yi, a hankali ta bude idanunta da suka yi ja ta sauke su akan wayarta, ganin karfe biyar saura kwata ta tashi cikin hanzari, ta fito falon gidan, wasu ta gani ta yi suna ta fira da shewa, sai Nafeesat da ke zaune tana fira ta kalli Hafsat tare da cewa
"Kin tashi daga barcin?"
",Eh gida zan tafi ki bani kwalaben codin guda biyu na je da su, don na ji yanzu damuwata kaso tamanin ta ragu."
"Okay zan baki kwalaben codin guda biyar tunda unguwarku kusa da ta su Shamsiyya ne ki biya ki bata kwalba uku."
"Ba da mota nake ba fa."
"Na sani don Allah ki biya tunda ba ku da nisa na san mai napep zai iya jiranki tunda drop za ki d'auka."
Ba don ta so ba ta ce.
"Kawo sauri nake yi?"
Haka Nafeesat ta bata kwalaben codin guda biyar ta zuba a cikin handbag dinta ta fita. Sai kuma ta dawo ta ce .
"Wai har yanzu tana gidan wannan d'an iskan mijin?"
"Eh mana suna tare iya wuya."
Wani ne dake zukar hayakin shisha ya kalli Hafsat ya ce
"Ai gara ita ta samu d'an iskan ya aure ta ke fa Ina naki mijin auren?"
"Kai farauta wallahi ka kiyaye ni ba na shiga sabgarka, idan ba haka ba wallahi zan tafka Maka rashin mutunci."
Ta ja tsuki ta yi tare da yin gaba tana cewa.
"Bana da lokacinka ."
A k'ofar wani matsakaicin gida mai napep din ya dire ta, ta sanar da shi yanzu za ta ba da sakon ta fito.
Kashe napep din ya yi yana zaman jiranta, tana tura k'ofar gidan da sallama ta ji shiru, don haka ta karasa k'ofar d'akin, sautin kuka da karar duka take ji yana fitowa daga cikin gidan, kukan Shamsiyya ce mijinta ke jibga, ihu take tana bashi hakuri yayin da shi Kuma yake dukanta har da zagi .
Da sauri ta juya ta koma Inda ta fito ta shiga Keke napep din da ya kawo ta, ta sanar da shi inda zai kai ta.
Wata ma'ikaciya ce ta shirya masu breakfast a dinning table, bayan ta gama ta nufi d'akin Nasreen tana knocking, izinina shiga ta ba ta don ta san wace ce, matashiyar budurwar ta sanar da ita an kammala breakfast sannan ta fito .
Har lokacin Nasreen na rike da waya tana Kiran lambar wayar Billy, amma ta ki dagawa, ganin haka ya sa ta kira wayar Zeenat.
Bugu biyu ta d'aga ba ta jira ta yi magana ba ta ce,
"Kina tare da Billy?"
"Ba na tare me ya faru?"
",Komai ma ya faru wallahi sai na ci ubanta akan abunda ta yi mani."
Kasancewar Billy ta bawa Zeenat labarin komai ya da Zeenat ta san dalilin Kiran wayar kumshe dariyarta ta yi sai da suka gama magana sannan ta saki dariyarta har da tintsirawa.
Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
🤦♀️ *'YAR MAYE*🤦♀️
(_The drug abuser_)
Na
Zainab Abdullahi K.NT
(Maman Ihsan)
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Page9️⃣6️⃣
Kasancewar Billy ta bawa Zeenat labarin komai ya sa ta san dalilin Kiran wayar, kumshe dariyarta ta yi sai da suka gama magana sannan ta saki dariyarta har da tintsirawa.
Da sallama ya shigi cikin d'akin, sanye yake cikin shigar suite bak'i sai bakin gilashin da ya sanya a idanunsa, ko amsa sallamar da ya yi ba ta yi ba ta kalle shi sannan ta d'auke idanunsa daga kallonsa.
Affan ne ya zo ya rungume Dadynsa yana jin dad'i.
"Kun yi breakfast ne?"
