Share this page
gado tana jiran ta idar. Bayan ta idar ne ta lalle ta tare da cewa. "Nihal" "Na'am." Ta amsa tana jiran jin me za ta ce. "Na ga ba ki ci abinci ba tun na safe, kar dai tunanin wannan me jajayen kunnuwa kike yi." Murmushi ta yi tare da cewa "Ni na cire Ajmal a cikin rayuwata kuma ina ƙoƙarin yakice soyayyarsa da nake yi a zuciyata, na haƙura don na san ba zan taɓa samun farin ciki daga gare shi ba " Kallonta Marka ke yi cikin tausaya wa yadda ta yi sanyi ta canza kamar ba ita ba. Dr Fu'ad ne ya fito daga ɗakin Ajmal bayan ya masa duk abinda zai masa ya masa allura ya yi barci, su Dady da ke zaune a downstairs ya ƙarasa wajensu. Ammi ta ce "Ya jikin nasa?" "Ya samu barci amma akwai buƙatar ya cire damuwa dake zuciyarsa don jikinsa ya hau fiye da ƙima, don idan bai yi wasa ba zai iya kamuwa da ciwon zuciya, nan ya cigaba da basu shawarwari kafin ya masu sallama zai dawo zuwa dare. Ammi har lokacin bata daina hawaye ba. *Bayan wata biyu* Ajmal ne zaune a bedroom ɗinsa saman sofa, ya canza idan ba ka yi masa farin sani ba to ba za ki gane shi ba, ya rame fuskar nan ta koma fayau, sai dogon wuya da karan hanci, fuskar nan buzu-buzu da gashi ba gyara. Gabaɗaya ba ƙarfi a jikinsa don ko abinci ya daina ci sai dai idan yunwa ta saka shi gaba ya sha hollandia da snacks. Ammi da Dady har sun gaji sun zuba masa idanu. Yana tsaka da tunani sai ya yinƙura kafin ya tashi ya fara aman jini, cikin wannan yanayi Ammi ta shigo ta same shi, cikin tashin hankali take kuka. Ganin kamar ya fara fita hayyacinsa ga aman da yake yi jini na fita zallah ya sa cikin kiɗima ta fita daga ɗakin, downstairs ta sauko ta ɗauki wayarta akan kujera, kuka take yi tana sosai ta dannawa Dr Fu'ad kira, bugu ɗaya ya ɗaga tare da yin sallama. Jin sautin kukanta ya sa ya katse kiran wayar cikin hanzarin ya fito daga office ɗinsa, duk da yawan patients dake jiransa bai kula su ba ya fice da hanzari. Gudu kawai yake yi a titi yana tausayin halin da abokinsa ke ciki, don ya san jikin ne ya yi tsanani. Yana horn securitys suka buɗe masa gate ɗin farko bayan sun tabbatar da shi ne, har gate ɗin da za ta sada su da main house ɗin da sauri security suka buɗe masa. Ba kowa falon da sauri ya haura upstairs ɗin har yana tsallake steps. Ƙofar falon ya tura da sallama, ba kowa don haka ya nufi bedroom ɗin. Nan ya tarar da shi kwance kamar babu rai a jikinsa. Ba tare da ɓata lokaci ba ya ɗauke shi tare da barin bedroom ɗin.Ammi na biye da shi a baya. Lokacin da suka fito ne bodyguard ɗinsa suka ga halin da boss ɗin nasu ke ciki, suna ganin Dr Fu'ad ya saka shi a bayan motar Ammi ta zaune gefen sa ta ɗaura kansa a saman cinyarta, sauran bodyguard ɗinsa Ahmad da wasu guda biyu suka mara masu baya. Bayan awannin uku. Dr Fu'ad ne ya fito daga ɗakin da Ajmal ke kwance ya kalli Ammi da sauran bodyguard ɗinsa da ke ƙofar ɗakin da aka kwantar da shi. "Ammi Ina son ganinki a office ɗina." Bin bayansa ta yi cikin sanyin jiki, da ka kalle ta ka san ta sha kuka. Suna shiga ya zauna a mazaunin sa yayin