Share this page
yanayinta tace "Baba Maude ya gajiyan aiki?" "Alhamdulillah" "ma sha Allah" tace tare da janye jikinta ta shige motan a natse, da sauri Lawuzata ƙariso ganin Ibrahim na ƙoƙarin kulle murfin, miƙa mata ruwan da ta dakko mata marasanyi tayi tare da faɗin "Allah ya tsare" "amen Anty Lawuza" tace cike da jindadin kulawan da tanunagareta.... Jan motan yayi a natse suka nufi gate ɗin farko daga cikin gida, suna gab da ƙarisawa ya miƙamata pass me ɗauke da sunanta da hoton ta, amsa tayi tare da faɗin "na menene?" "Ze miki amfani in zaki shigo" jiniina mai kai tayi tare da sakin murmushi... Suna ficewa daga gidan ta gyara zama tare da faɗin "shikenan tunda ka tafi Ibrahimshiru-shiru kamanta da mu ma" murmurshi ya saki tare da girgiza kai, "eh mana Ibrahim, wa ze ce zakaɗaulokaci haka ba ka zo ba" murmushi ya saki tare da faɗin "ba na da ƙarfin zuciyan zuwa ne, saubiyu ina yunƙurin hakan amma se in kasa ƙarisawa, wallahi in na tuna in naje ba zan taddaAntytare da ku ba, se in ji zuciyata na bugu da ƙarfi" ya idda maganan a raunane... Murmushi ta saki tare da faɗin "to ya za'ayi Ibrahim, wanda yafi mu santa da ƙaunanta shiyaɗauketa, dama tashi ce, amsan abinshi yayi, se dai mu yi ta mata addu'a" ta idda maganancikedadakiya, "haka ne wannan" yace a natse, "ka daina ma wannan tunanin Ibrahimdan Allahayi zumunci, tun bayan tafiyanka Yasmin da Farisat suke ta zancenka" murmushi ya saki taredafaɗin "in sha Allah zanje" "Allah ya yarda" ... Tace tare da bin hanyar da ido, shirun daƙiƙu suka yi kafin ta kalleshi kamar wanda aka tsungulatare da faɗin "dama da Uncle ka ke aiki?" Murmushi ya saki tare da faɗin "eh" "tun wani lokaci kake aiki da shi?" Tace tare da gyara zama, murmushi ya saki tare da faɗin "da alama a kainaki keson fara darasin lauyancin" dariya me sauƙin sauti ta saki tare da faɗin "so nake kawai inji" "shekaru sha takwas haka" yace a natse, "wow! Eighteen?" Tace tare da buɗe ido, jinjina matakai yayi tare da fadin "yeah" "lallai kun daɗe" "eh mun daɗe" "ya akayi ka fara aiki da Anty kuma?" Tace idonta ƙyam akan shi... Murmushi ya saki tare da faɗin "da alama labari ki ke son in baki" "in dai ka bani ba zanƙi sauraraba" tace fuska washe da murmushi, murmushi ya saki tare da gyara zama cike da tuna abubuwanda suka wuce yace "na gama digree babu aiki, ba inda ban buga wajen neman aiki ba ammabansamu ba, a lokacin akwai wacce nake matuƙar so da ƙauna, iyayenta sun matsa akan in fitoayi maganan aure, dan a lokacin duk an aurar da ƙanninta, ita kaɗai ta rage, gashi duk wandayafitoyace yana sonta tace tana da wanda ta tsaida... "Na shiga hali me tsanani a lokacin, ni kaɗai na san halin da nake ciki a wannan lokacin, banafatan ko maƙiyina ya shiga wannan halin, ita in na je kuka tana faɗamin halin matsin da takeciki, ni da kaina ina buƙatan abubuwa babu daman siya, komai se mahaifiyata ta ban, na gaji dagaske, banda buga-buga ba abinda nake yi, wanda be wuce in samu ɗari biyar zuwa ɗari bakwai baarana, ina cikin wannan hali, naji sanarwan campanyn SSB tana neman ma'aikata wanda sukakarancin Economic, banyi ƙasa a gwiwa ba na je saboda shi na karanta, ban saka rai ba sabodanaje irin wannan abubuwan da dama ban samu ba, Allah da ikon