Share this page
kwance a gado yayin da Abba ke tsaye yana kallonta tare da cewa. "Wannan tunani da kika sakawa kanki kada ya janyo maki rashin lafiya fa, ta yaya mai rai ba zai ci ya sha ba? Sai kuka kike tun jiya kin kasa samun sukuni." "Ta ya ya zan iya samun sukuni Mallam bayan ƴata guda ɗaya da ta rage mani tana cikin matsala." "Ki.cire wa kanki wannan tunanin in sha Allah ba ta cikin matsala za ta dawo lafiya da kanta." "Ina ji a jikina cewa tana cikin matsala babba, tana buƙatar taimakon mu." "Ta yaya kika sani." Kuka ne ta fashe da shi tare da cewa "Tun shekaranjiya nake ta mafarkai akanta, tana gudu tana ƙoƙarin zuwa wajen mu tana kira na tana cewa mu taimake ta mu yafe mata." Goge hawayen da ke kan fuskarta ta yi tare da cewa "Wallahi na ji a jikina ba ta cikin kwanciyar hankali, tana cikin mawuyacin hali. Ga shi ba ta san kowa ba a ƙasar nan , ina za ta je? Wani hali take ciki? Duk bamu sani ba . Waya sani ma ko tana raye." Ta ƙarasa maganar cikin matsanancin kuka. Shiru Abba ya yi tare da cewa "In sha Allah tana raye kuma za ta dawo cikin ƙoshin lafiya. Girgiza kai ta yi cikin takaici ta fara magana. "Yaushe za ta dawo gobe ko jibi? Wani tabbacin kake da shi? Lokacin da abin ya faru da ka tausaya ka saurare mu ai da hakan ba ta faru ba, korar da ka yi mata ba zai taɓa canza ta daga kasancewar ta ƴar da muka haifa ba. Ba'a taɓa canzawa tuwo suna duk lalacewarta 'yar mu ce dai ita ba zamu taɓa iya canza ta koge ta ba." Shiru ya yi duk ya shiga damuwa sakamakon ganin halin da Umma ke ciki ba. Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa. "Tabbas nasan cewa Ni ne na Kore ta daga gidan nan, amma abinda ta aikata ai ko waye hukuncin da zai ɗauka kenan Indai abu na gari ne da ya san ya bawa 'yarsa tarbiyya na ƙwarai. Me muka rage Amatullah da shi daidai gwargwado ina ƙoƙarin ganin na mata duk abinda ya dace na mata iya gwargwadon iyawata. Da farko shaye-shaye sannan na biyu ga cikin shege wani irin baƙin ciki ne wannan? Idan na barta a gidan nan kullun na kalle ta zuciyata za ta iya bugawa." Kukan Umma ne ya tsananta take cewa "Shikenan ka kore ta dan kade zuciyarki ta buga, to ni tawa zuciyar ta kusa bugawa kowa ya huta." Ɓangaren Hafsat kuwa sai washe gari ta samu Munnir ya je ya belinta. Amma duk da haka ta sha wuya a wajnsu dan sun dake ta ba laifi. Bayan sun fito ne ya buɗe mota ta shiga yayin da take tafiya a hankali , kafin ta ƙaraso wajen motar. "Kin ga ina da abun yi da ba za ki ɓata mani lokaci a banza ba." Ya ƙarasa maganar tana jefe mata wani mugun kallo. Buɗe murfin motar ta yi ta shiga ba tare da ta yi magana ba. "Wanna shine na farko kuma na ƙarshe da za ki kira ni a cikin harkokin banzarki. Me ya hana baki kira abokan shaye-shayen na ki sun zo sun karɓe ki ba? Ko da yake mai laifi baya karɓan mai laifi ko?" Wai Yaya Munnir me ya sa ba ka da tausayi ne? Ba ka ga halin da nake ciki ba ko tausaya mani ba ka yi ba kake cewa me ya sa na kira ka? Akwai wanda zan kira sama da kai ne? Kai ne mijin da zan aura kuma ɗan uwa na." Taɓe baki ya