Share this page
ne ko Kuma ba ka ganni ba ne?" Yadda take magana ne tana d'aga murya ga ta zaune gefensa ya sa shi yamutse fuska tare da dafe goshinsa. Don shi har ga Allah baya son hayaniya a rayuwarsa. Rufe laptop din dake Saman cinyarsa ya yi tare da cewa. "Na amsa sallamar da kika yi ai, yanzu ki fad'a mani me ye dalilin kirana da kika yi akan na zo Adamawa, Kuma don Allah ba na son ihu da fad'a kina zagin parents d'ina." Kallonsa take yi shekeke Sanam ta ce. "Meye Kuma poron?" Kallonta ya yi tare da cewa. "Ba na son kina zagin su Ammina da Dad kamar yadda kika yi a falo, ki Fadi zancen da za ki Fadi a Daren nan don gobe in sha Allah zan tafi." "Duk da ba son zaman garin nan kake yi ba kafin ka tafi dole ka je ka gaida kanwar mahifinka wato mahaifiyar Nihal, sannan Abun da ya saka na ce ka zo ba komai ba ne illa alkhairi, Wanda na San za ka ji dad'i da farin ciki, don ko ba ka mani magana yanzu ba dole wata rana sai ka mani." Kallonta ya yi kafin ya kau da kai tare da jingina bayansa a jinkin kujera ya kwantar da kansa idanunsa a lumshe kamar Mai barci." "Ina matarka take da yaronka." "Tana America." "Me take yi a Amuruka?" "Wajen iyayenta take?" "Yaushe za ta dawo?" "Ban sani ba." Ya bata amsa a takaice. Sai ya ji ta sake jefa masa wata tambayar. "Ina fatan dai ba sakinta ja yi ba ko wata matsala ce ta saka ta tafi ko?" Ba tare da ya bude idanunsa ya ce mata "Abunda ya saka kika kira ni kenan?" "Uhm kai dai ka sani, dama na kira ka ne don ina son na sake kulla dankon zumunci a tsakanin jikokina." Bai ce komai ba ya ji muryarta tana cewa. "Ina son hada aurenka da Nihal." Ba shiri ya bude idanunsa da suke a lumshe ya zuba mata su tare da cewa. "Wai waye za ki hada aurensa da Nihal?" "Kai mana." "To ba na ra'ayi." Ya fad'a fuskarsa a tsuke, kallonsa ta yi cikin kwantar da murya ta fara magana. "Haba Ajmalu kaga yar uwarka ce Nihal ka yarda ayi auren nan don Allah, saboda karfafa zumunci tsakanin iyayenku, ka ga ita kadai ce jikata mace tunda iyayenku biyu da mahaifinka da mahaifiyarta suka rage mani ina son na ga na hada ku raya sunnar ma'aiki. Ka ga ita ma tana masifar sonka, ka tausaya mata don Allah ka aure ta." Murmushin takaici ya yi tare da cewa. "Ina da mata ai ko, Kuma ba na ra'ayin auren mace biyu." "Ka kyale wannan banzan ra'ayin naka tunda ba inda aka ce namiji ba dole mace d'aya zai aura." Shiru ya mata bai tanka mata ba, zuwa can ta ce. "To ita yarinyar can da aka ce kayi mata ciki ta haifa maka yaro fa, na ji ance yar shaye-shaye ce kuka karuwa ce ta baro gidan iyayenta ta shigo yawon duniya, Kuma na ji an ce kana shirin aurenta ko?" "Eh idan har Amatullah ce zan aura." "Au da ka auri yar uwarka Mai mutunci da kima ka gwammaci ka auri karuwa ko? Lallai ba shakka ashe dama kai lalatacce ne ban sani ba, dama lalatacce sai lalatacciya to ka sani ba za ka taba aurenta ba sai Nihal za ka aura." Wani dariya ya yi Wanda ya saka ta saki baki tana kallonsa, don ba ta Saba ganin yana dariya ba. "Au dariya ma na baka?" Bai ce mata komai ba