Share this page
ke yi, ta kasasamun sukuni daga bugun da yake, natsuwan da ta ɗan samu na ƙoƙarin guduwa, yawunbakintaya ƙafe ƙaf, miƙewa a hankali tayi ta ɗau magani da ruwa ta sha ta ajiye ruwan a samanmadai-daicin fridge ɗin dake ɗakin ta wuce riƙe da roban maganin jakanta dake gefe ta ɗauka tasakatamaida ta rufe, haka tayi ta zaman jiran lokaci, 10:00am na bugawa ta miƙe ta goya jakantatakama akwati a natse ta fice, dan ta fahimci matuƙar ta cigaba da zaman anan tsaf za ta iyarasaiskan shaƙa... Ta ɓangaren former president kuwa tunda labarin dawowa gida da SSG ya ba wa jami'andaakaturo ya riski kunnuwan shi yake ɓaɓatun an ci mai zarafi har gida ba ze yarda ba se ya nemi haƙƙin shi, da wannan ɓaɓatu suka tattaro suka barshi, yana tabbatar da fitan su ya nufi bedroom ɗin shi a hanzarce kamar me shirin tashi sama, da ido su Jabiida dake hamdalanshadaƙyar suka bi shi, yana shiga ya danna ma ɗakin key ya zafi waya ya danna kira ya kara akunni tare da fara zagaye ɗakin... Ana ɗagawa ya tsaya cak tare da faɗin "yallaɓai na tsallake rijiya da baya, meyasa baka ankarardani zurfinta ba?" Wani banzan dariya aka saki daga can, tare da faɗin "yaro yarone, be sanwutaba se ta taka, barinka nayi ka taka ka ɗanɗani raɗaɗin dake tattare da shi na san zaka dawocikinhankalinka" "na dawo yallaɓai, na fahimci abinda ka ke ta son fahimtar dani" yace tare daɗagahannu, fashewa da dariya yayi tare da faɗin "kowa ya tuba dan wuya ba lada" "naji yallaɓai yanzume ne ne yakamata?" "Ka jira, ka kuma haƙuri ba yanzu ba, a kwai lokaci, yana nan tafe" "shikenan yallaɓai" yace a girmame tare da sauke wayan, tsaki ya ja me tsayi tare da faɗin"dasannu zaka shigo hannuna kai ma, bari dai mu kai ƙarshen wannan me ido a tsakar kan, zanwaiwayoka" yana kai nan ya nufi ƙofa ya buɗe ya fice.... A natse ya zauna a kujeran da aka ja mai, saurin serving ɗin shi sabon chef ɗin sa aka canzayayi tare da ja gefe ya tsaya cike da girmamawa, murmushi Hajiya ta sakin mai tare da faɗin"sannuda aiki, lallai kunyi ƙoƙari, duk da safen nan ku ka iya haɗa abincikan nan!" Murmushi ya saki batare da yace mata komai ba, "Hajiya bar mutun da aikin shi, in dai aiki ba na ka ba ne zaka gawahalanshi, amma in na ka ne ai a sauƙaƙe zaka ganshi" A'isha tace cike da murmushi, murmushi suka saki gaba ɗayan su ba tare da sun furta komai ba, ɗaga hannu a natse yayi ya ɗau cokalincike da dakiya ya ɗibi romon ƙafar saniya ya nufi baki ɗauke da bismillah, lumshe ido a natseyayi saboda rashin ɗanɗanon da yayi, a natse ta ke sakkowa babu garaje ko kaɗan, jiyo ƙarantakuntaya sa su zubawa wajen ido gaba ɗayansu, buɗe ido yayi a natse ya sauke a akan Insu da bayyananta kenan, da ɗin bin mamaki suka bi ta da ido.... Guntun murmurshi ya saki tare da saurin kauda kai saboda tsitstsinkewan da zuciyan shi yafara, "Insu!" Ibrahim yace cike da mamaki tare da miƙewa, marairaice fuska Lawiza tayi ta bazamataido cike da magiya, "me ne ne hakan Insu! Me ki ke shirin yi!" Yace cikin bayyana fargabanshi, kallon daƙiƙu ta mai ta kauda kai tare da sakin mai murmushin gefen baki ta saki hannunakwatin ta taka a natse ta ƙarisa inda suke, jan kujeran dake kusa da shi tayi ta zauna taredasakin