sajensa, a hankali ta fara magana.
"Dan Allah ka yi hak'uri na ga kamar kana fushi da ni."
Bai ce mata komai ba Kuma bai hana ta yi masa abunda take yi ba. Ganin haka ne ya sa ta sake narkewa a jikinsa tare da cewa.
"Na yi missing d'inka sosai wallahi, duk na bi na damu da nisantar da na yi da kai, ji na yi ba zan iya jurewa ba shi ne na zo dan na baka hak'uri, dan Allah ka mance da abunda ya faru a baya tsakanin mu in Sha Allah na canza Kuma zan gyara kura-kurai da na yi a baya, sanin kanka ne cewa ina sonka sosai fiye da komai da kowa a rayuwata."
Duk maganar da take yi bai ce mata komai ba Kuma bai hana ta abunda take masa a jikinsa ba, jin ya share ta ne ya sa ta cewa.
"Dan Allah na ji ba ka ce komai ba."
"Uhmm"
Shine kawai abunda ta ji daga gare shi, karshe ma zame ta ya yi daga jikinsa tare da sauka daga gadon, kai tsaye ya nufi hanyar bathroom don yin wanka, ganin haka ya sa ta sauko daga gadon ta rugu da gudu ta rungume shi ta baya tare da saka masa kukan munafurci.
Cak ya tsaya shi bai shiga bathroom ba Kuma bai zame ta daga jikinsa ba, Kuma bai hana ta kukan da take yi ba.
Ganin bai da niyyar kula ta ya sa ta sake bude sautin kukan da take yi, Wanda ta san baya son k'ara ko hayaniya dole zai kula ta. Hakan kuwa aka yi ji ya yi ba zai iya jurewa ba, dan haka ta juyo da ita suna fuskantar juna, kwantar da kanta ta yi a k'irjinsa tare da cigaba da kukan da take yi.
Ba tare da ya kalle ta ba ya fara magana yana cewa.
"Yanzu me na yi maki da kika saka ni gaba kika addabe ni da koke-koke, ni da kika yi wa laifi ban yi maki kuka ba amma ke ce za ki yi mani kuka, saboda Jin dad'i ko me?"
"Ni wallahi na ga ka na fushi da ni bayan na tuba amma ba ka yafe mani ba, wallahi ba zan iya jurewa ba zan canza ba zan sake ba."
Kallonta ya yi tare da cewa.
"Nasreen ba za ki taba canzawa ba, ko yanzu ban yarda da wannan..."
Kuka ta k'ara sakawa sosai Wanda hakan ya saka shi saurin cewa.
" Ya isa haka nan na ji, bari na yi wanka na fito ko?"
Da har za ta ce su shiga tare ganin haske a wayarsa ne ya sa ta d'aga kai alamar to.
Yana shiga ta karasa wajen wayarsa ta d'auka, dan ta ga alamar shigowar message, kasancewar ta san password na wayarsa sai ta bud'e.
Tana dubawa ta ga sunan Amatullah, cije leb'e ta tayi wato ta yi mata fad'a a waya amma dan ba ta da ziciya shi ne ta turo message ko?"
Budewa ta yi ta fara katantawa kamar haka.
_*Asslamu alaikum*_
_*Barka da safiya Abban Affan. Kuyi hak'uri idan na takura makiu, dama na kira ne dan na sanar da kai cewa Ammi ta ce na shirya na tafi saloon a wanke da kitso, kafin su Saliha su zo su mani lalle, to na san security ba zasu bari na tafi ba tare da izininka shi ne nake neman alfarma kira su ka masu magana su bari na tafi, ko Ya Ahmad sai ya kai ni dan ban san wajen ba.*_
Bayan Nasreen ta gama karantawa ta goge message d'in, sai tura mata reply kamar haka:
_*wslm Ahmad zamu fita da shi ne, dan haka ki fita ki tambayar waye Samuel ya kai ki shagon Saloon inji ni*_
Tana turawa ta goge sannan ta sannan ta kira Samuel k'ak'asa da murya ta bashi umarnin cewa Amatullah za ta fito zata nemi shi akan ya kai ta saloon, to ka da ya kai ta ya bi hanyar bayan gari za ta kira shi ta sanar da shi inda zai kai ta.
