Share this page
ya koma hanyar gida, shi Kuma Mallam Danladi ya shiga gidan yana kwalawa dansa kira. Mallam Abdullahi na komawa gida ya nufi d'akin Umma, huhabinta ya dauko mata ya zo ya saka mata, yana saka mata hijabi ne ya ji horn daga k'ofar gida, Hakan ya tabbatar masa da cewa sun iso. D'aukar ta ya yi ya nufi hanyar k'ofar gida, inda ya tatar da Mallam Danladi da dansa, inda ya shigar da ita bayan motar shi ma ya shiga, yayin da Mallam Danladi ya shiga gaba gefen direba. Babban asibitin gwamnati na garin suka nufa da ita, suna isa aka d'auke ta a kekan d'aukar marasa lafiya suka k'arasa da ita emergency. Munnir kuwa tunda Sadik ya sauke shi a gida ya ce ya tafi da motar gidansa ya aiko a kawo masa. Yana shiga falon ya yi sallama inda ya tarar da Mom d'insa da k'anwarsa Munnirat suna fira a babban falon . Amsa masa sallamar suka yi tare da zuba masa idanu suna karantar yanayinsa, da alama yana cikin damuwa ganin yanayinsa. Bai ce komai ba ya nufi part d'insa, Umma ta bi shi da Kallo don tun ba yau ba ta San akwai abunda ke damunsa sai dai yana boye mata ne kawai baya so ta sani, Hakan ya sa ta zuba masa idanu dan har tambayarsa ta yi akan tafiyar da zai yi ya ce abokinsa zai raka, ta yi ta yi ta fad'a mata gaskiya ya boye mata Shi Kuma ba komai ya saka shi boye mata ba sai ganin tana son ya auri 'yar k'nanwarta, Dan ya San har yanzu ba ta huce da maganar da ya yi ba na cewa baya son Hafsat 'yar uwarsa, Kuma Dad d'insa ya goya masa baya. Yana shiga ya turo k'ofar d'akinsa tare da murzawa k'ofar key. Munnirat ce ta biyo bayansa tana kiransa, Jin k'ofar a rufe ne ya saka ta yin knocking, yana junta ya yi banza da ita, zuwa can ya ce. "Mene ne?" "Yaya dan Allah ka bude k'ofar nan magana nake so mu yi da kai." Share ta ya yi ya fara cire hulansa da agogonsa, rigarsa ya cire ya bar farin singileti. Sannan ya nufi k'ofar ya bude mata. Shigowa ta yi tare da cewa. "Ya sannu da zuwa." "Yauwa." Ya amsa a takaice. Kallonta y yi tare da cewa "Mene ne kike son fad'a mani, ki fad'a da sauri ki fita ba na son dmuwa." Zama ta yi a bedside drawer tare da fara magana cikin kulawa ta ce. "Yaya dan Allah ka sanar da ni abunda ke damunka, gajinka cikin wannan yanayin ya saka ni cikin rashin Jin dad'i, Dan Allah ka da ka boye mani idan ma baka son Mom ta sani ne ba zan fad'a mata ba." Ta k'arasa maganar tana langwabe wuya. Kallonta y yi tare da nazarinta, tabbas zai so fad'a masa danuwarsa, amma ba zai iya sanar da ita gaskiya ba, Dan ba zai so kowa ya san halin da Hafsat ke ciki ba, Dan bai San yadda zasu d'auki lamarin ba, Musamman mahaifiyarsa, zai fi so a ce sai Hafsat ta dawo ta rabu da danta ya saura ba kowa a hannunta Sannan zai sanar da su. Dan idan ba haka ya tabbatar idan mom ta sani ba zata taba bari Hakan ya faru ba. Dubansa ya mai da zuwa ga Munnirat ya ce. "Ba abunda nake boye maki kin sani, dan haka ta shi ki fita." Tashi tsaye ta yi tana kallonsa tare da masa magiya, har jikinsa ya yi sanyi ya ce. "Zan sanar da ke komai amma yanzu