Share this page
tayar Mani da hankali?" Jin haka Munnir ya gane cewa shi ne Ajmal, da ta dauka ma baya jin Hausa, dan zubin larabawa ne da shi. Munnir ya ce. "Amatullah da ke zaune a gidanka na zo ɗauka na tafi da ita?" Wani kallo Ajmal ya wurga masa kafin ya ce. "A matsayin ka na wa?" "A matsayina na wanda zai aure ta, kuma kowa ya shaida mahaifinta ya bani auren ta ni Munnir." Gaban Ajmal ne ya faɗi jin kalaman Munnir, amma da ke bakin duniya ne hakan ya sa ba wanda ya gane hakan, sai ya daure ya ce "Wata shaida ce da kai da zai saka na tabbatar kai ne za ka tafi da ita? Ina Mamanta da Banbanta, ko yayanta?" Girgiza kai Munnir ya yi tare da cewa "Ba ko ɗaya wanda ya zo nine." Ajmal ya kalle shi da kyau tare da cewa. "Ba wata hujja da zai sa ka zo ka ce zaka tafi da wata a nan." Kallon security ya yi tare da cewa. "Ya bar ƙofar gidan nan a cikin mintuna biyu." Daga nan ya ja motarsa ya shige gidan lokacin da aka wangale masa gate. Daga nan Munnir ya tada hankali akan sai an fito masa da Amatullah, dan ba zai bar wajen ba tare da ita ba. *Daga wannan page din zanyi offline, zan ɗan tafi hutu sakamakon wata lalura, ku saka 'yata a addu'a Allah ya bata lafiya ya yaye mata, idan na dawo xan daukar maku daga inda na tsaya* *Nagode sosai Allah ya bar kauna, in sha Allah idan na samu cikakkiyar nutsuwa zan dawo na cigaba da typing fiye,da yadda nake yi a yanzu* *Daga alƙalamin*✍️ Zainab Abdullahi KNT (Maman Ihsan) 09065327995 🤦‍♀️ *'YAR MAYE*🤦‍♀️ (_The drug abuser_) 6️⃣8️⃣ _ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH_ _INA GODIYA SOSAI DA KULAWAR DA NA SAMU DAGA WURIN WASU DAGA WAJENKU. TUN DAGA KAN MASU KIRA DA MASU TURO SAKO INA GODIYA, HAR WADANDA SUKA KIRA BA SU SAME NI BA, MAI JIKI DA SAUKI ALLAH YA BAR KAUNA_. Daga nan Munnir ya tada hankali akan sai an fito masa da Amatullah, dan ba zai bar wajen ba tare da ita ba. Securitys da ke gate ɗin ba su kula shi ba, suka share shi wanda ganin haka ya sa shi ya nufi gate ɗin gidan, ƙoƙarin buɗewa yake yi amma ya kasa. Suna kallonsa ba kula shi ba, dan gate ɗin gidan ba irin gamagarin gate ba ne da kowa zai iya buɗewa sai wanda ya san kan gate ɗin ne kadai zai iya buɗe wa. Ganin haka ne ya sa Sadik da abokinsa dake cikin mota fitowa, ƙarasawa suka yi wajen da Munnir yake inda abokinsa da ke garin wanda shi ne ya masu jagora zuwa gidan, wato Hashim ya ce. "Munnir gara fa ka bar wajen nan, dan ka ji abinda mai gidan ya faɗa, dan wallahi ba za su bari ka shiga cikin gidan nan ba sai tare da izininsa." Yana rufe baki ɗaya daga cikin security ɗin ya ce. "Ku shiga motarku yanzu ku bar wajen nan!" Ya yi maganar cikin kakkausar murya, inda Munnir ya dube shi da niyyar yin magana ne sai Sadik ya ja hannunsa suka bar wajen, wajen motarsa shuka ƙarasa, buɗe masa Hashim ya yi amma Munnir ya dage akan cewa ba zai shiga motar ba, dai an fito masa da Amatullah. "Da alama kana da taurin kai ko? To idan ba ka bar wajen nan ba yanzu sai na nuna maka kai ƙaramin ƙwaro ne." Securityn ya yi maganar