Daga nan ta katse Kiran wayar Jin Ajmal na kokarin fitowa daga wanka.
Murmushi ta sakar masa tare da tashi tana cewa.
"Bari n taya ka shiryawa ko?"
Busar masa da gashin kansa ta fara yi bai hana ta ba, kallon fusakarsa ta yi ta jikin mirror tare da cewa.
"Daga yau ni zan dinga shirya ka fa?"
Ba tare da ya kalle ta ba ya ce.
"Gobe zamu tafi k'asar Qatar kwana biyu zamu yi sai mu dawo, daga nan Ba nan zamu dawo ba sai mun kai Amatullah wajen iyayenta."
Kamar ba komai da t shirya ta ce masa.
"Ma Sha Allah, to me zaku je yi k'asar Qatar?"
"Umma ce ta ce tana son ganin jikanta shi ya sa zamu fara kai su ta gansu sannan mu tafi ga iyayenta."
"Gaskiya ya kamata Kam amma gaskiya tare da ni za'a tafi."
Kallon t ya yi da cewa
"Me za ki tafi yi?"
"Dama ni na jima ban je k'asar Qatar Kuma Affan ma ai ya kamata mu je ya gaishe ta, Dan har garin su Amatullah da gidansu ya kamata mu je gaba d'aya."
Shiru ya yi zuwa can kuka ya ce
"Shikenan."
Amatullah na ganin message d'in da ya shigo wayar ta ta karanta, mamakin ta waye Samuel, tashi ta yi dama ta saka hijabi a rungume Abdallah suka fita, Sallama ta yi wa Ammi kan cewa zasu tafi, direba na jiranta, fatan dawowa lafiya Ammi ta mata sannan suka tafi, Dan Har Ammi ta so ta karbi yaron ganin yana kukan rigima kwana biyu ya sa ta barshi.
Amatullah na fita Samuel in ya k'araso tare da cewa .
"Kin fito Madam?"
Kallonsa ta yi ta ce.
"Kai ne Samuel?"
Jinjina mata kai ya yi tare da nuna mata mota, suka karasa ya bude mata bayan mortar ta shiga.
🤦♀️ *'YAR MAYE*🤦♀️
(_The drug abuser_)
7️⃣0️⃣
Jinjina mata kai ya yi tare da nuna mata mota, suka karasa ya bude mata ta bayan mortar ta shiga.
Ya ja motar suka bar gidan.
A tare suka fito downstairs Ammi dake zaune a falo ta d'aga kai ta kalle su, murmushi ta yi na jin dad'in ganinsu a tare dan ta lura akwai tashin jitiwa a tsakaninsu, kasancewar ba wanda ya mata magana a cikinsu ya sa ta yi shiru ba ta yi magana ba, dan kada su ga kamar ta saka masu idanu ne.
Da sallama suka k'araso wajen da take zaune, Ajmal cikin gairmamawa ya gaishe ta, ta amsa masa cikin sakin fuska da walwala. Nasreen ma ta gaishe da Ammi ta amsa cike da fara'a. Daidai lokacin da Affan ya k'araso a guje ya fad'a jikin kakarsa. Kallon Ammi ya yi tare da cewa.
"Ammi ina baby?"
Ammi ta gane cewa Abdallah yake nufi dan haka ta ce .
"Baby ya fita tare da Mom d'insa."
Da sauri Ajmal ya fara magana yana cewa.
"Fita zuwa ina Kuma?"
"Za ta wanke kai ne shi ne na ce a kai ta saloon su wanke mata a can?"
"Kin San fa Ammi ba na son fitan yarinyar nan, daga gidan nan, shin waye ya kai ta saloon d'in?"
Kallon rashin fahimta Ammi ta masa tare da cewa.
"Ban gane tambayar da kake mani ba, ita fa ta ce barj ta kira wayarka ta sanar da kai ka hada ta da Wanda zai kai ta can, saboda wai security dake bakin gate ka hana su barinta fita."
"To ai ba ta kira wayata ba, dan bami yi magana ba."