shi kawai se gashi na samu, Insucikin watanni kaɗan rayuwana ta fara tafiya canzawa, dan SSB mutum ne da yasan mutumci nakasan shi, sannan kyautatawan shi a gare mu me faɗi ne... Ba ya da buƙulu ga ma'aikacin shi, duk da mutum ne wanda ba zaka ce ga inda ya saka gababa, se dai ya iya kyautata zamantakewan shi da kowa, kafin shekara na auri matata, SSBda kanshi ya bani kyautan gida gift ɗin aure na, rayuwata ta ƙara haskawa a wannan lokacin, karamcinshi ya sa na ƙara dagewa wajen bautatama campany yanda ya kamata, sosai dagiyana ya sa nahaska a idanunshi, ya ƙara jawoni a jiki sosai, dan yace ya yarda dani, ya kuma amince dani"... "Haɗuwan mu na cika shekara uku a lokacin ɗiyata ta fari me suna Fatima sunan mahaifiyatatacika shekara ɗaya da rabi da haihuwa, SSB ya zo mun da batun ze saka ni wani aiki, wallahi banyi ko wani tunani ba a lokacin na amince tun kafin inji wani irin aiki ne, dan na san ba ze cutar dawanda be sani ba bare ni da ya sani, zaunar dani yayi ya mun bayanin komai akan Anty, sedai befaɗamin alaƙarshi da ita ba a lokacin, banji wani ɗarr ba na tambaye shi ranar tafiya, yaceinjedai in yi nazari nan da sati biyu, na ce mai ba wani nazari na amince, haka ya shirya muntafiyaBertuwa da shiga gidanku ta yaron shi dake can me suna Alhaji Sunusi... "Kinji yanda aka yi na fara aiki da shi, da yanda aka yi na fara aiki da Anty" ya idda maganantareda taka burki saboda ƙarisowa makarantar da suka yi, bin wajen da ido tayi cike da zallanmamaki, dan wajen be mata kama da makaranta ba, tun daga farkon anguwar kwaltane azubega wa su flower's da suka ma gefen katangar makarantar ƙawanya, karkata kai tayi ta karantasunan makaranta dake rubuce a jikin wani ƙaton allo dake ke saman ginin yana bada wasuhaske masu ɗaukan hankali, "Insiyyah Sa'eed University Of Law, ISUOL!" Tace a mugun mamakance, murmushi ya saki tare da faɗin "yeah" yayi maganan tare da jan mota ya ƙarisa ga security's danna gaban shi ya shige... Binciken su suka yi jin abinda ya kawo su ya sasu ba su hanya suka shige, "kana nufin wai saboda""saboda Anty" Ibrahim ya ƙarishe mata abinda take ƙoƙarin faɗi, "subhanallah! Saboda Antyyabuɗe school ɗin!" Tace tare da baza mai ido, "saboda ita ne" yace a hankali, "ya aka yi haka?Antyba ta sani ba" ta idda maganan a ruɗe... Murmushi ya saki tare da faɗin "waya faɗa miki ba ta sani ba?" Sakin baki da ido tayi ta bishi dakallon mamaki tare da faɗin "wait kana nufin kace mun Anty tasan Uncle ya buɗe school ɗinnandan ita ne!" "Eh, ta sani, ta taɓa zuwa ma lokacin da za'a yaye ɗalibai" yace cike da tabbaci, "wow, na gane time ɗin, dama nan ta zo?" "Eh" yace tare da dai-daita parking a kantamemen parkingspace ɗin makarantar.... "Uncle ya san ta zo?" "Eh, sun haɗu se dai bakin su be saɓa da juna ba, nan aka nema ma Sadam, se dai credit ɗin shi ba su kai yanda makarantar ke buƙata ba" yace tare da ɓalle motanyafita, buɗe ɓangarenta tayi ta sakko cike da mamaki, tare da faɗin "na fahimta shine ganin da sukawajuna bayan tsayin shekaru" jinjina mata kai yayi tare da faɗin "muje" ba musu ta bishi sukarankaya, banda bin makarantar da ya gama burgeta da ido ba abinda take, ɓangaren na musamma suka isa, jerun wasu ofisoshi ne wanda aka ƙawata da