da na sanin saninki a rayuwata na yi nadamar biyewa shawarwarin ki Allah ya wadaran halinki Hafsat. A dalilin ki na samu matsala da iyayena. Suka yi fushi da ni wanda Abba har yau ko gaisuwa ta baya amsawa, kin ruguza mani farin ciki na kin saka ni kuka, in sha Allah sai kin yi kuka da nadamar abinda kika mani."
"Okay tunda haka ne kin yanke alaƙar da ke tsakanin mu shikenan, amma sai dai sabuwar wayar da na siya maki nake buƙatar ta yanzun nan. Saboda haka ki zo ki kawo mani wayata, dan da tsada na siye ta kuma ba zan iya bar maki ita ba."
"Ai dama ko kin bar mani ita ba abinda zan da ita, sai dai yanzu dare ne ba zan iya fitowa ba."
"Idan ke ba za ki iya fitowa ba ni zan iya zuwa har cikin gidanku na karbi wayata."
Gaban Amatullah ne ya faɗi dan ta yiwa iyayenta alƙawarin rabuwa da Hafsat yanzu idan ta zo al'amuran za su sake damalmalewa ne. Dan haka dole ta dakatar da ita gara ita ta je ta same ta idan bari ta zo akwai matsala ran iyayenta zai ƙara ɓaci. Dan haka dole ta dakatar da ita daga zuwa gidan.
"Faɗa mani inda kike gobe in sha Allah zan kawo maki wayarki."
"Ba zan iya bari har sai gobe ba yau nake buƙatar wayata kuma yanzu."
Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa
"Ina zan kawo maki?"
"Ina club ne yanzu, a nan za ki kawo mani."
Shiru ta yi tana nazari kafin ta ɗora da cewa
"Shikenan yanzu zan fito na nemi mai abun hawa ya kawo ni."
Daga nan ta katse kiran wayar tare da miƙewa tsaye, dogon hijabinta ta saka tare ɗaukar wayar, kuɗi ta ɗauka Naira dubu daya ta fito tsakar gidan.
Ba kowa har ta yi niyyar zuwa ta sanarwa Ummanta da cewa za ta fita ta kaiwa Hafsat waya sai ta tuna cewa ta yiwa Ummanta alƙawarin ba ita ba Hafsat ba za ta sake kula ta ba. Dan haka sai ta fasa shiga ta fice tare da addu'ar Allah ya sa ta dawo ba wanda ya san ta fita.
Cikin ikon Allah kafin ta fita layin ta samu mai keke napep ta tsaida shi, sanar da shi club ɗin da zai kai ta ta yi tare da cewa idan ya ajiye ta zai jira ta saƙo kawai za ta bayar ya dawo da ita.
Shiga ta yi suka kama hanyar zuwa fita daga layin.
Acan club ɗin kuwa sai sautin kiɗa ke ta tashi da hayaniya, wasu na rawa suna cashewa yayin da wasu ke ta shaye-shaye wasu kuma na zaune suna kallon masu rawa.
Mai keke napep ya sauke Amatullah a ƙofar club ɗin wanda cikinsa hotel ne a ciki. Kallon mai keke napep ta yi tare da cewa.
"Mallam dan Allah ka yi haƙuri yanzu zan bada saƙo na dawo."
"Dakata Mallama fara bani kuɗin zuwa da na kawo ki, dan haka wasu ke yi su ajiye mutum ya na kiransa ƙarshe gudawa suke."
Murmushi ta yi tare da ciro dubu ɗaya ta bashi tana cewa.
"To ka riƙe kudin duka har da na dawo sai dai mu tafi ka ajiye ni dan na ga alamar ba ka yarda da ni bane."
Ya keɓi dubu ɗaya tare da kashe keken yana jiran dawowarta.
Shiga ta yi kasancewar ta taɓa zuwa tare da Hafsat.
Wani ɗaki ta nufa wanda nan ne ta san cewa Hafsat na ciki.
Knocking ta yi Hafsat ta ɗaga murya tare da tambayar waye, jin muryar Amatullah yasa ta tashi da farin ciki ta buɗeƙofar ta juya ciki.
