An dauko wannan littafi daga shafin https://thausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://thausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://thausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://thausanovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.thausanovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
🫀MUGUN TSOKA 🫀
{🫀TA'ARE KALLUƊE}
[Muscle Cramp🫀]
) عضلة سيئة (
🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
written and Created ~~~~~~~~~~~~~~ ِبسم الله الرحمن الرحيم
By
Yardajjiya👩 💻
Page. One
Zaune wata matashiyar budurwa me kimanin shekaru 22 da haihuwa take a saman cabinet
hannu riƙe da waya tana daƙila tana sakin murmushi, murmushi wacce ke tsaye gefen gas tasaki
tare da faɗin "Anty Farisat me zan saka yanzu?" Ɗago dara-daran idanunta wacce ke aikindaƙilar wayan tayi tare da zube mata su, karya kai tayi tare da faɗin "kai Sa'adatu yanzusenafaɗa miki me za ki sa? Tare da dake fa muka gani" Farisat tace cike da mamaki, murmurshi
Sa'adatu ta saki tare da faɗin "wallahi ban riƙe ba Anty Farisat" sakkowa daga inda take zaunetayi tare da jan kujera ta isa kusa da ita tare da faɗin "to zo mu ga me za'a sa a gaban, danni mana manta" dariya Sa'adatu ta saki tare da maida hankalinta ga wayan da Farisat ke dannawa....
Tura ƙofan da take tsaye a gabanshi wata matashiyar budurwa wacce ba zata gaza 18 ba tayi
tare da shiga ɗakin baki ɗauke da sallama, juyowa wata kyakykyawan matashiyar dattijuwawacce zata iya kai shekara 40 da haihuwa tayi fuska ɗauke da murmushi tare da faɗin "Yasminkin shirya?" Murmushi wacce aka kira da Yasmin tayi tare da faɗin "eh Anty" "to miƙo minhijabi
na mu tafi ni ma na gama kimtsawa" tace tare da miƙewa da ƙyar saboda cikin da take ɗaukedashi, jinjina kai Yasmin tayi ta wuce gefen da wedrobe yake da sauri ta buɗe, tana ɗakkowatarufeta dawo a natse ta miƙa mata, murmushi ta saki tare da faɗin "Insu ta fito?" "Na barta tanashiryawa" Yasmin tace da girmamawa, "to muje dan mu dawo da wuri kafin Yaya ya dawo" jinjinamata kai Yasmin tayi ta nufi ficewa Anty ta dafa mata baya a hankali.... Gyara zaman madai-daicin rigar da ke jikinta wata matashiyar budurwa ƴar kimanin shekaru16da haihuwa tayi ta juya gefe ta ɗakko baƙin abaya ta zura, veil ɗin shi ta naɗa a saman ka, kallonmirror dake gabanta tayi tare da gyara zaman veil ɗin, ganin ya zauna yanda take so ya satasakin wani nagartaccen murmushi, ma sha Allah, ingantaccen wushiryan da ubangijinta yamataya bayyana gunun burgewa, juya ido tayi tare da farrr da shi, ɓata fuska tayi tare da fara dube- duba hango abinda take nema ya sata sakin murmurshi tare da ɗauka ta maƙala a hujindakegefen hancinta na dama, ƙifta ido ɗaya tayi tare da faɗin "wow kwalliya ya kammala" tayi
maganan cikin zazzaƙan muryanta me taushi da zaƙi....
Tsayawa Anty tayi a ƙofar kitchen ta ɗaga murya tare da faɗin "Yasmin ce mata ta fito" jinjinakai
Yasmin tayi ta wuce, kallon Farisat da Sa'adatu dake ta ƙoƙarin haɗa jelof ɗin Canada tayi taredasakin murmurshi, "yau dai da alama zamu ci daɗi" Anty tace tare da sakin murmushi, ɗagokai
suka yi a tare, tare da sakin mata murmushi a tare, murmushi ita ma ta sakin musu idontanayawo akan su, "Anty har kin fito?" Farisat tace tare da kafeta da ido "Eh so nake in dawo kafinYaya ya dawo" jinjina kai tayi tare da faɗin "ko in zo muje tare?" "No sweetheart ba zan daɗebani
ma da izinin ubangiji" jinjina kai tayi tare da takowa a natse ta ƙariso kusa da ita, tare da faɗin"Anty kaman bakyada lafiya ko?" Dariya dattijuwar da ta ƙariso wajen riƙe da kuloli ma suɗaukan ido tayi tare da faɗin "ban da abin ki Hajiya Farisat yaushe ita kuma za tayi lafiya? Ai seranar da Ubangiji ya rabata da cikin nan lafiya" ɓata fuska Farisat tayi tare da faɗin "zamuɓatada kai Baba Mari" tayi maganan tare da kallon cikin da ke jikin Anty, murmushi Anty ta saki tareda girgiza kai....
