Share this page
yanzu akwai sauran wani ƙalubalen da ke gabannu, wato mahifin Amatullah, yana da matukar kafiya akan magana ɗaya ." Murmushi ta yi tare da cewa. "Kada ka damu idan har Amatullah rabonka ce za ku kasance a ƙarƙashin inuwar ma'aurata . Fatana ka yi ta addu'a komai zai koma dadidai da yardar Allah." "To Ammina in sha Allah." Daga nan suka cigaba da cin abincin ba wanda ya sake cewa komai . Da yammacin ranar sai ga Munnir ya yi parking motarsa a ƙofar gidan su Amatullah. Zaune ya yi a cikin motar, waysrsa ya ɗauka yana dannawa lambar wayar Amatullah Kira. Ta gama shafa mayyuka da kenan tana saka riga sai ga Kiran wayar Munnir ya shigo wayarta, sai da ta kammala saka kaya ta fesa tsadadden turaren da Ajmal ya ba ta sannan ɗauki wayar, lokacin da wata Kiran ta sake shigowa wayarta, ɗuka ta yi tare da sallama, ya sanar da ita yana waje. Hijabi ta saka sannan ta ɗauki flat shoe ta saka. Sai da ta buya ɗakin Umma bakin ta ɗauke da sallama ta shiga. Umma ba ta ciki sai Khalifa da kr ta sharar barci. Tsna ƙoƙarin fita Umma ta shigo da alama daga banɗaki take, sanar da ita zuwan Munnir ta yi sannan ta fice. Yana zaune a motarsa yana kallonta, murmushi tayi a zuciyiynsa yana addu'ar Allah ya mallaka masa wanna kyakkyawar halittar. Sanin ba ƙarasowa za ta yi ba don Abba ya ce bai yarda da zance a cikin mota ba. Fitowa ya yi ya nufi ƙafar shiga cikin gidan, a zaure ya same ta zaune akan bencin da suke zama don yin fira. Bakinsa ɗauke da sallama ya ƙarasa yana zama a gefenta, lumshe idanu ya yi sakamakon ƙanshin turarenta da ya shaƙa. Gaiishe shi ta yi ba yabo ba fallasa, ya amsa mata cike da jin daɗin ganinta. Fira suke yi yana cikin farin ciki duk sanda ya keɓe da ita, ita kuma ba yabo ba fallasa ba ta jin farin ciki na kasance wa da shi kuma ba ta baƙin ciki, kuma tana bashi kulawa yadda ya dace daidai gwargwado duk da ba ta kin soyayysrsa a zuciyarta. Idanunsa ne suka sauka an zoben diamond ɗin da Ajmal ya ba ta kyauta zoben akwai matukar kyau da ɗaukar ido. "My heart Ina kika samu wannan zoben?" Kallon zoben ta yi ta ce . "Ajmal ne ya bani." Take fuskarsa ta sauya daga fara'a zuwa rashinta, tsuke fuska ya yi tare da cewa. "Meye a tsakaninku da shi ne?" Ka manta shi uban ɗana ne?" "Na sani, bayan haka kuma fa?" Shuru ta yi don ta rasa me za ta ce masa. Zuwa can ta ce "To don ya bani zobe meye a ciki Munnir, da kai fa aka saka mani ranar aure to meye abun damuwa?" "Amatullah wannan zoben diamond ne fa ya siya maki, ba zoben azurfa ba ne ko gold, wannan zoben sai wani da wani suke amfani da shi, manyan mutane ke saka shi, tabbas wannan zoben na musamman ne na tabbata kuɗinsa za su iya kaiwa miliyan goma." Da sauri ta kalle shi tare da cewa. "Zobe kawai kake tunanin akwai na ten million?" Murmushin takaici ya yi tare da cewa. "Kinsan lu'ulu'u yafi zinari ko?" "Ina dai jin jin ana faɗa don ko zinari ba gane shi nake ba ballantana lu'ulu'u, duk da ance yafi zinari." "To wannan zoben da ya baki shine na lu'ulu'u." Shuru ta yi taba kallon