Ya yi maganar yana kalkon Nasreen da ta hade rai ita tana fushi ya mata laifi, ganin yanayinta da Kuma take-taken ta ne ya sa shi janyo Affan suka nufi k'ofar fita, dinning area suka Kara'sa, ya zaunar da shi, Mai aikin ne ta karaso wajen ta fara serving din su.
Da kansa ya yj feeding din Affan har ya koshi, wayarsa ke ruri wani abokin kasuwancinsa ne. Sai da ya tabbatar Affan ya k'oshi sannan ya barshi ya fice daga gidan.
Yana fita Nasreen ma ta tattara kayanta ta ja Afdan suka bar gidan.
*Bayan watanni biyar*
Abubuwa da yawa sun faru masu dadi da kuka akasin haka, har da auren Fadeela kawar Amatullah. zuwa yanzu kuwa Khalifa na tafiya da k'afarsa, don tun yana wata bakwai ya fara tafiya yanzu kuna watanninsa tara. Kafin yanzu kuwa Ajmal ya zo ya samu Abba da zancen auren Amatullah, amma Abba ya dage kan cewa ba zai taba canza magana ba matukar ba Munnir ne ya zo ya same shi da zancen ya janye ba wanda hakan abu ne mai matukar wahala. Har yanzu Ajmal na zuwa da sunan duba yaronsa, Kuma bai hakura da zancen neman auren Amatullah ba, don zuwa yanzu saura watanni biyar ne suka rage. Bangaren Nasreen kuwa ba abunda ya canza na halayyarta don har yanzu ba ta dauki zaman auren da Mahimmanci ba, ta dinga yi mani wasu abubuwan da ba su dace har yanzu tana zaune a gaban iyayenta kamar ba matar aure ba sun kasa tsawatar mata ba, sun zuba nata idanu sai dai ta yi abunda ranta ke so. Ko da Ajmal ma ya je kasar yanzu baya zuwa gidansu sai sai ya tafi makarantar su Affan ta ganshi a can, har ya bashi tsarabar da ya kawo masa.
Bangaren Nihal Kwa har yanzu ba ta daina dakon soyayyar Ajmal ba ta hakura ba, Kuma har yau Dady ya kasa zuwa Yola, saboda ya yi magana da Ajmal akan auren Nihal, Kuma yadda ya Fahimci Ajmal baya ra'ayin yarinyar kuna ya nuna masa cewa matukar tsamohuwar nan ta dage akan auren nan to ba zai ce komai ba amma ya na da tabbacin zumuncin da take son kullawa to tamkar lalata shi take Shirin yi.
Gobe Dad da Ammi har ma da Ajmal suke Shirin zuwa Yola suke Shirin zuwa Yola. Don Ajmal na nan ya zo Kaduna, sai dai baya cikin walwalarsa, kwana biyu dai ya dan fara canzawa.
Zaune yake a saman gadonsa ya makala wani karamin abu kamar earphone a kunnensa, sai dai shi karami sosai ne ba abunda yake ji a kunnensa sama da kukan Khalifa hankalinsa ya tashi sosai, don kukan ya yi yawa. Ga Miryar Amatullah yana ji tamkar za ta yi kuka tana cewa ita fa ta gaji duk irinn rarrashin da za ta masa ta masa bai yi shiru ba, za ta barshi be ya yi ta kukan nasa, ga Umma ta je ta'aziyya.
Wayarta ce ke ta ruri Ajmal na Kiran wayar amma ba ta d'aga ba,don ba ta da sukunin da za ta iya wani amsa waya yanzu.
Goya Khalifa ta yi tare da cewa.
"Ni wnnan allura ko jaraba, da zaran anyi yaro bai da sukunin."
Dak'yar ta samu ya yi barci sannan ta kira wayar Ajmal din, ba'a daga ba sai daga baya ya kira ta
Dagawa ta yi tare da yin sallama, bayan ya amsa mata ne yake tambaya me ya samu Khalifa yake zabga wannn irin ihu haka. Cikin mamaki ta ce.
"Ka na Ina ne?
"Ina Kaduna."