Tura ƙofan tayi a natse juyowa wacce ke gaban mirror tayi tare da baza mata wala-walanidanunta masu ɗaukan hankali, da mamaki Yasmin ta bi ta da ido tare da faɗin "wannankwalliyan duk na zuwa ina ne!" Farr tayi da ido tare da faɗin "na my Dr" dariya Yasmin ta saki
tare da faɗin "Anty ta fito" "okay" tace tare da ɗaukan jakan baya dake gefe ta goya ta dumfari
ƙofa, ficewa Yasmin dake gaba tayi ta dafa mata baya, kai tsaye bakin kitchen inda suka hangoAnty tsaye ita da Farisat suka yi, suna isa Anty ta saki murmushi ganin yanda tayi kyau taredafaɗin "Insu irin wannan ado haka kamar za ki tafi gasar kyau" nagartaccen murmushi ta saki tareda ƙarisawa kusa da ita ta zaro waya a aljihun dogon wandon jikinta ta ɗaga musu selfie, murmurshi Anty ta saki tare da faɗin "munyi kyau ko?" "Sosai Anty ke fa da photo copy ɗinki ceai dole ku yi kyau" Yasmin tace tare da sakin murmushi, matsowa Farisat tayi tare da faɗin"ɗagamana wani" ba musu ta ɗaga musu fuskokin su cike da murmushi, "to ya isa haka ku mujeko, kekuma koma kin bar Sa'adatu da aiki" "dama ba ita ke yi ba, tunda naga ta dage da se Sa'adatutakalli girkin nan na san yau se Sa'adatu tace wayyo Allah ni dan watan shan wahalar ta neyatsaya" Yasmin tace tare da sakin dariya, dariya Anty ta saki tare da faɗin "kar ki ce komai Farisatƙyale Yasmin neman zance take" "ba abinda zance mata ai Anty se kun dawo ki kula da kanki
please, kuma ku kula" ta idda maganan tare da hararan su ta koma ciki,....
Da murmushi a saman fuskokin su suka nufi farfadan gidan, ya subhanallah, kantamemengidane wanda ya samu nagartaccen gini, da sauri Insu ta nufi inda take ajiye keken hawanta, murmushi dattijon dake zaune cikin amintaccen shiga ya saki tare da faɗin "Hajiya yau daitaza'afita?" Murmushi ta saki tare da faɗin "in sha Allah" tana kai nan taja gefe ya ciro mata gangaroshi tayi har bakin motan da driver ya isa tayi, da sauri ya buɗe booth ya amsa ya saka, "wai dashi
za ki!" Yasmin tace da mamaki, "eh mana" tace tare da buɗe wa Anty baya, "a'a mu taka zuwabakin gate tukun" tace tare da kallon ta, kallo me cike da nazari ta mata tare da faɗin "Antyki nalafiya kuwa!" Murmushi Anty ta saki tare da faɗin "yau ku kan lafiyan ku kuwa? Ko waccesetamun wannan tambayan" murmushi Yasmin ta saki tare da faɗin "kaman kin yi sanyi ne Anty" "toba abinda ke damuna, ku muje" tace tare da kallon su, ba musu suka fara takawa, kallondriver
tayi tare da faɗin "Ibrahim mu haɗu a gate" jinjina kai yayi cike da girmamawa tare da faɗin"toHajiya" yana kai nan ya shige, kallon Dattijon dake gefe tayi tare da faɗin "Baba Kalla bari muleƙa asibiti" tashi yayi da sauri tare da faɗin "to Hajiya Allah ya ƙaro lafiya da nisan kwanamealbarka" murmurshi ta saki tare da faɗin "amen Baba Kalla" suna kai nan suka fice daga gateɗingidan da ya buɗe....