na gaji gobe zamu yi magana." Jinjina kai ta yi tare da cewa. "To Allah ya kai mu gobe." Da amin ya amsa sannan ta fice daga d'akin, shi Kuma ya nufi bathroom don yin wanka. Ammi ta Kalli Mahaifiyar ta tare da cewa. "Umma lafiya na ga tunda muka zo kika d'auki babyn nan sai kuka kawai kike yi?" Goge hawaye ta yi tare da cewa. "Ka da ki damu ki je ki yi wanka Ku ci abinci, farin ciki ne kawai nake yi ba wani abu ba." "Kwalawa d'aya daga cikin ma'ikatan gidan tsohuwar ta yi, ba jimawa sai ga ta ta k'araso cikin gairmamawa ta durkusar da kai alamar tana jira a bata umarnin Kiran da aka yi mata. Bayan ta goge hawayen ne ta cewa ma'ikaciyar ta kai Amatullah d'akin bak'i Ammi ta umarci Amatullah da ta bi bayan matar akai ta masauki zasu kawo mata abinci a can d'akin. Bayan Amatullah ta tafi an raka ta d'akin da zata zauna ne Ammi ta Kalli Mahaifiyar ta ta ce . "Ummata sanin cewa Ajmal ba ta hanyar aure suka haifi yaron nan ba ne ya sa kike kuk?" Gurgiza kai tsohuwar ta yi tare da cewa. "Yana matukar kama da Ajmal ba banbanci ga shi yaron da mahaifiyarsa sun shiga raina, ina Jin son su a cikin zuciyata, ji nake ina ma a ce matsayin mata da miji suka zo gaishe ni, da na fi kowa farin ciki, Dan Allah idan Kun je gaban iyayenta a nema masa auren yarinyar nan, dan sun dace da juna." Duk maganar da suke yi cikin harshen larabci suke yi, inda Ammi ta nuna mata cewa za'a nema masa aurenta, amam sai daga baya, kasancewar iyayen yarinyar na fushi da ita, sai an basu hak'uri an nemi yafiyarsu sun yafe mata kafin a yi maganar aure. Dama mahaifin Ajmal baya nan ya tafi k'asar Egypt ranar da zasu koma Nigeria shima zai dawo zasu hadu su je gidan su Amatullah. Daga nan ita ma Ammi ta mike ta nufi d'akin mahaifiyarta. Bangaren Ajmal kuwa bayan ya isa part d'insa ne Wanda ya Sha gyara sai kamshi da sanyi ke tashi, Wanda aka gyara masa dabida dawowarsa Kwantar da Affan ya yi Saman sofa, sannan ya nufi bedroom d'insa. Wanka ya yi sannan ya sauya kayan jikinsa zuwa k'ananan kaya, system d'insa ya janyo ya fara danne-danne a akai. Nasreen ce ta shigo ciki ita ma ta sauya kayan jikinta zuwa doguwar Riga mara nauyi, kasancewar a part din akwai d'akinsa da nata a ciki, Kasancewar kusan zamansa a k'asar yafi yawa saboda kakarsa bata iya jure rashinsa na tsawon lokaci, komai nasu akwai a part din. Zuba masa idanu ta yi tare da cewa. "Ba ka ci abinci ba honey shi ne ka zauna, pls ka taso muje muci abinci." Ba tare da ya kalle ta ba ya ce. "Kici abinci kawai kada ki tsaya jirana, akwai wani aikin da nake yi ne kina ba na Jin yunwa, shayi kawai nake bukata a halin yanzu." Ba tare da ta sake magana ba ta tashi ta fita, ba jimawa sai ta dawo hannunta rike da jug da cup. Zuba masa ta yi ta mika masa, amsa ya yi tare da kallonta, ganin fuskarta ba walwala ne ya rike cup din ba tare da ya Sha ba ya ce "Me ke damunki na ga kina cikin damuwa." Kawai sai ta fara yi masa kuka, ganin haka ya sa hankalinsa ya dan tashi, ajiuye cup din ya yi tare da riko hannunta cikin