mace a Kai ta gidan miji ba ta San sa ba fa, don ma zan masa gata zan ranshi da auren karuwa yar shaye-shaye da ake fad'a, na gama magana kowa ya tashi ya tafi. "
Tun kafin ta gama rufe baki Ajmal tuni ya bar wajen yana tunanin abunda zai yi wa wannan tsohuwar don wallahi ba zai bari ba.
Sanye take cikin dogon hijabi har kas, ta rufe fuskarta da nik'ab idan ba wanda ya santa ba ba zai gane ta ba.
D'akin Umma ta shiga lokacin Umma ta gama shirya Khalifa, karbarsa ta yi yana dariya alamar ya gane fita zasu yi.
Ajiye Khalifa ta yi tunda dama yana tafiya duk da tafiyar ba ta sauri, sallama suka yi wa Umma suka fita, tana rike da hannunsa suna tafiya a hankali.
"Amatullah ki d'auke shi mana, wannan tafiyar yaushe za ku isa bakin titi ?"
Cewar Umma.
.
"To Umma."
Amatullah ta fad'a tana d'aukar Khalifa suka nufi hanyar fita.
Tun kafin ta karasa bakin titi ta hangi wata mota bak'a a layin unguwarsu.
Bayan ta iso bakin titi ne ta ga motar ta biyo ta tare da parking a gabanta, ganin motar ta tsaya a gabanta ne ya sa ta tsuke fuska tare da matsawa gaba.
Wanda ke cikin motar ne ya ciro wayarsa ya duba photo da aka tura masa ta what's up, photon Amatullah ne sai na Khalifa.
Duk da Amatullah ta Saka nik'ab amma yana da tabbacin ita ce sabida Khalifa da ke tare da ita.
Kafin ya gama dubawa sai ya hangi har ta shiga cikin napep, sun tafi, a guje ya ja motar ya rufa masu baya.
*Kuyi hakuri da wannan*🙏
🤦♀️ *'YAR MAYE*🤦♀️
(_The drug abuser_)
Na
Zainab Abdullahi K.NT
(Maman Ihsan)
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Page9️⃣8️⃣
Kafin ya gama dubawa sai ya hangi har ta shige cikin nape din har sun tafi, a guje ya ja motar ya mara masu baya.
Tana hangen motar na binsu ta jikin mirror, hankalin ta ba karamin tashi ya yi ba ganin yadda motar ta bi kwanar da suka bi. Kara kankame Khalifa ta yi a jikinta tana addu'a Allah ya sa ba ita yake bi ba.
Kwanar da za ta sada su da gidan Fadeela suka bi Inda ta kira wayar Fadeela bugu d'aya ta d'aga tare da cewa.
"Amatullah kin karaso ne?"
"Na dai kusa amma don Allah idan har kin san cewa gate din gidanki a bude yake, idan a rufe ne ki yi sauri ki yi sauri ki bude mani ba sai na tsaya knocking ba."
Da to ta amsa mata kafin ta tashi ta nufi gate din don ta bude k'ofar.
Mai Nape na tsayawa k'ofar gidan ta Mika masa dubu d'aya ta shige a guje, yana cewa.
"Hajiya ga canjinki."
Ina ba ta kula shi ba, ta yi shugewarta ciki daidai lokacin da ta hangi motar ta kusa karasowa, tana shiga ta rufe gate din da sauri ta saka sakata ta rufe.
Ajiyar zuciya ta saukr tare da ajiye Khalifa, kallonta Fadeela ke yi tare da cewa.
"Lafiya kuwa kamar wacce aka Koro?"
"Ina fa lafiya wallahi wata bakar mota ce ke bina tun daga layin unguwarmu har nan."
"Ban gane ba."
"Mu shiga ciki zan maki bayani "
Fadeela ce ta dauki Khalifa suka shiga cikin falon, nan ma sai da Amatullah ta saka key ta rufe k'ofar sannan ta ce.
"Ko sun hauro Katanga kafin su bude k'ofar nan da wahala zuwa lokacin mun samu dauki."
"Kin ga ni da kin daga mani hankali, me ke faruwa."