Ita fa lamarin Ajmal ya na bata tsoro, mutum kamad Aljani, duk lokacin da take wani abu musamman idan akan yaronsa ne ko Kuma lamarin fita ne ya dinga mata magana kenan, hakan ya fara tun ranar da ya zo bayan ya tafi suka fita amso dinki ita da Fadeela.
Tana tsaka da tunani ta ji ya ce .
"Wani lokaci kuka yi allurar?"
"Yau da safe."
Ta bashi amsa zuciyarta cike da mamakin sanin halin da take ciki da yake yi, alhalin ba kasar ko garin wani lokaci. Da ace abunda ke faruwa a waje ne yake sani da za ta ce wani ya sa yake masa bincike yana bibiyarta. To wani lokacin abunda ke faruwa a dakinta waye zai sanar da shi? Jin muryarsa ta yi yana cewa.
"Ki bashi paracetamol Kuma ki Kara hakuri da shi don Allah ki daina fushi da shi kin ji?"
Kai kawai ta gyada' masa kamar yana kallonta, Inda ya cigaba da cewa.
"Ba ka biye lamarin yaro hakuri keke da shi, kin ga shi ba mai rigima ba ne zafin allurar ce ta saka shi."
Nan ya cigabada ba ta baki har ta ji ta daina jin haushin.
Sallama ya mata ya katse Kiran wayar, sannan ya zare abun a kunnensa.
Mamaki ne ke lullube a zuciyar Amatullah, don ita ta kasa gand ta wace hanya Ajmal ke sanin halin da take ciki? Shi Kuma baya son ta San cewa wannan zoben diamond da ya bata ta shine yake jin komai da take yi, a duk lokacin da ya so, hakan,sai dai ba kowane lokaci yake sauraren ta ba, musamman idan ya kunna ya ji suna fira da Mansur ko a waya ko a zahiri idan ya je zance baya sauraren firarsu, shi a tunaninsa zai iya jiyo abunda zai bata masa rai.
A washegarin ranar jirginsu ya sauka a garin Yola, Sudais ne ya zo airport ya d'auke su ya Kai su gidan Marka.
A harabar gidan ya yi parking din motar, Sudais da ke mazaunin direba Ajmal na gefensa, cikin hanzari ya fito ya budewa Dady da Ammi bayan motar suka fito, Kai tsaye suka nufi cikin gidan Sudais ya dawo ya bude gefen da Ajmal yake zaune.
"Yallabai bisimillah."
A hankali ya ziro k'afarsa ya fito daga cikin motar, suka nufi cikin gidan bayan Sudais ya bawa direba Marka umarnin ya shigo da kayan da ke cikin motar.
Da sallama Dady ya Shiga falon gidan Ammi na bayansa, Marka na zaune a Saman kujera ta d'aura kafa d'aya kan d'aya, ta amsa masu sallamar a takaice. Nihal ce xa ta fito daga dakinta ta karaso ta rungume Ammi tana dariya, Ammi ma rungume ta ta yi tare da d'an shafa bayanta. Dady ne ya durkusa gaban Marka tare da gaishe ta.
"Ina wuni?"
"Sai yau ka ga damar zuwa, wata nawa da na bukaci ganinka?"
.
"Ki yi hakuri don Allah abubuwa ne suka..."
D'aga masa hannu ta yi alamar dakatawa, sannan ta ce.
"Ya Isa."
Daidai lokacin da Sudais ya shigo Ajmal na bayansa, da sallama suka shigo cikin falon gabadaya fuskar Ajmal a tsuke take ba fara'a, kallo d'aya ya yi wa Marka ya d'auke Kai, ganin mahaifinsa da mahaifiyarsa na zaune a k'asa hakan ya sa ya zauna shima ba tare da ya kalli Marka ba ya ce.
"Ina wuni, mun same ku lafiya."
Tun kafin ta yi magana magana har ya mike tsaye ya kalli Ammi ya ce.
"Ammina zan d'an kwanta kaina na ciwo."
Jinjina masa kai ta yi yayin da ya shiga d'akin da yake sauka idan ya zo.
Ammi ta kalli Marka ta ce
"Barka da rana Marka."
"Yauwa barkan ki, ku tashi ku yi wanka ku huta ga abunci nan a shirya maku a dinning table."