zoben diamond ɗin ga wani abu mai ado a tsakiyar zoben. " A yanzu ba zan tilasta maki cire zoben nan ba duk da banji daɗin ganinsa a hannunki ba, kasancewar har yanzu baki riga kin zama mallakina ba amma ban ga dalilin baki zoben ba. Amma ki sani daga ranar da aka ɗaura mani aure da ke za ki cire wannan zoben daga hannunki." Jinjina masa Kai kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba. Misslin karfe goma Sha ɗaya na dare Ajmal ne sanye da kayan barci riga da wando na farare, sai takalminsu dake ƙafsrsa, Kai da komo yake yi a cikin bedroom ɗinsa. Ƙarasawa ya yi jikin window ɗakin ya yaye labulen window ɗin yana kallon harabar gidan, duk da dare ne amma gidan tamkar rana haka yake, saboda hasken fitilu, sai securities dake kula da gidan ya hango su a bakin aikinsu. Za ka ɗauka cewa kallonsu yake yi amma a zahiri ba su yake kallo ba hankalinsa ma na wata duniyar. Ji yake kamar ya ɗauki waysrsa ya kira ta ya ji muryarta amma yana tunanin ko ta yi barci baya son ya tayar da ita. Sai ya yanke shawarar tura mata saƙo idan ta masa reply ba ta yi barci ba kenan. Ɓangaren ita ma haka a wajenta kasa barci ta yi sai tunane-tunanen d take yi.Khalida na kwance a gefebta yana barci ita kuma sai juyi take yi akan gadon. Jin shigiwar message ya sa ta janyo wayar da ke gefen pillow da take kwance. _'kin yi barci ne_' Saƙon da ta karanta kenan wanda Ajmal ya turo mata, murmushi ta yi masa tare da tura masa reply. ' _Ban yi barci ba_' Take sai ga Kiran wayarsa ya shigo wayarta, da sauri da ɗaga tare da yin sallama, jin muryarta ya sa ya ƙarasa jikin gadon ya zauna. "Wa'alaiki salam." Gaiishe shi ta yi ya amsa tare da tanbayrta ya mutanen gidan, ta amsa da suna lafiya. "Ina yarona?" Kallon Khalifa da ke barci ta yi tare da cewa. "Yana barci ." "Okay, ina fatan yana lafiya ko?" Da eh ta amsa masa "Me ya hana ki barci?" "Tunanin ka." Ta faɗa tana Jira ta ji me zai ce don gaskiyarta ta faɗa masa. Murmushi mai sauti ya yi tare da cewa. "Na ɗauka ni kaɗai nake haukana akanki." "Me ya sa ka kasa yarda da son da nake maka?" "Ba kasa yarda na yi ba sai dai nawa son yafi naki,don ban iya haɗa soyayyarki da wata 'ya mace ba." "Kamar yadda nima ban haɗa soyyarka da wani ɗa namiji ba." "Are you sure?" Ta gane in da zancensa ya dosa, wato tana soyayya da Munnir yake nufi. Murmushin takaici ta yi tare da cewa. "Munnir biyayyar Abban ya. .." Katse ta ya yi ta hanyar cewa. "Ban tanbaye ki zancen wani ba." Sai ya kauda zancen ta hanyar cewa "Ina fatan Abba na gari ?" "Eh yana nan." Ta bashi amsa. Fira suka yi ta mintuna talatin sai ya ji ta na numfashi alamar barci ya ɗauke ta ba tare da ta shirya wa yinsa ba. Murmushi ya yi ya katse Kiran wayar. Washegari da safe Ammi na zaune a falo ta ji takunsa alamar zai sauko downstairs, ƙamshin turarenta ne ya gauraye falon, sanye yake cikin manyan kaya gezner ruwan sky blue anyi mata aiki da zare kalar dark blue, sai hula ita ma dark blue hannunsa ɗaure da tsadadden agogo yana sanye da baƙin takalmi sai ɗaukar ido yake