Da sallama Amatullah ta shiga ko kallon kirki ba ta yiwa Hafsata ba ballantana ta gaishe ta. Miƙa mata wayar ta yi ba ta amsa ba sai ta ga ta nufi fridge ta ɗauko lemun kwali ta ajiye mata a gabanta tare da cewa
"Bisimillah ki zauna ki sha lemu."
"Ba shi ya kawo ni ba, ga wayarki nan na kawo maki ba ni ba ke, ki mance cewa kin taɓa sani na a rayuwarki ."
Daga nan ta juya har ta kai bakin ƙofar fita sai ta ji muryar Hafsat tana cewa
"Wai ni za ki wa rashin mutunci bututu?"
"Ba rashin mutuncin da na maki domin kin cutar da rayuwata, kuma ba na san sake ganin ko mai kama da ke a rayuwata, ko a mafarki idan na ganki sai na yi sadaka."
Murmushi Hafsata ta yi tare da cewa
"Lallai ki kula da rayuwarki."
Ba ta ce komai ba ta fita daga ɗakin .
Tana zuwa lungun da za ta da za ta sada ta da hanyar fita ne ta ji wani zafi a damtsen hannunta na hagu, juyawa ta yi tare da kallon wajen da ta ji zafin sai ta ga allura ne da sirinji aka soka mata, ruwan airijin ne ta ga yana shiga jikinta a hankali, take ta ji kanta na juyawa duk wani kuzari na jikinta ya ƙare jikin duk ya mutu, ko hannunta ba za ta iya ɗagawa ba ballantana ƙafarta.
A hankali ta yi lu ta bayanta za ta fara sulalewa ƙasa lokacin da ruwan allurar ya gama shiga jikinta.
Da misalin ƙarfe goma sha biyun dare Umma ce ta fita daga ɗakinta ta ta nufi ban ɗaki, bayan ta fito ne ta lura da cewa ɗakin Amatullah a buɗe yake, kuma ga hasken ɗakin a kunne, dan haka sai ta yi tunanin barci ne ya ɗauke ta ba tare da ta rufe ƙofar ba ta kuma kashe hasken ɗakin.
Nufar ƙofar ɗakin ta yi dan ta tayar da ita ta tashi ta rufe ƙofar ɗakin, amma sai ta ga ba ta nan, kuma daga banɗaki ta fito ba ta ciki, kitchen ta nufa nan ma ta duba ba ta nan. Tashin hankali wanda ba'a saka masa rana.
Hankalin Umma ya tashi mutuƙar tashi ganin ganin Amatullah ba ta gidan nan, ƙofar gida ta ƙarasa ta ga rufe yake da sakata, wato ko da aka rufe gidan ba ta ciki kenan ta jima da fita. Daga gidan .
Tana nan tsaye a tsakar gida tana tunani dan dama kullun idan Amatullah za ta kwanta sai ta sallame ta, sa ta ji shiru yau ta ɗauka barci ne ya sace ta.
Kuka ne ya zo mata ta nufi ɗakin Abba sai ta ga ɗakin a buɗe dama bai cika rufe ɗaki ba sai dai idan lokacin sanyi ne, dan haka ba ta yi mamakin ganin ɗakinsa a buɗe ba.
Zaune yake da alama bai yi barci ba tunani ne yake yi, da kula ta shiga ɗakin Kallonta ya yi cikin tashin hankali ya mike tsaye tare da cewa.
"Lafiya?"
"Ba Lafiya Mallam"
"To me ya faru?"
"Mallam ba ta nan fa."
"Wace ce?"
Cikin kuka ta ce,
"Amatullah ta ɓata Mallam ba ta gidan nan ba ta nan ko da ka rufe gida, ga gidan da sakata amma ka ga bata nan."
Sai ta ga bai ce da ita komai ba ya yi shiru shi kaɗai ya san me yake ji a zuciyarsa.
"Mallam dan Allah mu fita mu nemo ta duk inda ta shiga."
Ɗagowa ya yi da idanunsa da suka kaɗa suka canza launi zuwa ja ya watsa mata wani irin kallo wanda ya sa ta faɗuwar gaba.
