse kiran, wani nagartaccen murmushi ta saki taredakomawa ta zauna ...
"Shila me kuma tayi!" Shiwa tace a tsorace, "sata" tace tare da sakin dariyar mugunta, "satakuma!" Suka ce cike da mamaki, "ƙwarai ba ƙaramin sata ba ne ai, babba ne, wanda ita dadanginta za su iya warkewa daga cutan talauci, se dai ba ta san mu ta satowa ba, Sa'adatukinaina ne? Ki jirayi ganin fuskan Shila wanda ba ki taɓa gani ba" ta idda maganan tare da fashewadadariya ta miƙe ƙafafu, bin ta kawai suka yi da ido cike da mamaki....
"Shine me!" Dattijon dake zaune a saman kujeran roban dake balcony ɗin shi yace tare dakafetada ido, "dawowa gida na yi, se ya janye maganan da ya furta" tace cike da taɓara tare da saddakai ƙasa, "tashi ki koma inda ki ka fito, babu mazaunin bazawara a gidana, "Daddy aure fa zeyi
kishiya ze mun!" Tace a mamakance tare da fara share hawaye, "mata nawa ne a gidana?" Yajefamata tambayan idon shi akan ta, "2" tace a hankali, "auh ba'ayi kenan nayi?" Yace ba taredayakauda idon shi akan ta ba, "kai ka tsaya ma kana mata dogon bayani Alhaji ta tashi ta komainda
ta fito, kuma wallahi tace zata ta da mai hankali ko za ta aikata wani shirme akan matarshi bamu ba ita"....
"Dama na daɗe ina faɗa miki ki guji ranar da zaki kai shi bango, ya yi miki me sauƙi ma, dayabarki tare da shi ya neman ma kan shi mafuta, ace ayi mace ba sanin daraja da mutumcinkanta, ke kenan bakya da aiki kullum se na waya, ba zan hanaki yin abinda ki ka ga shine dai-dai ba, sedai zan miki albishir ɗin zama Bowa a gidanki nan da wani lokaci, tashi ki wuce, kuma kai tsayeki
nufi gidanki, wallahi ko wani waje ki ka bi ya Allah ya isa" dattijuwan dake tsaye tun ɗazuabayan su tace idonta kafe akanta, kuka ta saki me ƙarfi tare da miƙewa zuciyanta na ƙuna, kaudakai suka yi daga kallonta har ta ja mota tabar gidan, kallonta dattijon yayi fuska washe damurmushi tare da miƙa mata hannu, kamawa tayi fuska cike da murmushi ta zagayo gabanshi.....
Comments fans🥰🙏
🫀MUGUWAR TSOKA 🫀
{🫀TA'ARE KALLUƊE}
[Muscle Cramp🫀]
) عضلة سيئة (
🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
written and Created ~~~~~~~~~~~~~~ ِبسم الله الرحمن الرحيم
By
Yardajjiya👩 💻
Page. Fifty five
Sautin taka matakala da ƙarfi ya sa hankulan su komawa ga wajen cike da mamaki, zare idosukayi gaba ɗayansu lokacin da Insu dake saɓe da Mairah cikin ado me matuƙar burgewa da ɗaukanhankali ta bayyanawa idanuwansu a guje tana haɗa matakalan a hanzarce, da alama akwai abintake san guje wa, ba su kai ga gano dalilin ba SSB dake tafe a bayanta ya bayyanan musushimaaguje da alama shi take gujewa, tana sakkowa cikin parlorn ta dire Mairah dake tiƙan dariyatayi
bayan Hajiya a guje tare da sakin ƙaran ceto.... Yana dirowa yayi inda take da sauri, ganin in ya iso wajen kamata ze yi yasata yin bayanKausaraguje tare da faɗin "Anty Kausar kicece ni" yin wajen Kausar yayi da sauri, "tsaya Sahabee, tsayatukun" Hajiya tace fuska cike da murmushi tare da kai hannu da niyyan kamashi, kaucewahannunta yayi tare da kai na shi hannun da zumman kamata....