ya janyo laptop d'insa ya cigaba da danne-danne duk surutun da ta ke masa bai ce mata komai ba ya share ta, da ya ga surutun nata ba Mai karewa ba ne bai da niyyar yin magana ya kalle ta ya ce "Ki fita." Da mamaki take kallonsa tare da cewa "Ba zan fita ba dan ubanka kai ka siye mani gidan ko kuwa?" "Idan ba ki fita da kafarki ba zan fitar da ke da kai na?" Nan fa ta dinga masifa ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, da ya gaji da surutun nata ne ya ajiye laptop d'insa,ba zato ba tsammani ta ji ya yi sama da ita ya d'aga ta, zaro idanu ta yi tana zaginsa amma ko sauraronta ba ya yi, haka ya fita d'auke da ita kamar ya d'auki yar baby. Jin surutun ta zagin da take masa ne ya sa Nihal da Sudais dake zaune a falo kallonsu, sakin baki suka yi yayin da Sudais ke ta dariya. Bai ajiye ta ko ina ba sai kan doguwar kujera Mai zaman mutum uku. "Kiyi zamanki a nan don kina damuna da yawa kada ki saka ni ciwon kai." Daga nan ya saka kai ya koma d'akin tare da murza key ya rufe. Cike da bacin rai Dad din Munnir ya ce "Haba Munnir da hankalinka da tunanin ka kake fad'a mani haka, shin yaron da ka ce tana da shi ta taba yin aure ne?" Kai kawai Munnir ya girgiza cikin sanyin jiki ya ce. "Ba ta taba yin aure ba " "Kana nufin d'an shege ta haifa?" "Eh Abba." Mummy ce ta Kalli Dady dake kallon Munnir ta ce. "Ai gashi nan da ka ce b zai auri diyar yar uwata ba saboda tana shaye-shaye to ga shi nan bayan yar shaye-shaye kuma karuwa ce zai aura wacce tafi Hafsat lalacewa, don Hafsat ba ta taba aikata abun kunya ba don cikin shege kuwa ai babban abun kunya ne. Kuma ku sani ba zan taba bari ya auri gurbatacciyar mace ba." Tana gama fadar haka ta fita. Dad ne ya maida dubansa ga Munnir ya ce "Na San halinka Kuma na San ba za ka taba zaben tumun dare ba, duk abunda ka yi na San kana da dalilin yin sa, ina son ka sanar dani gaskiyar dalilin yanke hukuncin auren nan." Nisawa yayi sannan ya bawa Dad labarin Amatullah tun ranar da ya fara ganin ta da haduwarta da Hafsat, da yadda Hafsat ta shiga rayuwarta ta lalata mata rayuwa da yadda ta saka ta shaye-shaye da yadda ta hada baki da wani ma'aikacin hotel aka yi mata fyade ta samu ciki da Koran da Abba ya mata har zuwa dawowarta ba abunda ya boye wa Dad d'insa. Tsananin tausayinnta ne ya kama Dad d'insa Munnirat da ke jinsu har da kuka ta yi, Kuma Dad ya masa alkawarin in Sha Allah gobe za'aje gidansu Amatullah a nema masa aurenta, cikin farin ciki ya rungume Dad din tare da masa godiya. Daga nan ya tashi ya nufi d'akinsa cike da farin ciki, burinsa ya kusa cika zai auri Amatullah. Marka kuwa tunda Ajmal ya dire ta akan kujera ta dinga zaginsa, Nihal Kam jikinta ne ya yi sanyi don ta San bukatar ta ba ta biya ba, don dai ta San tuna ta ga yanayin fusakarsa ta San ba nasara. "To wallahi ba ka isa ba ja'iri mara mutunci Kuma aure kamar anyi shi an gama." Kallon Nihal ta yi. "Kira mani ubansa a waya." Jiki na rawa ta ya d'auki waya ta lalubo lambar Dady ta kira bugu biyu ya d'aga. Cikin gairmamawa ya gaida mahaifiyar