Share this page
kula da yanayin da suke ciki, maida duban shi ga su Gude da suka zama kamandolaye yayi tare da faɗin "Muhammad Sudais ko?" Jinjina kai Abdallah yayi da sauri, "congrat baka ɗauke da cutan, Allah ya ƙara lafiya" wani ihun farin ciki Abdallah da Nafi'u suka saki, Gudekuwa kai tsaye sujud ta wuce dan gode wa mahaliccinta, Sudais kuwa ya kasa iya furta komai, besan farin ciki yana riskan mutun yakasa magana ba se a yau, "ku muje gida" Gude tace taredawuce wa gaba, riƙo Sudais suka yi tare da kallon su Abdull, ganin halin da suke ciki ya sa Abdallah sakin Sudais ya wuce da sauri ya kira doctor, nan aka kwashe su a ka yi ciki da suahanzarce.... Suna isa ƙofar gida suka fara cin karo da abin mamaki, decoration aka wa ƙofar gidan cikedaburgewa, murmushi suka saki tare da nufar ciki, anan suka soma diburburcewa dan sunfaratunanin anya gidan da suka sani suka shigo kuwa! suna isa ƙofan da ze sadasu da cikin gida, ƙaran tiskewan balanbalan ya shiga kunnuwansu, kafin su yi wani motsi, abubuwa masu ƙyalƙyali sun kawo musu ziyara, nan da nan fuskokin su ya washe da murmushi, suna cikinbinabin mamakin da ido farin ƙyalle da aka rubutu welcome home a ciki da manyan baƙi me ruwanzaiba ya ziyarci idanuwansu, murmushi Sudais ya saki tare da bin ƙyallen da ido, buɗe ƙofanparlorn Gude Farisat tayi fuska cike da murmushi cikin ƙwalliyar biki tare da faɗin "barka dadawowa gida Yaya Sudais" murmushi ya sakin mata cike da jin daɗi, "barka da dawowa gidabigYaya" Yasmin da ta leƙo ta bayanta tace fuska washe da murmushi, murmushi ya saki taredajinjina mata kai, nan su Nafi suka fiffito suka marabcesu, "bismillah ku shiga" Farisat tacetaredawuce wa gaba, ba musu suka rankaya suka shiga ciki, nan suka zama ƙauyawa, se bin parlorndaido suke saboda ganin yanda ya tsaru da kwalliya... "Wannan duk na dawowan Sudais gida ne!" Gude tace cike da mamaki, murmushi suka saki tareda ɗaga mata kai, "lallai Sudais ɗan gata ne kai" tace fuska cike da murmushi, "sosai Anty Gudega ruwan zafi can a sake mai ya watsa abinci na saman dining zamu wuce gidan biki damamunjira isowanku ne, su Anty Suwaiba sun ce ace miki in suka taso daga can za su biyo nan" "toshikenan ƴan albarka se kun dawo" tace cike da ƙauna, "ba dawowan yau ba, ana ɗaura aurezamu rankaya da su mu mika amarya Ɓadamayya, mu da dawowa se jibi" "yakamata ai kuneƙawayen" tace cike da girmama dattakon su, "Halima ku ɗauki naku kayan ku bi su" tayi maganan cike da jin hakan shine dai-dai, tsalle suka saki tare da shigewa ɗakinsu a guje.... Da sallama a saman laɓɓa suka shiga gidan, amsawa jama'an da ke cike maƙil a tsakar gidansuka yi cike da kulawa, "sannun ku dai" Yasmin tace tare da sakin musu murmushi ta wuce, "tokinga yaran da nake ta kwatanta miki ance kawun su Yayan Mamansu ne ze auretan" watadattijuwan mata tace a hankali, buɗe baki wacce take faɗawa tayi tare da kama haɓa, "ki cebabba ne, wacce ta haifi waƴan nan ai babba ce bare shi kuma da ya girmeta" "aikuwa dai, tobagwara shi ba ya yarda ze aura, shekara nawa ana fatan mijin ya zo shiru" wacce ta ba da labarintace cike da takaicin matar, girgiza kai Farisat da ta jiyosu tayi ta shige ɗaki kasantuwar itaceabaya.... Su