yana nuna Munnir da yatsarsa manuniya. Munnir ya kalle shi tare da cewa. "Kai ka isa ka faɗa mani maganar banza, ka san waye ni kuwa? To ba zan tafi ba zan ga mai saka ni dole." Hashim ne ya yi ƙasa da murya yana yiwa Munnir magana. "Ka ga waɗan nan mutanen fa ba su da mutunci, yanzu sai su yarfa ka anan, kuma bakin aikinsu suke, ba za su taɓa bari ka shiga ba sai an basu dama, idan kuma har ka taya kafiya to ni zan bar ku a nan." Nan Munnir ya fara ɗaga murya yana zaginsu, wanda hakan ya sa securitys guda biyu ƙarasowa wajen a fusace, inda daya ya kai masa hannu da niyyar dukan sa sai Hashim ya yi saurin shiga tsakani yana cewa. "Sorry sir yanzu za mu tafi abin bai kai can ba." Nan Hashim da Sadik suka ba su hakuri inda suka ja Munnir ya shiga mota suka bar wajen. Duk abinda ke faruwa akan idanun Ajmal yake faruwa, dan tunda ya shiga bedroom ɗinsa yake kallonsu ta CCTV camera. A hanya kuwa Hashim dake driving ne ya kalli Munnir tare da cewa. "Ai bai kamata ka yi faɗa da su ba, wadannan mutanen masu zubin samudawar da sun sha training wallahi duka ɗaya idan suka maka sai ya ɗauke ka tsawon wanni kafin ka san cewa kana raye ne ko kana mace, da ba dan da na shiga tsakaninku na bashi haƙuri ba wallahi da yanzu Allah ne kaɗai ya san abun da zai biyo baya, dan kwanaki na ji labarin da aka ce ɗaya daga cikin security ɗin nan ya yi wa wani duka ɗaya da Ambulance aka kai shi asibiti. Ƙarfi ne da su, faɗa da su ba riba. Yanzu abu ɗaya za ka yi shi ne ka je ka ɗauko iyayen yarinyar nan ko wani daga danginta, amma idan ka zo ka ce kai saurayinta ne kuma an san ba ta da kowa a nan, wanda a haka wasu farsutarta suke yi , ba za su yarda da kai ba. Dai dai idan yarinyar ce ta gan ka ta ce eh kai ne ba" Haka zuciyarsa ke masa zafi ta ce in sha Allah zai je ya sanarwa iyayenta cewa ya samo inda take, sai su zo da kan su. Da wannan tunanin ya bar zancen. Inda suka nufi masauki da niyyar gobe su koma su inda suka fito. Ajmal kuwa bayan ya ga tafiyar su Munnir a cctv camera ne ya ta shi ya nufi bathroom dan yin wanka, amma zuciyarsa na wajen tunanin cewa idan da gaske ne mahaifin Amatullah ya masa alƙawarin ba shi aurenta to shi ya zai yi? Daga ƙarshe ya bar zancen da cewa 'yan adawa ne dama kwanakin baya an yi yunkurin ƙwace babyn a hannunta, sai Allah ya taimaka Ahmad ya ƙaraso akan lokaci, ga kuma na cikin gida da aka biya har ɗakinta. Haka ya dinga tunani ƙarshe dai ya bar zancen a cewar masu son ganin bayansa ne. Bayan ya yi wanka ne ya shirya cikin ƙananan kaya ya ya sauko zuwa downstairs. Daidai lokacin da Amatullah ta fito daga ɗakinta rungume da babynta ta zauna kan doguwar kujera mai zaman mutum uku. Wayarta da ta shiga facebook ne take dubawa. Ta ga Munnir ya yi accepting friend request da ta tura masa, shi bai san wace ce ba dan photon Baby ya gani a profile ɗin ta. Pictures ɗinsa take ta kallo yana tuna mata da iyayenta, saboda yadda yake yawan zuwa da yadda Abbanta ke son sa. Ajmal ya ƙaraso wajen ta bayanta ya tsaya, wayar ya zubawa idanu