gilasai na ciki na hangoabindana waje ke yi, ƙarisawa ƙofar wani damfareren office suka yi, ɗaga kai tayi dan ganin muƙaminmamallakinshi.... "Vice chancellor" ta karanta a bayyane, knocking ɗin ƙofar Ibrahim yayi a natse, "yes comein" na'uran dake sanar da na waje abinda na ciki yace ta isar musu da saƙo, ba musu ya murdahandle ya tura a natse suka shiga bakuna ɗauke da sallama.... Da zallan mamaki Insu ke bin wanda ke zaune saman wani ni'imantaccen kujera da ido, murmushi ya sakin mata tare da faɗin "zo zauna" "Uncle Abubakar!" Tace cike da zaƙuwa, murmushi ya sakin mata tare da faɗin "yes" jan kujeran na kusa da wanda Ibrahimya zaunatayi ta zauna tare da faɗin "dama Education ka karanta Uncle Abubakar?" Murmushi ya saki taredajinjina mata kai... "Wow nice to see you" tace cike da farin ciki, murmushi ya saki tare da miƙawa Ibrahimhannu, "malam Ibrahim an ɓullo kenan?" "Wallahi oga Abubukar mun ɓullo" "Hajiya tace zaku shigoyau, zaman da nake ma na jiran ku ne, dan tun ɗazu na yakamata in fita, muna da wani meetingnanda 10 minute's" "okay to bari mu ƙarisa can office ɗin registerern ko?" Ibrahimyace tare damiƙewa.... "Eh ku mu ƙarisa can, se a mata ku wuce" Abubukar yace tare da miƙewa, "no uncle Abubakar kaje ka halarci meeting ɗin ka, na san wajen ze tara jama'a tunda yau aka fara registrationɗin, inlayi ya zo kan mu zamu kira ka" Insu tace tare da kallon shi, murmushi ya saki dan dama basonhakan yake ba, dan ba yanda ya iya ne, "okay Ibrahim ku ƙarisa can ɗin, muna gama meetingɗinzan same ku a can" "to" Ibrahim yace a girmame tare da nufar ƙofan, "uncle Abubakar munzooffice ɗinka ko ruwa baka ba mu ba fa" Insu tace kamar za ta saki kuka, "oh Allah mantawanayi uwar ƙorafi" yace tare da sakin dariya, murmushi ta saki tare da faɗin "mu dai ba zamu ƙi faɗinuncle Abubakar yayi mana rowan ruwa ba" tayi maganan tare da nufar ƙofa, "zo amshi kar ki sani a bakin duniya" yace murya cike da dariya, "a'a uncle Abubakar se da muka roƙa" tace taredaficewa, murmushi ya saki tare da bin ta da ido.... Kai tsaye ofishin registarer suka nufa, ilai kuwa jama'a ne cike, neman waje sukayi suka zaunajiran layi ya zo kan su, kallon Ibrahim tayi tare da faɗin "to ka ce kafin Uncle ya turo ka Bertuwakana da ƴa ma, to ya matarka tayi a lokacin?, kai ma ya kayi?" Ta idda tambayar idonta akanshi, murmushi ya saki tare da faɗin "ba abinda ba ta sani ba, komai akan shi ta sani, ko da magananzuwa Bertuwa ya bayyana na faɗa mata komai, tana da yakana da kawaici, ba ta bani matsalakokaɗan ba se fatan alheri da ta mun, ko da na tafi Bertuwa se da muka kwashe shakara gudabamu ga juna ba, ko da sau ɗaya ba ta taɓa takurawa akan hakan ba, ni ne ma ke ɗan nuna matadamuwa dan karta ga kaman ban damu ba, haka za tayi ta ba ni haƙuri" murmurshi Insutasaki tare da faɗin "lallai irin su ba sa da yawa, ka godewa Allah Ibrahim da Allah ya baka ita" "inagodemai a ko wani lokaci" yace fuska yalwace da murmushi... "To se aka yi yaya?" Tace tare da gyara zama murmushi ya saki tare da faɗin "tun daga wannanshekaran da muka kwashe ban ƙara ko sati biyu ba tare da na je na gansu ba, ban san ya akayi bawata rana na kai Anty wajen aiki kafin ta sauka a mota ta tambaye ni ina da aure kuwa? Nacemata