har da wannan dalilin yasa shi zuwa" jinjinamata kai tayi cike da gamsuwa, "ah lallai uncle Kamil ya yunƙuro" Farisat tace tare da sakinmurmushi, "aifa ba da wasa muka shigo Bertuwa ba" Insu tace tare da sakin murmushi.... Suna shiga cikin hospital ɗin suka sassakko, "haka aka gyara asibitin nan dama!" Safinat tacecike da burgeta da asibitin yayi, kallonta Rahma tayi tare da faɗin "tun yaushe! Aiki ma yafaratsufa" "lallai na daɗe ban shigo ba" tace tare da jinjina ƙoƙarin da gwamnati tayi a asibitin, "kai
jama'a har yanzu ban daina mamaki ba, Bertuwa ta amshe ma Ɓadamayya ɗiya guda ga
Ɓadamayya na shirin wasoso" Rahma tace tare da kallon su, "kai jama'a wallahi matsalatadakekenan, dawo da bara bana, ina mun gama wannan maganan!" Farisat tace tare da zaro wayantata dannawa Sadiya kira, ringing ɗaya ta ɗaga tare da ɗaga mata sallama cike da zumuɗi, "gamuaparking space zo ki shigar damu" "ganinan!" Tace cike da farin ciki....
"Tana kusa ko?" Rahma tace tare da kallonta, "eh gata nan tace" tayi maganan tare da binwajenda ido, ba su jima ba Sadiya da Harira suka iso cike da farin cikin ganinsu, "oh Yaa Allah wannanfarin ciki haka kaman an baku kyautan Hajji da Umrah" Insu tace cikin yanayinta, dariya Hariratasaki tare da faɗin "farin cikin ganinku ne ai" "to kafin mu idda farin cikin anan ku mu ƙarisaciki" Farisat tace tare da wucewa gaba, "oh baiwar Allah ba musan kin sani ba, ai da bamu sha
tsayiwan jira ba" Rahma tace tare da kama haba, juyowa tayi ta banka mata harara tare dafaɗin"Sadiya shige muje" ba musu ta shige fuska yalwace da murmushi....
Tura ƙofan ɗakin tayi baki ɗauke da sallama tare da faɗin ku shigo" ta idda maganan taredabasu hanya hannunta riƙe da ƙofan, shiga suka yi bakuna ɗauke da sallama, amsawa jama'a dakekusan cike da ɗakin suka yi fuskokin wasun su cike da murmushi....
"Bismillahnku, Farisat Insiyyah sannunku da zuwa, ke da ku ka shawo gajiyar hanya da hutawaki
ka yi ai Insiyyah" Mama tace cike da jin daɗin ganin su, murmushi ta saki tare da faɗin "ai
bakomai Mama" "sassannun ku da zuwa, Rahma Asiya Safinat, sannu Yasmin" murmushi sukasaki tare da kallon Hasinat da ta zare ido jin ta canza mata suna tare da danne dariyarsu....
"Sannunku Yaya Kabir" Yasmin tace da kulawa, "yawwa barkan ku da zuwa" yace fuska cikedamurmushi, "Yaya Salisu ya gajiyar hidima kai ne ban wa bangajiya ba" Farisat tace tare dakallonSarari, murmushi ya sakin cike da kame fuska tare da amsa mata, "wannan ne Yaya Lukmanko?"Tace tare da kallon Iƙilima da bakinta ya kasa rufuwa, jinjina mata kai tayi tare da faɗinshine, Kainuwa na Sarari" tayi maganan cike da fasa mai kai.... Murmushi ya saki tare da faɗin "ni ne Kainuwa dashen Allah, na Sarari me ƙara gudun doki" dariya suka saki idanunsu akan shi, nan suka shiga gaishe-gaishe cike da murmushi, "ya jikinnata?" Farisat tace idanta akan Sa'adatu...