Tafiya suke a natse suna taɓa hira murmurshi yalwace a saman fuskokin su, da sauri wani
matashi dake zaune a gefe shida abokan shi ya taso tare da faɗin "Anty ba dai masu kankwakwan nan suka jawo ki a ƙafa ba" yayi maganan tare da nuna Yasmin da Insu, murmurshi tasaki tare da faɗin "a'a ni na jawo su Salman, yau ba ka fita aiki ba ne?" "Na je ban jima da dawowaba" jinjina kai tayi tare da faɗin "bari mu leƙa asibiti" "waye ba lafiya!" Yace tare da zare ido, murmushi ta saki tare da faɗin "a'a lafiya lau, ba wani matsala" "oh to ma sha Allah shinewannan ta ci ado haka kamar me zuwa gasar kyawawa!" yayi maganan tare da kallon Insu, dariyaYasmin ta ƙyalƙyace da shi tare da faɗin "za taje ganin Dr Hisham ne" harara ya banka matatareda faɗin "kan ki na rawa ko?" Murmushi Anty ta saki tare da faɗin "ƙyale Yasmin Salmannemanmagana take" "to Anty ko in zo muje ne" "a'a je ka yi zamanka, Ibrahim na jiran mu a bakingate"
"okay to a dawo lafiya" yace cike da kulawa, murmushi ta saki tare da wuce wa, jawo hijabinYasmin dake niyyan bin bayan Anty yayi tare da faɗin "Farisat na gida ne?" Jinjina mai kai tayi
tare da sakin murmurshi, "ina wayanta yake?" Yace idon shi akan ta, "yana hannunta" tacetareda saurin wuce wa, cike da nazari ya bi ta da ido tare da mai-maita kalman yana hannunta, kenan
ta ga kiran da ya mata ta ƙi ɗauka, saurin kauda wannan batun yayi tare da komawa inda yataso.... Haka suka yi ta tafi a natse, duk inda suka haɗu da mutane se sun gaishe su a girmame, sunaisabakin gate suka gaisa da masu tsaron gate ɗin shiga anguwan suka haye mota Ibrahimyajasusukai asibiti, suna isa suka sakko suka shige ciki, tura ƙofan office ɗin Dr HishamInsu tayi taredafaɗin "my Dr" murmushi Dr Hisham dake sallaman patient yayi tare da faɗin "my patient" ɓatafuska tayi tare da juyowa ta kalli Anty" murmushi ta saki tare da faɗin "rabu da shi, ke ba patientɗin shi ba ne, murmushi ta saki tare da kallon shi, fuska cike da murmushi yace "wato kwanabiyukin yi lafiya shine ki ke cewa ke ba patient ɗina bace ko? Zamu haɗu nan kusa" zare ido tayi tareda faɗin "Anty so yake ku ƙara kawoni yayi ta zanɓaɗamin allura da ruwa" dariyan yanda tayi
maganan Anty ta saki tare da faɗin "rabu da shi" murmushi ya saki tare da faɗin "ki na shanmagani akan time?" Jinjina mai kai tayi tare da faɗin "yes sir" "good girl" yace tare da kallonYasmin dake ta sakin murmushi, "Yasmin ya yau ɗin?" Yace a natse, "Alhamdulillah Dr" taceanatse, "bismillah Anty" yace tare da bata hanya, "Anty bari in wuce in kun gama ki kira ni, innarigaku gamawa zan biyo tanan mu tafi, in kuma kun rigan shikenan, amma ku sanar min" jinjinamata kai Anty tayi da kulawa, "okay bye Anty, my Dr se mun yi waya" ta idda maganan taredasaurin juyawa, har ta kai ƙofa ta juyo da sauri ta dawo ta rungume Anty ta kai mata sumbaakumatu tare da faɗin "Allah ya ba ki lafiya me inganci Anty" tana kai nan ta juya ta bar wajendasauri, kai tsaye booth ta nufa, da sauri Ibrahim ya taso ya buɗe ya ciro mata, murmushi ta sakinmai tare da faɗin "Ibrahim za kayi albaraka" tana kai nan ta ɗane ta ja tabar wajen, murmurshi
Ibrahim da ya bita da ido ya saki tare da rufe booth ɗin ya samu waje ya zauna....
Tsaye yake a bakin katafaren kofar taro, banda kallan hanya ba abinda yake, tsayin mintunayaɗauka yana ƙarewa wayan dake riƙe a hannun shi kallo, shahada yayi ya danna number, ringingyayi har ya katse ba'a ɗaga ba, shiga whatsapp yayi kai tsaye, yaje saman number da ya rubuta(ƙanwata) ya fara rubuta nata saƙo, yana tabbatar da tafiyan saƙon ya ɗago kai tare da sakinnumfashi, fitowa daga ɗakin taron wani matashin saurayi wanda ba ze fi shi a shekaru ba yayi
tare da faɗin "yaya ta taso?" "Ina jiran jin abinda zata ce ne" yace tare da kafe hanya da ido.....