Zilliyewa tayi da sauri tayi bayan Yasmin tare da faɗin "Mahmah temako ba zan kuma ba" tayi
maganan da ƙarfi tare da shagwaɓe fuska hannayenta duka biyu akan kafaɗunta, murmushi tasaki tare da faɗin "se dai in ba Insu ba" "wayyo uncle Jamil" tace tare da yin inda yake a gujesaboda kai hannu da SSB yayi gareta, murmushi ya saki tare da faɗin "ni kin san miƙaki zanyi ko"tura baki tayi ta koma bayan Kamil "daga ni har ke haɗawa za'a yi, ga shawara ki koma bayanHajiya zaki fi samun temako" Kamil dake sakin murmushi yace tare da nuna mata hanya, zareidotayi ganin SSB na gab da isowa tare da daka tsalle ta nufi Hajiya, taku biyu yayi ya cafkota.... Ƙara ta saki da ƙarfi tare da faɗin "na yarda" murmushi ya saki tare da ɗagata sama ya farajuyi
da ita, ban da dariya ba abinda take ɓaɓɓaka cike da shauƙi, se da ya gaji dan kan shi ya sauketafuska cike da murmushi wanda ke fitowa daga ƙasan zuciyarshi tare da faɗin "da ki ka ce kemewayau ne" girgiza kai tayi tare da dafa shi saboda jirin da ke ɗibanta tare da faɗin "na ba dagari
ai ba zan kuma ba" murmushi ya saki tare da riƙota ya nufi kujera ya zaunar da ita, zama yayi aƙasa kusa da ƙafafunta tare da riƙo hannunta a natse ya ƙureta da ido.... Murmushi ta saki tare da faɗin "kafi kyau yin kyau" tare da jan dogon hancin shi, murmushi yasaki me faɗi tare da riƙo hannunta dake kan hanci shi, "so ki ke ya ƙara tsayi" yace fuska ashagwaɓe, dariya ta saki tare da faɗin "ai ya gama tsayi" "waya ce miki?" Yace tare da miƙewa.... Miƙewa tayi tare da faɗin "da amarya zaku dawo ko?" Narke fuska yayi ya lanƙwasar da kai gefenkafaɗan shi na dama tare da faɗin "su Jabir zaki wa wannan tambayan Gorgeous" "mu tafi ne?" Alhaji Munnir yace murya cike da murmushi, juyawa yayi ya banka mai harara tare da wucewainda Hajiya ke zaune tana bin su da ido fuska cike da murmushin farin ciki, zama yayi a kusada
ita tare da faɗin "za muje aurowa bawan Allah aure a mana fatan alheri" murmushi ta saki cikeda so da ƙauna tare da faɗin "Allah ya tsare ku ya kai ku lafiya ya dawo da ku lafiya, Allahyasaku ƙullo alheri" ta jero addu'o'in cike da fata, murmushi ya saki bayan ya bi bakin saura wajenamsawa da amin tare da miƙewa, juyawa inda ya barta yayi ganin ba ta wajen ya sa shi farawaige-waige, "gani ta nan" tace tare da ɗaga mai hannu, tsaye take kusa da Alhaji Jamil sunamagana.... Ƙarisawa wajen yayi a natse, murmushi ta saki tare da miƙa mai hannu, miƙa mata na shi yayi aanatse, musabaha suka yi idanuwan su cikin na juna, "Allah ya kai ku lafiya, ya dawo dakulafiya, ya tsare mana ku, ya kare mana ku da ga sharrin ƙarfe, da sharrin mutane da aljanu, Allahyasaku ƙullo alheri" "amin" yace tare da jawota a natse ya rungumeta ƙam, "ki kula" yace a hankali
tare da hitting ɗin bayanta, jinjina mai kai tayi a hankali, zare ta yayi cike da kulawa ya ja hannunAlhaji Jamil da ya juya yana magana da Kausar suka fice.... Sakin baki tayi cike da mamaki, da murmushin yanda ta yi su Jabir suka dafa musu baya, riƙohannunta Insu tayi tare da faɗin "kai Anty Kausar tafiya za su yi fa lokaci na ƙurewa" tayi
maganan tare da danne dariyar dake taso mata, ture ta tayi kaɗan tare da faɗin "kyace hakamana" dariya ta saki tare da wuce wa sama a guje, sauke numfashi me sauti A'isha da Lubabatusuka yi, kallon su Yasmin tayi tare da faɗin "lafiya!" "Ina fa lafiya! Wai dama haka suke wannanabubuwan a gaban ku!"... A'isha tayi tambayan cike da mamaki, murmushi Yasmin ta saki tare da faɗin "me suka yi?"
"Wannan ai be dace ba, in ita yarinya ce shi yaro ne da ze biye mata su yi ta caka-caka hakaagaban Hajiya?" A'isha tace da alamun ɓacin rai a muryanta, "to wata ƙila a ji naki, ni fa cewanayi
Hajiya ma ta tattara ta bar nan ɗin ta koma gidanta kar su dinga sata jin kunya a gaban sirikai, yanzu dan Allah dubi mutanen dake wajen nan ba su ji kunyar ko ɗaya daga ciki ba se wani
abubuwa suke kamar ba su san da wanzuwan su ba" Lubabatu tace cike da takaici, "kumadai
akwai san ɗaurawa kan ku damuwa, meye ruwan Hajiya da rayuwarsu?" Kausar tace idontaakansu, "dalla rufe mana baki" A'isha tace tare da kallon ta...