*Daga alƙalamin✍️*
Zainab Abdullahi KNT
(Maman Ihsan)
Love you oll😍😘
Comments & share
Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
🤦♀️ *ƳAR MAYE*🤦♀️
(_The drug abuser_)
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*SADAUKARWA*
Wannan shafin sadaukarwa ne ga duk macen da ta fuskanci ƙalubale da matsanancin rayuwa a dalilin ƙawa. Allah ka haɗa mu da mutane na ƙwarai a duk inda muke, duk wanda ya shigo rayuwarmu da niyyar cutar da mu Allah kada ka bashi ikon cutar damu, Allah ya shiga tsakanin nagari da mugu.
*GARGAƊI*
Wannan littafin mallakar marubucirsa ce, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
*BISMILLAHI RAHMANI RAHIM*
Page1️⃣3️⃣&1️⃣4️⃣
Ɗagowa ya yi da idanunsa da suka canza launi zuwa ja, ya watsa mata wani irin kallo wanda ya sa ta faɗuwar gaba.
"Ki je ɗakinki ki kwanta ki yi barci."
Kuka ne yazo mata ta kalle shi ta ce,
"Mallam ta ina zan iya barci a wannan hali da muke ciki?"
"Ka da ki sawa kanki damuwa hawan jini ya kama ki."
Fita ta yi daga ɗakin ta koma ɗakinta, ta zauna ta cigaba da rusa Kuka.
Daga Abba har Umma ba wanda ya rintsa kowanensu kwanan zaune ya yi, Daga bisani ne ma suka tashi suka je suka gabatar da sallolin nafilfili. Tare da addu'ar Allah ya shirya masu Amatullah da dukkanin musulmai.
Da aka kira sallar asuba ne Abba ya nufi masallaci yayin da Umma ta yi nata a gida.
A daren ranar da misalin karfe uku na dare Amatullah tana kwance a cikin bargo ba ta san inda kanta yake ba, a hankali ta fara motsa babbar yatsar ƙafarta. Jikinta duk ya yi nauyi ji take ba za ta iya tashi ba.
A hankali ta buɗe idanuta ta kalli saman ɗakin, pop da ta gani na saman ɗakin ne gabanta ya faɗi tana mamakin me ya kawo ta nan.
Yunƙurawa ta yi da niyyar tashi sai ta kasa, ta koma ta kwanta ƙwalla na fita daga idaninta. Daƙyar ta tattaro dukkan jarumtarta ta yunƙura ta tashi zaune, wani zugi da raɗaɗi take ji a can ƙasanta.
Yaye bargon ta yi ta kalli jinin da ya zuba daga jikinta, ga ta duk ta jiƙe da jini, ƙara ta saki tare da fashewa da matsanancin kuka mai cin rai.
Baƙin ciki da takaici ne ya ishe ta, ta rasa wani mara imani ne ya mata wannan aikin.
Kula ta dinga yi ita kaɗai a ɗauki, tashi ma kasawa ta yi, zaninta ta janyo ta ɗauka tare da mai da kayan jikinta, hijabinta ma ba ta gani ba, dan haka da rarrafe ta ƙarasa a bakin ƙofar, ta saka hannu ta murɗa handle ɗin ƙofar ɗakin.
Tana kuka ta buɗe ƙofar amma ta kasa fita sai kuka take. Nafeesat da ta fito daga ɗakin da ke kallon inda Amatullah take ne ta ji sautin kuka, da firgici ta juya dan ganin wace ce ke kuka.
A firgice ta zaro idanu tare da furta kalmar
"Subhanahi! Amatullah wa ya maki wannan aikin?"
Sautin kukanta ta ƙara tare da cewa
"Nima ban sani ba."
Ganin Amatullah na ƙoƙarin tashi ne ya sa Nafeesat ta ƙaraso wajenta da sauri ta taimaka mata ta miƙe tsaye.
Wani namiji ne ya fito daga ɗakin da Nafeesat ta fito, Kallonta ya yi tare da cewa
"Baby ina kuma za ki shiga wajen?"
"Ina zuwa ka fita inda za ka tafi sai ka dawo."