dan ganin me take kallo, photon Munnir da ya gani na ya saka shi jin wani iri a tare da shi. ' Kenan dama da gaske shi ne saurayin nata wanda wanda Abbanta ya yi alƙawarin aura masa? Kamar yadda ya faɗa masu a bakin gate, ga shi tana kallon photon sa ta yi zurfi a tunaninsa, kenan tana son sa? Amma ga shi na saka an kore shi, dole ne ma tunda bai zo da iyayenta ko wani nata ba bana da tabbacin ingancinsa da zan dauke Amatullah na damƙa masa, sai dai yanzu lokaci ya zo da zan je na damƙa ta a hannun iyayenta. Dan idan ya koma zai sanar da su inda take dole su biyo bayanta.' Ita kuma Amatullah duk da Idanunta na kan waya kamar yadda yake kallo Amma gabad'aya hankalinta na kan iyayenta ne su take tunani ba wai photon Munnir take kallo ba. Zagayowa ya yi ya zauna gefenta duk ba ta sani ba ta yi zurfi cikin tunanin da take yi. Hannunsa ya kai yana shafa kan Abdallah dake a saman cinyarta, sai a lokacin da ta ji kamar motsi ne da kalli Abdallah da sauri, sai ta yi tozali da hannun Ajmal dake shafa kan yaron, hannun ta zubawa idanu, tana kallon zara-zaran dogayen baƙin gashin da suke kwance luf a farar fatansa, gaba ɗaya Idanunta ya koma ga hannayen sa kasancewar rigar sanya saka gajeren hannu ne iya guiwar hannunsa, tun daga guiwar hannun nasa take kallo gashin da suka kwanta luf har zuwa ƙasan hannunsa, duk gashin ne zara-zaran yatsunsa da yake shafan kan Abdallah take kallo. Ɗauke Idanunta ta yi ta mayar kan fuskarsa sai ta ga yaron kawai yake kallo Amma fuskarsa ba walwala kamar akwai abinda ke damunsa, sanin ba tamabayarsa za ta yi ba kuma ba faɗa mata zai yi ba ya sa ta yi shiru ba ta ce komai ba. Wayarsa ce ta yi ƙara ya duba yana murmushi ya ɗauka, tare da sai ta fuskar wayar a fuskarsa. Daga fuskar wayarsa fuskar kakarsa ce ta bayyana, ita ce ta kira shi video call. Cikin harshen larabci suka fara magana inda take ce masa. "Assalamu alaikum" "Wa'alaiki salam, fatan kina cikin ƙoshin lafiya?" Ba ta amsa masa ba ta fara masa ƙorafin cewa tunda ya zo Nigeria wannan karon ya dade bai waiwayi can ƙasar Qatar ba. Wato ko ya manta da ita ne. Murmushi ya yi tare da cewa. "Ba haka ba ne tunda na dawo hankalina bai kwanta ba a wancan lokacin ne, yanzu kuma hankalina ya kwanta musamman idan na kalli Abdallah ina jin yaron har cikin zuciyata, ina son sa sosai tun ranar da na gane cewa ni ne ubansa, ba na son na yi nisa da shi ne duk inda nake hankalina yana kansa." Ya yi maganar yana Saita wayar yadda dukansu kakar za ta lalle su har Amatullah da Abdallah. Farin ciki ne ya lalluɓe Umman ji take ina ma ace mata da miji ne da d'an su a haka, ga shi sun dace da junansu sosai, murmushi ta yi tare da cewa. "Ina ma ace kai da ita miji da mata ne da na yi farin ciki sosai dan ta dace da kai, kai ma ka dace da ita. Sam Umman ba ta yi tunanin cewa Amatullah na jin larabci ba, dan haka sai ta juya harshen zuwa turanci inda take take cewa. "Barka da yamma ya kike?" Amatullah ta gaishe ta, bayan sun gama gaisawa ne ta juya yare zuwa larabci inda ta cigaba