Share this page
kanta cike da soyayyar ta yake kallonta, zama ta yi a gefensa cikin sanyin murya ta gaishe shi, ya amsa masa cike da kulawa. "Ya su Umma?" "Suna lafiya lau Alhamdulillah." "To ya gajiyan tafiya?" "Alhamdulillah." Ta fad'a kanta a sunkuye tana wasa da yatsun hannunta." ",To Dan Allah Amatullah duk abunda ya faru kada ki sake nisantar da kanki daga gare mu, domin muna da bukatar ki a kusa da mu." "In Sha Allah." Suna tsaka da fira ne ta ji wayarta na ruri, ganin Umma ce ya sa ta Kalli Munnir tare da cewa. "Bari na shiga ciki ban San dalilin da yasa Umma ke kira na ba " "Okay." Ya ce yana binta da idanu dan ta ji yadda idanunsa ke yawo a jikinta, sai da ta bacewa ganinsa ya saki ajiyayar zuciya. Tun kafin ta k'arasa ta ji kukan Abdallah ya karade tsakar gidan, da alama ya Farka daga barci ne, ko da ta shiga cikin d'akin ta tarar da Ummanta na bashi abincisa amma bai karba ba sai kuka yake yi da alama nono yake so. Tana shiga Umma ta mika mata shi ta ce. "Ki bashi ya Sha na hada masa kununsa bai Sha ba." Zama ta yi ta fara bashi nonon take ya yi shiru ya fara Sha Sai kusan mintuna ashirin sannan ya koma barci ta kwantar da shi Saman gadon ta fita ta koma wajen Munnir bayan ta mayar da hijabin da ta cire. Da sallama ta k'arasa wajansa ya amsa yana kallonta fusakarsa da murmushi ya ce. "Lafiya dai ko?" Murmushin ta maida masa martanin bayan ta zauna gefensa ta ce. "Lafiya lau baby ne ya Farka yana kuka." Sai yanayin fuskarsa ya sauya dan duk lokacin da ya tuna cewa tana da yaro sai ya ji ba dad'i a cikin zuciyarsa. Tunawa da ya yi da cewa da zai shigo ya ga wata sabuwar mota a k'ofar gidan. Bayan ya kalle ta ya ce. "Yauwa motar waye na gani a k'ofar gidan nan ko Kuna da bak'i ne a cikin gidan?" Shiru ta yi zuwa can ta ce. "Ba kowa mu kadai ne kamar yadda ka sani." "To motar ce ya kawo kanta?" Kanta a sunkuye ta ce. "Shine ya kawo mani wai idan zan..." Bai bari ta k'arasa maganar da za ta yi ba ya ce. "Shi waye ya kawo maki?" Ganin yadda take yanayain fusakarsa ya sauya da alama ransa ya baci ya sa ta yi shiru ba ta Tanka masa ba. Ganin ba ta da niyyar magana ne ya saka shi cewa. "Magana nake maki." "Baban baby ne ya kawo mani ita Kuma...." ",Dakata Amatullah ban gane me kike nufi ba, ina kika ajiye zancen auren da zamu yi ne? Kin San cewa akwai zancen aure tsakanina da ke kafin ki tafi, bayan kin dawo ya kamata ki ajiye duk wani da namiji ki fitar da shi ki mance da shi ki fudkanci sabuwar rayuwar da zamu yi." Nisawa ta yi tare da cewa. Na fahimce k ka Munnir sai dai ya kamata ka sani mancewa da Ajmal daga cikin rayuwa ya wani abu ne Mai kamar wahala, ba don komai ba ko don dan akwai zuri'a tsakani da shi ta Yaya zan iya mancewa da uban d'ana? Idan har kuwa zan iya mancewa da Ajmal to shima d'an da na haifa dole na mance da shi, kana ganin Hakan zai iya yiwuwa kuwa?" Ta k'arasa maganar tana kallonsa, shima ita yake Kallo fuskarsa ba annuri. "Ba zan iya cewa ki mance da shi ba amma ya kamata ki yanke duk wata alakar dake tsakani ki da shi,bayan alakar cewa shi uban danki