Share this page
haka ki fita harkar d'ana idan ba haka ba sai na d'aid'aita rayuwar ki na ruguzata, ko da yake rayuwarki ta riga da ta gama rugujewa, ki je ki cigaba da rainon Dan shegen da kika ajiye a gida." Amatullah kuka take yi sosai ta tashi ta nufi k'ofar fita ta fice daga gidan. Tafiya take yi ko ganin gabanta bata gani, ga shi ana kirayen sallar magrib, ga shi bata San kan unguwar ba tafiya kawai take yi bata ganin gabanta, sai kuka, wata dankareriyar mota ce ta tsaya a gaban ta, kafin ta ankare ta ji an janyo ta ta afka cikin motar, bade baki ta yi da niyyar yin ihu aka toshe mata baki. Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z 🤦‍♀️ *'YAR MAYE*🤦‍♀️ (_The drug abuser_) Na Zainab Abdullahi K.NT (Maman Ihsan) Page8️⃣9️⃣ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Amatullah kuka take yi sosai ta tashi ta nufi k'ofar fita ta fice daga cikin gidan. Tafiya take yi ko ganin gabanta ba ta yi, gashi ana kirayen sallar magrib gashi ba ta San kan unguwar ba tafiya kawai take yi ba ta ganin gabanta sai kuka take yi, wata dankareriyar mota ce ta tsaya a gabanta, kafin ta ankare ta ji an hanyo ta ta afka cikin motar, bude baki ta yi da niyyar yin ihu aka toshe mata baki. Idanunta da suke rintse ne ta bude ta sauke su akan farar fatar hannunsa da suke dauke da kwantaccen gashi, a hankali ta Maida dubanta kan fuskarsa da ke d'aure tamau. "Bana son hayaniya." Kallinsa ta sake yi a Karo na biyu kamar ba shi ne ya yi maganar ba, ajiyar zuciya Mai karfi ta sauke lokacin da idanunta suka Sauka akan fuskarsa, tattausan hannunsa da ke kan bakinta ya cire, sannan ya fara driving cikin nutsuwa, ganin ya cire hannunsa daga bakinta hakan ya ba ta damar cigaba da kukan ta. Parking ya yi a gefen hanya ba tare da ya kalle ta ba ya ce. "Ki yi mani shiru ko Kuma ki fita." Kallon fuskarsa da ke tsuke ta yi babu wasa a kan fuskarsa, don haka sai ta tsinci kanta da yin shiru sai dai ruwan hawayen da ke ambaliya a kan fuskarta, babu abunda ke tashi a cikin motar daga k'amshin turarensa sai sanyin A.C. Daidai lokacin da suka hau titi wajen wani masallaci ta ga ya yi parking a gefen titi, robar ruwa ya dauka a cikin motar ya fita, tana kallonsa ya yi alwala ya shiga cikin masallacin daidai lokacin da aka tayar da sallah. Cigaba ta yi da kukan da ta ke yi ranta na b'aci tare da Kuma tsanar mahaifiyar Munnir. Sai da aka idar da sallar sannan ya fito daga cikin masallacin ya nufi motarsa, budewa ya yi ya shiga har lokacin kuka take yi, jin a dauki mintuna bai tayar da motar ba ne ya Saka ta kallonsa, ta ga ita take kallo har lokacin fuskarsa a tsuke, ganin mugun kallon da yake mata ne ya sa ta yi saurin d'auke kanta daga kallonsa, so nawa zan fada maki ba na son hayaniya, ina ke da kafarki kika fito daga gida kika bi saurayi wani gida, shine za ki cika mani kunne da kuka da na yi maki meye?" . Shiru ta yi tana tunanin ya aka yi Ajmal ya san ta biyo Munnir ne, kuka ya aka yi ya san gidan da suka zo, shi yaushe ma ya dawo