Duba wayanta da taji shigowan saƙo tayi ganin number da ta rubuta (Yayana) yasata buɗewadasauri, ganin inda saƙon shi ya dosa ya sata saurin maida mai da amsa ta maida wayan, kallonAnty tayi tare da faɗin "Anty bari in je wajen nan kafin ku gama da Dr Hisham" jinjina matakai
Anty tayi tare da faɗin "ki kula da kan ki, ki amshi motan shi kuma Ibrahimya shigo ciki" "to" tacecike da farin ciki ta juya ta fice.....
Saurin ɗago wayan dake hannun shi yayi ya buɗe kai tsaye ya ga saƙonta, karantawa yayi yaɗago kai tare da faɗin "gata nan" jinjina mai kai na kusa da shi yayi tare da faɗin "alright" jinjinakai yayi tare da gyara tsayuwa.....
Tana ficewa Anty da ke jiran ficewanta ta rumtse ido tare da cije leɓen ƙasa da haƙwarantanasama, da sauri Dr Hisham ya ƙarisa kusa da ita tare da faɗin "Hajiya!" Ganin yanda jikinta yaɗaurawa lokaci guda ya sa shi ɗaukan wayan dake kan table ɗin gaban shi ya danna kira a na ɗagawayace "ku zo office yanzu" yana kai nan ya ajiye tare da faɗin "sannu Hajiya menene matsalan!" Murmushi ta saki tare da ɗago rinannun idanun da lokaci guda suka canza kalla ta kalle shi, cikeda dauriya tace "Dr ba na da lafiya" tayi maganan a harharɗe tare da duƙewa, da sauri ya
tallafota tare da bubbuga saman kumatunta dan ganin tana lumshe ido, knocked ɗin ƙofanakayi da ɗan sauti, "come in" yace da ɗan ƙarfi, turo ƙofan nurse ɗin dake gaba tayi tare da shigowa, ganin halin da Anty ke ciki ya sata juyawa da sauri ta ma sauran da suke tsaye a bakin ƙofamagana ta komo ciki da sauri....
Temaka musu yayi suka sata a saman gadon majinyata, bin su yayi a rikice tare da ƙoƙarinzarowayanshi dake aljihu, girgiza mai kai tayi tare da faɗin "kar ka kira kowa, ka bar su, ko wacceyautana shirin cika burinta ne" da mamaki ya bi ta da ido, dan se a lokacin Yasmin da ta fita tafaɗomai a zuciya, ana shigar da ita ɗakin ya juya da sauri ya maida wayan a aljihu ya fice da sauri, dama so yake ya kira Yaya....
Tana fita ta nufi inda ta hangi Ibrahim waya kare a kunnin shi, saukewa yayi da sauri ganintanadumfaroshi, murmushi ta sakin mai tare da faɗin "Anty tace ka bani key sannan ka shiga ciki kajirata" murmushi ya saki tare da faɗin "to" yana kai nan ya zaro makullin ya bata ya ja ya tsayaagefe, buɗe motan tayi ta shige ta ajiye wayanta a gefe, tun daga nesa Dr Hishamda ya fitoarikice ke ƙwala mata kira, daga ita har Ibrahim ba wanda ya ankara, key ta ma motan tanaƙoƙarin juyawa ya iso wajen tare da dukan glass ɗin da ƙarfi, da sauri Ibrahimya ƙarisa taredatambayan shi lafiya, da mamaki ta taka burki tare da ɗago kai ta kalleshi, alamu ya mata datafito, da sauri ta ɓalle murfin kusa da ita ta ɗau wayanta ta fito, "menene!" Tace a tsorace, "Hajiyajikin ya birkice" zare ido tayi tare da faɗin "me ku ka mata! Yanzu na barota lafiya fa" tayi
maganan a rikice tare da nufar ciki, dafa mata baya Dr Hisham da ya kasa ce mata komai shi daIbrahim suka yi...
