Share this page
ko a magana ta, ko ni mahaukaciya ce?" Yanke dariyar ya yi tare da cewa. "Exactly ke mahaukaciya ce babu tabgama, dan idan ba mahaukaciyar ba wace ce za ta yi irin abinda kika yi? Kuma aure na dake ki manta da zancen domin yanzu na samu guarantee na rabuwa da ke, an yi walƙiya kowa ya ganki, kowa ya san wace ce ke." Gudu kawai yake yi Kan titi saboda lokaci ta tafi, inda ya cigaba da magana yana cewa. "Alhamdulillahi tunda Dad ya ga gaskiyar abinda nake son sanar da shi, kuma ya fahimta har ya yanke hukuncin da ya dace to na gode Allah." A firgice ta kalle shi tare da cewa. "Wane hukunci ya yanke , ba dai raba ni da kai zai yi ba ko? Dan Wallahi ba zan iya rabuwa da kai ba." ",Kamar yadda ni ma ba zan iya rabuwa da Amatullah ba." Ƙarya ne wallahi ba Amatullah ba ce matarka Ni ce, ni za ka aura ba Amatullah ba, na riga da na gina katangar ƙarfe a tsakaninka da Amatullah har abada. A kai ba ita, idan har ka aure ta to sai dai idan bayan rai na ne, idan kuma ba haka ba salwanta rayuwarka kai da Amatullah, idan har ka shiga duniya neman Amatullah to ni ma sai na shiga duniya neman katangar da zan gina tsakaninka da ita, idan har ban aikata abinda na faɗa ba to a canza mani suna." *Daga alƙalamin*✍️ Zainab Abdullahi KNT (Maman Ihsan) 09065327995 Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z 🤦‍♀️ *YAR MAYE*🤦‍♀️ (_The drug abuser_) *NA* Zainab Abdullahi KNT (Maman Ihsan) https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *GARGAƊI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. Ban yarda a karanta mani shi a youtube ko a maida shi audio ba tare da izinina ba. *BISIMILLAHI RAHMANI RAHIM* Page6️⃣1️⃣ Idan har ka shiga duniya neman Amatullah, to ni ma sai na shiga duniya neman katangar da zan gina tsakaninka da ita. Idan har ban aikata abinda na faɗa ba to a canza mani suna. "Canza suna nawa kuwa ai sunanki ya riga da ya dad'e da canzawa." Parking ya yi a kofar gidansu, ba tare da ya kalle ta ba ya ce. "Fita." Ba musu ta fi ta daga cikin motar zuciyarta na mata zafi, dan yanzu kam ta riga da ta gane kwata-kwata Munnir ba ya ƙaunarta. Buga murfin motar ta yi da ƙarfi ta nufi cikin gidan a fusace, tsuki ya yi tare da barin wajen. Ko sallama babu ta danna kai cikin falon, ba tare da ta kalli gefen Mamanta ke zaune ba ta nufi bedroom ɗin ta. Tana shiga ta murza key ta rufe sannan ta faɗa kan gado ta fashe da matsanancin kuka. Cikin tashin hankali Mamanta ta nufi ƙofar tana bugawa tare da kiran sunan Hafsat. Ganin ba ta da niyyar budewa ne ya saka fita waje, tana tamabayar mai gadin ko Hafsat tare da wa take, nan ya sanar da ita cewa ya ji tsayawar mota ya leka ya ga ita da Munnir ne. Komawa ciki ta yi dan ta gane dalilin kukanta wato Munnir ne ya bata mata rai, dan ta lura yanzu ba ya zuwa wajen Hafsat da daɗewa, da idan ya zo unguwar sai ya zo ya gaishe ta amma yanzu ko shigowa gaishe ta ba ya yi, ranta ne ya ɓaci dan haka ta suri gyalenta da wayarta ta fice daga