Nihal ce ta dauki jakkar kayan Ammi tana cewa.
"Ammina mu je na raka ki."
Murmushi ta sakar mata tare da mikewa suka nufi d'akin da aka warewa Ammi a duk lokacin da ta zo.
Abba ma ya mike cikin sanyin jiki don ya ga yanayin fuskar Marka ba sauki.
Suna zaune a dinning area suna cin abinci, Marka, Dady, Ammi, Sudais, sai Nihal. Marka ce ta kalli Sudais ta ce
" Ina shi basaraken yake?"
Sanin cewa tana magana ne akan Ajmal ya sa Sudais cewa ya ce baya jin dad'in jikinsa mu yi ta cin abinci."
Tabe baki Marka ta yi tare da cewa.
"Duk tsiyarsa ya yi duk abunda zai yi ya gama bai Isa ya tsallake hukuncina ba."
Ba wanda ya yi magana Ammi kalli d'aya za ka mata ka gane cewa tana cikin damuwa.
Hajiya Laila mahaifiyar Nihal da Sudais ce ta shigo bakinta d'auke da sallama, kallo d'aya za ka mata ka gane cewa tana cikin farin ciki.
Gaisawa suka yi da duk jama'ar da ke wajen, ganin ba Ajmal a cikinsu ya sa ta ce.
"Ina d'ana yake ban gani shi ba."
"Yana ciki wai baya jin dad'i."
",Cewar Nihal tana kallon Mahifiyarta."
"Subhanallah Sudais yakamata ka duba shi ai ko?"
"Mama ina jiran tashi daga barci ne."
Bangaren Ajmal kuwa yana kwance a kan gado ya lumshe idanu kamar mai barci, amma a zahirin gaskiya ba barci yake yi ba idanunsa biyu, tunani kawai yake yi yadda zai bullowa matsalolin da suka tinkaro shi.
Ga soyayyar Amatullah da ke hana shi sukuni, gefe guda kuma ga matsalar Nasreen da ya rasa yadda zai yi da ita, sannan ga wannan tsohuwar da ke neman lika massa auren Nihal.
Sudais ne ya shigo bakinsa d'auke da sallama, a zuciyarsa ya amsa masa har lokacin bai bude idanu ba.
Zama ya yi gefen gadon tare da dada goshin Ajmal sai dai bai ji wani abu Mai kama da zazzabi a tare da shi ba.
"Man yakamata ka cire damuwar da ke cikin zuciyarsa, gudun dorawa kanka wata cutar.
"Ta Ina zan rabu da damuwa ne Sudais, na San ka san da zancen Amatullah ko?"
Ya yi tamabayar yana kallon Sudais.
"Eh na sani ba yarinyar da ta haifa Maka yaro ba?"
"Eh ita ce, Kuma wallahi ita kadai nake so a cikin zuciyata, ba na jin zan iya auren wata mace idan ba ita ba, zan iya cutuwa idan ban same ta ba, ita ce farin ciki na idan na rasa ta na rasa farin ciki, ka yi hakuri Sudais na san za ka ji ba dadi idan na fada maka cewar ba na son kanwarka."
.
Murmushi Sudais ya yi tare da cewa
"Ka da ka damu don ba ka son 'yar uwata ai ba lafinka ba ne Kuma na tabbata ba wai kana mata kiyayya ba ne, ba ka jin ta ne kawaj a matsayin matar da za ka iya aure. Kuma ai wannan ba matsala ba ne ai so a cikin zuciya take."
Jinjina Kai ya yi yana cikin jin dad'in yadda Sudais ke da Fahimta.
.
"Yauwa na gode sosai da ka fahimce ni, soyayar da nake wa Nihal na 'yan uwantaka be bayan haka ba na jin komai game da ita."
"Ka tashi mu fita Tsohuwar nan tana jiran mu."
Tashi ya yi cikin sanyin jiki suka fita daga d'akin.
Marka ce ke zaune a kan kujera mai zaman mutum d'aya, gefe Kuma Dady ne da Ammi zaune kan kujera mai zaman mutum uku, sai Mama mahaifiyar Nihal zane a kan kujerar da ke gefen Marka.