da Ammi ta zauna a kujerar da ke fuskantar sa. "Ammi gaskiya ba zan ɓoye maki ba Ajmal na cikin mawuyacin hali, jininsa ya hau fiye da ƙima ga zuciyarsa tana bugawa fiye da ƙa'ida, a gaskiya akwai matsala don ciwon zuciya mai tsanani ya kama shi, ya kamata a nema masa abinda yake so a kiyaye ɓacin ransa, sannan ayi ƙokarin nema masa abinda yake so." Ajiyar zuciya Ammi ta sauke tare da cewa. "Kada ka damu za ku yi iyakacin ƙaƙarinmu, abokinka ne shi ka san komai ba sai na faɗa maka ba " Shawarwari ya sake ba ta sannan ta nemi iznin ganinsa, ya nuna ba komai za ta iya zuwa ganinsa. Satinsu biyu a asibiti aka sallame shi bayan ya samu sauƙi, sai dai ko magana baya son yi daga eh sai a'a. Ɓangaren Amatullah ba ta san me ke faruwa ba, don wayoyinsa gabɗaya an kashe, ba ta gwada kiran wayarsa ba domin gani take ƙarin damuwa ne kawai Gara ta koyawa zuciyarta haƙuri da juriyar rashinsa, duk da ta sha kuka har ta godewa Allah. Ɓangaren Ajmal ma kuwa sosai Ammi da Dady je kula da shi, suna bakin ƙoƙarin su wajen saka shi farin ciki, amma duk da haka ba abinda ya canza daga gare shi. Hatta kamarsa Ummi sai da ta zo daga ƙasar Qatar don saboda rashin lafiyarsa ta zo ta zauna da su. Wata ranar ne sai ga kiran waya daga daga Umman Amatullah ta kira Ammi. Har sai da ta katse aka sake kira sannan Ammi da ke zaune a falo ita da Ummi suna fira ta ɗaga kiran wayar. "Assalamu alaikum" Daga can ɓangaren Umman Amatullah ta amsa da wa'alaiki salam, daga don Ammi ba ta gane wa ke kira ba don ba ta da lambar Ammi, duk da suna gaisawa amma da wayar Amatullah take ba ta su gaisa. "Da wa nake magana?" Ammi ta yi tambayar. "Umman Amatullah ce." Umma ta ba ta amsa. "Ayya dake ban da lambar shi ya sa ban gane ba, ya kuke ina Amatullah da Abdallah." "Suna lafiya." "Ma sha Allah ki yi haƙuri kwana biyu ban kira na ji lafiyar su ba kasancewar ba na cikin natsuwa ne gwbaɗaya." "Ayyah ba komai Allah ya sa lafiya dai." "Eh kusan haka, Ajmal ne ya yi fama da ciwon zuciya amma yanzu Alhamdulillah da sauƙi." "Subhanallah, ya jikin nashi." "Da sauƙi." "To Allah ya ƙara masa lafiya ya yaye masa." "Ameen ya rabbi." "To dama an yaye mijin naki ne yau saura watanni biyu auren Amatullah, duk da ta ce za ta je gidan miji da ɗanta na ce ba zai yiwu ba sai na ji daga bakinku duk abinda Ajmal ya ce shikenan don na san zai karɓi ɗansa ne " Shiru Ammi ta yi sannan ta ce. "Zan yi magana da shi duk shawarar da muka yanke zan kira ki." Sallama suka yi Umma ta kashe kiran wayar, juyawa da za ta yi ta hangi Amatullah dake tsaye bakin ƙofar tana kuka sai dai ta toshe hannayenta da tafukan hannunta, hakan ya sa sautin kukan ba ya fita. Umma ta san cewa ta ji zancen da suke yi ne kasancewar a handsfree ta saka wayar. Ammi kuwa bayan ta ajiye wayar daidai lokacin da Ajmal ke saukowa daga downstairs yana tafiya kamar wanda ba ya so, da kallon tausayi Ammi ke binsa fridge ya nufa da ke falon da ke falon da alama akwai abinda yake son ɗauka. Ammi ce ta kalli Umminta tare da cewa. "Mahaifiyar Amatullah ce ta kira