na shiga ɗakin suka saki ihu saboda ganin yanda Iƙilima ta haɗu ta haɗe a cikin wata ni'imtacciyar lace dark green, lalli da kitson nan ma sha Allah, tunda Allah ya ba da wadataccengashin, "ƴan rainin hankali se yanzu ake ganinku? Ai na so ƴan ɗaurin auren su dawo muwuce, ku ji a salansa" Rahma tace tare da banka musu harara, dariya Farisat ta saki tare da faɗin"ai amarya ba zata bi ku ba kuwa, dan ƙafata ƙafarta" "lallai baki ji da kyau ba, ga malamangoyazotafiya da ita ina zata tsaya jiranki" "wallahi ba su dawo da wuri ba ne, se yanzu, dawowansufitowan mu" Farisat tace tare da gyara zama, "haba ai kun zaunu ba ƙarya" "ke dai bari inaSafinat?" "Gani toilet na shiga" Safinat da ta shigo tace tare da zama kusa da Halima, "ki kasancea dama na" tace tare da sakin murmushi.... "Ƴan ɗaurin auren sun iso ne?" Yasmin tace a natse, "tun yaushe har sun tattara sun tafi canindaza'a ɗauran" Hasinat tace tare da kallonta, "ma sha Allah, Allah yasa a ɗaura alheri, se mufarashiri dan ana gama ɗaurawa uncle Jamil yace se tafiya" Farisat tace tare da miƙewa, sallamaSadiya da ta gama haɗuwa a nata tufafin tayi tare da faɗin "ma sha Allah dama ke na zo nema, bakin ce ƴan uwan Baba biyu na Mama biyu za'a ɗauka ba?" Tayi maganan idonta akan Farisat, "eh"tace idonta akan ta, "to ga su can ko wacce na shirin zuwa, wai da su za'a tafi dukansu" "rabudasu rakiya airport za su yi" Hasinat tace tare da sakin dariya, "wallahi kuwa" Harira da ta shigotace cike da takaici, "yawwa Harira da Nafi da Halima za su zauna matsayin ƙawayen Amarya, keda Safinat da Hasinat matsayin ƙannin amarya, ni da Yasmin da Rahma as Auntie's, Ummi daMama (Maman Harira) sune cikon gurabai ukun da aka ba wa ƴan uwan uwa da uba, ina gahakanyayi ko?" Ta idda naganan tare da kallon su, "sosai ma" Sadiya tace cike da jin daɗi, "to mutashi kar su yi ta jiran mu" tace tare da kallon su, ba musu suka mimmiƙe kowa ta saɓi kayanta.... A tamanin ta taka burki a ƙofar gidan, ji ka ke ƙiiiiii, hakan ya ja da yawan hankalin matasananguwa dake cike da farin cikin auren Iƙilima, fitowa tayi a fusace ko rufe ƙofan ba ta samuzarafin yi ba ta wuce ciki a hanzarce, ji take dama ta rufe ido ta buɗe ta ganta a gaban SadiyadaIƙilima, tana shiga kallo ya dawo kanta, ko kula da yawan jama'an dake gidan ba tayi ba tafaraƙwalawa Sadiya da Iƙilima kira, da mamaki suka fiffito dan ganin ko lafiya, a fusace tayi kanSadiya dake ƙoƙarin saka takalmi ta jawota da ƙarfi ta yasar da ita a gefe, "dan... Ubanki wayabaku daman zuwa wajen Abdull har ku mishi magana a kaina? Na saku ne? Na shiga rayuwarkune?Ko na damu da abinda ku ke aikatawa ne? Kun ce in manta daku na shafe babun ku a rayuwatamenene na min bi ta da ƙullin! wallahi duk wacce ta ƙara gigin kusanta na ko abinda nakesose na sata nadaman rayuwarta a cikin ku, banzaye marasa aikin yi" jawota Iƙilima da ta isa wajentayi a fusace, tana juyowa ta sauke mata maruka biyu kafiyayyu a kunci ɗaya, cikin tsan-tsanɓacin rai tace "waya damu dake da har zaki zo har gidan ubanta ki ce zaki mata warning!"