Nan Amatullah ta bata labarin ganin motar da ta yi a layin su da binta da motar ke yi har ta shigo nan.
Shiru Fadeela ta yi tare da cewa.
"To ko dai son ki yake yi ne ya saka shi yake bibiyarki?"
"Wallahi ban yarda da shi ba, da so na yake yi a lokacin da ya ganni Ina tafiya a layin mu kafin na k'arasa bakin titi ne zai mani magana ya bayyana kansa, amma haka fa ya tsaya a gabanta ga gilashin motar tinted ne na waje baya ganin na ciki, wallahi ban yarda da shi na na tsorata, sabida sau buyu hakan na faruwa da ni a Kaduna, akwai ranar da Khalifa na jariri Ammin Ajmal ta ce wa wani bodyguard din Ajmal ya kai ni asibiti ayiwa Khalifa rigakafi haka aka biyo ni da mota lokacin da na fito Ina jiran a d'auke ni, wallahi har barazana suka mani kan na basu yaron nan cikin iKon Allah sai ga bodyguard din ya karaso shi ne da suka gan shi suka gudu. Kuma akwai ranar da matar Ajmal Nasreen ta saka wani ya d'auke ni da sunan zai Kai ni saloon, ke nifa na san halin da na Shiga shi ya sa hankalina ya tashi."
Tana gama rufe baki sai ga Kiran wayar Ajmal ya shigo wayarta, dauka ta yi tare da yin sallama.
"Assalamu alaikum"
"Wa'alaiki salam, ki tsaya a gidan da kike sannan ki turo mani adireshin gidan zan Saka a zo a mayar da ke har gida, idan har ba ni ne na ce ki fito daga gidan ba kada ki fito."
Yana gama fad'ar haka ya katse Kiran wayar, don damuwar da ke zuciyarsa ba za ta iya barinsa ya yi dogon magana ba.
Cire wayar daga kunnenta ta yi tare da cewa.
"Lamarin wannan mutimin fa yana bani tsoro, mutum kamar Aljani?"
"Meke faruwa?"
Fadeela ta jefa mata tambayar?"
"Wallahi lamarin Ajmal ne ke bani mamaki, yadda yake sanin komai game da ni daga Inda yake, tun ranar da muka je wajen telanki har yau yana sanin komai da nake aikatawa, da ace a d'akina ne kawai da na ce CCTV camera ya Saka mani to fa a ko Ina yana sanin halin da nake ciki ne wallahi, wai na tura masa adireshin gidan nan zai aiko a d'auke ni, Kuma bai san ma fito daga gida ba."
Jinjina Kai Fadeela ta yi tare da cewa
"Lallai lamarin da mamaki kuwa. Ko ya saka ana bibiyarki ne?"
"Idan ya saka ana bibiyata a waje to a gida fa Kuma a d'akina fa?"
"Haka ne Kuma."
Tashi Fadeela ta yi ta nufi kitchen ta kawo mata ruwa da abinci, ta kawowa Khalifa biscuits.
Ruwa kawai Amatullah ta iya sha ta shiga duniyar tunani.
Wayarta ce ta soma ruri, tana dubawa ta ga Ajmal ne ta daga da sauri tare da yin sallama.
"Ki fita waje za ki ga wata farar mota ta zo daukar ki sai ki shiga shi ne wanda na tura wa adireshin gidan da kike, zai kai ki har gida ."
Yana gama fadar haka ya katse Kiran wayar.
Kallon Fadeela ta yi ta ce.
"Ya aiko a dauke ni zan tafi."
Okay to muje na raka ki don na ga wucewarki hankali na zai fi kwanciya."
.
Ɗaukar Kalifa ta yi jikinta duk ya yi sanyi, duk da a tsorace take ta tabbata Ajmal mai tsaya mata akan komai ne."
Ajmal kuwa bayan Amatullah ta tura masa adireshin gidan da ta je ne ya kira DPO a waya ya sanar da shi taimakon da yake so a masa, yana son ya tura jami'ansa biyu su je su dauki Amatullah su kai ta gida.