Kai tsaye office ɗin Dr Hisham ta nufa, da sauri yace "tana labour room" a guje tayi wajen, tanazuwa ta tsaya a bakin ƙofan saboda cin karo da Anty da Nurses ke temaka mata akan tayi nishi
tayi, kasantuwar ƙofar na glass ana iya hango abinda ke faruwa ta ciki, zare ido tayi tare dajuyawa ta sauri ta fara laluben wayanta, "waya na" tace tare da kallon Ibrahim, miƙa matayayi
jiki a mace, saboda lokacin da Dr Hisham ya faɗa mata halin da Anty ke ciki yarda wayantayi tawuce, da sauri ta amsa ta danna number da ta rubuta(Yaya) ringing biyu ya ɗauka, a rikicetace"Yaya ka zo Anty na labour" ba ta jira amsan da ze ba ta ba ta katse ta danna number da tarubuta(Anty Farisat) se da ya kusa tsinkewa ta ɗaga, ko kafin tace wani abu, ta tari numfashinta dafaɗin "Anty Farisat Anty na labour" ta idda maganan tare da fashewa da kuka, katse wayanta
can Farisat tayi, ganin ta katse yasata maida akalan kiran ga number da ta rubuta (Yaya Sadam)
yana ɗagawa ta kora mai bayani, shima katsewa yayi ta can ba tare da yace mata komai ba....
Saurin ƙarisawa inda take Ibrahim yayi tare da faɗin "Hajiya Yasmin ki kwantar da hankalinki insha Allah zata sauka lafiya" jinjina mai kai tayi hawaye na tsere a saman kumatunta tare dafaɗin"in sha Allah Ibrahim" tana kai nan ta danna number da ta rubuta (Insu) tare da alamunluv, ringing yayi har har ya katse ba ta ɗaga ba, ƙara kira tayi nan ma shiru, tana ƙoƙarin kirannaukuwani matashin dattijo wanda ze iya kai 47 ya faɗo a rikice, yarda wayan tayi ta nufeshi a guje, tana isa ta faɗa jikin shi tare da sakin kuka, "heee daina mana" yace tare da ɗagota ya farasharemata hawaye, "Yaya Anty" tace cikin rishin kuka, "komai ze tafi dai-dai in sha Allah" yace taredashafa kanta, jinjina kai tayi tare da faɗin "in sha Allah" haka suka cigaba da jiran tsammani, basusamu cikakkun mintina 20 ba Farisat da Sadam suka faɗo a rikice, Farisat ko veil babu, a gujetayi inda ta hangi su Yaya zata fara kuka ya mata alamun kar tayi da ido ya riƙota ya rungume, "Yaya ina Antyn!" Sadam yace tare da kallon shi, "suna ciki" yace tare da nuna mai ɗakin, nemanwaje yayi ya zauna banda tsinkewa ba abinda zuciyan shi take, "mu mata addu'a" Ibrahimdadukna shi jikin yayi sanyi yace a hankali, jinjina mai kai suka yi suka fara jawo addu'o'i.... Da sauri ta sauka daga saman keken ta ajiyeta a gefen inda motoci da mashina ke fake ta wuceƙofar wajen a guje, tana isa bakin ƙofar da wasu majiya ƙarfi ke tsaye ta ciro pass a aljihunwandon jikinta ta miƙa musu, amsa ɗaya daga cikin su yayi, jinjina mata kai yayi ya bata taamsata wuce da sauri ta tura madaidaicin ƙofar, tana shiga sauti ya ratsa kunnuwanta, da sauri tanufi
inda ta hango jerin matasan dake sanye da kaya iri ɗaya, cikin azama matashiyar da ke tsayeagefe ta nufota, tana isowa tace "Insu me ya tsaidaki haka!" Shagwaɓe fuska tayi tare da faɗin"wallahi Anty muka raka hospital" "ba ta da lafiya!" Tace a ɗan rikice, murmushi ta saki taredafaɗin "no lafiyanta lau taje ganin my Dr ne" murmurshi matashiyar budurwan ta saki taredafaɗin "kin kyauta, saura kaɗan Teacher ya saki ihu" dariya ta saki tare da juyawa da nufinwucewa, cin karo tayi da matashin saurayi tsaye yana bin ta da ido, zare ido tayi tare da kallonmatashiyar dake gefenta, alamun me ya tsaida ita ya mata da hannu, kama kunnuwa tayi dahannayenta tare da shagwaɓe fuska tace "sorry Teacher" harara ya balla mata tare da mataalamun ta wuce, da sauri ta wuce ta shige ɗakin da aka ba su, tana shiga ta fara ɓalle maɓallinabayan jikinta, wuce wa matashiyar budurwan tayi ta ɗakko mata kayan da zata saka, tanaajiye
abayan, ta miƙa mata tare da faɗin "muna ta kiran ki" "wayan na silent ne" tace tare da zurakayan, banda walwali ba abinda suke da ɗaukan ido, baby hijab marron ta saka kalan kayantareda faɗin "minti nawa ya rage mu shiga?" "Sun shiga tun ɗazu" tace tare da maƙalamata makilfonɗin dake haɗe da ji sauti, "oh Allah" tace tare da zura takalmi ta fice da sauri, dafa mata bayatayi
suna fita suka tadda Teacher tsaye da alamun jiran su yake, "ki bi ta nan akwai igiya se ki saukalokacin da ya dace" jinjina mai kai tayi tare da wucewa da sauri ta haye inda ya nuna mata, tanaisa ta kama igiyan tare da kallon yanda suke rawan, ana canza launin fitillu ta dira cikinnatasalon, ihu ƴan kallo suka saka tare da fara ambatan sunanta, "Insu! Insu!! Insu!!!" Saka
hannayenta a baki tayi ta sumbata ta ciro ta watsa musu tare da fara taka rawa cikin binsautinƙidan da dukkanin wanin iyawanta...