ne, Kuma duk wata kyauta ko wani ziyara ba wannan a tsakaninki da shi, ba don komai ba sai don aure za ki yi Kuma Wanda zai aure ki ba zai juri ganin kina mu'amala da wani namijin ba, sannan ki mayar masa da makullin motar da ya baki ya d'auki motarsa." "Ni dama fa ban karba ba hasalima ko da ya bani ban karba ba ashe ya boye ne a jikin rigar baby sai bayan ya bar k'asar sannan na sani. Kuma yanzu ma baya k'asar Yana can ya tafi k'asar Germany. Duk da a waya na sanar da shi bana so ya ce wai yaronsa ya siyawa bayan son na dinga masa yawo da yaro cikin rana." Tana gama magana ne sai ta ga Kiran Ajmal ya kira ta video call. Kamar ba za ta daga ba har sai da Kiran ya kusa katsewa ta d'aga. Kyawawan fuskarsa ta yi araba da shi akan screen din wayarta, sanar yake da kananun kaya ya zuba mata fararen kyawawan idanunsa masu cike da kwarjini. Kasancewar shi ba mutum Mai yawan murmushi ba ne ko dariya amma fuskarsa a sake take da alama ya jy farin ciki da ganin ta. "Sarauniyata ya kike?" Cikin sanyin muryarta tare da shakkar Munnir ta ce. "Ina wuni." Ya amsa mata da "lafiya lau ya kuke?" "Alhamdulillah." Munnir ne ya tashi fa niyyar tafiya dan ji yake zuciyarsa na masa zafi, tashin da yazo yi ne kasancewar ta bayanta ya zagaya Hakan ya saka Ajmal ya gan shi. Take shima yanayinsa ya sauya sai dai kasancewar shi mutum ne da ba kowa ne ke iya karantar yanayinsa ba ya da ba ta ga canji a wirinsa ba, sai dai kawai ta ga ya kashe wayar. Zuwa lokacin kk har Munnir ya nufi wajen motarsa zai shiga kenan ya juyo Jin takun tafiyarta, juyawa ya yi suka yi Ido biyu ta k'arasa wajansa. "Har za ka tafi ne?" "Eh." Ya amsa mata a takaice. ",Shine ko sallama babu?" "Na ga gaba d'aya hankalinki ba damunsa zan yi yadda nake so ba, da farko yaro ya fara kuka kin tashi kin tafi kin barni a zaune, tsawon mintuna ina jira, kina dawowa Kuma sai ga uban yaron ya kira ki nan ma so kike na sake bata wani lokacin ina jira kamar mara abun yi?" Daga nan bai sake wata wata maganar ba ya shige cikin motarsa ya ja tare da barin k'ofar gidan. Komawa ta yi cikin sanyin jiki Dan ita ba ta San yadda Munnir ke so ta yi da shi ba. Abba ne ya dawo sai da ya tsaya daga waje ya karewa motar nan Kallo sannan ya bar wajen ya shiga gidan. Kwalawa Amatullah kira ya yi ta fito tambayarta ya yi motar waye tun jiya take k'ofar gidan. Nan ta sanar da su yadda suka yi da Ajmal akan motar, shima Abba bai goyi bayan ta karbi motar ba Dan haka da motar da ATM card din ya ce ta ajiye dan ga alkawarin aurenta da ya yi wa Munnir bai kamata ace tana cin kudin wani saurayin ba. *ADAMAWA* Nihal ce ta fito daga cikin d'akin mahaifiyarta Hajiya Laila, Kallo d'aya Hajiya Laila ta yi wa Nihal ta saki tsuki tare da cewa "Wai ke har yanzu ba Zaki saukakawa kanki akan Ajmal ba ko shi kadai ne namiji a duniyar nan, kin tashi kin keashi jiki kin koma Kaduna a tunanina ziyara kika tafi ashe ke ba haka saboda soyayyar Ajmal kika tafi, yanzu kin dawo kina ta ta kuka ba cin abinci kirki sai tunani gabadaya na saka gane kanki, to gara ma ki cirewa kanki damuwa