nasa ya ce. "Please Nasreen ki daina kukan ki sanar da ni abunda ke damunki, ko Kina son hankalina ya tashi ne?" "Honey ni dai wallahi bana son yarinyar nan bana kaunar ganin ta a kusa da mu, ka nisantar da kanka daga gare ta wallahi zuciyata za ta iya fashewa idan ina ganin ta." Shiru ya yi tare da cewa tare da yin tunani kafin ya ce. "Meye matsalarki da wannan yarinyar? Ki sani kaddara ce ta hada mu da ita, sannan Kuma ga Rabon d'a a tsakaninmu, Kuma ina kaunar d'an da ta haifa kamar yadda nake kaunar d'an da kika haifa, dukkansu 'ya'yana ne ba na son na yi nisa da kowannensu." "To ba sai ka karbi babyn daga hannunta ba sai ka bawa Ammi ta kula da shi ita Kuma ka fita harkarta, tunda dama ba wani sanin ta kayi ba sai da wannan abun ya faru, sai mu ba yi zaman mu daga ni sai kai." Kallonta ya yi tare da cewa. "Nasreen ba zan maki k'arya ba a gaskiya kina da matsala dangane da zamantakewar aure, ke kanki kin sani idan na cigaba da zama da ke a haka ke kadai cutuwa zan yi, Kuma ba zai yiwu na dinga cutuwa ba alhalim ina da damar da zan nemawa kai na mafita tunda ke kin gaza." Ya k'arasa maganar yana tashi tsaye zai nufi k'ofar fita, a guje ta bi bayansa ta rungume shi ta baya tana cewa. "Ka fito kawai ka ce mani dama kana son ta ba wai ka nuna cewa son yaron kake yi ba, ka mance alkawarin da ka mani ba zaka auri wata mace bayan ni ba, shi ne za ka je ka auro wata karuwa 'yar shaye-shaye wacce ta gama yawon iskancin ta a duniya ta rude ka ka yi lalata da ita ta hada baki da wasu munafukai aka ce ja yi mata ciki shi ne ka yarda ka karbi d'an shegen da..." Kasa k'arasa maganar ta yi Sakamakon tsawar da ya daka mata, ganin bacin ran da ke kan fuskarta kadai ya isa ya ya sanar da ita yanda yake ji a cikin zuciyarsa. Janye ta ya yi daga jikinsa ya kalle ta da idanunsa da suka canza launi zuwa ja ya fara magana. "Zan maki gargadi akan firucin da kike yi mata dad'i akan Amatullah ya Abdallah, kada na dake ji kin kira ta da sunan karuwa Dan ita ba karuwa ba ce, zuwanta hotel din da ta yi a lokacin kuskure ne, haduwata da ita Kuma tsautsayi ne ya hada mu, abunda muka aikata Kuma nasan zunubi ne, amma daga ni har ita ba mai laifi akan abunda muka aikata Allah shi ne shaida, ko da duk duniyar nan zaku taru Ku kira ta da karuwa to ni zan fito na karyata Ku. Domin a cikakkiyar budurwa na same ta, ni na raba ta da budurcinta na 'ya mace, Wanda a dalilina ne har iyayenta suka kore ta daga gida ta shiga gararin rayuwa ta Sha wahala sosai daboda ni kafin Allah ya iyakance mata sanadiyayar Kade ta da na yi da mota, Kuma an tabbatar Dan da ta haifa d'ana ne idan na rabu da ita ai ban yi mata adalci ba, dan haka ba zan iya rabuwa da ita ba." "Au dama da saninka kenan ka aikata abunda ka aikata, kake ikirarin ba kai ba ne baka San ka yi ba, tunda har ka iya sanin a cikakkiyar budurwa ka same ta ka sani kenan." Murmushin takaici ya yi tare da cewa. "Eh na sani." Yana gama fad'ar haka ya fice daga cikin d'akin, ya barta nan durkushe tana kuka. Bangaren