"ah dole mu faso, abu namu maganin a kwaɓe mu" Insu tacecikeda farin ciki, kallonsu su Salman suke cike da mamakin jin sunayensu, su kuwa banda murmushi
ba abinda suke saki....
"Wani group ne haka?" Samir yace tare da gyara zama, "ba group ba ne kaman ko wanne, gidauniyar temako ne, marasa ƙarfi, marayu, da dai sauransu, brother Shureimda abokanshi gasunan su suka buɗe mana, Alhamdulillah an cimma abubuwa da dama, yanzu dai haka tanadaregister da gwammati, sannan ana ta samu member's a tafiyan" Sadam ya koro mai bayanincikeda farin cikin jin sunan shi a waƴanda za'a wa ƙarin matsayi, "ma sha Allah, lallai be kamataayi
tafiyan bani ba" yace fuska cike da murmushi, "kwantar da hankalin ka, admin nike zan saka"
Insu tace cike da yanayinta, murmushi suka saki tare da bin ta da ido....
"Ai wannan admin's ɗin da za'ayi ze ƙarawa wasu wuta" Farisat tace tare da sakin dariya, "aikuwaakwai masu jira dan Minha ta ƙosa, tace har girka ta fara" Annur yace fuska yalwace da
murmurshi, dariya suka saki idansu akan shi, "ku tsaya, ban gane ba, Yaya Annur meneneaƙasawanda ban sani ba! Magana ɗaya biyu Minha, anya kuwa!" Tace cike da zargi, dariya ya saki tareda faɗin "ai anyan nan kuwa shine" zare ido tayi tare da faɗin "yaushe aka yi haka! Yaya Annur
dika-dika shekarunka nawa da aure!" "Biyar" yace a dake, shine zaka ƙara wani!" "In sha Allah, ai
sisternki zan aura" "to duk da haka, Allah ya nuna mana, ance so sone, amma san kai yafi" dariyasuka saki tare da bin ta da ido, "wallahi fa, in tana so ai muna tare da ita, se dai Anty Ladifatarungumi sorry" "ai ta runguma ma, tabi abin da addu'a" yace cike da murmushi, "a gaidata" tace
cike da yanayinta....
"Yawwa Insu, bar zancen nan ina da magana dake" Sagir yace tare da yafutota, ba musutamiƙetayi inda yake, "in kaji kira samu ne" tace tare da zama a gefen shi, "zamu sa labulene" yacetareda gyara zama, "to musa me kauri" dariya suka saki tare da bin ta da ido, "akwai wata da nagakin sa a statut ɗinki kusan one month da ya wuce" "to! Wani hoto kenan!" Tace da mamaki, "tokaman dai na biki ne haka, na ga kinyi posting ɗin jama'a tare da Amaryan da yawa, sumawandanake maganan kinyi su da amaryan da yawa, se dai akwai wanda ki ka sa su uku Nafisat natsakiyansu da milki ɗin lace, su kuma suna tsaye a gefenta da brown ɗin lace" ya idda maganancike da fatan ta fahimta....
"Oh! Na bikin Asma ne na gane, me ya faru?" Ta jefa mai tambayan tare da gyara zama, "ohInsu"yace murya cike da murmushi, kafe shi da ido tayi na ta fuska cike da mamaki, "to shikenanɗayadaga ciki ne ta kame muku ni" yace tare da kafeta da ido, fiddo ido waje tayi tare da kallonindasaura suke ganin yanda suke sakin murmushi ya sata sakin nata murmushin tare da fadin"wakenan a ciki!" "To ba na ce gata ba, amma kaman ita ce a ɓangaren daman Nafisat, bari innunamiki ita na ɗauki hoton" "maza nuna ta" tace tare da gyara zama, "to an samu abinda ake so" Sadam yace tare da sakin dariya, "ai a wannan fannin zamu mutu, hanyar haɗa sunna ma'aiki ba"tace tare da sakin dariya, "in Insu fa ta ji maganan haɗa aure jikinta har zikiri yake" Salmanyacetare da sakin dariya, dariya suka kwashe da shi idansu akanta....
"Kin ganta" Sagir yace tare da miƙa mata wayan bayan yayi zooming ɗin fuskan Fadila, "wow!