eh, tun daga ranar na koma weekend a gida, duk ƙarshe sati se tace in shirya inje ingaiyalina, tun ina tantama tasan wani abu har na bari dan ba ta nuna mun ko wacce alama ba" murmushi Insu ta saki tare da faɗin "tana sane da waye kai" jinjina mata kai yayi tare da faɗin"nasan zata gane, se dai ba zata nuna ba" yayi maganan tare da sakin dariya, dariya Insu ta saki tareda bin shi da ido... "Zan so sanin matarka da ƴaƴanka please ka gabatar da ni garesu" murmushi ya saki taredafaɗin "ita tana tare da ke, su kuma za su zo gaisheki" "wacece!" Tace da mamaki, ganin ya saki murmushi ya juya kai yasata faɗin "tsaya! Tsaya! Ba dai Anty Lawuza ba ce!" Murmushi yasaki tare da faɗin "ba ita ba ce, shikenan?" "Wow! Anty Lawuza da ma matarka ce! Subhanallah" taidda maganan a mamakance, "hee kar ki tara mana jama'a" yace tare da kallon mutanendakezazaune suna jiran a zo kan su, "wallahi nayi mamaki ne" tace fuska yalwace da murmushi, "toki bari" yace tare da miƙewa, bari in zagaya in ki na buƙatan wani abu just call me" jinjina mai kai tayi ya wuce.... Haka ta cigaba da zama, tun tana kallon facebook ta koma tiktok ta koma istgramta komatwitter, tana gaji da kalle-kallen ta koma whattapp, ganin babu wani saƙo me mahimmanci yasata posting ɗin hoton da suka ɗauka da sauran ma'aikatan a statut ta kashe datan ta cigabada zuba ido, kallon agogo tayi ganin ɗaya saura ya sata miƙewa tare da tambayan ma'aikatanwajentoilet, nuna mata side ɗin da toilet ɗin mata yake yayi cike da kula, godiya ta mai ta nufi can.... Tana shiga tsakin wajen ya burgeta, toilet ne sun kai 70 ko wanne tsaf-tsaf, babu wani alamunzarni ko wari ko wani abu makamancin hakan, buɗe ɗaya daga ciki tayi ta shige, kammalaabindaza tayi hankali kwance tayi ta fito ta fice daga ɓangaren.... Kai tsaye inda ta hango an rubuta female masjid tayi, duƙawa tayi a natse ta buɗe fanfo tafaraɗaura alwala cike da natsuwa, tana kammalawa ta shige masjid se a lokacin ta tuna ba ta ɗakkohijab ba, tana cikin wannan tunanin ta hango jerin hijabs rataye a saman manyan dake samanwajen, nagartaccen murmushi ta saki tare da ciro daya ta saka ta kabbarta sallah.... Tana idarwa da azkhair ta ɗau ɗaya daga cikin Alƙur'anin dake jere a gefe ta fara karantawacikeda natsuwa, sosai tayi karatu, se da ta tabbatar da natsuwa ya shigeta sosai sannan ta maidatamiƙe ta cire hijabin ta maida inda ta ɗakko ta fice a natse.... Tana idarwa ta miƙe ta fito, da Ibrahim suka jero da shi ma ya gabatar na da shi faralin sukakoma can, "ma sha Allah Ibrahim daga wannan ne se mu" tace tare da nuna matashiyar budurwan dake zaune a gefe tare da wani dattijo, murmushi ya saki tare da faɗin "zama yaƙarekenan?" "Na ƙosa, ba na son jira wallahi" tace cikin ɓata fuska, murmurshi ya saki ba taredayacemata komai ba, na ciki na fitowa waƴanda daga su se su Insu suka tashi suka shiga, ko cikakkunmintuna 3 ba su yi ba suka fito jiki a sanyaye... "Muje Ibrahim sun fito" tace tare da miƙewa, ko kafin Ibrahim ya miƙe masinjan registarer yafitotare da ma wanda Insu ba ta san ma lokacin da suka iso wajen ba magana akan su tashi sushiga, tashi ɗaya daga ciki yayi da sauri ya isa mota ya buɗewa wata kyakykyawan matashiyar budurwaƴar kimanin shekaru 