wai an yaye jikana bikin Amatullah saura watanni biyu, shi ne Amatullah ta ce ba za ta iya rabuwa da yaron ba, za ta je gidan mijinta da yaron kuma Ajmal ya sha faɗa a baya cewa ba zai bar ɗansa a hannun..., Ƙasa ƙarasa maganar ta yi sakamakon jin ƙarar fuɗuwar robar ruwa da Ajmal ya saki, take ya dace saitin zuciyarsa yana durƙusawa a wajen. Nan da nan ya yi kamar wanda baya numfashi. Ihun Ammi da Ummi ne suka saka Ahmad dake tsaye daga ƙofar falon shigowa da sauri. Wunin ranar Amatullah ba ta iya cin abinci ba, kuma ba ga yunwa ba abinda take yi illa kuwa kawai sallah kawai ke fito da ita. A asibiti kuwa likitoci uku ne akan ke kan Ajmal ana ta ƙoƙarin ceto rayuwarsa. Ka na ganinsa za ka za ta baya da rayuwa a jikinsa Ammi kuka take ga Dady baya ƙasar ma gabaɗaya. Ammi ta kalli mahaifiyarta ta ce don Allah ta tsaya da shi tafiya ce ta taso mata ta gaggawa, Ummi tana mamakin wani tafiya ne haka a irin wannan yanayi, amma ganin ba wanda yafi ta damuwa da ɗanta ya sa ta masu Allah ya dawo da ita lafiya. Fita ta yi ta samu Ahmad a waje ta kira shi gefe. "Ahmad tafiya za mu yi yanzu." Da mamaki ya kalle ta tare da cewa. "Asibitin sun kasa ne za ku je wani wajen?" "Zan tafi din nema wa ɗana mafita ko zai samu sassauci daga zuciyarsa" Allah ya bashi lafiya, to ina za mu je?" "Minna jihar niger" "Okay wajen Amatullah za mu tafi." "Okay wajen Amatullah ko?' Girgiza kai Ammi ta yi cikin takaici ta ce. ".Kasan adireshin yaron da zai auri Amatullah?'" ,"Eh na sani." "Gidansu za ka kai ni." "Okay Allah ya kai mu lafiya" "Ka bincika idan za mu samu jirgin da zai tafi idan babu mu bi mota." Jinjina Kai ya yi cikin ladabi ya bar wajen. Amatullah kuwa ko da Munnir ya zo ƙin fita ta yi, sai da Ammi ta mata faɗa sannan ta fita, ko da ya ga idanun ta a kumbure alamar ta sha kuka hankalinsa tashi ya yi, duk yadda ya so ta sanar da shi matsalar ta bai samu amsa ba, don haka ya ce ta koma ciki shima ya ja motar da ya bar ƙofar gidan. Da misalin ƙarfe biyar na yamma motar su Ammi ta tsaya a ƙofar gidan, horn ya yi duk da mai gadin bai san waye ba amma ganin falleliyar mota mai ɗaukar idanu ya sa da sauri ya wangale gate ɗin gidan. Bayan Ahmad ya yi parking ne ya ke nunawa Ammi ƙofar da za ta shiga, a hankali ta auri fararen ƙafarta waje, wanda yake sanye da flat shoe baƙi, abaya ce mai ruwan ƙasa a jikinta. Kai tsaye ta nufi ƙofar falon da sallama ta tsaya tana knocking, wata mai aikin Mum ce ta zo ta bude ƙofar. "Sannu da zuwa Hajiya." "Yauwa sannu. Masu gidan na nan?" "Eh shigo ciki." A daya daga cikin kujerun da ke falon Ammi ta zauna, yayin da mai aikin ta nufi ciki. Ba jimawa ta dawo ta cewa Ammi "Tana zuwa." Daga nan ta bar wajen. Ammi na zaune tayi tagumi ta ji motsi a gabanta alama ta yi zurfi a tunani har matar gidan ta shigo ba ta sani ba." Ammi ta ɗaga kai tana cewa. "Barka da fit..." Kasa ƙarasawa ta yi ta miƙe a tsaye cikin a firgice tana kallon Mum ɗin Munnir cikin mamaki da al'ajabi. Matar da rabon da ya saka ta a idanunta tsawon shekaru talatin da biyu