Nan DPO ya samu jami'an tsaron guda biyu ya sanar da su aikin da yake so su yi masa.
Nan da nan kuwa suka zo bayan sun iso ne suka kira DPO suka sanar da shi, hakan ya saka shi ya kira wayar Ajmal ya sanar da shi.
Bayan sun gama waya sai daya daga cikin police biyu da suka zo ya karasa wajen motar da ke bin Amatullah, Kano knocking ya yi har sau uku sannan ya zuge gilashin motar wani mutum ne a ciki yana sanye da facemask da bakin gilashi, kallonsa police din ya yi tare da cewa.
"Me kake yi a nan?"
"Yallabai na zo wajen abokina ne, baya nan sai na tsaya jiransa, mun yi waya ba yanzu zai dawo ba hakan ya saka ma zan wuce."
Ya karasa maganar yana yayar da mota, da sauri ya bar wajen daidai lokacin da Amatullah suke fitowa daga gidan.
Wajen motar suka karasa wajen farar motar kamar yadda Ajmal ya sanar da su, kasancewar gilashin motar a sauke ne ya zsa suka yi masu sallama, amsawa suka yi dukkansu suna sanye cikin uniform ɗin ɗan sanda, daya ne ya kalle su tare da cewa.
"Wace ce Amatullah a cikinku?"
"Ni ce."
Amatullah ta fada tana kallonsa, wanda ke zaune gefen me zaman banza ne ya fito daga motar ya zagayo tare da bude mata bayan motar.
"Ranki ya daɗe ki shiga.".
.
Ba musu ta shiga bayan motar bayan ta shigar da Kalifa, sallama ta yi wa ƙawarta suka tayar da motar suka bar wajen.
Sai da suka kai ta har kofar gidansu , Godiya ta yi masu sannan suka tayar da motar suka bar wajen.
Zaune yake a ɗakin da ya sauka, sai daman huci yake yi kamar ma wani mayinwacin zaki. Sudais ne ya kalle shi cikin kwantar da murya ya ce.
"Don Allah Ajmal k yi hakuri ko ruwan tea ne ka saka a cikinka. Rabonka da abinci fa tun jiya, ta yaya rayuwa za ta yiwu da yunwa, wa ya faɗa maka ana zuciya da abinci ne?"
Ya yi maganar cikin tausayin Ajmal ɗin.
"Sudais Please leave me alone, ba na bukatar kowa a kusa da Ni kuma ba ba na bukatar saka komai a bakina."
Ya maganar yana kauda kai gefe don ganin kowa ma baya so.
"Ina ba zai yiwu ba ma ba yadda za"ayi hakan ta faru."
Sudais ne ya kalli Ajmal da ke surutai ya ce.
" A halin yanzu ba abinda zai hana aurenka da Nihal idan har ba daya daga cikin abu biyun nan ka aikata."
Yana gama fadar haka ne ya kalli Ajmal Ajmal tare da cewa
A idan ba haka ba ka ajiye a ranka sai ka auri Nihal, don Dady ma bai Issa ya tsallake zancen ta ba."
Cikin tashin hankali ya mike tare da cewa.
"Ka faɗa mani ina Kur'ani Please."
Ajiyar zuciya Sudais sauke tare da cewa.
"Hanya ta farko ita ce sai dai idan bijirewa umarnin mahaifinka za ka yi. Hakan zai saka a fasa auren musamman idan gudawa ka yi ta hanyar tattare kayanka, ni kuma ba zan so ka aikata haka ba."
Girgiza Kai Ajmal ya yi tare da cewa.
"Faɗi hanya ta biyu don wannan ba mai yiwuwa ba ne."
"Hanya ta biyu kuwa sai dai idan za ka je wajen Bappah ka sanar da shi abinda Marka ke kokarin aikatawa wanda kai kuma ba ka so, shi kadai ne ya isa ya dakatar da ita daga wannan hadin da take kokarin yi, don tana jin maganar sa kamar yadda ba za ka tsallake ta mahaifinka ba hakan ita ma ba za ta tsallake ta sa ba ."