Umman Amaty kuwa an yi nasaran ceton rayuwarta, numfashin ta ya dawo, ba abunda take ji kamar yadda zuciyarta ke mata zafi, dan ciwon zuciya ya kama ta, Sakamakon yawan kuka fa damuwa akan tunanin Amatullah. Amatullah kuwa a can bangaren nata ta matsu suyi kwanaki biyi su bar k'asar, dan ta kosa ta je ta ga Ummanta. Duk da a gefe d'aya tana fargabar haduwarta da iyayen nata, ba ta san yadda zasu karbe ta ba idan ta koma masu da tsarabar yaro Wanda ba ta hanyar halal ta same shi ba, kuka sosai take yi idan ta tuna abunda ya faru. A kwana biyun nan da suka yi a k'asar Qatar ta samu kulawa saosai daga wajen kakar Ajmal, dan ta nuna mata kauna, ita da yaron da ta haifa. Ammi ma ba daga baya ba sun nuna mata kulawa sosai idan an an bata Abdallah sai dai idan nono zai sha. Nasreen kuwa tunda ta ga yadda Ajmal ya nuna bacin ransa akan zancen rabuwarsa da Amatullah, ta ke ta fushi da shi , shima ya share ta, ta dinga zaman kadaici Dan ko bangaren Kakar Ajmal idan ta je ta gaishe su da safe ba ta sake zuwa, idan Amatullah ta gaishe ta ko bata amsawa sai dai idan ta ga idon mutane a wajen. A haka suka yi kwanaki biyi ran da zasu tafi kakar Ajmal ba ta hada mata Sha tara na arziki Dan akwati hudu ta yi mata na kaya ita da Abdallah, kayan sakwa ta takalma da jakkuna har zuwa kayan cosmetics da turarurruka. Haka suka baro k'asar Qatar cikin farin ciki da kewar tsohuwar. K'arfe d'aya na tana jiriginsu ya sauka a 9ja, tun lokacin gaban Amatullah ke fad'uwa da fargabar haduwarta da iyayen ta. Ahmad suka gani tare da wasu bodyguards na Ajmal guda hudu, inda suka zo daukarsu da motaoci guda uku. Ammi da Amatullah da Nasreen suna bayan mota, a gaba Kuma Ahmad ke driving sai Ajmal dake gafensa, Mota d'aya na gabansu d'aya a bayansu yayin da ta su motar ke tsakiya, kallon Ahmad Ajmal ya yi tare da cewa. "Kun kwaso duka kayan nata da ba Abdallah ko?" "Eh komai mun kwasu Yallabai suna bayan mota." Ahmad ya tambayi Amatullah adireshin gidan iyayen nata, ta yi masa kwatance kasancewar ya san garin shima. A hankali motocinsu suka kunno kai cikin unguwar, yamutse fuska Nasreen ke yi ganin yanayin unguwar Wanda ko ba'a fad'a maka ba ka San na talakawa ne, bisa la'akari da yanayin unguwar da rashin kyan hanya da gudajen dake unguwar. Parking mitocin suka yi a wani madaidaicin gida na masu karamin karfi, fitowa suka yi inda bodyguards din nasa suka fito tare da bude masu bayan motar. Makota har sun fara lekowa Jin an ce ga wasu dankara fankaran motoci sun shigo layin, ganin Amatullah ya sa wasu ke nuna ta da cewa ta dawo Amatullah ce wacce ta gudu ta dawo. Cikin sanyin jiki ta Kalli Abdallah Wanda ke rungume a hannun Ammi, sannan ta Kalli Ajmal Wanda shima ita yake Kallo, idanunta ne suka ciko da k'walla, gani ta yi ya girgiza mata kai alamar kada ta yi kuka. Hakan ya sa ta Mai da hawayen tare da Mai da dubanta ga k'ofar gidan. Bi tashar TASKAR MAMAN IHSAN a WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z 🤦‍♀️ *'YAR MAYE*🤦‍♀️ (_The drug abuser_) Page 