... "Mu mun manta da wata halitta me zubi dake ma bare kuma ke, ba ma da lokacin ɓatawa akanki bare har mu damu kan mu akan abinda ya shafe ki, ki je ki nemi wanda ya ma rayuwarki katsalandar ba Iƙilima da Sadiya ba, ga hanya nan ki bi ki fice yanzu kafin zuciya ta ɗibemumumiki abinda ba zaki taɓa mantawa ba har ki koma ga mahaliccinki" zare hannunta da ta dafekuncinta da ya sha mari tayi cike da mamaki tare da faɗin "ni ki ka mara Iƙilima?" "Ta maratakuma mari banza" Sadiya tace tare da miƙewa a harzuƙe, wuri-wuri ta fara dan neman abindazata iya naƙasasu, idonta na sauka akan taɓarya ta nufi inda yake a guje ta ɗakko ta nufesuafusace, da sauri Yasmin ta sha gabanta tare da ƙureta da ido, "matsamun a hanya Yasmin, wannan ba abinda ya shafe ki ba ne" tace rai ɓace, "ban tsaya dan abinda ki ke tunani ba, nasanzuciyarki ta raya miki dan tuna baya na yi hakan ko? To ba haka ba ne, na shiga tsakani nedanyanzu ita ɗin ɗaya daga cikin ahalin mu ce, kafin wani ya kai ga cutar da yatsan ɗan cikinahalinmu se ya wuce matakai kamar dai haka" bude baki tayi da zumman ba ta amsa Ɗan kuka danahannun daman Sarari suka faɗo gidan.... Shigowa Kabir yayi tare da faɗin "ga motoci nan masu raka amarya su taso, sun wuce airport su" "ku muje jama'an arziƙi muna da abubuwan yi, amarya me capasity zamu kai, abin na jirgi dajirgi ne" Farisat tace tare da wuce wa, "aure! Wa ze yi auren!" Sa'adatu tace da mamaki, "Iƙilima" Yasmin tace tare da watsa mata kallon kyama da tsana, "a ina ta samu mijin!" Tambayanyakuɓuto mata da alaman da zuciyanta take, "Allah ya kawo shi, ba ruwanki a inda ta same shi" tana kai nan ta wuce ta barta da su Ɗan kuka, haka suka rankaya suka fice, da masu rakiyabakinmota zuwa masu rakiya airport, suna fita suka shishshige mota suka ɗauki hanya, suna tabbatarda ficewan su a anguwan ɗaya daga cikin matasan dake zaune a wajen ya saki fito me ƙarfi wani duka Ɗan kuka ya kai mata a gwuiɓi, ko kafin ta samu daidaito Ɗan amanan Sarari ya taɗiyeta, ji kake tim a ƙasa" ta faɗi da ƙarfi ta bugu da bangon wajen, wani marayan kuka ta saki taredakama kanta dake masifan zafi.... Shigowa Kainuwa yayi ya bi ta da kallon sakanni, ɗago kai yayi ya kallesu tare da faɗin "kujawota waje" yana kai nan ya fice, babu musu suka jata kamar kayan wanki suka fice da ita, agaban Sarari dake zaune saman kujera suka watsata, "wato ke ƴar iska, na yi miki gargaɗi akankar ki ƙara shigowa anguwan nan sau nawa!" Jin tayi shiru ya sa shi faɗin "wato ba ki ji bakenan?" Murya a kausashe, "dalili ya sani shigowa, da ƙanninka ba su shiga gonata ba, ba abindaze kawo ni anguwar, ka gargaɗesu akan shiga harka ta, bana jinkiri wajen ɗaukan hukunci gawanda yayi ƙoƙarin kutse a rayuwata ba ko waye shi" ta idda maganan a harzuƙe cike da rufewanido, sakin ido da baki suka yi tare da bin ta da ido, ganin irin kallon mamakin da suke bintadashi yasa Kabir da zuciya ta zowa wuya fizgan sandan dake hannun ɗaya daga cikin su ya nufetaaharzuƙe, yana isa be yi wata-wata ba ya ɗaga sandan ya zube mata a baya da dukkanin ƙarfinshi, "wash!" Tace da ƙarfi tare da gantsarewa, ƙara ɗagawa yayi ya zube mata, bajewa tayi a wajencike da azaba tare da murƙuƙusu, ganin yanda yake dukanta da sandan ya sa Sarari kallonKainuwa, murmushi ya saki tare da takawa ya isa kusa da shi ya riƙe sandan da yake ƙoƙarinsauke mata.... "Wannan