"Rufe bakin ki Kausar, su yi abinda yafi haka ma a gabana, hakan nake san gani shi yasa nakezaune da su, bance ku zo inda nake dole ba bare ku ga abinda ze dame ku" ta idda magananasukunance tare da kallon stairs inda sautin sakkowan Insu ya riski kunnuwan su, tana
bayyanuwa idanunsu ta sakin musu murmushi tare da gyara jakan bayanta, ƙarisawa kusadaHajiya tayi tare da faɗin "zan tafi Hajiya" "Allah ya tsare ki kula ƴar albarka" "in sha Allah" tacetare da runguman Yasmin "Mahmah se na dawo" "Allah ya tsare" tace cike da kulawa, "Auntie'sse na dawo" tace da ɗan ƙarfi tare da ɗaga musu hannu, "Mairah bye" tace tare da kallonMairahdake jikin Kausar, ɗaga mata hannu tayi alamun bye, murmushi ta saki tare da ficewa da sauri....
Fitowa tayi daga cikin motan da kallo ɗaya zaka mai kasan kuɗi ya koka da ƙarfi, gyara facemaskɗin saman fuskanta tayi tare da bin farfajiyan asibitin da ido, numfashi ta saki me sauti taredazaro glass a jakan dake riƙe a hannunta, sakawa a saman fuskanta tayi tare da gyara zamanshi
da kyau ta sai-saita yanayinta ta nufi cikin asibitin a natse, tana shiga sashin da aka kwatantamata ta hango Gude dake janye da akwatin kayan Sudais ta fito daga ɗaya daga cikin ɗakunandake jere a wajen....
Tsayawa cak tayi tare da jingina da bango gefenta da sauri, zuwa tayi ta gittata ta wuce batareda ta lura da wanzuwanta ba, sauke numfashi tayi tare da ɗagowa ta fara takawa a natsetanufi
ciki, tana kai jiki ɗakin da aka kwatanta mata aka buɗe ƙofan, ja baya tayi da sauri, farar
dattijuwa dake kama da Abdull sak ne ta fito cike da kamala ta wuce, sauke numfashi tayi mesauti cike da samun sassauci tare da ɗaga kai sama, tana sakko da kan da niyya shiga ta saukeido akan Abdull da inda aka sassareshi ke naɗe da bandeji, ƙureta da ido yayi da alamunsangane waye, "Abdull!" Tace cike da zaƙuwa tare da rungume shi ƙam, "auchh" yace da ƙarfi, saurinsakin shi tayi tare da faɗin "sorry! I'm sorry" ....
Jingina da bangon wajen yayi tare da ɗago kai ya watsa mata kallon tsana da ƙyama, "Abdull!"
Tace da sauri tare da nufarshi, ɗaga mata hannu yayi tare da faɗin "kar ki kuskura ki matsoni, meya kawo ki wajena! Kin zo ki ga ko ni ma sun kashe nin ne?" Ya yi maganan murya a mugunkausashe wanda yaja hankalin Sudais da Nafi'u da Abdallah da suka fito, dan komawa gidadanSudais ya samu sallama.... Tsaya cak suka yi tare da zuba musu ido, girgiza kai tayi cike da tsoro me haɗe da mamaki taredasa hannu ta cire glass da facemask ɗin saman fuskanta da sauri cikin ɗin bin kiɗima tace"kasanme ka ke faɗamin kuwa Abdull! Ka da zafin ciwo da ɗimuwa ya saka ka furta min kalmomindabasu dace dani ba, Sa'adatunka ce fa wacce tayi sadaukarwa da dama dan ta rayu da kai" ta iddamaganan tare da matsawa gare shi, wani dumm ƙirjin Sudais ya bada lokacin da ta furta sunanta, se da ta furta sunanta sannan tantamanshi na ita ɗin ne ya goge, "ba dai danni ba dan kanki dai
Sa'adatu, ai san kan ki ba ze barki ki yi dubi ga wanin ki bare har ki temake shi, saboda sankanki
da ki ke yau ba Ziza a duniya, ni ma da da ƙaran kwana da na tafi" .. Rufe mai baki da tafin hannunta tayi da sauri tare da faɗin "daina faɗin haka, ba abinda zesameka Abdull, zamu rayu inuwa guda ni da kai, na ingantomana rayuwarmu, rayuwarmu tanangabaza tayi hasken da duniya zata sheda" fincike bakin shi yayi da ƙarfi tare da sa hannu biyuyaingijeta da ƙarfi, taga-taga tayi daƙyar Allah ya ba ta ikon riƙe bango, ba ta dawo daga zallanmamakin turetan da ta shiga ba saukan muryan shi a kausashe ya doki kunnuwanta, "ke har