7️⃣3️⃣ Cikin sanyin jiki ta Kalli Abdallah Wanda ke rungume a hannun Ammi, sannan ta Kalli Ajmal Wanda shima ita yake Kallo, idanunta ne suka ciko da k'walla. Gani ta yi ya girgiza mata kai alamar kada ta yi kuka. Hakan ya sa ta mai da hawayen tare da maida dubanta ga k'ofar gidan. Wayar Ajmal ce ta yi ruri Wanda hakan ya sa ya ciro wayar daga cikin aljihunsa ya duba, ganin Dady ne ya yi saurin picking. "Hello Barka da rana Dady." Daga can bangaren kuwa Dady dake bayan mota direbansa na gaba yana tuki ya ce. "Barka dai Son, Kun iso kenan?" "Eh Dady ga mu nan mun iso k'ofar gidansu yanzu." "Okay ka saka a turo mani adireshin gidan yanzu. Dan mun kusa shigowa garin." Okay ya ce tare da kashe wayar, Mai da dubansa ya yi ga Ahmad ya sanar da shi cewa ya turawa Dady adireshin gidan. Ammi ce ta Kalli Amatullah tare da cewa. "Mu shiga gidan mana da ko?" Gabanta na tsananta fad'uwa ta yi gaba yayin da Ammi da Nasreen suka bi bayanta, Ajmal da sauran security suka tsaya daga waje. Da sallama ta tura k'ofar gidan Wanda yake da k'ofar fale-fale, ta shiga tana karewa gidan Kallo, Ammi ma suna biye da ita, sai dai shiru da ta ji da Kuma ganin d'akunan gidan kowanne a rufe ya sa ta tabbatar da ba kowa a gidan. Kallon Ammi ta yi tare da cewa. Ba kowa a gidan, ina ga sun fita, sai dai na tabbatar Ummata ba zata dade ba zata dawo, Dan ba ta jimawa idan ta fita. Benci dake ajiye a k'asar bishiyar ne ta d'auki wani teohon zanin Ummanta ta goge, kallon Ammi ta yi tare da cewa. "Bisimillah Ku zauna." Ammi ce ta zauna Nasreen Kuma ta yi tsaye kamar ba ta ji abunda suka fad'a ba, kallon ta Amatullah ta yi tare da cewa. "Anty ki zauna mana." Yamutse fuska ta yi tare da karewa gidan Kallo sannan ta zauna, duk da cewar gida ne na talakawa amma da dukkan alama masu gidan na da tsafta, dan komai na gidan tsaf ne a tsaftace yake. Tana so ta debo masu ruwan Sha amma ta kasa, sanin kanta ne cewa ko ruwan ledar pure water basa sha ballantana ruwan tunkuyar kasa da suke Sha a gidan. Amma duk da haka sai ta nufi kitchen ta dauko kofin silver ta ciko shi da ruwa ta kawo masu. Ga mamakin ta sai gani ta yi Ammi ta d'auki ruwan ta sha, Nasreen dai ta ce ba zata Sha ba. Jin shiru ne ya sa Ajmal da ke cikin mota shi da Affan dake rungume a jikinsa ya kira wayar Ammi. Bayan ta daga ne yake tambayar ta halin da ake ciki, ta sanar da shi ba kowa gidan. Hakan ya sa ya ce to su fito su je su kama masauki, Dan su ci abinci su yi wanka. Bayan Ammi ta kashe wayar ne ta Kalli Amatullah ta ce. "To tunda ba sa nan ko za ki bi mu masauki sai mu huta zuwa yamma maybe sun dawo sai mu dawo." Nasreen na Jin haka ta mike tsaye tare da cewa. "Gaskiya Kam dan na gaji wallahi." Amatullah ce ta ce. ",Ammi to Ku je ku dawo ni zan jira har Ummata ta dawo, idan ta dawo za ta same ni a gidan." Ta yi maganar tana sakin murmushi na Jin dad'in dawowarta gida, duk da k'asar zuciyarta cike take da fargaba. Sallama Amimi ta mata suka bar gidan, ta zauna tana jiran dawowar Ummanta. Daga nan suka