yi tare da jan motar sannan ya fara magana. "Ai na faɗa maki cewa ki cire zancen aure a ranki dan ni kam ba zan iya auren ki ba. Har yau ba zan gaji da faɗa maki ba, Amatullah dai ita nake so." "Ai wallahi gara da ni kan Amatullah. Dan Iya shaye-shaye ne kawai ita kuma bayan shaye-shaye ga bin maza, ƙarshe ma da cikin shega ubanta ya Kore ta. Ka ga kuwa duk lalacewar masa ta fi kashin shanu." Murmishin takaici ya yi tare da cewa "Tabbas da saka hannun ki wajen lalacewar tarbiyyar Amatullah, dan farkon haɗuwata da ita ba haka take ba, sai bayan da ta sauya na gane cewa tana tare da ke, ranar da mahaifinta ya fahimci bata zuwa makaranta mun je makarantarsu bata nan, muna dawowa na ga kina sauke ta a mota. Wannan dalilin ya sa na dasa ayar tambaya akanki. Ina kike kaita a duk lokacin da ta bar gidansu da niyyar zuwa makaranta? Kuma sai bayan an tashi ki dawo da ita?" "Kaga Mallam daga taimako za ka fara zargina? Ganinta na yi a hanya tana tafiya tana maye alamar a buge take na tsaya na ɗauke ta na rage mata hanya shine laifi." "Ƙarya kike, amma ko ma mene ne zan gano gaskiya, kuma wallahi idan na gano ke ce ummul'aba'isin komai sai kin ɗanɗani kuɗarki." Daga nan ta figi motar suka ɗau hanya. "Yunawa nake ji ko za ka tsaya a kan hanya ka siya mun abinda zan ci. Dan ba son cin abinci nake ba." Ko kallonta ma bai yi ba kuma fuskarsa a haɗe. Taɓe baki ta yi tare da cewa "Duk dai wannan abun akan Amatulla ne ko?" Dariya ta yi tare da cewa "Kada ka ɓatawa kanka lokaci domin kuwa Amatullah ba wanda ya san duniyar da take. Iyayenta sun kore ta kuma na san har abada ba za ta taɓa dawowa ba, gara ka daina ɓatawa kanka lokaci. Mu rufawa juna asiri kawai." Juyawa ya yi ta kalle ta tare da cewa "Mu rufawa juna asiri fa kika ce? Ke ba ki isa ki rufa mani asiri ba wallahi sai dai ni na rufa maki ballantana ba zan iya auren fasiƙa ba." Dariya ta kece da shi tare da cewa "Fasiƙai dai domin idan ni fasiƙa ce kaima fasiƙi ne dan na ga tare da kai muka aikata fasiƙancin" Tsuki ya yi cikin takaici ya ce, "Ina takaicin faɗawa tarkonki da na yi a baya, kuma tunda na gane cewa ke ba cikakkiyar budurwa ba ce kin rasa budurcnki na fasa auren ki, dan ban san cewa bayan shaye-shaye kina haɗa da bin maza ba, sha sha sha ballagaza jaka." Maganarsa haka ta daki zuciyarta, maganar ta mata zafi sosai sai Da nata daure saboda tana masifar son Munnir kuma ba abunda ba za ta iya aikatawa a kansa ba. Birni ya yi a ƙofar gidan su Hafsara mai gadi ya buɗe masa gate ya shiga. Yana parking ne ra fito a guje ta nufi cikin gidan. Fitowa ya yi shima ya nufi cikin gidan. Tana zuwa ta faɗa jikin Mum ɗinta tare da fashewa da kuka. Cikin tashin hankali Mum ta fara tambayarta abinda ya same ta ina kuma ta shiga kwana biyu. Muryar Munnir da ke shigowa suka ji yana cewa "A wani kango aka maka ta ta je siyen kayan shaye-shaye a wajenasu siyarwa, shine jami'an N.D.L.E.A. suka kama ta can ta kwana." Ga mamakinsa sai ta ga Mum ɗin ko a jikinta, madadin ta mata faɗa amma sai ta sai ma ta fara tsinewa waɗanda suka kama