same shi yana ta sintiri a ɗakinsa ya kai ya kawo. Tana shigowa bakinta ɗauke da sallama ya amsa mata fuskarsa babu walwala.
"Alhaji lafiya kuwa na ga alama ka shiga damuwa."
"Tamabaya ta kike lafiya bayan abun da idanunki ya nuna maki, wato dama har yaron nan ya sanar da ke ɗabi'ar yarinyar nan shi ne kuka yi biris da lamarin?"
"To ya zan yi Alhaji da ni da mahaifiyar Hafsat uwarmu ɗaya ubanmu ɗaya, ai hannunka bai ruɓewa ka yanke ka yar."
Murmushi ya yi tare da cewa.
"Ni ko idan hannuna ya ruɓe tsab zan zan yanke shi na yar tun kafin ya kai ga cinye mani sassan jikina."
"Me kake nufi Alhaji."
"Sam wannan yarinyar ba za ta taɓa zama matar ɗana ba, wace tarbiyya ce ga 'yar shaye-shaye? Ai Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce ku zaɓawa wa 'ya'yanku uwa ta gari wacce..."
"Dakata Alhaji hakan da kake kokarin yi ba daidai ba ne, ta yaya dan Allah ya jarabe ta da shaye-shaye za ka guje ta ai ƙaddara ce daga Allah."
"Kin ga ba ruwan ƙaddara illa ƙarancin tarbiyya da ke damun Hafsat."
Ta buɗe baki da niyyar magana ya ɗora da cewa.
"Ba wata magana da zan sake saurara akan ki, bayan duk abinda za ki faɗa ba alkhairi ba ne, a baya na yi kuskuren biyewa zuciyata akanki, wanda a yanzu shi ne nake ganin babban katoɓarar da na aikata a rayuwata, wanda har yanzu ban samu damar gyara kura-kurai da na yi a sanadiyar ki ba, a yanzu bani da wani farin ciki da ya wuce na koma cikin ahalina. Duk hakan ya faru a dalilin ki ne Maryam, ta ya zan cigaba da biye maki bayan nadama ce za ta biyo baya. Ba zan taɓa bari ɗana ya auri mara tarbiyya ba, nayi kuskure baya wanda ba zan taɓa bari ɗana ya aikata makamancin abinda na aikata ba, sai dai ya nemo 'yar gidan tarbiyya ya aura."
"Wannan maganganun naka fa sun fara isa ta haka na, akan me za ka dinga jifa na da mugayen kalamai, Munnir dai shi ya ga Hafsat ya ce yana so don haka baya da wata matar da ta wuce ta."
"Zan gani ke ce maɗaurin auren ko kuma ni?"
Yana fadar haka ya fita, a falo ya haɗu da Munnirat ta fito daga ɗakinta ganin Mahaifinta ya sa ta saki fara'a tare da cewa.
"Dady yaushe ka shigo?"
Murmushi ya yi tare da cewa
"Aura ban jima da shigowa ba, barci kike ne?"
Murmushi kawai ta yi inda ta cigaba da cewa.
"Ke baki gajiya da barci dai, ina yayanki ne?"
Kallon ƙofar ɗakin Munnir ta yi tare da cewa.
"Bari na duba ko yana ciki."
Ƙofar ɗakin ta dosa yayin da Alhaji Yusuf ya zauna a ɗaya daga cikin kujeru da ke falo. zaman sa kenan sai ga Hajiya Maryam ta fito daga ɗakinsa ranta a ɓace.
Munnirat ce ke knocking a ƙofar ɗakin Munnir tare da kiran sunansa, jin muryar ƙanwarsa ce ya sa shi fitowa.
Kallonata ya yi fuska a tsuke ya ce.
"Lafiya?"
"Dad ya ce na kira ka?"
Kallon Mahaifinsa ya yi dake zaune kan kujerar shi da mahaifiyarsa.
Ƙarasawa suka yi suka zauna a gaban su. Dad ne ya kalli Munnir tare da cewa.
"Ya batun aurenki da Hafsat?"
"Dad ni tuntuni na riga da na fasa aurenta Hafsat kuma na sanarwa Mu..."
Mum ce ta daka masa tsawan ta hanyar cewa.
"Ba ka isa ba wallahi, ni za ka watsawa ƙasa a Idanu?"