shiga motocinsu suka bar k'ofar gidan. Bangaren Umman Amatullah kuwa jikinta ya yi sauki, dan har an basu takaddar sallama, sai dai ba kudi a hannun Abba Wanda zai basu, saboda zai biya kudin gado sannan akwai wasu magaungunar da aka rubuta masu zasu Siya. Dan haka ya bar Umma ya ce ta jira shi ya je ya dawo. Kai tsaye ya nufi gida bayan ya tare Mai Keke nape ya sanar da shi unguwar da zai kai shi. Bangaren Amatullah tunda ta ji tashin mitocin Ajmal jikinta ya yi sanyi, makota da ke lekowa Suna mata Barka da zuwa ne ke ta shigowa, duk da cewar mafi yawancin su gulma ce suka zo gani. Ganin ba ta sakar masu fuska ba ne kuma ba ta amsa masu tambayoyin da suke mata ba ne ya sa suka dinga zamewa suna fita. Dan duk tambaya biyi suke mata wai ina ta tafi tsawon lokaci, Kuma wannan yaron nata ne? Bayan kowa ya watse ne tana rungume da Abdallah tana fargabar haduwarta da Abbanta. Dan ta San yana da d'aukar zafi da Kuma yanke hukunci cikin fushi ba tare da yin bincike ba, Dan tana tuna irin dukar mutuwar da ya yi mata bayan ya ji cewa ciki ne da ita, da Kuma korar ta da ya yi na cewa kada ta sake saka kafa a cikin gidan nan. Yau ga shi ta sako kafa ba ta sani ba zai karbe ta ko akasin haka, sai yanzu take da na sanin rashin bin su Ammi masauki da ba ta yi ba, da yanzu sai dai su dawo tare Kuma maybe ganin mutuncin iyayen Ajmal da da Kuma bayani da za su mashi ya fahimci ba ta laifi ya yafe mata. Tana rungume da Abdallah da ke ta sharar barci har zuwa lokacin ta fashe da kuka. Sai da suka yi nisa da tafiya sannan Ammi ta lura da wayar Amatullah, d'auka ta yi tare da kallon Nasreen ta ce. "Wato Amatullah tsabar d'auki ne ya sa ta mance da wayarta, idan mun dawo anjima za ta gani, sai dai na so a ce wayar na hannunta, dan sanin halin da take ciki, da Kuma dawowar iyayenta gida. Ajmal dai bai ce komai ba, dan jikinsa ya yi sanyi sosai, ya rasa dalilin haka, Dan ji yake zuciyarsa na neman tsinkewa. Dady ne ya kira Ammi a waya ta sanar da shi halin da ake ciki. Wani tsadadden hotel suka yi parking, inda Ahmad ya fita ya kama masu d'akuna. Dawowa ya yi ya masu jagora zuwa ciki, D'akin Ammi ya fara budewa bayan ta shiga ne ya nuna wa Ajmal d'akin da ke kusa da Ammi, ya ce. "Sir ga naku d'akin, na duba komai ba wata matsala." Yana rufe baki ne sai Nasreen ta shiga da sauri Dan a gajiye take, Ajmal shima bin bayanta ya yi. Sauran security ma duk suka nufi masaukin da Ahmad ya tanadar masu. Abba ma ya kira Ammi a waya ta shaida masa sunan hotel da suke da lambar d'akin, dan zuwa lokacin ya iso cikin garin. Ordern abinci suka yi daga hotel din, inda kowanne d'akin sai da aka kai masu abinci. Ajmal wanka ya yi ya sauya kayan jikinsa zuwa wani yadi mai ruwan hoda. Masallaci ya nufa dan gabatar da sallar azahar. Nasreen kuwa zama ta yi ta ci abincin ta koshi ta kora da lemu da ruwa sannan ta kwanta Saman lafiyayyen gadon ta fara barci. Bayan Ajmal ya dawo masallaci a falon d'akin ya zauna Saman sofa, jinginar da bayansa ya yi da jikin kujerar tare da