idan ba ya son ki ba dole sai ki fita harkarsa. Kukar Nihal ne ya karo ta fara magana . "Wallahi shi kadai nake dj shi zan aura idan har ba same shi ba sai dai ayi uwar watsi kowa ta rasa. Da mamaki mahifinyarta ta kalle ta tare da cewa "Ban gane me kike nufi ba." "Mamy wallahi ba zan barj ya auri Amatullah ba sai dai kowa ta rasa idan ban same shi ba ita ma haka." Ta k'arasa maganar tana fashewa da kuka Mamy ta janyo ta ta rungume ta tana bubbuga bayanta alamar rarrashi, tambayarta ta yi tare da cewa. "Wace ce Amatullah, bayan matarsa Nasreen yana da wata mata ce?" "Mamy wata karuwa ce ta zo da jaririn gidan wai Ajmal ne ya mata ciki ta haihu, shine Amminsa ta bata masauki suka dinga renon yaron har wurin mahaifiyarta can k'asar Qatar duka tafi tare shi ya sa nima na bar gidan wallahi Mamy ina son sa." Shiru Hajiya Laila ta yi tare da cewa. "Kada ki damu ki je ki sanarwa Marka ita kadai ce na San za ta maki maganain matsalarki." Goge hawaye ta yi ta d'auki mayafinta da key din motar ta nufi gidan kakarsu Hajiya Marka. Waya Mamy ta d'auka ta kira yayanta a waya wato Dad din Ajmal, bugu niyu ya d'aga tare da cewa. "Hello Laila ya kike?" , "Yaya ba lafiya fa 'yarka Nihal tun bayan da ta dawo." Subahanalilahi me ya faru, bari na k'arasa gidan sai muyi magana. Bi tashar TASKAR MAMAN IHSAN a WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z 🤦‍♀️ *YAR MAYE*🤦‍♀️ (_The drug abuser_) Page7️⃣9️⃣ "Subahanalilahi me ya faru, bari na k'arasa gidan sai muyi magana." Kasa karasawa gidan ya yi dan haka kawai ya ji hankalinsa bai kwanta ba, lalubo lambar Mamy ya yi ya dannan mata kira, ba bugu d'aya ta daga ba tare da ta ce komai ba, can sai ta ji sallamar Dad cikin wayar, ta amsa masa rai a bace. ",Laila lafiya meke faruwa ne?" "Yanzu Yaya za ka ce baka San me ke faruwa a cikin gidanka ba, mu biyi muka ragewa wa mahaifiyarmu tunda shi wancan ta sallamawa duniya shi baya daga cikin mu yanzu..." Katse ta ya yi ta hanayar cewa "Fadi maganar ki kai tsaye Laila." Dan har ga Allah ba ya son ana tayar da maganar d'an uwan nasu zuciyarsa zafi take masa. "Yaya kasan cewa zuwan da Nihal ta yi Kaduna ta yi ta zama a gidanka gabannin dawowar Ajmal ba haka kawai bane?" Cikin rashin gane inda zancenta ya dosa ya ce. "Ban gane me kike nufi ba har yanzu akwai wata alakar ce a tsakaninsu?" "Yaya Nihal tana tsananin son Ajmal sosai Hakan ya saka ta je gidan yadda zasu shaku da juna ko Allah zai za su daidaita kansu kaga ai mu abun farin ciki ne a wajen mu, ko ba komai ai an sake kulla dankon zumunci." Shiru ya yi tare da nisawa kafin ya ce. "Wannan ai ba wata matsala ba ce idan har sun daidaita kansu Kuma sun amince suna son junansu ai ba wata matsala." D'an Jim ta yi kafin ta ce. "Yaya na ji labarin wata yarinyar wai har da d'a a tsakaninsu ta Yaya hakan ta faru?" "Okay Amatullah kenan wato abun ne ya zo muna muma a rudu kafin aka samo bakin zaren, nan ya sanar da ita a takaice haduwar Amatullah da Ajmal a hotel da yadda komai ya faru har dawowarta gidan duk ya sanar da ita, daga karshe Kuma ya sanar da