Nihal ce zaune a k'asa saman center carpet. Kaaraswa suka yi suka zauna a k'asa gefen da Nihal ke zaune.
Kallon Mama Ajmal ya yi tare da cewa.
"Ina wuni Mama?"
"Lafiya lau Son ya kake?"
"Alhamdulilllah."
"An ce ba ka jin dad'i ya jikin."
Nan ma ya sake amsawa da Alhamdulilllah.
Gyaran murya Marka ta yi tare da cewa.
"Na san Kun San dalilin taruwarmu a nan ko, to na tara ku a nan ne saboda magana mai Mahimmanci da zan sanar da ku, ko Kuma na ce zan bayar da umarni don ba shawara ba ne umarni ne wanda ya zama dole ku aikata shi kafin ku hadu da fushina."
.
Ta karasa maganar tana kallon Dady wanda kansa ke a sunkuye yana sairaron ta.
Wayar Ajmal ce ta yi ruri wanda ya kamata ya katse Kiran ko ya nemi izini na minti d'aya.
Ba tare da la'akari da mutanen da ke wajen ba ya daga wayar ganin Amatullah ce ke kira.
"Assalamu alaikum sanyin idanunta."
Gaba d'aya suka kalle shi har da Marka.
Shi ko wayrsa ya cigaba da yi hankali kwance.
"Ya kike ina d'ana?"
Daga can bangaren ta yi dariya tare da cewa
",Yana barci."
"Ki shafa mani kansa."
"In Sha Allah, kana lafiya?"
"Ina fa nake lafiya gani nan duk kewarki ta addabe ni, ji nake yi kamar na yi tsuntsu na zo gare ki."
"Ya Ajmal Ina son ka sosai amma gani nake yi kamar ba wata hanya da ta rage muna na mallakar juna."
Murmushi ya yi cike da kwarin guiwa ya ce
"Waye ya fad'a maki haka, ai ke tawa ce ni naki ne tare za mu yi rayuwa mu hayayyafa dan duk wanda ya ce zai raba ni da ke to wata kila ba rabon za'yi da shi ne, kin San fa an ce rabo ajali ne , idan mutum ya dage wajen raba masoya mutuwa yake yi..."
Jin a taba k'afarsa ne ya sa ya kalli Sudais wanda ya taba k'afarsa sannan ya maida dubansa ga suran jama'ar ganin kallon da suke masa, ga Marka da ta Shiga wani Hali sakamakon jin maganar da yake yi a waya kamar yana mata gargadi ne.
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
🤦♀️ *'YAR MAYE*🤦♀️
(_The drug abuser_)
Na
Zainab Abdullahi K.NT
(Maman Ihsan)
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Page9️⃣7️⃣
Jin an taba taba k'afarsa ne ya sa ya kalli Sudais wanda ya taba k'afarsa, sannan ya maida dubansa ga suran jama'ar ganin kallon da suke masa ga Marka da ta shiga wani hali sakamakon jin maganar da yake yi a waya kamar yana mata gargadi ne.
Ko a jikinsa bai damu da kallon da ake masa ba, ya mai da wayar kunnensa ya cewa Amatullah.
"Am busy right now but I will call you later."
"Okay"
Ta ce tare da katse Kiran wayar. Ajiye wayar ya yi a saman cinyarsa kafin ya daga Kai ya kalli Ammi ganin yanayin fuskarta ta sauya, rausayar da idanu ya yi tare da kallon k'asa alamar yana ba ta hak'uri.
Jin muryar Marka yayi tana cewa.
"Ka gama? Fitsararre mara kunya."
Kallon Dady da Ammi ta yi tare da cewa.
"Kuna ji a gabanku yake gasa mani magana ko? Har ni yake cewa rabo ajali ne idan mutum ya raba masoya mutuwa yake yi ko?"
Ganin tana neman daurawa iyayensa laifi ne ya sa shi cewa.
"Ni na kira sunanki ne, ai ba dake nake ba misali nake ba ta."
"Raina mani hankali kake so ka yi Ajmalu, ai maganark magana ce mai harshen Damo."