"To ba ma ce ga yanayin shi yau ba, dan tunda ta tashi a haka take" Harira tace tare da zubemaSa'adatu idanunta, "a hakan nan na taddata tunda na iso" Iƙilima tace tare da gyara zama, murmushi Sadiya ta saki tare da faɗin "wataƙila ta gano an sheƙe ango Abdull a mafarki neshiyasa take zaman makoki" tayi maganan cike da iya shege, dariya Harira da Iƙilima sukasaki
tare da kallon Sa'adatu da ta ɗago kai ta zube ma Sadiya rikitattun idanunta da suka kaɗelokaci
guda... Bin shi da ido su Farisat da ba su gane inda maganan ya nufa ba suka yi dan san ƙarin bayani, "ai
ba a mafarki ba ne a zahiri ne" muryan Sarari ya doki kunnuwansu, juyo da dubansu gaba ɗayakan shi suka yi cike da mamaki, kauda kai yayi tare da faɗin "ya mutu" "ya mutu!" Harira daSadiya da Iƙilima suka ce a rikice tare da maida dubansu kan Sa'adatu da ta zabura idantaakanshi, "ita kuma ta kashe shi, kisan walaƙanci" yace idanshi kyam akanta, ba su Iƙilima da kalman
ita ta kashe shi da ya doka ba har su Insu se da suka yi suman zaune dan jin tayi kisa....
"Wani magana ka ke haka Salisu!" Mama tace cike da firgici, "Salisu kasan abinda ka ke faɗi
kuwa!" Kabir yace tare da nufarshi a zafafe, "gaskiyan kenan Mama ita ta kashe shi da
hannayenta, ta zo nan tana muku ƙaryan wai tana son shi, makirci ne, shirine kawai dantserewaalhakin rai amma ita ta kashe shi ta zo nan tana muku ƙaryan hauka" ya idda maganan a ƙufuleƙirjin shi na sama da ƙasa....
Tsayawa Kabir yayi cak daga yunƙurin zuwa gareshi da yake tare da faɗin "ya aka yi ka sani!"
"Ranar da muka je ƙaddamar mata da aiki muka tadda abun, bayan mun gama abinda ya kai mumun fito da ita muka sanarwa ƴan sanda, can wajen su iyayenshi suka je suka amshe shi, munjebayan kwana uku, in kunji irin kalaman da mahaifiyarshi take faɗi game da tarayyarshi daitasekun zubda mata da hawaye, tace ta dalilinta ɗanta ya soma ja da magananta, ya bijire mata, lokacin da ya gane gaskiya ya tuba suka gane ta saka mai HIV, tana cikin jimamin nan ne
mutuwarshi ya risketa, sannan tace ta je har asibiti wajen shi sun yi cacan baki akan se ta
mallakeshi ita ɗaya, munce meyasa ba ta faɗawa police ba? Tace "ta barwa Allah, sakayyantadaga gare shi take nema" haƙƙin yaron nan da mahaifiyarshi da ƴan uwanshi ba ze taɓa bari tarayu cikin kwanciyar hankali ba" Kainuwa ya jero bayanin cike da takaicin hali irin na ta....
Juyawa da duban su kan Sa'adatu da ko gezau ba tayi ba suka yi cike da mamaki me haɗedatsoro da firgici, "Sa'adatu meyasa ki ka kashe shi! Meya miki! Dama irin son da ki ke mishi kenan!
Masoyi be taɓa kashe abinda yake so ba" Mama ta jero mata tambayoyin cike da firgicindatashiga idanta na zubda ruwan hawaye, da sauri Sadiya ta nufeta ta riƙo kafaɗunta cike da firgici
tace "kiyi magana mana Sa'adatu! Ki ƙaryata, ki ce ba zaki iya kisan kai ba!" Tayi maganantaredagirgizata a ruɗe...
"Ai ba zata ƙaryata ba, wannan da ku ke gani iblishiyace a suffan mutane, tunda ta iya halakauban da ya haifeta, ya raine ta, ya tsaya mata, ya ilmantar da ita, ya tufatar da ita har lahirabawanda zata ƙyale" Sarari yace tare da jan tsaki ya juya kai, "me!" Kabir yace a razane taredaisakusa da shi ta riko shi a firgice, su Insu kuwa gaba ɗaya miƙewa suka yi tare da zube mataidoarazane, sakinta Sadiya tayi a firgice tare da sakin baki da idon dake tsirarar da ruwan hawayeasaman fuskanta....