aikin na mu ne, na ka ba da umurni ne mu bi babban Yaya, bar mana ita mun sanyandazamu yi da ita" ya idda maganan cike da rarrashi, sakin mai sandan yayi ya matsa gefe taredasakin numfarfashi, kallon yaran dake tsaye suna jiran umurni Kainuwa yayi kafin wuce wansecond sun rufu akanta, suna duka da dukkanin ƙarfin su, nan da nan mutanen anguwa mazadamata suka fito, ba ban bakin da ba su yi ba amma ko kallon inda suke ba su yi ba, ganin zasuiyakisan kai ya sa ɗaya daga cikin dattijan dake gefe ya kalli matashin dake kusa dashi tare dafaɗin"maza hanzarta ka kira Malam Sulaiman in ba haka ba za su kashe yarinyar nan" da guduyajuyayayi gidan su Harari, be jima ba ya dawo tare da Baban Harira dake a rikice dan jin bayanindamatashin ya mai, "ashsha subhanallahi wani aiki ku ke haka Salisu!" Yace cike da damuwa.... "Baba rabu da su suyi aikin lada, ko sun kasheta sun rage mugun iri ne" Kainuwa yace cikedarashin damuwa da abinda ya faɗan, "bar wannan maganan ahka Lukman, ya da hankalinkadasaninka zaka ɗaurawa kan ka nauyin da baka san lokacin da aka aikata ba, haba Kabir kanawajenake wannan aikin!" Ya idda maganan idon shi akan Kabir, murmushi ya saki tare da sosa ƙyeya, "Salisu dubi girman Allah da darajar ma'aikin shi ka ce su ƙyale yarinyar nan kar su kasheta, kubarta da nauyin zunnuban da ta ɗaukan wa kanta, kar ku ɗauke mata shi, ku barta da tsiyandata shukawa kanta kaɗai ya isheta" ya idda maganan cike da roƙo, ganin yanda Sarari ke kallonmasudukan yasa Ƙanin Harira matashi ɗan 21 year's wuce wa gidan man dake gefen su a guje, sumfutan fetur ɗin da ake zuba ma wani a ƙaramin galon yayi ya wuce a guje, kai tsaye wajenmotan ta yayi ya fara zazzagawa.... "Ku rabu da ita taci arziƙin masu arziƙi" Kainuwa yace tare da kallon su, ba musu suka mammatsadaga kanta duk da ba haka suka so ba, "miƙe ki bar anguwan nan, mu kan mu ba buƙatanganinki muke ba" Baba yace rai ɓace, goge jinin dake bin bakinta tayi tare da miƙewa ta nufi motantayanda take tafiyan kawai ze sanar da ba bugun wasa suka mata ba, tana kama mariƙin murfinmotan ya ƙyatta ashanan da ya amso wajen me shayin ƙofar gidan su tare da jefawa a motan, bumm" wuta ya tashi, sakin ƙofar tayi da sauri saboda laso fuskanta da wuta yayi, kafintayi wani yunƙuri guguwan wutan ya watsar da ita gefe, "oh shitt" yace cike da baƙin ciki dan ba hakayasoba, ya so ta ƙone ƙurmus a cikin wutan ne.... Murmushi Kabir ya saki tare da kallon shi, narke fuska yayi alamun ba haka ya so ba" nufartaƊankuka da amanar Sarari suka yi tare da fizganta suka watsar da ita gefen hanya tare da nunamatahanya fuskoki ba wasa, miƙewa tayi jiki na ɓari ta miƙe hanyan tana tafe tana ɗingisawa, dantafahimci barin anguwar shi ne maslaha, dan tsaf za su iya kasheta in ta cigaba da zama, tanaɓacewa ganinsu mota ta faka a gabanta, ko kafin tayi tunanin waye maza biyu sanye da hulanfuska baƙaƙe sun diro, juyawa tayi da zumman guduwa ɗaya daga ciki ya cafkota tare da dannebakinta ya turata cikin motan, bayansu ɗayan ya bi ya rufe murfin motan da sauri suka takamotan a sittin suka bar anguwar.... "Allah ya muku albarka da jin maganan da ku ka yi ya shirya ku" Baba yace cike da jin daɗi, jinjinamai kai suka