musu murmushi, ba wanda ya samu zarafin maida mata da martani, murmushi ta kumasaki tare da jinjina kai ta kauda ido daga gare su ta maida ga SSB da hannun shi ke kyarma.... Murmushi ta saki tare da buɗe baki a natse tare da faɗin "good morning Uncle" "morning" yaceadake tare da ɗago ido ya baza mata fuska ɗauke da murmushin da be san ta inda ya fito ba, danyasan ba ya da ƙarfin zuciyan fidda murmurshi a wannan yanayin.... "Zan tafi" tace a hankali idonta ƙyam akan shi, jinjina mata kai yayi tare da faɗin "to" jinjinakai tayi tare da danne kukan da ke san kuɓuce mata, ba haka ta so ji daga gare shi ba, so tayi yatambayeta ina? Ko yace ba inda zaki tafi kina tare da ni, se dai ba ta ji abinda take fata ba, saukejakan bayanta tayi a natse ta jawo file ɗin da Yaya ya bata da zata dawo a hankali ta ajiyeagabanta, ɗago kai tayi ta bi fuskokinsu dake cike da fargaba da ido, sakin murmushi ta yi tamaida dubanta gare shi, ba tare da da kauda ido daga kan shi ba ta tura file ɗin gaban shi taredafaɗin "if you sign here I will have the great opportunity to marry him" ta yi maganan a dakebatare da ta kauda ido daga gare shi ba.... Guntun murmurshi ya saki tare da jinjina kai ya sauke ido a hankali daga gareta ya zuba mafileɗin ƙirjinshi na bugu da ƙarfi, "pen" yace a hankali kamar me koyon magana, saka hannuajakatayi ta zarowa a hankali ta ajiye mai, ɗauka yayi a natse ya buɗe file ɗin a natse takardanbuƙataryarjewan ɓangarori biyu akan raba aure ne daga babbar kotun Bertuwa wanda barrister Abdussamad Umar ya saka hannu matsayin wanda ya amso takardan daga Alkali babbankotun, murmushi ya saki a hankali ya saka hannu a wajen da ake buƙatan miji ya saka a natse kamar babu wani abu dake shirin tsaida mai da numfashin da yake shaƙa da fesarwa da ƙyar.... Yana gamawa ya ajiye pen ɗin a natse tare da ɗago ido ya kalleta, kafe idonta yake a indayasakahannun zuciyarta na ƙunan da tun da ta mallaki hankalinta ba ta taɓa jin wannan yanayinba, "you have a great chance" yace a hankali, jinjina kai tayi ba tare da ta kalleshi ba ta ja fileɗingabanta, maidawa a jaka tayi a natse ta dau pen ɗin ta maida, tana shirin ɗagowa murya Alhaji Jamil ya doki kunnuwanta, "wani file ne wannan ɗin!" Ɗago kai tayi a dake tare da faɗin"naneman raba aure ne da kotu ta bada akawo mai" tayi maganan tare da sakin murmushi.... "What! Jabir yace a razane tare da miƙewa zumbur, kallon SSB da ke sakin murmushin ƙarfinhali yayi tare da faɗin "what do you due!" Ganin be ce mai komai ba ya juya duban shi ga Insutaredafaɗin "me ku ka yi kenan! Me hakan ke nufi kenan! Me kuka aikata haka!" Ya idda jero tambayoyin kamar ze fasa ihu, kama baki su Alhaji Munnir suka yi cike da tsan-tsan mamaki me haɗe da firgici, ɗago kai tayi a natse ta share hawayen da ya kasa dannuwa tare da faɗin"abindayakamata muka aikata uncle Jabir, dama be kamata muguwar wasan nan ta kawo har yazuaraye ba" tana kai nan ta juya ga SSB dake bin ta da ido cike da mamaki tare da faɗin "akwai wani labari da zan baka yanzu Uncle, zaka saurara?" Ta idda maganan tare da kafe shi da ido, jinjinamata kai yayi a hankali, murmushi me faɗi ta saki tare da goge hawaye ta gyara zama... "Anyi