Cikin rawar laɓɓa Iƙilima ta buɗe baki da zumman magana, sallaman Salman da SadamdaKamil
ne ya ƙagar mata da abinda take niyyan faɗi, "ni ce nan, ni ce na kasheshi! Eh ni ce na sa Zizatakai ma doctor alluran da ze ta'azzara ciwon shi, yanda ze mutu ba tare da wani zargi ba, ni cenan, kuma banyi danashina ko kaɗan ba, tuntuni dama yakamata ya mutu saboda katsalandandayayi
a rayuwata, nayi alƙawarin kauda duk wanda ya ce ze kawo mun tsaiko akan hanyata, tunlokacin da duniya ta mai tofin Allah ya tsine akan fyaɗen da ya ma ɗiyar cikin shi yakamatayamutu amma yaƙi, so nake ya mutu, so nake inji baya motsi, amma duk ya daure, da nayi zatonkashe me ƙoƙarin fuddoshi ze sa ya gane ba'a buƙatan ya cigaba da rayuwa, se dai ya cigabadadaurewa, na aika mai da ɗan aike can ya ki dubawa, na je da kaina na kai mai yaƙi, be samusukuni ba har se da ya fito, shiyasa na shirya mai sauƙaƙaƙƙen mutuwa kamar yanda yayi, babuzargin kowa, babu wanda ya kashe shi, lokacin shine yayi ya mace kamar yanda aka faɗa muku, shikenan ya mutu an rufe babin shi, Sa'adatu ta ƙara tumɓatsa ta ƙara haskawa" ta idda
maganan kaman taɓaɓɓiya..... A tsorace suke bin ta da idanuwa cike da firgice, "ki, kin, kince kashe me temaka mai ya fito, mekike nufi ds hakan!" Yasmin tace zuciyanta na bugun da ba ta taɓa ji ba idanta akan Sa'adatudake bin su da ido, dariya ta saki me sauti tare da faɗin "a sauƙaƙe kasheta nayi" tayi magananba tare da wani shakku ba, "wa ki ka kashen!" Suka ce a tsorace bakuna a haɗe, "barrister AminaSa'eed Bertuwa!" tace tare da kwashewa da dariya me haɗe da sautin kuka, kallonta sukeafirgice, cike da tashin hankali Kabir yace ba ta cikin hankalinta, ƙarya take, ta haukace!" "Kai nemaƙaryaci mahaukaci, amma ni a hankali na nake, ni ne nan Sa'adatu ɗiyar Hamza da Maryam, ai
yakamata ku san ɓoyayyun saran da na kai muku a duhu"....
"Ni na kasheta saboda kamani da tayi turmi da taɓarya da Sudais, banso cutar da ita ba dukdataganmu, binciken da ta fara yi akaina da gano asalin abinda ya faru tsakanina da Baba da faraƙoƙarin fiddo da shi da tayi yasa ni aikata inda zan aikashi" tayi maganan babu wani alamudakenuna ba ta cikin hankalinta, "ta ta tayaya!" Yamsin ta jefa mata tambaya tare da tafiya luuu, dasauri Sadam da jikin shi ke tsuma ya riƙota, "canza mata magani nayi kamar yanda na canzawaƴarta Insu da zata tafi makaranta" tayi maganan tare da kwashewa da dariya tare da ɗagakai
sama, se da tayi me isanta ta sakko da kan ƙasa, ganin yanda suke kallonta ya sata faɗin, "taɗauka ba wanda yasan tana ɗauke da ciwon, abinda ba ta sani na na daɗe da sani" se kumatakwashe da dariya, tsahirtawa tayi tare da faɗin, "ni Dr Hisham ke bawa maganin in kawomatainya shigo makaranta, anan nake samun daman canzawa, wayyo Barrister ba ta sani ba tayi tasha, zuciyanta na rauni, tana shiga watan haihuwa ta fara ciwace-ciwace, wayyo daɗi shirina yatafi
dai-dai, zazzaɓin da tayi ana saura 7days ta mutum shi ya bani daman cika burina, ina school DrHisham ya turomin alluran da zan siya in mata saboda tafiya da yayi" fashewa da dariya mehaɗeda kuka tayi tare da faɗin "kawai na canzo da poison ɗin dake shiga jiki a hankali, tana kallonaina zura mata har na gama, har na juya zan fita tace "nagode Sa'adatu sannu da ƙoƙari" jinjinamata kai nayi na fice, ina fita na kwashe da dariya kaman haka na wuce ɗaki....