Fadila ce! Ma sha Allah, Allah Alhamdulillah, kai Yaya Sagir na yi matuƙar farin ciki, in shaAllahdakai za'ayi, kar ka damu zan share maka hanya" tace cike da farin ciki tare da miƙa mai wayan, "nagode ƴar uwa, nasan zaki iya" yace cike da farin ciki, "kwantar da hankalinka kana dani" tacetare da ɗaukan wayanta da ke ruri, ɗaga kiran da sauri tayi tare da karawa a kunni, shirundaƙikutayi kafin tace gani nan uncle" ta zare wayan, miƙewa tayi tare da faɗin "bari mu leƙa canmunazuwa, uncle Shureim in ban dawo da wuri ba ka kiran please akwai magana" murmushi yasakin
mata tare da jinjina mata kai, "Yaya Samir ina dawowa" tace tare da ficewa da sauri, da fuskoki
me cike da murmushi suka bi ta....
Sallama tayi ta shigo parlorn hannunta riƙe da na Hasinat da kanta ke duƙe, ajiyeta tayi samankujeran dake kallon wanda Kamil ke zaune, ɗagowa tayi fuska cike da murmushi tare da faɗin"uncle ka dinga duba time, kar a shiga haƙƙin Nafsii" tayi maganan murya a marairaice, murmushi ya sakin mata tare da jinjina kai, murmushi ta saki tare da faɗin "Anty Hasinat fatannasara" tana kai nan ta juya ta fice da sauri..... Murmushi ya saki ganin yanda ta kasa ɗago kai tare da sai-saita murya cike da kamalanshi yace"barka da wannan lokacin" "ina wuni" tace a ɗan hanzarce, murmushi ya saki wanda ba tagagarajiyo sautin fitan shi ba tare da faɗin "Alhamdulillah na ɗauka kin kurman ce ai, tunda na gakinzama bebiya" murmushi ta saki tare da ƙara sadda kai, "to da fari dai sunana Kamil, Kamil Sadam, duk da na san daughterna tayi miki bayanin komai, amma zan mai-maita da bakina, a gaskiyanatsuwarki da kama kan ki, da yanayin jan ajinki suna daga cikin abinda suka ingizoni gareki, ahsannan kafin in iso gareki na tuntuɓi iyaye saboda kar in shiga haƙƙin wani ko yana tare dake, duk da dai daughter tace mun ba kowa, amma dai na sa ta ƙara tambaya, amHasinat ba dawasana zo ba, idan kin lura ba yaro bane ni, duk da ba zan yarda a sani cikin manyan ba, dan dasaurana" ya tsagaita sautin murmushin shi na fidda amo, ɗan ɗagowa tayi ta mai kallon sakanni tamaida kai....
"Ma sha Allah, ina da mata ɗaya da yara uku, ba gazawanta yasa na ji ina san mallakan ki ba, nadai ji ina sanki ne, kuma ina fata ku zame min mataye na gari, iyaye na gari wa ƴaƴana, Allahyasa kina da sha'awan auren me mata?" Ya idda maganan tare da kafeta da ido, murmushindabega wanzuwan shi ba se sautin shi ta saki tare da faɗin "Allah ya zaɓa abinda yafi zama alheri"
"amin" yace cike da farin ciki, "in sha Allah zan amshi numberki wajen daughter, amma faki yi
haƙuri dan ina da takura, ina son kula fiye da yanda zaki zato" murmushi ta saki ba tare datacekomai ba, "okay kafin ƙasa ta tsage ki nemi shigewa bari mu zo mu wuce, na ga dare ya nausa"
yace tare da miƙewa, murmushi ta kuma saki cike da jin nauyi ta miƙe, takawa yayi a natseyadoshi fita daga parlorn ta dafa mai baya....