kenan. Mamaki ya hana ta magana yayin da Mum ke jifanta da wani kallo wanda ba wanda ya isa ya gane ko na mene ne ba, kafin ta daki wani murmushi tana cewa. "Daina mamaki ni ɗin ce dai." *Maman Ihsan ce*✍️ Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z 🤦‍♀️ *'YAR MAYE*🤦‍♀️ (_The drug abuser_) *Na* Zainab Abdullahi KNT (Maman Ihsan) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page1️⃣0️⃣2️⃣ Mamaki ya hana ta magana yayin da Mum ke jifanta da wani kallo wanda ba wanda ya isa ya gane ko na mene ba, Kafin ta saki wani murmushi tana cewa. "Daina mamaki ni ɗin ce dai." Jinjina Kai Ammi ta yi tare da cewa. "Ikon Allah." "Ai Mun riga mun yanke alaƙa da ku tun tsawon shekaru talatin da biyu da suka wuce, ba mu ba ku har abada tunda har waccan tsohuwar ta nuna ƙiyayyarta gare ni saboda ina auren ɗanta, amma ke ta nuna soyayya ta ɗauke ki a matsayin suruka yayin da ta nuna ƙiyayyarta a gare ni ta kore ni daga cikin ahalinta sai dai bata yi nasara ba domin na raba ta da ɗanta har abada ba zai taɓa waiwayarta ba, babban ɗanta mafi soyuwa a gare ta na san har yanzu tana jin zafin rashinsa wata kila ma baƙin cikin haka ya yi sanadiyyar mutuwarta. Idan kuma tana raye na san har yanzu akwai tabo a zuciyarta." Murmushin takaici Ammi ta yi tare da cewa. "Yanzu abin alfahari ne gare ki Fatima ko? Kin yi nasarar raba uwa da ɗanta kike ganin kin kyauta?" "Me ya kawo ki gidana.?" "Ina fatan kece mahaifiyar Munnir wanda zai auri Amatullah?" Gabanta ne ya faɗi kafin ta yi ƙarfin halin cewa. "Eh akwai abinda ya faru ne, ko kina da alaƙa da ita ne?" "Na zo ne da ƙoƙon barata a wajenku." Kallon rashin fahimta Mummy ta yi mata kafin ta ce. "Me kike nufi?" "Da so samu ne zan so a kira shi Munnir ɗin da Yaya ayi maganar a gabansu." "Ba sa nan ki sanar da ni abinda ya kawo ki sai ki bar gidan nan don bana bukatar wata alaƙa ta haɗa mu da ku don Munnir ɗin ma baya gari don ko yana nan ba zan bari ki hadu da shi ko mahaifinsa ba don ban san da me kika zo ba." "Ba abinda na zo da shi sai alkhairi, ina neman arziki ne Munnir ya sadaukarwa ɗan uwansa Amatullah, domin rayuwarsa tana cikin barazana." "Ban fahimci me kike son cewa ba ki yi mani bayani yadda zan gane." "Wato na san ba za ki rasa jin labarin Amatullah tana da ɗan da ta haifa ba ko, to ba kowa ba ne uban yaron face ɗana Ajmal wanda wanda kika sani wanda kika tafi kika barni ina goyon sa." Cikin mamaki Mummy ke kallonta kafin ta ce. "Yanzu ya kike so ayi?" "Wato akwai soyayya mai karfin gaske a tsakanin Ajmal da Amatullah." Daga nan ta sanar da Mummy labarin komai tun daga ranar da aka shirya masu musu wannan al'amari a hotel ya kasance ta da yadda ya kaɗe ta a mota ya kai ta asibiti da wahalar da ta sha bayan Abbanta ya kore ta har zuwa haihuwa da komai sai da ta sanarwar Mummy. Kafin ta haɗa hannayenta biyu alamar roƙo ta ce. "Don Allah ku taimaki rayuwar ɗana ku tausaya wa halin da yake ciki Munnir ya sadaukarwa ɗan uwansa Amatullah ko hankalinsa zai kwanta, ko ba komai ɗan uwansa ne da mahaifin Munnir da mahaifin