ta. Ransa ne ya ɓaci ya fara magana tana cewa "Mum wai shin ita ce da da laifi amma laifinsu kike gani? Me ye amfanin irin wannan rayuwar da ta daukar..." Tsawar da Mum ta daka masa tare da cewa "Haba Munnir Hafsat da 'yar uwarki ce kuma wacce kake shirin aure, me ya sa ba za ka goyi bayan naka ba sai wasu can?" "Mum maganar gaskiya..." Dakatar da shi ta yi ta hanyar ɗaga masa hannu . "Ya isa Munnir za ka iya tafiya bari na ɗauko maka saƙo da za ka kaiwa Ummanka." Daga nan ta nufi bedroom ɗinta yana mamakin a ce ba za ta taɓa ganin laifin Hafsat ba komai ta yi daidai ne. A can ɓangaren Ajmal kuwa bayan ta farfaɗo ne yana kwance sai kallon kowa yake yi ɗaya bayan ɗaya. Amminsa da Dad sai matarsa Nasreen da take riƙe da hannun ɗan su Affan. Gefe guda kuma kuma kuma Amintaccen bodyguard ɗinsa ne Ahmad, yayin da abokinsa Dr Fu'ad ke tsaye a gefe ya zubawa AJMAL idanu. Kallo ɗaya Ajmal ya yi wa Dr Fu'ad ya ɗauke idanunsa bayan ya watsa masa wani mugun kallo. Affan ne ya ƙarasa wajen gadon tare da riƙe hannun AJMAL ya ce, "Dady ka tashi daga barci?" Kai ya gyaɗa masa ba tare da ya ce komai ba. Dad ɗin Ajmal ne ya kalli Hajiya Bilkisu ya ce, "Hajiya mu koma wancan asibitin ina son na ga yarinyar nan." Jinjina kai ta yi tare da cewa "Muje Alhaji." Daga nan suka fita su biyu yayin da Nasreen ta zauna akan kujera ta zubawa mijinta idanu. A reception suka ga Nurse dake ɗauke da jaririn Amatullah. Hajiya Bilkisu ta bata umarnin ta biyo su. Ahmad ne ya biyo bayansu ya ce su shiga ya kai su. Ahmad na zaune a mazaunin direba yayin da Nurse ɗin mai suna Hauwa'u ta zauna gefen Ahmad. Dad da Ammi suna baya. Amatulla da ke kwance sai aikin kuka take ne ta ga an fito ƙofar ɗakin, ɗaga kai ta yi dan ganin mai shigowa harlikacin ba ta daina kuka ba, dan har idanunta sun kumbura fuskarta ta yi jajir abu ga farar fata. Nurse da ke kula da ita ta gani dan haka ta share hawayenta tare da ɗan tashi ta kishingiɗa. "Har yanzu baki daina aikin kuka ba sai kanki ya yi ciwo? Kina son zazzaɓi ya rufe ki ko?" Dad ne da Ammi suka shigo ɗakin tare da sallama. Gaba ɗayansu suka amsa yayin da Amatullah ta gaishe su. Suka amsa mata ba yabo ba fallasa. Shiru ɗakin ya ɗauka kafin Dad ya yi gyaran murya ya kalli Nurse ya ce ta basu wuri zasu yi magana da ita. Ba musu ta kwantar da Babyn tare da ficewa. Kallon Amatullah ya yi tare da cewa "Yarinya mene ne sunanki?" Cikin muryar kuka ta fita fara dakushewa ta ce, "Suna na Amatullah" "Daga wane giri kike?" "Minna Niger state" "Shekarunki nawa?" "Goma sha takwas." "Mene ne gaskiyar abinda ke tsakaninki da Ajamal ne, da har aka tabbatar da cewa ɗansa ne?" "Ba wani abinda ke tsakanina da shi hasalima ban taɓa ganinsa ba sai jiya na fara ganinsa." "Kenen da gaske ne da ya ce an siye ki ne dan ki masa sharri akan cewa cikin da kika haifa nasa ne, kuma aka siye sauran likitoci suka haɗa bakinsu ɗaya?" Kuka ne ta fashe da shi tare da cewa "Wallahi ban taɓa yiwa kowa sharri ba?" "To ki sani daga yanzu ba kasar nan iya binciken zai tsaya ba har ƙasar waje zan saka