Fitowa Dr Hisham yayi jiki a mace, ganin sun zuba mai ido ya sa shi nufar office ɗin shi da sauri, fitowa wata nurse tayi riƙe da takarda a hannu tare da faɗin "Amina Abdussamad" ganinbawanda ya nuna alamun ya fahimci abinda take cewa ya sata mai-maita sunan da ƙarfi, da sauri
suka mimmiƙe tare da zuba mata ido, "I'm sorry she was gone" zare ido suka yi gaba ɗayansutare da bin bakinta da ido, tangal-tangal Yaya yayi Ibrahim da kalaman suka dukanwa
ƙwaƙwalwa da zuciya yayi saurin taro shi, ko kafin ya gama taroshi Farisat da Yasmin sunzube, duƙewa Sadam yayi akan su tare da fashewa da razanannen kuka, banda salati ba abinda
Ibrahim ke yi, iya tashin hankali ya ganta da idanun shi a yau, da sauri Nurses suka ƙarisotaredatemaka musu....
Tsalle tayi ta riƙo igiyan dake gefe tare da fara juyi tana watsa musu sumba da hannu, bandaihuba abinda jama'an dake cike a wajen ke yi, sauka tayi tare da sakin numfarfashi me haɗe damurmushi, dawo da hasken wajen dai-dai a kayi tare da sallaman su suka fice, miƙewa waccezata faɗi result tayi fuska faɗaɗe da murmushi tare da kiran na uku, a guje suka shiga cikedafarin ciki, saka ma wanda ya jagoranci rawan ƙarfen azurfa tayi tare da numa musu gefe sukatsaya, kiran na biyu ta yi suka shiga suma aka sa musu na su aka nuna musu wajen tsayuwasukatsaya, kallon group biyu da ya rage tayi fuska faɗaɗe da fara'a, ganin yanda duk suka zubamataido ya sata faɗin "in faɗi na ɗaya ko in kar in faɗa?" Ihu jama'an wajen suka saki tare da faɗin"afaɗa!" "Write dancers" tace da ƙarfi, ihu su Insu suka saki tare da shigewa da gudu, saka mataƙarfen azurfa tayi tare da ɗakko kofu ta miƙa musu, amsa sukayi cike da farin ciki, tare dasakin
ihu, miƙa ma Insu hannu tayi suka yi musabaha tare da faɗin "congrat" jinjina mata kai tayi tareda ɗaga kofin sama, nan aka fara zuba musu hotuna, tattarosu Teacher yayi suka nufi ɗakindaaka ba su....
Suna shiga ko wacce ta fara canza kaya zuwa kayanta da ta zo da shi a jiki, "Insu wai meyasaduklokacin da ake neman ki ba za'a taɓa samun ki ba ne?" Teacher yace rai ɓace, "sorry Teacher, tana silent ne banji ba ina tuƙi time ɗin" hararanta yayi tare da faɗin "Ziyada ki dinga matafaɗa" murmushi matashiyar budurwan da ta tarbota ɗazu ta saki tare da faɗin "in sha Allah Teacher"....
Saka gawar Nurses suka yi a bayan ambulance tare da sakkowa, saurin shiga Farisat da tundasuka farfaɗo hawaye be daina zuba a saman fuskan
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 109