kasar ne, ko dai Umma ce ta masa kwatancen gidan, girgiza Kai ta yi don ta san Umma ba ta san gidan ba. Sanyin ba mai ba ta amsa ne ya sa ta bar tunanin zucin, Kuma tana mamakin yadda Ajmal ya canza mata yana mata magana kamar yana jin haushin ta, duk da ya ga tana cikin damuwa amma baya da niyyar rarrashinta. A haka suka karasa ya yi parking a k'ofar gidan, ta bude zata fita kenan ta ji muryarsa yana cewa. "Ki kawo mani yarona na ganshi." Kallonsa ta yi kamar ba shi ya yi maganar ba, don bai kalle ta ba ma Kuma har lokacin bai saki fuska ba. Fita ta yi daga cikin motar ta nufi k'ofar gidan nasu, bakinta d'auke da sallama ta shiga gidan, Umma da ke kokari shiga d'akin Abba hannunta d'auke da tiren abunci za ta Kai masa ne ta tsaya tana kallon Amatullah, bayan ta amsa sallamar ne ta ce "Ke da na ce kada ki kai magrib shine sai yanzu kika dawo?" Ba ta bari Umma ta kalli fuskarta ba ta yi saurin cewa. "Ki yi hakuri Umma." Daga nan kuma ta shiga d'akin ta ta rage kayan jikinta ta fito d'aure da babban towel ta Saka karamin hijbi ta fito don watsa ruwa, ruwa ta d'iba a bokiti ta nufi band'aki. Sauri-sauri ta fito ta daura alwala, ta shiga d'akin nata. Bangaren Nasreen kuwa tun ranar da ta sumbaci Ajmal har ya fisge mata gashin attached din da aka mata Kari ta nufi gida, da kuka ta shiga cikin gidan Mum din ta ta mike cikin tashin hankali take tambayarta abunda ya faru, sai a lokacin ta lura har da kawayenta da ta bari a wajen birthday sun biyo ta, ba ta yi was kowa magana ba ta wuce bedroom dinta Hakan ya saka Mum din ta ta sallami kowa ta bi bayan 'yarta. Dak'yar Mum ta samu Nasreen ta bude mata k'ofar d'akin ta shiga, duk yadda Mum ta so Nasreen ta sanar da ita abunda ya faru ki ta yi, illa iyaka ta ce sun samu sabani ne da Ajmal, don ta lura Mum za ta iya kashe mata aure ne don ba zata gyara ba sai dai ta bata, ita kuka tana son mijinta ba ta shirya rabuwa da shi ba. Amatullah sam ta mance da ta bar Ajmal a waje cikin mota, yana jiran ta kawo masa d'ansa, don tunda ta fito wanka ta dauro alwala ta gabatar da sallar magrib, ta zauna tana azkar. Yana zaune a motarsa har aka kira sallar isha'i ya fita ya nufi wani masallacin dake cikin unguwar. Tana idar da sallar isha'i ta kwanta a Saman sallayar, Umma ce ta shigo bakinta d'auke da sallama, tana rungume da Khalifa. Kallon Amatullah ta yi tare da cewa. "Lafiya kike kuwa?" "Lafiya lau Umma." "Na ga kamar kina da damuwa." "Ba komai Ummata." "To yaron nan fa yana bukatar ki bashi Mama ya Sha." Yamutse fuska ta yi tare da cewa "Umma don Allah ki bashi Madara ya sha." "Amatullah tun safe da kika bashi Nono ya sha baki sake bashi ba shin baya damunki ne?" "Murmushi ta yi kawai don nonon nata sun cika har sun fara mata ciwo sai dai ba za ta iya bashi ba yanzu, ta rasa me ke mata dadi. Fita Umma ta yi kasancewar akwai madararsa a dakinta ta debi ruwan zafi ta hada masa a bulunboti ta fara bashi. Sallama ta ji daga tsakar gidan, don ta ji muryarsa kuma ta gane wane ne, don haka