a tafi ayi bincike idan gaskiya ta fito to wallahi za ki yi nadama na har karshen rayuwarki." Kuka take kamar ranta zai fita ba kakkautawa tana cewa Wallahi ban san komai ba ban san waye uban yaron nan ba zan iya ɗaukar al-qur'ani na na yi rantsuwa da shi akan cewa ban san waye uban ɗana ba." Yadda take magana ne tana kuka ya sa jikinsu ya yi sanyi da dukkan alamu iya gaskiyar ta ce take faɗa sun gani a cikin idanuta. Ammi ce ta fara rarrashinta daƙyar ta tsagaita kukan da take yi . Ammi ta dafa kafaɗarta tare da cewa "Ina son ki sanar dani labarin rayuwarki da zuwanki nan." Nan ta kwashe labarinta tun daga lokacin da Hafsata ta shigo rayuwarta da yadda ta fara shaye-shaye har ranar da ta yi nadama ta cigaba da zama gida da bin Umarnin iyayenta. Har zuwa ranar da Hafsat ta kira ta ta kawo mata waya da bayan ta maida mata tana shirin komawa gida aka soka mata wannan allurar da tun daga lokacin ba ta iya tuna komai, har zuwa bayyanar cikinta da korar da Abbanta ya mata. Har lokacin da ta koma gidan Nafeesat da zama ta cigaba da shaye-shaye har dawowarta Kaduna da wahalar da ta sha na rashin muhalli da rayuwar kunci da yunwa da kwanan da take a makarantar primary har ranar da Ajamal ya kaɗe ta. Umma mai dai da idanuta suka cika da ƙwalla na tausayin Amatullah, hawaye ne ya fito daga idanun Ammi. Abba ma ya tausaya mata. Amatullah kam sautin kukanta ne kawai ke tashi a ɗakin. Turo ƙofar aka yi aka shigo, Ajamal ne da Nasreen sai Affan da ke bayansu. Daga karshe sai Dr Fu'ad ya shigo da sallama. Kallonsu ya yi tare da gaishe su. Dr Fu'ad ne ya ce "Ina uwar jarinin ne?" Sai a lokacin ne ta ɗago kai ta kalli Dr Fu'ad. Zaro idanu tayi cikin mamaki yana Kallonta tare da cewa "Ke ce?" *Daga alƙalamin*✍️ Zainab Abdullahi KNT (Maman Ihsan) 09065327995 Comments & share Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z 🤦‍♀️ *'YAR MAYE*🤦‍♀️ (_The drug abuser_) *NA* Zainab Abdullahi KNT (Maman Ihsan) https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *GARGAƊI* Ban yarda ba kuma ban amince ba a maida Mani wannan book ɗin audio ko a karanta mani shi a youtube ba tare da izinina ba. Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. Page3️⃣4️⃣&3️⃣5️⃣ *BISIMILLAHI RAHMANI RAHIM* Zaro idanu ya yi cikin mamaki yana kallonta tare da cewa "Kece?" Ɗago kai ta yi itama ta kalle shi. Itama mamaki ne ya kamata, da sauri ta sunkuyar da kanta ƙasa hawaye na faɗa fitowa daga idanunta. Ammi ce ta kalli Dr Fu'ad ta ce, "A ina ka san ta?" Girgiza kai ya yi tare da cewa "Ban san ta ba." Kallon tuhuma Ammi ta ma masa tare da cewa "To ya aka yi ka yi mamaki da ganinta, ita ma tana kallon ka ta ta sunkuyar da kanta ƙasa?" "Ammi ki yarda da zancen da na faɗa maki nan san ta ba." Kallon Amatullah Ammi ta yi tare da cewa "Kin san shi ne?" Kan ta a ƙasa idanunta na tsiyayaar da ƙwalla ta ce, "Ban san shi ba." "To me ya sa da kika gan shi kika sunkuyar da kai ƙasa da sauri?" "Ba komai." "Shikenan tunda haka kuka ce koma dai mene ne za mu gano shi." Ajmal ne ya kalle ta tare da cewa "Yadda