kallon sama. Gaba d'aya hankalinsa ya koma kan Amatullah, da babynta. Tunaninnsa bai dai ya iyayenta zasu karbe ta ba, shin za ta samu matsala da su ko kuwa, ga wayarta tare da su ballantana ya kira ta dan ya ji halin da suke ciki. Abba na komawa gidan da niyyar dauko kudin da zai biya asibiti kudin sallama sai ya ga k'ofar gidan a bud'e, mamaki ya yi ganin ya bar k'ofar a rufe, a hankali ya k'arasa tare da shiga da Sallama d'auke a bakinsa. "Assalamu alaikum." "Amatullah dake zaune ce ta amsa masa sallamar, da sauri ya juyo ya Kalli inda ya ji an amsa sallamar, dan tabbas ba zai taba mancewa da wannan muryar ba. Ganin Amatullah kanta a sunkuye tana rungume da baby na barci a hannunta ya sa ya tsuke fuska, a hankali ta zamo daga kan bencin da take zaune ta durkusa saman guiwarta ta kasa daga kai ta Kalli mahaifin nata. Hawaye ne kawai ke zuba daga idanunta yana diga a rigar Abdallah. Kamar daga masa ta ji muryarsa yana cewa "Me kika zo yi?" Kuka ne ya subucuce mata ta kasa magana Banda sautin kukanta ba abunda kake ji. "Na ce me ya kawo ki Kuma!" "Abbana bana da inda yafi nan a halin yanzu dan..." Dakatar da ita ya yi ta hanyar cewa. "Ba na son Jin komai daga bakin ki, ki koma inda ya fiye maki nan, ki koma can ki cigaba da zama a wajensa." "Abba bana da kowa da yafi..." "Bari ki ji na fad'a maki." Dakatar da ita ya yi ta hanayar cewa. "Tsawon wannan lokacin kina ina?" Kanta a sunkuye ta ce. "Ina Kaduna." A wajen wa kike Kuma gidan waye kike zaune, shin uban wannan yaron da kika haifa Wanda ya maki ciki a gidansa kike zaune? Eh ko a'a?" "Eh Abba." Ta fad'a kanta a sunkuye? Murmushin takaici ya yi tare da cewa. "Kwanaki uku da suka wuce na je har gidan an sanar da ni ba ki k'asar? Tare da shi kuka tafi?" "Eh Abba amma ba..." Daga hannu ya yi ya ce. "Ya isa!" "Tashi ki fita bana son sake ganin fuskarki a gidan nan, da farko kin fad'a harkar shaye-shaye, bai maki ba duk da haka sai da kika fara bin maza har da cikin shege hakan ya sa na kore ki, sai daga baya Ummanki ke sanar dani ba laifinki ba ne kin fad'a tarkon muguwar k'awa ce ta shirya maki gadar zare kika fad'a, a lokacin na yi nadamar korar ki da na yi har na ke addu'ar Allah ya dawo mani da ke lafiya ko don halin da Ummanki ke ciki na rashinki, ashe ke ba haka ba ne zaman dadiro kike yi da wanda ya maki cikin tsawon lokaci. Cikin bakin ciki na nufi garin Kaduna na tarar da har Kun fita wata k'asar da shi. To ki bude kunnuwanki ki saurare ni da kyau, ba zan aibata ki da bakina ba kuka ba zan tsine maki ba sai dai na ce ki yi nisa da mu dan dawowarki a nan ba za ki iya zama da mu ba saboda rayuwar da kike ciki, ka da kwana biyi ki sake komawa rayuwar da kika yi a baya ki sake saka mahaifiyarki cikin wani hali, dan be haka salin alin ki tashi ki tafi tun kafin ta ji labarin zuwanki na hakura da ke domin da mutunci na ba zan haifi karuwa ba." Rintse idanu ta yi cikin Jin zafi da k'unar kalamam mahaifin nata ta fara magana. "Abba wallahi ni ba karuwa ba ce ban

Chapter 31 of 51