yi. Murmushi Ammi ta saki ganin yana kallonta fuskarsa ɗauke da annuri. "Wai har lokacin ɗaurin auren ya yi ne?" "Eh Ammi ga angon ma sai Kiran wayata yake ta yi sai ka ce nine wakilin nasa." Murmushi ta yi tare da cewa "Ai kaima ka San yadda Majeed ke ƙaunarka, Kai ne dai ba ka damu da mutane ba" Murmushi kawai ya yi. "Munyi waya da Dadynka ya faɗa mani sun shiga airport yanzu ma na San jirginsu ya tashi." Murmushin farin ciki ya yi tare da cewa "Allah ya saka Baffa ya samu shawo kan Abban Amatullah ya bani ita." Murmushi Mom ma ta yi daidai lokacin da kira. Wayar Dr fu'ad ya shigo wayar Ajmal, ya fita yana amsa waya. Amintaccen bodyguard ɗinsa Ahmad dake bakin ƙofar ya take masa baya. Sauran kuma suna hango boss ɗin nasu suka taso. Motoci guda biyar ne za su fita da su, biyu a gaban wacce zai shiga biyu ma a bayanta. Ta tsakiyar Ahmad ya buɗe masa sai ɗaukar ido motar ke yi, sauran ma suka shuga a Jere motocin suka fita har bakin titi. Ɓangaren su Baffa kuwa bayan Dr Khalil abokin Ajmal da ke garin Minna kuwa shi ne ya ɗauko su ya kawo su har masauki. Baffa ne da Amininsa sai Dady. Bayan sun ci abinci sun huta ne Dr Khalil ya ɗauke su a motarsa har zuwa gidan su Amatullah. Yaro Dr Khalil ya tura don ya yi masu sallama da Abba, bayan yaron ya dawo ne ya ce baya nan ya tafi kasuwa, Dr Khalil ya sake tura yaron wai don Allah a kira shi ya dawo ya yi baƙi daga nesa suke. Jin haka ya sa Umma ta umarci Amatullah ta kira Abba ta sanar da shi, ya ce yana nan dawowa. Babban tabarma Umma ta bawa yaron ya shimfiɗa masu a zaure Bayan yaron ya sanar da su Dr Khalil ya bashi kuɗi ya tafi yana godiya. Shiga zauren suka yi suka zauna a tabarma suna jiran isowar Abba. Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z 🤦‍♀️ *'YAR MAYE*🤦‍♀️ (_The drug sbuser_) *NA* Zainab Abduullahi K.N.T (Maman Ihsan) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page1️⃣0️⃣0️⃣ Shiga zauren suka yi suka a tabarma suna jiran isowar Abba. Suna nan zaune suna ɗan taɓa fira har mai adaidaita sahu ya ƙaraso ƙofar gidan. Bayan ya sallame shi ya tafi Abba ya tsaya yana kallon dalleliyar motar dake ajiye a ƙofar gidansa, a tunaninsa Ajmal ne don shi yake zuwa da motoci daban-daban kuma masu kyau da ɗaukar ido. Nufar zauren ya yi bakinsa ɗauke da sallama, gabaɗaya suka amsa masa sallamar a tare, mamaki ne na ganinsu ɗauke a fuskarsa, don da ka gansu ka san manyan mutane ne. Ƙarasawa ya yi ya cire takalmin da ke ƙafarsa. Cikin girmamawa ya gaida Baffa da Amininsa, suka amsa cikin fara'a tare da miƙa masa hannu suka yi musafaha. Daga nan ya gaisa da Dady da Dr Khalil. Ƙoƙarin tashi yake yi tare da cewa. "Bari a kawo maku ruwan sha." Baffa ya yi saurin dakatar da shi tare da cewa "Kada ka damu kanka daga madaukaki muke, Alhamdulillahi." Komawa ya yi ya zauna tare da zuba masu ido yana jiran jin abinda za su faɗa. Gyaran murya Baffa ya yi tare da cewa. "Na san kana mamakin ganin mu ko, musamman da ba ka san mu ba." "Haka ne Baba ban sanku ba gara ma wannan kamar na so na shaida