ita maida ta gidan iyayenta da suka yi da yadda Ammi ta kawo shawarar a nema masa aurenta, amma ya ce kafin nan sai an ji daga bakin shi da yarinyar idan sun..." Ta yi saurin katse shi da cewa "Haba Yaya idan sun shirya kansu akan me, ga yar uwarsa tana masifar sonsa kamar za ta mutu shine kake zancen wata, wa ma ya sani ko da hadin bakinta ta saka shi ya fad'a tarkonta dan saboda son dukiya." Daidai lokacin da direban sa ya yi horn Maigadi ya bude masa gate din ya shiga, Dad dai sallama ya mata tare da katse Kiran wayar da niyyar anjima zai kira ta. Wata dattijuwar mata ce Mai kimanin shekaru saba'in a duniya ta fito daga cikin bedroom d'in ta, d'aya daga cikin kujerun dake falon ta zauna yayin ta mai aikinta ta fito daga cikin kitchen hannunta rike da tire da aka jera breakfast a ciki, durkusawa ta yi gaban matar bayan ta ajiye tire din Saman center table dake falon. Kofi ta d'auka tana kokarin hada mata shayi sai suka ji an turo k'ofar da shigowa falon da karfi, gaba d'aya suka juya da sauri suna kallon mai shigowa, Nihal ce ta shigo a guje, kan Tsohuwar matar ta nufa tare da durkusawa a gabanta ta kwantar da kanta a saman cinyarta tana kuka. Cikin tashin hankali ta janyo ta ta zaunar da ita kusa da ita bayan ta rungume ta ta ce. "Nihal lafiya kuwa me ya faru?" "Marka wallahi ba zan iya jurewa ba za ki iya rasa ni matukar ban same shi ba." "Waye ne kike magana akansa?" "Ya Ajmal." Da sauri Marka ta kalle ta Jin sunan da ta ambata ya ba ta mamaki. Bangaren Amatullah kuwa ta damu da rashin Kiran da Ajmal bai mata ba, tana zaune a tsakar gidan ta gaji da zama ta koma d'akinta zama ta yi kan katifarta zancen Abba ne ke mata yawo a kwakwalwarta na cewa ya yi wa Munnir alkawarin aurenta, tabbas ta san tun kafin wanan tsautsayin ya afka mata ta san Munnir ke zuwa wajenta kasancewar Abbanta ya yarda da shi, Hakan ya saka ko da zo ya sanarwa Abba ya ga Amatullah yana son zan aure ta sai Abba ya ga gurmansa kai tsaye ya bashi izinin ya dinga zuwa zance wajenta, daga nan ya fara zuwa Kuma duk lokacin da zai zo iyaka ya fad'a mata abunda ke ransa na soyayyar da yake mata,amma ko sau daya bai tambaye ta cewa ta amince tana son sa ko ba ta son sa ba, Kuma ita ba ta nuna masa wani yanayin na rashin so ba, saboda Abbanta ya amince da shi, shim kanshi Abban bai tana tambayar ta ko tana son Munnir ko ba ta son sa ba. Sai dai abu guda ta sani ba ta taba Jin ta tsani Munnir ba Kuma ba ta taba damuwa da shi ba ko yawan tuaninsa ko mafarkinsa ba, sai dai abunda ke ba ta mamaki yadda tafiyar Ajmal kwana biyu kenan amma gaba d'aya tunaninnsa ya addabe ta, dan jiya daddare ma har mafarkinsa ta yi ba ta San dalilin ba, ko ta yi yunkurin cire shi daga zuciyarta Sam ta kasa. Bangaren Munnir na abun duniya ya ishe shi, gaba d'aya ya rasa yadda zai bullowa lamarin, ya d'auka idan Allah ya sa Amatullah ta dawo gaban iyayenta komai ya kare ba wata matsala dan bai yi tunanin cewa za Amatullah za ta dawo da babyn da ta haifa ba, ya d'auka can za ta barshi ko wajen ubansa ko gidan marayu, amma abun mamaki sai