21 da haihuwa mota ta fito cike da yauƙi, kauda kai tayi daga kallonsutamaida kan waƴanda suka fito tare da faɗin "meya faru!" "Yace mu jira waƴan nan su shigatukunse mu shiga" budurwan tace a natse, da mamaki ta bi ta da ido... "Ibrahim kana ji wai su fito wanda suka zo yanzu su shiga tukun!" Tace da ɗin bin mamaki, "bari inyi magana da su" yace tare da ƙoƙarin shiga, da sauri masinja ya tare shi tare da faɗin "jiratukun, waƴan nan su fito" "ya jira me! Insu tace tare da miƙewa a fusace.... "No Insu, kar ki fara" yace tare da saurin ƙarisowa inda take, dan yasan ba abinda ta tsanairinrainin hankali, wucewa bakin office ɗin tayi a fusace ta tsaya tare da faɗin "wallahi ba wandazeshiga daga sama, yanda kowa ya jira suma su zauna su jira" da mamaki wanda ya buɗewa yarinyar mota ta fito ya kalleta tare da faɗin "ke kin san ɗiyar wacece kuwa? Ɗiyar former governorn jahar Yarban ce" ya idda maganan cike da nuna zallan alfahari... "Shine me!, Ƙanin uba na ne? Ko na uwata? Au former ne ma kenan, na ɗauka me ci ne ma, asheme ritaya ne" ta idda maganan ko a jikinta, "ke kar ki kawo mana shashanci anan mana, basuwaje su shige" masinja yace cike da takaici, "malam yi aikin gabanka, nawa nake, ba ta yandazamu zauna muna kallon wata ƙatuwa ta zo ta shige a sama alhalin mun kashe duk uzurorinmumun zauna jira, saboda yanda muka ɗau abin da mahimmanci ne yasa mu yin hakan ba wai bamada uzurorin yi ba, wannan ma yaushe zata fahimci daraja da mahimmanci abinda ta zo karantaba, tun daga farko ba ku nuna mata darajar shi da kiman shi ba" ta idda maganan cike da takaici.... Sakin baki suka yi suna bin ta da ido, sauran masu jira kuwa farin ciki da mamakin ƙarfinhalintakawai suke, "ban waje ko ni ma bazan shiga ba ne?" Masinja yace a harzuƙe tare da watsamataharara, jirga mai tayi ya shige, kauda kai daga kallon da matashiyar budurwan ke bin ta dashi tayi ko a jikinta, "zo zauna tukun Insu" Ibrahim yace tare da kallon ta, ta na ƙoƙarin wuce waregistarer ya buɗe ƙofan ya fito... "Lafiya me ke faruwa?" Yace tare da bin su da ido, "muna zaune zaman jiran layi ya zo kanmu, semuka ga an ma wanda ko cikakkun mintina ashirin ba su yi da zuwa ba, dan har na je yinsallahba su zo ba" Insu tace a sukunance, "shine me? Kar ku tada mana da hayaniya anan, ba kalanshirmammun makarantun da ku ka saba tsiyataku ba ne, nan ISUOL ne, dan haka ku shigahankulan ku, yallaɓai bismillah" ya idda maganan tare da musu iso, "yi haƙuri yallaɓai ba wandaze shiga wajen nan se waƴan nan bayin Allahn, daga su se mu" Insiyyah tace idonta akanshi, damamaki ya kalleta tare da faɗin "an shigar da form ɗinta?" Yayi maganan tare da kallonmasinja, "eh" yace tare da kallon shi... "A cire shi daga sauran da za'a ma registration" yace idon shi a nata da taƙi kaucewa, saurindanna number Abubakar Ibrahim yayi ya ja gefe, "wannan shine shara'ar dama da ku ke koyarwa?Dama wannan shine abinda yaran mutane ke koyo? Wannan shine gaskiya da sanin makamanaikin da ake cewa makarantar tana da shi? Tirr da wawayen shuwagabanni waƴanda ba susamma me suke ba" ta yi maganan zuciya a ɓace, "insu please calm down, kin san yanayinki" Ibrahim yace cike da damuwa... "Ibrahim kaji abinda wannan mutumin ke cewa fa, ka na fa