Share this page
mata?" "What's the difference between..." "Stopped bana so, har za ka iya zama da wata bayan ni?" "Me zai hana ki dawo ina da bukatarki ko dan siyasar da ke gaba na yanzu." Tashi ta yi a guje tana kuka ta fita taɓe baki ya yi tare da kashe wayarsa. A falon gidan ta same Dad ɗin ta da Mom ta sanar da su halin da ake ciki, kuma ta ce gobe za ta koma Nigeria ba za ta bari a aura masa wata ba . Iyayenta sun yi farin cikin jin za ta koma don dama soyayyar da suke mata ne ya saka ba sa iya mata faɗa, sai abinda ta ga dama ra yi. Key ɗin motarta ta ɗauka ta nufi makarantar su Affan dan sanar da su zai koma Nigeria da karatu. Kiran sallar magrib ne ya farkar da Amatullah daga barcin da take yi. Kuma sai ta tashi da zazzaɓi da ciwon kai ga yunwa kamar wacce ta yi azumi. Daƙyar ta lallaɓa ta fito sai ta ga Bohol daga can gefe,ƙara sawa ta yi bayan ta waiga ta ga ba kowa dake Kallonta. Buta ta ɗauka ta d'ebi ruwa ta zagaya baya ta yi fitsari, sannan ta yi alwala ta koma cikin class din ta ta fito. Dama windows a rufe suke sai ta rufe class ɗin da sakata ta ciki, kasancewar akwai wutar nepa haske ya gauraye class ɗin. Kashe fanka ta yi saboda sanyi da take ji, Akan ɗankwalinta ta yi sallah bayan idar da sallar magrib ne ta zauna ta yi azkar har aka kira sallar isha'i ta gabatar. Yunwa ce gaba ɗaya ta addabe ta gashi ba ta da kudin da za ta siye abinda za ta ci a cikinta. Haka ta kwanta tana kukan tausayin rayuwar da ta tsinci kanta a ciki. Kuka ta ke yi sosai har sai da ta ji kukan yana neman zame mata ciwo ta tsagaita. A haka ta yi barcin wahala ga sauro kamar ba gobe, sai cizonta suke yi ga kukan sauro a kunne da suka dame ta. Ƙarshe dai sai da ta lulluɓe jikinta daga kanta har tafin ƙafarta. Amma duk da haka ba ta tsira ba ta dai samu sauƙi. Da asuba ta ta ji ana kiran sallar asuba ne ta tashi, fita ta yi don yin alwala. Tana zuwa wajen Bohol ɗin sai ya yi daidai da ƙarasowar mai gadin makarantar. Gabanta ne ya faɗi dan ba ta yi tunanin za ta gan shi ba. Abun da ya bata mamaki sai jin Muryarsa ta yi yana cewa "Ƴata kin tashi?" Shiru ta yi tana tunani dama ya san tana nan ne kenan. "Eh Baba, dama ka ga shiga na ne?" Murmushi ya yi tare da cewa "Ai tun jiya da kika zo da jaka akan idona , na ga sanda kika shiga har sanda kika fito kikayi alwalar magrib akan idona ne." Durƙusawa ta yi tare da cewa "Baba dan Allah ka rufa mani asiri bani da kowa a garin nan, kullun cikin rabe-raben neman wajen kwana nake, kada ka Kore ni a nan ban taɓa samun wurin da na yi barci ba sai yanzu, kullun zullumi da fargaba ke hana ni barci." "Ba zan Kore ki ba sai dai ni mai gadi ne a wannan makaranta, kuma ba ni kaɗai bene, mu biyu ne idan wannan satin na yi wani sati shine yake zuwa ya yi gadin. Zan masa bayaninki, amma kullun ki tabbatar ƙarfe shida ne safe za ki bar nan ki tafi wani waje, idan yara sun tashi daga makaranta karfe biyu zuwa karfe uku za ki dinga zuwa lokacin kowa ya watse. A ranar Ajmal ya tashi cikin tsananin farin ciki da walwala, domin dawowar matarsa da ɗansa. Ya