falon. Direba na zaune a harabar gidan ya ga ta fito, da sauri ya tashi ya nufi wajen mota, dan ya san fita za ta yi. Bayan motar ya bude mata ta shiga sannan ya zagaya ya zauna ya ja motar, Idanunta na kan wayarta ta ce masa. "Gidan yayata za ka kai ni." "To Hajiya." Daga nan ya ja motar zuwa gidan su Munnir. Mum da Munnirat na zaune a folo sai ga Mama ta faɗo kamar wacce aka jeho. Kallonata Mum ta yi tare da cewa. "Lafiya kuwa na ganki a haka me ke faruwa?" "Ba dole ki ganni a haka ba, Hafsat ta dawo gida sai koke-koke ta ke yi gaba ɗaya ta ƙi ta saurare ni, ko magana ba ta yi ba ta shiga ɗaki ta rufe kanta a ciki, hakan ya saka na tambaya ita da wa suka zo, aka sanar da ni cewa tare da Munnir suke, hakan ya saka na ce bari na zo na tamabaya meke haɗa ta faɗa da Munnir ne? Dan daga baya baya zuwa tana yawan kawo Mani ƙoƙarin baya kula ta ya daina sonta, to yanzu abu har ya kai..." Ganin Dad da ke zuwa ne ya saka ta yin shiru. Kallonsa ta yi tare da cewa "Ina kwana?" "Lafiya lau" Ya amsa tare da zama a kan kujera, kallonta ya yi tare da cewa. "Ki zauna mana." Ba musu ta zauna inda ya kalli Munnirat ya ce. "Tashi ki shiga ciki." Nan take Munnirat ta tashi ta basu waje inda ya kalli Mama ta ce. "Tun wani lokaci Hafsat ta bar gida?" "Tun jiya da safe." Ta bashi amsa tana kallonsa dan jin me zai ce. Cigaba da magana ya yi inda ya ce. "Tun jiya da safe har rana ta yi aka yi yammaci ba ta dawo gida ba a matsayinki na uwa mai bada tarbiyya me ya kamata ki yi?" Cikin nuna rashin damuwarta ta ce "To ai Hafsat ba ƙaramar yarinya ba ce, tana fita ta kwana a gidan ƙawayenta ba wani abu ba ne." "Bai kamata ki yadda cewa a gidan ƙawarta take kwana ba, kin taɓa yin bincike dan tabbatar da cewa a gidan ƙawayenta take kwana? Idan ma haka ne me yasa za ki barta Yakamata a ce duk inda take da zaran kin ga yamma ta yi ba ta dawo ba ki neme ta..." Maganar da ta yi ne ya saka shi yin shiru, inda take cewa. "To ni na san yarinyata ba yarinyar banza ba ce, ballantana ace wai ta je yawon banza ne. Ni yanzu so nake a yanke ranar auren Hafsat da ɗan uwanta Munnir." Dad ya kalle ta da kyau tare da cewa. "Ba zancen aure tsakanin Munnir da Hafsa." Da sauri ta kalle shi cike da mamakin maganarsa. "Sai na ji kamar kunnena bai jiyo mani daidai ba, dan na san zancen da na ji bai dace ace ka fade ba ta ba." "Kunne ki daidai ya jiyi maki, abinda na faɗa kenan na soke." "To saboda me na ga dai duk 'yan uwa ne da mahaifinta Munnir da ni Maihaifiyar Hafsat uwarmu ɗaya ubanmu ɗaya. To akan me ye za'a fasa?" "Kin ga ba dogon zance zan tsaya yi ba, ki maida hankali wajen tarbiyyar 'yarki da cusa mata aƙida mai kyau a cikin zuciyarta, duk da cewar kin makara a yanzu, dan itace tun yana ɗanye ake lanƙwasa shi, idan har kika bari ya bushe sannan kika ce zaki lanƙwasa shi ba zai lanƙwasu ba sai dai ya karye, kuma ni ba zan iya bari ta zama uwar jikokina ba dan ban ga tarbiyyar da za ta iya bawa 'ya'yanta ba, tukunnah ma dai