ta tashi ta bar wajen a guje.
Mai da bindigarsa ya yi tare da cewa.
"Kin san su ne?
Girgiza kai ta yi idanunta ne zubar da hawaye.
"Sun yi maki wata magana ne?"
"Tambaya ta suka fara yi wai ni ce Amatullah, na amsa cewa ni ce shine ne suka ce na basu babyn su tafi da shi ko kuma su kashe ni kuma su tafi da shi."
Mamaki ya ke yi yadda suka zo karɓar babyn? To wa ya aiko su?
Kallonta ya yi tare da cewa
"Baki ji ciwo ba ko?"
Kai ta girgiza masa kawai."
"Babyn fa kamar kin danne shi ko?"
"A'a akan hannuna ne na faɗi."
Mota suka shiga inda ya miƙa mata babyn daga nan suka bar wajen, zuciyarsa sai saƙe-saƙe take yi su waye su kuma wa ya turo su.
Har suka isa gida bayan sun yi fito daga motar ne ya miƙa mata babyn, ta amsa ta nufi ɓangaren ma'aikatan gidan, hannunta ɗaya rataye da jakkar magunguna da aka basu.
Ahmad ya nufi cikin gidan kai tsaye part ɗin Ammi ya nufa. Knocking ya yi ta bashi izinin shigowa.
Zaune ya same ta akan kujera yayin da da Ajmal ke zaune a saman carpet fuskarsa ba walwala. Da alama Mun faɗa take masa.
Da sallama Ahmad ya shiga falon inda suka amsa masa su duka a tare. Murmushi Ammy ta yi tare da cewa.
"Ahmad har kun dawo?"
Daidai lokacin da Nihal ke fitowa daga bedroom ɗin ta, ta ƙaraso tare da kwanciya akan cinyar Mom.
"Eh mun dawo Ammi."
"Kun samu ganin likita?"
"Eh mun gan shi Ammi."
Shiru ya yi tare da wani tunani kafin ya ce,
"Ammi akwai wadanda suke sarautar rayuwar babyn nan."
Da mamaki ta lalle shi kafin ta tamabaye shi cewa.
"Ban gane me kake son cewa ba."
Nan ya bata labarin duk abinda ya faru daga zuwansu ganin likita a office ɗin sa har dawowarsa da ya hange ta tana gudu.
Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa
"To su waye su?"
"Wallahi ban sani ba, sun gudu. sai dai da dukkan alamu ba Amatullah ce a gabansu ba wannan jaririn suke farauta."
Da mamaki Amma ke jinjina lamarin tare da kallon Ajmal ta ga ya yi shiru amma da alamar yana sauraren su.
"Rabin raina ba ka ji me Ahmad ke faɗa ba?"
"Ammi ina ji."
"To yanzu me kake tunani?"
"Ammina ba abinda nake tunani domin ban san wace ce ita ba, ban san me ye shirinta ba, ta yiwu wadanda suka aiko ta wajen mu ne su..."
Kallon da Amminta masa ne ya sa ya yi shiru bai ƙarara maganar ba, inda Nihal ta ɗora da cewa.
"Ammi ki bar shi ya faɗi gaskiya yarinyar nan kwata-kwata ban yarda da ita ba, zubin munafukai ne da ita ki ganta tana ta sunkuyar da kai, daga ganinta ba ta da gaskiya turo ta aka yi shi..."
"Ya isa Nihal."
Anmi ta faɗa da kakkausar murya. Kafin ta mai da sunanta zuwa ga Ahmad ta ce
"Ka kawo ta nan."
Fita Ahmad ya yi inda Anmi ta cigaba da yiwa Ajmal faɗa cikin harshen larabci.
Yayinda da Nihal ba ta so hakan ba, ta so ne a ce ta yi da yaren da ta ke ji, ko ba komai za ta san me suke tattauna.
Zuwa can sai ga Ahmad ya shiga da sallama, yayin da Amatullah ta biyo bayansa ita ma sallamar ta yi, suka amsa masu a tare.
Cikin girmamawa ta duka har ƙasa ta gaida Ammi. Ta amsa mata cike da fara'a tare da karbar babyn.
Satar kallon Ajmal ta yi tare da cewa
"Ina wuni?"
Idanunsa na kan waya bai kalle ta ba ballanta ta saka ran zai amsa. Kallonsa Anmi ta yi tare da cewa.