ta ce. "Wa'alaika salam, sannunka da zuwa." K'ofar d'akin Umman ya karaso Inda ta ce masa ya shigo ciki, bakinsa d'auke da sallama ya yaye labulen d'akin ya shiga. Durkusawa ya yi cikin girmamawa ya gaida Umma, ta masa tana masa ya su Amminsa. Har lokacin tana bawa Khalifa Madara. Kallon gudan jinin nada ya yi cike da kaunarsa, yana ta shan madara abunsa. Amatullah dake kwance a dakinta Saman sallaya ta ji muryarsa sai da gabanta ya fadi, sam bacin rai da take ciki ya hana ta tuna da yana waje yana jiran ta Kai masa yaronsa, tsawon awa daya Kenn ta barshi, lumshe idanunta ta yi tana tuna irin cin mutunci da Mom din Munnir ta mata, tana Kuma tunanin zaman da zasu yi da matar idan har Munnir ne ya aure ta. Bayan Umma ta gama bashi madara ya koshi ne ta gyara masa jiki sannan ta miko masa shi tana cewa. "Je ka gaisa da Abbanka ko?" Karbar yaron ya yi yana sakin murmushi don har ga Allah Umma ba karamin burge shi take yi ba. Sai da ta ajiye masa abinci da ruwa . Fita ta yi ta nufi d'akin Amatullah da sallama a bakinta, amma ta yi Nisa a duniyar tunanin ba ta ma san Umma ta shigo ba, sai da ta taba ta, mamaki ne ya kama Umma ganin hawayen dake kan fuskar Amatullah. "Tashi ki je ku gaisa da Abban Khalifa anjima zamu yi magana." Daga nan Umma ta fita ta nufi d'akin Abba don ta ga takalminsa alamar ya dawo. Amatullah goge hawayen da ke kan fuskarta ta yi tare da gyara zaman hijab dinta sannan ta fita bayan ta dauki wayarta. Da sallama ta shiga d'akin Umma, ciki-ciki ya amsa mata yana rungume da d'ansa, zama ta yi a Saman tabarmar da ke d'akin wanda Ajmal ke zaune a kai,cikin sanyin murya ta ce. "Ina wuni.' Bai amsa mata ba sai cigaba da wasa da yaronsa da yake yi, kallonsa ta yi ta ga ko Inda take bai kalla ba, ita ta rasa me ta masa haka tunda ya dauko ta a mota yake jin haushin ta, yanzu ta gaishe sa ko kallo ba ta ishe shi ba. "Me ya faru na ga kin fito daga wancan gidan kina kuka?" "Gidansu Munnir ne mun..." "Na sani." Kallonsa ta yi tare da tunanin ta ya ya ya san gidan da abunda suka je yi, ko dai Aljani ne shi. "Me yasa kika fito ke kadai Kuma kina kuka?" "Mahaifiyarsa ce ba ta Sona?" Shiru ya yi yana kallonsa tare da nazarin kalamanta, don har k'walla sun cika idanunta. "Me ta ce maki?" Nan ta kwashe yadda suka yi ta sanar da shi, taune lips dinsa ya yi idanusa a lumshe. "Ke Kuma kina son d'anta ko?" Tura baki ta yi tare da cewa "Ai na fad'a maka a waya." "Amma shine kika kwashi jiki kika bishi ko?" "Dole ne ba yadda zan yi tunda Abba ya amince." Tayi magana tana kuka. "Zan tafi idan kin samu nutsuwa gobe sai na zo mu tattauna abunda ta kawo ni, Ina fatan za ki bani hadin kai." Zuwa lokacin har Khalifa ya yi barci a jikinsa, kwantar da shi ya yi Saman doguwar kijera sannan ya yi masa kiss a goshi ya fice daga d'akin, don har lokacin ma haushin Amatullah ya ke ji, don ya sanar da ita a waya ta bari idan ya zo sai su san abun yi, amma ta tashi ta shiga motarsa har gidansu gashi an wulakanta ta. Yana fita ya ga