shin kin san Hafsat tana shaye-shaye?" Taɓe baki ta yi tare da cewa. "Wai haka na ji Munnir ya faɗa mani a baya,sai dai ban ɗauka da gaske ba ne, ba wani shaye-shaye da take sharrin mutane ne." Murmushin takaici ya yi tare da cewa. "Gaskiya kina ganin kamar soyayya kike babbar maƙiyiyarta ba so nunawa Hafsat to kece ke ƙara lalata ta. Da kaina na kawo ta gidan nan jiya tana cikin maye, zancen aure babu dan Munnir, ya je ya nemi yarinya mai tarbiyya ya aura." Mama ta kalli Mum tare da cewa. "Kina jin abinda mijinki ke faɗa ko? Yanzu ya dace ya mani haka ina jininki?" Sanin halin Dad da Mama ta yi yanzu ne ya saka ta cewa. "Yanzu Dad ɗin Munnir ka duba wannan..." Tashi ya yi ta bar masu falon, Kallonta Mama ta yi tare da cewa. "Lallai Yaya kin yi sanyi da yawa, yaushe kika yi saken da har Dad ɗin Munnir ya fi karfinki? Ke da a baya duk abinda kika faɗa ta zauna yanzu kin daina juya shi sai shi ne yake juya ki?" Lallai Yaya kin yi barci." Shiru kawai ta yi ta kasa cewa komai, dan ita ma yanzu lamarinsa mamaki yake ba ta. "Yaya wallahi idan Hafsat ta ji labarin fasa auren." "Kar ki damu komai zai daidaita, sallama ta mata ta koma gida. A hanyar ta ta komawa gida mamaki take yadda Dad yake magana amma Mum ta kasa dakatar da shi kamar yadda ta saba a baya, ina ikon nata yake? Gaskiya ta yi barci c yawa dan su namiji bai isa ya yanke hukunci ba sai abinda suka ce, dan haka ta sakawa ranar cewa auren Munnir da Hafsa ba makawa sai anyi shi. Ammi ta saka an kwaso duka kayan Amatullah da na Baby an dawo da su ɓangaren da suke, ɗakin Amatullah na kusa da ɗakin Nihal. Haka rayuwa ta canza gaba da tafiya daidai Ajmal ta janye zancen takatarsa, sai dai har yanzu bai daina bada tauna da tallafi ga marasa shi kamar yadda ya saba ba, amma zancen takara sam ya ce ya janye, duk da cewar abokin mahaifinsa tsohon Gwamnan bai so hakan ba, dan ya kira Ajmal a waya nan Ajmal ke faɗa masa shawarar da ya yanke. A gefe ɗaya kuma Ajmal ya sakawa jami'an tsaro ƙahon zuƙa akan lallai sai sun kama Hafsat, dan shi a yanzu bai da babban burin da ya wuce a ce an kama Ko wace ce, sai dai ya lura da abu ɗaya idan ya tambayi Amatullah akan maganar da da dukkan alamar ba zata rasa sanin wace ce ba tunda har ta bada aiki akanta, kenan ta san wace ce sai dai ya yarda cewa ba ta zargin kowa koma wace ce. Ganin yadda Ajamal ya damu ne ya sa DPO ya ƙara tsananta bincike, dan tunda ranar da abin ya faru ba su samu ganin fuskar wacce ta bada aikin ba sai dai ko ba ranar ba tana zuwa hotel ɗin, idan aka cigaba da bibuya za'a iya ganinta cikin mutane da suke hada-hadar zuwa wajen. Hakan kuwa aka yi lokacin da Inda DPO ya saka aka fara binciken cctv camera. Ana nuna mutane dake wucewa tare da zuƙo fusakarsu ko Allah zai saka INDAKUƊINKA ya ga wacce ta saka shi wannan aiki. INDAKUƊINKA ya zuba idanu kuwa inda yake duba fuskokin matan da ke wajen suna shige da fice. Cikin ikon Allah sai suka ga shi sun ji INDAKUƊINKA ya ce. "Ga ta