Share this page
zo nan garin kuma a gidan nan. Jinjina kai ya yi tare da cewa "Eh ita ce yallaɓai me ya kawo ta nan?" "Wannan ba damuwarta ba ne ka fara mai da kanka wajen makomarka." Kallonsu DPO ya yi tare da cewa. "Wannan da kuke gani shi ne musabbabin komai da ke faruwa na rashin daɗi ga Ajmal." Gaba ɗaya suka mai da dubansu ga INDAKUƊINKA. Inda DPO ya cigaba da cewa "Wannan da kuke gani shi ne wata ta bashi kwangilar a lalata rayuwar Amatullah." Kallonsu ya yi daya bayan daya ya cigaba da cewa. Amma dai ku ji daga bakinsa. Kallon INDAKUƊINKA ya yi tare da cewa. "Ka maimaita abinda ka faɗa ɗazu a gaban Ajmal " Shiru ya yi sai da DPO ya daka masa tsawa wanda ya saka shi buɗe baki ya yi ya fara basu labarin kamar yadda ya bawa Ajmal. Komai bai rage ba ya sanar da su zuwan Hafsat har zuwa alluran da ya mata da maganin da ya sakawa Ajmal, tare da faruwar komai. Daidai lokacin da ya gama ba su labarin ne suka ga Ajmal ya rugo a guje, gaba ɗaya suka zuba masa idanu suna kallon gudn me yake yi. Sai suka ga ta nufo wajen Amatullah wacce ta yanke jiki za ta faɗi, ya tare ta ta faɗa jikinsa. *Daga alƙamin*✍️ Zainab Abdullahi KNT (Maman Ihsan) 09065327995 Comments & share Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z 🤦‍♀️ *YAR MAYE*🤦‍♀️ (_The drug abuser_) *NA* Zainab Abdullahi KNT (Maman Ihsan) https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *GARGAƊI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. Ban yarda a karanta mani shi a youtube ko a maida shi audio ba tare da izinina ba. *BISIMILLAHI RAHMANI RAHIM* Not edit Page5️⃣1️⃣ Sai suka ga ya nufo wajen Amatullah wacce ta yanke jiki za ta za ta faɗi, ya tare ta ta faɗa jikinsa. Hankalin kowa ya dawo wajensu, dan su gaba ɗaya hankalinsu na kan INDAKUƊINKA na bayanin da yake masu, Ajmal wanda saukowarsa kenan daga downstairs ya ga halin da take ciki. Hakan ya saka ya karaso ya taimaka mata ba tare da ta faɗi ta bugu a ƙasa ba. Gaba ɗaya hankalinsu ya dawo wajen Amatullah ganin halin da take ciki, kowa ya tausaya mata. Nasreen ita kuma hankalinta a tashe yake a wajen, dan labarin INDAKUƊINKA ba ƙaramin tayar mata da hankali ya yi ba, tana ganin yanzu ya tabbata kowa ya shaida cewa Ajmal ne uban yaron nan, girgiza kai ta yi yayin da hawaye je zarya akan fuksarta. Wucewa ta yi daga wajen ta nufa upstairs tana zubar da hawaye, anan ko ba wanda ya san halin da take ciki sai Nihal wacce ta saka mata idanu, tana lura da halin da take ciki. Tana shiga cikin bedroom ɗin ta ta saka key ta rufe tare da fashewa da kuka ta ce . "Ina ba zai taɓa yiwu ba hakan ba za ta faru ba, Ajmal yana da mace kama ta ne zai yi mu'amala da wata ko a cikin wani hali take hakan ba mai yiwuwa ba ne, sannan har da ɗa? Kai wannan ba gaskiya ba ne wannan mafarkin ya isa haka nan ya kamata na farka daga wannan barcin." Marin fuskarta take yi tare da cewa. "Nasreen farka ki buɗe idanunki wannan lamarin ba zahiri ba ne mafarki ne, ya kamata ki farka daga wannan mummunar mafarkin da kike yi." Sai marin fuskarta take wai ta farka zuwa