shi." Ya ƙarasa maganar yana kallon Dady. "Shi ya taɓa zuwa sau ɗaya." Abba ya jinjina kai don tabbas ya taɓa ganin Dady sai dai ya mance in da ya san shi. Mai da hankali ya yi kan Baffa da ke magana. "Mu iyaye ne a wajen Ajmal kuma mun zo ne daga Adamawa." Sai a lokacin Abba ya gane inda ya san Dady shi ne mahaifin Ajmal tare suka dawo da Amatullah gida bayan ya Korea ta. Haƙiƙa muna mai ƙara baka haƙuri akan abinda ya faru tsakanin jikana da ƴarka, domin na san kai mahaifi ne a wajen yarinyar, ba wanda zai fi ku jin zafin abun sama da kai da mahaifiyarta, don ba iyayen da zasu so a ce ga 'yarsu ta haifa masu jika ba ta hanyar aure ba, duk da na san yadda abun ya faru ba laifin ɗaya daga cikinsu amma ba'a so haka ba." Nisawa ya yi kafin ya ɗaura da cewa. "Mun zo ne da ƙoƙon bararmu a wajen ka tare da duba dacewar hakan saboda abinda ya faru, muna nemawa jikana auren 'yarka domin su kasance a karkashin inuwar ma'surata cikin rufi asiri su reni ɗansu da Allah ya basu, yaro ya tashi a gaban uwa da uba zai fi samun cikakkiyar tarbiyya da kuma rufin asiri ba zai tashi yana tambayar ina mahaifinsa ko mahaifiyarsa ba ballantana a sanar da shi ta hanyar da aka same shi hakan zai saka ya shiga wani hali.' Kallon Abba ya ya cikin ido wanda hakan ya saka Abba ya sunkuyar da idanunsa sakamakon kwarjinin da Baffa ya masa. Jikana yana matukar son yarinyar nan da abinda ya haifa masa wanda ya ƙi zaɓin da aka masa akan son da yake mata, hakan ya saka muka taso tun daga Adamawa har zuwa nan domin nema masa izini a wajen ka." Shiru Abba ya yi na minti ɗaya kafin ya ɗaura da cewa. " A zahirin gaskiya akwai yaron da ke neman aurenta tun kafin ta canza halayyar ta, ya nemi na bashi izini yana zuwa wajen ta suna fira kwatsam wata rana ciki ya bayyana a i jikinta, bayan ya ji labarin komai har da korar da na kata ta bar gida ya shuga tashin hankalin sosai, ya yi yawon nemanta don ya dawo da ita gida bai dake ta ba, a halin da muke ciki yanzu samun namiji wanda zai ga yarinyar da zai aura da cikin wani kuma har da shaye-shaye amma bai daina son ta ba sai ma nemanta da yake yi har ya gaji ya daina. Kuma haka yake kyautata mana yana zuwa ko ta dawo ko mun samu labarin ta, na ce ya fita harkata amma yaƙi. Kwatsam bayan tsawon watanni sai ya zo da zancen ya gano tana Kaduna nan da nan ya tafi Kaduna ya gano inda take sai dai security sun hana ya ganta, duk da ya ji ba daɗi musamman da ya gane a gidan Ajmal take zaune wanda shi ne wanda ya mata cikin. Haka ya dawo cikin sanyin jiki, kafin na bishi muka tafi, sai dai ba mu same ta ba wai bata ƙasar, cikin ƙunar zuciya muka dawo, dai bayan kwana biyu sai ta dawo da Jariri sai Ajmal da iyayensa. Suka ba mu haƙuri tare da labarin komai. Duk da haka saurayin da ke neman aurenta bai guje ta ba, na kira shi na sanar da halin da take ciki, ga mamaki na ya nuna yana sonta a haka har yanzu." Ajiyar zuciya ya sauke tare da kallon Baffa ya ce "Idan ban aura masa ita ba na kyauta masa?" Daga Baffa har amininsa da Dady sun gamsu da