Jinjina Kai ta yi tare da kallon Ammi ta ce.
"Balkisu irin tarbiyyar taki kenan ko? Ko da yake ba zan ce tarbiyyar ki kadai ba ce har da ta mahaifiyarki da ya tashi a hannunta bai san maganar da zai fadawa kowa ba sai dai duk aunda ya zo bakinsa ya fad'a. Bai iya girmama mutane ba sai dai a barshi ya yi abunda ransa ke so ko to mu nan kasar ba ta marasa tarbiyyar ba ne idan iyaye suka yanke hukunci dole yaro ya bi ko yana so ko baya so, idan Kuma ya ki yin biyayya to za mu iya cire shi daga cikin mu."
Kallon Marka ya yi na yan sakanni kafin ya ce.
"Ba rashin tarbiyya ba ne na koyo daga wajen Umma kakata, sai dai na adalci wanda shi ne mabudin zaman lafiya, ba tauye hakkina kowa ba tarsasawa mutum ya aikata abunda ba ya so ana barin kowa ne ya yi abunda yake so matukar bai sabawa addinin musulunci ba ana bari mutum yavyi rayuwar 'yanci, da wannan irin ak'idar ta ki ne ya saka kika rasa babban d'anki har yanzu bai sa kin..."
Kafin ya k'arasa maganar da ya yi niyya ne Dady ya sauke masa lafiyayyen mari a fuska.
Sunkuyar da kansa ya yi kasa yana jin Dady na cewa
"A gabanmi za ka yi wa mahafiyarmu rashin kunya?"
"Ka gafarce ni Dady."
Ya yi magana kansa a sunkuye , Inda Dady ya cigaba da cewa.
"Dukkan mu nan ba wanda ya Isa ya ja da maganarta, duk shawarar da yanke akan mu da 'ya'yanmu, saboda haka duk shawar da ta yanke akan ka ta zauna ko ka na so ko ba ka so."
Marka kuwa zuwa lokacin kuwa idanunta sun rikede zuwa ja ta fara matsar k'walla tana cewa .
"Shikenan Balkisu kin haifo mana bala'i a cikin zuri'a, Ibrahim yau Kai ne ka haifi d'an da zai yi ja in ja da ni?"
Dady ya durk'usa a kan guiwarsa yana cewa.
"Ki yi hakuri Marka ba na son ganin zubar hawayen ki, duk shawarar da kika yanke akan yaran nan ya zauna, ko gobe kika ce a d'aura masu aure zan d'aura masu, don Allah ki daina kuka ."
Tashi ta yi ta nufi dakinta zuciyarta baka kirin, yau Ajmal ya fama mata tabon da ke cikin zuciyarta na tsawon shekaru talatin.
Ganin ta bar wajen ne Dady shi ma ya tashi ya bar gidan, Mama kuwa Mahifiyar Nihal ranta ya Kai kololuwa wajen b'aci sai dai ta yi shiru ne kawai ta kasa magana, tashi ta yi ta nufi d'akin Mahaifiyarta. Ammi ma tashi ta yi idanunta cike da k'walla ta bar wajen, Nihal ma ta nufi dakinta tana kuka. Sudais ne ya janyo hannun Ajmal ya mike tsaye, Kai tsaye suka nufi d'akin da Ajmla ya sauka.
Motarsa ce ta yi parking a parking space da ke cikin jami'ar, wanda nan ne lectures ke ajiye motocinsu. Bai fito ba sai ya dauki wayarsa tare da lalubo lambar wayar Amatullah. Bugu biyu ta d'auka tare da yin sallama
"Assalamu alaikum."
Lumshe idanunsa ya yi sakamakon jin zazzak'ar muryarta, cikin wani irin yanayi ya ce
"Wa'alaiki salam Gimbiyata."
"Ina kwana?"
Ta gaishe shi, ya amsa cikin sigar tsokana ya ce.
"Ina na iya kwana."
"Subhanallah me ya faru?"
Murmushi ya yi jin ta damu da shi, ya ce.