zahiri ta bar wannan mafarkin da take yi. A can falo kuwa bayan Ajmal ya kwantar da Amatullah kan kujera ne, Dad ya kalli Dr Fu'ad tare da cewa. "Fu'ad ko dai akwai wata matsala ne?" Murmishi ya yi tare da girgiza kai alamar ba matsala sannan ya ce, "Ta suma ne sakamakon jin wannan labarin ya matuƙar girgiza ta ne, kamar yadda Ajmal ya girgiza ya suma a asibitina bayan ta tabbatar da cewa ɗansa ne. Sai dai da dukkan alama ma yarinyar nan Amatullah tana buƙatar kulawar likita, dan tun bayan haihuwar da ta yi na lura da ita, kasancewar ba kwanciyar hankali a tattare da kowa ya sa ban kula ba, amma tana buƙata a mata ƙarin ruwa a jikinta." Kallon fridge da ke gafensu ya yi tare da cewa "Za'a samu ruwa nan ko?" Da sauri ya nufi fridge ya buɗe ya ɗauko robar ruwa. Daidai lokacin da Nasreen ke saukowa daga zuwa downstairs, ɗankwalin da ke kanta ma ta cire, duk kan ya hargitse dama sunan ba tsayi ba. Kai tsaye ta nufi INDAKUƊINKA ta ɗaya hannu ta sauke masa mauka guda biyu, wuyar rigarsa ta cacumo tare da cewa. "Waye ya turo ka nan gidan Wallahi ban yarda da cewa mijinana ne uban wannan shegen yaro ba, ka zo ka hargitse wa mutane gida, ta ya ya hakan za ta faru kai ma jiyanka kudi akan yi ne ko me? Ko kuma kai da ita bakinku ɗaya?" Haka ta dinga sambatu tana yi tana dukan INDAKUƊINKA, Anmi ce ta zo ta janye ta. Dad ya kalli DPO ya ce, "D.P O ka tafi da shi station kafin komai ya lafa" Jinjina kai ya yi tare da cewa. "Okay bari mu je." Sai kin Muryar Nasreen suka yi tana cewa. "Kai ma munafukin police ne kai DPO har da haɗin bakinka a cikin wannan lamari. Munafuki" Haka ta dinga suratai tana sambatu ita kaɗai, kallon Ajmal ya yi tare da cewa. "Ka kai ta ɗakinta." Ba musu ya ja hannun Nasreen suka nufi ɗakinta Har lokacin ba ta daina masifa tana zage-zage ba, sanin halinta ne ya saka ya rufe ta a ɗakin ta waje sannan ya nufi downstairs. A can kuwa sau uku Fu'ad na watsawa Amatullah ruwa ba ta farfaɗo ba. Sai a na huɗu ne ta saki wani ajiyar zuciya tare da fashewa da kuka. "Me na yi maku kai da ita ne da kuka cutar da rayuwata? Saboda son kuɗinka har ka iya aikata mani haka ba tare da ka yi tunani akan mahaifiyarka da ƙanwarka ba ko? Shin 'yan Adam ne ku ma kuwa? Ba tare da hakki ba kun cutar da rayuwata kun ruguza mani farin cikina kun mamaye zuciyata da damuwoyi, kamar yadda dahu kan mamaye ɗaki bayan kashe fitila. Ta yi amfani da kai wajen ruguza rayuwata kun saka na rasa kowa nawa na rasa komai kun saka iyayena sun kore ni daga gida, Abbana ya ce baya son sake ganina na bar masa gidansa, ya Kore ni cikin duhun dare haka na fito ba tare da sanin inda zan dosa ba. Wanda a dalilin haka na sake komawa harkar shaye-shaye wanda na ɗauki alƙawarin dainawa, kun saka na bar garin iyayena da ba tashi na sani, na tsinci kai na a wani garin da ban san kowa ba, bani da kowa bani da komai, wurn kwana ya gagare ni yau na kwana nan gobe na kwana can kafin na samu matsuguni, wanda har na kai na kawo a rana ɗaya sau ɗaya nake cin abinci, duk da na kasance ina ɗauke da ciki haka na dinga