hujjarsa, don ba kowane namiji ne zai iya ace ga budurwarsa nan bayan ta fad'a harkar shaye-shaye ta yi cikin shege sannan ta dawo kuma ya amince zai aire ta a haka ba. "Kana da gaskiya Mallam Abdullahi, don idan aka yi la'akar da dad'ewar da ya yi yana son ta tun kafin Ajmal ya San ta, mu dama munyi la'akari ne da yaro dake tsakaninsu da Ajmal saboda makomar yaron don zai fi dacewa a ce shi ne ya aure ta ba Wani ba, gudun ita ma za ta iya fuskantar wata k'alubalen a gidan Wani mijin ko daga gare shi ko daga danginsa akan k'addarar da ta same ta ka San abun isgilanci da gori baya wa mutane wahala. Sannan abu na biyu na ji ance Ajmal d'in take so ba Wani ba, ka ga tirsasawa mace akan mijin aure ba fa'ida gara ka barta ta zab'i son ranta don zaman aure zama ne na hak'uri yaran yanzu ba kamar na da ba ne anyi kana so ina so ya aka k'are ballantana ni ba na so, kada ka tilastawa 'yarka, ba wai ina fad'in haka don ka bawa jikana aurenta ba ne a'a ina fad'a maka ne a matsayin shawara." Jinjina Kai Abba ya yi yana cewa. "Kar ka damu na san Munnir ba zai mata gori ko Wani abu akan rayuwar da ta yi a baya ba, kuma na ce ya sanar da iyayensa komai akan Amatullah sun amince ba komai ya aure ta a haka bayan ta yaye yaron da take shayarwa. Ita kuma Amatullah zan sake tuntub'arta a yanzu duk da Ina da tabbacin ba za ta k'i Munnir ba yadda suka dad'e suna soyayya." Tashi ya yi ya nufi cikin gidan don dai yana tunanin suna son ya bawa d'ansu aurenta ne y sa suke cewa ba ta son zaɓinsa. Da sallama ya shiga cikin gidan Amatullah da ke wanke kayan Umma ta amsa inda Abba ya umarce ta da ta same shi a ɗakin Umma. Da sallama ya shiga Umma dake ninke kayan wankin da suka bushe ta amsa tare da cewa. "Har baƙin sun tafi ne?" "A'a Wani sabon al'amari suka zo da shi na nema kan nema wanda hakan bai dace ba." "Su waye su?" "Iyayen Ajmal ne." Amatullah da ke ƙoƙarin shigowa ne ta ji gabants ya buga da ƙarfi har sai da ta rintse ido ta kasa ƙarasowa cikin ɗakin. Abba ya cigaba da cewa "Ki duba hallaci irin na Munnir idan Amatullah ba ta aure shi ba ai bamu kyauta masa ba amanarsa za ta kama mu tun yana gwagwarmayar nemanta na masa alƙawarin aurenta iyayensa sun zo an Saka rana idan Amatullah ta ce ba ta son sa ai ta Zubar mani da ƙima ne wajen mutane, zan zama ƙaramin mutum a wajen iyayensa." Umma ta ce "Haka ne amma ya fi dacewa ta auri uban ɗanta ko...." Abba ne ya dakatar da ita ta hanyar cewa "Wani zance kike ƙoƙarin faɗa, kin mnace ɗawainiyar da yaron nan ya yi da mu ko akan lalurar ki da hawan junin da 'yarki ta Saka ki waye ya dinga kula da lafiyarki ta hanyar Kai ki asibiti na tsawon watanni sai da Amatullah ta dawo kika warke, haka ya dinga wahalar nemanta duk da zugin mutane ya toshe kunne bai ƙyamace ta ba don wani ya zo daga sama wanda shi ne sanadin rugujewar rayuwarta na bashi ita na hana wanda ya mata halacci, to idan ma zuga ta kike yi gara ki daina ba wanda ya dace da ita sama da Munnir." Amatullah dake tsaye a waje tana jin komai hawaye ne kawai ke