nan." Sake zuƙo wa dan ya tabbatar abinda yake faɗa. "Tabbas ita ce wannan ita ce matar." Ita da Nafeesat ne biyu ne suna jerawa zuwa shiga hotel ɗin. Ɗaya daga cikinsu cikinsu ne ya ce, "To ai ita wannan ɗayar na sanya sosai." "Wa ka sani daga ciki, ita wacce ake zargi ko kawarta?" Manajan Hotel ɗin ne ya yi maganar. "A'a ƙawarta dai dan kullum da da yamma tana cikin hotel ɗin nan, duk yammaci sai ta shigo wata rana ana take kwana." "Okay to abinda nake so da ku idan har ta shigo za mu kira ku a waya mu sanar da ku." Manajan ne ya yi maganar yana kallon Jami'an tsaron, inda inspector ya lalle shi ya ce. "Za mu bar sergeant ya zauna a nan har zuwa yammaci, zai kasance cikin shigar farin kaya dan kada jama'a su fara tunanin wani abu ne ya faru." Jinjina kai Manajan ya yi tare da cewa. "Shikenan yallaɓai." Godiya suka masu tare da sallama suka tafi, bayan DPO ya tabbatar da cewa ya samu hotunan Hafsat a wayarsa, sannan ya kira sergeant a waya ya sanar da shi aikin da zai yi. Amatullah ce a cikin kitchen ta ɗauko caton ɗin robar ruwa,dan ba ta shan ruwa mai sanyi na fridge, shi ne Amma ta sanar da ita cewa akwai a kitchen ra ɗauko ta kawo ɗaki ta ajiye tana sha. Nihal ce ta shigo kitchen ɗin daidai lokacin da Amatullah ke ƙoƙarin fita, kallonata ta yi daga sama har ƙasa kafin ta ce. "Ina za ki kai ruwan nan?" Kamar ba za ta amsa mata ba sai kuma ta ce "Ɗakina." "Na tambaye ki mana shin a gidanku wani irin ruwa kike sha?" Kallonta Amatullah ta yi na wasu sakanni mafin ta bata amsa ne Nihal din ta ƙara cewa . "No ka da ki damu tambaya ce kawai na yi ba da wani nufi ba." Amatullah ba ta ce mata komai ba sai ƙoƙarin fita daga kitchen ɗin da take yi. Jin muryar Nihal ce ta dakatar da ita . "Dole ki zauna mana kin samu ɗaula da jin daɗi, babu a house an baro gaban tsohon mai dattin hula da..." Tsawan da Amatullah ta daka mata ne ya ya saka ta yin shiru tsananin ɓacin rai ta gani a kan fuskar Amatullah, dan sai da ta tsorata. "Dakata Nihal duk abinda za ki yi ki tsaya a iya ni, ka da ki taɓa cewa za ki ci mutuncin iyayena, dan idan har kika jaraba yin hakan za ki ga ɓacin raina, zan iya shanye komai amma ban da taɓa mani iyayena. Suna da matukar mutun..." Kafin ta ƙarasa Nihal ta faɗa ce mata. "Mutunci da kike ƙoƙarin cewa ko? To ina talaka ya ga mutunci ai babu girma ba mutunci ga talaka, 'yar matsiyata kawai dan kin..." Saukar marin da ta ji ne ya saka ta dakatawa tare da dafe ƙuncinta. Kallon Amatullah da mamaki take yadda ta iya ɗaya hannu ta mare ta. Ɗaga hannu ta yi da niyyar ranawa sai Amatullah ta riƙe hannun tare da cewa. "Ka da ki yi wannan ganganicin, dan na faɗa maki duk wulaƙanci da za ki Mani zan jure, amma ka da ki saka iyayensu dab wallahi ba wanda ya isa ya ce zai zage su ko wulakanta su na ƙyale shi, dan haka ki kiyaye ni." Ta ƙarasa maganar cike da gargaɗi, sannan ta saki hannun Nihal ruwan da ta dauko ma nan ta barshi bakin Kofar kitchen ɗin ta nufi ɗakinta. Baƙin ciki ne ya