Tsahirtawa tayi tare da fashewa da dariya me haɗe da kuka lokaci guda, "na firgita da nagabatanuna alamun ciwo a jikinta, ranar da zata tafi na je na sameta a ɗaki akan ba ta jin komai nasauyi
se tace min "eh" na sakin mata murmushi na tashi, se tace "lafiya Sa'adatu!" "Na ce ba komai, nazo duba ko bata jin daɗi ne, se tace mun, "zo zauna" ba musu na koma na zauna, kawai setafaramun wasu zantuka "ban sani ba ko zan tashi ko ba zan tashi ba, ina jin rauni a Wannan kwanakinsosai, aa'adatu ki ji tsoron Allah, ki riƙe gaskiya, ki zama ƴar halas, kar ki zama butulu, nafahimci rayuwar da ki ka zaɓa yafi miki kowa da komai, ina roƙon ki nisan ce Ni yarana yawanci
mata ne, ki nesa da su, kar ki sauya musu tunani" murmushi na sakin mata na jinjina matakai
alamun na gamsu na miƙe na fice, tunda na koma ɗaki nake jin takaicin kaina akan meyasabanshaƙeta ta mutu a take a wajen ba, se dai kalmanta na farko na ba ta jin zata tashi, shi ya sani jinsanyi, sannan na ɗau alƙawarin se na maida yaran na ta da take tsoron a ɓata su karuwai yandatana can ma za'a kai mata labari"...
"Ina cikin wannan ɓacin ran ki ka zo akan in zo muyi girkin da muka gani, muna kitchen segasusun fito dan tafiya asibiti, kuna tambayanta lafiyarta ni kallon yanda zan kawo ƙarshenmurmushin saman fuskanta dake danne damuwarta nake, koda Yasmin ta kira akan naƙudayataso mata na yi matuƙar farin ciki dan na san ba zata tsallake ba, bayan tafiyanku na ci dariyatasan raina, koda aka dawo da gawarta na tabbatar da ta mutu da gaske ji nayi na fara taka tsaninnasara, kukan da nake yi a zahiri ba shi ba ne a baɗini, a baɗini dariya nake ƙyaƙyatawa inabinkuda ido, ina kallon yaran da take cewa kar a ɓata musu tarbiyya ga su ta tafi ta bar ni da suseabinda na so yi da su, ta tafi ta bar duniya, taurin kanta da san kanta ya kawo ƙarshenta dawuri" ta idda maganan ko a jikinta ta na ƙyaƙyata dariya.....
Zabura Sadam yayi da nufin isa gareta, saurin riƙoshi Insu da jikinta ke ɓari tayi juyowa yayi afusace dan ganin wanda ke shirin hana shi kai na ta numfashin ƙarshe, ganin Insu dake girgizamai kai hawaye na ambaliya a fuskanta ya sa jikin shi sanyi, "Insu!" Yace cikin rawar muryatareda rungumota da ƙarfi suka fashe da kuka a tare, da sauri Kabir ya isa inda take ya shaƙotajiki naɓari tare da faɗin "ke ba mutum bace, dabba ce, mutuwa shi yafi dacewa dake, barin ki a duniyamatsala ne" yayi maganan cike da tashin hankali, "saketa Kabiru saketa" Mama tace cikinrishinkuka, girgiza kai yayi tare da faɗin "Mama se ta mutu kamar yanda ta kashe su, ita fa ta kashesuda hannunta, menene amfanin makashi!" Ya idda maganan cike da tashin hankali, "babukam, amma ka jira mahukunta su hukuntata, kar a ɗau hukunci a hannunta" ganin yaƙi sakinta gashi
se kakarin mutuwa take saboda mugun shaƙa da ya mata ya sa Farisat da ilahirin jikinta keɓari
tace "dan Allah ka saketa, mun barta da mahaliccinmu, shi muke so ya bi mana kadin mu, bazamu nemi adalci a wajen kowa ba se a wajen shi, ba ya barci, Anty dai ba ta mata komai basekyautatawa, ba mu ƴaƴanta ba, hatta maƙofta sun sani, Allah ya saka mata daga wannnanzaluncin da ta mata" tana kai nan ta juya riƙe da hannun Yasmin dake dafe da kai saboda bugunda yake mata suka fice....