yi cike da jin daɗin addu'ar da ya musu, juyawa yayi ka ko kunnin matashindayacinnawa mitan wuta tare da murɗewa da ƙarfi tare da faɗin "baka ji ko?" "Auch Baba" yacetareda saka hannunshi biyu a wajen kunnin, murmushi Kabir ya saki tare da faɗin "a mai afwa" "kadinga mai nasiha Aliyu be jin magana" yace tare da sakin mai kunnin ya wuce gida, nan saurasuka fara watsewa, kallon Kainuwa Sarari yayi tare da faɗin "a shirya mana fita yau akwai operation" yana kai nan ya wuce, ihu suka saki cike da jin daɗi, murmushi Kabir ya saki taredagirgiza kai yaja hannun Aliyu da farin ciki ya lulluɓe suka juya suka nufi gida.... Tafiya suka yi da ita me tsayi wanda ba ta san ko ina suka nufa ba saboda tamke mata idodabakin ƙyalle me kauri da suka yi, suna isa inda aka ba su umurnin kaita suka taka burki buɗemotan suka yi suka fito jaye da ita suka nufi kangon gidan saman dake wajen, jefa ta sukayi aɗakin da suka shiga tare da koma wa gefe suka tsaya, murmushi Shila dake zaune a samankujeran roba da muƙarrabanta shiryayyu ta saki tare da ba ma ɗaya umurnin kwance mataido, ba musu ya ƙarisa inda take ya riƙo gashinta da ƙarfi ya kwance mata ƙyallen tare da wankamata lafiyayyan mari, ko gezau ba tayi ba saboda sauke ido akan Shila dake zaune tana sakinmata murmushin da ta barwa kanta sani da tayi, guntun murmushi ta saki tare da kauda fuska.... Ta sowa tayi ta ƙariso inda take a natse ta duƙa irin durƙuson Hajiyayyun nan tare da faɗin"bazan ja dogon zance da ke ba Sa'adatu, abinda ki ka satan ma Alhaji Namadi nake son ki miƙomincikin ruwan sanyi, ki yi tafiyanki in yi nawa, ba ma da haɗi, kin sani na sani" ta idda maganantareda bin fuskanta da ido, wani banzan dariya ta saki me sauti tare da faɗin "labari ya isko ki kenan?Na san za'ayi hakan" "ban tambayeki dogon bayani ba, inda abinda ki ka sata yake zaki faɗamana, kar ki yi jayayya ko taurin kai ki zama me wayau" tayi maganan a kausashe, "zaki mutubaki ji ba kuwa" tace a dake tare da kallon ta, wani guntun murmushi ta saki idonta ƙyama natatare da miƙewa a natse ta koma inda ta tashi tare da faɗin "da alama tana buƙatan ku tambayetada kan ku" ko kafin ta rufe baki sun rufu akan ta, dukanta suke ba ji ba gani, kafin wuce wan20minute's ta gama ficewa daga hayyacinta, sun kumbura mata ido baki, sun canza mata halittanfuska gaba ɗaya, ban da jan numfashi daƙyar ba abinda take.... Murmushi Shila da ta dakatar da su ta saki tare da ɗago kanta dake sunkuye da hannu, cikedamurmushin da be ɓace a saman fuskanta ba tace "na san yanzu kin shirya, in baki shirya basuashirye suke su saki faɗa dole" jinjina kai tayi daƙyar idonta dake mar-mar a sama fuskanta, murmushi ta saki tare da faɗin "da ki ka ce kema shegiyace, a she da sauranki, yana ina!" Tacecike da kaushin murya, "matso" tace cikin jan numfashi da ƙyar, kallon su tayi fuska washeda murmushi tare da faɗin "kar ku kasa kunni sirri zamu yi" ta idda maganan tare da kecewa dadariya, dariya suka saki cike da mugunta, matsawa tayi da kunninta saitin bakinta tare dafaɗin"ina ji" motsa laɓɓa daƙyar tayi tare da faɗin "yana jahannama kusa dake" ta idda maganantareda tofa mata miyan bakinta dake haɗe da jini da majina, saurin matsawa tayi