wani kyakykyawan masaurata a shekarun baya, komai na masarautan na dabanne, ƙawaceyake da abubuwa na musamman, hatta da mamulka da jama'an ciki, sarakuna biyu ke mulkanta, sarakunan nan shaƙiƙan abokaine wanda shaƙuwar su da amintansu ya saka iyalansu zamakamar su wato abu guda" goge hawaye tayi fuska ɗauke da murmushi tare da faɗin "sunadayarakyawawa masu matuƙar biyayya garesu, a cikin yaran nan akwai yarima da gimbiya na musamman, sannan mafiya soyuwa a garesu, yarima da gimbiya sun fi kowa shaƙuwa a wannanmasarauta, ɗaya ba ya iya jin ya cika se ɗaya na a tare da shi, lokacin da suka furtawa junansukalman so sun yi ƙanƙanta da iya fahimtar menene ita, ba wanda ya saka su son junan su, sudakan su suka ga yakamata su so juna, a haka suka taso cike da mafarkin mallakan juna"... Tana kai nan ta tsahirta tare da jan hanci ta goge hawaye tare da sakin mai murmushi ganinidonshi da ya kaɗe tsaye ƙyam a nata, murmushi ya sakin mata cike da jin ta ƙara matsawabalallai ya iya dake raunin shi ba, su Hajiya kuwa zuba mata ido kawai suka yi fuska na shatatanruwan hawaye.... "Bayan sun kai munzalin sanin menene rayuwa yarima yayi nisa da gimbiya saboda nemanilimi, a wannan lokacin yarimar wani masarauta ya kutso kan shi a rayuwar gimbiya" jan numfashi tayi tare da dake kukan dake san ƙwace mata tare dw cigaba da faɗin, "ya sota tsakani da Allah, dukda san da yake mata be kai wanda yarimarta ke mata ba, se dai ta gane wani gaskiya da tagagara ganewa lokacin da yarimanta ke tare da ita wato ba son yarimanta take ba shaƙuwaneya haddasa mata haka, ruɗun shaƙuwa ne ya ruɗeta ta amsa buƙatan shi, a lokacin nantaji zataiya fito na fito da duk wanda ze hanata mallakan wannan yariman, da ta fahimci ba zata iya rayuwa ba tare da shi ba, idonta ya rufe, ta mance karamcin yarimarta, ta mance da rauninyarimarta, ta mance da ƙaunar da yarimarta yake tsan-tsan mata, ta mance zata iya tarwatsarayuwar yarimarta, ta zari takobi ta fito filin daga dan fito na fito da duk wanda ze kawo katatsaiko wajen mallakan yarimar da ya kutso rayuwarta, ba ta tsaya da raunata mutane ba sedatamallaki wannan yarima, se da ta mallake shi sannan rufaffen idonta ya buɗe, a lokacin ta fahimci lahanin da ta ma kanta, a lokacin ta ji da ma ba ta aikata hakan ba, a lokacin nadama da danashina mara amfani ya risketa, komai ya ƙare, wannan ƙayataccen masarautar me cikedatarin so da ƙauna ya ruguje saboda ita, waƴan nan adalan sarakunan sun mutu saboda ita, waƴannan amintattun iyalan na su sun mutu saboda ita, sauran yaran nan sun mutu saboda ita, baabinda ya rage a ciki masarauta, masarauta ta zama kufai" ta idda maganan tare da fashewadakuka ke ƙuna ta sadda kai ƙasa, se da ta koka sosai sannan ta ɗago ta fara goge hawaye a natsetare da sakin murmushi, goge hawaye Alhaji Jamil yayi tare da jan kujeran da yake kai bayayasauka ƙasa ya zauna yana me sakin kukan dake ta so mai tare da tuna shuɗaɗɗun abubuwa.... Kamo hannun shi tayi a hankali tare da faɗin "ta azabtu, ta wahaltu, ta jigatu, ta roƙi ubangiji yaɗauketa ya maidata gare shi ko zata samu sasauci saboda a kullum nadaman abinda ta aikatama yarimarta kasheta yake da ranta, babu ranar da rana