Jinjina kai ya yi tare da cewa
"Okay."
Ya bar wajen yayin da Nafeesat ta taimakawa Amatullah suka shiga shiga toilet din da ke cikin ɗakin.
Ruwan zafi ta haɗa mata tare da Kallonta cikinn tausayawa ta ce
"Amatullah sai kin daure fa amma idan kika daure za ki ji sauƙin raɗaɗin da kike ji.
Jinjina kai kawai Amatullah ta yi sai hawaye dake fita daga cikin idanunta.
Bayan Nafeesat ta gama hada ruwan ta tabbatar da zai yi dai-dai sannan ta bawa Amatullah umarnin ta shige.
A hankali ta zauna cikin ruwan zafin, ƙara ta saki na azaba,ta yunƙura za ta tashi sai Nafeesat ta yi saurin riƙe ta ba ta bari ta tashi ba.
Sai da ta canza mata ruwa sau biyu, sannan a na uku ne ta barta ta ce,
Tayi wanka tana jiranta a ɗakin.gaba ɗaya ranta ya gama ɓaci dan ta san cewa mawuyacin abu ne Amatullah ta yarda a mata wannan aikin.
Fita ta yi daga ɗakin zuciyarta cike da saƙe-saƙe. Ba komawa ta fito hannunta dauke da doguwar riga na material da ƙaramin mayafi.
Dai-dai lokacin da Amatullah ta fito tana tafiya a hankali, ba laifi ta rage jin zafin da take ji .
Nafeesat ta miƙa mata kayan da ke hannunta ta karɓa ta saka, har lokacin hawaye bai daina kwaranya daga idanunta ba.
Hannunta kawai ta ja tare da cewa
"Wa ya kawo ki wannan ɗakin?"
Kuka ta fashe da shi tare da cewa
"Wallahi ban sani ba ban san komai ba."
A firgice Nafeesat ta kalle ta tare da zare idanu ta ce,
"Kina nufin ba ki san lokacin da kika zo ɗakin nan ba? Kuma ba ki san wanda ya maki wannan aikin ba?"
"Wallahi bansan komai ba farkawar na yi na ganini awannan ɗakin."
"To daga ina kike kafin kika tsinci kanki a nan?"
Nan ta bawa Nafeesat labarin komai da yadda suka yi da iyayenta har kiran wayar da Hafsat ta mata da kawo mata waya har izuwa alluran da ta ji an soka mata ta sulale za ta faɗi ta ji an riko ta, daga nan ba abinda ta tuna.
Ajiyar zuciya Nafeesat ta sake tare da ɗaukar wayarta ta dannawa Hafsat kira?
Ya na ta ringing ba ta ɗaga ba, daga nan ta ja hannun Amatullah suka fice daga ɗakin.
Kai tsaye ta nufi gidanta da ita dake kusa da club, Amatullah ne ta coge a ƙofar gidan alamar ba za ta tafi ba. Kallonta ta yi da murmushi a fuskarta ta ce,
"Ka da ki damu Amatullah ba cutar da ke zan yi ba, ina son Hafsata ta zo ne inji dalilin da ya sa Hafsata ta aka aka maki wannan ɗanyen aikin?"
Shiga suka yi Amatullah sai tafiya take yi a hankali, wanda bai sani ba zai ɗauka yanga ne.
"Shamsiya ce a falo tare da wata ƙawarta suna fira.
Suna ganin shugabar ta su suka fara gaishe ta, ta amsa tare da tambayar ko Hafsat ta zo, suka sanar da ita cewa ba ta zo ba.
Shiga kitchen Nafeesat ta yi yayin da ta ke cewa Amatullah ta ba ta mintuna biyu, ita dai Amatullah hankalinta na wurin Abbanta da Ummanta,ba ta san ya za ta ce masu idan ta koma gida ba.
Nafeesat ce ta fito daga kitchen rike da kofin tea da ledar bread a hannunta. Miƙawa Amatullah ta yi tare da cewa
"Karɓi ki sha."
Kuka ta saka mai cin rai tana cewa
"Aunty Nafeesat ba zan iya shan komai ba, wallahi ban san inda zan saka raina ba. Me zan cew..."