ta sa, ko amsawa ba ta yi ba ta fara masifa "Ibarahim ka haifo mana bala'i ban sani ba sai yau, ashe yaron nan bai da mutunci ban sani ba?" "Wani yaro kike magana?" "Wani yaro kake da shi?" "Ajmal kike nufi?" "To kana da wani yaro ne bayan shi?" "Subahanalilahi me ya yi ?" "Me ye ma baiyi ba, wai ni zan shiga ina masa maganar hada shi aure da yar uwarsa shine yake cewa na fita masa d'aki, da naki fita ina masa fad'a shine ya cure ni kamar kayan wanki ya zo ya yi wurgi da ni kan kujera ya koma ya garkame k'ofa?" Dafe goshi Dady ya yi tare da kallon Ammi dake kan kujera wacce ita ma shi take Kallo. Ya ma rasa ta cewa don ya San tabbas Ajmal ba ya jitiwa da Marka saboda ta fiye surutu da magana, Wanda shi Kuma abunda ya tsana kenan a rayuwarsa. Hak'uri ya bawa mahaifiyar ta sa wacce Ke ta ruwan masifa. "To shi da ita sun daidaita suna son junansu ne?" "Ban damu da wannan ba aure ne ko yana so ko baya so sai an d'aura shi na gama yanke magana." Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z 🤦‍♀️ *YAR MAYE*🤦‍♀️ (_The drug abuser_) Page 8️⃣6️⃣ "Ban damu da wannan ba, aure ne yana so ko baya so sai an d'aura shi na gama magana." Tun kafin ya ce komai har ta katse Kiran wayar. Kallon Ammi ya yi da duk jikinta ya yi sanyi ya ce. "Kina jin abunda take fad'a ko?" Jinjina kai kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba, gefe d'aya Kuma tana tausayin d'an nata, don ta lura ya dade da kamuwa da son Amatullah a zuciyarsa Kuma ita ma Kanta tana son ya aure ta ko saboda d'a dake tsakaninsu. Ba ta isa ta yi jayayya da maganar Marka ba don ko Abba ba zanli yi jayayya da maganar ta ba ballanata ita, amma damuwarta shine ta San cewa Ajmal baya son Nihal don ko zaman da ta zo ta zauna da su ta lura da yadda Nihal din ke shige masa sai dai sam bai ba ta fuska ba, don ta lura baya yin Nihal din don ma wani lokaci idan ya ga idan Ammi ne yake dan kula ta, yanzu idan aka hada su aure a haka ya zaman nasu zai kasance tunda baya son ta Kuma ta fi kowa sanin halinsa Nihal ce kawai za ta Sha wahala. Tashi ta yi ta nufi bedroom d'in ta, wayar Ajmal ta kira tare da Kara wayar a kunne. Bangaren Ajmal kuwa tun da ya fitar da Marka a d'akin ya dawo ya zube a kan gadon bayan ya rufe k'ofar da key. Duniyar tunani ya lula yayin da ya lumshe idanunsa fusakar Amatullah kawai yake gani a idanunsa. Tsawon lokaci ya na haka har wayarsa ta soma ruri, bai kula ba idanunsa a lumshe har wayar ta katse bai bude idanunsa ba Kuma yana ji, sake Kiran wayar aka yi sai da ta kusa katsewa sannan ya bude manyan idanuwansa a hankali,kansa ya juya sannan ya mika hannunsa ya janyo wayar, ganin Sunan Amminsa ne ya saka shi sakin ajiyar zuciya sannan ya d'aga wayar. "Assalamu alaikum ya Ammina." Jin muryarsa kadai ta gane cewa yana cikin damuwa, amsa sallamar ta yi tare da cewa. "Lafiya kuwa na ji muryarka ta sauya kamar kana cikin damuwa." Nisawa ya yi don shi bai d'auki maganar Marka da mahimmanci ba, don shi Kam ya kudiri niyyar cewa ba Wanda ya isa ya saka shi auren wata yarinyar