"Ba ka ji tana gaishe ka ba ne?"
"Lafiya lau."
Ya amsa har lokacin bai lalle ta ba.
Kallo Nihal ta yi tare da cewa.
"Ina wuni Aunty?"
"Ke! Wace ce Aunty ta ki? Ko kallona ka da na..."
Anmi ta dakatar da ita ta hanyar cewa
"Nihal."
Kallon Anmi ta yi tare da cewa
"Na'am."
"Ki na son mu samu matsala da ke?"
"A'a ba na so."
"To ki daina wannan halin ba na son shi ɗan Adam daraja ne da shi, ka da ki taba wulaƙanta shi."
"Ki yi hakuri Ammi."
Tashi ta yi daga cinyar Ammi ganin Anmi na son ɗora babyn akan cinyarta.
Kallon Ajmal ta yi tare da yi masa magana da harshen larabci ta ce,
"Wane suna za ka sakawa yaron?"
Da mamaki ya kalle ta tare da cewa.
"Sunan kamar yadda ko wane mahaifi ke sakawa ɗansa."
"Amina wai kina nafin cewa kin yarda da maganar da mutane suke faɗa kan cewa wannan yaron ɗana ne?"
"Ba haka nake nufi ba, amma ina mai umartarka da ka yi wa yaron huɗu ba."
Buɗe baki ya yi da niyyar yin magana sai ta katse shi da cewa.
"Umarni ne."
Ta faɗa babu wasa a fuskarta, baƙin ciki ne ya cika masa zuciya dan shi har yanzu bai yarda cewa yana da wani ɗa ba.
Amatullah ce kawai a wajen ta fahimci maganar da suke yi, kasancewar tana ɗan jin larabci duk da ba sosai ba, amma a islamiyyarsu shi malamai ke masu, kuma tana yawan karanta littafan larabci da fassara. So ta fahimci zancen da Ajmal ke yi da Amminsa.
Kallon Ammimsa ya yi tare da cewa
"Shikenan."
Miƙa masa yaron ta yi tare da cewa ga shi nan.
Kallon yaron ya yi na tsawon mintuna biyu ba tare da ya ƙyafta idanu ba.
Maida dubansa ya yi zuwa ga Amminsa cikin wani irin murya da ke bayyana rashin jin daɗinsa ya ce,
"Wane suna za'a saka masa?"
"Ka tambaye ta idan akwai sunan da take so."
Kallonta ya yi kanta a sunkuye ya ce,
"Wane suna kike so a masa huɗuba da shi?"
Muryarta na rawa ta ce,
"Ba na da sunan da nake son a saka masa."
Dubansa ya mai da ga Ammimsa jin me za ta ce. Sai ya ji tana cewa.
"Amatullah wane suna kike son a sa..."
Kafin ta ƙarasa maganar ne ta ji muryar Amatullah cikin kuka tana cewa.
"Duk sunan da aka saka masa na amince Allah ya albarka ce shi."
Anmi ce ta amsa da Amin sannan ta kalli Ajmal ta ce,
"Ka saka masa ko suna mai kyau."
Shiru ya yi dan bai san me zai ce mata ba. Sai zuwa can ya ji muryarta tana cewa.
"Ka saka masa BAWAN ALLAH."
Jinjina kai ya yi tare da cewa
"To Ammina."
Daga nan ya yi masa huɗuba da Abdullah.
Miƙawa wa Amma babyn ya fita.
Anmi ta kalli yaron tare da masa addu'ar Allah ya raya shi ya.
Ranar da suka cika sati ɗaya ne aka yanka masa manyan raguna guda biyu, wannan aikin Dad ne, inda guda ɗaya aka gyarawa mai jegon ita kaɗai, aka soya aka kai mata har ɗakinta.
Ɗayan kuma aka rabawa sauran jama'a har ma'aikatan gidan.
Ranar Ammi ta ce Amatullah ta zo part ɗinta, nan ta fito mata da tsaddun kaya kala biyar da ta saka aka ɗinka mata, haka Abdullahi ma.
Ranar Ammi ta nuna mata gata sosai da sosai, ta samu kulawar da kowace mai jegon take buƙata.