Kafin ta kai ƙarshen zancenta sai ga Hafsata ta shigo, kallon juna suka yi kafin Hafsat ta ɗauke kanta tare da taɓe baki.
Nafeesat ce ta kalle ta tare da cewa
"Hafsat anya ke bil'adama ce kuwa? Anya kina da imani kuwa? Kina kishin 'yar uwarki mace Kuwa? Wane irin rashin imani ne wannan? Kin saka ta shaye-shaye sannan kuma yanzu kuma saka akayi repe ɗin ta me ye ribarki akan wannan abun?"
"Ban gane me kike nufi ba?"
"Ai dama kin faɗa sai kin yi sanadiyar da za ta rasa budurcinta ko kin mata ne? To burinki ya cika komai ya faru. Wane ne kika sanya shi ya mata wannan ɗanyen aiki?"
"Oh abinda ya faru kenan?"
"Ka da ki raina wa mutane hankali mana? "
"Bari ki ji Nafeesat, bani da masaniyar abinda ya faru, tabbas maganarki haka ne na faɗi wannan zancen kuma ko da ta zo kawo mani waya na so na idasa nufinna akanta amma sai ba ta sha lemun da ke da wannan magani ba, ta fita ni na ɗauka tana gidansu ashe akwai abinda ya faru, to ta ya ya zan san..."
"Ka da ki raina mana hankali mu ba jahilai bane da za mu yarda da abinda kike faɗa?"
"To tunda ba ku yarda ba shikenan ba abinda zan ce maku, tun farko ku je ku nemi wanda ya mata wannan aikin amma ni bansan shi ba."
Tana gama faɗar haka ta juya ta fice daga gidan gaba ɗaya.
Amatullah ce ta durƙushe a wajen tana kuka , hatta Nafeesat sai da ta zubar da hawaye
na tausayin Amatullah. Ta rasa yadda za ta yi da ita ba, ga Hafsat ta bijire mana ga shi bamu da wata hujja duk da har yanzu ina zarginta.
Kuka sosai Amatullah ke yi tare da cewa kiran sunan Abbanta da Ummanta. Na feesat ta ce,
" Bari na ce wajen masu kula da wajen na sa abinciko muna sauna wanda ya kama ɗakin."
Daga nan ta fita nan Amatullah ta cigaba da kuka, bayan kamar mintuna ashirin sai ga ta ta dawo cikin sanyin jiki, kallo ɗaya za ka mata ka gane cewa ba nasara.
Daga kafaɗar Amatullah ta yi tare da cewa
"Yanzu na dawo an bincika ba wanda ya kama wannan ɗakin, tsawon kwanaki uku ɗakin ba kowa, kuma na sa abinciko jiya ko sunga wani alamu na rashin yarda daga wani? Nan ma ba nasara."
Nan Amatullah ta miƙe bayan ta yiwa mai Nafeesat sallama , Nafeesat ta raka ta har wajen abin hawa.
Nafeesat ce ta biya shi kuma mai.adaidata .
Har ƙofar gida ya kai Amatullah ta fito ta yi tsaye ta kasa shiga gidan ga kuma tunanin me za ta ce masu kuma ga wannan kayan na jikinta wanda basu san ta da shi ba fa?
A hankali take tafiya saboda ƙasa ta har yanzu tana jin raɗaɗi.
Da sallama ɗauke a bakinta ta shiga gidan, Ummanta da ke zaune kan kujerar tsakar gida ta mike d sauri tare da zuba mata idanu, ganin kayan jikinta ba wanda ta tafi da shi ba ne ya sa ta jin wani iri. Ƙarasawa ta yi gaban Ummanta tare da durƙusawa a kan guiwar ƙafarta ta ce,
"Umma ina kwana?"
"Ba ta amsa ba ta yi shiru tare da zuba mata idanu, kuka ya ƙwacewa Amatullah ta fara magana.
Na san cewa ba za ki sake yarda da zancena ba saboda bisa la'akari da alƙawarin da na yi jiya Yau kinga na saɓa ko? Za ki yi tunanin tubar ƙarya ce na yi..."