zata fito ta faɗi ba tare da ta zubdahawaye me cike da ɗin bin nadama ba, kullum mutuwa take saboda nadama, se dai yarimayahanata zuwa inda yake bare ta roƙeshi yafiya akan abinda ta aikata mai, ba ta samu damanisagare shi ba har mutuwar da ta dinga fata ya risketa, se dai kafin ta tafi ta wakilta ɗaya dagacikinƴaƴanta data je ta nema mata wannan yafiya da ta mutu tana burin ji daga bakin shi" zamejiki ƙasa tayi ta damƙe hannun shi da ƙarfi ta ɗago kai ta baza mai idonta da yayi sharkaf da hawayetare da faɗin "dan girman Allah Uncle ka yafe wa Anty, har mutuwanta ya risketa ba ta dawani buri se san jin kalman yafiya daga gareka, tayi nadama, akan shi ta koma ga mahaliccinta, tayi danashinan wanda se da ya haddasa mata ciwuka mabanbanta, ka yi haƙuri ta aikata makakuskure se dai ba lefinta ba ne lefin MUGUWAR TSOKAR da ta nemi rikita tunaninta ne, sabodawannan lefin muka kasa gane kanta, saboda wannan kuskuren mahaifin mu ya rayu da itacikinzillimi da fargaba" ta idda maganan kuka me ƙarfi na kuɓuce mata, kuka su A'isha suka saki mesauti tare da bin Insu da ido cike da tausayawa..... Zaro hanky yayi a aljihun gefen rigar jikin shi a natse, miƙewa yayi cike da rashin garaje yamiƙarda ita, ya bata hankyn da kulawa tare da sakin mata murmushi, jinjina kai tayi ta fara gogewaa natse, "na fahimci wani gaskiya akan ƙaunar da muka wa junan mu, na fahimci dalilin da yasataaikata haka, na mata uzuri akan hakan, na daɗe da yafe mata tun ranar da igiyoyinshi ya haukanta na yafe mata har abada" ya iddasa maganan tare da goge guntun hawayen da suka zubomai tare da sakin mata murmushi, zare jajayen idanunta tayi waje cike da farin ciki ta saki dariyame faɗi tare da faɗin "da gaske! Uncle da gaske ka yafe wa Anty!" Ta yi maganan a matuƙar mamakance tare da kafe shi da ido, jinjina mata kai yayi tare da sakin murmushi, ganin irinkallon da take bin shi da shi ya sa shi faɗin "na yafe mata" rungume shi tayi da ƙarfi tare dasakinkuka me ƙarfi, be yi yunƙurin zareta ba, saboda samun sassaucin da yayi daga barazananfasoƙirjin shi da zuciyan shi take, be kuma hanata kukan ba duk da sukan zuciyan shi da kukankeyi, se da ta gaji dan kanta ta zare jikinta a nashi tare da faɗin "mun gode, mun gode sosai Uncle, kai na daban ne, Allah ya yafe maka dukkanin kurakurenka, Anty zata ji gamsuwar yafiyankagaretaduk da ba ta raye, ina da tabbaci akan haka" ta idda maganan murmushin na mamaye fuskantatare da jan hanci, murmushi ya saki tare da jinjina mata kai.. "Kayi haƙuri da kutsowa rayuwarka da muka yi ba tare da neman izininka ba, ba dan komai mukayi haka ba se dan Anty ta buƙaci hakan" tayi maganan idonta a na shi, murmushi ya saki taredagirgiza kai dan ya san in har ya buɗe laɓɓa ba lallai harshen shi ta iya ɗagawa dan furta kalmakoɗaya ba, murmushi ta saki tare da saɓa jakanta ta juya ga Hajiya cike da dakewa tace "Hajiya" kuka Hajiya ta saki cike da rauni, murmushi ta saki tare da sadda kai, dan ita ma ta kasa dannenata raunin a wannan lokacin, takawa tayi har inda take ta rumgumeta tare da faɗin "ki maidahankali ga karatun ki, kar ki bari wani abu ya kai wa ƙwazonki hari" jinjina kai tayi tare da sakinmurmushi me tafe da