da cewa Ajamal. "Ya kamata ka aure ta cikin rufin asiri ku reni ɗan da Allah ya baki." Gajeren Murmushi ya yi tare da cewa "Tun kwanakin baya na yi tunanin haka har na mata magana amma sai ta nuna ba ta amince ba, sai dai har yanzu na kasa fahimtar cewa so na ne ba ta yi ko kuma saboda iyayenta sun yi alƙawarin bayar da ita ga wani ne." "Akwai wanda iyayenta suka yi wa alƙawarin aurenta ne?" Tsohuwar ta yi tamabayar cike da fargaba, dan Amatullah ta shiga ranta lokaci guda. "Eh haka ne dan yau wani ya zo na hana a bari ya shigo, dan ban yarda da shi ba, amma yanzu sai na ga tana kallon photon sa a waya hakan ya tabbatar mani da cewa ashe yana da gaskiya saurayinta ne." "Kuma mahaifinta ya masa alkawarin hada aurenta da shi ?" Jinjina kai ya yi tare da cewa "Haka dai ya faɗa." "Shin ita tana son shi ne?" "Wallahi ban sani ba, amma zan gano gaskiyar maganar. Sai dai lokaci ya kure Mani, dan ya kamata gobe ko jibi ta koma ga iyayenta, dama a cikin satin nan muka yi magana da Ammina kan cewa za mu mayar da ita, amma tunda an zo neman ta ya kamata muyi gaggawar kai ta." Shiru tsohuwar ta yi kafin ta ɗora da cewa. "Amma ina neman wata alfarma kafin ku kai ta gida ina son ka fara kawo ta na gani jikana kafin komawarta gida. Dan idan ta koma can be lallai na gani jikana nan kusa ba, saboda haka daga yanzu ka fara mata shirye-shiryen tafiya nan ƙasar." Bayan ta kashe kiran wayar ne ta kira Anni ta sanar da ita cewa zuwa jibi tana son ganin jikanta, idan sun kawo ta jibi suka yi kwana biyu sai su mai da ita zuwa ga iyayen ta. Ammi ta amince dan har da ita za su tafi dan ya kamata ta je ta bawa iyayen Amatullah haƙuri, idan sun tafi ƙasar Qatar ɗin su uku da Ammi da Ajmal sai Amatullah da babynta. Amatullah kuwa duk maganar da Ajmal ke yi da kakarsa tana jin su,kallonsa ta yi tare da cewa. "Munnir ne ya zo wajena a garin nan?" Ba tare da ya kalle ta ba ya ce. "Ban shi ba." "Na ji fa kana cewa wanda Babana zai aura mani ne ya zo yau?" "Dama kina jin larabci ne?" "Eh ana koya mana a islamiyya kuka ina yawan karanta littattafan koyon larabci Abbana ma yana Mani." "Bari na nuna maka photon sa ka gani ko shi ne." Ta yi magana tana duba wayarta, bai tsaya saurarenta ba ta bar wajen dan kishinta ne a cikin zuciyarsa, har zai haura upstairs ya juyo ya kallee ta ya ce. "Na san kin ji maganar da muka yi ki fara shiri jibi in sha Allah za mu tafi ƙasar Qatar kwana biyu zamu yi ki koma ga iyayenki." Murmushi ta yi dan ta ji daɗi har cikin ranta. Ɓangaren Munnir kuwa ana idar da sallar asuba suka kama hanya, Allah Allah yake su isa ya je ya sanarwa iyayen Amatullah zancen ya gano inda take. Ko da suka isa garin Minna bai zame ko ina ba sai kafar gidan su Amatullah. Duk yadda Sadik ya so ya bari ya huta sam bai bari ba. Bayan an masu iso ne suka shiga shi da Sadik inda yake basu labarin inda Amatullah take wato Kaduna. Umma ta yi farin cikin jin cewa an gano inda 'yarta tilo take. Abba ne ya kalli Munnir tare da cewa. "A wani wajen take ne a Kaduna." Munnir