kallon abinda yake shirin koyamana ni da sauran ɗaliban dake fatan shiga school ɗin, "tun ranar registration ya nuna mana za muiyadanne gaskiya mu bayyana ƙarya, in haka ne banga amfanin shiga makarantar ba ma, kai kasansunan wa makarantar ta ci?" Tace rai ɓace tare da kallon shi, "Insiyya Sa'eed, jarumar da tayi fitona fito da duk wani mara gaskiya, wacce ta zaɓi bayyana gaskiya ko da ze yi ajalinta, waccetanisanci ƙarya akan aikinta duk yawan abinda ze bata, sannan kai saboda baka san dan wani aƙidaaka gina ba ka fito tsakiyan makarantar kana tauye ma me hakki hakki? Waye kai?" Ta iddamaganan a fusace... "Ke ni ki ke son nunawa aikina!" Yace da mamaki, "yes kai ne, na fika sanin me ye aikin na kadaka ke buɗe murya wajen faɗa, dan tun ina ciki ake faɗa min menene aikin, Uwata lawyer ce, ubalawyer ne, ɗan uwana, lawyer yake shirin zama nan kusa, ni ma kuma shine mafarkina a yanzu, dan haka baka isa gaya mun me ne ne shari'a ba, in ana gada ni ƴar gado ce" ta idda maganantare da baza mai ido... "Waye ke?" Yace cike da mamaki, dan ya fara shan jinin jikin shi da kalamanta, "kar ka sosaninwacece ita, dan ba zaka so ji ba a wannan hali" Abubakar yace fuska a ɗaure, "sorry sir" yacetareda sunkuyar da kai, "wuce ki je kuyi" yace tare da kallon ta, "ba ni ba ne a layi uncle Abubakar waƴan nan ne" tace tare da nuna matashiyar budurwan da Insu tayi mugun burgeta, "uncle!" Registrer yace a tsorace, "ku shiga se mu shiga" Insu tace tare da kallon su fuska yalwacedamurmushi... "To uwar rigima komai ya wuce ko?" Abubukar yace tare da kallon ta, "ya wuce uncle" tacetareda sakin murmushi, ba su jima ba suka fito, suna fitowa suka shige, suna gamawa suka bataIDcard ɗinta ta amsa cike da farin ciki, "in ka gama aikin yau ka tabbatar ka zo office" Abubukar yace tare da nufar ƙofa, bin shi su Insu suka yi rai fes, share zufa registarer yayi tare da binsudaido... "Uncle Abubakar mun gode sosai, se nan da sati" jinjina mata kai yayi tare da faɗin "duk abindaya shige miki duhu ki tuntuɓeni" "in sha Allah uncle Abubakar" tace tare da shigewa mota, rufemata murfin yayi Ibrahim da ya shiga mazaunin shi yaja suka wuce, "SSB" ƴar former governor tace da mamaki, tare da bin motan da ido har suka ɓacewa ganinta.... "Wannan address ɗin zaka kai ni Ibrahim" tace tare da nuna mai address ɗin, "gidan Anty Lailahne ai" yace tare da kallon ta, "eh dama ka sani ne?" "Eh na sani, ina zuwa lokaci zuwa lokaci, mugaisa" yace tare da kallon ta, "to can zamu, wallahi yunwa nake ji" tace tare da yamutse fuska.... Murmushi ya saki tare da faɗin "na ce zaki ci wani abu kin ce a'a, yanzu kuma kina kukanyunwa" "yanzu na fara ji" tace tare da yamutsa fuska, "se ki yi haƙuri mu ƙarisa" yace tare da maidahankalin shi ga hanya... "Ibrahim ya akayi Anty Lawuza ta fara aiki a gidan?" Tace tare da kallon shi ta mirror, murmushi ya saki tare da faɗin "SSB ya buƙata" "kaman ya ya?" Tace idonta akan shi, "ina Bertuwa yakirani akan in ina da wanda na yarda da ita in turo ta yana son ta saka mai ido akan matar da akaauramai saboda ana zargin tana biye-biye" "subhanallah" Insu tace tare da kallon shi, "dalilindayasana tura ta neman aikin kenan, saboda tana da kwalin diploma" "shine har yanzu ba ta