kika saka sunama ya ɓaci kima ta ta zube a cikin mutane haka nake so ki je ki wanke Ni ta hanyar bayyanar da gaskiyar lamari. Idan kuma ba haka ba to gaskiya ban san abinda zan iya aikatawa ba, wanda kuma hakan zai mani daɗi, yayin da ke kuma hakan zai maki muni." Daga nan ya ja hannun Affan suka fita Nasreen ta mara masa baya. Dr Fu'ad ma fita ya yi daga ɗakin. Abba ne ya kalli Ammi tare da cewa "Mu tafi ko?" Daidai lokacin da jaririn ya tsandare da kuka kamar wanda ake aikawa allura. Juyawa suka yi suna kallonsa sannan suka kalli Amatullah, gani suka yi ko a jikinta ba ta ma kalli inda yaron yake ba ballantana ta ji wani abu a ranta. Ammi ce ta ƙarasa wajen gadon jaririn tare da ɗauko shi ta zo ta miƙawa Amatullah shi. Ko kallonsa Amatullah bata yi ba ballantana ta karɓe shi. "Ki karɓe shi ki bashi nono ya sha." "Ba zan iya karɓar shi ba ballantana har na bashi mama ya sha, tunda har ya fito duniya Alhamdulillahi a kai shi gidan marayu a riƙe shi a can." "Saboda me ya sa ke ba za ki riƙe shi ba?" "Saboda shi na rasa farin ciki na da kwanciyar hankali, saboda shi iyaye na suka Kore ni daga gida, idan na koma da shi bakin cikin da suke ciki zai karu, gara na koma ni kaɗai na nemi yafiyarsu hakan zai sa su yi saurin saukowa ba zan kunyata ba." Kukan da yaron ke yi ne ya sa nurse da ke kula da ita Hauwa'u ta shigo da sauri. "Wai har yanzu ba za ki karɓi yaron nan ba?" Kallon Ammi ta yi tare da cewa "Na rarrarshe ta na lallaɓe ta akan ta bashi nono ko kallonsa ma bata yi ba, tunda ya zo duniya wai tana tsoron ta kalle shi ma balle har ya shiga ranta ta so shi." Haka Ammi da wannan nurse suka dinga rarrashin ta akan ta bashi nono amma sam ta ƙi, dan tana gani idan ta fara shayar da shi zai bata matsala ba za ta iya rabuwa da shi ba, hakan kuma matsala ce a rayuwarta. Amimi ce ta yi ajiyar zuciya tare da cewa "Yanzu idan aka kai shi gidan marayu ke ina za ki nufa?" Nima ban sani ba Abbana ya Kore ni ya ce kada na sake komawa gidansa bani da kowa a ƙasar nan, ni kafin ban san yadda zan kula da kaina ba balle jaririn da na haifa." Ta ƙarasa maganar tana mai fashewa da matsanancin kuka. Tausayinta ne ya kama Ammi dan tabbas yarinyar na buƙatar taimako, dan haka ta kalli mijinta tare da cewa "Alhaji yarinyar nan rayuwarta abin tausayi ne tana bukatar taimako." "Duk yadda kika yi daidai ne." Kallon Amatullah ta yi tare da cewa "Idan aka sallame ki daga nan zan ɗauke ki mu tafi gidana da ke, kafin nan sai mu san abin yi, zancen yaro kuma tunda kin ce ba za ki shayar da shi ba to bazan takura maki ba, duk da cewar ba abinda ya kai nonon uwa tashiri a wurin jariri. Zan sa Doctor ya rubuta sunan abincin da za mu siya wanda zai maye gurbin nonon da ba ki bashi ba." Kuka ne ya kufce mata ta fara godiya tare da yi wa Ammi addu'a, ta kasa gane kukan farin ciki ne ko na baƙin ciki. Miƙawa nurse babyn tayi tare da cewa "Bari na je na samu Doctor ɗin." Doctor ya rubuta masu kalar madaran da za su dinga bawa jaririn, ya kuma ce zuwa gobe za'a sallame ta tunda ya ga jikinta ya yi