Tana zaune ita kaɗai a bedroom ɗin Ammi ta ci kwalliya cikin wani tsadadden leshi wanda aka mata ɗinkin riga da siket. Musamman Ammi ta kira mai makeup ta mata kwalliya.
Sannan ra gayyaci nurse guda biyu da suka kula da Amatulla, kasancewar su ma 'yan mata ne kuma ta ga sun nuna kulawarsa kanta, da alama ta ku ta zo ɗaya.
Suka zo kuwa inda suka zauna a falon Ammi suka dinga janta da fira, har ta sake jiki da su ta yi nishad'i a ranar wanda ta mance tun wani tsawon lokaci ne ba ta yi nishad'i haka ba. Har suna tsokananta musamman da suka ga ta canza sosai ta yi kyau a cikin sati ɗaya.
Tunawa da ta yi lokacin da ta dinga garamba a cikin garin Kaduna, ga ciki ga ba wajen kwana, ga yunwa har wasu na mata kallon kamar mahaukaciya ce ita, amma yanzu ga shi Amma ta mata gata ta gama mata komai.
Yanzu babban birninta daya ne ta koma wajen iyayenta Abbanta ya yafe mata ta karɓe ta a matsayin 'yarsa.
Sai dai ta yaya idan suka ganta da yaro za su karɓe ta, da cikin ma ya suka kare ballantana ga goyon yaro. Ta ya ya za ta fuskanci iyayenta anya ba gudawa za ta yi ta bar su da yaron nan ba.
Tana tsaka da tunaninta kenan ta ji an dafa ta, juyawa ta yi tana duban Saliha wacce ta dafa ta, murmushi suka sakarwa juna inda take cewa
"Ƙawata tunanin me kike yi?"
"Ba komai."
Jinjina kai ta yi tare da cewa
",Ki rage damuwa kin ji."
Madina ma ta ce
"Gaskiya ki faɗa mata kam, dan zai iya zama maki wani ciwon."
Daga haka suka dinga janta da fira har ta saki jiki.
Fira ta yi daɗi suka shagala da fira har da dariya.
Ajmal ne ya shigo falon sanye yake da gezner fara a jikinsa, fuskarsa sanye da farin glass sai yayin da kwantaccen sahensa ya kwanta luf akan fusakrsa. Baƙar hula ce akansa, wanda daga bayansa kana gannin kwantaccen gashin kansa ta ƙeyarsa, hannunsa sanye da agogon Diamond. Ƙafarsa sanye da baƙin takalmi ƙafa ciki, ya yi kyau sosai kwarjinsa da haibarsa ba za su bari mai kallomsa ya ɗauke ido daga kallonsa ba.
Gaba ɗaya sun shagala da fira, har ya wuce su a falon Ammi ba su ga shigowrsa ba, sai da ya shiga hankalin su ya dawo sakamakon jin daddaden ƙamshin turarensa ya ratsa su.
Amatullah ce ta ce
"Na ji kamar mutum ya shigo."
Madina ta ce,
"Maybe Ammi ce."
Ji ta yi kamar kukan Abdallah daga cikin bedroom na Ammi. Ta shi ta yi bayan da kalli Saliha da Madina ta ce,
"Ina zuwa."
Ta nufi hanyar bedroom ɗin.
A can cikin bedroom ɗin kuwa Ajmal na shiga ya tarar da Baby na ta kuka sosai, kallon yaron ya yi ya ɗauke kansa, ganin Ammi ba ta ciki da alamar ba kowa a cikin dakin ya sake kallon Abdallah.
Juyawa ya yi da nufin barin ɗakin sai kuma ya ji zuciyarsa ba ta kwanta ba, dan haka ya nufi wajen Babyn ta miƙa hannu ya ɗauke shi.
Amatullah ce ta turo ƙofar ta shigo cikin ɗakin bakinta dauke da sallama.
Ba tare da ya kalli mai shigowa ya amsa.
Jin yaron na kuka ne ya sa ta ƙarasa wajensa tare da miƙa hannu alamar ya ba ta yaron.
Ɗagowa ya yi ya kalle ta, idanunsu ne suka sarƙe cikin na juna, wanda kowanne su ya kasa cire idanunsu daga cikin na dan uwansa.
Kukan yaron ne ya dawo da shi hayyacinsa. Tsuke fuska ya yi tare da watsa mata mugun kallo, miƙa mata yaron, ya nufi hanyar fita.