hawaye, janye jikinta Hajiya tayi a natse zuciyanta na matuƙar ƙuna, ɗagokai tayi ta zube ma su Jabir kauda kai Jabir da Abubakar da Alhaji Munnir suka yi da sauri, ɗagahannu tayi tare da faɗin "zo mu zauna, zo mu saɓa ne, in akwai wani abu da na taɓawa ɗayankuabisa sani ko rashin sani dan Allah ya yafe mun, ni na yafe komai" da sauri Alhaji Jamil da Kamil suka riƙe hannun tare da girgiza mata kai, murmushi ta saki tare da jinjina kai hawaye na binkumatunta, "Allah ya yafe mana, ba abinda ki ka taɓa mana" Yasmin tace tare da saurinkaudakai.... A'isha da Kausar kuwa ba su samu bakin magana ba dan sun san ba za su iya ba, Lubabatukuwako kallon inda take ba tayi ba dan wani mugun takaici ne ya danne ƙirjinta, dan ba ta ga dalilindaze sa a ƙi faɗa mata magana akan halin da ze iya shiga ba in ta tafi, "Anty Lawiza" tace a hankali, saurin juyawa Lawiza tayi tare da saki kuka, murmushi ta saki tare da goge hawaye, haɗa hannaye ta kuma a natse idonta na yawo a saman fuskokin su tare da faɗin "dan Allah kumantadani, kar wanin ku ya kusanto inda nake dan Allah" ta idda roƙon muryanta na rawa, da ɗinbinmamaki suka bi ta da ido, "mun manta dake tun yanzu ma" Ibrahim yace a zuciye, jinina kai tayi tare da sakin murmushi ta ɗaga kafa da niyyan barin wajen, "makarantarki fa?" Abubakar yaceasanyaye, tsayawa tayi tare da Juyowa ta kalleshi tare da faɗin "zan cigaba da yi a can, akwai naonline ma zan dinga ɗaukan lecture's a can" jinjina mata kai yayi tare da faɗin "branch ɗinInsoul ze iso can" yayi maganan cike da rashin jin daɗi, kallon shi tayi fuska ɗauke da murmushi taredafaɗin "Uncle!" Jinjina mata kai yayi tare da kauda kai, saboda kukan da ke taso mai, juyawagaSSB dake tsaye tayi tare da faɗin "Uncle nagode" murmushi ya saki ba tare da yace mata komai ba.... "Kar ku kashe ni a zukatan ku, in rayu anan" tace tare da kallon su Fadila dake ta risƙankuka, jinjina mata kai suka yi cike da rauni, "Baba Maude" tace tare da sakin ma Maude dake ta shararhawaye murmushi, juyawa da sauri tayi ta fice kamar za ta ci ta baki, murmushi ta saki taredadanne kukan dake shirin kuɓuce mata ta taka a natse ta isa ga akwatin ta, "hoto ko kin bar munne?" Yayi maganar kamar wanda aka dukeshi a tsakiyan baya, tsayawa cak tayi ta juyo a natsetare da faɗin "in dai kana so Uncle" jinjina mata kai yayi a natse, "na bar maka, amma kar kazamakamar ni, me magana da fatalwa" tayi maganan tare da zaro ido cike da yanayinta, murmushi suka saki tare da bin ta da ido, jinjina mata kai yayi idon shi akan ta, "ga wannan na manta" tacetare da miƙa mai hanky, kai hannu yayi ze amsa ta janye da sauri tare da faɗin "Uncle se kaamsakuma! Ba zaka bar mun ba?" Ta idda maganan kaman zata saki kuka, murmushi ya saki taredamatsawa kusa da ita a natse.... "Cike da ɗinbin kulawa ya riƙo hannunta ya ɗago a hankali ya sumbata se da ya ɗau daƙiƙuyaɗago kai tare da faɗin "be careful with your medicine" yayi maganan a hankali, jinjina kai tayi tare da faɗin "in sha Allah" hitting ɗin saman kumatun ta yayi a natse tare da sakin murmushi yawuce a natse ya nufi up stairs, bin shi suka yi da ido cike da tausayawa, yana gab da ɓacewaganinsu ya juyo a natse tare da