Umma na fitowa daga d'akin Abba. Kallon ta yi tare da cewa "Abba na nan ne?". "Eh yana ciki." Baking kafar ya karasa suka gaisa da Abba sannan ya masu sallama ya fice. Bangaren Munnir bayan ya Isa Inda Mom ta aike shi sai dai aka sanar da shi Hajiya Kubra ba ta nan, ya kira Mom ya sanar da ita bata nan zai dawo, Mom ta hana ya nuna mata cewar ya bar Amatullah ta ce tana kula da ita ya bari ta zo, ba don ransa ya so ba har aka kira magrib ya yi sallah sannan ta dawo ta sallame shi ta bashi sakon Mom dinsa. Ko da ya koma gida bata nan ya tambayi Mom ina Amatullah ta ce ai ta Saka direba ya mayar da ita gida bai so ba ya so bin bayan ta, Mom ta hana shi dole ya hakura sai dai ya yi kokari Kiran wayarta ba ta shiga. Lokacin da Umma ta shiga d'akin ta tarar da Amatullah na kuka. Hannunta Umma ta rike cikin sanyin murya ta ce. "Amatu wai me ke damunki ne, kin saka ni cikin damuwa, ko kina da wanda za ki fadawa damuwarki bayan ni ne?" "Umma mahaifiyarsa ba ta so na." "Wa kenan?" "Shi." "Kin ga ki yi mani bayani yadda zan gane, shi wa?" "Umma wai idan mace ta yi ciki ta haihu Kuma ba ta da miji shikenan ta zama 'yar iska a idanun mutane? Umma me ya sa wasu mutane ba su bincike kawai suke yankewa mutum hukunci, Allah ya sani ni ba 'yar iska ba ce ban taba aikata fasikanci ba tsautsayi ne da Kuma kaddara amma me ya sa mutane suka kasa fahimta ta Umma?" Nan ta kwashe abunda ya faru ta sanarwa mahaifiyarta. Ta karasa maganar tana sakin kuka mai cin rai. K'walla ce ta tausayin 'yarta ta d'auke da yatsar hannunta, sannan ta sake rike hannunta da kyau ta ce "Amatullah na san cewa ke baiwar Allah ce mai yadda da kaddara Mai kyau ko mara kyau, Kai kina godiya da duk abunda Allah ya aiko maki da shi mai dadi ko mara dadi, mai jiran kaddara duk rad'ad'inta ki had'iye ta, kina umarni da kyakkyawa kiyi hani da mummuna, duk ma wanda ya maki wannan fahimta rashin sanin wace ce ke ne, saboda haka kada maganar mutane ya dame ki, ki manta da wannan zancen kada ki Saka shi a ranki, Kuma in Sha Allah zamu tattauna da mahaifinki akan wannan zancen, don a gaskiya akwai matsala tunda har mahaifiyarsa ta iya maki haka don gudun abunda zai je ya dawo." Cikin sanyin jiki ta tashi ta nufi dakinta tana tunanin yadda zamansu zai kasance da Munnir, da mahaifiyarsa, ga Abba kaifi d'aya ne. Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z 🤦‍♀️ *'YAR MAYE*🤦‍♀️ (_The drug abuser_) Na Zainab Abdullahi K.NT (Maman Ihsan) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️* Page9️⃣0️⃣ Cikin sanyin jiki ta tashi ta nufi d'akin tana tunanin yadda zamansu zai kasance da Munnir da mahaifiyarsa ga Abba kaifi d'aya ne. A ranar dai ki abincin kirki ba ta ci ba haka ta kwana, barcin kirki ma ba ta samu ta yi ba, daga karshe dai tashi ta yi tsakar dare ta dauro alwala ta zo ta fara gabatar da sallolin nafila, ba ita ta kwanta ba sai karfe hud'u na asuba barci ya d'auke ta a Saman sallayar. *ADAMAWA* Tun da Ajmal ya bar gidan Marka ke ta masifa tana zaginsa