ya gyara zama tare da cewa. "Ai Abba idan ka ji sai ka yi mamaki,wai gidan shi wanda ya mata cikin ne take zaune a gidansa duk tsawon wannan lokaci. Ta ya ya daga ita sai shi, sannan ba mijinta ba sannan ba muharramin ta ba ta tare da gidansa da hankalinta da tunaninta zaman me take yi a gidansa, sannan na je na ce masa ni ne Wanda zai aure ta amma mutumin nan ya sa masu gadin gidansa suka kore ni?" Tunda Munnir yake magana jikin Umma ya yi sanyi Abba ransa ya gama ɓaci ya fara tunanin Amatullah ba ta shiryu ba, ba amfanin su dinga tunaninta da damuwa da ita, su cire ta kawai shi ya fi sauƙi. 🤦‍♀️ *'YAR MAYE*🤦‍♀️ (_The drog abuser_) 6️⃣9️⃣ Tunda Munnir yake magana jikin Umma ya yi sanyi Abba da ransa ya gama b'aci ya fara tunanin Amatullah ba ta shiryu ba, ba amfanin su dinga tunaninta da damuwa da ita, su cire ta kawai shi ya fi sauki. Sadik dake zaune gefen Munnir ne ya lura da yanayin iyayen Amatullah, dan haka sai ya d'an tokari Munnir alamar ya isa haka Nan, shi Kuma Munnir ya cigaba da maganar da yake yi, Wanda ganin haka ya sa Sadik saurin cewa. "Am yanxu maganar ta isa haka nan, yanzu Alhamdulillah tunda har mun San inda take komai mai sauki ne." Abba ne ya Kalli Sadik ya ce. "Ba amfanin zuwa inda take tunda har ba ta San ta waiwayi gida ba, domin yadda ta iya zuwa ta tare a gidansa a matsayin wace ce, matarsa, k'anwarsa, ko 'yarsa?" "Abba ka da ka kawo wannan tunanin a zuciyarka, domin kuwa, ba a yadda na ji labarin cewa korar ta ka yi ta tafi, ina ganin yanzu tsoro da fargaban sake dawowa take yi, saboda ba ta San me zai je ya dawo ba, amma na tabbatar da ta San cewa Kun yafe mata da da dawo. Yanzu tunda shi Wanda take zaune a gidansa ya hana a ganta na tabbatar idan Ku ne da kanku Kun ka je bai ida ya hana Ku ganin 'yarku ba." Umma ce ta yi saurin cewa cewa. "Ni ma tunanin da na yi kenan, Amatullah tawa ba za ta tare a gidan saurayi daga shi sai ita haka kawai ba, ak..." Kafin ta karasa maganar da za ta yi ne sai Abba ya dakatar da ita ta hanyar cewa. "Dama ke baki ganin laifinta duk abunda ta yi kokarin kare ta kike yi." Goge hawayen fuskarta ta yi tare da cewa. "Ba haka ba ne Abban Amatullah, ni dai dan Allah ka je ka dawo mani da ita gida, za mu je komai daga bakinta." Shiru ne ya biyo baya, ba Wanda ya sake yin magana, kafin Abba ya Kalli Munnir ya ce. "Zuwa jibi sai mu tafi can garin da take , tunda ka San gida ko?" Jinjina kai ya yi tare da cewa "In Sha Allah Abba." Umma ce ta tari numfashin Abba ta hanyar cewa. "Jibi ya yi nisa Mallam ka bari zuwa gobe in Sha Allah sai Ku tafi." "Kada ki damu da yau da gobe duk d'aya ne a wajen Allah." Shiru kawai ta yi b don ranta yana so ba, sai fai kawai ta ce masa. "Allah ya kai mu jibin rai da lafiya." Suka amsa da ameen. Daga nan Munnir suka masu sallama da niyyar jibi da asuba za su zo su d'auke Abba. Daga haka suka yi sallama, suka tafi daga gidan. Kamar yadda Amatullah ta rok'i Ajmal akan cewa ya sa a saki Hafsat haka aka yi, dan Ajmal ya sa an sake Hafsat daga oafishin 