dainaba?" Tace tare da kafe shi da ido, murmushi ya saki tare da faɗin "tace aikin na mata daɗi, tanasoncigaba da yi" "Allah me ikon"... Tace da mamaki, ƙaramar dariya ya saki tare da faɗin "za ta iya sadaukar da dukkan lokutantaakan aikin SSB dan karamcin shi a gareta me yalwa ne, ita ke kula da duk wata mata da za'a kawo dan SSB a wannan gidan" "wai Ibrahim da gaske Uncle matar goma ya aura?" Insutacetareda bayyana zallan mamakinta a saman fuskanta, "inji wa?" Yace murmushi ɗauke a samanfuskan shi, "ji na yi" tace cike da basarwa, murmushi ya saki tare da faɗin "ba goma ba ne, shabiyu ne" yayi maganan tare da karya lungu da ze sadashi da ƙofar gidan Lailah... "Twelve!" Tace tare da zabura ido waje fuska cike da zallan mamaki, murmushi ya saki taredafaɗin "eh" "amma Anty ba ta sani ba ko?" Tace cike da son tabbaci, "maybe, amma ba za takasasanin biyun farko da Hajiya ta neman mishi su da kanta ba" jinjina kai tayi tare da faɗin "hakane""ba wanda yasan da waƴan nan se Hajiya da sauran ƴan uwa, ni ma na sani ne saboda sakoni dayayi a rayuwarshi, goman ƙarshe yawancin duniya ta sani, suma ba Hajiya ta nema ba, iyayendakan su kan zo neman alfarma, Hajiya ba ta ƙiyawa saboda macece me dattako, se dai rashinhaƙuri kan sa su neman saki in sun kwashi abinda ya kawo su, duk ciki ba wacce ke iya haƙurinshekara ɗaya ko biyu, watanni ne"... "Ba ya saki se dai suje kotu ta raba, to ko sanin fuskokin su ba yi yake ba, wasun su har sukagama zaman su basu saka shi a ido ba, wacce dalilinta Lawuza ta fara aiki a gidan, yawanbanzatake, tana da saurayi a gefe, har cikin gida take shigo dashi, a matsayin ɗan uwanta, su aikatamasha'a, akwai Maude shugaban masu aikin cikin gida, ita ta fara zargin wani abu ta samuHajiya da maganar, ita kuma Hajiya ta sanar da shi, shine ya tuntuɓeni da maganan, danbesonMaude ta tabbatar da kanta, dan macece wacce ba ta iya ma bakinta ba, akwai surutu kamar ke" ya idda maganan tare da taka burki a ƙofar gidan Lailah, "Kakata ce ai" tace tare da tura baki tabuɗe motan ta sauka.... Comments fans🙏🥰 🫀MUGUWAR TSOKA 🫀 {🫀TA'ARE KALLUƊE} [Muscle Cramp🫀] ) عضلة سيئة ( 🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_ https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 written and Created ~~~~~~~~~~~~~~ ِبسم الله الرحمن الرحيم By Yardajjiya👩 💻 Page. Seventeen (Bari mu leƙa Bertuwa) Ko da suka koma ɗakunansu ba su kwantar ba, alwala suka yo suka fara kaiwa rabbil izzati kukansu, se da suka tabbatar sun gamsu dan kan su sannan suka ɗaura tasbihi da hailala da istigifari.... Se da suka gabatar da sallahn asuba sannan suka kai kawunan su ga katifa, ta ɓangarensuHabiba ma ba su rumtsa ba se da suka gabatar da sallah... Ƙarfe bakwai dai-dai Nafisat ta miƙe ido cike da barci ta faɗa toilet, a hanzarce ta watsa ruwatafito ta shafa lotion sama-sama ta saka uniform ta ɗau back ɗin ta ta fice da sauri, "au ke damazaki je makarantar?" Babiya tace tare da bin ta da ido, hamma ta saki tare da fadin "zani Hajiya, inasu Sahabee? Ba dai sun tafi ba ko?" Tayi maganan ido waje, "yanzu suka fice, sun dage mawai jiranki za suyi, na ce su tattara su tafi, wataƙila ba za ki ba ne" "zani" tace tare da ficewa dasauri... Ba ta jima

Chapter 21 of 109