Dad ne ya lalle ta tare da cewa.
"Kowace uwa tana da burin ta ga ɗanta ya auri 'yar mutunci, kowace uwa tana da burin ta ga ɗanta ya auri yar gidan tarbiyya wacce za ta tarbiyyartar da 'ya'ysnsu, amma idan ya kasance yarinya 'ya shaye-shaye ce wace irin al'umma kike ganin za ta samar wa zuri'a mu?"
Kallon Munnir ya yi tare da cewa.
"Ka je ka zaɓawa 'ya'yanka uwa ta gari, Allah ya maku albarka ta shi ku tafi."
Jan hannun Munnirat ya yi fuskar kowanensu cike da Murmushi, ɗakin Munnir suka nufa,suna shiga Munnirat ta ce.
"Yaya rana ɗaya nake son fa ayi aurenmu da kai."
"Ke kina da saurayi ne?"
Dariya ta yi tare da cewa,
"Kai ma su baka da budurwa."
Murmushin takaici ya yi tare da cewa.
"Ina da ita sunanta Amatullah, amma zuwa yanzu ba ta garin nan hasalima ban sana wane gari take ba, amma kullun ina addu'a Allah ya dawo Mani da ita lafiya."
A falo kuwa Alhaji Yusufne ya kalli Hajiya Maryam tare da cewa.
"Ina fatan ba za ki jayyaya da ni ba a lokacin da na ce maki na soke auren ɗana da 'yar ƙanwarki."
Shiru ta yi ba tare da ta ce komai ba.
Da misalin ƙarfe goma sha ɗaya na dare Hafsat ce kwance a saman gadon iya, barci ne yq fara ɗaukar ta, dan haka iya ta kalle ta tare da cewa.
"Hafsat dare ya yi wannan firar dai ta kare ga shi kina ta gyangyaɗi."
Tashi ta yi ta nufi hanyar fita idnunta ta ce.
"Iya tunda ya sha mama ba zai farka ba dan ba ya farkawar dare, idan ma ya farka ki bashi madararsa ya sha, sai da safe."
Daga haka ta fice iya na cewa.
"Allah ya tashe mu lafiya."
Amatullah na fita iya ta murzawa ƙofar key ta dawo ta rage hasken ɗakin sannan ta haye saman gado ta kwanta gefen Abdallah dake cikin kayan sanyi da lallusan bargo.
Amatulla na shiga sakinta sai da gabanta ya faɗi, ganin ƙofar a buɗe bayan ta san ta rufe, dube-dube take yi ko wani ya shigo ba ta ga kowa ba, dan haka har toilet ta leka dan haka ta koma ta rufe kofar da key ta bar key ɗin a jikin ƙofar.
Kasancewar dama ta yi shirin barci ne ta je ɗakin iya ya sa alwala kawai ta yi na kwanciya barci ta zo ta haye saman gadon ta rage hasken ɗakin sannan ta fara addu'ar kwanciya barci.
Tana kwanciya kenan sai ta ga an kunna hasken ɗakin, a ruɗe ta tashi tare da kallon waye.
Ba za ta shaida waye ba kasancewar ya rufe fuskarsa da tun hular nan dake rufe kai da fuska, idanunsa kawai take gani sai bakinsa, sai hudar dake saitin hancinsa alamar shaƙar numfashi. Yana sanye da ƙananan kaya baƙar riga da baƙin wando.
Tsore ne ya kamata jikinta ya fara rawa ta fara magana.
"Waye kai kuma me ya kawo ka ɗakina."
"Ban zo nan da na cutar da ke ba amma idan har kika mani taurin kai to fa."
Ya ɗaga gabar rigarsa ta ga wuƙa a soke a wandonsa, inda ya cigaba da cewa.
"Ina jaririnku yake?"
Gabanta ne ya fadi inda cikin rawar murya ta fara cewa.
"Jaririna kuma? Me za ka masa, ina za ka kai shi?"
"Zan fitar da shi daga cikin gidan nan ne, na nisanta shi da ke da kuma ubansa, dan barinsa a raye barazana ne ga rayuwar wasu. Amma idan aka kawar da shi hankalin kowa zai kwanta, bayan na dauke shi kenan ku yi nesa da garin nan, ki tafi inda ba wanda zai ji labarin ki, idan kuma kika yi taurin kai duk abinda ya same ki ke ce kika janyo wa kanki."