Bin bayansa ta yi da kallo tana taɓe baki.
Wayarsa ce ta fara ruri lokacin da ya isa babban falon, ya ciro wayrsa daga aljihunsa ya duba. D.P.O ne daga Minna.
Ɗagawa ya yi tare da karawa a kunnensa ya ya fara magana.
"Hello D.P.O akwai wani labari ne?"
Daga can ɓangaren D.P.O yana zaune a ofishinsa ya ce,
"Da ɗuminsa kuwa. Yanzu zan muka samu labarin IN DA RANKA yake, ashe ma yana kusa da kai bamu sani ba.
*Daga alƙamin*✍️
Zainab Abdullahi KNT
(Maman Ihsan)
09065327995
Comments & share
Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
🤦♀️ *YAR MAYE*🤦♀️
(_The drug abuser_)
*NA*
Zainab Abdullahi KNT
(Maman Ihsan)
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*GARGAƊI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
Ban yarda a karanta mani shi a youtube ko a maida shi audio ba tare da izinina ba.
*BISIMILLAHI RAHMANI RAHIM*
Page4️⃣8️⃣
Da ɗuminsa kuwa. Yanzu nan muka samu labarin INDARANKA yake, ashe ma yana kusa da kai ba mu sani ba."
Bakinsa har rawa yake yi wajen cewa.
"A ina yake!?"
"Ashe wai ƙauyansu a jaharku take."
"Me ye sunan ƙauyen?"
"Wani ƙauye ne wai shi Garun gabas."
Ajmal ya nanata sunan a cikin zuciyarsa.
'Garun gabas.'
"Ka taɓa jin sunan ƙauyen ne?"
Kai ya girgiza tare da cewa.
"A'a."
Daga nan ne D.P.O ya ce,
"Mun samu wannan sanarwar ce ta bakin abokinsa da ya zo ya ce muna ya tuna sunan ƙauyen."
Godiya Ajmal ya masa tare da katse kiran wayar ya nufi hanyar fita. Yadda ya fita ne a yanayinsa security ɗinsa suka gane ba lafiya. Dan idan sun gansa a irin wannan yanayin to sun san fitar ta daban ne.
Dan haka suka ƙarasa wajen motocinsa yayin da Ahmad ya budewa Ajmal motar da zai shiga. Yayin da shima ya shiga ya zauna gefen Direba. Sauran security kowa suka shiga cikin motocin, inda suka shirya motoci biyar har da na Ajmal.
Ammi dake zaune a falon Dady tare da Dady ta ji karar buɗe gate. A zuciyarta ta ce,
'ina kuma zai tafi?"
Kallonta Dady ya yi tare da cewa
"Kina tunanin shalelen yaronki ne?"
"Eh na ga a cikin yanayin damuwa da yake ciki bai cika fita ba, amma yau na ga ya fita, sai nake ji kamar ba lafiya ba."
Murmushi Dady ya yi tare da cewa.
"Zaman gidan ne nake gani ya ishe sa, mutumin da bai saba zama ba."
Wayarsa ya ɗauka tare da dannawa ya kira wata lamba.
D.P.O yana zaune a ofishinsa wayarsa da ke kan table ya fara ruri, dubawa ya yi tare da ɗaukar kiran wayar
"Hello barka da yammaci yallai."
"Yauwa barka dai, ya aiki?"
"Mun gode Allah."
"Kana ina ne yanzu?"
"Ina ofishina ne."
"Idan ba damuwa ko za ka iya zuwa ka same ni a guest house ɗina yanzu."
"Ba damuwa ina nan zuwa yanzu in sha Allah."
Daga nan ya katse kiran wayar, suka nufi guest house ɗinsa.
*MINNA NIGER STATE*
Kwance take a tsakar gidan akan tabarma, duk ta rame kamar ba ita ba. Wata maƙociyarsu ce ta shigo gidan bakinta ɗauke da sallama.
"Assalamu alaikum"
Umman Amatullah dake kwance kan tabarma ne ta amsa mata sallamar ta ta.
Ƙarasawa ta yi wajen tabarmar tare da cewa.
"Umman Amatullah ina wuni."
Da ƙyar ta iya amsa mata gaisuwar da take mata.
Kallonta ta yi tare da cewa
"Anya kina cin abinci kuwa?"