"Waye Bappah?"
"Hana kar ka bani kunya mana, kodayake ba abin mamaki ba ne tunda ba a wannan ƙasar ka tashi ba, kuma ko ka zo kai ba mai yawan shiga jama'a ba ne ballantana ka san waye shi. Bappah shi wa ne a wajen Marka kuma shi ne ya rike ta a hannunsu bayan mutuwar iyayensu, shi ne madadin uba a wajen ta kamar dai yadda ka ji hausawa na cewa babban wa uba, ba ta tsallake duk wani umarnin sa ba kasancewar tun suna yara iyayensu suka rasu, kuma shi suka barwa amanar Marka da k'anwar Marka wacce muke kira da Yelwa, duk shi ke iko da su sai dai fa yana da zafi da tsauri ban shi da sauƙin kai."
Wannan ba damuwa ba ne indai zai dakatar da ita ai a shirye nake akan komai."
"To mu yafi yanzu."
Girgiza Kai Sudais ya yi tare da cewa
"No ka bari dai zuwa gobe da safe sai mu tafi in sha Allah, yanzu yamma ta yi duk da ina tsoron Mama ta yi fushi da ni akan abinda zan aikata, don na lura ita ma tana son farin cikin 'yarta autarta Nihal, Ni ma ina son farin cikinta 'yar uwata gidan jini na, sai dai zan yi haka ne saboda ina da tabbacin ba za ta samu farin ciki a zamantakewar da za ku yi da ita ba, saboda ba ita kake so ba, ni kuma zan so daga kai har ita kowa ya yi auren farin ciki ya samu abokin rayuwar da ke son sa hakan zai sa su farantawa juna rai."
Ajmal ya rasa wani yanayi yake ciki ga farin cikin za'a yiwa Marka magana ta janye gefe guda kuma ga kunyar Sudais da ya ji, don ya tabbatar Sudais bai ji daɗin nuna ƙiyayyar ƴar uwarsa da ya yi ba, ko ba komai ita jininsa ne kuka duk son da yake yi wa Ajmal bai kai wanda yake yi wa Nihal ba, yanzu ƙiri-kiri ya nuna baya son Nihal ƙanwarsa fa kenan, kuma ga shi yana shirin taimakon sa.
Cikin sanyin murya ya ce.
"Wato Sudais ba wai ba na son Nihal ba ne kwata-kwata ai ƴar uwata ce kuma..."
"Ɗaga masa hannu ya yi alamar dakatarwa sannan ya ƙamaro murmushin yaƙe ya ce.
"Kada ka damu na fahimci matsalar ka, mafita kawai nake nema maku daga kai har ita."
"Bari na baka labarin Amatullah watakila za ka gane dalilin da ya sa na dage da son aurenta da kuma son kasancewa tare da ɗan."
Zaune take a ɗakin Umma a gaban Umma tana riskar kuka, ta kasa cewa komai ga Umma ta yi tambayar har ta gaji da ƙyale ta.
"Kin ga idan har ban kai da za ki iya faɗa mani matsalar ki ba ki tashi ki bani wuri."
Cikin kuka ta fara magana tana cewa.
"Don Allah Umma kada ku aura mani shi, wallahi ba shi ne a zuciyata ba, bana iya yiwa Abba gardama ne kawai ya saka na yi shiru."
Shiru Umma ta yi tare da cewa.
"Waye a zuciyarki?"
"Ajmal."
Ta faɗa a takaice."
"Amma kin san ba wanda ya isa daga ni har ke mu tunkare shi da wannan maganar ko?"
"Umma ki saka baki don Allah."
"Ba ni da ta cewa dole ne ki auri wanda ya zaɓa maki ko kina so ko baki so, gara ma ki koyawa kanki soyayyar sa gurbin da kika bawa Ajmal ki bashi ya zauna a ciki."
Kuka ne ya ci karfin ta ta tashi ta nufi ɗakinta, Umma ta bita da kallon tausayin 'yar ta ta amma ba yadda ta iya sanin waye Mallam Abdullahi, ba ta isa ta masa wannan zancen ba.