da babu soyayyar ta a cikin zuciyarsa, don haka ya saki murmushi tare da cewa. "Ba abunda ke damuna Ammina." "Yaushe ka fara boye mani matsalarka?" Murmushi Mai sauti ya saki tare da cewa. "Matukar ina da damuwa ba Wanda zan fara sanarwa sama da ke, don ni wannan abun ba d'auke shi da mahimmanci ba, don da na San dalilin Kiran wayar da ta yi kenan da ban zo garin nan ba wallahi." Duk maganar da suke yi cikin harshen larabci suke yin ta, nisawa Ammi ta yi tare da cewa. "Ka bi ta a hankali don ka San ba Wanda ya isa ya yi jayayya akan maganar da ta zo da ita, ko shawara ta yanke ba Mai ja da ita. A cikin 'ya'yanta, idan kuwa wani ya yi jayayya da maganar ta to za ta sallama shi ne kamar yadda ta sallama wan mahaifinka babban danta kenan, Wanda har yau ba Wanda ya San inda yake ko maganarsa ba Wanda ya isa ya yi ta a gabanta, Kuma na tabbatar da mahaifinka ba zai bari ta kai wannan matakin akan sa ba, don haka ka bi a sannu don idan ta dagawa mahaifinka hankali kai ma ka San me zai biyo baya." Nan dai ta cigaba da bashi shawarar yadda zai lallaba tsohuwar nan su rabu lafiya, ya amsa da to kawai dan shi bai ga dalilin da zai ya tsaya lallabata ta ba. Sallama suka yi sannan ya katse Kiran wayar. Bangaren Munnir kuwa tunda mahaifinsa ya amince Kuma ya fahimci shi don haka bai da damuwa da aurensa da Amatullah, don ya San dama Dad ne nai nemo masa auren Kuma ya amince da ya ji labarin yarinyar don haka ya ji kaso saba'in na danuwarsa ta ragu, yanzu Mom ita ce matsalar sa don bai San yadda zai fahimtar da ita ba har ta fahimtar kamar yadda Dad ya fahimta. Da safe bayan ya dawo daga sallar asuba kai tsaye d'akin Mom din ya nufa, da sallama a bakinsa ya shiga d'akin. Tana zaune bakin gado da alama salla ta idar, durkusawa ya yi cikin gairmamawa ya gaishe ta, ta amsa masa da fara'a Wanda ta kwana biyu ba ta masa ba. "Ina kwana Mom?" "Lafiya lau Alhamdulillah, ka tashi lafiya?" "Alhamdulillah." Fadada fara'ar ta ta yi tana cewa "Ma Sha Allah." Ita a tunaninta Dad ya Hana Munnir auren Amatullah, don tunda ta ji Munnir na cewa tayi cikin shege Kuma tana shaye-shaye shi ya sa ta bar wajen cikin murna tana tunanin Dad ba zai bari ba. Zama ya yi cikin kwantar da murya yana cewa. "Am Mom." "Na'm." Ta amsa tana Mai zuba masa idanu, don a tunaninta zai mata maganar Hafsat ce, don a tunaninta gara Hafsat a akan Amatullah." "Mom don Allah ina son ki fahimce ni da Kuma dalilina na wannan auren..." Katse shi ta yi ta hanyar cewa. "Ba komai ai yanzu ka gane gaskiya, abunda nake hango maka. Duk tsiya gara Hafsat." "Mom baki gane ba ne, ki tsaya ki saurare ni na baki labarin Amatullah wallahi sai kin tausaya mata, Kuma sai kin kaunace ta kamar yadda Dad ya tasusaya mata ya amince da zan..." Da sauri ta katse shi ta hanyar crewa. "Ya amince?" Gyada mata kai kawai ya yi ba tare da ya yi magana ba. "Zuciyarta ce ke mata zafi sosai, ranta ya baci, Kuma ta San cewa idan har Dad ya amince ya nema masa auren yarinyar nan ba yadda zata yi, don neman aure dama uba ne ke yi ba uwa