Sai a lokacin ya tuna da cewa ta kira Nasreen ba ta d'auka har take mata fad'a.
Wayarsa ya ciro daga cikin aljihu ya kira Ahmad a waya.
Bugu niyu ya d'aga daga cikin wayar yake cewa.
"Morning sir."
Bai amsa masa ba ya fara tambayarsa ina yake, ya sanar da shi cewa yana d'akinsa.
Kallon Ammi Ajmal ya yi tare da cire wayar daga kunnensa ya ce.
"Anya kuwa ba ta cikin d'akinta?"
"Ina zaune anan fa ta fita."
Mai da wayar a kunnensa ya yi tare da cewa.
"Amatullah ba ta fito ba?"
Ahmad ya amsa masa da cewa.
"Ban sani ba sir, yanzu nake fitowa."
"Ka bincika mani waye ya fita."
Daga nan ya katse Kiran wayar yana lalubo lambar wayar Amatullah.
Kira ya dannan mata ba ta d'aga ba,har sai uku yana kira ba'a daga ba.
Nasreen ce ta kalle shi tare da cewa.
"Muje muyi breakfast ko?"
Girgiz mata kai kawai ya yi tare da cewa.
"Ki je kiyi breakfast kawai."
Kallonsa ta yi tare da cewa.
"Kai fa?"
"Kada ki damu."
Abunda ya iya cewa kenan, sannan ya nufi d'akin Amatullah.
Yana shiga d'akin ya fara dube-dube, ba kowa har bathroom ya yi knocking gani yake kamar tana gudan tunda Ahmad na nan. Dan ya san Ahmad ne kawai zata iya cewa zata fita ya kai ta.
Kiran Ahmad ne ya shigo cikin wayar ta sa , bayan ya d'aga kiran wayar ne Ahmad ke shaida masa cewa an ce Samuel ne ya fita daga gidan. Ya tambayar ko tare da waye suka fita ba Wanda ya gani kasancewar motar mai bak'in gilashi ne.
Gaba d'aya sai ya ji hankalinsa ya kasa keanciy, dan haka sai ya nufi d'akinsa.
Nasreen dama ko da Ajmal ya ce ta je ta yi breakfast d'akinta ta nufa, wayar ta ta d'auka ta kira lambar wayar Fareeda.
Bayan Fareeda ta d'auka ne ta ce.
"Hello k'awata."
Daga can bangaren Fareeda ta masa da .
"Ma'am ya kike?"
"Ina lafiya."
"Fatan kin yi amfanin da shawara ta?"
"Nayi kuwa har na k'ara da tawa basirar."
Murmushi mai sauti Fareeda ta yi tare da cewa
"Dakyau, wata basirar kika k'ara da ita?"
Nan Nasreen ta bata labarin abunda ta yi tun da shigarta dakin Ajmal har tura message da ta yi da Kiran Samuel duk ta bata labarin komai.
Dafe goshi Fareeda ta yi tare da cewa.
"Wai ke me yasa ba Kya tunani kafin ki aiwatar da abu ne? Ta ya ya za ki aikata wannan d'anyen aikin? To wallahi tun wuri ki dakatar da shi ki janye kudirin ki akan abunda kike kokarin aikata wa, Dan na san CCTV camera ta d'auki komai idan wani abu ya faru mijinki zai binciko komai."
Daga nan ta katse Kiran wayar, sai a lokacin Nasreen ta yi tunanin maganar kawarta gaskiya ne. Dan haka da sauri ta kira lambar wayar Samuel.
Daidai lokacin da Samuel ya yi parking a gefen hanya, Dan zuwa lokacin Amatullah har ta fara kuka, Dan tun da ta ga ga sunbar cikin gari tana ta masa magana cewa ina zai kai ta ya yi kamar ba ya Jin ta sai ta fara kuka ganin irin gudun da yake yi, ta d'auki waya da niyyar Kiran Ajmal ya fisge wayar.
Daga nan ta fara kuka ta sadakar yau sai yadda Allah ya yi da ita.
Suna zaune a cikin motar ne ta ji wayarsa na ruri, da sauri ya d'aga wayar, bai yi magana ba zuwa can ta ji ya ce.