daga shi har Amminsa. Wayarta ta dauka ta nawa Nihal tana cewa. "Karb'i ki kira mani ubansa, idan shi ban isa da shi ba ai na isa da ubansa, karbar wayar Nihal ta yi cikin rawar jiki ta lalubo lambar wayar Dad ta danna masa kira. kasancewar lokacin Dad ya koma barci Kuma wayar na silent ne ya sa bai san an kira ba, sai da aka masa kira uku bai daga ba sannan Nihal ta kalli Marka tana cewa. "Bai d'aga ba ina tunanin ya kwanta kamar I yanzu." Tsuki Marka ta ja tana cewa. "Barshi anjima zai d'aga ai. Zan yi magana da shi ne idan kuma shima bijire mani zai yi kamar yadda d'an uwansa ya bijire mani a shekarun baya ya zabi mace ai kaina ne to zan sani." Kallonta Nihal ta yi tare da cewa. "Marka wai dan Allah wani d'anki ne ya bijire maki, ban taba sanin sa ba Kuma..." Tsawar da Marka ta daka mata ne ya da hanjin cikinta ne ya kad'a ganin yadda idanun Marka suka canza launi zuwa ja, ta fara magana cikin kausashshiyar murya tana cewa. "Ka da ki sake mani magana akan sa 'ya'yana guda biyu ne Ibrahim da Laila, don haka ka da ki sake mani tambaya akansa, a waje na ya dade da mutuwa." Daga nan ta nufi bedroom dinta Nihal ta bi ta da kallo. Bayan awa d'aya da faruwar haka Dad ya kira Marka kasancewar ya farka ya ga missed calls dinta, bayan ta daga ne ya yi mata sallama, ba ta tsaya amsa masa sallamar ba ta fara fad'a. "Ibrahim wace ni a wajenka?" Cikin sanyin murya Dady ya ce "Mahaifiyata." "Na isa da kai ko ban isa ba.?" "Shiru ya yi na dan lokaci kafin ya ce. "Ai ba abunda za ki unarce ni da shi na bijire maki." "Me ya Saka danka ban isa da shi ba?" "Kiyi hakuri dan Allah." "To idan ban yi hakuri ba ya kake so na yi ne, yaro gaba d'aya bai san girman manya ba, irin tarbiyyar da waccan kakar ta sa mai jajayen kunnuwa ta bashi kenan ko? Wato sai abunda ransa ya masa ne kawai zai yi ba wanda ya Isa ya tursasa shi ko? To ka sanar da shi aure da Nihal ko yana so ko yana k'i sai anyi shi, sai dai idan aka Kai masa ita gidansa ya yi gunduwa-gunduwa da naman jikinta." Shiru Dady ya yi ya ma rasa abun cewa, jin shiru ne ya Saka ta cewa. " Ibrahim ko baka ji na ne?" Ajiyar zuciya ya sauke sannan cikin kwantar da murya ya soma magana. "Kiyi hakuri karshen watan nan zan zo ADAMAWA sai mu tattauna akai." "Allah ya kawo ka lafiya." Ameen ya amsa sannan ya mata sallama ya kashe Kiran wayar. "Umma kuwa kasa isashshen barci ita ma ta yi, don gaba d'aya zancen mahaifiyar Munnir ne ya tsaya mata a rai, ta rasa wace irinn suruka ce Amatullah za ta hadu da ita, gaskiya har yanzu rayuwar Amatullah akwai sauran kalubale, sai dai ta yanke shawarar za ta samu Abban Amatullah da zancen don gaskiya ba za ta yarda Amatullah ta auri mutumin da mahaifiyarsa ba ta son ta ba." Hakan kuwa aka yi da safe bayan Mallam Abdullahi ya karya kafin ya fita ne Umma ta shiga dakinsa bakinta d'auke da sallama. Amsawa ya yi ta shiga ta same shi zaune a Saman sallayar ya kunna radio yana sauraren labaran BBC. Ganin kamar akwai magana a bakinta ya Saka shi kashe radion tare da zuba mata idanu bayan ta zauna a gefen sa. "Ummu Amatullah ya aka yi ne, tun dazu na lura kamar akwai magana a bakin ki ko?" Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta dube shi cikin nutsuwa ta fara magana. "Dama Mallam akan zancen Amatullah ne da Munnir da ake Shirin aura masa ita, ya kamata ka duba lamarin nan da kyau, duk da shi yaron dai bai da wata matsala da ba zamu bashi auren Amatullah ba, amma mahaifiyarsa ce matsalar." Nan ta kwashe duk abunda ya faru ta sanar da shi. Nisawa ya yi tare da dogon tunani kafin ya kalle ta ya ce. "Yanzu ya kike so a yi?" "A gaskiya ban yarda 'yata ta auri yaron da mahaifiyarsa ba ta kaunar ta ba, don ba abunda ba za ta iya aikata mata ba, don duk matar da ta yi haka babu tawaru'u a cikin zuciyarta. Kawai ni dama tun farko na So a ce ta auri uban d'anta, su rufawa juna asiri ya aure ta su reni d'ansu da kansu, ta yadda ba wanda ma zai yi tunanin cewa ba ta hanyar aure suka haifi yaron ba, don yana kaunar d'ansa Kuma na tabbata ba zai iya banbanta shi da sauran 'ya'yan da zasu haifa ba. Kuma ka ga ai yaron dan mutunci ne a zamanin ga da muke ciki mafi yawan mazaje da sun lalata rayuwar mace shikenan sun gama da ita, ba za su sake waiwayarta ba sun samu abunda suke so, ko da ta samu ciki fa to ba zasu yarda a danganta su da yaron ba zasu guji yaron ne su nina kiyayyarsu akan yaron, amma ka ga shi da ke d'an mutunci ne bai guje ta ba ita da d'nta, ko da ya aure ta ba wanda zai san cewa ba ta hanyar aure aka same shi ba sai makusantarsa da suka San da zancen. Idan Kuma Munnir ta aura Kowa sai ya san ce cewa ta taba yin ciki kafin auren tunda sun da wani yaron ta tafi kuma shi Munnir din ai ba tabbas ko zai k'unace yaron ka da ya nuna masa tsana ko ya dinga nuna banbanci tsakanin sa da sauran 'ya'yan da zasu haifa. Ka yi nazarin maganar da na maka." Kallonta Mallam Abdullahi ya yi ganin ta yi shiru ya ce. "Kin gama?" Shiru ta yi tana fargabar maganar da za ta fito daga bakinsa. "To na ji maganganun da kika yi kuka na fahimci Inda kika dosa, a zahirin gaskiya mahaifiyar Munnir ba ta kyauta ba amma wannan bai zama babban dalilin da zai Saka na canza magana ta ba, domin ba ta da matsala da Munnir sai da mahaifiyarsa, Kuma ya kamata ki sani ba da mahaifiyar Munnir za ta yi zaman aure ba da Munnir za ta yi, Kuma ba gida d'aya za su zauna ba don ya sanar da ni ya kammaka gininsa, to ki kwantar da hankalinki ki yi masu addu'a." "Amma Mallam ba ka ganin kiyayyar da take wa Amatullah ba zai shafi yaran da za su haifa.?" "Kin ga ki bar maganar nan kawai, ai Munnir bai cancanci mu hana masa Amatullah ba, ki duba tsawon lokacin da yake son ta idan wani ne lokacin da ya ji labarin yarinyar da zai aura ta yi cikin shege ga shaye-shaye har mahaifinta ya Kore ta da cikin shege tsawon lokaci ba ta nan, ba wanda ya san Inda take, ko da ya hadu da ita har ta haihu ki fad'a maza nawa ne zasu iya wannan jihadin su aure ta bayan ta dawo?" Nisawa ya yi tare da cewa. "Saboda halaccin