Umma ta bashi labarin abinda ya faru tsakaninta da Hafsat da kuma yadda ta fita kai mata saƙo. Tabbas da ya tsaya a lokacin da ransa ta ɓaci ya saurari Umma da sun nemi mafita. Amma lokacin gaba ɗaya ransa ya gama ɓaci baya sauraren kowa balle ya fahimci gaskiyar lamari .
Amma gaba ɗaya shi ya ɓata komai ga shi yanzu basu da labarin halin da take ciki da kuma inda take. Ga saurayin da ke son aurenta Munnir tunda ya dawo yake sintiri da ya ji cewa ta ɓata shima ya shiga tashin hankali. Kusan kullum sai ta zo gidan akan cewa ko anji labarin inda take ko ta kira waya. Kullun amsa ɗaya suke bashi shine ba labarinta har yanzu.
Ya gama karaɗe gari bai ganta ba shima ta zubawa sarautar Allah idanu.
Kullun cikin addu'a suke Allah ya bayyana masu ita ta dawo da ita gida.
A cikin daren ne aka yi mata aiki inda aka ciro ɗa namiji fari sol kyakkyawan gaske kuwa kamar su ɗaya da mahaifiyarsa.
Da asuba bayan an idar da sallar asuba ne Ajmal daga masallaci ya nufi wajen motarsa, wayoyinsa ya dauko inda ya ci karo da missed call barkatai.
Shiga cikin motar ya yi inda ya dannawa Ammynsa kira.
Bugu ɗaya ta ɗaga kamar tana jira. Dama akan sallaya take tana azkar wayar na gefenta.
"Farin cikina lafiya lau kake kuwa me ya sa baka dawo gida ba kuma baka kira ka sanar ba? Duk hankalinsu a tashe yake me ke faruwa?"
Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa
"Umma da sauƙin."
Ban gane da sauƙi ba bayan meeting ɗinku ma baka samu halarta ba, shugaban jam'iyyar ku ne yake tabbatar wa Dad ɗinka suma basu ganka ba ana ta kiran waya baka ɗaga ba suma hankalinsu ya tashi."
"Akan hanyar zuwa meeting ɗin ne na kaɗe wata mata ɗauke da tsohon ciki."
Salati Ammy ta saka tare da cewa
"Ina fatan daga ita har dan ba abinda ya same su ko?"
"Ina saka rana haka, an dai yi nasarar ceto rayuwar yaron amma ita har yanzu dai bata farka ba."
"Wane asibitin kuke?"
"Sabon asibitin da na gina wanda na saka masa suna *BILMAL HOSPITAL* na kai ta."
"Okay na gane asibitin"
Daga nan ya katse ya kira shugaban jam'iyyar ta su saboda ya ga missed call ɗinsa da yawa.
Bugu biyu ya ɗaga inda suka gaisa ya masa bayanin abunda ya faru akan hanyarsa ta zuwa meeting, ya kuma tabbatar masa yana asibiti a nan ya kwana. Duk wadanda suka kira shi bai samu ɗagawa ba sai ya sanar da su accident da ya samu akan hanya.
Cikin ƙanƙanin lokaci labari ya zageye gari kasancewar sa mutum mai farin jini da yawan jama'a, wasu na cewa accident ya samu wasu na cewa matarsa ce ya kawo ta haihuwa.
Sakamakon lokacin da ta shigo asibitin ya ɗauko Amatullah daga cikin mota ne yana gudu da ita wasu sun ɗauki video ɗaya yake rike da ita yana gudu, nan aka fara turawa a social media Governor ya kai matarsa asibiti zata haihu, ga shi nan ɗauke da ita yana sauri dan a ceto rayuwarsa.
Wannan ko aikin wani ɗan adawar siyasa ne ya yaɗa wannan zancen. Yayin da kuma daga gefe wasu ke posting cewa ai wannan ba matarsa ba ce, domin sun san matarsa tazo neman ƙuriar su akan siyasar mijinta, har aka yi posting matarsa da take kamfen tana wayarwa mata kai akan mahimmancin katin zaɓen su.
To idan wacce ta taya shi kamfen matarsa ce to wannan kuma da ya kawo asibiti fa wace alaƙa ce a tsakaninsu?