Ajmal uwarsu ɗaya ubansu ɗaya, idan aka tsaya jinin Ajmal dole aga jinin Munnir idan kika ga halin da yake ciki sai kin tausaya masa akan soyayya ya shiga wani hali na..." Kasa ƙarasa abinda ta yi niyyar faɗa ta yi sakamakon kalaman Mummy da suka daki dodon kunnenta. "Ai ko sai dai ya mutu, idan har sai ɗana ya sadaukarwa ɗan ki soyayya sannan zai samu lafiya to tun wuri ku je ku nemi likafani. Ke bari na faɗa maki abinda ba ki sani ba wallahi bana ƙaunar ɗana ya auri Amatullah tunda na ji labarin abinda ta aikata nake ƙyamar ta shigo cikin zuri'ata ina neman hanyar da zan dakatar da wannan aure. Amma yanzu na ji ina son wannan aure ko ba komai na san zai yi sanadiyar baƙin cikinku. Ni kuma yanzu na fara son wannan aure na zubar da makaman yaƙina ba gudu ba ja da baya aure sai anyi shi ba fashi idan ya so sai dai wasu su haɗiyi zuciya su mutu." Kallon al'ajabi take bin Mummy da shi wato har yanzu halinta na nan ba abinda ya canza. "Haba Fatima ai ko wani ne ba za ki yi masa wannan fatan ba ballantana ɗana, shin na taɓa maki wani abu ko mahaifin Ajmal ya maki abinda za ki ƙullace mu har haka ne, ina matsala tsakaninki da sirikarki ce." "Dalla gafara shi Ibrahim ɗin mijinki ba shi ne babban munafukin ba, ki tashi ki bar gidan nan tun kafin na tafka maki rashin mutunci,don yanzu zan saka bayi waje da ke, aure tsakanin Munnir da Amatullah ba fashi." Ƙwallar da ke idanunta ta goge sannan ta kalli Mummy ta ce "Kar ki damu Fatima yanzu zan tafi, amma ina son ganin Yaya." Baya nan ba za ki gani shi ba. Nuna mata kofar fita ta yi, Ammi ta tashi ta bar falon tana mata sai an jima, amma ko tanka mata ba ta yi ba sai masifar da take yi. Fita ta yi ta samu Ahmad zaune cikin motar, ganin yanayin ta ya tabbatar masa ba nasara, fitowa ya yi cikin sanyin jiki ya bude mata bayan motar ta shiga, horn suka yi Maigadi ya bude masu gate suka fice. A gefen hanya ne ta sa Ahmad yin parking. "Ahmad ban san yadda zan yi ba, ashe yaron nan ɗan uwan Ajmal ne da mahaifinsa da mahaifin Ajmal uwa ɗaya uba daya suke." Kallon mamaki Ahmad ke yi wa Ammi kafin ya ce "To ya aka yi ba wanda ya sani sai yanzu?" "Wato ya bar gida da danginsa ne saboda matarsa ba wanda ya san inda yake sai yau da na zo." Tunawa da ta yi da yadda suka rabu da Mummy da halin da Ajmal ke ciki ya saka ya yin kuka mai tauna zuciya. Ahmad ya dinga rarrashinta yana bata baki akan cewa zai samu lafiya in Sha Allah. Bayan ya tsagaita kukan da take yi ne Ahmad na shirin yiwa motar key ne suka hangi wata mota na zuwa, kamar an ce Ammi ta waiga sai idanunta ya sauka akan Mahaifin Munnir. "Ahmad wannan ne ƙanin Yayan mahaifin Ajmal da na fito gidansa yanzu, juyawa ta yi daidai lokacin da direbansa ke kunna kai cikin gidan. "To mu koma baya kenan ko?" "Eh mu koma amma ba zan shiga ciki ba ka tura mai gadin ya yi sallama da shi saboda wulaƙancin matarsa." "Okay." Ya faɗa yayin da yake juyawa don komawa. A ƙofar gidan ya yi parking Sannan ya fita zuwa ƙofar gate ɗin gidan yana knocking. Maigadi ya leƙo tare da tambayar