Sai dai za ta taya ta da addu'a Allah ya zaɓa mata mafi alheri a cikinsu.
Washegari da misalin karfe tara na safe Sudais ya ƙaraso kafar gidan Marka, sai dai a waje ya yi parking yana zaune a motarsa ya kira wayar Ajmal ya shaida masa yana waje, dama sun ajiye magana karfe tara zasu tafi.
Ajmal dama ya shirya isowar Sudais kawai yake jira, don haka ya fito daga dakin da ya kasance nasa, ba kowa a falo da alama ba su tashi daga barci ba, motsi ya ji a kitchen ya tabbatar mai aikin Marka ce .
Fita ya yi ya je ya samu Sudais a waje, yana zaune a cikin motarsa yana jiran fitowar Ajmal.
Marfin motar ya bude ya shiga gefen Sudais, gaiswa suka yi Sannan ya yi wa motar key suka bar wajen.
Tafiyar mintuna talatin suka yi kafin suka iso kofar wani gida. A ƙofar gidan ya yi parking suka fito a tare, kai tsaye Sudais ya tura koafar gidan tare sa yin sallama.
Kasancewar lokacin sanyi ne ba kowa a waje dakunan gidan an tura. Ƙofar da ya kasance na Bappah suka nufa, knocking suka yi ya basu izinin shigowa.
Da sallama a bakinsu suka shiga cikin falon.
Yana zaune a saman kujera yana shan shayi kasancewar dakin ba haske sosai farin gemunsa kawai ake gani, amsa masu sallamar ya yi tare da cewa.
"Muryar wa nake ji haka kamar Sudais?"
"Eh nine Baffa."
"To ka kunna fitilar ɗakin ko?"
Hannu Sudais ya sa ya kunna fitilar ɗakin.
Take haske ya gauraye ɗakin ya kalle su tare da nuna masu wajen zama, saman center carpet suka zauna suka gaishe shi cikin girmamawa. Ya amsa cikin sakin fuska tare da tambaye Sudais mutanen gida, ya amsa masu suna lafiya.
Kallon Ajmal ya yi kamar ya so ya gane shi amma ya kasa tuna inda ya san shi, duk da cewa yana zubi da larabawa amma ya ji a jikinsa yana da kusanci da shi.
"Wannan fa waye shi kamar na waye shi ko?"
Murmushi Sudais ya yi tare da cewa.
"Duk tsufarka har yanzu ba ka ruɗe irin na tsofaffi ba, to ai jikanka ne Ajmal."
Zaro manyan idanunsa ya yi tare da cewa
"A'a'a ka ce babban baƙo ne da mu a gidan."
Nan suka gaisa da Ajmal yana tambayar sa ya Dady ya koma jiya wai ya zo gaishe shi, ya sanar da shi yana lafiya. Ya tambaye shi Ammi nan ma ya amsa masa da tana lafiya.
Shayi ya ce su zuba su sha suka ce a'a. Shiru ne ya biyo baya, Bappah ne ya katse shirun ta hanyar cewa.
"Ya dai na ga kamar da magana a bakina ku."
Ya yi maganar yana kallon Ajmal tare da cewa.
"Ɗan Balarabe ya aka yi ne, don ba ka da kirkin ziyara ballantana ka dinga zuwa gaishe ni na mance rabon da na ganka, duk da ba wani zuwa garin kake ba ai ya dace idan ka zo ka gaida dangin mahaifinka ko?"
"Afuwa Baffa za'a gyara?"
"To Allah ya sa, ya matarka da yara?"
"Suna lafiya."
"Ma sha Allah."
Sudais ne ya kalli Baffa ya ce
"Dama Baffa mun zo ne neman wata alfarma."
"Alfarma kuma, Allah ya sa zan iya."
"Ameen."
Nan ya bawa Baffa labarin komai tun daga abinda ya faru tsakanin Ajmal da Amatullah da samun cikinta da gwagwarmayar rayuwa da ta sha har i yanzu da yake neman aurenta. Da yadda Marka ta yi ruwa ta yi tsaki kan cewa ba zai auri Amatullah ba sai Nihal wacce kuma baya son ta.