sa an gyara mata ɗakinta an shirya masu girki na musamman. Ammi ma ta yi farin ciki jin za su dawo. Shi da masu tsaronsa ne suka je taro ta daga airport. Tun akan hanayar su ta zuwa guda take ta ganin poster ɗin mijinta a titi, mamaki ne ya kama ta, kallonsa ta yi tare da cewa "Dadyn Affan me nake gani haka?" Kallonta ya yi yana ɗauke da Affan a saman ƙafarsa ya ce, "Name fa?" "Wa nake gani ya fito takarar Gwamnan?" Murmushin gefen baki ya yi tare da shafar gefen fuskar Affan ya ce, "Ban ga wa kike magana ba ai." Zuba masa idanu ta yi tana kallon rainin hankali irin nasa, kafin ta ce, "Bana da 'yanci ko darajar da za ka yi shawara da ni ko?" "Nima ba shawara aka yi da ni ba, hasalima ba yadda na iya dole ya sa na amince." "Amma shine ka kasa sanar da ni?" "Ke ce ba ki bani damar hakan ba, na kira ki a ranar da na yi niyyar sanar da ke amma kika ce wai ke yanzu baki da lokacin da za ki tasya bani shawara idan zan yi abu, ai ni ba yaro bane na san me yakamata. Wannan zancen na ki ya bata mani rai ko ba komai na nuna ina son mu yi shawara zaki saurare ni ballantana ina mijinki ba ki damu da..." Shiru ya yi ganin Affan yana kallonsa, duk da taro na yana da shekaru huɗu amma ya san duk maganar da suke. Tsuke fuska ta yi dan ba ta dawo ba fa sai yaushe za ta sani oho Murmushi ta yi tare da riko hannunta cikin nasa ya ce, "Allah ya huci zuciyarki tuba nake yi." Murmushi ta yi don ko ba komai ta san cigaba ne yazo masu. *BAYAN WATA UKU* Haka rayuwa ta cigaba da tafiya wasu, har zuwa lokacin. Amatullah tana rayuwa ne a cikin wannan makarantar primary, duk ta rame ta yi baƙi kamar ba ita ba, abincin da za ta ci daƙyar take samunsa wata rana haka za ta kwana da yunwa ba ta ci ba. Idan ta tashi da karfe shida ne safe za ta bar makarantar sai ta ajiye jakar kayanta a cikin aikin, dan a cikin class da take kwana akwai inda silin ya fashe sai ta taka kujera ta ɗora jakar kayanta ta fita. Sai karfe uku na rana bayan ɗalibai sun watse sai ta dawo. Ta zauna har dare ba ta fita. Wata rana ta kan je ƙofar gidan da aka taɓa rabon abinci ta tsaya wajen, ranar da aka raba ta karɓa ranar da kuma ba'a raba ba idan ta gaji da zama sai ta bar wajen. Ranar da safe ba ta ci komai ba har da ta yi ba abinda ta ci wasa-wasa har magrib ta yi ba ta ci komai ba, ga ciwon ciki ya addabe ta sosai. Jikinta har rawa yake saboda tsabar yunwa tana kuka. Tana fitowa daga class ɗin ta hangi mai gadin makarantar ya buɗe kwanon tuwo yana ci. Kasancewar masu gadin su biyu ne kuma wannan ne dattijo wancan saurayi na. Cikin Sa'a sai ya kasance dattijo ke da duty. Da sallama ta ƙarasa wajensa ya amsa mata tare da cewa "Ƴata kin fito?" "Eh Baba." Sai ya ga ta durƙusa a gabansa ta yi shiru kanta a sunkuye. "Lafiya ƴata ko akwai abinda kike bukata ne?" "Am Baba dan Allah ka taimaka mani da abinci yunwa nake ji tun safe ban karya ba har zuwa daren nan." "Subhanahi garin ya hakan ya faru? Fitar da kike ba wajen aiki kike zuwa ba?" "A'a ba na da wajen aiki, kawai dai ina fita ne idan Allah ya sa zan samu abinda zan