'yan sanda. Wanda daga baya Kuma Ajmal ya yi wani tunani, inda aka saki Hafsat to ina makomar indakud'inka. Dan shi Hafsat ce ta saka shi yin aiki, ita ya yiwa aiki, dan umarninta ya bi. Dan haka Ajmal ma ya saka aka saki INDAKUD'INKA. Washegari duk wani shirye-shiryen tafiya kasar Qaatar an kammmala wa Amatullah. Zuciyarata fari tas, ba komai ne ya saka ta farin ciki ba sai komawa da za ta yi gida, Dan ko ba komai idan ya kadance ga ta ga Ummanta ma kadai ya ishe ta farin ciki. Ana gobe za ta tafi ne ta kira Saliha da Madina ta sanar da su, sun taya ta murnar komawa ta ga iyayen ta, inda suka ce za su zo suyi mata lalle da kitso. Duk waninar da ake toyawa Nasreen ba ta sani ba, ba ta San komai game da shirin tafiyar ta su ba,sai da Affan ya tafi d'akin Dadynsa wato Ajmal, ya fito sannan ya shiga d'akin Nasreen. Tana zaune ta yi tagumi, tana tunanin maganganun da kawarta Fareeda take yawan fad'a mata, kan cewa ta cire wannan kishin na hauka da jahilci dake damunta, ta rungumi mijinta ko hankalinsa ya karkato kanta. Tana tsaka da da wannan tunanin ne sai Affan ya shigo d'akin nata a guje, jikinta ya fad'a yana cewa. "Mom wai Dady je yi tafiya da Ammi." Shafa kansa ta yi tare da cewa. "To Affan." Sai Jin muryarsa ta yi yana cewa. "Da Anci Amatuiya je je." Gabanta ne ya yi muguwar fad'uwa Jin wai har da Amatullah zai yi tafiyar. A zabure ta mik'e tare da cire Affan daga jikinta ta fara magana cikin tashin hankali. "Affan waye ya fad'a maka cewa da Amatullah za su ya yi tafiyar?" "Dady." Yaron ya fad'a yana kallon Mum d'insa. Waya ta d'auka tana lalubo lambar Fareeda, cikin tashin hankali har ifanunta sun fito waje. Bata d'auka ba har wayar ya katse, sai da ta sake kira ne sannan ta d'auka, tana Jin an d'auka ta saka kuka, Fareeda na Jin kukan Nasreen ta yi murmushin takaici, tare da cewa. ",Ai idan dai har ba canzawa kika yi ba kuka yanzu kika fara yin sa." "Dakatawa da kukan ta yi tare da cewa. "Au haka ma za ki fad'a?" "Eh mana tunda ba ki Jin shawara. Yanzu me kuma ya faru?" "Wai fa Ajmal ne za su hi tafiya shi da Ammi da Wannan yarinyar." Shiru Fareeda ta yi tare da cewa "Wace yarinyar?" "Amatullah take ko wace ce?" "Okay na gane me kika cewa, yanzu ina zasu tafi da ita, Kuma me zasu je yi?" "Ina zan Sani Fareeda, Affan ne ya shigo yake sanar mani." ",Ajmal bai fad'a maki ba?" Fareeda ta yi tambayar tana jiran amsar daga bakin Nasreen. "Ba abunda ya fad'a mani, ke ni fa wallahi kwana biyi kenan ban yi maganar kirki da shi ba." "Ke yanzu ba ki ji kunyar fafar haka ba, kina tare da miji baki San yadda za ki kula da shi ba, ba ki San yadda za ki ka hankalinsa ba zuwa gare ki ba, ta ya ya hankalinsa ba zai karkata zuwa ga wata macen ba.?" "Ni dai ba wannan ba shawara za ki bani, akan tafiyar da za su yi." ",Ki fara binciko ina zasu je da Kuma me zasu je yi sai na sanar da ke yadda za ki yi ki magance matsalarki." Yamutse fuska ta yi tare da cewa. "Ta ya ya zan gane bayan ba shiri muke ba?" "Ke banza idan Zaki ajiye girman kai da wannan