Shiru Baffa ya yi yana sauraren sa tare da tausaya wa rayuwar da Amatullah ta shiga a baya, nisawa ya yi tare da cewa.
"Ka kwantar da hankalinka ka ji?"
Jinjina Kai Ajmal ya yi tare da cewa.
"Ina sha Allah."
"Yauwa haka nake so zuwa anjima zan zo na same ta idan har ba ka auri Amatullah ba to dama can Allah ya yi ba matarka ba ce ."
Godiya suka yi masa cikin jin daɗi, suka taso zasu fito ya mara masu baya, a tsakar gidan ya kira matarsa ta fito suka gaisa, sannan suka masu sallama suka tafi bayan Ajmal ya masu kyautar kudi masu yawa.
Da misalin karfe uku na rana Baffa ne a falon Marka, shi da Marka da Dady, sai Ammi da Mama.
Kallon Marka ya yi tare da cewa
"Duk na ji abinda kika yi da wanda kike kokarin ƙullawa, wai ke yaushe ne za ki ladabtu a rayuwarki? Abinda ya faru shekaru talatin da biyu da suka wuce bai ishe ki ishara ba, na ɗauka wannan kadai ya isa ya ishe ki hujja akan tirsasa yaro da raba shi abinda yake so, amma na ga alamar har yanzu ba ki yi nadamar abinda kika aikata ba ko? Ai na ɗauka rasa ɗan ki da kika yi wanda har yau baki san inda yake ba ya sa kin yi laushi, to bari ki ji ba zan taba bari ki aikata son zuciyarki ki taiyewa wasu ..."
Amma Baffa yarinyar da yake son ya aura fa karuwa ce zai kawo muna a cikin zuri'armu 'yar shaye-shaye wacce ta bar gaban iyayenta ta shiga..."
Shima katse ta ya yi ta hanyar cewa
"Idan ma karuwa ce haramun ne auren ta, ai na ga ana daukar karuqa ma daga gidan karuwai a aure ta, bai haramta ba sai ta yi istibra'i, ballantana ita wannan ma ba ƙaruwar ba ce azal ce ta faɗa kansu cikin ƙudirar Allah kuwa har da rabo a tsakanin su. Tunda suna son juna kuma an tabbatar ɗan sa ne ya ce zai aure ya meye naki a ciki, ki takurawa 'ya'yan ki jikokin ma ba za ki bar su ba?" To wallahi ba zai yiwu ba wannan zancen na soke kuma ka da na sake kin kin tayar da wannan magana idan har na isa."
Yana gama fadar haka ya kalli Dady da Ammi ya ce .
"Ina yaron yake ?"
Da sauri Ammi da zuciyarta ta yi fari da jin hukuncin Baffa ta ce yana ciki bari na kira wayarsa
Lalubo lambar wayarsa ta yi tare da danna masa kira, bugu biyu ya daga kafin ya yi magana ta ce.
"Ka zo falo"
Da rawar jiki ya fito dama jiran kiran yake don ya tabbatar Baffa ya zo.
Da sallama a bakinsa ya ƙaraso falon suka amsa masa gabad'aya, kallo ɗaya ya yi wa Marka ya ga idanunta sun rikede zuwa ja sallar tashin hankali kawai ake gani a idanunta.
Zama ya yi bayan ya gaishe su, Mama ma har ƙwalla ta yi don ta yi burin Nihal ta auri Ajmal saboda wata manufa da take da shi, hakan ya saka ta dinga zuga Nihal akan ta takurawa Marka.
Kallonsa Baffa ya yi tare da cewa.
Duk da an ce yarinyar iyayenta sun tsayar mata da wanda za ta aura, kuma an ce ba ta son wancan ɗin kai take so, duk da ba'a naman aure cikin aure amma kasancewar ga yaro a tsakanin ku kuma kai ne zaɓinta ba wancan ba zan yi amfani da wannan dama mu je mu samu iyayenta da maganar aurenka ko albarkacin yaron da ke tsakaninku."