"Tunaninki ne kawai ke dawainiya da ni, na kasa barci na kasa walwala ji nake yi kamar wani al'amari ne ke Shirin faruwa da ni Kuma mara dad'i."
"Ka ga yanzu ka daina tunanin abunda ba alkhairi ba ne a wajen ka, ka yi addu'a Allah yana tare da Kai."
Duba time ya yi ya ga saura minutes ya shiga lokacin da zai koyar kasancewar sa lecturer.
"Lokacin da zan shiga na koyar da lectures ya yi bari na shiga idan na fito zan kira ki."
"To a fito lafiya."
Sallama ya mata ya sannan ya fita daga motar, ko office din sa bai je ba ganin lokaci ya kure.
Wadanda ke zaune waje suna fira ganin sir Munnir Kuma sun san lokacinsa ne ya sa suka shiga ciki class.
Washegari da misalin karfe goma na safiya kowa ya hadu a dinning area suna breakfast, mutum d'aya ne babu wato Ajmal, Ammi ma gaba d'aya ba ta cikin walwalarta sakamakon ganin halin da gudan d'an nata tilo da Allah ya bata cikin damuwa. Marka da Nihal cin abuncinsu suke yi hankali kwance, Dady ma baya cikin walwala yana dai tura abincin ne amma ba wai don yana jin dad'in ci ba. Sudais dai ya hada shayi ya nufi d'akin da Ajmal yake don Kai masa, saboda ya yi ya fito su yi breakfast amma fir ya ki yarda.
Hajiya Laila ce ta yi sallama ta shigo cikin falon, gabadaya d'aya suka amsa mata, ta gida mahaifiyarta sannan ta juya kan Dady ta gaishe shi. Sannan ta gaida Ammi.
Komawa ta yi falon tana zaman jiransu Inda take tamabayar ba ta ga Ajmal da Sudais ba.
Bayan mintuna talatin sun bar dinning area sun hadu a falo. Mai aikin Marka ce ke tattare kayan da suka yi amfani da su.
Bayan mintuna talatin, zaune suke a falon gidan daga kan Ammi har 'ya'yan ta da jikokinta.
Marka ce ta yi gyaran murya tare da cewa.
"Ibrahim."
Dady ya daga Kai ya kalli Marka tare da cewa
"Na'am."
"Wace ce ni a wajenka?"
Cikin sanyin murya ya ce.
"Mahaidiya ce ke a gare ni "
"Shin tinda nake da Kai na taba zartar da hukunci akanka ko umartar ka da aikata wani abu ka kasa?"
"Ban taba ba Kuma ba na fatar ranar da zan bijire miki akan ko ma mene ne."
"Alhamdulilllah"
Marka ta fad'a bayan ta jinjina Kai, sannan ta cigaba da cewa.
"Ina fatan kamar yadda kake mani biyayya da bin umarnina akan ko ma mene ne Ina fatan haka d',anka yake mai biyayya a gare ka."
Jinjina kai Dady ya yi tare da cewa.
"In sha Allah, bai taba kaucewa umarnina ba."
"Dakayu."
Kallon Ajmal ta yi na dan lokaci kafin ta ce.
"Ibrahim ina mai umartarka da ka bawa d'anka umarnin ya yi biyayya akan duk abinda ka zartar akansa."
Shiru falon ya yi ana jiran me za ta fad'a, sai da ta dauki tsawon mintuna biyu kafin ta ce
"Ina son daga yau asabar zuwa ranar wata asabar din ka d'aura auren d'anka da 'yar k'anwarka Nihal."
Da sauri Dady ya kalle ta daga shi har Ammi don ba su yi tsammanin cewa za ta yanke hukunci haka cikin gaggawa ba. Ajmal Kuwa bai wani girgiza ba don ya san karshen alawa k'asa. Sai dai ya kidiri niyyar ba zai taba yarda da wannan hadin ba, sai ya yi duk abunda zai yiwu.
Abba ya kalli Marka ya ce.
"To yadda kika ce haka za'ayi, amma na so a basu damar fuskar juna kafin a yanke hukunci."
"Ba wannan magana mu a da can da ake aurar da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 44 Chapter of 51