"Okay."
Daga nan ta ga ya mik'o mata wayar ta. Ya juya akalar motar ya koma hanyar da suka baro.
CCTV camera Ajmal ya duba yana kallonta tun fitowarta har zuwa lokacin da Samuel ya k'araso ya bude mata mota har fitarsu.
Wayarsa ya lalubo, ya dannawa Samuel kira, bugu d'aya ya d'aga sannan ya yi parking.
"Tambayarsa ya yi inda ya kai Amatullah ya sanar da shi cewa yanzu zai kai ta saloon, dama ya tsaya ne kai wani sako da Nasreen ta aike shi Hakan ya saka ba su isa saloon ba.
Katse Kiran wayar ya yi ganin Kiran Amatullah na shigowa wayarsa
Bayan ya d'aga kira wayar kafin ya yi magana ne ya ji muryarta ta ce .
"Yaya."
Jin muryarta kamar t yi kuka ne ya saka hankalinsa ya tashi, da sauri ya ce.
"Me ya same ki ne ina ta kira baki dagawa?"
Kallon Samuel ta yi cikin tsoronsa ta kasa cewa ya amshe mata waya, Dan haka sai ta ce.
"Zan maka message."
Daga nan ta katse Kiran wayar ta fara tura masa message kamar haka.
_Yaya ban yarda da shi ba please ka zo ko ka turo Ahmad ya kai ni_
Tana turawa ba jimawa sai ga reply ya mata da cewa.
_Okay ina zuwa_
Wayar Samuel ce ta yi ringing inda Ajmal ya bashi umarnin ya tsaya inda yake. Nan Samuel ke sanar da shi cewa sun k'araso saloon d'in ya bashi address na wajen sai Ajmal ya bashi umarinin ya wuce ya barta gashin nan zai zo da kansa.
Bayan ta shiga shagon Samuel ya bar wajen.
Amatullah ta shiga ciki ta gaida wadanda ta samu ciki ta zauna tana jira.
Wayarta ce ta yi ruri ta duba ta ga Ajmal ne ke kiran wayar. Bayan ta d'auka ne ta saka masa kuka. Cikin tashin hankali ya fara tambayar ta yana cewa.
"Meke faruwa ne kina ina kika ke da waye?"
Cikin kuka ta fara magana tana cewa.
"Ina wajen saloon d'in da ya sanar da kai."
"Ki shiga ciki ina zuwa yanzu."
Bai jira cewarta ba ya katse Kiran wayar tare da fitowa falon.
Ammi da ke zaune a falo ganin yanayainsa ya sa ta mike tsaye tare da cewa.
"Lafiya kuwa?"
Bai tsaya ba yana tafiya yana cewa.
"Ba komai Ammi ina zuwa yanzu."
Yana fita bodyguards d'insa suka taso zuwa inda yake, da hannu ya dakatar da su ya nufi d'aya daga cikin mitocin da ke gidan.
Shiga ya yi ya yiwa motar key horn yake dannawa ba kakkautawa, nan da nan aka wangale masa gate ya nufi unguwar da Amatullah take, kasancewar ya san wajen saloon d'in nan matarsa Nasreen ke zuwa.
Munnir yana zaune a mota wajen mai zaman banza yayin da Sadik ke driving. Kallonsa Sadik ya yi sannan ya kau da kansa tare da cewa.
"Amma abokina yanayin yadda ka yi wa iyayen Amatullah magana fa ka san ba zai masu dad'i ba, bisa la'akari da cewa suna tunanin ta tuba ta yi nadama zuwanka ya saka masu shakku akan ta.."
Ajiyar zuciya Munnir ya sauke tare da cewa.
"Ai nima daga baya na yi tunanin haka, wallahi rai na ne ya baci da abunda gayen nan ya yi mani, sannan itama ai bai kamata ta zauna gidansa ba bayan ya lalata mata rayuwa zaman me take yi a gidansa, karatu yake koya mata?"
"Koma mene ne dai ka kyautata masu zato, sannan idan Allah ya kai mu gobe muka tafi zamu ji komai idan ya so daga baya zaka yanke mata hukunci."