Kuka ta fashe da shi yana tunanin inda za ta dosa, ga shi tana ganin wahalaeta ta kare ta samu waje ashe wasu na shirin mai da rayuwarta irin ta baya, ta cigaba da watangaririya akan titi.
Tsawan ya daka mata tare da cewa.
"Where the boy?"
"Baya tare da ni?"
"Ina kika kai shi, ko sai kin ji jiki za ki fito da shi?"
Gadan-gadan ya nufo ta tsalle ɗaya ta yi ta dira daga saman gadon ta nufi ƙofar toilet a guje, bin bayanta ya yi amma kafin ya ƙarasa har ta murza key, ta rufe ƙofar.
Dukan ƙofar take yi tare da cewa.
"Ki buɗe kofar nan idan ba ki buɗe ba kika bari na ɓalle kofar nan to na lahira sai ya fi ki jin daɗi."
Dukan ƙofar yake yi tare da mata barazana dan ta bude. Ita ko sai kuka take yi sosai tare da karanta duk addu'ar da ta zo bakinta.
Ganin yadda yake dukan ƙofar ne kamar zai ɓalle ya sa ta ɗaga kanta ta kalli window dake toilet ɗin.
Ganin ya yi nisa ba zata iya kai masa ba ya sa ta yi tunanin taka toilet site ta mik'e tsaye, miƙe tsaye tare da buɗe murya tana cewa.
"Taimako! A taimake ni! Taimako!"
Kasancewar akwai security da basa barci suna ta sintiri a cikin gidan ne hakan ya sa wasu security guda biyu suka ji ihunta.
Kallon juna suka yi inda suka dake jin ihnunta daya daga cikinsu ne ya ce.
"Daga can sashen nake jin ihun."
A guje suka yi ɓangaren ma'ikatan gidan, inda suka tarar da ƙoafar falon a bude, sai dai duka dakunan a rufe, suka rasa daga wani waje ne ake ihun, ɗaya ya nuna ɗakin Amatullah tare da cewa.
"Daga nan ne nake jiyo ihun."
Kutsa kai suka yi ciki ba kowa dai duka ji ihu a banɗaki, ƙara sawa suka yi tare da cewa.
"Lafiya me ke faruwa anan?"
Saukowa ta yi tare da cewa.
"Su waye ku?"
Haɗa baki suka yi wajen cewa.
"Securitys ne."
Da sauri ta buɗe tare da fashewa da kuka.
"Lafiya me ya faru?"
"Wani ne ya shigo mani ɗaki yana kokarin kashe ni da babynta."
"Ina babyn naki yake?"
Tare suka haɗa baki wajen faɗa.
"Yana ɗakin iya ne"
"Shi wanda ya shigo ba ki san fuskarsa ba ne?"
Girgiza kai ta yi tare da cewa
"Ban san shi ba saboda ya rufe fuskarsa."
Jin hayaniya ya sa sauran ma'ikatan gidan maƙotan da ke kusa aka fito, aka dinga ƙwanƙwasawa juna kofa ana tambayar lafiyar juna, jin ba wata matsala ta sa security suka ce su kwantar da hankalinsu su koma ciki. Amatullah kam bin iya ta yi ɗakinta suka shige suka rufe kofar.
Fita security suka yi bayan sun duba ɗakin gaba ɗaya bangaren ba kowa har suka fita, nan ma suka zaga ya ba su ga naki kowa ba.
Haka suka sanar da sauran security suka bincike gidan ba kowa.
Washegari da misalin ƙarfe goma na na safe Ammi da Nihal sai Nasreen suna zaune a dinning room suna breakfast.
Ajmal ne ya ƙaraso wajen yana ɗauke da Affan a kafaɗarsa. Wayarsa ce ta yi ringing daidai lokacin da ya karaso wajen.
"Security ɗinsa Ahmad ya kira shi a waya, bayan ya ɗaga ne Ahmad ke sanar da shi abinda ya faru. A ruɗe ya ce.
"What?" Ta ya hakan za ta faru ina ita Amatullah da babyn?"