"Allah ya shirya mana zukatan mu" Daddyn dake zaune kusa da Mami yace fuska cike da alhini, "ai Daddy komai ya wuce, ta tafi, taje ta girbi abinda ta shuka" Insu dake zaune gefen Mami tacetare da sakin murmushi, "wallahi abin ya rikitani, a masallaci can barrister ya faɗamin maganan, duk na ruɗe na dawo gida Maminku ma ta tisamin, na ce a'a! Wannan wata iriyar butuluce" "ai
gaskiya mu ma ta girgiza ƙwaƙwalenmu Daddy, amma ai akwai Allah" tace tare da ɗago wayantadake ruri, ganin uncle Kamil na yawo a saman screen ɗin ya sata miƙewa tare da faɗin "Daddyseda safe, na so mu sha hiran yaushe gamo, amma zan shigo da safe in sha Allah, Mami se dasafe" murmushi suka sakin mata cike da kulawa me haɗe da ƙauna suka sa mata albarka ta juyataficeda sauri, murmushi Daddy ya saki tare da faɗin "duk inda yaran nan suke alheri na biye dasu, "ai
dacen uwa ta gari da suka yi shi ya haifar da hakan" Mami tace fuska cike da murmushi..... Tana fita ta tadda su tsaye da alamu ita suke jira, "oh Allah uncle Kamil da sauri haka!" Tacecikeda mamaki, "to tace ta ƙulla aminta da kunya" yace fuska cike da murmushi, harara ta juyatabanka mata tare da faɗin "kar ki sa a koma da ƴan Bertuwa matsayin ƙauyawa a baki, wallahi dawaye wan mu" murmushi ya saki tare da faɗin "gaskiya kam ga waye wa nan" "uncle Kamil a'afa"tace tare da kallon shi, murmushi ya saki tare da faɗin "naji, bari dai muga ko gaba in na zoza'aji
kunyata, daga nan se in yanke hukunci" murmushi ta saki tare da faɗin "to ka kawo mafita, AntyHasinat koma ciki bari mu wuce" jinjina kai tayi tare da faɗin "Allah ya tashe mu lafiya" a sanyayeta juya ta shige, murmushi Kamil da ya bita da ido ya saki tare da faɗin "muje daughter" bamusuta shige suka nufi gida.....
Tura ƙofan general parlor tayi a natse, da mamaki ta tsaya turus tana bin waƴanda ke zauneidansu akanta da ido, Sadam, Yasmin, Samir, "baku kwanta ba!" Tace tare da fara takowa ciki, harara Sadam ya zabga mata ya miƙe tare da faɗin "taya zamu yi barci bayan kun fita a wannanlokacin" ya idda maganan tare da nufar bedroom ɗin shi, "oh Allah mun zama ƴan yaye" taceahankali tare da sakin murmushi ta ƙarisa ta zauna kusa da Samir...
"Yaya Samir yakamata ka je ka kwanta haka" tace cike da kulawa, "yanzu kuwa baby Insu, banada wani zillimi, barci zanyi me cike da aminci" yace cike da zumuɗi, kallon Yasmin tayi taredamata alamun "lafiya!" Jinjina mata kai tayi fuska cike da murmushi, murmushi ya saki taredafaɗin "ni zaki tambaya, dama su Mommy sun yafewa Anty ba ku faɗamin ba!" "Oh, to ai labarindanace maka zan dawo in baka kenan, shine wato baby ta rigani" tace tare da balla mata hararawasa, dariya ta saki tare da bin ta da ido, murmushi ya saki cike da farin ciki tare da faɗin"ni nakasa haƙuri na tambayeta" "aiko sun yafi juna gaba ɗayansu, Mommy ma a hannayenta tacika"
"haka baby tace mun, Allah mun gode maka, Allah ka haskaka makwancin baiwarka" yacehawaye na biyo kuncin shi" "amin, dan Allah Yaya Samir ya isa haka, muje ka kwanta" murmushi
ya saki tare da miƙewa cike da so da ƙauna yace "kuje ku kwanta" jinjina mai kai suka yi sukabi
shi da ido har ya shige.... Sauke numfashi suka yi tare ra kallon juna, "ina Malama ƴar jarida?" Tace tare da sakin hamma, "yunwa ko?" Tace da kulawa, "no barci ne" "muje mu kwanta, mijinta ya lallaɓata sun tafi badaɗewa" miƙewa tayi tare da sakin dariya cike da yanayinta tace "nasan za'ayi haka, tundatakemaganan kwanan fa be ce komai ba" murmushi ta saki tare da faɗin "ai ya kanainayeta dararrashi da ban baki sun tafi" "meyasa baki bi su uncle Shureim ba baby!" Tace da mamaki idantaakanta, jan hannunta tayi suka nufi ɗakinta na da, suna shiga ta rufe ƙofan tare da faɗin"kinaBertuwa fa baby Insu, taya zan samu kwanciyar hankali in na koma bayan duk abubuwannandasuka faru yau"....