ba, gashi yanzu ko ta yi masa asiri ba ya cinsa, abun ya fara damunta, don ada idan har ta nuna kalar bak'i ta ce fari ne Dad bai isa ya yi mata gardama ba, shima zai ce fari ne ko da kuwa ba haka ba, amma yanzu wai shi ne yake jayayya da maganar ta. Kallon Munnir ta yi tare da cewa. "Ka kawo mani yarinyar idan ka samu lokaci." Murmushin Jin dad'i ya yi tare da mata godiya, murmushin yak'e ta yi masa sannan ta jinjina kai, cikin farin ciki ya bar d'akin zuciyarsa fara tas. Bangaren Nihal kuwa ko barcin kirki ba ta yi ba ta Kuna hana Marka ta yi barcin kirki, sai kuka take mata ganin yadda ko Kallo ba ta ishi Ajmal ba, Marka da ta matsa masa da magana na sai dauko ta ya yi kamar tsumma ya zo ya zube kan kujera. Inda Marka ke Kara kwantar mata da hankali akan cewa aurenta da Ajmal sai anyi shi. Da sassafe ba ta karaya ba ta sake shiga cikin kitchen ta hada masa lafiyayyen breakfast don ta burge shi. Tana jera breakfast a dinning area ta ji motsin bude k'ofa, juyawa ta yi inda ta yi tozali da Ajmal sanye cikin farar jallabiya da alama daga masallaci yake. Cikin sanyin murya ta ce. "Ya Ajmal ina kwana." Ko kallonta bai yi ba ballantana ta saka ran zai amsa mata. Binsa ta yi da Kallo har ya bacewa ganinta, a hankali ta lumshe idanunta cikin zuciyarta tana cewa. 'Ka yi duk wani Jin kai da da takamar da za ka yi da sannu za ka dawo a tafin hannu na sai yadda na yi da kai, don sai na rama wulakancin da kake mani sai ka dawo kana bani hak'uri.' Yana shiga kuwa ya fara tattara kayansa don barin garin, don ya kudiri niyyar barin garin ba zai sake kwana ciki ba. Nihal kuwa d'akin Marka ta koma ta nufi bathroom din ta, don a lokacin barci ma Marka ke yi, wanka ta shiga ta yi inda ta fito daure da towel, zama ta yi gaban dressing mirror don yin kwalliya. Dad din Munnir kuwa Kiran abikansa a waya ya sanar da su zancen zuwa nemawa Munnir auren Amatullah, abikansa guda uku ya kira ya sanar da su, inda suka ajiye da misalin k'arfe goma Sha d'aya zasu hadu don zuwa, bisa jagorancin Sadik abokin Munnir. Kwalliya Nihal ta tsantsara mai kyau, inda ya shirya cikin Riga da siket na material, dinkin ya masifar matse ta don duk surar jikinta a bayyane suke, k'arin gashin attached din ta ta yi ne ta sake shi har gadon bayanta. Turarurruka ya feshe jikinta da su sannan ta fito sanye da takalmi Mai tsini tana tafiya d'ad'd'aya. Kai tsaye ta nufi bedroom d'in da Ajmal yake ciki, knocking ta yi daga bakin k'ofa, daidai lokacin da ya gama rufe jakkar kayansa, yana sanye cikin kananun kaya bakin wando da t-shirt ja nai gajeren hannu, yana d'aure igiyar takalminsa Wanda takalminsa ma ya kasance ja ne kalar rigar da ya saka.don shi a tuaninsa Sudais ne ya zo kasancewar ya kira shi a waya kan cewa ya zo ya kai shi airport. Don haka ya bada izinin shigowa. Nihal ce ta shigo bakinta d'auke da sallama, can k'asan makoshinsa ya amsa don idan ba Wanda ya lura da bakinsa ba ba zai San ya amsa ba. A hankali take taku d'aya bayan d'aya, Kallo d'aya ya yi mata ya d'auke kai, don haka ta