ta dawo da shi a hannu kuka iyayenta suka karbe su sannan ga uban yaron yana neman kawo masa cikas a rayuwarsa sai wani gata yake nunawa yaron kamar d'an Sunna da aka haifa ta hanyar halal. Mutane suna yi wa mace ciki sun gama da su kenan sai dai su gudu su barsu ba zasu yarda a alakanta su da yaron ba saboda zubewar mutuncinsu amma shi wannan ya ga alamar baya ya bawa kunya ba gaba ba. Tsuki ya yi tare da gyara kwanciyarsa yana ta tunanin hanyar bi. Turo k'ofar d'akin nasa aka yi da sallama, Mom d'insa ce fuskarta a tsuke , dan har yanzu tana nan akan bakanta sai ya auri Hafsat. Tashi zaune yayi tare da zuba mata idanu ya ce. "Mom barka da rana." Ba ta amsa masa ba ta kalle shi ta ce. "Ya zancen mu?" "Wani zance Kuma Mom?" "Ka fini sani ai." Ta yi maganar tana hararsa, kallonta ya yi kafin ya kau da kansa ya ce. ",Mom ai na d'auka mun wuce wannan wajen, Dady ma ya yanke hukunci ya ce ba zan taba auren 'yar shaye-shaye ba, Mom wallahi ba zan iya auren Hafsat ba ke kanki idan kina son jikokinki su samu tarbiya me kyau ba za ki so a ce na auri wann..." Dakatar da shi ta yi ta hanyar daka masa tsawa sannan ta ce. "To bari ka ji sanin kanta ne da ni da mahaifiyar yarinyar nan uwa d'aya uba daya muke, Kuma dole ka aure ta." "Mom ba zan ce zan tsallake maganar ki ba, amma matukar kika aura mani Hafsat wallahi zan aikata abunda ba zai yiwa kowa dad'i ba nadama ne zai biyo baya." Baki ta saki tana kallonsa da mamakin Jin kalamansa. Marka ce ta sake kallon Nihal dake kuka ta ce. "Shi Ajmal din ya San kina son sa?" Gyada kai ta yi tare da share hawayen dake fuskarta ta ce. "Ya sani Ammi amma sai yake sharewa kamar bai gane be." "Yanzu ya kike so ayi?" "Tunda ke kika haifi Dad Kuma Dad din mahaifinsa ne sai ki bawa Dad umarnin cewa ya saka Ajmal ya aure ni tunda shima ba zai bijirewa umarnin mahaifinsa ba." Nisawa Marka ta yi tare da cewa. "Anya za ki iya zama da wannan mutum Mai murd'ad'd'en halin? Mutumin da baya wasa da dariya kullun fuska a tsuke ga mishkilancin tsiya, ko macen da yake so ai sai ta yi hak'uri da shi ballantana wacce ya so, kina ganin ko nan ya zo idan ina jansa da wasan kaka da jika ina masa surutu ko biye ni bayan yi ballany dariya sai ma ya dinga danne-danne a wayarsa idan na dame shi ma daj ya tashi ya fita wai baya son hayaniya." Kuka Nihal ta sake sakawa dakyar Marka ta rarrashi ta tare da cewa zata San yadda za ta yi akan lamarin. Tunani Marka ta yi dan ba wata kusanci a tsaknin ta da Ajmal dan kasancewar kasancewar Dad a can k'asar Qatar ya je ya auro Ammi balarabiyar Qasar ce, ta yarda ta biyo Dad Nigeria ko da ya kawo ta nan gidan Marka zaman kurame suke yi Dan Marka daga fulatanci sai hausa take ji, bata Jin turanci ko larabci balle suyi magana da Ammi sai dai idan kawai wani a kusa Ammi zata yi magana da turanci a fassarawa Marka. Har suka koma Kaduna Dan can Dad yake aiki. Bayan Ammi ta haifi Ajmal ya yi wato daj ya kadance rabin zamansa a wajen Amminsa rabin Kuma a can k'asar Qatar wajen Umma mahaifiyar Ammi Allah ya jarabeta da son Ajmal dan yaron Ammi