Dakatawa ta yi jin muryar Umma na cewa
"Ina kika kwana?"
Shiru ta yi tare da yin tunani ina za ta ce masu club ko hotel? Tana tsaka da tunani kenan sai ga Abba ya fito daga ɗakinsa.
Kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kansa, tashi ta yi zata ƙarasa gabansa ya daga mata hannu.
"Ba na buƙatar jin komai daga bakinki dan duk abinda zai fito yanzu ƙarya ce, ba na buƙatar ki zo inda nake ko ki gaishe ni, tunda kin fi ƙarfin mu kin zama ƴar kanta.
Kuka ne ya ƙwace mata Abban ya fice daga gidan.
Umma ce ta kalle ta tare da cewar
"Ina kika kwana?"
Shiru ta kasa magana sai kuka kawai take yi kamar ranta zai fita, sai da Umma ta tambaye ta a karo na biyu ne sannan ta amsa mata,
da cewa.
"Umma na san na maku laifi na roƙe ku akan na daina, sai ga shi yau na sake wani laifin da ya fi na baya. Amma na maki alƙawarin cewa daga yanzu idan har na sake makamancin wannan ko na sake fita ƙodar gida ba tare da ke ce kika Umarce ni ba to a ranar duk hukuncin da kika yanke akaina na amince, wallahi ba zan sake ba karo na ƙarshe kenan da zan nemi afuwarki kan bijire maki in sha Allah."
Shiru Umma ta yi ta zuba mata idanu tare jin tausayi ta da dukkan alamu ta sha kuka dan idaninta a kumbura suke.
"Ina kika kwana?"
"Umma fita da na yi daga gidan nan kuskure ne abinda ya faru da ni ƙaddarata ce kowane bawa bai isa ya kaucewa ƙaddara ba duk abinda ya samu bawa muƙaddari ne daga Allah, ki taya ni da addu'ar Allah ya bani ikon cinye wannan jarabawar . Dan Allah Umma ki bar maganar nan wallahi ba zan sake ba."
Shiri Umma ta yi tare da zuba mata idanu yadda take ta riskar kuka, ba ta iya fushi da Amatullah, dan haka ta ce,
Daga yau idan har kika sake kada ma ki sake riƙon afuwa daga gare ni.
Girgiza kai ta yi tare da yin murmushi ta ce
"Na amince."
"Abbana fa?"
"Abbanki yana da zafi kinsan haka amma idan ya ga kin canza kin koma yadda ya san ki a baya zai sauko."
"Ina sha Allah Umma."
Tuna abinda ya faru da ita ne ya sa ta yi saurin fashewa da kuka, Umma da mamaki ta kalle ta tare da cewa
"Lafiya kukan me ye kuma na ce na yafe maki ko."
Shiru ta yi tare da cewa
"To Amma na daina."
Daga nan ta ce,
"Umma bari na shiga ɗaki na kwanta. Barci na ke ji."
"Yanzu akwai abinda za ki iya ɓoye mani? Ina kika kwana? Bayan shaye-shaye kin fara bin..."
Kasa ƙarasa maganar ta yi dan nauyinsa bakinta. Gaban Hafsat ne ya faɗi duk da ta yi ƙoƙarin dai-daita tafiyarta ko Umma ta gane ne.
Kuka ta saka tare da cewa
"Na san me kike ƙoƙarin cewa Umma kina son cewa bayan shaye-shaye ina bin maza ko? Umma kina tunanin da hankalina da tunani na zan iya bawa namiji kaina yadda na tsani mazinata, tabbas ina ƴar maye ce amma ba mazinaciya ba."
Ta ƙarasa maganar ƙirjinta na dukan uku uku
"Ina kika kwana kuma kayan da ke jikinki fa?"
"Na ƙawata ce nawa sun lalace ne kwata ce ta ɓata mani shne ta ce na canza da nata."
Tana gama faɗar haka ta yi saurin shigewa ɗaki dan kuka ne ya zo mata.