saka a bakina." Girgiza kai Mallam Musa ya yi tare da cewa "To ina mijinki da iyayenki suke?" Kuka ne ya suɓuce mata,sai ta yi nadamar mata wannan tamabaya. "Kin ga ki yi haƙuri in sha Allah sauki yana tare da tsanani." Abincin da yake ci tuwon dawa ne da miyar kuka ya mika mata. Hannunta na rawa ta karba tana godiya ta nufi cikin class ɗin. Hannu baka hannu ƙwarya ta fara cin abinci, dan kwanon tuwon a cike yake ga miyar daban a kwanon silba. Cikin kankanin lokaci ta cinye tuwon nan tasss sannan ta janyo kofin ruwa da ta ke ta sha bai mata maganin yunwa ba. Ruwan ma ta shanye sannan ta yi gyatsa tare da yin hamdala ga Allah. Daga nan kuma sai ta cigaba da sana'ar ta wato kuka. Sai da ta yi kuka mai kasarta sannan ta tashi ta fita da kwanoni zuwa wajen Bohol ta wanke ta kai masa tare da kara masa godiya. Washe gari ne tana tsaka ta yawonta a cikin gari sai ta ji mutane suna cewa za su je a basu kudi, kuma sai ta ga suka mata ne ba maza. Dan haka sai ta tamabaya me ke faruwa. Sai wata ta ke ce mata Ajmal ne ke raba kuɗi yau Da mamaki ta kalle ta tare da cewa "Waye Ajmal kuma?" Wata ce ta kalle shi tare da cewa "Ke kina garin nan baki da labarin Ajmal? " Juyawa ta yi ta kalli poster na Ajamal da aka manna a titi yana dariya. "Kin gansa da nan shine Ajmal sabon Governor din mu na gobe in sha Allah. Mutumin kirki ne mai taimakon talakawa yana yawan rabon kayan abinci da sutura da kudi ga talakawa. Ko waɗanda basu zuwa gidansa suna da labarinsa. Yau aka ce za'a kawo mota uku ta shinkafa duk wanda ya je ƙofar gidan lallai ne a bashi buhu ɗaya. Harda kuɗi dubu biyar biyar kowane mutum." Shiri Amatullah ta yi tana saurarenta har ta gama kafin ta ɗora da tambayarta. "Ina ne gidansa ina son zuwa." "Ka da ki damu can zamu je tare da sauran abokan tafiyata. Amma sai kin kula saboda na ga kina da ciki ka masu juna biyu bai dace suna shiga cikin cunkoso ba. "Ka da ki damu zan kula da kaina." Daga nan sai sauran abokan tafiyar suka ƙaraso suka kama hanya dan zuwa gidan Ajmal. *Daga alƙalamin*✍️ Zainab Abdullahi KNT (Maman Ihsan) Love You oll 🤦‍♀️ *ƳAR MAYE*🤦‍♀️ (_The drug abuser_) *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Dedicated to *JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION* *GARGAƊI* Wannan littafin mallakar marubucirsa ce, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. *BISMILLAHI RAHMANI RAHIM* Page2️⃣4️⃣&2️⃣5️⃣ Daga nan sai sauran abokan tafiyar suka ƙaraso suka kama hanya dan zuwa gidan Ajmal. ƙofar gidan a cike yake da mutane anyi layi na ban mamaki. Duk da ance sai ƙarfe huɗu za'a fara rabon amma wasu tun safe suna ƙofar gidan anan suka wuni. Zaune take a bayan mota yayin da Affan ke zaune a gefenta hannunsa riƙe da IPad yana game. Direba ne ke jansu sai wani security dake gefen Direba. Waya take yi da ƙawarta da Kenya fasa mata kai tana ƙara kambama ta wai ita yanzu first lady ce. Jin yadda Direba ke ta danna horn ya sa ta cire wayar daga kunnenta tana kallon me ke faruwa. Ganin yadda aka cika ƙofar gidan ne ya sa ta fusata tana cewa "Which can't thing be this? Mutane kamar dabbobi sun zo sun cikawa mutane ƙofar gida ba yadda mutum zai shiga." Kallon security din ta yi tare da cewa "Ka je ka basu umarnin su bar wajen nan, idan ba haka ba duk wulaƙancin da aka masu su suka siya." "Madam am sorry to say, ba zan iya koransu ba saboda idan yallaɓai ya ji zai iya nima ya ya Kore ni dan ya ce ka da wanda ya wulaƙanta su." Tsuki ta yi da niyyar fitowa tana faɗin "Yanzu za su bar wajen nan." "Madam ki dakata." Tsayawa ta yi tana kallon sa ta ce, "How dare you da za ka dakatar da kana a karkashi na?" "Am sorry, amma shawara ne zan baki dan Allah ka da ki fita." "Ahmad wai ni sa'anka ne da kake dakatar da ni?" "Ba haka bane, idan kika fita kika Kore su yallaɓai ba zai ji daɗi ba. Kuma kinga suna ganin girmansa da mutuncinsa suna kallonsa a matsayin wani garkuwa a gare su, kuma kinga kina shirin zama first lady wannan halin bai kamata ki nuna masu ba saboda siyasa sai kana kyautawa mutane za su soka. Idan kuma wulaƙanta su zasu ga baƙin ki za su gani yanzu kyautatawa ne ya kamace ki." Tabbas zancen Ahmad gaskiya ne shi ya sa ta haƙura tare da cewa "Ya rage naka kasan yadda za ka yi mu shiga ciki." Daga nan bata sake magana ba ta kwantar da kanta da bayan seat na mota. Bayan kamar mintuna goma ne Ahmad ya dawo tare da cewa Direba su shiga ciki. Bayan ya yi parking motar ne Ahmad ya fito da sauri ya bude mata murfin motar ta fito. Sannan ya ɗauko Affan dake riƙe da IPad. Cikin gida suka shiga inda suka suka tarar da Ammy babban falon gidan. Ahmad ne ya gaishe ta tare da ajiye Affan akan kujera kusa da Ammy sannan ya fita. Ammy ta kalle su tare da cewa "Kun dawo?" "Sannu Ammy mun dawo ." Nasreen ce ta yi maganar tare da yin tsuki. Kallonta Ammy tayi tare da cewa "Ke da waye kuma?" "Ammy baki ga yadda mabarata suka cika ƙofar gidan nan ba? Wallahi abun takaici sai ka ce kasuwa ake ci." Murmushi Ammy tayi tare da cewa "Yau kika fara gani ne?" "A'a Ammy amma na yau sun yi yawa gaskiya." "Kinsan abinda ya sa zasu yi yawa yau saboda ba iya kudi ya ce zai raba ba ya sa an kawo masa mota uku na shinkafa ga kuɗi da zai haɗa masu da shi, shi ya sa kika ga yawan nasu. Musamman awannan lokacin da ake fama da tsadar rayuwa abinci ya yi tsada sosai ga rashin kuɗi wani baida abinda zai ci na yau balle na gobe." Taɓe baki ta yi tare da cewa "Haka ne." Ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan ne ta fito daga kitchen, Nasreen ta kalle ta tare da cewa "Kije can ɓangarenku ki kira mani Laraba." Cikin girmamawa ta amsa tare da barin wajen da sauri ta nufi ɓangaren ma'aikatan gidan. Ba komawa sai ga wata mata mai kimanin shekaru arba'in ta zo ta durƙusa cikin girmamawa ta ce, "Gani Hajiya" Ba tare da ta kalle ta ba ta ce, "Ki ɗauki Affan ki je ɗakinsa ki yi masa wanka ki sauya masa kayan jikinsa." "An gama." Laraba ta faɗa tare da mik'ewa ta ɗauki Affan ta nufi ɓangaren iyayensa da shi dan zuwa ɗakinsa. Ita kuma ta kallo Ammy tare da cewa "Ammy bari na shiga na watsa ruwa." "To Nasreen a fito lafiya." Part ɗin