turnike Nihal dan ta rasa me za ta yiwa Amatullah, dan ko riƙon da ta yi wa hannunta ta kasa ƙwacewa har sai da Amatullah ta ga dama ta saki hannun. Amatullah na shiga ɗaki ta ta fara haɗa kayanta tana shirin barin gidan, dan ta san ƙarshen zamanta a gidan ya zo tunda har ta daga gannu ta mari 'yar masu gida. Ita ta dauka cewa Nihal Ammi ce ta haife ta, dan haka take shirya kayansa dan ta bar gidan kafin masu gidan su Kore ta da kansu, gara ta koma ta cigaba da rayuwar titi akan ta zauna idan za'a ci mutuncin ya da iyayenta. Harhaɗa kayanta take yi da na babyn a cikin babbar haka, duk da ba ta da kuɗi amma ta san cewa za ta koma irin rayuwar da ta yi da ciki ne na kunci da yunwa ta koma sai ta roki abinda za ta ci, amma a ganinta ya fiye mata kwanciyar hankali tunda ba wanda zai tozarta ta. Duk da ta san lokacin ita kadai ne ta jure yunwa rana da iska da ruwa, ga matsalar wajen kwana daga kango sai ajin yara 'yan makaranta da yake ke kwana, yanzu ga jariri ya za ta yi da shi? Kallon yaron take cike da tausayinsa. Hafsat ce ta fito daga cikin ɗakinta ta samu Mamanta a falo sai Safa da marwa take yi, Kallonta ta yi tare da cewa. "Mama lafiya kike cikin damuwa?" "Hafsat idan kin ji abinda ke faruwa wallahi sai kin fi Ni shiga cikin damuwa." "Me ya faru Mama?" Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa. "Dad d'in Munnir ne ya ce an fasa aurenki da Munnir." Gabanta ne ya yi mummunar faɗuwa inda ta ji ƙafarta ba za su iya ɗaukar ta ba, dan haka ta zube a wajen tana kuka. Mama ba ta hana ta ba sai da ta yi mai isarta sannan ta koma ɗalibta ta ɗauki dogon hijab ta saka, sannan ta dauki Makulkin motarta ta bar ɗakin. Mama na tamyarta ina za ta je amma ina ba ta amsa mata ba, ta fice. Horn ta yi maigadin ya bude mata gate ta nufi University da Munnir yake aiki. Office d'insa ta nufa ba ta ciki a kulle ta ga office ɗin, tamabayar wani ta yi ya sanar da ta ita cewa sir Munnir yana koyar da lecture yanzu, ta tamabaye shi ya kwatanta mata wajen. Yana tsaye yana koyarwa sai ya ji muryar Hafsat daga waje tana cewa. "Ina son Magama da kai." Mamaki yake zuwannta nan ne ya sa ba za ta kira shi a waya ba. Ga shi gaba ɗaya ɗaliban nasa shi suke kallo, idan ya share Hafsat za ta iya tara masa jama'a shi kuma ba zai so hakan ba, dan haka ya ce ta jira shi a waje. Fita ta yi tana ta safa da marwa tana jiransa, kasancewar lokacin fitarsa ya yi ne ya sa ya fito, ya nufi office ɗin sa tana biye da shi a a baya. Suna shiga ciki ta fashe da kuka tare da nufarsa da niyyar rungumarsa ya ja da baya, dakatar da ita ya yi ta hanyar daka masa tsawa. "Dakata! Me ye haka?" Kuka ta saka masa ba tare da ta yi magana ba, ganin ba ta da niyyar cewa komai ne ya saka shi cewa. "Idan har ba ki da niyyar magana zan fita na baki waje, dan ina da abun yi kin gane ko?" Cikin kuka ta fara magana tana cewa. "Dan Allah Ya Munnir ka da ka bari Dad ya raba mu, wallahi ina sonka, kuma zan bi duk abinda kake so, ko da na bana son