rayuwar yunwa da wahala, har na kai sai na yi barar abincin da zan ci, wasu suna tausaya mani ganin ina ɗauke da ciki wasu na mani kallon mahaukaciya. Tabbas kun ruguza mani rayuwata ku jira rugujewar ta ku rayuwar dan na san Allah ba zai taɓa barinku ba." Kuka take sosai tana sambatu yayin da Ajmala shima kukan yake yi, Ammi ma hawaye take zubawa. Hatta Dady da Fu'ad da Ahmad jikinsu ya yi sanyi . Ammi ce ta ƙarasa jikin Amatullah tare da riƙo hannunta cikin ta ta hannun ta ce. "Amatullah" Sai a lokacin ta buɗe idanunta ta fara kallon mutanen da ke wajen ɗaya bayan ɗaya. Sai dai ba ta ga wannan mutumin ba da shi da police officer da ya kawo shi. Tashi zaune ta yi a hankali sannan ta mike tsaye, jiri ne ta ji yana neman ɗaukarta, ta yi saurin zama. Fu'ad ne ya kalli Ammi tare da cewa. "Ammi a kaita ɗakinta na zo na duba ta." Kai Ammi ta jinjina alamar gamsuwa sannan ta kalli Nihal da ta yi mutuwar tsaye, tun da ta ji labarin da INDAKUƊINKA ya bada ne ta sandare a wajen. "Nihal taimaka mata zuwa ɗakinta." Sai da Ammi ta sake magana kusan sau biyar sannan ta ji ta." Riƙe ta ta yi suka nufi part ɗin da take. Har lokacin Ajmala bai daina kukan da yake ba, daƙyar Ammi ta rarrashe shi ya tsagaita kukan da yake yi. Fu'ad ne ya fita daga gidan dan ɗauko kayan aiki. Ammi ce ta bi bayan Amatullah inda ta same ta kwance a har lokacin tana kuka. Nihal na tsaye a kanta ta zuba mata idanu. Iya ce ta shigo take tambayar abinda ya faru, Nihal ko kallon banza ba ta yi mata ba ballantana ta amsa mata. Ammi ce ta shigo bakinta ɗauke da sallama. Kallon Iya ta yi tare da umartarta da ta je ta kawo mata tea. Zama ta yi gefen gadon tare da janyo Amatullah ta ɗaura kanta a saman cinyarta. Iya ta kawo mata tea da bread sai soyayyen ƙwai, an jera a faranti. Da ƙyar aka iya lallaɓa ta ta sha ruwan tea kawai bayan haka ba ta iya cin komai ba Fu'ad ne ya shigo bakinsa ɗauke da sallama Ahmad ne a bayansa. Jakar hannunsa ya ajiye a gefe, inda Ammi ta tashi ta fita, Nihal ma da iya suka mara mata baya, Ahmad ma fita ya yi. Idanuwan ta ya kalla yana murmushi tare da cewa "Sannu Amatullah." Jinjina kai kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba. Duba ta ya yi sosai kafin ya yi mata ƙarin ruwa. Ɓangaren Ajmala kuwa tunda Ammi ta rarrashe shi ya daina kuka ne ya nufi ɗakin Nasreen ya buɗe ta, sai faman masifa take yi, bai kula ta ba ya yi ficewarsa zuwa bedroom ɗin sa. Wayarsa ya ɗauka tare da lalubo lamabar wayar DPO ya danna masa kira, bugu biyu ya ɗauka tare da cewa. "Hello." "D.P.O ina yaron nan yake?" "Yana rufe anan ranka ya daɗe." Jinjina kai Ajmal ya yi tare da cewa "Ina son a binciko yarinyar nan a duk inda take a faɗin ƙasar nan, sai ta girbi abinda ta shuka." "Kada ka damu ranka ya daɗe za mu sanar da jami'an da ke can, za'a kama ta da yardar Allah." Katse wayar ya yi tare da kiran DPO na can garin Minna. Yana fitowa daga station ya nufi wajen motarsu ne wayatsa ta soma ringing. Bugu biyu ya ɗauka tare da cewa "Yallaɓai ya kake?" "Alhamdulillahi" Ajmal ya amsa masa tare da