su ta nufa ta shiga bedroom. dai-dai lokacin da Ajmal ya fito daga bathroom, da alama wanka ya yi yana sanye da farin bathrobe a jikinsa. Kallonsa ta yi tare da cewa "Dama ka na ciki? Yakamata ka sallami waɗanncan mabarata da suka cika wa mutane gaban gidan." Luhulun idanunsa ya zuba mata ya ma rasa me zai ce mata. Dan haka ya share ta tare da nufar gaban dressing mirror hannunsa riƙe da karamin towel yana goge ruwan da ke kansa. Ganin bai ce mata komai ba ne ya dauki jona handryer yana busar da gashin kansa. "Kodayake Indai kai ne talakawar nan baka haɗa su da komai ba, kana ƙaunarsu har cikin ranka." "Eh ina ƙaunar su kuma ina tausayin su saboda halin da suke ciki abun a tausaya masu ne." Taɓe baki ta yi tare da cewa "Haka ne tunda kasa siyasa a gaba ." "Ko kafin na shiga siyasa ma ɗabi'a ta ce. Taimakawa marasa shi cikin gari da wajen gari Kuwa." Kallon manya manyan buhun gana mazgo ta yi wanda aka cika su maƙil da kuɗaɗen da za'a raba wa mutane ta yi sannan ta kalle shi ba tare da ta yi magana ba ta koma falonta dan amsa wayar da aka kira ta. Kasancewar sai an fara raba kudin kafin a raba shinkafa ya sa aka fara layin kuɗin. Security ɗin Ajamal ne suke raba kuɗin kowace mace dubu biyar biyar ake rabawa. Anbi komai daki-daki yadda Yakamata kowace mace ta samu Naira dubi biyar wadanda suka je da ƙananan yara ma kowane yaro yana da dubu biyu. Kuma duk yawan ƙananan yara da aka je da su sai an baki na kowane yaro. Lokacin da rabon kudin ya kai wajen Amatullah ta samu ta yi farin ciki sosai tare da sanyawa Ajmal albarka. Daga nan aka fara bin layin shinkafa sai dai wajen bin layin shinkafa ba kamar na kudi bane, domin kuwa sai cunkushewa suka yi suna ta ture-ture idan ma ba masu karfi ba ba zasu iya bauta bin layin ba wasu ana ture su suna faɗuwa. Duk yadda security suka yi akan abi a hankali abun ya ci tura sosai. Amatullah da ta shiga layin ta ga ta fara jin jiki ga ta da tsohon ciki zasu iya illata ta da abinda ke cikinta. Hakan ya sa ta haƙura ta koma gefe tana kallon masu bin layin. Ƙarshe haka ta hakura ya koma makaranta bayan ta siye garin rogo da sugar da gyaɗa, dan ba zata iya siyen abinci mai tsada ba dan zata yi maneji da kuɗin kada su k'areda wuri. Dan idan Mallam Musa ke da duty yana taimaka mata da abinci. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya har cikin Amatullah ya shiga watanni tara. Hafsata ce zaune akan carpet ta sanya kwalaben Benelin a gabanta, ki ta yi ba zasu mata ba, dan haka ta ɗauki makulli motarta ta bar gidan. Wani kango ta dosa tare da yin parking a kofar kangon. Wasu maza guda huɗu ne a ciki ɗaya yana rataye da baƙar hamada ke dauke da kayan maye. Tana shiga ta kalle su tare da cewa " Guys akwai kayan aiki a ƙasa?." "Akwai ai dole a baki." Yana cirowa ya miƙa mata kenan sai suka ga anyi masu dirar mikiya, an ɗora masu bindiga kowannnsu. Mai siyar da kayan ne ya ce, "Mun shiga uku masu kama 'yan shaye-shaye ne suka kama mu. Mun shiga hannu." Haka aka tasa ƙeyarsu cikin mota aka tafi da su Hafsat ta shiga tashin hankali. Wata