Gaba ɗaya hankalinsu ya dawo kansa,jin me yake cewa. Jin muryarsa suka yi ya sake cewa.
"Okay ka kawo su nan."
Bayan ya cire wayar daga kunnensa ne Amma ta kalle shi tare da cewa.
"Me ke faruwa?"
"Wai wani na ya shiga ɗakin Amatulla a daren jiya."
"Subhanahi ba abinda ya same ta ko?"
Ammi ta yi maganar cikin nuna damuwa.
"Ahmad ke sanar da ni yanzu, dan haka na ce a kawo su nan ɓangaren."
*Daga alƙalamin*✍️
Zainab Abdullahi KNT
(Maman Ihsan)
09065327995
Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
🤦♀️ *YAR MAYE*🤦♀️
(_The drug abuser_)
*NA*
Zainab Abdullahi KNT
(Maman Ihsan)
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*GARGAƊI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
Ban yarda a karanta mani shi a youtube ko a maida shi audio ba tare da izinina ba.
*BISIMILLAHI RAHMANI RAHIM*
Page6️⃣0️⃣
"Ahmad ke sanar da ni yanzu , dan haka na ce a kawo su nan ɓangaren."
Shiru wajen ya ɗauka idan ban da Affan dake ta surutunsa da Dadynsa, duk da hankalin dadyn baya tare da shi, hakan ya saka bai biye masa ba. Kallon Dadynsa ya yi da ya yi tsaye ya kasa zama ya ce,
"Dady ka ko ka jauna miyi biyekfac."
Maganarsa sa ce ta bawa Ammi dariya, Ajmal ɗin ma bai san yana yi ba, dan haka ya ja hannun Ajmal tare da yin kuka kasancewar kuka ba ya masa wuya.
Kukan nasa ne ya janyo hankalin Ajmal har ya ce.
" Affan lafiya?"
Sai ya masa nuni da abincin da aka zuba masu, gane me yaron ke nufi ne ya saka shi ɗaukarsa suka ƙarasa gaban dinning table suka zauna.
Nan Affan ya fara shan ruwan shayi.
Ahmad ne ya yi sallama yana rike da babyn yayin da Amatullah ke biye a bayansa.
Da sauri Ajmal ya mike ya ƙarasa gabansu yana mai karɓar yaron, kallon Amatullah ya yi tare da cewa.
"Me ke faruwa?"
"Wani ne ya shigo mani ɗaki cikin dare."
A ɗan ruɗe ya fara magana yana cewa
"Bai taɓa ki ba ko? Ba abinda ya maki? Me ya faru da ya shigo?"
Ta buɗe baki da niyyar yin magana kenan sai Nasreen ta ce.
" Ƙarya kike munafukar banza, duk matakan tsaron da ke gidan nan akwai wanda ya isa ya shigo gidan nan ne? Ga yawan masu tsaro idan masu duty rana sun kwanta masu dutyn dare za su fara aiki ba barci suna zagaye da gidan nan dan ganin me ke faruwa sannan za ki wani..."
"Dakata Nasreen wace hujja kike da ita da za ki ƙaryata ta? Me ye ribata idan ta yi ƙarya?"
Ajmal ne ya yi maganar yana kallon Nasreen fuskarsa a tsuke. Inda ta cigaba da cewa.
"Me ya saka lokacin da security suka shiga ba su ga wani ba, kuma na tabbatar sai sun bincike gidan nan kafin su dakata, da ace gaskiya ne wani ya shiga to ba makawa sai an kama shi."
Ammi ce ta kalli Amatullah da ta sunkuyar da kai ƙwallon cike a Idanunta ta ce.
"Amatullah zo ki zauna mu yi breakfast."
Girgiza kai ta yi tare da cewa.
"Na yi karin kumallo yanzu na gama, na koshi Ammi."
"Okay ki zauna a falo ina zuwa."
Daga nan ta juya zuwa falo ya yin da suka bi ta da kallo. Ammi ta kalli Ajmal tare da cewa.
"Ka zauna mana ga breakfast nan na jiranka."
Girgiza kai ya yi tare da cewa
"Ammi bana jin cin komai."
Affan ne ya kalli Dadynsa tare da cewa.
"Dady baby ne?"
Gyaɗa masa kai Ajmal ya yi tare da cewa.
"Eh Baby ne, this is your junior brother."