Takawa Salman yayi ya isa garesu, janye hannun Kabir yayi a wuyanta, cikin saita kukandayakeyace "ku barta, mun kai kukan mu gun wanda ya halicci baiwar da ta kashe" yana kai nanyajuyatare da ba su Rahma umurnin su je, ɗago kai Hasinat da idanta ya gama kaɗewa tayi ta watsamai
wani razanan nan kallo, saurin riƙota yayi dan yasan abinda za ta yi a ƙarshe, fashewa da kukatayi tare da ƙoƙarin kwacewa riƙon da ya mata, jan ƙarfen gadon dake kusa da ita Rahma tayi ahanzarce tayi inda take kafin wani yayi yunƙurin tsaidata ta lafta mata a kai, ƙara ta saki taredatafiya luuu zata zube a gadon, ƙara ɗagawa yayi Sadam yayi saurin sakin Insu ya nufeta yariƙeƙarfen, "saki Sadam! Saki wallahi se ta mutu ita ma" tace cikin rishin kuka, jawota yayi ya
rungume ƙam hawaye na ambaliya a saman fuskan shi, kyara murya Kamil yayi a natse taredatakowa ciki ya riƙe hannun Insu da Sadam suka fice, tattaro su Rahma dake kuka kamar zasumutu Salman yayi suka fice.....
"Shegiya, kema se na kashe ki, se kin mutu, ba ke ce yarinyar da take matuƙar so ba, se kinbita, ba zan huta ba se na ga bakya numfashi, ko da yake ina kaunce ma za'a mun aikin, mutanendasuke zagaye da mijinki su za su yi ajalin ku ke da shi, se sun shafe babun rayuwarku a doronduniya, se an manta da an taɓa halitta masu kama da ku ma" tayi maganan a wahalce taredasakin dariya tana shafo jinin dake bin gefen fuskanta.... Kallonta suke cike da mamaki, fashewa da kuka Iƙilima tayi cike da tashin hankali ya za tayi, "daina kuka Iƙilima, be kamata ki zubdawa wannan walaƙantacciyan hawaye ba" Kabir yacecikeda tsananta da ya diran mai lokaci guda, girgiza kai tayi tare da faɗin "ba ita nake mawa baYayaKabir, kaina nake koka mawa, da wani idan zan kalli fuskan Farisat daYasmin da Insu! Ta yazaniya kallon su bare in nemi yafiyan abinda jinina ta aikata gare su, bana da bakin ba su haƙuri YayaKabir, ta sare su a wuri mafi haɗarin gaske, da wani idon zan kalli mijina da ko da yaushe yakeban labarin irin soyayyan da suke mata, da wani fuska zan fuskanci ƴan uwan shi da mahaifiyarshi da ta maidata ɗiyar cikinta, bana da kalaman kare kaina Yaya Kabir, me zan cewa Sa'eeddake hannuna! Ce mai zanyi ƴar uwa tace ta kawo ƙarshen numfashin mahaifiyarshi da yakematuƙar ƙauna? Me zance mai! Ku temake ni ku faɗa min, kaina ya ƙulle, shikenan rayuwar farinciki da nake hangowa ya zo ƙarshe"...
"Sa'adatu ta kawo ƙarshen komai, ta cuce ni, ta cuci bayin Allah, ta wargazamun farin ciki, kafinki gai ga Insu Sa'adatu ki fara kasheni! Na gaji da wannan rayuwar, kin hanamu rayuwar farinciki, ƙaddarar mu ce ke, ke ce tashin hankalin mu" ta idda maganan tare da zubewa a ƙasa cikinrishinkuka, fashewa da dariya Sa'adatu dake bin ta da ido tayi tare da mata kallo me cike da wulaƙanci, "ai dama na faɗa muku se na tarwatsa rayuwarku kamar yanda ku ka tarwatsa nawa, damakunatunanin zan barku ku mallaki muradanku bayan kun saka wanda nake matuƙar so da ƙaunayagujeni, ku ne silan komai, ku ne sanadin mutuwar Abdull, ta dalilin kalamanku ya gujeni, maganganunku su suka yi tasiri a zuciyarshi har yake ƙoƙarin guduwa daga gareni, ku jirazandawo kan ku a hankali" miƙewa Iƙilima tayi a fusace tayi inda take, tana isa ta haye kanta tasoma jibganta ba ji ba gani tana kuka me taɓa zuciya, babu wanda yayi yunƙurin hanata bintakaiwa sukayi da ido, ganin tana gab da sheƙawa ya sa Sadiya goge hawaye ta isa gare su, janyeIƙilima tayi da ƙarfi ta diro kallon sakanni ta mata tare da ɗaga ido da nufin isa ga Sa'adatu, turoƙofan da doctor da ke sanye da facemask da nurse's uku suka yi ne ya sa ta maida ƙafartaaƙasasuka bi su da ido.... Ganin irin kallon da suke musu ya sa doctorn kallon ɗaya daga cikin nurse's ɗin, murmurshi tasaki tare da faɗin "yau za'a fara mata alluran da aka rubuta, in ba damuwa ku ɗan bamuwaje"
"an canza lokaci ne? Doctor yace se tayi wata ɗaya tukun" "eh an canza, doctor bismillah" nurseɗin tace da sauri tare da wuce wa inda Sa'adatu ke yashe a saman gado tana sakin numfarfashi, bin ta yayi da ido a natse, fasa alluran nurse tayi ta ja a sirinji, miƙa mai tayi a natse, amsayayi yamata godiya ya jawo hannunta ya ɗaure, yana samun jijiya ya zurƙama mata be damu da kowacce bane a ciki....