yanzu mafarkin rayuwa inuwa guda ki ke dani? To ki daina dan abinda ba ze taɓa yuwuwabakenan, yanzu na sanki, na san baƙaƙen ɗabi'un ki wanda ki ke ɓoye mun, hayan iyayen da ki kayi
ya isko ni, wallahi ko ke ɗaya ki ka rage a duniya ba zan aure ki ba, Sa'adatu, ko ke ce magani
tsakanin rayuwa da mutuwa zan gummaci mutuwa da in shaki, maƙaryaciya mazinaciya, maha'inciya, ke annobace, banga abinda zanyi da wacce ta ma mahaifinta fyaɗe ba" gauuu, taɗauke shi da wani kyakykyawan mari wanda se da yayi taga-tagan faɗi, zare ido su Sudais sukayi
cike da mamaki, dai-dai lokacin dattijuwan da ta fita a ɗakin da Gude suka iso wajen.... Nuna shi tayi da hannu jiki na ɓari cike da ɓacin rai tare da faɗin "kama isa, nice matarka taduniya Abdull, da ni kaɗai zaka rayu, ban da masaniya akan waƴanda suka aikata muku hakan, se
dai na sha alwashin isa garesu ko su waye su in ɗaukan muku fansa, ka daina magana kamanmara wayau mana, buɗe idonka da kyau ka kalleni, Sa'adatunka ce fa, me sonka da ƙaunar ka, zan iya komai akan ka ka sani, zan iya sadaukar da komai dan kai ka sani" ta idda nagananmuryana rawa, "ƙarya ki ke Sa'adatu, na dawo daga rakiyan ƙarairayinki, kai na ma yi wawta danaaminta da wacce uwa da uba suka mutu da takaicinta, baki san wanda ya aikata mana hakabawato? To ni na sani, ɗan uwanki dake neman ki ido rufe ne, na san komai akan ki wanda ki kaɗaulokaci me tsayi ki na ɓoye mun, daga sharrin da ki ka laƙawa mahaifinki akan shi ya nemeki
zuwa turashi gidan yari da ki ka yi da mutuwansu da sabon duniya da ki ka buɗe" ya idda
maganan cike da ɗin bin takaici da ƙyama da tsana....
Sakin baki tayi da ɗin bin mamaki tare da faɗin "waya faɗa maka hakan!Ƙarya ne, so sukesurabamu, ƙarya wanda ya faɗa maka hakan yake, shi ya mun fyaɗe" ta idda maganan a rikicetareda nufarshi "dakata anan, ƴan uwanki za su miki ƙarya ne? To su suka faɗa min" "Iƙilima Sadiyazan tarwatsa rayuwarku kuwa" tace cike da fusata tare da ɗago kai ta kalleshi, da sauri
dattijuwan dake tsaye a gefe cike da mamaki ta ƙariso tare da faɗin "Abdullmuminu wacecewannan ɗin?" "Wacce ku ka ce kar in aura ne na ƙi jin maganarku, wacce a dalilinta na faɗawannan halin da nake ciki ne" ya idda maganan murya a kausashe.... Ɗago kai tayi ta kalli Sa'adatu cike da takaicinta da take ji tace "ya isa haka dan Allah, tarayyanna ku ya isa haka, dan Allah ki fita a rayuwar ɗana, ko ze samu yaga haske a rayuwar shi" "baindazani ina tare da shi har ƙarshen rayuwa" tayi maganan a fusace, "zako ki wahalta dan na amshi
tayin auren wanda suka ban tun farko" yace a kausashe, wani wawan dariya ta saki tare dafaɗin"ka farka daga mafarkin auren wata da ka ke, dan ni Sa'adatu ni ce marufin asirinka ɗakerufe"
"bangane ba" yace tare da ƙureta da ido, "ka je ka binciki kan ka kafin ka fara maganan aurenwatana, dan ba lafiyayye ka ke ba, ina jiran dawowanka gare ni" tana idda naganan ta maidafacemask da glass ɗin dake hannunta fuska cike da makirin murmushi wanda ta barwankantasanin ko na meye ta juya ta barsu sake da baki da ido, akan su Sudais da ke tsaye na su bakunanda idon a sake ta sauke ido....