abun zan koyawa kaina son abun ko mene ne." "Hafsat a gaskiya ko da Dad bai yi haka ba nima ba zan iya aurenki ba, na faɗa maki tun a baya ba ki ɗauki maganar serious ba saboda kina taƙama da Mum, ita kuma Mum a ƙarƙashin Dad take dole ta yi biyayya ga duk abinda ya faɗa." "Munnir idan ba ka aure ni ba ba zan taba barin ka ka auri wata mace ba, idan kuma ka ce ƙarya ne bisimillah mu zuba mu gani." Fita ta yi daga affice ɗin kamar za ta tashi sama, bin bayanta ya yi da kallo tare da taɓe baki. Driving take yi tana kuka, yayin da take ta zuba gudu a saman titi zuciyarta na mata zugi Idanunta na zubar da hawaye, tsanar Dad ne ya ɗarsu a cikin zuciyarta, magana take yi a cikin ranta. "Hmm lallai idan har ban samu abinda nake so ba wanda zai same shi, Dad dan ka ga Mahaifina ba ya raye ne ko? To zan aikata abinda ba zai maka daɗi ba." Wayarta ce ta yi ruri juyawa ta yi ta kalli wayar ganin Nafeesat ke kira ya sa ta ɗaga wayar ta kara a kunnenta. *Daga alƙamin*✍️ Zainab Abdullahi KNT (Maman Ihsan) 09065327995 Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z 🤦‍♀️ *'YAR MAYE*🤦‍♀️ (_The drug abuser_) *NA* Zainab Abdullahi KNT (Maman Ihsan) https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *GARGAƊI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. Ban yarda a karanta mani shi a youtube ko a maida shi audio ba tare da izinina ba. *BISIMILLAHI RAHMANI RAHIM* Page6️⃣2️⃣ Wayarta ce ta yi ruri ta juya ta kalli wayar, ganin Nafeesat ce ke kiran wayar ya sa ta ɗaga wayar tare da karawa a kunnenta. "Hello ƙawata ina zuwa zan kira ki anijima akwai magana da nake so mu tattauna akai." Daga can ɓangaren Nafeesat dake fitowa daga gidanta ne waya kare a kunnenta ta ce. "Okay ina jiran kiran naki dan nima yanzu zan shiga club ba zan bari sai dare ba." "Okay." Hafsat ta faɗa tare da kara wayar a kunnenta. Amatullah gaba ɗaya ta gama haɗa kayanta na barin gidan, sai ta giya Abdallah a bayanta, dogon hijab ta dauka ta saka sannan ta janyo akwatin da ta zuba kayansu. Ajmal na zaune a bedroom ɗinsa na'ura mai ƙwaƙwalwa ne a gabansa, bayan waya yake yi da Dr Fu'ad kamar an ce ya kalli na'urar sai ya ga Amatullah ta tana jan akwatin kaya. Tsayawa ta yi tana dube-dube da ta tabbatar ba kowa a falon sai ta fara sanɗa a hankali ta fice daga falon. Wayarsa ya ɗauka ya kira security dake kula da ƙofar ya basu umarnin cewa ka da su bari Amatullah ta fita daga gidan nan. Sannan ya kara jaddada masu cewa ki ba yau ba ka da su bari ta fita sai tare da izininsa, sai ta kira su ya basu dama sannan ta fita ko da ba ita kadai ba ce tare da wasu ne fitar. Sannan ya katse kiran wayar yana mamakin me zai saka ta guduwa. Amatullah tana zuwa bakin gate ɗin ta kalli security ta ce. "Dan Allah ku buɗe mani ƙofa zan tafi." Kamar duwatsu haka suka yi ba wanda ya motsa ballantana ya kalle ta. Ganin haka ya saka ta nufar ƙofar gate ɗin suna kallonta amma sai ta kasa budewa. Jiyowa ta yi ta lalle su ranta a bace ta ce