Yana gama zube mata ya mata fatan samun lafiya ya wuce a natse suka dafa mai baya, yanafitasuka sassauke ajiyan zuciya tare da kallon Sa'adatu da ta miƙe zaune a daddafe ta zuba musuido, ganin yanda fuskokin su ya canza ya sata fashewa da dariya tare da nuna su da ya tsa, a harzuƙeKabir ya nufeta, saurin riƙoshi Sarari yayi tare da faɗin "ashe kana da zuciya har haka Kabir! Kai
fa kace a yafe mata, a jata a jiki, a rumgumeta zata shiryu, ko ka manta ne!" Ya idda jero
maganan idan shi akan shi, girgiza kai yayi cikin tashin hankali tare da faɗin "ba wannanba, bame irin halin wannan ba, ba sheɗaniyar nan ba, ka fi ni sanyin zuciya Salisu, yau na tabbatar
haƙurarrene kai, ba zan iya haƙurin cigaba da ganin tana numfashi ba bayan na san ita ta kashemana mahaifi" yayi maganan cike da gaskiyanshi....
Murmushi ya saki tare da bin shi da ido, "Sa'adatu!" Harira tace tare da isa gareta da sauri, maidaduban su gareta suka yi, murƙususu kawai take tare da jan numfashi da ƙyar, kallonta kawai
suke ba wanda ke da niyyan ɗaga ƙafa bare isa gareta, "je kira likitan" Mama tace a tsorace, tashi
tayi ta fice a guje, takawa a natse Sadiya tayi ta isa gareta ɗagota tayi a natse ta bi fuskantadaido, sai-saita kanta tayi cike da dakiya tace "suwa ye za su kawo ƙarshen Insu da mijinta?" Kallonyanda ta kame fuska tayi tare da faɗin "ba ruwanki da sani" jinjina mata kai tayi tare da sakintata miƙe cikin son razanata tace "Yaya Kabir kulle ƙofa, ba doctorn da ze zo dubata, mu bartaahaka har ta mutu" nufar ƙofan Kabir yayi da sauri, "Alhaji Namadi da mutanen shi ne, sukesankawo karshen shi matuƙar ya yi gaddama ga muradinsu" tace a wahalce cike da nemanagaji, "meyasa suke bibiyanki?" Ta jefa mata tambayan a dake, "na ɗauki systemɗin shi dake ɗaukedatsare-tsaren su da meeting's ɗin da suka yiyyi da komai da komai, shiyasa suke bi na" ta cetareda sakin ƙara saboda wani ɓari da jikinta ya ɗauka, "yana ina?" Tace tare da isa gareta sabodazaburan da ta fara, "yana ma'ajiyan bank na MJ, key ɗin bude ma'ajiyan na gefen kabarinBaba" tace kamar wacce aka duki bayanta da ƙarfi tare da ƙoƙarin rikota, ja baya tayi da sauri cikedamamakin ƙarfin halinta, murmushin takaici Sarari ya saki tare da bin ta da ido, "ki mutuSa'adatu, kar ki sake ki rayu, dan in ki ka dage se kin rayu zan kashe ki da hannayena" tace tare da juyawataja hannun Iƙilima tare da faɗi muje"....