cike da razani tareda baza mata ido, dariya ta saki mara sauti wanda kallo ɗaya zaka mai kasan a wahalce takeyi ... Miƙewa tayi a harzuƙe tare da faɗin "ku daketa har se tayi magana dan kanta" tayi maganantareda zaro waya ta danna number ta kara a kunni, kaman jiran kiran ake ringing ɗaya aka ɗaga, "gata mun sameta yallaɓai" "ta baku!" Yace a rikice, "a'a ba dukan da ba su mata ba, numfashi madaƙyar dake fiddawa amma ta ƙi faɗa" "kina da hankali kuwa!" Yace da ƙarfi, "sorry yallaɓai" tacea hankali, "sorry for your self, in ta mutu fa, na faɗa miki abinda take tattare dashi rayuwatane, cewa nayi ku amsa se ku mata abinda ya dace, ba cewa nayi ku kasheta kafin ku amsa ba" "yayi maganan da ƙarfi, "ku dakata!" Tace da ƙarfi, tsayawa suka yi cak tare da kallonta, alamutamusu da su matsa gefe ba musu suka matsa, "haɗani video call da ita" yace cike da samunsassauci, "to yallaɓai" tace tare da maida kiran video ta matsa kusa da ita ta kara mata wayanafuskanta da ta ɗago.... "Wannan wani irin wawanci ne Shila! Haka na ce ku yi mata! Dama ba zaki iya aikin ba ki kacezaki iya?" Yayi maganan zuciya a mugun ɓace saboda yanda ya ga ta koma lokaci guda, "sorryyallaɓai" ta kuma cewa jiki na ɓari, tsaki ya ja tare da gyara zama, "Sa'adatu!" Yace a natse, buɗeidon dake mar-mar a hankali tayi tare da kallon screen ɗin, ganin hasken screen ɗin na cutar daidonta ya sata maida idon ta rufe tare da tofar da jinin da ya cika mata baki, "oh shitt, ba kukyauta mun ba" yace cike da damuwa, "afwan yallaɓai taurin kai ta so yi" "tayi mana ina ruwanki"yace cike da damuwa, "ayi haƙuri yallaɓai" ta kuma cewa cike da girmamawa.... Murmushi Sa'adatu dake jiyo su ras ta saki tare da motsa laɓɓa a hankali cikin muryanta dayadisashe tace "abinda ka ke buƙata na hannu na, kuma rashin komawa na gida yau shi ze fiddowaduniya abinda ka ke tsoron su ji" "ke! ke! Tsaya!" Yace cike da fargaba, buɗe ido tayi tare da sauke wa akan shi, "baby!" Tace cike da shaƙiyanci, "Sa'adatu ina yake! Abinda ki ke tare dashi rayuwata ne, ki riƙe komai da ki ka ɗauka ki dawo mun da shi!" Ya idda maganan da ƙarfi, "ni matawa rayuwar ai tana hannunka, kwanciyar hankalinka da cigaban rayuwarka cikin aminci kamarda, shine komawata gida a raye" tayi maganan tare da murmusawa, "me ki ke nufi!" Yaceidowaje, murmusawa ta kuma tare da faɗin "saɓanin shi babu daɗin ji, zuwa gobe bommm, wutazata ta shi, babu motan kwana-kwanan da za ta iya kashewa, bom ɗin na hannuna, kai kumakana da maganin kashe shi kafin na tashe shi, mu yi wani wasa mana" ta idda maganancikedaƙarfin hali dan a jikkace take.... "Shila ku sake ta, ku ƙyaleta ta tafi" yace a hanzarce, "yallaɓai!" Tace cike da mamaki, "na cekuƙyaleta shin bakwaji ne!" Yace da ƙarfi, "to yallaɓai" tace cike da girmamawa, "Sa'adatukar ki wasa da wuta, dan ze iya koneki ƙurmus" yace cike da gargaɗi, murmushi ta saki tare da faɗin"Sa'adatun da kanta wuta ce, wasa da wuta ɗabi'a tace dan yana ƙara mun ƙarfi da izza, kar kamun baraza ban fito filin ba se da na shirya" tayi maganan a dake, bin ta kawai suka yi da idocikeda mamakin ƙarfin halinta, ɗagata maza biyu da Shila ta bawa umurni suka yi "ku maidataindaku ka ɗakkota" tace ba din rai