Da safiyar Hajiya Bilkisu da Nasreen suka zo asibitin, Dad ɗinsa ma ya zo asibitin dan sun damu da abinda ya faru.
Abu kamar wasa sai ga zance ya zagaye ko ina musamman da aka tabbatar da cewa wannan ba matarsa ba ce, sai zancen ksruwarsa ya zagaye gari cewa ya jawo ksruwarsa za ta haifa masa ɗa yayin da wasu ke cewa dadironsa ce.
Suna office ɗin Doctor shi da ahalinsa wayarsa ta fara ruri ya ɗaga bayan ya duba shugaban jam'iyyar su ne ke kiransa.
"Ajmal ne nake gani ne wai ka aikata?"
Cikin rashin gane inda zancensa ya dosa ya ce,
"Ban gane ba fa."
"Ka ɗauki wayarki ya shiga yanar gizo ko ta ina zancenta ake."
Daga nan ya katse kiran, Ajamal ya shiga social media ya ci karo da tashin hankali, ga lokacin da ya ɗauko Amatullah daga mota ga kuma photon matarsa a gefe. Ana nuna cewa ga matarsa a gefe ita kuma wannan wace ce?
Kowa na tofa albarkacin bakinsu wasu na cewa ksruwarsa wasu dadironsa, wasu na cewa dama halinsa ne bin matan banza yanzu asiri da ya tono sama bai cancanci matsayin da yake nema ba a matsayinsa na fasiƙi.
Kowa da irin comments da yake a akai.
Wani jiri ne ya ji yana neman ɗaukarsa jingina ya yi da bangon office ɗin Doctor wayarsa ce ta faɗi ƙasa.
*Daga alƙalamin*✍️
Zainab Abdullahi KNT
(Maman Ihsan)
09065327995
08168611693
Love you oll😍😘
Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
🤦♀️ *ƳAR MAYE*🤦♀️
(_The drug abuser_)
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Dedicated to
*JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION*
*GARGAƊI*
Wannan littafin mallakar marubucirsa ce, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
*BISMILLAHI RAHMANI RAHIM*
Page2️⃣8️⃣&2️⃣9️⃣
Wani jiri ne ya ji yana neman ɗaukarsa, jingina ya yi da bangon office ɗin Doctor. Wayarsa ce ta faɗi ƙasa.
Gaba ɗaya hankalin su Ammy ne ya dawo kansa, tare da tambayarta abinda ke faruwa. Kasa magana ya yi illa kawai nuni da wayarsa da yake masu.
Nasreen ce ta ɗauki wayar ta duba abinda ke faruwa sannan ta miƙa wa su Dad. Dubawa suka yi sannan suka kalle shi. Ammy ce ta fara cewa .
"Kada wannan abun ya dame ka ko kaɗan, tunda ja shiga siyasa ba irin tuggu da ba za'a shirya maka ba, domin tana dan har kana takara kuskure kaɗan idan ka ya zai zama makama a wajen abokan adawarka ne. Laifi kaɗan idan ka yi za'a maida shi babba ne. Kai dai kawai ka kasance mai hakuri da juriya domin sune tushen samun nasara a rayuwa. Ko da wasa ka da ka bari su ga rauninka."
Haka ta cigaba da bashi ƙwarin guiwa har ya samu hankalinsa ya ɗan kwanta.
Ɓangaren Hafsat kuwa haka suka kwana a office ɗin N.D.G.L.E.A sun sha wuya sosai dan ba ƙaramin suka suka masu ba, musamman su mazan sun fi jin jiki sosai dan wani sai da haƙoransa suka fita. Hafsata ma ta sha duk sosai har fuskarta sai da ta kumbura. Kasancewar ta mace ce ya sa suka bata damar ta kira wani nata.
Bata waya suka yi ta saka lambar wayar Munnir ta kira shi.
Yana kwance yana barci kasancewar safiya ce, wayar tana ringing bai ɗaya d'aga ba, da ta sake kira sai ya katse kiran ba tare da sanin wa ke kiransa ba.
Ganin ba'a ɗaya ɗaga ba ya sa ɗaya daga cikin jami'an da ke wajen ya karɓi wayar tare da cewa ta koma ciki.
Kuka take sosai tana roƙonsu akan su sake bata damar kira, ba wanda ya saurare ta suka sake mai da ta ciki.