sake tamabayarsa. "Ya aikin na ku?" "Alhamdulillahi." "Ma sha Allah, ka san an samu nasarar kama yaron nan ko?" "Eh na sani." "Okay yanzu ita yarinyar da ta bashi wannan aikin nake son a kama ta ko wace ce ita kuwa." "An gama sai dai muna son mu samu bayanan iya yarinyar." "To ni dai duk yadda za'ayi ku tabbatar kun kama wannan tsinanniyar." "Kada ka damu zamu yi iya ƙoƙarin mu." "Ba iya ƙoƙarin ku nake so ku yi ba fiye da ƙoƙarin ku nake so kuyi." Bai jira cewar sa ba ya katse kiran wayar. A daren ranar da misalin ƙarfe sha biyu ne dare Ajmala ya kasa barci, sai tunanin Jaririn da Amatullah ta haifa yake yi. Gaba daya barci ya ƙara da masa sai juyi yake yi shi kaɗai. Ji yayi hankalinsa ba zai taɓa kwanciya ba idan bai je ya ga ɗansa ba. Dan haka ya nufi ƙofar fita ya ya yi daga ɗakin, downstairs ma ba kowa kasancewar kowa ya yi barci a wannan lokaci. Ƙoafar fita ta buɗe ya fice daga falon. Security na kwai a harabar gidan, wanda hasken gidan ya zagaya ko ina tamkar rana ne ba dare ba Ahmad ya hanga tsaye tare a harabar gidan, kafin ma ya kira shi har Ahmad ɗin ya zo wajensa. "Sir akwai abinda kake so ne?" "Ɗakin yarinyar nan nake so ka nuna mani." Mamaki ya kama Ahmad bayan ya duba a time ya ce wa uban gidansa. "Sir yanzu fa dare ya yi ƙarfe ɗaya ake nema yanzu." Kallon da Ajmal ya masa ne ya sa shi cewa. "Sorry sir." Daga nan suka nufi ɓangaren ma'aikatan gidan. Kai tsaye har bedroom da Amatullah ke kwance ya nuna masa, dan haka da hannu ya nuna masa hanyar fita Ba musu Ahmad ya fice yayin da Ajmal ya shiga cikin ɗakin bakinsa ɗauke da sallma. Tsayawa ya yi a jikin ƙofar tare da jingina bayansa da ƙoafar, hannunsa ya rungume yana kallonsu. Da ke ba ta kashe hasken ɗakin ba hakan ya sa ya samu kallonsu da kyau. Tana sanye cikin riga da wando farare na barci, masu laushi da santsi tana kwance tana barci. Sai dai da kukan alamau ta sha kuka kafin ta yi barcin dan hawaye ne suka bushe a idanunta, kuma har yanzu idonta a kumbura suke. Gadon baby ba kowa dan ba ta kwantar da shi a gadon ba, sai suka kwanta nata gadon yana gefenta. A hankali ya ƙarasa bakin gadon tare da durƙusawa saman ƙafarsa, yana kallon yaron yana kuka. Hannunsa ya miƙa jikin yaron da niyyar ɗaukarsa. *Ku yi hakuri da wannan bana iya dogon typing yanzu* *Daga alƙalamin*✍️ Zainab Abdullahi KNT (Maman Ihsan) 09065327995 Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z 🤦‍♀️ *YAR MAYE*🤦‍♀️ (_The drug abuser_) *NA* Zainab Abdullahi KNT (Maman Ihsan) https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *GARGAƊI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. Ban yarda a karanta mani shi a youtube ko a maida shi audio ba tare da izinina ba. *BISIMILLAHI RAHMANI RAHIM* Page5️⃣2️⃣ Hannunsa ya miƙa jikin yaron da niyyar ɗaukarsa sai ya janye hannunsa da sauri, sakamakon ganin Amatullah ta miƙo hannunta tare da sa shi jikin babyn. Tsayawa ya yi ya zuba mata idanu ganin yadda idanunta suka kumbura ga fuksarta da shaidar hawayen da ya bushe, alamar dai ta ci kuka sosai Kafin ta yi barci. Tausayin