"Wow! Gurgu ma yana wajen kenan, ka sauƙaƙa mun ba se na yi tattaki gareka dan isar makadasaƙo ba" wani banzan kallo Gude ta jefa mata tare da shiga tsakaninta da Sudais, "ah-ahdakataba gareshi zani ba, dan bana da lokacin miskini, kinga wan can" tayi maganan tare da nunaAbdull da tashin hankali ya gama bayyana a saman fuskan shi, "shine mijina ki yi ƙoƙari ki kai
ɗanki a duba lafiyarshi dan kar abun ya haɗe mishi biyu" tana kai nan ta juya fuska cike damurmushin shaƙiyanci.... Tana ɓacewa fuskokin su ta ɗaure fuska ɓacin ran da take dannewa ya bayyana a harzuƙetanufi
mota dan ji take in bata kawo ƙarshen numfashin Sadiya da Iƙilima ba yau ba zata iya barci ba, tana ɓacewa ganinsu Abdull da jikin shi ke ɓari yace "Umma!" Ya fashe da raunataccen kuka, tare da zubewa a wajen, bin shi tayi cikin rawar murya tare da faɗin "Abdullmuminu wani alaƙaya taɓa shiga tsakanin ku ne!" Jinjina mata kai yayi jiki na kyarma, fashewa da kuka tayi cikedarashin madafa.... Kallon Sudais dake haɗiyar zuciya Gude tayi tare da faɗin "muje Sudais" girgiza kai yayi taredafaɗin "bari mu yi gwaji" "wai ka yarda da abinda wannan mahaukaciyan tace ne!" Abdallahyacerai ɓa ce" "kasan fa komai Abdallah, please Momy ina son a gwadani" yace a hankali idanshi dasuka canza launi akan Gude, jinjina mai kai tayi jiki a mugun mace ta wuce dan magana dadoctor, kallon Abdull dake sharɓan kuka yayi cike da tausayawa tare da kallon Nafi'u, ba musu yawuceinda suke tare da ƙoƙarin temaka mishi ya miƙe...
Tunda suka fito ɗaga dakin gwajin ƙirazan su da na su Gude ke bugu, har wani rawan sanyi suke, ƙafan nan kuwa se kyarma take taƙi natsuwa waje ɗaya, addu'a kam ba su bar mai-maita dukwanda ta zo musu kai ba, duk wanda yayi ido biyu da su a wannan yanayin se ya yi muguntausaya musu, a wannan hali doctor ya fito tare da nurses biyu, miƙewa Gude tayi zumbur
zuciyanta na tsinkewa tare da faɗin "me gwajin ya nuna doctor! Dan Allah doctor kar ka cemunɗana Sudais ya kamu da wannan ciwon" ta idda maganan muryanta na rawa hawaye na wankefuskanta, "I'm sorry Hajiya, mun san da damuwa amma cuta ba shi ne ƙarshen rayuwa ba, akwai
maganin shi yanzu wanda mutum in yana sha ze iya rayuwa kamar sauran marasa ciwon, zeyi
aure ya haihu ba tare da ɗan shi ko ƴar shi ta kamu da ciwon ba, please zauna" ya idda maganancike da son fahimtar da ita, sakin baki kawai suka yi tare da bin shi da ido, "ta tabbata kenaninada shi" Sudais yace a rikice, "dan Allah ku kwantar da hankalin ku ya faɗi result" ɗaya dagacikinnurses ɗin tace tare da kallon su....
"Ku muje gida" Sudais yace murya na ƙaƙƙagewa tare da kallon Abdallah da jikkunansuyayi
mugun sanyi, "Abdullmuminu Shafi'u" doctor yace a natse, dumm ƙirjin Abdull da na Ummayabuga da mugun ƙarfi, a razane suka ɗago kai suka zuba mai idon da suka fiffito waje ba taredasun sami zarafin cewa komai ba, ganin irin kallon da doctorn yake musu yasa Umma cewa"na'amga yi nan"....
"Ku yi haƙuri da abinda zan faɗa, kamar yanda na ce muku da farko cuta ba shine mutuwaba, sannan ze iya rayuwa kamar kowanni mutum mara cutan, ya samu ciwon ya kuma yi tasiri ajikinshi sosai saboda be shan magani, yakamata ya fara shan magani dan kar ya kai shi ƙasa" tundayafara bayani Umma tayi suman tsaye, Abdull kuwa ji da ganin shi ne ya bar gan-gan jikinshi ɗif, ba wanda ya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 88 Chapter of 109