Kula take sosai da sosai dan a kwana ɗaya da ta yi ita kadai ta san irin wuyar da ta sha. Ga azabtuwa da duka sannan kuma ga rashin wuri mai kyau inda aka aje su ba za ta iya yin barci mai kyau ba.
Haka ta dinga kuka kamar ranta zai fita, ihunta ne yasa wani daga cikinkin jami'an ƙarasowa ya daka mata tsawa dole ta haɗiye sauran kukan nata.
Munnir kuwa ko da ya tashi daga barci ma ya g cewa Hafsat ke kiransa tsuki ya yi tare da jefer da wayar kan gado. Bathroom ya shiga don yin wanka.
Ɓangaren Ajmal kuwa abu ya wuce tunanin su, domin sai kiransa ake a waya ta ko ina, kuma ba akan komai ba sai akan abinda suka gani a yanar gizo. Kasancewar sa sanannen mutum ya sa labarin ya zagaye ko ina.
Cikin ƙanƙanin lokaci aka dinga tururuwar zuwa asibiti wasu na zuwa ne saboda sun ji an ce ya samu accident san su duba jikinsa suga halin da yake ciki, yayin da wasu kuma suna zuwa ne dan su tabbatar da gaskiyar lamari na cewa ba matarsa ya ɗauko ba ksruwarsa ce ko kuma dadironsa ce.
Abu kamar wasa sai ga 'yan jarida da ma'aikatan gidan rediyo da na gidan TV duk sun zo dan sanin haƙikanin gaskiyar lamarin abinda ke faruwa da Gwamnansu na gobe.
Wayoyinsa ake ta kira ba kakkautawa, duk wayoyin guda uku ake kira ba wacce ba ta ringing. Rasa wace kira zai amsa ya yi.
Ɗaya daga cikin wayoyin ne ya ɗauka a hannunsa tare da amsa kiran. Shugaban jam'iyyarsu ce da sakataren jam'iyar suka shigo asibitin, kasancewar asibitin na cike da jama'a ne ya sa suka tsaya daga can waje suna son sanin inda yake.
Ɗaya wayar ya yi tare da yin sallama
"Assalamu alaikum"
Shugaban jam'iyyar da ke daga bakin asibitin shi sa sakataren jam'iyar ne ya amsa sa
"Wa'alaikumus salam"
"Barka da safiya yallaɓai"
"Yauwa Barka dai Ajmal ya kake?"
"Alhamdulillahi"
"Kana cikin asibitin ne?"
"Eh ina ciki."
"To ko zamu iya ganinsa yanzu?"
"Ka yi hakuri gaskiya bana cikin yanayin da zan iya magana da kowa."
"Aiko ya zama dole ka yi magana da mutane domin asibitin nan a cike yake da mutane, hatta 'yan jarida duk sun taru suna son jin ta bakinka, dan ma an rufe ƙofar shiga ne ya sa basu sami shiga ba, hatta tarin jama'a da masoyanka sun halarci asibitin nan dan duba halin da kake ciki.
Katse wayar ya yi tare da nufar wajen window ya leƙa.
Zaro idanu waje ya yi cike mamakin ta ya zancen nan ya zagaye gari haka. Su Ammy da Dad har da Nasreen suka yaye abulayan windows dan ganin me yake gani.
Ba ƙaramin mamaki abin ya basu ba, Nasreen ta kalle shi ta ce,
"To me suke son sani ne?"
"Suna son jin me zan faɗa akan jita-jita dake yawo a gari."
A hankali Amatullah ta bude idanuta da suka mata nauyi, ta tuna lokacin da ta fito daga makarantar nan. Tafiya take cikin duhun dare ba tare da sanin ina ta dosa ba, wasu zafafan hawaye ne ke fita daga idanuwanta, kallon titsetsen cikin da ke jikinta ta yi, yayin da kukanta ya tsananta cikin baƙin ciki da nadamar faɗawarta harkar shaye-shaye, ta rintse idanuta tare da cije laɓɓanta. Ta faɗa duniyar tunanin tare da zancen zuci
'Na shiga uku na biyewa shawarwarin muguwar ƙawa, na yi nadamar saninki a rayuwata Hafsat, Allah ya wadaran halinki Hafsat sai Allah ya mani sakayya akank.'