ya so ba" ba musu suka jata suka fice da ita, "a saka ma dukwani motsinta ido" yace tare da katse kiran ƙitt, tsaki Shila ta saki cike da takaici, tare da nufar ƙofanfita dafa mata baya muƙarrabanta suka yi da sauri.... Suna shiga cikin anguwar suka taka burki , buɗe murfin motan suka yi suka hurgota wajetafaɗintim, "wash" tace tare da kama ƙafarta dake aika ma ƙwakwalwanta da saƙok azaba, ɗagokai tayi a wahalce ganin yanda jama'a suka fara taruwa a wajen ya sata ƙoƙartawa ta miƙe da ƙyar tafara jan ƙafa, ban da addu'an samun abun hawa ba abinda take a ƙasan zuci, dan ba ta sanlabari ya iske su Sarari kafin ta bar anguwan, a cikin wannan firgici napep ya zo wucewa, da sauri tatsaidashi da hannu biyu, yana tsayawa ta riƙe ƙarfe ta shiga da sauri tare da faɗa mai indazekaita, "subhanallahi Hajiya waya aikata miki wannan abu haka, asibiti yakamata mu fara zuwa, ko police station ki shigar da bayanai" me napep ɗin yace cike da kulawa, ko kallon inda yakebatayi ba bare yayi tsammanin samun amsa, ganin haka ya sa shi tsuke bakin shi ya maida hankalinshi ga tuƙi da hanya.... Banda sautin kuka ba abinda yake tashi a ɗakin, tun da suka dawo hayyacin su suke sharɓankuka babu me ƙarfin zuciyan hana ɗayanshi yi, jan hanci Umma tayi tare da faɗin "Allahmasheda ne a irin tarbiyyan da muka ba ku kai da sauran ƴan uwanka, duniya ma tasheda, sedai kai naka ƙaddaran ta zo da abu me firgitarwa Abdullmuminu, na girgiza da jin wannan abu dakaketare da shi, sannan na yi godiya ga mahaliccina da ni kaɗai na ji mahaifinku be ji ba, Abdullmuminu ba zan tambayeka komai a kai ba, se dai zan ce maka ka ji tsoron mahaliccinka, kar ka tsorace mu ka ɓoye zahirinka ka bayyana mana baɗini, lallai yarinyar nan taa yi manamugun sara wanda ba mu san ranar warkewan shi ba" ta idda naganan cikin rishin kuka.... "Ze warke a yau Umma, ki daina kuka, ban aikata komai da ita a cikin hayyacina ba, da zuciyaɗaya na ƙaunaceta, na so kuma aurenta, bugar dani tayi ta samun ƙwayan ta'azzara sha'awaharna je gareta, sau ɗaya ne ya faru ban bari ya kuma faruwa ba, ki yafe mun, ku yafe mun, ni nesanadin zubar hawayenki yau, ban so in zama gobe" yana idda naganan ya miƙe ya nufi ƙofa, "inazaka?" Tace murya a sanyaye idonta akan shi, "ki koma gida zan dawo zuwa anjima" yace adaketare da danne kukan dake taso mai ya fice, sauke ajiyan zuciya me ƙarfi tayi tare da miƙewa.... "Wow! Ma sha Allah! Idan ku na ganin abinda nawa ke gani kuwa! Yaa subhanallah yanzudukwannan mallakin Anty Iƙilima ne! ALLAH buwayi, Anty Iƙilima buɗe ido ki ga baiwar da mahaliccinki ya miki ki gode mai" Farisat dake bin ɗakin da ido tace tare da kallon inda Iƙilimakezaune, ganin ta kasa ko motsa yatsa yasa ta faɗin "Sadiya yaye mata mayafin nan duk mune, babu bare, wanda yace kin yi rashin kunya shima be da kunya" dariya suka saki cike da burgesuda side ɗin yayi, "gaskiya waje se ma sha Allah, wanna shi ake kira shigo da akwatin ka" Rahmatace ido na bin ɗakin, "ai akwatin ma an hutashsheta Anty Rahma" Yasmin tace tare da nunamusu saitin akwatina biyu dake jere a gefe.... "Yaa ilahi wa sayyadi, kai jama'a kun taɓa jin amarya me capasity kuwa?" Farisat tace tareda nufar wajen

Chapter 89 of 109