yarinyar ne yake ji har cikin ransa, tabbas ya san ta sha wahala a rayuwarta dan ya ji yadda take ta sambatu ɗazu, na Irin gwagwarmayar da ta sha bayan ta bar gaban iyayenta, a zuciyarsa yake jin ba daɗi, dan gani yake kamar shi ne Ummul aba'isin faruwar komai, saboda shi ne ya yi rape ɗin ta, duk da ba laifinsa ba ne amma ya ya ɗaurwa kansa wannan alhakin. Dan da ace bai yi ba amma da ba zai zama shi ne sanadin komai ba, kuma ga shi sai Allah ya sa da rabon samun ɗa a tsakaninsu. Kuka ne ya zo masa, yana kallon yaron hawaye na shatatowa daga idanunsa, ganin Amatullah ta janye hannunta ne ya sa ya ɗauki babyn tare da zuba masa idanu yana Kum cigaba da kukansa. Kan yaron ya shafa wanda ke a cike da suman jinjirtaka, zubawa yaron idanu ya yi tare da maganar zuci. 'Tabbas Ammina kin yi gaskiya ke Da Ummi da kuka ce yaron nan yana kama da ni, wanda ni ban ga kakannina da shi ba sai yanzu. Wanda da a makance nake gani nake ba daidai idanunku ke faɗa maku ba, ashe ni ne idanuna ke faɗa mani ba daidai ba. Saboda. Lokacin kwata kwata ban yi tsammanin haka ba. Dan ni ba fasiƙi ba ne kuma ban taɓa aikata zina ba, hasalima na tsani mazinata. Amma yau da kaina na gane cewa na taɓa aikatawa, babban abun takaici ma yarinya da ta kasance cikakkiyar budurwa ni ne farkon wanda ya fara kusantarta. Na raba ta da budurcnta wanda a dalilin haka ta rasa farin cikin ta, sai dai kash iyayen sun kore ta a sanadin haka, kuma dalilin cikin ɗana. Nima fa ina da babban laifi tunda da ni aka yi amfani wajen aikata komai. Amma tabbas ku jira sakamakon abinda kuka aikata dan sai kun yi nadama na har abada.' Yana zaune a ƙasa jikin gadon har lokacin lokacin yaron na rungume a hannunsa, shiga kuma sai zubar da hawaye yake yi. Sama da mintuna talatin suna a haka, kafin Amatullah ta motsa da niyyar kai hannu jikin babyn jin ba ta taɓa shi ba ne ya sa ta miƙa hannunta tana ltaube, sai ta ji ta shafa sunan kai, ita a tunaninta gashin kan babyn ta shafa, shi za shafa ba ta san na Ajmal ba ne, kasancewar shi ma Ajmal jinsin mahaifiyarsa ya ɗauko wato larabawa. Dan haka gashin kan Ajmal mai laushi ne da santsi a nannaɗe irin na larabawa, dan kallo ɗaya za ka masa ka gane cewa shi Balarabe ne. Dan haka da ta ji ta shafo gashin kan Ajmal da ya karantar da kansa a gadon yayin da gangar jikinsa ke ƙasa,sai kawai ta cigaba da barcinta don a tunaninta kan Abdallah ta shafa ba ta san na uban Abdallah ta shafa ba. Dama cikin barci take. Duk da cewar ba ta saba kwanciya gado ɗaya da shi ba a gadon baby yake kwana. Ajmal na jin yadda take shafa gashin kansa bai bai damu ba, zuwa can sai ya ji abinda take masa yana saka shi cikin wani yanayi, jikinsa ya fara mutuwa wanda hakan ya sa ya zare kansa daga saman gadon.sai hannunta ya saka a saman katifa. A hankali ya kwantar da Abdallah a gadon. Ganin za ta bude idanu ne alamar za ta farka tana motsawa ya sa shugaban saurin kwanciya ƙasan ties ɗin ɗakin. Da sauri ta buɗe idanunta sakamakon jin ba inda hannunta ya ke ta ji Abdallah ba, ganin yana kwance a inda ta