Na ce ku buɗe mani kofa kun share ni kamar ba da ku nake ba. Wani mai baƙin kaya da baƙin glass ne ya dodo ta fuskarsa a murtuƙe, kallinta ta yi tare da cewa. "Go back" Ganin alamar ba barinta fita za su yi ba ya saka ta waige-waige ki za ta hangi Ahmad. Can kuwa ta hangi shi yana waya, haɗa Idanu suka yi ya sakar mata murmushi. Itama mai da masa da martani ta yi, ganin ta da akwatin kaya ya saka shi tasowa ya nufi bakin gate ɗin. "Ya Ahmad ina wuni?" Bai amsa ba sai tambayar ta da ya yi. "Ya na ganki da jaka ina zuwa haka?" "Gida zan koma." "Kin yi sallama da mutanen gidan ne?" Sunkuyar da kai ta yi daya daga cikin security ya yiwa Ahmad maganar cewa Boss ne ya hana a bari ta fita. Da ido suka yi magana dan Amatullah ba ta san me ke faruwa ba. Ahmad ya kalle ta tare da cewa. "Ki yi hakuri ki koma dan ba za su bari ki fita ba sai da izinin masu gidan." Gabanta ne ya faɗi tana tuna me zai biyo baya, tana tsaka da tunanin ne ta ji Ahmad na cewa. "Mu je ko?" Kallonsa ta yi ta ga har ya ja akwatinta ta nufi komawa cikin gidan. Tsayawa ya yi tare da juyowa ya kalle ta tare da cewa. "Ki taho mana." Ƙarasawa ta yi kusa da shi ta ce. "Na san kora ta za su yi ina gudun abinda ka iya je ya dawo." "Ban gane me kike son cewa ba." "Na mari ƴar masu gida dole na bar masu gida." "Wa kika mara?" "Nihal ce ta za yi iyayena na ga ba zan iya jurewa ba shi ne na mare ta." Shiru ya yi tare da zuba mata Idanu kafin ya ce. "Ka da ki damu." "Ƴar masu guda fa na mara." "Nihal ba ƴar gidan nan ba ce, ƴar ƙanwar Dad ce ta zo ne daga Adamawa." Shiru ta yi na dan lokaci kafin ta ce. "Duk da haka ban san ne zai je ya dawo ba." Ka da ki damu ba abinda zai faru, dan ko Ammi idan ta ji abinda ta maki za ta mata faɗa ne." Daga nan bai sake magana ba ya yi gaba tana biye da shi a baya. Suna shiga falon ya ajiye mata akwatin kayan sai ta ji yana cewa. "Barka da warhaka yallaɓai." Amatullah dai ba ta ga kowa ba ta ji Ahmad na gaida mutum, sai da ta lura da inda yake kallo sannan ta hango Ajmal a saman upstairs ya rungume hannayensa a kafada yana kallonta. Ahmad ne ya fita ita kuma ta ja akwati zuwa ɗakinta. Tana shiga ta ajiye akwatin kayanta, ne ta cire hijabinta, kwantar da Abdallah ta yi akan gado. Juyowa da ta yi ta gan shi a gabanta, fusakarsa babu walwala. "Ina kika yi niyyar zuwa kuma me ye dalilin guduwarki?" "Ni fa..." Kasa ƙarasa maganar ta yi sakamakon cikin idanunsa da ta kalla, tsabar kwarjininnsa ne ya sa ta kasa cewa komai. "An yi maki wani abu ne?" Kai ta girgiza alamar a'a sannan ya ce. "To dan Allah ka da ki sake tunanin tafiya ki jira lokaci nan ba da dadewa ba za ki ganki a gaban iyayenki." Gyaɗa masa kai kawai ta yi kanta a sunkuye tana wasa da yatsun hannunta. Wayarsa ce ta yi ruri daga cikin aljihunsa, cirowa ya yi ya duba inda ya ga DPO ne ke kiransa. Picking ya yi tare da yin sallama. "Hello Assalamu alaikum." Daga can ɓangaren DPO da ke zaune a ofishin sa waya na kare a kunnensa

Chapter 23 of 51