Girgiza kai ta yi tare da cewa,
"Wannan ciwon nawa ba na yinwa ko magani ba ne. Babban maganin da zai wariyar da wannan ciwon nawa shi ne na ga Amatullah. Ban san wani hali take ciki ba, tunda Mallam ta Kore ta ta bar gidan nan ni na san har yau ba mu ji labarin ta ba wanda da ya san halin da take yi ciki."
Ta ƙarasa maganar tare da cewa da zuba hawaye.
Tausayinta ya kama Inna Rabi, cikin tausayawa ta fara magana.
"Ka da ki damu ki yi ta yi mata addu'a ba dare ba rana, in sha Allah ba za ta fadi ƙasa banza ba, addu'ar ki ne zai ta bibiyarta a duk inda take."
"Wallahi kullun a cikin yi wa Amatullah addu'a nake ba dare ba rana, ina addu'a Allah ya kare ta a duk inda take, yanzu ne watan haihuwar cikinta, yanzu ban san a wane hali take ciki ba, ta haihu ne ko kuma cikin ya zube ko ma ta rasu wajen haihuwar cikin ban sani ba, saboda ina yawan yin mugayen mafarki da ita . Ga shi bata san kowa ba ina zata dosa ne a cikin rini wannan halin da ta tafi yanzu tana ina be, su waye suka san halin da ta ke ciki ba."
Ta ƙarasa maganar tana matsanancin kuka, tausayinta ne ta kama Inna Rabi, nan ta dinga rarrashinta tare da bata baki.
Ba abinda Umman Amatullah je yawan tunawa kamar lokacin ta take kula tana rokon Abbanta ya yafe mata ba laifinta ba ne, amma ya shafawa idanunsa toka ya Kore ta daga gidan.
Abu kamar wasa daga kukan nan sai tari ya biyo baya, daga tarin kuma sai ga amai ta fara, anan jini take yi wanda ya tayar da hankalin Inna Rabi.
Ɓangaren Munnir kuwa tun ranar da ya tafi club ya tarar da Hafsat za ta sha giya ne hankalinsa ya yi matuƙar tashi da lamarinta, sam bai taba tunani bayan syrup da take sha har ta kai giya ba, a bunckensa ya gano har shisha tana sha, Hafsat ta wuce saninsa. Kuma ya ga har yanzu iyayen na su na shirin saka masa ranar bikin aurensu.
Shi a cikin zuciyarsa kuwa har yanzu son Amatullah ce a cikin zuciyarsa, ya yi iya yadda zai yi amma ya kasa cire soyayyar ta.
Mahaifin Amatullah bai ɓoye masa komai ba, ya sanar da shi gaskiya da shaye-shaye da ta fara da ciki da ta yi wanda a dalilinsa ne ya Kore ta.
Munnir ya ce ya ji ya gani ya kuma amince zai aure ta a haka nan. Dan haka ya yanke shawarar sanarwa mahaifiyarsa gaskiya. Tashi ya yi daga bedroom ɗin sa ya nufi falon.
Zaune ya samu Mamansa tana kallon t.v.
Zama ya yi a gabanta kamar mai roƙon gafara.
"Munnir lafiya ya dai na ga kamar akwai abinda ke damunka."
Jinjina kai ya yi tare da cewa.
"Mama wata magana nake so mu yi duk da ban san ya za ki ɗauki lamarin ba."
Jinjina kai ta yi tare da cewa
"Ina jin ka."
"Mama na fasa auren Hafsat."
Da mamaki ta lalle shi tare da cewa
"Me ya saka ka fasa auren nata?"
"Hafsat tana shaye-shaye tun da dadewa na sani, amma ban sanar da ke ba ne domin na ɗauka iya syrup kawai take sha. A tunanina zan iya canza ta, yanzu ashe ban sani ba Hafsat har da giya da shisha tana sha."
A razane Mamansa ke kallonsa tare da cewa
"Giya fa ka ce?"
Jinjina kai ya yi tare da cewa
"Ƙwarai kuwa Mama."
"Munnir ka san fa da mahaifinka da mahaifiyar Hafsat wa da ƙanwa ce ko? Ka da ka zo da wani zancen da ba shi ne ba, idan har ka san cewa ba kanda tabbas akan abinda kake faɗa ka fito fili ka faɗa mani, idan son Hafsat ne ba ka yi ka sanar da ni, don na fahimci dama ita ce ke sonka."