rana da misalin ƙarfe goma na dare Amatullah ta tashi da matsanancin yunwa, ji yayi ba zata iya kwana haka ba. Tashi tayi ta fita daga class ɗin ko zata samu abinda zata ci. Tafiya take cikin duhun dare ba tare da sanin ina zata je ba, cikin baƙin ciki da nadamar faɗawarta harkar shaye-shaye. Ga ta ɗauke da tsohon ciki haihuwa yanzu ko anjima. Tana takaicin rashin sanin waye uban ɗan da ke cikinta. Wata tsaddiyar mota ne ke tafe a guje kan titi ba tare da saninta ba wannan motar t kaɗe ta. A hankali idanunta ya sauka akan motar lambar da ke jikin motar wanda aka rubuta AJMAL 1. Cikin rashin hankali Ajmal ya fito daga cikin motar ya ƙaraso wajenta, baiyi wata-wata ba ya ɗauke ta da sauri tare da saka ta a bayan motar. *Daga alƙalamin* Zainab Abdullahi KNT (Maman Ihsan) 09065327995 🤦‍♀️ *ƳAR MAYE*🤦‍♀️ (_The drug abuser_) *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Dedicated to *JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION* *GARGAƊI* Wannan littafin mallakar marubucirsa ce, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. *BISMILLAHI RAHMANI RAHIM* Page2️⃣6️⃣&2️⃣7️⃣ Cikin rashin tashin hankali Ajmal ya fito daga cikin motar ya ƙara wajenta, baiyi wata-wata ba ya ɗauke ta da sauri tare da saka ta a bayan motar. Gudu yake sosai a cikin motar kamar zai tashi sam. Cikin mintuna goma ya isa wani asibiti asibitinsa da ya gina kwanan nan. Ganin yanda ya shigo a guje ne ya sa hankalin jama'ar da ke farfadan asibitin ya dawo kansa. Zubawa motar ido suka yi suna kallon waye zai fito, ganin Ajmal ya sa wasu suka dinga tambayar kansu. 'Lafiya suka ganshi shi kaɗai haka? Bayan motar ta buɗe da sauri ya ɗauko Amatullah wacce ta riga da ta suma. Yana riƙe da ita ya nufi cikin asibitin ko da aka kawo masa keken ɗaukar marasa lafiya bai bi ta kansu ba dan hankalinsa a tashe yake yana addu'ar Allah dai ya sa ba kashe ta ya yi ba. Emergency room ya nufa da ita wanda gaba ɗaya asibitin ta dauka cewa ga yallaɓai Ajmal nan ya kawo wata mai ciki matarsa ce. Nan da nan labari ya isa ga Doctor ya nufi inda Ajmal yake. Bayan sun karɓe ta ne suka ce ya kwantar da hankali ya ɗan jira su a waje. Ba musu ta fita waje shiga dai Addu'arsa ɗaya Allah ya sa tana da ranta bata mutu ba. Can gidansa kuwa ganin har ƙarfe goma sha ɗaya ta yi Ajmal bai dawo ba ne ya sa hankalin Ammy tashi. Duk da tana a ɗalibta ne amma ta tabbatar da cewa Ajmal bai dawo gidan ba, saboda idan har ya dawo to ƙa'idarsa ne sai ya fara shiga ɗakinta ya gaishe ta tare da mata sallama kafin ya nufi ɗakinsa. Wayarta ta lalubo tare da danna masa kira tana ringing ba'a ɗaga ba, dan haka sai ta kira ɗayan layinsa nan ma bai ɗaga ba. Hankalinta ne ya tashi dan ta fara shakku akan cewa ba lafiya ba dan jikinta ya bata hakan. Kiran lambar Nasreen ta yi dan ta ji ko ya dawo gida nan ma Nasreen bata ɗaga ba, asali ma barcinta take bata ma san wayar na ringing ba. Shi kuma Ajmal wayarsa na cikin mota ne bata tare da shi bai san an kira wayar ba. Wasu daga cikin jama'ar dake asibitin me ma suka zo kansa suna