Wani kallo Nasreen ta watsa masa tare da cewa.
"Never"
Affan ya tashi yana dariya ya ce.
"Dady jan yi waca da ci."
Dariya ya masa tare da cewa.
"Affan bai yi ƙwari ba, ka bari zuwa gaba sai ku dinga wasa tare."
Ammi ce ta tashi ta je ta samu Amatullah tare tana zaune akan Centre carpet ta rakuɓe, kallonata Ammi ta yi tare da cewa.
"Amatullah"
Ta kira sunanta yayin da take zama akan kujera, Amatullah cikin sanyin murya ta ce.
"Ina kwana Ammi."
"Lafiya lau kin tashi lafiya?"
Amatullah ta amsa mata da lafiya. Inda Ammi ta cigaba da cewa.
"Ya muka ji da fargaba?"
Ta amsa da Alhamdulillahi.
Ajmal ne ya ƙaraso wajen Ammi ta karɓi Abdallah da ke hannunsa, haɗa Idanu Ajmal da Amatullah suka yi idanunsu ya sarƙe jikin na juna,da sauri ta sunkuyar da kanta tare da ce masa.
"Ina kwana?"
Murmushi ya yi tare da cewa.
"Kin tashi lafiya?"
"Alhamdulillahi."
Ammi ta kalle ta tare da cewa.
"Amatullah ki bamu labarin abinda ya faru a daren jiya."
Daidai lokacin da Nihal ta karaso wajen yayinda da Nasreen ta haura upstairs abunta. Affan ya karaso a guje ya zo wajen Dadynsa yana dariya.
Ɗaukarsa ya yi ya zaunar da shi a saman cinyarsa.
Nan Amatullah ta basu labarin abinda ya faru tun daga fitowarta daga ɗakin iya har komawarta da shirin kwanciya da ta yi duk ta basu labari.
Shiru suka yi gaba ɗaya falon tunaninsu akan waye wannan.
Ajmal ne ya yi ajiyar zuciya tare da cewa.
Waye yake da zarrar da zai iya shigowa cikin gidan nan har ya fita ba wanda ya gan shi? Ba zai yiwu ba sai dai idan an haɗa baki da ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan nan, idan kuwa an gano waye wallahi sai ya ɗanɗani kuɗarsa."
Ammi ce ta ɗora da cewa.
"Anya kuwa cikin ma'ikatan gidan nan ne?"
"Ammina ba abun mamaki ba ne fa, dan hakan ta faru ba wani abu ba ne, ɗan Adam fa ba'a iya masa, bar ganin suna mana aiki muna biyansu kowane wata idan wani ta saka su su kashe mu aka masu alƙawarin miliyoyin kuɗaɗe wallahi zasu iya nawa aka yi, Indai akan kuɗi ne, dan wannan ma ai ƙaramin abu ne dan sun nemi ɗauke babyn tare da mata barazana kan ta yi nesa da mu."
Nisawa ya yi kafin ya ɗora da cewa.
"Sai dai abinda ke ɗaure mani mai waye wannan da yake son ɗauke yaron, sannan meye ribarsa akan haka? Wannan shi ne abinda nake son ganowa. Amma kafin nan Ammi ina son ya kasance yarinyar nan da babynta su zauna a wannan ɓangaren tare da mu..."
Kafin ya ƙarasa maganar da zaiyi ne ya ji muryar Nihal afirgice tana cewa
"What's?"
Dakatawa ya yi yana kallonta da lulun idanunsa masu cike da kwarjini, ji ta yi ta kasa cewa komai dan ya mata kwarjini da yawa. Inda ya cigaba da cewa.
"Ammi za ta fi samun tsaro a anan idan tana tare da mu, fiye da can tunda hakan ya faru zamansu a can ba ƙaramar barazana ba ce."
Nihal ce ta fara magana ba tare da ta lalle shi ba idanunta na kan wayarta.
"Ta dawo nan ɓangaren da zaman a matsayinta na wace ce?"
Tayi maganar daidai lokacin da wayar Ammi ke ƙara, kira ya shigo cikin wayar.dan haka sai ta tashi ta nufi bedroom d'in ta.
Kallon Nihal Ajmal ya yi tare da cewa.