kwantar da shi ne ya sa ta mamaki ai kamar suman kansa ta ji tana shafawa, sai dai kuma shi ai yana sanye da hula. Ba yadda za'ayi ta shafa gashin kansa, tashi zaune ta yi tana mamakin wannan lamari. Tunawa da ta yi da ta yi ba ta rufe ƙofa jiya ba ya sa ta wani tunani, dan daga kuka sai barci ya ɗauke ta ba tare da ta shirya ba. Dan haka sai ta yunƙura za ta tashi ta sauka ta je ta rufe ƙofar. Shi kuma Ajmal na nan kwance ƙasa, yana jiran ta koma barci ya tashi ya fita zuwa ɗakinsa, dan ba ya son ta san ta shigo ɗakin. Saukowa da ta yi ta sauko da niyyar zuwa rufe ƙofa, sai ji ta yi ta taka abu ashe ƙafar Ajmal ta taka, wanda shi kuma wajen janye ƙafarsa ne ƙafarsa ta zame sai ta faɗa saman jikinsa, ya saka hannyensa a riƙe ta gam a jikinsa kamar mai tsoron a ƙwace ta. Tsorata ta yi ta buɗe baki za ta yi ihu kenan sai yana rafin hannunsa ya rufe mata baki, zaro idanunta ta yi tana kallonsa. Shima cikin idanunta yake ta kallo. Tsawon mintuna uku suka ɗauka a haka suna kallon juna, bayan ya cire hannunsa daga bakinta ne ta fara kiciniyar tashi daga jikinsa, sakinta ya yi inda ta miƙe tsaye tana kallomsa cikin mamaki. "Me ya kawo ka ɗakina a daidai wannan lokaci?" Kallon agogon ɗakin ta yi ta ga ƙarfe ɗaya na dare. "Na ce me ka zo yi?" "Na zo ganin ɗana ne." "Ɗan ka?" "Eh ko ba nawa ba ne?" "Tura baki ta yi kamar yadda ta saba idan babu ji daɗi ba." "To me ya saka sai dare za ka fansa?" "Sai daren ne na ji ba zan iya barci ba sai na gansa ." "Hmmm dama akwai ranar da za ka yarda cewa ɗan ka ne? Lokacin da likitoci suka tabbatar ba ƙaryatawa ka yi ba?" "Sai da na ga hujja a idanu na kafin bayarda." "Wace irin hujja?" Tashi tsaye ya yi tare da matsawa dab da ita, har suna jiyo numfashin juna. "Hujjar da dole ta saka na gasgata ko da likitoci ba su faɗa ba, dan na ga komai da idanuna." "Ta ya ya?" "Video da abun ya faru." "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un na shiga uku." Ta faɗa tana ɗora hannu aka, wane irin tashin hankali ne a ce ga video da ke lalata da ita? Hawaye ne suka fara zarya a saman fuskarta. "Ke wasa fa nake maki ba wani video, kada ki damu kin ji?" Tura baki ta yi ya zuba mata idanu yana kallon ɗan ƙaramin bakin, cije laɓɓansa ya yi tare da cewa. "Idan muna magana ki daina tura bakin nan, dan za ki iya saka ni na aikata abinda bai dace ba." Kallomsa ta yi cikin rashin gane me yake nufi. "Sai da safe." Daga nan ya fice ya nufi part ɗin su. A babban falosu yana bayan ta shiga ya tura k'ofar ne ta ji ana cewa "Daga ina kake a daidai wannan lokaci?" Juyawa ya yi da mamaki yake kallonta. Nihal ce take tsaye rungume da hannye. "Inda kika aike ni." Daga nan ya fara tafiya zai haura upstairs. "Wait Ya Ajmal." Tsayawa ya ba tare da ya juyi ba. Har ta ƙarasa kusa da shi sai kai hancinta gaban rigarsa, tana shinshinawa. "Ke me ye haka?" Cikin baƙin ciki da takaici ta ce, "Amma wallahi ka bani mamaki, ka rasa da wa za ka dinga mu'amala sai waccan kucakar yarinyar ? Ka bar matarka a ɗaki sannan ka je ɗakin wata karuwa ballagaza." "Ke ki iya bakinki