ya dauko sak balarabe na za ka ce Dan Africa ba ne shi. Ko karatu a can ya yi idan ya zo Nigeria sai hutu Hakan ya saka bai shaku da dangin mahaifinsa ba, Dan ba wata shajuwa tsaninsu da Marka ko ya ce baya jimawa sai ya tafi. Nisawa Marka ta yi tana tunanin yadda zata yi da lamarin Nihal. Wata ranar Asabar Amatullah na zaune a tsakar gidan tana wanke wanke-wanke, sai ta ji k'amshin turarensa Wanda ya sa ta ji gabansa ya fad'i, dan k'amshin turarensa nada tasiri Wanda tun kafin ya k'araso wajen da zai zo turarensa zai Riga shi isowa. Kuma duk k'amshin turaren da jama'ar waje suka saka indai ya k'araso wajen sai kamshinsa ya doke nasu. Da sauri ta daga kai ta Kalli k'ofar shigowa gidan daidai lokacin da ya yi sallama ya shigo, kasa amsawa ta yi Umma dake fitowa daga d'akin ce ta amsa masa sallamar tare da masa sannu da zuwa tare da bashi zinin shigowa. A hankali ya ke takunsa cikin kasaita da mazantaka har ya k'araso inda Amatullah ke tsaye tana kallonsa tana mamakin yaushe ya shigo k'asar ko kiran ta a waya kwana biyu ya daina. Suna hada idanu da sauri ta janye idanunsa saboda kwarjinin dake cikin idanunsa masu rikita duk Wanda ya yi idanu buyu da shi. Durkusawa ya yi cike da gairmamawa ya gaida Umma, ta amsa masa itama cikin fara'a tare da tambayarsa ya su Ammi, ya amsa masu da suna lafiya. Kansa a sunkuye ba Wanda ya sake magana a cikinsu, Umma ce ta katse shirun da Kiran Amatullah ta ce ta kawo masa ruwa. Kasancewar cikin siyayyen da ya yi masu kafin ya tafi har da cartoon din ruwan gora ya sa ta nufi d'akinta, har lokacin Abdallah na barci, ruwa ta d'auka gora d'aya ta dora a tire ta d'auki Kofi ta hada ta fita waje. Har lokacin kansa a sunkuye daidai tana karasawa wajen Umma ta tashi ta basu waje. Zama ta yi suna fuskantar juna ta ajiye tiren sannan ta zuba masa ruwan a Kofi ta ajiye masa sannan ta kalle shi ta ce. "Ina wuni?" Ya d'aga kai ya kalle ta sannan ya amsa da " lafiya lau" "Ya su Ammi suna lafiya?" Kai kawai ya jinjina mata ba tare da ya yi magana ba, duk da ta San halin sa na rashin yawan magana amma ai wannan tambaya ce ta masa ya kamata ya bata amsa ba wai ya d'aga kai ba, dan haka ita ma ta share shi. Kallonta ya yi tare da cewa "Ina Khalifa yake?" Cikin rashin gane abunda yake nufi ya ta ce masa. "Waye Kuma Khalifa?" Kallonta ya yi kamar ba zai yi magana ba sai Kuma ya ce. "Ya sunan Babynki?" "Sunan Abbana ne da shi?" "To sunan kike kira ko Kuma kina kiransa da asalin sunansa ne?" "Baby nake kiransa." Ta bashi amsa idanunsa a kanta sannan ya ce "To ki dinga kiransa da Khalifa." Jinjina kai ta yi tare da cewa. "In Sha Allah." "Abba baya gidan ne?" "Eh ya fita." Tashi ya yi daga kan tabarmar ya saka takalminsa sannan ya ce. "Ki shiga d'akin ki dauko mani Khalifa ina cikin mota." Daga nan ya nufi hanyar fita ita ma ta nufi d'akinta inda ta tarar da Abdallah yana barci ta kalle shi tare da sakin murmushi ta ce. "Dad d'inka ya saka maka Khalifa zo na kai ka ka ganshi ya ganka." Tayi maganar bayan ta yi rolling kanta da mayafin abayar da ke jikinta Sanan ta d'auke