"Baby da kin koma, ba wani abu fa, kin manta alƙawarin mu ne!" Girgiza kai tayi tare da faɗin"zamu rayu, rayuwa me cike da farin ciki, zamu danne damuwoyin mu a ƙasa zukatanmu, muwanzar da farin ciki a saman fuskokin mu, zamu saka kowa farin ciki ko da mu ba ma marabadashi" ta jero maganan idanta akan Insu, "zuciyata da taki ɗaya ce Insu, ba zan iya barin ki a cikindamuwa ba, kamar yanda na san ba zaki bari na ba" da sauri ta matso gareta ta rungumetaƙaƙam, tare da faɗin "ni ƴar gata ce, dan ina da kafaɗan koka damuwana" tayi magananhawayena biyo kuncinta, hitting bayanta ta fara a hankali tare da sakin na ta hawayen....
Se da suka daɗe a haka kafin su saki juna, kallon juna suka yi fuskoki cike da murmushi, "babykincanza fa" Insu tace cike da shaƙiyanci, harara ta zabga mata tare da faɗin "kar ma ki fara, inwannan canjin ne ai kin fi ni yinshi ƴar rainin wayau" dariya ta saki tare da nufar gado ta hayetazaro waya ta danna kira tare da zamewa ta kwanta, hayowa Yasmin tayi ta kwanta a kusadaitatare da faɗin "ina uncle Kamil ɗin?" "Ya wuce side ɗin Yaya" "ta ƙofar baya ya wuce?" Tacetaredakallon ta, jinjina mata kai tayi tare da faɗin "ai ta can yakamata ya bi" jinjina kai tayi cike dafahimta...
Tunda ya haye sama ya shinfiɗar da Mairah ya wuce toilet ya watsa ruwa ya fito ya shirya cikinkayan barci ya haye kusa da ita ya gyara mata kwanciya ya ɗau system ya kunna ga fara aiki
hankali kwance, yana tsaka da abinda yake wayan shi ta ɗau kuwwa, waigawa ta inda ya ajiyetayayi ganin sunan da ya sama number na yawo a saman screen ɗin ya sa shi sakin nagartaccenmurmushi tare da rufe system ɗin ya maida ma'ajiyar shi ya ɗau wayan ya zame a hankali taredakatse kiran ya maida wani kiran....
Tana ganin ya katse kiran ta saki murmushi tare da kallon Yasmin dake bin ta da ido, ko kafintasamu zarafin cewa wani abu wani kiran ya shigo, ɗagawa tayi a natse ta kara a kunni taredalumshe ido, murmushi ya saki tare da lumshe na shi idon, "um" tace a ciki-ciki, murmushi yakuma saki tare da faɗin "babu sallama?" "Assalamu alaikum" tace cikin zazzaƙan muryanta, amsawa yayi sautin murmushi na fita a muryanshi, "ina ki ka shiga haka?" Yace a hankali....
"Kai ya ɗau zafi" tace a hankali, "i know, kar ki ce komai about issue ɗin nan" "okay, ina farincikinAbbie?" "Gata gefen Abbie tayi barci, amma kin san wani abu?" "A'a" tace a hankali, tayi matuƙar
kewanki fa, se kuka take zata Ami" murmushi ta saki cike da nata kewan da tayi, "na fita!" Muryanshi me cike da shauƙi ya doki kunnuwanta a hankali, murmushi ta saki tare da fadin"I
know" "Kin san wani abu?" Yace murya ƙasa-ƙasa....
"A'a!" Ita ma tace cikin muryan rowa, "matuƙar ki ka ɗau tsayin lokaci ba tare da kin dawogareni
ba zan gaza Insiyyah! Ki dinga tunawa da bugun zuciyata ki ka tafi, kar ki bari in galabaita" murmushi ta saki me faɗi tare da faɗin "in dai Insiyyah na numfashi to ba zata yi nisa da kai ba, kai ne farin cikinta fa, ko ka manta ne!" "A'a ban manta" yace a hankali, "ka ci abinci?" Taceahankali, "ban san meyasa ba tsoro ya hanani ci" yace murya ƙasa-ƙasa, "no ba zamu kwanadayunwa ba, kar ka manta da jarumai ne mu, ba wani ƙaramin abinda ze razanamu" "tsoro nakeji" yace a hankali, "Nafsii! Tace murya cike da rarrashi, "um" yace a maƙoshi....