Bata sake tuna komai ba sai farkawar ta ganta kwance a asibiti.
Ji ta yi a ƙarin cikin da ke jikinta,wata nurse ce zaune a gefenta ta sakar mata murmushi tare da nuna mata Baby da ke kwance akan gadon jarirai.
Komawa ya yi ya zauna wayoyinsa ake ta kira ba kakkautawa, da ya amsa wannan zai aje ya amsa wancan. Kafin ya gama magana wani kiran na sake shigowa. Gajiya ya yi dan haka ya kashe wayoyinsa gaba ɗaya, dan duk kiran da ake masa akan magana ɗaya ne.
Yanke shawar fita ya yi dan ya fuskanci jama'a.
'Yan jarida na matsowa da lasifika suna saitawa saitin bakinsa, yayin da ma'aikatan gidan TV ke hasko shi da babban video Camera dan ganinsa da maganar da zai yi.
Tamabayar da suka fara masa ita ce.
"Ranka ya daɗe shin da gaske ne matarsa aka ganka ɗauke da ita da ciki wai ɗanka ne ta haifa?"
Murmishin takaici ya yi tare da cewa
"Ku bari ta fito ku tambaye ta da kanku sai ta baku amsa."
Bayan wasu 'yan mintuna sai ga ta ta fito hannunta ɗauke da jariri, kanta a sunkuye. Sau kallo ta koma kanta.
Kallonta ya yi tare da cewa
"Ki faɗa masu waye uban ɗan da kika haifa."
Shiru ta yi ta kasa magana sai hawaye da ke tsiyaya daga idanunta. Ammy da Dad da Nasreen suma zuba mata idanu suka yi.
Ajamal ne ya sake maimaita kalamansa.
Sunkuyar da kai ta sake yi tare da fashewa da kuka ta ce,
"Nima ban san waye ubansa ba."
Sai suka fara jin wasu daga cikin mutane na cewa
"Ai ba zata faɗa cewa ɗansa bane saboda ya mata barazana kada kimarsa da mutuncinsa su zube a idanun mutane kasancewarsa ɗan siyasa."
Nan aka dinga hayaniya abu ne son zama rigima kowa da abinda yake cewa. Dad ne daka masu tsawa.
"Ku dakata! Sanin kanku ne cewa ɗana baya ƙasar nan tsawon shekara ɗaya. Watansa biyar da dawowa Nigeria, watanni tara ake haihuwar yaro, amma likitoci za su tabbatar mana da wannan gaskiyar lamari. Ta hanyar D.N.A (deoxyribonucleic acid)ta wannan hanyar ne za'a iya tabbatar da cewa shine uban yaron ko ba shi ba ne."
Wata nurse ce ta zo ta karɓi bayan daga hannun Amatullah tare da janta su koma ciki, kasancewar jikinta ba ƙarfi kuma ga shi aiki aka mata.
Daga nan hayaniya ya kare aka tsaya jiran sakamakon gwajin da za'ayi.
Bayan Munnir ya fito daga wanka ne ya shirya cikin ƙananan kaya farar riga da baƙin wando. Ya fara turarensa ya ɗaura agogonsa sannan ya ɗauki wayarsa ya kunna.
Duba lambar da aka dinga kiransa da ita ya yi kamar ya share ka da ka kira, amma sai ya yanke shawarar kira dan ya tabbatar da waye mai kiransa.
Kwance take a kan gadon asibitin idanuwanta ne kawai ke kwaranya da ruwan hawaye, yanzu ya za ta yi da rayuwarta? Idan aka aka sallame ta daga asibitin nan ba ta san kowa a garin nan ba, bata da kowa ina za ta zauna ta yi jegon haihuwar da ta yi, ina za ta dinga samun ruwan zafin da za ta dinga fasa jikinta da na jaririn da ta haifa? Wa zai kula da ita da jaririn idan aka tambaye ta ina uban yaron da ta haifa da wani baki zata iya cewa shege ne shi bai da uba?. Kuma ba ta san waye ubansa ba.
Kuka ne mai cin rai ya taso mata har tana shiɗewa kamar numfashinta zai ɗauke.
Gaba ɗaya an taru ana jiran sakamakon da Doctor zai kawo. Ajamal da iyayensa da matarsa hatta Nihad ta zo da Affan.