Za ta dawo nan ɓangaren da zama ne a matsayinta ta uwar ɗan me gidan, nan gidan ɗanta ne za ta saki jiki ta wala bana son wani ya takura mata, ko kaɗan bana son a yi mata ko kallon banza ne tana da iko a cikin gidan nan a matsayinta na uwar ɗana."
Taɓe baki Nihal ta yi sannan ta ce.
"Ai da sauki tunda uwar ɗanka ce wane iko take da shi a gidan nan, tunda ba aurenta ka yi ba kuma ɗan da kake ikirarin cewa ɗan ka ne saboda tana uwarsa tana da iko da gidan ai ko a musulunci shege baya gadon ubansa, ko mutuwa ka yi duk tarin dukiyar da kake da su ko allura ba zai gada a ciki ba, dan haka ni ban ga abun ado ga ɗan shege ba, ko kunya bakwa ji sai wani so da kake nuna masu dama ka manta da su ka maida hankali wajen yin istigfari ko Allah zai..."
Dakatawa ta yi da maganar ganin yadda idanunsa suke rikiɗe zuwa ja, tana ganin ya nufo ta ta haɗiye yawun wahala tare da rintse Idanunta, shaƙo wauyar ta yi ta miƙar da ita tsaye ɗaga hannu ya yi da niyyar marinta sai ga Ammi ta dawo, ganin abinda yake ƙoƙarin aikatawa ne ya sa ta kiran sunansa da ƙarfi. Wanda hakan ya saka shi dakatawa ya sake ta.
Komawa ya yi ya zauna yana wuci kamar wani mayunwacin za ki, dan maganar da ta faɗa masa haƙiƙa ya bala'in ɓata masa rai.
"Tun da ta ga yanayinsa ta san ransa ya matukar ɓaci, kuma ta san cewa Nihal ce ta janyo komai, dan haka ta kalli Nihal tare da cewa.
"Me kika masa?"
"Ammi akan yarinyar nan ne fa."
"Nihal ka da ki shiga abinda ba ruwanka, ki zuba masu Idanu matukar dai ba kin ga abinda ya saɓawa addini ba ne, ba na son tashin hankali ki kiyaye zama da shi na san halinki na san na sa, dan haka ki kiyaye abinda zai janyo maku saɓani."
"To Ammi zan kiyaye."
Daga nan ta tafi ɗakinta inda Ammi ta kalli Amatullah dake kuka ta ce.
"Ki daina kuka nan gidanku ne ki dauka haka ne, idan kin ga abinda daidai ba ki mani magana."
Goge hawayen fuskarta ta yi dan har ga Allah ya fi son zama a ɓangaren ma'aikatan gidan, dan da alama zamanta a ɓangaren masu gidan akwai ƙalubale sosai a gabanta. Musamman ta bangaren Nasreen da Nihal. A hankali ta soma magana tana cewa.
"Dan Allah ku barni na koma can wajen zan fi sakin jiki."
Ammi ce ta kalli Ajmal inda ya bawa Amatullah amsa da cewa.
"Zamanki a can barazana ce a rayuwarku a halin yanzu, ko kin manta da abinda ya faru ne a daren jiya?"
"Girgiza kai ta yi tare da tuna abinda ya faru, kuma tabbas gaskiya ne dan haka ta yi shiru ba tare da ta ce komai ba."
Affan dake wasa da IPad ne ya kalli Amatullah tare da cewa.
"Dady taya kuka?"
"Murmushi ya yi tare da kallon Affan ya ce.
"Ta daina kuka."
Ya sake tambayar Ajmal tare da cewa.
"Wace ce?"
"Antynka ce."
Tashi ya yi ta zauna gabanta tare da goge mata hawayen fuskarta ya ce.
"Anty waye ya duce ci?"
Murmushi ta masa tare da cewa
"Ba wanda ya duke ni."
Amince ta ce wa Affan ya kira mata Kande ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan ne. Da gudu ya nufi kitchen ya kira ta duka taho tare.
Durƙusawa ta yi tare da gaishe da su, inda Ammi ta sanar da ita cewa.
Ta kai Amatullah ɗakin baƙi, nan Amatullah ta mike ta bi bayan Kande, suka nufi ɗakin baƙi.