"Kwanciyar hankalin Insiyyah kasantuwa a gefenka ne, ba zan iya nisantanka ba, zan dawo" "nasani, se dai zuciyata na ƙaryatawa" "shareta dama ba ko da yaushe take raya mana dai-dai ba, kafasan sarauniyar san kaine ita" "yeah" yace a hankali, "yanzu kamata yayi muci abinci"
"Gorgeous kalli time dare yayi sosai fa, sannan ba zan iya cin abu me nauyi ba kin san haka" "okayka sha tea, ina ce donuts ɗinka na kusa?" "Eh gashi can ma ina hangoshi" "shikenan bari inmaMahmah magana ta haɗo maka" "okay ƴar albarka" yace cike da ƙauna, murmushi ta saki taredafaɗin "alƙawari in ta kawo" tace a hankali, "nayi alƙawari zan sha cup biyu" murmushi ta saki tareda faɗin "wannan shine Nafsii na, abin alfahari na" murmushi ya saki tare da faɗin "baki ji ba" "inaji" tace a hankali "ina sanki!" Murmushi ta saki tare da faɗin "ina sanka! Ina sanka!! Ina sanka!!!
Da dukkanin zuciyata" tana kainan ta zare wayan tana jiyo sautin dariyarshi me cike da farinciki
ta katse kiran....
Fuska cike da murmushi ta maida kira kan number Yasmin Ɓadamayya, tana ɗagawa tace"Mahmah!" "Insu!" Tace a hankali, "ba dai kin fara barci ba?" "No zaune nake ina karatu" "please
Mahmah tea muke so, irin wannan haɗaɗɗen haɗin da aka saba" murmurshi ta saki tare dafaɗin"to bari in tashi" "yawwa Mahmah na, se na kira" ta idda faɗi tare da saurin katse kiran danyandataji tana amsa mata magana ta san akwai magana a bakinta, bin ta da ido kawai Yasmintakecikeda mamaki, murmushi ta saki tare da ajiye wayan a bedside drower ta kai hannu ta shafa samanidan Yasmin dake kanta....
"Baby Insu haka ki ka yi nisa!" Tace da mamaki, "na tafi baby, asalin tafiya, kullumji nake anaƙaramin san shi a cikin zuciyata, ji nake idan na rasa shi tsaf za'a iya rasani!" Ta idda maganancike da gaskiyanta, dariya ta ƙyalƙyace dashi cike da burgeta da tayi, "baby Insu Allah ya ƙaradanƙon soyayya" murmushi ta saki tare da ƙwaƙwumota, "sake ni wallahi ba Uncle bane ni" tacetare da ƙyalƙyacewa da dariya tana ƙoƙarin ƙwace kanta....
Comments fans🥰🙏
🫀MUGUWAR TSOKA 🫀
{🫀TA'ARE KALLUƊE}
[Muscle Cramp🫀]
) عضلة سيئة (
🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
written and Created ~~~~~~~~~~~~~~ ِبسم الله الرحمن الرحيم
By
Yardajjiya👩 💻
Page. Sixty three
"Me ki ke jira har yanzu baki shirya ba! Ko an ƙara lokacin tafiyan na ku ne?" Kabir da ya shigoyatadda Iƙilima zaune ba tare da shirin tafiya ba yace cike da mamaki, kauda kai tayi tare dagogehawayen da ya kawo idonta....
"To kai ma ka faɗi dai Kabir, tun ɗazu nake fama da ita akan ta tashi ta shirya kar su yi ta jirantaba daɗi, amma yanda ka ganta a haka ba ta ko motsa ba, se hawaye da take ta aukin sharewa" Mama dake zaune a ɗakin ta gefe tace cike da damuwa, duƙawa kusa da ita yayi tare da faɗin"Iƙilima lafiya kuwa!" Fashewa da ƙaƙƙarfan kuka tayi tare da girgiza kai cike da rashin madafa, "ba zan iya ba Yaya Kabir, ba na da idan kallon su wallahi, ba ma za su ƙara aminta dani ba, ta
ruguzamin rayuwar da nake farin cikin samu, ta tarwatsa komai Yaya Kabir komai ya ƙare!" Taidda maganan cike da ƙunan zuci hawaye na bin kuncinta.... Rungumota yayi da sauri yana haɗiyan zuciya, banda bugu ba abinda zuciya shi dake tafarfasakeyi, "me muka ma Sa'adatu a rayuwa! Mun so ta ta ƙimu, mun nuna mata kula ta watsar, dukdahaka ba mu yi fushi ba, mun cigaba da mata addu'an shiriya daga mahaliccinta, amma ita bandabita da ƙulli ba abinda take mana, yanzu Yaya Kabir ya za'ayi su yarda dani su amsheni bayanƴaruwata ita ta kawo ƙarshen numfashin abar so da ƙaunansu" "shiiii ya isa haka" yace a daketareda shafa bayanta haɗe da bugu a hankali....