k'araso har gaban sa cikin kashe murya ta ce. "Ya Ajmal barka da safiya." "Yauwa." Ya amsa a takaice. Ba ta damu ba ta sake cewa. "Breakfast d'inka ko na kawo maka a nan ne.?" Bai kalle ta ba tsadadden agogon hannunsa ya duba lokaci, don ya matsu Sudais ya zo ." "Ke ce kika sanarwa Marka kina son aurena ko?" Zuba masa idanu ta yi daidai lokacin da ya dora idanu akan ta Wanda kwayar idanunsa ke rikita ta, da sauri ta d'auke Kanta don wani kaifi da kwarjin da idanunsa ke mata. "Ki sani ba zancen aure tsakanina da ke soyayyar 'yan uwantaja nake maki kar ki manta da wannan." "Wayarsa ce ta soma ruri, ganin Amatullah ne ya saka shi d'auka, don ya rasa daga jiya zuwa yau sai kiransa take, idan ya tambaye ta sai ta ce ba komai. Har ta katse bai daga ba sai da Kiran ta katse sannan ya kira ta video call. Tana zaune a Saman sallaya sanye take da hijabi da alama tun sallar asuba take zaune a wajen. Daga kiran wayar ta yi ta zuba wa wayar dara-daran idanunta, ta kasa cewa kaomia Kuma da alamar tana cikin damuwa, don idanunta har sun sauya launi zuwa ja." Tsawon mintuna biyar ba Wanda ya yi magana a cikinsu, fuskarta a sunkuye shi Kuma ya zubawa fuskarta idanu kamar Mai karantar wani Abu. A hankali ta dago kai ta kalle shi tare sunkuyar da kai ta ce. "Ina kwana?" "Meke damunki?" "Ba komai." "Kin ga idan akwai abunfa ke damunki ki sanar da ni, idan har na cancanta, ko ba komai ai ni uban danki ne Kinga ki don albarkacin Khalifa ya kamata na Dan halin da kike ciki ko Ummin Khalifa." Yadda ya kira sunan ta ne ya saka ta ji wani irin har ta kalle shi. "Ina yarona?" "Yana barci." Ta juyar da wayar daidai inda Khalifa ke barci, sanye cikin kayan sanyi an lullub'e shi da bargo." "Ki shafa mani kansa." "Fad'a mani matsalar ki." "Wai yau zasu zo." "Su waye?" Don shi bai gane akan me take magana ba. "Iyayen Munnir." "Me zasu zo yi?" Kamar zata yi kuka ta fara magana. "Abba ya ce ya turo ayi maganar aure na da shi." Wani irin yanayin Ajmal ya tsinci kansa a ciki Wanda ya ji zuciyarsa ta masa wani nauyi, ya zubawa Amatullah idanu yana karantar yanayinta, don ya ga tana cikin damuwa, amma sai dai shi a tunaunsa tana son Munnir, tunda lokacin da ya mata zancen auren ta da zai yi sai ta nuna ita ba ta son sa tana da Wanda take so Hakan ya saka bai sake mata maganar ba sai dai ya dinga fakewa da sunan zuwa wajen yaronsa da kiranta ta don Jin ladiyar yaron amma yana dama da soyayyar ta a zuciyarsa. Don tabbatar da zarginsa sai ya nuna kamar maganar ba ta dame shi ba alahalin hankalinsa a tashe yake. "To ai farin ciki za ki yi tunda kin ce baki so na kina da Wanda za ki aura." Tura baki ta yi tana cewa "Ni yaushe na ce ba na sonka? Cewa na yi ina da Wanda zan aura." "To shi ai kike cewa kina so za ki aura?" "Ni ba haka nake nufi ba cewa na yi Abbana ya zaba mani shi Kuma na San baya canza magana." Ya fahimci ba ta son auren Munnir amma yana son ya gasgata soyayyar da take masa, don haka ya ce. "To yanzu baki son auren Munnir ko?" Shiru ta masa inda ya sake cewa "To yanzu wa kike