Jan ajin naki da ba zai kare ki da komai ba ki ajiye, ki je ki yi masa sallama ki gaishe shi, cikin nutsuwa da gairmamawa ki watsar da makaman ki na San bai da matsala zai sanar da ke zai yi tafiya ba sai kin tambaye shi ba, idan Kuma kika nuna cewa saboda zai yi tafiya da yarinyar nan ne kika shigo ki tambaye shi to nan ma ba Zaki samu cikakkiuar amsar da kike so ba." Nan dai ta cigaba da ba ta shawarwari sannan ta katse Kiran wayar. Kallon agogo ta yi ta ga karfre goma da rabi na safiya, ballantana weekend baya fita da wuri, ta San yana kwance yana barci. Dan haka ta shiga bathroom tayi wanka. Man shafawarta ta shafa sai powder da turare ta feshe jikinta da su sun fi kala uku. Doguwar Riga ta material k'ananan kaya riga da siket ta saka, siket d'in iya guiwarta ta tasaya. Kallon Affan ta yi ta ce masa ya je wajan Larai kula da shi ta yi masa wanka da ta bashi breakfast d'insa . Yana fita ita ma ta nufi d'akin Ajmal, tura k'ofar ta yi can ta hango shi kwance Saman makeken gadonsa, ya lullub'e da lallusan bargo. Ba abunda ke tashi a d'akin sai sanyin ac da k'amshin room freshener. Da alama ya koma barci, Dan haka sai ta k'arasa wa ta yi gaban gadon, ganin idanusa a lumshe yana barci kamar ta juya ta fita sai ta tuna shawara da Fareeda ta ba ta, dan haka ta tsaya tana nazari, sannan ta maida dubanta zuwa ga kyakkyawar fusakarsa, da idan yana barci ma wani k'ara kyau yake yi. Haurawa ta yi Saman gadon nasa tare da Jan bargo ta shige ciki ta rufe jikinta kamar yadda shima ya rufe. Yana Jin ta tun shigowarta d'akin har zuwa haurawa da ta yi Saman gadon. Yana Jin ta amma sai ya share kamar yana barci, yana mamakin me ya shigo da ita d'akinsa a zuciyarsa, dan in ya san ba ta shigowa sai da dalili. Fusakarsa ta zubawa idanu sannan ta kwantar kanta Saman fad'ad'd'an kirjinsa sannan ta rungume shi. Zuwa lokacin ta San yana Jin ta share ta yi amma sai ta d'aga kai ta kalle shi sai ta ga shima ita yake Kallo. Daidai lokacin wayarsa take ruri, ya kai hannu zai d'auka kenan sai Nasreen ta riga shi d'aukar wayar ganin haka ya ya mai da hannunsa ya kau da kai duk da cewar bai San wa ke Kiran wayar ba, ta lura kamar yana fushi da ita ne. Wayar fake ruri ta duba ta ga Amatullah ke Kiran wayar, take sai zuciyarta ta fara tafasa. Kallonsa ta yi ta ga ya kau da kai da sai ta yi saurin d'aukar wayar ta kara a kunnenta. Amatullah dake zaune sanye da hijabi Abdallah na rungume a hannunta waya na kare a kunnenta. Jin an d'aga wayar ne ya saka Amatullah cewa. "Assalamu alaikum ina kwana Baban Affan." "To mayya bai tashi daga barci ba." Jin muryar Nasreen ne ya saka Amatullah fad'uwar gaba, cikin sanyin murya ya ce. "Ki yi hak'uri Mom Affan ban sani ba ne." Tsuki ta yi tare da katse Kiran wayar. Kallonta ya yi tare da cewa akan me za ki amsa wayata,ko ba na nan ka da ki sake d'aukar wayata ballantana ina nan." Murmushin ta k'ak'aro tare da cewa "Am sorry" Daga nan ta sake rungume shi ta kwanta a jikinsa, tana shafar gashin kansa har zuwa

Chapter 28 of 51