Se da ya tabbatar ta samu natsuwa kafin ya ɗagota ya share mata ragowan hawayen taredafaɗin "tashi ki shirya jar su yi ta jiranki" girgiza kai tayi tare da buɗe baki a hankali, "kar ki cekomai tashi ki yi abinda na ce" yace cikin katsen hanzarinta, ƙwal-ƙwal idonta dake kallonnashi
idon yayi, "kar ki damu ba ma da yaƙini akan abinda ki ka faɗi, zato ne da hasashe, ki shiryamuje, in dai suka ce ki dawo ba zamu ja ba, ba kuma zamu ce musu dan mene ba, amma yanzubamadahurumin yanke wannan hukuncin" ya idda maganan cike da kulawa...
"Yawwa to kin ji abinda dai ya dace, idan anje suka ce a dawo shikenan, amma yanzu ba mujebamu yanke musu wannan tsatstsauran hukunci haka mu da su duk ba zamu ji daɗi ba, mazamiƙeki shirya Iƙilimatu Allah na tare da me gaskiya" Mama tace cike da kulawa, jinjina kai tayi taredamiƙewa a natse ta wuce, sauke numfashi Kabir da ya bi ta da ido yayi tare da maida dubanshi gaMama....
"Ina yaran nan?" Yace a natse, "sun fita ɗazu babu daɗewa, se dai nayi nauyin bakin tambayansuinda za su amma na san ba za su wuce gida ko shagon Ɗan liti ba" jinjina kai yayi tare da zarowaya ya danna number Sadiya, ringing biyu Sadiya da ta tsaya sallaman me napep ta ɗagaaɗarere tare da ɗaga mai sallama....
"Kuna ina?" Ya jefa mata tambaya ba wasa, "gamu a wajen nan isowan mu kenan" tace a hankali, shirun sakanni yayi kafin yace "ku kula da kyau, in kun fito ku wuto airport can zamu yanzu" "toAnty Iƙiliman zata koma ne?" Tace a sanyaye, "in ta zauna me zata miki?" Yace tare da katsekiran, zaro wayan tayi tare da bin shi da ido, "waye!" Harira tace a ɗarare, "Yaya Kabir" taceahankali, "me ya ce!" Tace a firgice....
"Wai in mun fito mu wuce airport" tace tare da maida wayan a jaka ta fuskanci bankin dakegabansu, "tsoro nake ji Sadiya" Harira tace baki na rawa, girgiza mata kai tayi tare da faɗin"ki
daure" tana kai nan taja hannunta suka nufi ciki.... Suna shiga suka ƙara tsurewa dan yanda wajen ke dauke da tsaro na musamman, da sauri ɗayadaga cikin ma'aikatan dake tarba ta iso gare su ta marabcesu tare da tambayan su abindasukebuƙata, cikin rawar baki Harira tace "ah, am munn, mun zo ɗaukan ajiya ne" ta idda maganantare da sakin murmushin ƙarfin hali.... Bin su da ido tayi cike da ɗan shakku tare da faɗin "suna" kallon Sadiya Harira tayi tare damataalamun tayi magana, saurin faɗin "Sa'adatu" tayi tare da kallon ta, "please cikakken suna" taceidanta na yawo akan fuskokin su, "eh shine na faɗa miki Sa'adatu mu" "Sa'adatu Abdull" Hariratayi saurin katse mata hanzari daga sunan Baba da take shirin faɗi....