Jinjina kai Munnir ya yi sannan ya Kalli Sadik ya ce.
"Haka ne, wannan ba halina bane amma in Sha Allah Hakan ba zata sake faruwa kawai kishi ne ya sa na Fadi haka.
Suna tsaka da tafiya kamar an ce ta wai ga ya Kalli gefensa, sai ya hango Hafsat tsaye akan titi, da kayan da yake jikinta lokacin da take hannun yansanda.
"Tsaya! Tsaya! Tsaya!"
Munnir ya fad'a Wanda hakan ya sa Sadik sauka gefen titi ya tsaida motar, kallonsa ya yi kafin ya yi magana har Munnir ya bude murfin motar ya fita, kallonta yake da mamaki a fusakarsa yayin ita ma shi take Kallo tana murmushi Wanda ita kadai ta San ma'anarsa.
K'arasa wa y yi tare da cewa
"Gudowa kika yi daga offishin yansanda ko?"
Wani dariya ta k'yalk'yace da ita tare cewa .
"Guduwa, ai ni ba mai guduwa ba ce kai ma ka San ba zan taba guduwa ba."
"K'arya kike yi ba yadda za'ayi a sake ki, dan badinki a cikin al'umma ba karamar hatsari ba ne."
Ya yi maganar yana rike hannunta. Kasancewar ta san ba guduwa ta yi ba Hakan ya sa bata damu ba, wayarsa ya lalubo ya nemo lambar wayar inspector ya danna masa kira.
Bayan inspector ya d'auki waya ne Munnir ke tambayarsa akan Hafsat, nan ya shaida masa cewa eh Ajmal ne ya bada umarnin a sake ta.
Murmushin takaici ya yi tare da sakin hannunta, nan Kuma Hafsat ta saki murmushi tare da cewa.
"Da alamar ba ka yi farin cikin fitowa ta ba, gudun na zame maka matsala nan gaba ko? To ka da ka damu indai matsala kullun a cikinta kake, ba za ka taba fita daga matsala ba har sai ranar da ka aure ni."
"Wannan karon idan har kika yi yunkurin shiga sabga ta to wallahi zan manta cewa 'yar uwata ce ke, zan maki abunda baki taba tunani ba."
Yana gama fadar haka ya shiga cikin motar Sadik ma ya shiga suka bar wajen, bin motar ta yi da harara.
Ajmal na parking a wajen gaban saloon d'in ya fito daga cikin motar, daidai lokacin da za'a fara wa Amatullah.
Wayarta ce ta yi ruri ba ta daga ba kasancewar ita ake yi wa, d'aya daga cikin matan da ke wajen ne ta rike mata Abdallah.
Jin wayar ta katse ne ya sa ya karasa Jikin shagon Saloon d'in, k'ofar gilashi ne daga ciki ana ganin mutumin da ke wajen.
Wasu 'yan mata da ke ciki ne suka hangi Ajmal ta waje d'aya ta ce.
"Wannan ba Ajmal Ibrahim Tafida ba ne?"
Gaban Amatullah ya Fadi Jin an ambaci sunan Ajmal, lokacin wayarta na cikin jaka Kuma wayar a silent take, so ba ta ma San yana kira ba.
Dayar budurwar ce tace.
"Shi ne mana ke baki gane shi ba ne, ai ni gayen ya yi mani ne wallahi, ya hadu ba k'arya."
Wata ta ce,
"Wai na ji an ce ya janye takarar da yake yi ko?"
"Eh ya janye tunda an ce an gano gaskiya ba ya da laifi akan abunda ya faru aka bukaci ya dawo bayan an dakatar da shi."
Wacce aka gamawa kitso yanzu ne ta tashi ta kalle shi ta cikin gilashin tare da cewa.
"Ko ba laifinsa ba ne dai ya aikata yana da d'an shege lallai haka abun yake ba wanda zai karyata ta, kuka fa an ce yarknyar da babyn suna zaune fa a gidansa sannan a ce ba laifinsa ba ne?"
Wacce ke rike da Abdallah ne ta ce.