Likitan ne ya ƙaraso wajen tare da kallon Ajamal ya masa magana cikin cikin raɗa ya ce,
"Yallaɓai ka zo mu yi magana a sirrance."
Ajmal cikin yarda da kansa ya ce,
"Ba wani zancen sirri ka faɗa a gaban kowa ya san cewa ni ne uban yaron ko ba ni bana?"
Jin haka ya sa Doctor jinjina kai tare da cewa shikenan yallaɓai amma a matsayinka na ɗan takarar Governor na jihar nan zan so ka zo mu krɓe saboda kimarka da..."
Tsawa ya daka masa tare da cewa
"Ka sanar damu sakamakon abinda kenan kowa ya sani "
Jin hakan ya sa kowa ya dawo da hankalinsa ga Doctor 'yan jarida sai kutso kai suke.
Doctor ya cije laɓɓansa na ƙasa kafin ya ce,
"Wannan jaririn ba kowa bane ubansa face yallaɓai Ajmal."
Cikin tsananin tashin hankali da firgita Ajamal ya kalle shi tare da cewa.
"Wane Ajamal ɗin?"
Ajiyar zuciya Doctor ya sauke tare da cewa
"Ajmal Ibrahim Tafida ɗan takarar Gwamnan jihar nan garkuwar talakawa."
*Daga alƙalamin*
Zainab Abdullahi KNT
(Maman Ihsan)
09065327995
*Yawan comments yawan typing, kuyi shiru ku ga shiru kuwa*🤷♀️
🤦♀️ *ƳAR MAYE*🤦♀️
(_The drug abuser_)
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Dedicated to
*JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION*
*GARGAƊI*
Wannan littafin mallakar marubucirsa ce, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
*BISMILLAHI RAHMANI RAHIM*
Page3️⃣0️⃣&3️⃣1️⃣
"Ajmal Ibrahim Tafida ɗan takarar Gwamnan jihar nan garkuwar talaka."
Jinsa da ganinsa sai da suka ɗauke na wasu na ƴan daƙiƙu, ji yayi konnensa gaba ɗaya baya jin komai duk hayaniya da ake yi sai wani shiri ya ke ji. Idanuwansa kuwa duhu kawai yake gani.
Nan mutane suka fara ce ce ku ce, wasu na cewa akwai dama ba mutumin ƙwarai bane ungulu ne da kan zabo. Wasu na cewa kura ne lulluɓe da fatar akuya gara da Allah ya tona asirinsa kafin ya kai ga hawa kujerar mulki.
Idanuwansa ne suka rikiɗe zuwa jajir kamar garwashin wuta. Zuciyarsa sai tafarfasa yake yi sosai.
A fusace ya janyo wuyar rigar Doctor tare da shaƙe wuyansa.
"Wa ya siye ka? Kuma nawa aka biya ka da ka ɓata mani suna?"
Girgiza kai Doctor ke yi ya kasa magana sakamakon riƙe wuyar rigarsa da ya yi ya shaƙe masa wuya.
Daƙyar ya iya cewa
"Yallaɓai dan Allah ka sake ni."
Hakan bai sa ya sake shi ba sai da ya tambaye shi da cewa.
"Za ka faɗi gaskiya ko kuwa?"
Gyaɗa kai ya yi tare da cewa
"Eh zan faɗa"
Daƙyar ya iya ƙarasa maganar.
Bayan ya saki wuyan rigarsa ne sannan ya samu numfashinsa ya dawo dai-dai.
Kallon Ajmal ya yi tare da cewa
"Me ye riba ta idan na maka ƙazafi? Sannan kuma ina aiki a ƙarƙashin ka kai ne mamallakin wannan asibitin da na ke aiki, ba yadda za'ayi na maka sharrin abinda baka aikata ba."
Kallon Doctor ya yi cikin ɓacin rai da fusata ya ce,
Take your correction Doctor, ta ya ya za ka ce abinda na aikata? Akan idaonka na aikata?"
"Am sorry sir. A DNA test uses deoxyribonucleic acid ( DNA ) usually take from a check swab - to determine a child's biological father ( non - birthing parent). A kanyi DNA test gurin tabbatar da Mahaifin yaron."