Juyawa tayi ta kalli jerin waƴanda suke zaune computer's a gabansu tare da faɗin "kuma nasearching ɗin Sa'adatu Abdull" ba musu suka fara, juyowa tayi idanta na yawo a saman fuskokinsu, dakewa suka yi kaman ƙirazansu ba sa barazanan ɓallo ƙirjinsu, "na samu Ma" ɗaya dagaciki
yace tare da ɗaga hannu.... Kafe su da ido tayi tare da faɗin "please ku zauna bari a kawo muku key" tana kai nan ta wuce, sauke ƙaƙƙarfan ajiyan zuciya suka yi tare da kallon juna, zama suka yi a dake, kallon SadiyaHarira tayi tare da faɗin "keyn me za ta ba mu! Ina yana hannun mu?" "Allah masani Harira, abinya soma ɗaure mun kai, "Allah ka fidda mu lafiya" Harira tace tare da haɗiye kakkauranyawudake shirin cika mata baki.... Ba su jima da zama ba ta dawo cike da girmamawa tare faɗin "bismillahn ku" tana kai nantawuce tare da wanda ke tsaye a gefenta da madaidaicin keke, tashi suka yi a hanzarce, cikedaneman mafita Sadiya tace number asusun ma nawa ne?" "Wallahi na manta, kaman ba ta faɗabafa" Harira tace a ɗan tsorace, "ta faɗa" Sadiya tace ƙirjinta na bugawa da ƙarfi....
Suna isa gefen asusukan ta juyo fuska cike da murmushi ta miƙa musu key ɗin da ta ɗakkoasaman keken ta miƙa musu tare da musu fatan sa'a ta wuce, "mun shigesu, to wannene! Gashi
cctv n baje a wajen bare mu gwagwgwada" Harira tace a rikice, lumshe ido Sadiya tayi taredafaɗin "Sa'adatu me ki ka yi haka kenan!" Tayi maganan tare da baza idanunta akan key ɗindatake ta jujjuyawa cike da neman mafita, faɗawa idanta yayi akan number asusun dake jikinkeyn, cike da farin cikin samun mafita tace Harira na ga number!" "A ina!" Tace cike da ruɗu mehaɗeda jin daɗi" "natsu ana kallon mu" tace tare da matsawa gefen asusunan, babu ɓata lokaci tafara
bin numbobin da ido, tana kai kan wanda suke nema ta zura key da bismillah ta murɗa....
Sauke ajiyan zuciya tayi ganin ya buɗu zura hannu tayi a natse, jin hannunta ya taɓi wani abuyazata zarowa da sauri,madai-daicin akwatine me ɗaukan ido, miƙa ma Harira tayi tare da maidahannu, jin ba komai ya sata zarowa a natse ta kulle suka nufi barin wajen, suna fitowa sukataddasu tsaye da alamun su suke jira... Murmushi ɗauke a saman fuska tace muje ku sa hannu" ba musu Sadiya ta bi ta, suna shigabaɓata lokaci aka ba ta takardan da ba ta san ko na menene ba ta saka hannu ta basu keynsukamata godiya ta fito, sauri-sauri gudu-gudu suka fice daga wajen, suna ganinsu a bakin hanyasuka sauke numfashi me ƙarfi tare da kallon juna, "muje ba amfanin tsayawan mu anan" Hariratace tare da waige-waige, jinjina mata kai Sadiya tayi tare da tsaida me napep ɗin da ya zowuce....
"Yanzu se yaushe kenan?" Samir dake tsaye gefen Insu dake magana da Habiba yace idanshi
akan ta, "ina ce zaka zo can?" Tace nata idan akan shi, "ze je mana, ai yakamata yaje ya mamegirma shugaban ƙasa godiya akan jajircewan da yayi har ya fito" Ali ya tari zance da faɗinhaka, jinjina kai yayi tare da faɗin "next week amma ba a wannan week ɗin ba" "Allah ya kai mu" tacefuska faɗaɗe da murmushi....
"Yakamata ki kira Anty Iƙiliman muji ko zata tafi yau ɗin, kar ku tafi ya zo abun ya dameta" Yasmin tace idanta akan Insu, "haba baby ƴar uwarta ce fa ta rasu, zata buƙaci lokaci da ƴanuwanta dan rage damuwa" Insu tace cike da ganin hukuncin da ta yanke shine dai-dai, "ku
kammala sallaman na ji an fara kiran
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 102 Chapter of 109