da ya yi ne ya Saka ba zan iya hana shi auren Amatullah ba, sai dai idan shi ne ya ce ya fasa." Shiru Umma ta yi daga bisani ta ce. "Allah ya tabbatar muna da abunda yafi zama alkhairi." Da Ameen ya amsa yayin da ta tashi ta fice daga d'akin. Bangaren Ammi kuwa zaune take a dinning table ta kasa yin breakfast, tun da Dady ya sanar ita yadda suka yi da Marka sai hankalinta ya tashi, don ta san dole tilon d'anta zai shiga cikin damuwa, don ta san halinsa idan baya son abu, don ita shaida ce baya kaunar Nihal ta ya ya za'a hada su aure, ta san a halin yanzu Amatullah ce kadai a cikin zuciyarsa, ga shi ta ji labarin anyi wa yarinyar baiko da wani, to ya makoman d'an nata don ta so a ce shine ya aure ta ko don su kula da d'ansu Kuma jikanta. Wayarta ta lalubo ta nemo lambar shalelen nata ta danna masa kira Rurin da wayar ke yi ne ya farkar da shi daga barci, a hankali ya bude idanusa ya sauke akan wayar, don dama ya kashe duk wayoyinsa, don baya son damuwa, waya data ya bari a kunne wacce ya san ba kowa ne ke da lambar ba sai na jikinsa Ganin Ammi ce ya sa ya dauki wayar da sauri ya Kara a kunne tare da yin sallama. "Assalamu alaikum Ammina." "Wa'alaika salam rabin raina." Gaishe da ita ya yi ta amsa cikin sanyin murya. "Ammina lafiya kuwa?" "Ba ta bashi amsa ba ta ce masa. "Wai ya zancen Amatullah ne har yanzu ba ku samu matsaya ba?" Girgiza mata Kai kawai ya yi kamar tana kallonsa kafin ta cigaba da cewa "Kwanakin baya sai da na ce Dadynka ya je ya nemo maka auren yarinyar ka ce a dakara tukunna, ai ga na hausawa nan a bari ya huce shi kr kawo rabon wani." Murmushi Ajmal ya saki cike da kwarin guiwa ya ce. "Ammina Amatullah tawa ce in Sha Allah. A baya dalilin da ya Saka na ce maki a dakata saboda na san mahaifinta ya riga ya yi alkawainn bawa yaron aurenta ko Dady ya je abunda zai fad'a kenan." "To yanzu ya ake ciki?" "An Saka masu rana da yaron sai dai Mahaifiyar yaron ba ta son d'anta ta auri Amatullah infact dai ba ta kaunar ta, jiya suka je gaishe da ita." Nan ya sanar da Ammi yadda Amatullah ta bashi labarin komai, Ammi ma ba ta ji dadi hakan ba kuma ta ga rashin kyautawar mahaifiyar Munnir din. "Ya kuka yi da Marka ne ta sanar da Dadynka zancen auren ka da Nihal." "Ammi ki rabu da wannan tsohuwar don ba zan taba auren Nihal ba sai dai Amatullah. Duk abunda za ta yi ta je ta yi ta yi ba za ta nuna mani mulkin mallaka ba." "Amma ai ta isa da mahaifinka ko.?" "Ta isa da shi Ammi." "Shi kuka ya isa da kai ko?" "Eh Ammi amma ba zan taba auren Nihal ba za ta yi ta gama." "Ka ga don Allah ka bi ta a hankali bana son abunda zai d'aga Mani hankali." "Shikenan Ammina." Daga haka suka taba fira kafin suka yi sallama. Zuwa lokacin har abincin da mai aikin ta zuba mata har ya yi sanyi. Da misalin karfe sha d'aya na rana wata dankareriyar mota ce ta yi parking a k'ofar gidan Mallam Abdullahi, jingina bayansa ya yi jikin kujerar motar da yake zaune mazaunin direba idanunsa ya lumshe kamar mai barci ba

Chapter 40 of 51