shi suka fice. D'akin Umma ta shiga ta yi sallama ta sanar da ita yana waje za ta je ta kai masa Khalifa. Daga nan ta nufi k'ofar fita yana zaune cikin mota mazaunin direba ya lumshe idanunsa kamar Mai barci, bude murfin motar ta yi ta shiga tare da sallama. Ba ta ji muryarsa ya amsa ba sai dai ta ga labbansa ya motsa alamar ya amsa mata sallamar. "Bude idanunsa ya yi tare da sauke su akan Abdallah dake barci har lokacin, murmushi ya sanarwa yaron har dimple d'insa ya lotsa, cikin son yaron da kaunarsa ya mika hannu ya karbe shi tare da rungume shi a k'irjinsa. Tsayawa ta yi tana kallonsa yadda murmushi ke masa kyau idan ya yi, ji ya yi a jikinsa tana kallonsa Dan haka ya cire fuskar daga jikin yaron ya kalle ta ya ga shi kawai take Kallo. ",Kallon fa." Da sauri ta sunkuyar da kanta cikin Jin kunya, sai Kuma ta ce. "Ni ban kalle ka ba." Ta yi maganar tana tura baki, kallonta ya yi ya dan lumshe idanunsa tare da sake bude su akan ta. "ATM card din da na baki ba ki taba cire kudi ciki ba, sannan Kuma na turo da direban da zai koya maki driving ko da ba za ki je driving school ba amma kin ce masa baki so ya tafi me kike nufi?" "Abba ne bai goyi bayan hakan ba ya ce na mayar maka da su." Shiru ya yi sannan ya ce. "Karfre nawa zai dawo?" "Sai k'arfe biyar na yamma idan ya tashi daga kasuwa." Abdallah ne ya fara kuka da alama rikon ne baya so don har yanzu barci ne a idanunsa, da alama kwanciya yake so don haka ta ce. "Kasan barci yake yi na d'auko shi kwanciyar yake so bari na je na kwantar da shi." Ta yi magana tana kokarin karbar yaron, hannunsa da nata ne suka hadu wajen karbar yaron, da sauri ta kalle shi tare da cewa. "Ya Ajmal baka da lafiya ne?" Idanu ya lumshe sannan ya bude su a hankali ya ce. "Lafiya ta lau." "Na ji jikinka da zafi ne da alama ba ka jin dad'i." Bai ce mata komai ba ya mika mata yaron, ta karba tana kallonsa cikin tausayawa don da alama zazzabi ke damunsa. ",ina zuwa." Ta fad'a tana fita daga motar don kwantar da Abdallah. Tana fita ya jinginar da kansa ta kujerar motar tare da lumshe idanunsa. Wayarsa ce ta yi ruri, har sai da ta kusa katsewa ya bude idanunsa ya duba Wanda ke kiransa, Khalil ne Abokinsa dake nan garin. Daga kiran wayar ya yi tare da karawa a kunnensa amma bai yi magana ba yana saurare. "Haba Ajmal sai da na ce ka jira ni nazo na duba ka kafin ka tafi, dan kasan baka da lafiya bai kamata ka yi wasa da lafiyarka ba, yanzu kana ina ne?" A hankali motsa labbansa ya ce "Kada ka damu ina k'ofar gidan su Amatullah ne, na je ganin yaro na." "To idan ka koma hotel ka kira ni na zo na duba ka na kawo maka magani." "Okay." Ya fad'a tare da katse Kiran wayar, lumshe idanunsa ya yi Dan kansa da ke Sara masa saboda tsananin ciwon da kansa ke yi, ga shi nan da kwana uku yake son ya sake barin k'asar. Bi tashar TASKAR MAMAN IHSAN a WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z 🤦‍♀️ *YAR MAYE*🤦‍♀️ (_The drug abuser_) Page8️⃣0️⃣ Ya fad'a tare da katse Kiran wayar, lumshe idanunsa ya yi dan kansa dake Sara masa saboda tsananin ciwon

Chapter 34 of 51