"Idan har na tafi wani asibitin aka tabbatar da gaskiyar maganar cewa ba ni ne mahaifinsa ba wallahi sai na daure ka har har sai igiya ta rage."
Jinjina kai Doctor ya yi ba tare da wani tunani ba ya ce,
"Na amince duk hukuncin da ka ga dama ka ɗauka akaina a shirye nake."
Daga nan wajen ya ɗauki hayaniya yayin da wasu ke cewa aiko wannan likitan sai ya ɗanɗani kuɗarsa. Yayin da wasu ke ala wadai da halin Ajmal suna cewa borin kunya kawai Ajmal ke yi. Ba yadda za'a masa ƙarya a aibitinsa kuma ma'ikacinsa.
Wayarsa ya ɗauka tare da kira security ɗinsa ya basu umarnin zuwa su same shi a sabon asibitin da ya gina.
Cikin ɗaki kuwa Amatullah ce kwance tana kuka, yayin da wata nurse da ke kula da ita tana ta rarrashinta.
"Ya isa haka nan ba ki ga halin da kike ciki ba ne? CS aka maki aka ciro b
Baby daga cikin cikinki yakamata ki nutsu haka nan ki daina wannan kukan."
Ba ta daina ba kuma ba ta kalli Nurse ɗin ba, dan tashin hankalin da take ciki yanzu ya fi na lokacin da take da ciki. Dan yanzu ba ta san inda za ta nufa da wannan jaririn ba, tunawa ta yi da iyayenta musamman Ummanta, yanzu da ace cikin ta hanyar aure ta same shi ya kasance ɗan sunna da za ta ga gata da kulawa daga wajen Ummanta. Yanzu ta ina za ta fara yiwa jaririn nan wanka da ɗaukar ɗawainiyarsa, da suturansa da lafiyarsa ga ita kanta ba ta san yadda za ta kula da kanta ta hanyar jego ba. Ɗaya kamar sama ta yi yayinda da ƙwalla ke bin gefe da gefen idanunta.
'Ya Allah kai ne fatan bawa gani na zo da ƙoƙon barata Allah ka rufa mani asiri Allah ka iya mani, bani da iyawa sai naka ka fini sanin halin da nake ciki ka kawo mani mafita.'
Ammin Ajmal ce ta shigo ɗakin, kallo ɗaya Amatullah ta karanta gane cewa ita ce mahaifin wannan mutumin da ake ta magana akansa ne.
Ammi ra wuce gadon da Amatullah ke kwance kai tsaye ta nufi gadon da jaririn ta ke kwance.
Kasancewar asibitin Ajmal ne ƙa'idar asibitin duk wacce ta haihi kyauta ne, kuma kayan haihuwa da kaya da socs da huluna duk su ne suke sakawa yaro.
Bayan Ammi ra zagaya wajen gadon Baby ne ta tsaya, zuba masa idanu sosai ta yi tana ƙarewa Bayan kallo.
Sannan ta nufi gadon da Amatullah ke kwance, zuba mata idanu ta yi tare da cewa.
"Sannu ko?"
"Ina wuni Mama."
"Lafiya lau ya jiki?"
"Alhamdulillahi"
"Ma sha Allah"
"Yarinya zan maki tamabaya ne a matsayin Uwa. Shin ke matar aure ce ko budurwa?"
Kuka ne mai cin rai ya kufcewa Amatullah ta dinga yi har da sheshsheƙa, Ammi ta lura daka kukan na kusa kaɗan take jira kafin. Dan haka Umma ba ta yi yinƙurin hana ta ba ta ba ta barta har sai da ta yi mai isarta.
Bayan ta yi shiru ns ta kalli Ammi tare da cewa
"Ban taɓa auren ."
Jinjima na kai Ammi ta yi tare da cewa .
"Yanzu zan tambaye ki ɗan Allah ki tabbatar kin sanar da ni gaskiyar lamari, ka da ki ɓoye mani komai. Ki sanar dani gaskiyar lamari ki tuna cewa za ki mutu ki koma ga mahaliccin ki, wa ye uban wannan yaron?
"Cikn kuka ta fara magana."
"Wallahi ban sani ba, ban san waye ubansa ba, nima ƙaddara ta faɗa mani ba da son raina hakan ta faru ba."