Ɓangaren Hafsat kuwa tun barcin da take yi a ɗakin Mum na ita ta farka ba sai ƙarfe tara na safiya.
A hankali ta buɗe Idanunta tana kallon ɗakin Mum, tana mamaki sai a lokacin wasu abubuwan suke dawo mata a cikin ƙwakwalwarta. Dafe kai ta yi tare da cewa.
"Na shiga uku. Yanzu nan gidan kowa ya san halin da nake ciki? Me zan faɗa masu, dama Munnir yana neman yadda zai yi ya rabu da ni ba dama, to yanzu ya samu hanya."
Tunawa da ta yi da Mum ya saka ta sakin murmushi, dan ta san ko ba komai Mum ba zata taɓa bari ya rabu da ita ba, dan haka sai ta yi hamdala ta godewa Allah da ya saka Mun na ƙaunarta.
Tashi ta yi ta kalli kayan dake jikinta sai kunya ta kama ta, dan haka sai ta buɗe wardrobe ɗin Mum ta ɗauki hijabin Mum ta saka, kai tsaye ta nufi hanyar falo dan ta ga idan ba kowa ta fice daga cikin gidan.
Ƙarar buɗe ƙofar da ta yi suka jiyo suna zaune a dinning area suna breakfast.
A hankali ta fara sanɗa tana tafiya, tana kawowa daidai saitin dinning area ta waiga sai suka hada Idanu da Dad, gabanta ne ya yi muguwar faduwa, a hankali ta fara takowa zuwa wajen Idanunta a ƙasa.
Kamar wata Saliha ta durƙusa har ƙasa ta gaida Dad, ya amsa mata ba yabo ba fallasa. Sannan ta gaida Mum ta amsa mata ba walwala a tare da ita, hakan ya saka ta ɗaga kai tana kallon Mum, ganin kallon da take mata ne ya saka ta sha jinin jikinta.
Idanu suka haɗa da Munnir ganin mugun kallon da yake mata ne ya sa ta ɗan harare shi tare da murguɗa masa baki, sai a idanun Dad, sannan ta ce.
"Ya Munnir ina kwana."
Banza da ita ya yi kamar bai ji me take faɗa ba, Munnirat ce ta gaida Hacsat kasancewar ta girme ta.
"Zauna mu yi breakfast mana."
Mum ce ta fadi haka tana kallon Hafsat.
Girgiza kai Hafsat ta yi tare da cewa
"Ammi zan tafi gida ne yanzu."
Okay shikenan tunda haka kika ce, kallon Munnir da ya kammala breakfast ta yi tare da cewa.
"Ka tashi ka kai ta gida."
"Mum ni kuma zan kai ta gida? Ƙarfe tara fa yanzu kin san kuma yau ƙarfe tara zan shiga..."
Hannu ta ɗaga masa alamar dakatarwa, sannan ta ce.
" Lecture ne ballantana ka ce idan time ya yi ba za'a barka ka shiga lecture ba, hasalima kai ne malamin da ke koyar da lecture ɗin."
"To Mum ko mu ne muke koyarwa ai bai kamata..."
Kana ɓatawa kanka lokaci ne gara ma ka tashi kana ƙara makara ne."
Ba musu ya tashi tare da yi masu sallama ya ɗauki jakkarsa ya fice.
Hafsat ta bi bayansa cike da jin daɗi, wajen motarsa ya nufa tana biye da shi a baya, ya shiga motar itama ta zagaya ta zauna a gefensa, fuskarsa a tsuke take har ya tada motar ya yi horn mai gadi ya bude masa gate ya fice daga gidan.
Suna cikin tafiya ne Hafsat ta kalle shi tare da cewa.
"Wai Ya Munnir me na yi maka ne da ka tsane ni har haka, sai dai gara ka fauwalawa Allah komai domin mu Allah ya haɗa aurenmu ne, kamata ya yi a ce ka cire damuwar da ke zuciyarta ka fuskanci ƙaddararka, wato ni kenan zamu yi au...."
Dariya da yake ƙyaƙyatawa ne ya saka ta yanke maganar da take yi tare da tsuke fuska a fusace ta fara magana.
"Wai me ka ɗauke ni ne, mahaukaciya ko me? Magana me mahimmanci nake yi kana dariya. Shin me ye na dariya a jikina
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 22 Chapter of 51