kyau. Ammi ta yiwa nurse da ke kula da Amatullah kyautar kuɗi, tare da neman alfarmar cewa ta tsaya ta kwana da ita yau tunda gobe za'a sallame su. Nan nurse ta yi mata godiya tare da yi mata alƙawarin cewa za ta tsaya ta kwana tare da su. A can ɓangaren Ajmal kuwa tunda suka bar asibitin a hanyar komarsa gida Sa tuna abinda likitoci suke faɗa, ya na tuna yadda duniya ta lalace yanzu da kowa za'a iya haɗa baki a cutar da kai, har da abokinka. Haka zuciyarsa ke masa zafi sosai, yayin da ita kuma Nasreen sai surfa masu zagi take yi daga Amatullah har likitocin. Shi dai ba abinda ya ce mata illa kawai abinda ke zuciyarsa ma kaɗai ya ishe shi. Suna isa gida kuwa ko jira a buɗe masa ƙofar bai yi ba ya buɗe tare da fitowa da sauri ya nufi part ɗin su. Yana shiga ya fara dunƙule hannunsa yana naushin bangon bedroom ɗin sa. Idanunsa sun rikiɗe sun yi jajir. Nasreen ce ta ke bubbuga ƙofa tare da kiran sunansa, amma ina ko jinta baya yi. Zama ya yi turu tare da fashewa da kuka wiwi kamar ƙaramin yaro. Kuka yake sosai ba kakkautawa, kukan da wanda tunda ya zo duniya bai taɓa yin makamancin sa ba, hankalin Nasreen ne ya tashi sosai, tana dukan kofar a banza.kiran wayar Dad ta yi ta sanar da shi. Halin da ake ciki. Nan da nan Dad da Ammi suka kama hanyar dawowa gida. Koda suka iso gidan duk kofar a rufe, Dad da Ammi suka dinga knocking suna kiran sunansa amma a banza dan ba ya jinsu. Dad ne ya kalli Nasreen tare da umartar ta ta kawo key. Da hanzarin ta je ɗakinta ta ɗauko key ta zo tana zirawa ta buɗe. Har suna rige-rigen shiga ciki ɗakin nasa. Can suka hango shi kwance sai kuka yake yana dukan ƙasan ɗakin. Koda suka ƙarasa gare shi idanunsa duk sun rikiɗe zuwa ja, ga jikinsa duk ya yi zafi sosai. Hankalinsu ne ya daɗa tashi Dad ne ya ce, "Bari na kira Doctor Fu'ad ya zo ya duba ka." Ɗagawa Dad hannu ya yi alamar ya bari, ba ya so. Daƙyar da rarrashi suka dinga bashi magana masu daɗi tare da masa alƙawarin cewa za su binciko gaskiyar magana ya kwantar da hankalinsa har ya haƙura. Kallonsu ya yi tare da ce masu yana son kaɗaicewa shi kaɗai dan Allah su fita, ya masu alƙawarin ba zai sake ba. Dad da Ammi suka fita yayin da Nasreen ta tsaya, kallonta ya yi sannan ya nuna mata ƙofa ba tare da ya yi magana ba. Ta fahimci yana nufin ta fita ne dan haka ta buɗe da niyyar magana ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu, ganin ba wasa a fuskarsa ya sa ta fita ta ja masa kofar. Ƙarasawa ya yi jikin ƙofar tare murzawa kofar key ya bar key ɗin a jikin ƙofar. Tunda ya shiga bai fito ba haka ya wuni a cikin ɗakin ba ci ba sha, sai dai idan lokacin sallah ya yi zai shiga bathroom ya ɗauro alwala ya zo ya yi sallah a cikin ɗakin. Har lokacin cin abincin dare ya yi bai fito ba, gaba ɗaya sun hallara a dinning table, amma har lokacin AJMAL bai fito ba tunawa Ammi ta yi rabonsa da abinci tun tun jiya, ko breakfast bai yi ba ga shi yanzu har ƙarfe tara na dare. Kallon Dad ta yi tare da cewa "Yanzu haka za mu zuba masa idanu?" "To maybe zai ji naki, dan ko da na ga lokacin sallar