faɗin "Ibrahim ka tabbata ta tashi kafin ka dawo" jinjina kai Ibrahim yayi duk da be so hakan ba, wuce wa yayi ba tare da ya kuma juyowa ba, yana ɓacewaganinta ta ja akwatin ta nufi ƙofa hawayen da take ta dannewa zuwan su suka biyo kuncinta, "bi ta Ibrahim" Hajiya tace murya na rawa, juyawa yayi ya dafa mata baya a mugun zafafe.... Wuce ta yayi da sauri ya wuce inda mota yake jawowa yayi ya fito da shi tare da fakawa nesadaita, sallaman ma'aikatan wajen tayi a natse hawayen nan kuwa ya kasa tsayawa duk da murmushin da take ta sakin musu, haka suka yi ta amsawa jikkuna a mace cike da kewa.... A guje Jabir ya dafa mai baya, kai tsaye balcony ya wuce, yana isa ya tadda shi tsaye ƙyamidonshi akan Insu da ta nufi motar da Ibrahim ya faka, murmushin takaici ya saki tare da faɗin"banzata zaka iya ɗaukan wuƙa da hannunka ka daɓawa kan ka ba, se gashi ka aikata da kanka, amma kayi matuƙar burgeni" ya idda maganan cike da ɓacin zuciya, guntun murmurshi yasaki ba tare da ya kauda ido daga kanta ba, "kasan abinda ka aikata kuwa! In baka sani ba bari infaɗamaka, tarwatsa rayuwarka kayi, cutuwa zaka yi fiye da tunaninka in baka sani ba!" Ya iddamaganan da ƙarfi, "na sani" yace a dake, "wow da abin mamaki ka ke kasan zaka cutu sannankaaikata aikin yarinta, in ita yarinya ce kai yaro ne! In ita ta kasa hangen abinda ze faru a gabakai ka kasa hange ne!" Juyowa yayi cike da karaya tare da faɗin "na hango komai Jabir na hango, sedai hakan ba ze hanani hangen na ta mafutan ba" "ita ma shirme take, ƙuruciya ne ya hanatafahimtar me take shirin yi wa kanta, ƙwayan idonta be bayyana komai se tsan-tsan ƙaunar datake maka, na lura da hakan ba tun yau ba, SSB Insu kai take so kaine kaɗai a zuciyarta, kainaƙwarin gwiwarta, kaine farin cikinta, akwai dalilin da yasa ta aikata haka, imma tana sonfahimtar abinda ba ta sani ba, imma tana son nema maka farin ciki, cikin biyu akwai ɗaya, sedai abinda ba ta sani ba ka kamu da sonta fiye da tunaninta, lokaci be ƙure maka ba, ka je ka dakatarda ita, ka faɗa mata abinda take son sani, ka faɗa mata ta tsaya a gefenka ita ce rayuwarka, kamaimaita mata kalamanka" ya idda maganan a ruɗe saboda ƙarisawa kusa da motan da Insutayi, guntun murmurshi ya saki tare da faɗin.... "Ruɗun yarinta ne kawai ba wani abu ba, ba ni take buƙata ba, na mata girma Jabir matashi takebuƙata wanda ze kula da ita fiye da yanda zan kula da ita, nan da wani lokaci zata manta komai, zata fuskanci rayuwarta" ya idda maganan a hankali saboda shigewa motan da tayi ta rufeIbrahim ya ja, "kai kuma me ke damunka tunda ita ruɗun yarinta ne?" Jabir yace a dake, idonshi ƙyam akan shi, guntun murmurshi ya saki tare da juyawa dan barin wajen, "wani lokaci zakaɗauka kana dannewa?" Yace ba tare da ya motsa daga inda yake ba, "tsayin rayuwa" yaceadaketare da ɗaga ƙafa ya bar wajen, girgiza kai Jabir yayi tare da faɗin "Ya Rahimagajinka bawankake nema" ya idda maganan tare da guntsan numfashi ya fesar da ƙarfi tare da saka hannunshi yashafi kanshi ya gangaro saman fuskan shi ya damƙe da ƙarfi.... Suna hawa saman titi ta tattare jiki waje guda ta saka kai a tsakanin gwuwoyinta ta fashedaƙaƙƙarfan kuka, kuka take me taɓa zuciyan