Faɗowa dakin Harira tayi cike da tashin hankali doctor da nurse's biye da ita, kai tsaye indaSa'adatu take doctor tayi, yayinda nurse's suka ba su umurnin jiransu a waje, ba musu sukafice, suna fita suka tadda su Farisat da suka kasa taku ko ɗaya bayan fitansu zazzaune a ƙasa sunasharɓan kuka me cike da rauni, saurin juyawa Iƙilima tayi da nufin barin wajen, kamota Mamatayi jiki a mace tare da girgiza mata kai.... Haka suka cigaba da tsayiwan jira, "yakamata mu koma gida haka" Salman yace tare da kallonFarisat, jinjina mai kai tayi tare da umurtansu murya a shaƙe, yunƙurawa suka fara jukkunaaraunane, fitowa doctor da nurse's suka yi jikkuna a mace, "lafiya doctor?" Harira tace a tsorace, "kuyi haƙuri da abinda zan faɗa, ta cika" "Alhamdulillah" Iƙilima da Sadiya suka ce bakunaahaɗe, bin su da ido suka yi cike da zallan mamaki, "ina nufin fa ta mutu!" Doctor tace mamakintanafita
a saman fuskanta da muryanta....
"Mun fahimta kuje" Kabir yace fuska a ɗaure, zukata cike da mamaki suka wuce, "shiru suInsusuka yi cike da mamakin wai ta mutu, yanzu fa suka barota a ciki tana faffaɗan mugganabindataaikata tana dariya cike da nishaɗi, "lallai Allah Allah ne" Rahma tace babu alamun jimami asaman fuskanta, "dama zafin fitan raine yasata wannan surutan kenan" Safinat tace ko a jikinta, "ƙarshenta ne yazo shiyasa Allah ya matseta ta rattafo abinda tayi, Allah ka kiyashemu ƙarsheirin wannan, ku duba fa ku gani, ta tafi da nauyin tsiyatakun da ta shuka, dan ba tayi nadamaba"Hasinat tace cike da baƙin ciki, "yakamata ku tafi yamma ya kawo jiki" Mama tace idanta akansu, "yanzu kuwa Allah ya ƙara nauyin ƙasa" Rahma tace tare da maida dubanta gare su..... Goge hawaye Farisat tayi tare da faɗin "ai ba mu ga ta komawa gida ba Mama, Yaya Kabir kujeku cike komai a bada gawanta a koma da ita gida a sallaceta akaita, gatan da zamu iya matakenan tunda da sauran lokaci kafin garin ya rufe" cike da mamakin dattako irin na su sukabi tada ido, "dan Allah Farisat kuje, Sa'adatu ba ta can-canci wannan karamcin daga gareku ba"
Iƙilima tace tare da fashewa da kuka, murmushi Insu ta saki tare da faɗin "duk abinda ta aikataba mu ta aikatawa ba, kanta ta aikatawa, wannan tsakaninta da mahaliccinta ne, ba ma dadamuwa da shi, matsayin mu na ƴan adam munji ba daɗi, se dai hakan ba ze hanamu matagatanƙarshe ba, dan Allah ku je ku yi abinda ya dace" jinjina kai Sarari yayi ya wuce shi da Kainuwa.....
Comments fans🥰🙏
🫀MUGUWAR TSOKA 🫀
{🫀TA'ARE KALLUƊE}
[Muscle Cramp🫀]
) عضلة سيئة (
🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
written and Created ~~~~~~~~~~~~~~ ِبسم الله الرحمن الرحيم
By
Yardajjiya👩 💻
Page. Sixty two
Zaune suke a cikin mota ta gefen asibiti ta waje, idanunsu akan gate ɗin asibitin da jama'akekai
komo, da alamu akwai abinda suke jira, banda kallon agogunan da ke ɗaure a tsintsiyan
hannayensu ba abinda suke, jin kukan ambulance da ya fito da motan su Insu da ya biyobayanshi ga sa su kallon juna, ganin Kabir da Sarari da ke bayan motan Salman da ya kwashi suIƙilima ya sa su sakin wani nagartaccen murmushi suka kalli juna.... Karkatawa kaɗan, wanda ke mazaunin driver yayi ya zaro waya ya danna kira ya kara wayanakunni, ana ɗagawa yace "aiki ya kammala, ta tafi" sautin murmushi me cike da jin daɗi neyabayyana a kunnin shi, murmushi ya saki tare da faɗin "godiya nake yallaɓai" "Ni ke da godiya, kafaranta mu tabbas, zaka samu sakamakon hakan" muryan Alhaji
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 100 Chapter of 109