magrib ya yi ban gan shi ba na ƙwanƙwasa masa kofa ya ce zai yi sallarsa a ɗaki, da alama har yanzu bai huce ba." Tashi Ammi ta yi ta nufi ɗakinsa, duk rarrashin duniyar nan ta yi shi amma bai buɗe ba, sai ce mata ya yi ya samu abinda ya ci a fridge baya son komai sai da safe. Haka ta haƙura ta koma wajen cin abincin, ba wanda ya ci abincin kirki haka suka tashi cikin sanyin jiki. Washe gari ma haka tun da asuba da ya idar da sallar ya bar gidan bayan ya nemi amintaccen bodyguard d'insa Ahmad. Bayan Ahmad ya sauke shi a unguwar da ya buƙata ne ya ce ya tafi idan ya gama abinda zai yi zai kira shi ya zo ya ɗauke shi. Da sassafe suka nufi ɗakinsa baya nan, hankalinsu ya tashi sosai, sai da Ahmad ya kwantar masu da hankali ta hanyar cewa kada su damu ya fita ne dan ya rage damuwar da yake ciki ta hanyar ziyartar wurin shaƙatawa. Haka suka haƙura tunda sun ji inda ya tafi. Da misalin ƙarfe biyar na yamma ne Doctor ya kira Ammi cewa su ɗauki Amatulla da jaririnta. Ammi ta tura Ahmad kan cewa ya je ya d'auko ta daga asibiti. Bayan ya ɗauko su daga asibiti ne suna kan hanyar zuwa gida wayarsa ta yi ringing, ganin boss ɗin sa ne ke kiransa ya sa ya ɗaga da sauri ɗagawa. "Yallaɓai barka da yammaci." "Ka zo ka ɗauke ni a inda ka ajiye ni." Daga nan ya kashe wayar tare da cewa "Baiwar Allah ki yi hakuri zan biya na ɗauki me gidana." Cikin sanyin murya Amatullah ta ce, "Ba damuwa." Daga nan ya ɗauki hanyar inda zai ɗauko Ajmal. *Daga alƙalamin*✍️ Zainab Abdullahi KNT (Maman Ihsan) 09065327995 Love you oll😍😘 🤦‍♀️ *'YAR MAYE*🤦‍♀️ (_The drog abuser_) *Na* Zainab Abdullahi KNT (Maman Ihsan) 🤦‍♀️ *'YAR MAYE*🤦‍♀️ (_The drog abuser_) *Na* Zainab Abdullahi KNT (Maman Ihsan) https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *GARGAƊI* Ban yarda ba kuma ban amince a juya mani littafi ta kowace siga ba, ko a karanta mani shi a youtube ko a maida shi audio ba tare da izinina ba. Page3️⃣6️⃣&3️⃣7️⃣ Daga nan ya ɗauki hanyar inda zai ɗauko AJMAL. Bayan ya isa wajen da ya aje shi ne yana da niyyar ɗaukar wayarsa ya kira shi ne ya hange shi yana ƙarasowa. Yana zuwa ya buɗe murfin gaban motar ya shiga, yadda ya saba zama bayan motar kam yau bai zauna ba. Kallon shi Ahmad ya yi tare da cewa "Barka da yammaci sir." Jinjina masa kai kawai ya ya ba tare da ya yi magana ba, illa ya kwanta da kansa a jikin kujerar motar idanunsa a lumshe. Sai da suka yi tafiyar mintuna goma sai jaririn ya ɗan fara kuka. A firgice Ajmal ya buɗe idanunsa tare da kai dubansa bayan motar. Ganin Amatullah a bayan motar tana rike da jariri ne ya sa shi daka tsawa tare da kallon Ahmad ya ce, "Dakatar da driving ɗin da kake." Gafen hanya ya samu yi parking. Yayin da Ajmal ya juya cikin kakkausar murya ya fara magana. "Me kuma kike nema a wajena? Ɓata sunan bai ishe ki bane?" Juyawa ya yi ya maida dubansa ga Ahmad tare da cewa "Me take yi a cikin motata?" "Sir dama Ammi ce ta ce, na ɗauko ta." "Ina za ka kaita?" "Gida ta ce na taho ta ita." "What?" Jinjina kai Ahmad ya yi tare da cewa "Haka Ammi ta

Chapter 10 of 51