"Amma Kuma bani mamaki wallahi, to ina ruwanku ne , mutane nawa suke aikata abunda ya fi na shi ba Wanda ya yi magana saboda baku San su ba, saboda yana babban mutum dan takarar da ya yi suna yasa kike ta wannan maganar, Kuma ko Ku yarda ko kar Ku yarda an ce mutumin kirki ne kaddara tana kan kowa abunda mahifina ya fad'a kenan."
Kasancewar saloon d'in matan manya da yaran manyan mutane ke zuwa, nan wata ta ce to mahifina naki ai kowa ya sani barawon gwamnati ne har aka kore shi."
Nan Abu ya so zama fad'a tsakaninsu Amatullah ba ta ce komai ba sai ma kunyar kada su gane ita ce yarknyar da suke maganar ya mata ciki.
Mai saloon ta raba wannan fad'a inda ta nufi waje wajen Ajmal ta bar d'aya daga cikin ma'ikatan ta ta k'arasa wa Amatullah.
Tana fita ta gaishe shi cikin gairmamawa tare da tambayarsa ko akwai abunda yake so ne, nan ya ce ta tambayar masa ko akwai Amatullah cikin wadanda suke wajen.
Dawowa ta yi tare da cewa
"A cikinki wace ce Amatullah?"
Cikin sanyin murya ta ce.
"Ni ce."
Kowa ya kalle ta sannan suka Mai da kallonsu ga Mai saloon d'in, dan Jin me zata fad'a, sai suka ki ta ce .
"Sir Ajmal ne ya zo wajenki."
Kallon jakkarta ta yi tare da cewa.
"Bari na kira shi."
Wayarta ta ciro taga missed calls d'insa, kiransa ta yi bugu d'aya ya d'aga, matayen da ke ciki su kalle ta su Kalli Ajmal dake waje Dan su tabbatar da ita yake waya.
Jin ya d'aga kiran wayar ne ya sa ta cewa
"Assalamu alaikum."
Ya amsa da
"wa'alaiki Salam."
"Dan Allah ka yi hak'uri an fara mani ne ba zan iya fitowa ba."
Murmushi ya yi tare da cewa.
"Hak'uri na me kuma gimbiya, zan jira ko nan da gobe ne."
"To na gode."
Ta fad'a cikin sanyin murya, sai ta ji ya ce.
"Ina babyna?"
Kallon Abdallah dake rungume wajen wata mta ta yi tare da cewa.
"Yana barci wata ce ta karbe shi."
"Okay"
Ya fad'a lokacin da ya juya yake sauka daga steps d'in, a tunanin ta tafiya zai yi kamar za ta yi kuka ta ce.
"Kada ka tafi ka bar mu"
"Kar ki damu ina nan ina juranku."
Bayan ta kashe wayar ne ta ga kowa na kallonta wata na nuna ta da hannu tana Jin maganar da wasu ke fad'a, suna cewa wai ita ce wacce ya yi wa cikin ashe dama, wasu na cewa ba wani kaddara tunda ga shi yana tare da ita ana nuna Abdallah ana cewa shine jaririn da suka haifa wata cewa ta hi ga shi kamar an tsaga kara shi da Abdallah.
Haka dai suke ta magana ba ta kula su ba, zuwa can sai kiransa ya sake shigowa Inda yake mata maganar kudin saloon zai bata, ta nuna masa ai Ammi ta bata har ta biya.
Ko da aka gama mata har da gyaran kafa duk anyi mata sannan ta karbi Abdallah ta masu sallama ta ta fito.
Nan ta same shi jama'a sun zagaye shi yana ta raba masu kudi, tana gefe tana kallonsa sai da kudin hannunsa suka kare, ya d'aga masu hannu alamar sun kare sannan suka waste, ya bude mata gaban mota ta shiga suka bar wajen.
A hanya yana ta tambayar abunda ya d'aga mata hankali ta ce b koamai amma kada ya sake hada ta da Samuel ya kai ta wani wajen bata yarda da shi ba, shi duk bai gane ba saboda ba shi ya turo Samuel ba Nasreen ce amma sai dai ya bata hak'uri akan ta kwantar da hankalinta.
A ranar bayan su Saliha sun zo aka yi mata lalle na zanen fulawa da kitso ta yi kyau Sosa.