kwaranya a idanuwanta don a yanzu ba ta isa ta cewa Abba ba ta son Munnir ba." Ƙwala mata Kiran da Abba ya yi ne ya sa ta komai baya ta ɗauki buta ta wanke fuska ta goge sannan ta shiga da sallama knata a ƙasa. Bayan sun amsa mata sallama ne ta zauna a ƙasan ɗakin, Abba ya Kira sunanta. "Amatullah." Ta amsa ba tare da ta ɗaga Kai ba. "Kina son mijin da na Saka maki rana da shi ko baki son sa?" Tuna kalamansa da ya yi wa Umma ta sa ta ce. "Ba na da zaɓi duk wanda ka zaɓa mani na amince ko ma waye." Tayi magana idanuwanta na cika da ƙwalla. "To ni dai Munnir na zaɓa maki saboda cancantars, idan kuma baki son sa ki sanar da ni wanda kike so." "Abba na amince da zaɓinka Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi." "Allah ya naki albarka." "Daga nan ya tashi ta fita." Yana fita ta faɗa jikin Umma tare da sakin marayan kuka, bubbuga bayan ta Umma kawai ke yi ta kasa magana don ta fahimci ƴarta. Ba ta son ta watsawa mahaifinta ƙasa a idanu ne kawai ya sa ta ce haka, amma da daɗewa ta fahimci ba son Munnir take yi ba ta amince ne kawai don Abbanta ya masa alƙawarin ba sa aurenta. Bayan Abba ya koma wajen su Dady ya sanar da su cewa yarinyar ta ce wanda aka Saka mata rana da shi take so, ba yadda suka iya cikin sanyin jiki suka masa sallama suka bar gidan. Kai tsaye hotel suka koma suka sa Dr Khalil ya Siya masu tikitin jirgi gabe da safe sai su kama hanya. Wunin ranar Amatullah sukuku ta yi shi don ko Kiran wayar da Munnir ya mata ƙin ɗagawa ta yi ƙarshe ma ta kashe wayar gabaɗaya. Duk yadda Ajmal ya so Dady ya sanar da shi yadda suka yi bai sanar ba, cewa ya yi idan ya dawo zai ji. Ya Kira wayar Amatullah ya ji a kashe, mamaki ya kama shi amma haka ya share. Washegari jirgin safe suka kama hanyar Abuja, daga nan suka shiga jirgin da zai Kai su Yola. Lokacin da Marka ta ke ji daga bakin Baffa zancen yarinyar ta ce wanda aka Saka mata rana take so an janye zancen neman da Ajmal ke mata ya sa Marka farin cikin daga ita har Nihal. Sai dai abunda ya basu rashin jin daɗi shi ne yadda Baffa ya ce ya soke zancen Ajmal ya auri Nihal tunda ya ce baya son ta, amma idan shi da kansa ya dawo ya ce zai aure ta to Alhamdulillah amma bai yarda a tilasta masa aurenta ba kamar yadda Marka ta yi yunƙurin yi, a haka aka bar zancen duk da Marka ba su so haka ba. Washegari Dady ya dawo Kaduna, suns zaune a falo shi da Ammi da Ajmal, nan ya sanar masu abunda ya faru, gabaɗaya Ajmal ji ya yi komai ya ɗauke masa na Wucin gadi,haka ya zauna kamar mutum mutumi, sai da Dady ya dafa kafaɗarsa sannan ya dawo daidai. Kai ya shiga girgizawa cikin Wani irin yanayi ya miƙe yana tafiya baya ganin gabansa, Wani duhu ne ya mamaye masa idanu daƙyar ya haura upstairs din da iKon Allah ya isa ɗakinsa yana tafiya kamar wanda yake maye, yana shiga cikin ɗakin ya zube a ƙasa. 09065327995 Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z 🤦‍♀️ *'YAR MAYE*🤦‍♀️ (The drug abuser) *NA* Zainab Abdullahi KNT (Maman Ihsan) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *SADAUKARWA* Wannan