kafin ki yi nadamar faɗar abunda kike faɗa." "Nadama akan na fadi gaskiya?" "Wace gaskiya?" "Tun ƙarfe goma sha biyu na fito zan shiga kitchen na nemi abinda zan ci sai na ga kana fita daga falo, na leƙa ta window na ga ka nufi ɓangaren da waccan yarinyar take, sama da awa ɗaya kana can sai yanzu ka dawo jikinka na ƙamshin turaren ta." Da mamaki yake kallonta. "Wato tun sha biyu shi ne kike tsaye a nan kina jira na ko? Wane turare kike magana bayan nawa da ba saba amfani da shi." "Ba naka ba ne, wannan turaren yarinyar can ne na ji ƙamshinsa a jikinka, kuma dama nima shi nake amfani da shi Ammi ta ba ta kyautar da take shafawa bayan ni da ita ba mai amfani da shi, kai na san ƙamshin turaren ka." Juyawa ya yi da niyyar tafiya. Ta sake taran gabansa. "Idan har baka haɗa jiki da ita va ba yadda za'ayi turarennta ya shafi jikinka. Idan ni ce na rungume ka za ka fara daka mani tsawar wai kai ba muharramina ba ne kai mai tsoron Allah, to ita waccen muharramarka ce da ka haɗa jiki da ita?" Ture ta gefe ya yi ya haura upstairs ya nufi ɗakinsa. Durƙushewa ta yi a wajen tana kuka tare da sake jin tsanar Amatullah a zuciyarta. Tunda ta ga Ajmal ya nufi part ɗin ma'aikatan gidan ta san inda zai je, shi ya sa ta kasa samun nutsuwa ta gaba ɗaya, abincin da ta fito da niyyar nema ba ta nema ba, ta fasa yunwar ma ta daina ji, tsananin zafi zuciyarta ke mata. Dan haka tana ta safa da marwa a cikin falon har sama da awa ɗaya ba ta ga ya fito ba. Tashi ta yi a wannan daren duk da kasancewa dare ya yi sosai sai dai gaba ɗaya gidan hasken fitilu ne kamar rana, ga wasu security da basa barci sai ka da kawo suke ta ko ina. Kai tsaye ta nufi ɓangaren ma'aikatan gidan ta tura ƙofar falon ta ji a buɗe, dan haka ta nufi bedroom na Amatullah. Sai ta ji ta a datse hakan ya sa ta fara knocking. Amatullah da take kwance ne ta ji knocking ta taso tana tunanin ko Ajmal ne ya sake dawowa, dan ba wanda ke mata knocking cikin dare. "Buɗe ƙofar ta yi tare da cewa me ka dawo yi kuma yan..." Kasa ƙarasa maganar ta yi sakamakon yadda aka turo ƙofar da ƙarfi, har ta buge ta. Mamaki ne ya kama ta ganin Nihal ta shigo ɗakin tana mata wani banzan kallo. "Kin ɗauka ta dawo ne kike tambaya me ya dawo yi?" Cikin ƙarfin hali ta ce, "Aunty Nihal me ya faru na ga kin shigo cikin daren nan?" "Me ya faru kike tambaya ta? Me Ya Ajmal ya zo yi a ɗakinki a cikin Wannan daren? Kuma me kuke yi fiye da awa ɗaya yana cikin ɗakinki? Sannan ya aka yi naji ƙamshin turarensa a jikinki?" Mamaki ne ya kama Amatullah dan ita ba ta san ma Ajmal ya daɗe a cikin ɗakin ba, tunda tana barci sai da ta farka ne ta zo sauka ta taka shi a rashin sanin yana wajen. "Aunty Nihal wallahi bai dad'e ba fa? Hasalima bai wuce mintuna sha biyar ba, kuma na farka ne gan shi kwance a..." Asjariyar da Nihal ta yi ne ya sa Amatullah yin shiru. "Kin farka kika ganshi kwance?" Girgiza kai ta yi tare da cewa. "Ka da ki bari ki zama abokiyar gaba a waje na, domin idan har kika zama abokiyar gabata to ina da illoli da yawa da zan iya

Chapter 17 of 51