"Mama wallahi da gaske nake yi ba sharri na mata ba."
"Me ye hujjarka?"
"Ki bani nan da kwanaki biyu zan kawo maki hujja."
Jinjina kai ta yi tare da cewa
"Allah ya kai mu."
D.P.O ya ƙaraso guest house din Ajmal kamar yadda ya bukaci ganinsa.
A babban falonsa suka zauna su biyu suka keɓe suna magana, Ajmal bai ɓoye masa komai ba ya sanar da shi abinda ke faruwa.
Sannan ya kara da cewa ka san ƙauyen da ake cewa .
"Ka san ina ne Garun gabas?"
Jinjina kai ya yi tare da cewa,
"Na san ƙauyen."
"Okay a can ƙauyen ya tafi, so nake a kawo mani shi nan."
"An gama Excellency."
"Yanayin fuskarsa ce ta sauya, duk da cewa dama baya cikin walwala.
"Ba na son a sake kirana da wannan sunan."
"Yallaɓai kuwa ai dole a kira ka, dama wannan matsalar ce take neman kawo maka shamaki da kujerar Gwamna, kuma yanzu tunda ka gane gaskiya idan aka kamo shi ya fadi gaskiya ai dole ne a barka ka cigaba da takarar ka. Dan har yau har gobe akwai mutanen da soyayyar da suke maka bai ragu a cikin zuciryasu ba, infact wasu ma ba su yarda cewa ka aikata hakan ba, dan dama akasari 'yan adawarka ta siyasa ne ke assasa Lamarin."
DPO ba wai saboda siyasa ba ne a'a ni dama siyasa ba wai tana gabana ba ne, asalima mai girma Gwamna ne ya sa mahaifina ya tilasta ni."
"Ayyah Allah sarki Excellency ya duba cancantarka ne, kuma duk wannan abun da ya faru ga shi baya ƙasar yana can wajen binciken lafiyarsa."
"In sha Allah next week zai dawo."
Jinjina kai DPO ya yi tare da cewa
"Allah ya bashi lafiya."
"Ameen."
"DPO yanzu nake bukatar a tafi ƙauyen nan."
"An gama yallaɓai."
Sallama ya masa inda ya tafi ya shiga motarsa ya bar guest house ɗin.
DPO da ke can jihar Niger ne ya turawa Ajmal pic din INDAKUƊINKA. Shi ya turawa DPO.
Photon aka mayar da shi zuwa na kati inda jami'an 'yan sanda suka tafi da motarsu zuwa ƙauyen.
Sai yamma liƙis ne Saliha da Madina suka yi wa Amatullah addu'a da sallama suka tafi,inda Ammi ta haɗa masu sha tara na arziki.
Amatullah kamar za ta yi kuka da za su tafi, sai dai ta masu godiya inda suka mata alƙawarin dawowa.
Wunin ranar ta samu farin ciki sosai sai da yammacin ne Iya ta ta zo ɗaukar su ita da Baby inda zasu koma ɓangaren su.
Anmi ta haɗa mata kayan a wata 'yar jaka ta karɓa tana godiya da haka suka fito zuwa babban falon.
Gaban Amatullah ne ya faɗi ganin wani irin mugun kallon da Nasreen matar Ajmal ke jiranta da shi, kallo ne mai cike da tsana da tsantsan ƙiyayya.
Sunkuyar da kai ta yi za ta wuce sai ta ji muryar Nihal na cewa.
"An gama shagali sunan ɗan shegen ne?"
Idanun Amatullah ne ya sauya kala zuwa ja, inda ta ji muryar Nihal na cewa.
"Zo nan."
Ƙarasawa ta yi cikin sanyin jiki, Nihal ta kalli satar kallon Nasreen ta ga idanunta na kan Amatullah dan haka dan ta cusa mata baƙin ciki sai ta ɓoye na ta baƙin ciki ta danne zuciyarta daga tsabar Amatullah da babyn.
Bayan Amatullah ta ƙarasa gabanta ne ta ce,
"Amatullah ya na ga kina wani ɗari-ɗari ki saki jikinki ba wanda ya isa ya takura maki, nan gidan uban ɗan ki ne, ɗan ma wanda ya yi kama da ubansa dama kyan ɗa ya gaji ubansa."