Ahmad ko lafiya, ya sanar da shi cewa yana son ya masa sallama da mai gidan ne. Rufe ƙofar ya yi tare da tare da nufar cikin gidan, sallama ya yi a ƙafar falo Dad dake zaune a saman kujera ya amsa masa tare da bashi izinin shigowa. Shiga ya yi cikin ladabi ya gaishe shi tare da sanar da shi wani na sallama da shi a waje. Bayan fitar mai gadin shima Dad ya fita inda ya tarar da Ahmad a waje, miƙa masa hannu ya yi suka yi musafaha yana shirin yin magana idanunsa ya sauka akan Ammi dake fitowa daga cikin motar. Mamaki yake yi a hankali ya furta. "Bilkisu." "Na'am Yaya." "Ikon Allah, daga ina kike ina Ibrahim da kuka yara? Dama kin san nan ne?" Murmushi ta yi tare da cewa. "Yaya maganar na da tsayi." "To bisimillahi shigo daga ciki mana ." Ya yi maganar cikin farin ciki tare da mata jagora zuwa ciki." Da sallama ta shigo falon ya amsa cike da farin ciki na ganinta tare da nuna mata wajen zama, daidai lokacin da Mum ta shigo falon wanda ta haɗe fuska tare da cewa "Tashi ki fita me ya sake dawo da ke kuma?" Kallon mamaki Dad ya mata tare da cewa. Dama ta shigo kika kore ta, yanzu rashin mutuncin naki har ya kai ki kori Bilkisu, to bari ki ji har ta bar gidan nan kada ki sake mata magana mara daɗi." Mamakin take ta rasa dalilin da ya sa yanzu alkadarinta ya karye, ashirin ko ta yi yanzu a banza tun kafin lokacin da Munnir ya so auren Amatullah ta hana ta ga Dad ya tsaya tsayin daka har da kafa mata doka ta fara ganin canji. Yanzu gabaɗaya baya jin maganar ta , a fuskance ta koma ciki. Dad ya ƙwalawa mai aiki kira bayan ta zo ya bata umarnin ta kawo wa Ammi abinci da abinsha kafin ya fito. Daga nan ya tashi ya bata wuri don ta samu damar cin abincin. Ba ta da mutuwar da za ta iya cin abinci don haka ruwa kawai ta iya sha. Ba jimawa Dad ya fito tare da zama kan daya daga cikin kujerar falon. "Sannu Bilkisu, dama kin san inda muke ne?" "Ban sani ba yaya hasalima na zo garin nan da gidan nan ba tare da masana cewa kune masu gidan ba." Shiru Dad ya yi tare da jinjina Kai ya ce. "Ikon Allah kenan." Murmushi kawai Ammi ta yi. "To me ya kawo ki gidan tunda kin ce ba ki san na waye ba gidan?" "Dama na zo ne wajen Munnir da iyayensa, ashe kune iyayen nasa ban sani ba." "Eh mune Allah ya sa ba wani laifi ya aikata ba." "Ba abinda ya aikata mun zo ne da ƙoƙon bara a wajensa." Nan ta yi masa bayanin komai da yake faruwa har zuwa halin da Ajmal ke ciki yanzu. Sai da ta gama Dad ya dago ya kalle ta tare da cewa. "Tirƙashi." "Kada ki damu komai zai zo da sauƙi da Munnir da shi Ajmal duk ɗaya ne a wajena Allah ya bashi lafiya. In sha Allah Munnir ba zai aure ta ba Ajmal ne za aure ta domin shi yafi cancanta da ita ba Munnir ba, kuma na tabbatar son da Munnir ke mata bai kai wanda Ajmal ke yi mata ba kuma za ta fi samun farin ciki a gidan Ajmal fiye da gidan Munnir." Mummy ce ta fado kamar wacce aka jefa daga sama. "Zancen me na ji kana yi? To wallahi ba zai yiwu ba akan me za'ayi masa ƙwacen yarinyar da yake so ka bawa mutanen da ba ƙaunarmu suke yi ba?" Wani kallo Dad ya