shafin sadaukarwa ne gare Jajirtattu writers association, ina matuƙar alfahari da ku. Allah ya ƙara mana ƙwarin guiwa. Page1️⃣0️⃣1️⃣ Kai ya shiga girgizawa cikin wani irin yanayi ya miƙe yana tafiya baya ganin gabansa, wani duhu ne ya mamaye masa idanu daƙyar ya haura upstairs ɗin da ikon Allah ya isa ɗakinsa yana tafiya kamar wanda yake maye yana shiga ɗakin ya zube ƙasa. Cikin tashin hankali Dady da Ammi suka biyo bayansa, tura ƙofar suka yi ta buɗe suka shiga, zaune suka ganshi kamar mutum mutumi. Ƙwalla ne ya cika idanun Ammi ganin halin da tilon ɗanta ke ciki. Abba ne ya ƙarasa gabansa tare da durƙusawa ya dafa kafaɗarsa. "Son ka yi hakuri ka ɗauki ƙaddara wani abun muna sonsa amma idan ba alkhairi ba ne a wajenmu ba za mu same shi ba, ka yi addu'a Allah zai musanya maka da mafi..." Girgiza kai ya shiga yi yana cewa. "No Dady Amatullah alkhairi ce a rayuwata za mu rayu a karkarshin inuwar ma'aurata, ba wanda ya dace da ita sai ni, me ya sa za ta yi mani haka wallahi tana so na hasalima wancan da za ta aura ba shine a zuciyarta ba Dady, ni ne a zuciyarta ni take so." "Son dole ka haƙura da yarinyar nan tunda ta fada ba ta son ka wanda aka saka masu ranar aure take so..." Jin kalaman Dady yake yi da zafi tamkar ana watsa masa garwashin wuta a zuciya, kamar wani zararre ya tashi yana layi ya ɗauki wayarsa ya lalubo lambar wayarta ya danna mata kira, cikin sa'a wannan karon ta shiga, sai dai har ya mata kira biyar ba ta ɗaga ba, kuma bai fasa kira ba abinda bai taɓa yi ba a rayuwarsa, ya yi ta kira ba'a ɗagawa. Sai a kira na biyar ta ɗaga ba tare da ta yi magana ba. "Amatullah da gaske kin ce wancan kike so ba ni ba, kin manta abinda kika taɓa faɗa mani a baya cewa ni kike so ba shi ba, kada ki cutar da ziciyata ki cutar da ta ki." "Ya Ajmal ka yi haƙuri duk abinda suka sanar da kai haka ne, ta yiwu ba rabon za mu mallaki juna ga yaronka nan da zarar na yaye shi zai dawo gare ka don na san ba barinsa za ka yi a hannun kowa ba ina maka fatan alkhairi." Tana gama faɗar haka ya katse wayar, bin wayar ya yi da kallo kafin ya sake ta ta faɗi ƙasa. Dafe saitin zuciyarsa ya yi da ke masa zafi, nunfashinsa ke barazanar ɗaukewa yayin da yake kokawa da numfashin nasa, hankalin Dady da Ammi ya masifar tashi, kuka Ammi take yi na tashin hankalin da ya riske ta. Ganin haka ya sa Ammi lalubo lambar wayar Dr Fu'ad ta danna masa kira, yana ɗagawa cikin kuka take sanar da shi, shima hankalinsa ya tashi da jin halin da aminin nasa ke ciki. Nan ya sanar da ita yanzu zai kamo hanya. Amatullah kuwa suna gama waya da Ajmal ta kashe wayar tare da fashewa da matsanancin kuka, tana tausayin halin da suke ciki daga ita har Ajmal, ta kuka yi addu'a idan shine alkhairi a gare ta Allah ya mallaka mata shi. *ADAMAWA* Zaune take akan sallaya bayan ta idar da sallar la'asar addu'a take yi a zuciyarta Allah ya cire mata soyayyar Ajmal ya haɗa ta da wanda yake son ta. Marka ce ta shigo cikin ɗakin, ganin tana addu'a ne ya sa ta zauna bakin

Chapter 46 of 51