Nasreen ta taɓe baki tare da cewa.
"Wace hujja kike da shi da za ki danganta yaron nan da mijina? Ai mijina ta fi ƙarfin ajin yarinyar nan wallahi, wayayyun mata masu aji masu aji ma ya gansu bai ƙyasa ba ballantana wannan bagidajiyar wacce ko..."
Shiru ta yi jin Anmi na ƙarasowa, Anmi ta kalli Iya da Amatullah ta ce,
"Kuna nan ne?"
"Nihal ta miƙa wa Amatullah yaron tana cewa za ku iya tafiya."
Anmi ta zauna kan kujera ta kalle Nasreen da Nihal ta ce,
"Fira kuke yi ne?"
"Anmi ki fadawa Nihal ta fita harkata, tana shiga mun hanci da ƙudundune ina ɗaya mata ƙafa ne saboda darajar mai daraja. Amma wallahi idan har ta cigaba da tunzura ni matakin da zan ɗauka kanta ba zai mata daɗi ba."
Nihal ta mike tsaye tare da cewa.
"Ke Nasreen ki fita a harka ta ki kiyaye ni wallahi, ke a zuwa da za ki ɗauki mataki akai..."
Ammi ta dakatar da Nihal ta hanyar cewa.
"Ya isa haka nan."
Kallonsu ɗaya bayan ɗaya ta yi tare da cewa.
"Me ke faruwa?"
"Anmi kamar Nihal za ta dinga gaya mani magana tana cewa wai yaron wannan kucakar yarinyar ne ya yi kama da mijina har tana cewa yanzu aka haifi yaron da ke kama da ubansa ba, kyau kenan wai ta saki jiki nan gidan uban ɗanta ne ba wanda ta isa ya takura mata?"
Ammin ta gane inda zancen ya dosa dan haka ta bawa Nasreen hakuri tare da yiwa Nihal faɗa. Dan ta san da biyu ta faɗa, dan Amminta daɗe da sanin cewa Nihal ta Kamu da son Ajmal. Hakan ya sa take kishi da matarsa.
Durba ne ya yi sallama ya shigo riƙe da hannun Affan ɗayar hannun kuma yana rike da hannunsa.
Affan na ganin kakarsa ya ruga a guje tare da faɗawa jikinta yana dariya.
"Granny Dadyna yana gida?"
"Affan baka yi gaisuwa ba fa."
Dariya ta yi tare da gaishe ta Kakarsa sannan Mum ɗinsa sai Nihal.
Bayan ya gaishe su ne ya ce,
"Dadyna fa ina ya tafi ya barni? Na masa magana zan je yawo ya ce zai kai ni, shi ne ya tafi ya barni?"
Daga nan ya fara kukan shagwaɓa, yana cewa sai an kira masa Dadynsa.
Ba shiri Ammi ta ɗauki waya ta dannawa Ajmal kira.
Yana can kwance a guest house ɗinsa yana waya da DPO inda yake tabbatar masa da cewa yaransa na can sun tafi ƙauyen za su kamo yaron dan sun tafi da photon yaron.
Ganin ɗayar wayarsa na ruri ne ya sa ya yi masa sallama tare da katse kiran wayar. Sannan ya dauki kiran Amminsa.
Tun kafin ya yi magana ne ya ji muryar Affan na rigima yana kuka, murmushi ya yi dan ya san cewa rigimar Affan ne ya saka Ammi ta kira shi. Yaron shekarunsa huɗu amma idan ya tashi rigimarsa ya fi na ɗan shakara biyu.
Jin muryar Dad din ne ya sa shi ƙara sautin kukansa.
"Affan me ya faru ne?"
Kuka kawai yake yi, duk yadda Ajmal ya so ya yi shiru bai yi ba hakan ya sa ya shirya barin guest house ɗinsa dan ya koma gida.
Fitowa ya yi yayin da bayan fitowarsa Ahmad ya rufe gidan.
Security nasa da ke waje ne kowa ya matso wajensa, ya har lokacin Wayar na kunnensa yana aikin rarrashin Affan.
Motoci suka shige yayin da security dake kula da ƙafa suka buɗe masu gate suke fice motocinsa a jere.
A can ƙauyen na Garun gabas motar 'yan sana'ar suka
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 51