*KADUNA*
Hajiya Bilkisu ce ta shigo cikin kitchen ɗin yayin da ma'aikatan gidan ke ta aikace-aikace, kallon ma'ikatan ta yi tare da cewa ku tabbatar kun kammala komai akan lokaci, dan Alhaji ya ce ƙarfe sha biyu na rana za su ƙaraso, manyan baƙi ne ku yi hanzarin gamawa ba tare da an samu matsala ba."
Cikin girmamawa suka amsa da to, daga nan ta fice zuwa falo inda Alhaji Ibrahim Tafida ke zaune yana kallon news.
"Alhaji wai wasu baƙi ne za su zo da ka ce na sa ma'ikatq su yi girki kala-kala?"
"Mai girma Gwamna ne zai zo da kansa na so ya bari na zo na same shi sai ya nuna mani tafiyar ba tawa ba ce ta ki ce?"
Nuna kanta ta yi da yatsarta manuniya tare da cewa
"Ni kuma?"
"Eh yana neman amincewarki ne dan ki amince da cewa an tsayar da ɗanki Ajmal takarar Gwamnan jihar nan."
Take fara'ar fuskarta ta ɗauke kallo ɗaya za ka mata ka ga ɓacin ran dake kan fuskarta.
*Daga alƙalamin*✍️
Zainab Abdullahi KNT
(Maman Ihsan)
Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
🤦♀️ *ƳAR MAYE*🤦♀️
(_The drug abuser_)
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*SADAUKARWA*
Wannan shafin sadaukarwa ne ga duk macen da ta fuskanci ƙalubale da matsanancin rayuwa a dalilin ƙawa. Allah ka haɗa mu da mutane na ƙwarai a duk inda muke, duk wanda ya shigo rayuwarmu da niyyar cutar da mu Allah kada ka bashi ikon cutar damu, Allah ya shiga tsakanin nagari da mugu.
*GARGAƊI*
Wannan littafin mallakar marubucirsa ce, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
*BISMILLAHI RAHMANI RAHIM*
Page1️⃣3️⃣&1️⃣4️⃣
Ɗagowa ya yi da idanunsa da suka canza launi zuwa ja, ya watsa mata wani irin kallo wanda ya sa ta faɗuwar gaba.
"Ki je ɗakinki ki kwanta ki yi barci."
Kuka ne yazo mata ta kalle shi ta ce,
"Mallam ta ina zan iya barci a wannan hali da muke ciki?"
"Ka da ki sawa kanki damuwa hawan jini ya kama ki."
Fita ta yi daga ɗakin ta koma ɗakinta, ta zauna ta cigaba da rusa Kuka.
Daga Abba har Umma ba wanda ya rintsa kowanensu kwanan zaune ya yi, Daga bisani ne ma suka tashi suka je suka gabatar da sallolin nafilfili. Tare da addu'ar Allah ya shirya masu Amatullah da dukkanin musulmai.
Da aka kira sallar asuba ne Abba ya nufi masallaci yayin da Umma ta yi nata a gida.
A daren ranar da misalin karfe uku na dare Amatullah tana kwance a cikin bargo ba ta san inda kanta yake ba, a hankali ta fara motsa babbar yatsar ƙafarta. Jikinta duk ya yi nauyi ji take ba za ta iya tashi ba.
A hankali ta buɗe idanuta ta kalli saman ɗakin, pop da ta gani na saman ɗakin ne gabanta ya faɗi tana mamakin me ya kawo ta nan.
Yunƙurawa ta yi da niyyar tashi sai ta kasa, ta koma ta kwanta ƙwalla na fita daga idaninta. Daƙyar ta tattaro dukkan jarumtarta ta yunƙura ta tashi zaune, wani zugi da raɗaɗi take ji a can ƙasanta.
Yaye bargon ta yi ta kalli jinin da ya zuba daga jikinta, ga ta duk ta jiƙe da jini, ƙara ta saki tare da fashewa da matsanancin kuka mai cin rai.
Baƙin ciki da takaici ne ya ishe ta, ta rasa wani mara imani ne ya mata wannan aikin.
Kula ta dinga yi ita kaɗai a ɗauki, tashi ma kasawa ta yi, zaninta ta janyo ta ɗauka tare da mai da kayan jikinta, hijabinta ma
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 51