"To ki sani idan ma wasu ne suka saka ki wannan aiki to ki sani kina cikin matsala dan idan aka sake tabbatar da cewa ƙarya ne kika faɗa kotu za'a kai ki."
"Hajiya ni fa ba cewa na yi shine uban yarona ba, cewa na ban san waye ba."
Daga nan Ammi ta fita inda ta tarar da su Dady, Dad, ne ya nemi su tafi wani asibiti .dan tabbatar da gaskiyar lamari. Wata nurse ce da ke kula da su ta ɗauki jaririn ta bisu suka tafi tare, yayin da Amatullah aka barta kwance a asibitin kasancewar halin da take ciki.
Haka suka ɗunguma zuwa wani asibiti nan ma aka tabbatar da cewa ɗnasa ne.
Asibitoci biyar suka nufa duk sakamakon gwajin iri ɗaya ne , ko ina cewa ake ɗansa ne.
Daga ƙarshe ne ya ce, sai dai idan mutum ɗaya ne ya tabbatar masa da gaskiyar maganar da zai yarda.
Kiran abokinsa kuma amininsa Doctor Fu'ad ya yi, nan yake tambayar sa yana asibiti ya amsa masa da eh.
Daga nan ne kuma ya kalli mahaifinsa ya ce,
"Dad kafin yanzu duk asibitin da kuka buƙaci mu tafi can muke zuwa, amma yanzu ina so ku nufi inda nake so don nan ne kawai hankalina zai iya kwanciya.
Kallon Direba da ya yi tare da bashi umarnin cewa su tafi asibitin Dr Fu'ad.
Bayan sun ƙwrasa Ajmal ya yi masa bayani cike da ƙwarin guiwa dan ya tabbatar ba za'a taɓa hada baki da shi a cuce shi ba.
Bayan wani lokaci shima ya tabbatar da zancen da zancen da sauran likitoci suka faɗa.
Tashin hankali.
Ajmal ya kalle shi cike da mamaki tare da cewa
"Yanzu da kai za'a haɗa baki a shirya mani munaƙisa? Kafin kowa sanin fiye da shekara ɗaya bana ƙasar nan, watanni biyar baya na dawo, saboda shine za ka faɗi haka?"
Wani jiri ne ya ɗibe shi ya zube a wajen sumamme. Ammimsa ba abinda take sai kuka mai tsuma zuciyar mai saurare. Sauran jama'a suka yi kansa, Dad ɗiinsa ma mutuwar tsaye ya yi.
*Daga alƙalamin*✍️
Zainab Abdullahi KNT
(Maman Ihsan)
Domin neman ƙarin bayani
09065327995
Love you oll😘😍
🤦♀️ *'YAR MAYE*🤦♀️
(_The drug abuser_)
*NA*
Zainab Abdullahi KNT
(Maman Ihsan)
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*SADAUKARWA*
Wannan shafin sadaukarwa ne ga duk mace da ta fuskanci ƙalubalen rayuwa a sanadiyar muguwar ƙawa. Allah ya haɗa mu da masu ƙaunarmu a duk inda muke, ka kada ka bamu ikon cutar da kowa kuma Allah ka kare mu daga sharrin masu sharri.
*GARGAƊI*
Ban yarda ba kuma ban amince a maida mani book audio ba tare da izinina ba ko a karanta mani shi a youtube ba tare da amincewata ba.
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce dan haka ban yarda a sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba.
*BISMILLAHI RAHMANI RAHIM*
Page3️⃣2️⃣&3️⃣3️⃣
Wani jiri ne ya ɗibe shi ya zube a wajen sumamme. Ammimsa ba abinda take sai kuka mai tsuma zuciyar mai saurare, sauran jama'a suka yi kansa, Dad ɗinsa ma mutuwar tsaye ya yi a wajen.
Dr Fu'ad ne da ɗaya daga cikin bodyguard ɗinsa ne suka shiga da shi ɗakin da Dr Fu'ad ya buƙata.
Ɓangaren Ummanta kuwa haka yau ta tashi da rashin lafiya, gaba ɗaya ta kasa gane wa jikinta. Abinci ma rabonta da shi tun jiya da rana, ba abinda take sai kuka da tunani. Abba haka ya dinga bata baki akan ta yi shiru ta dina wannan tunani amma abu ya faskara. Tana
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 51