gaishe shi, sanin shi waye da kuma kyawawan mu'amalarsa da mutane, hakan ya sa suka damu akan halin da ya ke ciki. Wasu suna ta kwantar masa da hankali ta hanyar cewa kada ya damu zata haihu lafiya, tunda sun ga tana da tsohon ciki suna ta addu'a Allah ya sauke ta lafiya. Shi dai cewa kai yayi Amin tare da sallamarsu dan baya son hayaniya. Su kansu ma'aikatan asibitin a tunaninsu matarsa ce sai dai kuma ganin kayan jikinta duk sun kuɗe ne ya sa suka fara shakku akan haka. Tiyata ne za'a mata cikin gaggawa a ciro ɗan da ke cikinta. Dan haka Doctor ya samu Ajmal akan ana buƙatar sanya hannun mijinta kafin ayi mata aiki cikin gaggawa. Shiru ya yi tare da nazari to shi a irin wannan yanayin ina zai san inda mijinta yake, kuma bata cikin hayyacinta ballantana ta bada lambar wayarsa kuma ga shi cikin gaggawa ake buƙatar mata aikin. Ajiyar zuciya ya sauke ba tare da cewa komai ba kawai ya amshi takardar ya sa hannu. Daga nan Doctor ya ce, "Excellency ko za ka dan shiga cikin Office ɗina ka zauna ne akwai wajen zama har da wurin kwanciya ka sani sai ka huta a can." "Kada ka damu cigaba da aikinka kawai." Daga nan Doctor ya juya ya bar wajen dan komawa ciki. Ammy ce ta yi sallama a falon Dady ta shiga, yana zaune yana kallon news ya amsa mata sallamar. Ƙarasawa ta yi tare da zama gefensa tana cewa "Barka da hutawa Alhaji." Kallonta ya yi tare da cewa "Barkanki da zuwa Hajiya." Shiru ta yi kafin ta fara magana "Alhaji ko kasan inda Ajmal ya tafi ne?" "Eh na sani." "Ina ya tafi?" "Meeting ne suka je kinsan siyasa ballantana yanzu da zaɓe ke ƙaratowa suna yawan meeting. Idan kin lura tunda aka yi zaɓen primary election ya cinye yayinn da abokan karawarsa suka faɗi abubuwa suka masa yawa." "Wane irin meeting ne har bayan ƙarfe goma sha ɗaya basu dawo ba?" "Kada ki damu yana kan hanyar dawowa in sha Allah. Matarsa ta ce bai dawo ba?" "Na kira wayarta bata ɗaga ba amma nasan bai dawo ba tunda ban gan shi ba, ita kuma yanzu haka tana nan tana aikin barcin da baya isar ta." "Kada ki damu dama meeting ɗin daddare zasu yi shi, dan ya sanar da ni cewa ƙarfe tara ne zasu yi meeting ɗin zuwa 11 zasu tashi." "Wane irin meeting ne a ce sai dare ne ai bai yi ba wallahi, to yanzu ga shi ƙarfe goma sha ɗaya da mintuna arba'in da biyar bai dawo ba." Murmushi ya yi tare da cewa "Wannan ɗan gold ɗin na ji da shi, ai idan sun tashi karfe 11 ba lallai a ce ya iso gida sha ɗaya ba, sai ya ɗauki mintuna hanya kafin ya iso kuma ba lallai su tashi 11 daidai ba." Ɓangaren Umman Amatullah ma zaune ta ke sakamakon mummunar mafarkin da ta yi da Amatullah, wai Amatullah ce take ta kiran sunanta tana neman agaji. Tunda ta farka daga barcin bata iya komawa ba kenan. Kuka take dan tun ranar da Amatullah Abbanta ya Kore ta har yau Ummanta ta kasa samun nutsuwa tsawon watanni bakwai kenan. Kuma kullun sai ta yiwa Abba maganar Amatullah tun ransa na ɓaci ta dinga mata faɗa har yaO shima yanzu ya damu akan rashin ta a kusa da su. Kuma ya yi nadamar yanke hukuncin da ya yi cikin fushi, musamman da

Chapter 8 of 51