yi mata sannan ya ce ",Ke ƙaunar yarinyar kike yi ne ballantana ki fara faɗa?" "Ko ba na ƙaunarta ba zai yiwu a fasa wannan aure saboda ɗansu ba ." "Kamar yadda na je na nema wa Munnir auren Amatullah haka zan je na janye zancen auren na nema wa Ajmal aurenta na gama magana." Yana gama faɗar haka ya kauda kansa daga kallon Mum." Mum kuwa mamaki ne ya kara cika ta don ba yada za ta yi da Dad yanzu duk ashirin da take masa yanzu ya daina tasiri akansa ya daina jin maganar ta tsabar bakin ciki ta takaici. "Yanzu yana wani asibiti ne?" "Yana asibitinsa wanda shi ne ya gina asibitin ya zuba ma'aikatan lafiya." "Okay yanzu ki huta zuwa gobe za mu je in sha Allah." "Na gode Yaya, amma ka nemi amincewar shi Munnir ɗin idan ya amince zai bar masa yarinyar." "Kada ki damu zai kasance mai biyayya ga abinda zan fada masa." Jinjina Kai ta yi tare da masa godiya har da hawayen farin ciki. "To yanzu ki shiga ciki ki huta zuwa gobe sai ku kama hanya." Tuna cewa ba za su jitu da Mummy ba ya sa ta ce. "Kada ka damu Yaya mun kama masauki." Duk yadda ya so ki ta yi haka ya barta ta tafi. Ganin fuskarta ya sa Ahmad ya fahimci halin da take ciki, a haka suka kama hanya. Horn ya yi a bakin wani tangamemen gida, mai gadin ya leƙo bayan ya kalli Ahmad sai ya wangale masa gate ɗin gidan. Shiga ya yi kai tsaye ya nufi parking space inda wasu haɗaɗdun motoci guda biyu ke ajiye a wajen. Ahmad ya fito ya buɗewa Ammi ta fito yayin da Maigadi ya ƙaraso wajen, cikin girmamawa ya gaishe su tare da tambayar Ahmad yana cewa. "Ina mai gidan ne ba ka zo tare da shi ba ne?" "Eh." Ahmad ya bashi amsa a taƙaice. Maigadin ya kalli Ammi tare da cewa. "Da alama wannan ce mahaifiyar mai gidan ko, na ga kamanni sosai ." Murmushi kawai Ammi ta yi Ahmad kuwa ko tanka masa bai ba, don ya kula mutumin ya fiye surutu da shishshigi." Bayan Ahmad ya buɗe ƙofar falon ne suka tsinci kansu a babban falon gidan, wanda ke dauke da kayan more rayuwa na zamani iri-iri. "Ammi ki zauna." "Ahmad wannan gidan waye." "Ammi gidan Ajmal ne kasancewar ya yana yawan zuwa garin kuma a hotel yake sauka, hakan ya saka na bashi shawarar ya siye gida kawai ya dinga sauka, madadin kwanan hotel, shine muka nemi wannan gidan ya siya." Jinjina Kai ta yi tare da yi masu addu'a a zuciyarta. Ɗaya daga cikin cikin bedroom ɗin da ke nan downstairs ya kai Ammi don ta huta. Ɓangaren Dad ɗin Munnir kuwa ya yanke shawarar sai Munnir ya dawo daga tafiyar da ya tafi kafin ya sanar da shi komai. Gefe ɗaya kuma zuciyarsa fara tas don ya kusa haɗuwa da ahalinsa, don tun satin da ya wuce hankalinsa ya koma wajen danginsa amma yan tsoron tarbar da za su masa, zuciyarsa cike da fargaban haɗuwarsa da Marka. Shi kansa bai san dalilin da ya saka tsawon shekaru talatin ya share danginsa ko tunaninsu baya yi ballantana ya waiwaye su, hasalima da zaran ya tuna da su sai ya ji baya ƙaunar sake ganinsu a rayuwarsa. Ammi ce ta kira lambar mijinta don ta masa kyakkyawan albishir na haɗuwa da ɗan uwansa amma wayar ba ta shiga. Ahmad ne

Chapter 47 of 51