Nan aka dinga shirin tafiya Ammi, Ajmal Nasreen, Amatullah sai Affan da Abdallah.
Dan Nasreen ta matsala ita ma sai an je da ita har gidansu Amatullah, duk da sun nuna mata cewa Qatar zasu fara zuwa amm ta ce sai ta bi su.
K'arfe goma na safe jiriginsu ya tashi, ya yin da Kuma a can bangaren Munnir ya taho tare da Abban 🤦♀️ *'YAR MAYE*🤦♀️
(_The drug abuser_)
7️⃣0️⃣
Jinjina mata kai ya yi tare da nuna mata mota, suka karasa ya bude mata ta bayan mortar ta shiga.
Ya ja motar suka bar gidan.
A tare suka fito downstairs Ammi dake zaune a falo ta d'aga kai ta kalle su, murmushi ta yi na jin dad'in ganinsu a tare dan ta lura akwai tashin jitiwa a tsakaninsu, kasancewar ba wanda ya mata magana a cikinsu ya sa ta yi shiru ba ta yi magana ba, dan kada su ga kamar ta saka masu idanu ne.
Da sallama suka k'araso wajen da take zaune, Ajmal cikin gairmamawa ya gaishe ta, ta amsa masa cikin sakin fuska da walwala. Nasreen ma ta gaishe da Ammi ta amsa cike da fara'a. Daidai lokacin da Affan ya k'araso a guje ya fad'a jikin kakarsa. Kallon Ammi ya yi tare da cewa.
"Ammi ina baby?"
Ammi ta gane cewa Abdallah yake nufi dan haka ta ce .
"Baby ya fita tare da Mom d'insa."
Da sauri Ajmal ya fara magana yana cewa.
"Fita zuwa ina Kuma?"
"Za ta wanke kai ne shi ne na ce a kai ta saloon su wanke mata a can?"
"Kin San fa Ammi ba na son fitan yarinyar nan, daga gidan nan, shin waye ya kai ta saloon d'in?"
Kallon rashin fahimta Ammi ta masa tare da cewa.
"Ban gane tambayar da kake mani ba, ita fa ta ce barj ta kira wayarka ta sanar da kai ka hada ta da Wanda zai kai ta can, saboda wai security dake bakin gate ka hana su barinta fita."
"To ai ba ta kira wayata ba, dan bami yi magana ba."
Sai a lokacin ya tuna da cewa ta kira Nasreen ba ta d'auka har take mata fad'a.
Wayarsa ya ciro daga cikin aljihu ya kira Ahmad a waya.
Bugu niyu ya d'aga daga cikin wayar yake cewa.
"Morning sir."
Bai amsa masa ba ya fara tambayarsa ina yake, ya sanar da shi cewa yana d'akinsa.
Kallon Ammi Ajmal ya yi tare da cire wayar daga kunnensa ya ce.
"Anya kuwa ba ta cikin d'akinta?"
"Ina zaune anan fa ta fita."
Mai da wayar a kunnensa ya yi tare da cewa.
"Amatullah ba ta fito ba?"
Ahmad ya amsa masa da cewa.
"Ban sani ba sir, yanzu nake fitowa."
"Ka bincika mani waye ya fita."
Daga nan ya katse Kiran wayar yana lalubo lambar wayar Amatullah.
Kira ya dannan mata ba ta d'aga ba,har sai uku yana kira ba'a daga ba.
Nasreen ce ta kalle shi tare da cewa.
"Muje muyi breakfast ko?"
Girgiz mata kai kawai ya yi tare da cewa.
"Ki je kiyi breakfast kawai."
Kallonsa ta yi tare da cewa.
"Kai fa?"
"Kada ki damu."
Abunda ya iya cewa kenan, sannan ya nufi d'akin Amatullah.
Yana shiga d'akin ya fara dube-dube, ba kowa har bathroom ya yi knocking gani yake kamar tana gudan tunda Ahmad na nan. Dan ya san Ahmad ne kawai zata iya cewa zata fita ya kai ta.
Kiran Ahmad ne ya shigo cikin wayar ta sa , bayan ya d'aga kiran wayar ne
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 29 Chapter of 51