Farin cikin da ke kan fuskar Ajmal baya ɓoyuwa, sai dai fargabar Annan Amatullah yake yi.
Baffa ya kalli Dady ya ce.
"Ibrahim."
"Na'am Baffa."
Ya amsa cikin girmamawa.
"Zuwa jibi in sha Allah tare da kai da aminina za mu je mahaifin yarinyar."
Jinjina Kai Dady ya yi tare da cewa.
"Allah ya kai mu Baffa."
Sallama Baffa ya masu ya nufi hanyar fita Marka da Mama kasa magana suka yi su kaɗai suka san tashin hankalin da suke ciki.
*Daga alƙalami*✍️
Zainab Abdullahi KNT
(Maman Ihsan)
09065327995
*🤦♀️'YAR MAYE*🤦♀️
(_The drug abuser_)
*NA*
Zainab Abduullahi K.NT
(Maman Ihsan)
Page9️⃣9️⃣
Sallama Baffa ya masu ya nufi hanyar fita, Marka da Mama kasa magana suka yi su kaɗai suka san tashin hankalin da suke ciki.
Washegari da safe Ajmal da Ammi suka nufi airport don komawa Kaduna, Dady kuma ta tsaya da niyyar sai sun tafi nemawa Ajmla auren Amatullah kamar yadda Baffa ya ce.
Zuciyar Ammi da Ajmal cike da farin cikin abunda Baffa ya yi, fatansu Allah ya sa Abban Amatullah ya amince da zancen da su Baffa za su je masa da shi.
Amatullah kuwa tana kwance a saman gadonta tana tunanin abubuwan da suka faru da ita a baya. Musamman abunda ya faru jiya ya tsaya mata a rai, ta rasa gane waye wanna mutumin kuma turo shi aka yi ko kuma zuwan kansa ne, me ya sa yake bibiyarta?
Wayarta ce ta yi ruri ta duba ta gani, Munnir ne ke Kiran wayarta madadin ta ɗaga Kiran wayar sai ta faɗa duniyar tunani. Tabbas ba ta jin tsanar Munnir a ranta kuma ba ta jin sonsa, amma ba ta da wani zaɓi da ya rage ta koyawa kanta sonsa, don ta San tabbas Munnir ne wanda zai aure ta.
Ƙarar Kiran wayar ne da ya sake Kira a karo na biyu ya dawo da ita daga duniyar tunani da ta lula, ɗagawa ta yi tare da yin sallama.
"Assalamu alaikum."
Lumshe idanu ya yi tare da sauke ajiyar zuciya ya amsa da.
"Wa'alaiki salam farin cikina fatan kina lafiya?"
"Alhamdulillahi, ya aiki?"
"Mun gode Allah gani nan kewarki ya addabe ni, yanzu zan shirya sai na zo na ga sanyin idanuna."
Gajeren murmushi ta yi tare da cewa.
"Allah ya kawo ka lafiya."
"Ameen sai na zo."
Nisawa ya yi tare da cewa
"Faɗa mani wani abu mai daɗi."
"Me kake so na faɗa maka Munnir?"
"Koma mene ne."
Gajeren murmushi ta yi tare da cewa.
"Allah ya ƙarawa rayuwa albarka da kwanciyar hankali."
"Ameen my heart."
Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa
"I love you so much."
"Thank you."
Ta faɗa cikin ƙosawa.
"Ba haka ya kamata ki ce ba. Kamata y la yi i Nima ki maida mani da maratanin abinda na ce ba wai ki ce thank you ba."
"Love you too.".
Ta faɗa tare da katse Kiran wayar. Jifa da wayar ta yi a kan gado tana adduar Dana kada ya zo.
Ammi da sun isa lafiya zuciyiynsu farare, adduar Allah ya ɗora su kan Abban Amatullah suke yi. Suna zaune a dinning table suna cin abinci, Ammi na kallon Ajmal da yake juya cokali ya kasa cin abinci.
'ina ce yanzu dai hankalin ka ya kwanta tunda an shawo kan matsalar, amma sai tunani kake yi miye matsalar kuma?"
"Ammina har
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 45 Chapter of 51