so?" "Dan harararsa ta yi cikin sigar shagwaba Wanda hakan ya saka shi sakin murmushi Mai sauti, don ya gane abunda take nufi, Kuma har ga Allah ya ji dad'in Hakan sosai, nan ya kwatar mata da hankali akan cewa zuwansu ba shine auren ba ta kwantar da hankalinta komai zai tafi daidai, ya kuka mata alkawarin zuwa gare ta wani sati. Nan ya dinga Janta da fira har ta saki rai sannan ya mata sallama ya katse Kiran wayar. Sai a lokacin ya tuna da Nihal a cikin d'akin wacde ta cika ta yi bam, fita ta yi da sauri tare da banko kofar da karfi ta fice, tabe baki ya yi tare da sake lalubo lambar Sudais, nan ya sanar da shi ya shigo gidan. Trolley bag d'insa ya janyo tare da baro d'akin ya nufi falon gidan. Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z 🤦‍♀️ *'YAR MAYE*🤦‍♀️ (_The drug abuser_) Page8️⃣7️⃣ Trolley bag d'insa ya janyo tare da baro d'akin ya nufi falon gidan. Yana k'arasowa falon ba kowa har ya nufi hanyar fita sai ya ji motsin bude k'ofa, juyawa ya yi sai ya ga Nihal ce tare da Marka suka fito cikin hanzari, da alama ta sanar da ita ne don haka ta fito ba shiri. Kallonsa Marka ke yi da mamaki shi Kuma ya bude baki yana fadin. "Ina kwana kin tashi lafiya?" "Da ban kwana ba za ka ganni ne, mara mutunci Wanda bai San abun arziki ba, ina za ka tafi ba ka bari an tsaida magana d'aya ba, ko ka d'auka wasa nake maka, idan Kuma har kana ganin kai ban isa da kai ba to shi ubanka na isa da shi, zan saka shi ya sa ka yi abunda ba ka yi niyyar yin sa ba." Ajiye trolley d'insa ya yi a a hankali ya k'arasa wajen da Marka take tasye yana sakin wani murmushi, sunkuyawa ya yi daidai saitin fuskarta yana cewa. "Wai me ya sa kika fiye son tashin hankali ne da rigima? Wanda a wannan shekarun naki bai kamata ace kina saka damuwa a ranki ba ko saboda hawan jini, maganar gaskiya Kuma zan fad'a maki ita ne, ba na son na auri Nihal saboda ba ta da gurbi a cikin zuciyata, idan Kuma kika matsa kika takura wallahi ita 'yar lelen taki za ki jawa, don wallahi ita ce za ta Sha bakar wahala, don ina Mai tabbatar maki da cewa sai kin yi nadamar hada aure na da ita, Kuma da ka kanki za ki warware Kullin da kika kulla." Yana kaiwa nan ya ja trolley d'insa ya kai hannu ya Murda handle din k'ofar zai fita ya jiyi sautin muryarta tana cewa. "Ba shakka fitsararre mara kunyan yaro, har ni za ka yi wa barazana, don ma zan yi maka gata saboda kai baka iya zaben macen aure ba, tashin farko ka je ka auro yarinyar da ta tashi a cikin turawa mata tarbiya da tashin sanin darajar mutane, wacce ma bata San darajar auren ba, don ita ta San darajar aure ba za ta barka ta dinga yawo kasashen turawa ba tsawon lokaci ba ta dawo ba, don ma lalacewa ace wai tana gidan iyayenta zaune da aure a kanta, ga dabi'arta ba irin na hausa Fulani ba yarinyar kamar 'yar kafurai, madadin idan zaka Kara aure ta biyu ka auri Nihal yar mutunci shine wai kake shirin auro karuwa wacce ta bar gidan iyayenta ta shigo yawon duniya har da cikin shege ta lika maka wai naka kai kuka da ke soko ne

Chapter 38 of 51