me sauraren, wanda ke fitowa daga ƙasan zuciyanta, duk da kukan da take na dukanshi amma ko kallon gefen da take be yi ba, tsula gudu kawai yakekamar me shirin barin gari, be samu taka burki ba se da ya isa parking space ɗin dake cikinairport, ɗago kai tayi a hankali saboda tsayawan da taji yayi, bin wajen tayi da ido, ganinsunƙariso ya sata goge hawaye tare da buɗe baki da zumman magana "fita" yace a dake ba taredaya kalleta ba, murmushi ta saki tare da jan hanci ta zare belt ɗin jikinta ta buɗe ƙofan a hankali ta sauka, sakkowa yayi ya buɗe booth ya sakko mata da akwati ya ajiye mata, "kayi haƙuri, nayi hakan ne dan sama mai farin ciki, zamana kusa da shi ba abinda ze haifar mai se rashin sakewa" tayi maganan murya na rawa, wani wawan murmurshi me cike da ɗin bin takaici ya saki taredafaɗin "I see, zeyi farin ciki sosai kuwa" jinjina kai tayi ta ja a kwatin a hankali ta nufi ciki bataredata damu da hawayen da suke tsere a saman fuskanta ba, juyawa yayi a hankali jiki a sanyayeyanufi mota ringing ɗin da wayan shi ya ɗauka ya sa shi saurin dakatawa ya zaro, ganin me kirayasa shi saurin ɗagawa ya kara a kunni.... "Kun isa?" Yace a dake, "eh ta shige ciki" "kar ka baro wajen se jirginsu ya tashi, 11 za sutashi" jinjina kai yayi tare da faɗin "to a raunane, murmushi ya saki wanda ya jiyo sautinshi ras yazarewayan ya katse kiran, bazama fuskanta dake cikin hoton ta ita da Anty ido yayi kamar ne nemanwani abu, murmushi ya saki tare da lumshe ido, a sukunance hawayen da suka cika idonsukagangaro, "na daɗe da fahimtar ba Insiyyat ka so ba Insiyyah ka so, ruɗun shaƙuwa ne ya sakukeikirarin san juna kai sa Insiyyat, meyasa ka barta ta tafi!" Hajiya tace cike da damuwa, "umurninmahaifiyarta ta zo cikawa ta cika wani zama ya rage mata anan kuma?" Yayi maganan a raunaneidon shi akanta.... Girgiza kai tayi tare da faɗin "tana sonka" "ba ta fahimci me take so ba Hajiya" yace a hankali, "kana da daman tsaidata dan fahimtar da ita abinda take so" murmushi ya saki tare da faɗin"tadaɗe da cire tsammani, ta ba wa wani dama, kar san zuciya ya samu tauye mata haƙƙi, mumakowa adalci ko da zamu ƙare ba komai, gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah" yana kai nanyaraɓeta ya nufi ɗakin shi, "kaifa?" Tace murya a raunane, "zan jure kamar dai haka" yace taredashigewa ciki da sauri, goge hawaye tayi jiki a sanyaye ta juya ta sauka down stairs.... Yana shiga ya rufe ƙofan a hankali ya jingina da jikin ƙofar tare da lumshe ido, tsere hawayesukafara a saman fuskan, shafo hawayen da hannun dama yayi ya buɗe ido a hankali ya kallah, murmushi ya saki me tarin ma'anoni tare da faɗin "ki kasance cikin farin ciki, ba zan jure ganinwaƴan nan na tsere a saman fuskan ki ba" yana kai nan ya zame ƙasa jiki na ɓari, ƙudundunejikinshi yayi waje ɗaya saboda wani sanyi da ya kawo mai ziyaran bazata lokaci guda, kafin wucewanwasu daƙiƙu ya fice daga hayyacin shi banda sakin numfashi me zafi babu abinda yake, kwanciyayayi a saman tiles ɗin yana jawo addu'o'in da suka zo bakin shi tare da fizgo numfashi da ƙyar, awannan yanayin Alhaji Jamil da ya zo magana da shi ya taddashi.... Tana shiga wajen jira ta tadda

Chapter 57 of 109